Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

breast, suna mata zafi wasu lokutan, sedai ta kasa ganewa, is it the normal stage of puberty, ko kuma wata matsala ce daban, dan tana jin ana wayar da kai akan breast cancer, dan recently anyi taro a makarantar, na wayarwa da mata kai, akan ciwon sanƙaran mama, amma ita ta kasa gane a wani hali take? Gashi ba yadda za'ai taiwa Ummanta zancen, gashi ba wanda za ta iya gayawa damuwarta, a yanzu haka duk da ta na kwana guri ɗaya da Ummanta ta tashi, amma Babu wanda take da kusanci da shi a yanzu kamar Sadik, sedai shima ɗin Maganar tayi matuƙar nauyin da ba zata iya tambayarsa ba.

"Lafiya naga kin yi shiru kina kallona? What's wrong ki gayamin please"

Ajiyar zuciya tayi, cikin sassanyar muryarta tace "bakomai fa"

Ya kwaikwayeta yace "ban yadda ba gaskiya"

Hakan ya bata dariya da seda tai murmushi, yace "oya gayamin ina jinki"

"Dagaske nake bakomai, bacci nake ji ne"

'ba kya bacci sosai ne a gida?"

"Eh ina yin karatu da daddare"

"Wow that's very good ai, amma ki dinga rangwantawa kanki kinji Hubby na, bikin yaya na ya kusa, za'ayi events da aka shirya a gidan mu, amma akwai party da zan organising, so akwai kalar outpit ɗin da za'a saka, ayi order dake zaki saka?"

"A'a baza'a barni ba a gidanmu"

"Ok ba damuwa, nasan dama ba lallai a barki b, but I just decided to tell you ne, amma dai ko sau ɗaya zaki zo ko?"

"Eh Insha Allah"

"Yawwa my wife"

Sunkuyar da kai tayi ƙasa, dama yasan hakan ne ze faru, dan wannan kalaman nasa nauyi suke mata.

"Farhan" ya kira sunan ta.

"Na'am" ta amsa.

"Next week zan karɓo exams card ɗina, na kusa Barin makarantar nan Insha Allah"

Ai da sauri ta ɗago ta kalli Sadik tace "dan Allah dagaske ka ke?"

"Am serious, zanyi Waec ne in kammala karatuna akan lokaci"

Take jikin Farhan yai wani irin sanyi, ta kasa cewa uffan se dai damuwa ta bayyana ƙarara ta mamaye fuskarta.

"Farhan" ya kira sunanta.

A sanyaye ta kalle shi, yace "kin san meyasa nai haka? Duk cikin planing ɗina ne na in mallake ki, dan Allah Farhan kar ki kalli hakan da wata fuska daban, i really love you wlh, duk saboda nake wannan fighting ɗin, kimin addu'a samun nasara, bari in tafi aji kar Wannan jarababben mutumin yazo yai min masifa"

Ya tashi ya kalleta yace "I love You baby" ya kashe mata ido ɗaya ya juya ya fita.

Ai yana fita ta bawa hawayen da take ta kokawa da su damar zubowa, ta kifa kanta kawai ta fara kuka ƙasa ƙasa.

"Yanzu idan Prince ya dena zuwa Makarantar nan ya za tayi, a duk ranar da ba ta ganshi ba, tana shiga mummunar damuwa, se gashi ze bar makarantar gaba ɗaya, nan hawaye suka cigaba da zarya a kuncinta, ta sa hanky tana gogewa, tun a lokacin taji ta fara kewar masoyin nata, take ta manta da damuwar ta ta farko dake damunta.

Shi kansa Sadik tunda ya gaya mata yaga damuwa a fuskarsa, ya shiga damuwa shima, take yaji wani irin tausayinta ya kamashi sosai, shikansa ya san zeyi missing ɗinta, sedai barinsa makarantar ba yana nufin ya bar Farhan ba, akwai yiwuwar ya fara neman Hanyar cinma burinsa, na aurar wadda yake so a Wannan shekarun.

"Idan ka aureta Yanzu tata rayuwar fa? Karatun ta fa?" Wata zuciyar ta tambayeshi.

'ta ƙarasa a gidana' ya bawa kansa amsa.

Da gudu ta sheƙo ta kan varrender, tana ƙoƙarin ƙarasawa ajinsu "Lilly! Lilly" tsayawa Lilly tayi tana kallon Sir Nazir dake ta ƙwala mata kira kamar mafarauci.

"Why are you running like this? Where is your jacket?"

Ta kalli jikinta daga ita se inner shirt, da skirt ɗin ta iya gwiwa, ta cire jacket ɗin ta ajiye a aji, ta kalleshi tace "tana aji"

"Meyasa kike yawo a haka? Baki san kin fara girma ba, kuma kina gudu a cikin yara haka? Ga hijjabin ki ƙarami, Why are you exhibiting childish behavior, don't you know you are at your Adolescents period, you have to maintain your body?"

A ranta tace "ji ɗan iska, seka gayamin a Adolescents period nake, ai nima na sani"

Ta tura baki cike da sangarta.

Yace "idan na kuma ganin kin kuma cire jacket ɗinki kina gudu haka, sena zane ki, wuce ki ban guri"

Tafiya tayi tana yatsuna fuska.

Tana zuwa Ajinsu tace "hmm ƙawayen amana kun san abunda ya faru kuwa?"

Haseena tace "ya za'ai mu sani se kin faɗa"

Lilly tace "mhmm wannan sir Nazir ɗin ne na taho da gudu ya wani tsaida ni, wai meyasa nake yawo ba jacket nake gudu, wai ban san na fara girma bane na shiga Adolescents period, kuji min ɗan air mutum"

Shewa suka yi Haseena tace "Ya ƙyasa ne yaseen, shine ya gaza shiruu seda ya tanka, ya tsaida ke ne kawai dan kawai ya sake kalla sosai"

Ihu suka saka gaba ɗaya, tai wani juya tai girgiza tace "gani ba taɓawa ba asarar ido, nan gani nam bari ɗumamen mayya, kuma wallahi yawo ba jacket yanzu na fara, ke ni fa na kusa dena saka wannan ɗan hijjabin ma, haka zan dinga yawo, mutum ya kalla ko kuma ya runtse idonsa"

Yasmin tace "to Allah ya temake ka abubuwa sun fara fitowa ace ba zakai gayu da abunka ba, wani abun ma se munje Final year lokacin sun gama fitowa, lokacin ne zega yadda ake abu, yadda zamu addabi makarantar nan, ai ya gani ya kasa shiru shine ya tanka miki, sun tsole masa ido"

Lilly tace "aikuwa in hakane ya shiga tara mutumin nan, dan sena ganshi ma zan dinga kasawa da gud"

Yasmin tace "ai base kinyi gudu ba, kya yiwa kan ki ɓarna ai, kina tafe kina ɗan bada style ma ya isa, ban gaya muku ba ma, na fa samo mana littafin nan, ku kunji abubuwa a ciki kuwa"

Haseena tace "dan Allah dagaske ko da wasa?"

"Wallahi dagaske nake, ke kunga yadda aka fayyace komai ban dai karanta ba, page ɗaya kawai na karanta, amma naji sena zo da wayata mu karanta tare, kai akwai tafasassun abubuwa a littafin nan"

Lilly tace "shegiyar kaya, ai a kawo mana littafin nan, muji abubuwa kawai"

Su kaita shewa, ita kam sam Farhan hankalinta baya kansu, hankalinta kacokan yana kan maganar da sukayi da Prince ɗinta.

Shikansa Prince har aka tashi jikinsa a sanyaye yake, yaje ƙofar makarantar ya tsaya yana jiran fitowar Farhan.

Aikuwa ya hangota ta fito daga cikin makarantar, idanunta sunyi jawur sosai, tana tafiya a hankali, daga inda yake tsaye yake kallonta, kullum ƙara girma take tana kyau abunta, sheɗan ne ya fara ƙawata masa ita, da ɗarsuwar wani abu daban a ransa, take yace "Subhanallah" ya dawo hayyacinsa.

Tana ɗaga ido sukai ido huɗu da shi, murmushin dole tai masa, yace "ke muke jira taho mu tafi gida"

"A'a zan tafi ai"

"Bana son gaddama fa"

Ba yadda ta iya haka ta bishi ta shiga motar, suna tafiya yace "Anya ba kuka ki kai ba, naga idonki ya ƙara ja"

"Ba kuka nai ba, dama ina ciwon ido wani lokacin"

"Ciwon ido, lallai ma ashe makauniya ce matar tawa, gaskiya sena rage sadakin da zan bayar" yai maganar yana murmushi.

Direba ko a ransa yace 'ikon Allah, ji wani kwaɗo da fitsara wai ita game saurayi ta shiga motarsa yana mata kalaman banza na RUƊIN ƘURUCIYA, banda haka ina Sadik ina wata budurwa dan kawai yana ganin ya na da tsawon ƙafa!?"

Seda suka kai Farhan gida sannan suka wuce gida, babban abunda yaiwa Sadii daɗi be wuce yadda yau gidansu ba mutane ba, hakan yai masa daɗi sosai.

A ƙofar shiga BQ ɗin su ya haɗu da Dr. Ya kalleshi yace "Sadii yau kamar ba ka dawo da wuri ba, ina ka tsaya ne?"

Sadik yace "mun sauke Farhan a gida ne, sannan muka taho?"

"Wace kuma Farhan?"

"My wife to be insha Allah" Sadik ya faɗa kansa tsaye.

Usman yace "kasan me kace kuwa?"

"Eh mana na sani, budurwata ce da nake burin Aure, kuma insha Allah daga bikinka se nawa"

Usman ya jinjina kai yace "ba laifin ka bane, tashen balaga ne da RUƊIN ƘURUCIYA, ke ɗibar ka"

Sadik yace "tashen balaga kuma? Oho koma dai menene, I mean what I say wallahi"

Yana gama maganar ya wuce Usman, ya shige.

Usman ya bishi da kallo, kawai ya girgiza kai, ya juya ya nufi in da motocin gidan suke.

Sadik yai wanka yai salla, ya tafi ganin Mummynsa, sedai yana zuwa ya tarar ba ta nan wai ta fita.

Haushi ne ya kama shi ya shiga Kitchen, ya tarar Khairat na dafa indomie, tana yi tana bin wata waƙa da ke tashi a wayarta.

"Ss ke 'yar bainu" yai maganar da sigar tsokana.

Waiwayowa tai ta kalli Sadik, tace "ka ga karka kuma cemin 'yar bainu"

Yai murmushin yace "ke dallacan uwar fushi, ina Mother ta tafi ne?"

"Nima ban sani ba, da Mummy ta ɗakkoni daga makaranta tazo ta ajiyeni suka fita tare"

"To dafa indomie da ni, tunda Mother ba ta nan"

"Baza'a dafa ɗin ba, 'yar bainu ta dafa maka"

Dariya yayi yace "ke akwai zazzafan party da bikin dr. Fa, zamu shirya na 'yan school ɗin mu, kema za'a baki Card in da wanda zaki gayyata"

Tsalle tai tace "wow, dole muje ai, kai za'a cashe fa Prince"

"Ke dalla can, har wata rawa kika iya?"

"Taɓ kaji ka, wace kalar rawa ce ban iya ba? Wallahi na iya rawa"

Sadik yace "To yi mu gani, kuma in baki iya ba ba inda zaki"

Yai maganar yana ciro wayar a aljihunsa, ya duba wayar ya saka mata waƙa, take Khairat ta fara rawa tana juyi, tana karairaya jikinta.

Tafi ya fara yi mata yace "ba ƙarya kin iya, zaki je gurin partyn nan, let me join you"

Nam suka shiga rawa shida Khairat a Kitchen, ya riƙe hannun Khairat yaana juaya ta suna rawa tare, kamar yaran turawa.

"Lalalala! Innalillahi taɓɗijan, dama abunda kuke yi kenan? To wallahi sena gayawa Inna kuna abunda be dace ba, kuna taɓa juna bayan tace ba kyau.





Ayshercool
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

     

                              13-14







A tare Khairat da Sadik suka juyo suna kallon Nana, dake tsaye tana musu kallon banza.

Khairat tace "is this girl serious?"

Sadik yace "A beg forget about her, she's mentally abnormal"

"Nima na gani"

Cikin tsiwa Nana tace "Wallahi Inna ta hana, tace babu kyau, kwata kwata babu kyau irin wannan abun, amma kai kuma kazo kana taɓata, tace marasa tarbiyya ne suke haka, kuma Allah ze fushi da mutum, Allah ya hana amma ka ke aikatawa, wallahi se na gaya mata"

"Dan ubanki tsayuwar  me kike a gurin baki tafi gayamatan ba? Kifi ruwa gudu banza da baki kamar mazirari"

"Kaine banza bani ba wallahi"

Ta juya ta tafi ɗakinsu da sauri dan ta sanar da Inna.

"Innarmu, Inna" ta shiga ƙwalawa Innan kira.

Inna tace "Ya akayi meye kike kirana haka?"

Se kuma Nana tayi saroro ta kasa Magana, kawai ta basar tace "kawai nemanki nake"

"Dan kina nemana seki biyoni da wannan kiran Kamar wata sa'arki?"

"To yi haƙuri"

"Naƙi haƙurin"

Nana ta ɗan sosa kai, ta nemi guri ta zauna.


A yanzu Kusan duk lokacin da Sadik ze shiga gida ya haɗu da Inna, se tai masa faɗan wani abun, kodai na sumar kansa, ko rashin son mutane, ko kuma taɓara, saboda haka yana dawo wa daga makaranta, yake ficewa yawon sa baze dawo ba se dare, se ya tabbatar da Inna tai bacci, se ya shigo ya ɗau Abincin sa ya fice ya bar falon, in ma Mother ze gani ya ganta a lokacin.

Wasu lokutan da ya fara ɓuruntu ze ɗau Abinci Nana ke farkawa daga bacci, ta fuskanci baya shigowa se kowa yai bacci, dan haka ta sa ido sosai ta lura be zo ɗaukar abinci da wuri ba, dan haka ta gane se daren ze zo ya ɗauka.

Har sun kwanta bacci, Nana ta daidaici Inna tai bacci, ta miƙe cikin sanɗa ta fito falon, ta janyo ƙofar falon ta rufe, ta kulle da mukulli ta ciki, ta nemi guri ta kunna TV tai zamanta tana kallon cartoon.

Wajen sha ɗaya da rabi na dare, Sadik yazo yana murɗa ƙofa ze shigo dan ya ɗau Abinci, amma yaji a rufe gam.

Ya jinjina ƙofar yaji ta a kulle, nan ya shiga ƙwanƙwasawa, nan ma ba wani respond.

Yayi mamakin yadda aka rufe ƙofar falon haka, dan ba'a cika rufeta ba, ko da yaushe tana buɗe, saboda ita ce babbar ƙofar da zata sada ka da kowane sashi na cikin gidan, amma abun mamaki yau an rufeta.

Ya zaga ya ɗaga labulen window, yaga koda wani a falon, ya hango hijjabin ta akan 2 seater, yana ganin hijjabin yasan itace, saboda kullum haka take yawo cikin hijjabin nan kamar me takaba, be taɓa ganin ta cire shi ba, kullum da hijjabi take yawo.

"Ke malama zo ki buɗe min ƙofar nan"

Banza tai dashi taƙi ko waigo wa balle ta kalleshi.

"Wai ba magana nake miki bane?"

"Ka nemi ke ta zo ta buɗe maka" ta bashi amsa

"Dalla ki buɗe zan ɗau Abinci"

Tasowa Nana tai, ta nufi inda yake tsaye a window tace "ba za'a ɗakko ba ɗin, idan kana son cin Abincin ka dinga zuwa da wuri kana ɗauka, base ka gama gantalin ka ba sannan kazo kana ɓuruntu kamar ɓera ka tasheni daga bacci ba"

Buɗe baki yai yana mamaki yace "tunda gidan ubanki ne ai dole ki samun doka"

"Ai dama bance Gidan babana bane, gidan babana yana ƙuaye ya mutu, ya barni a gidan Hakimi"

"Ke bana son iskanci, dalla ki buɗemin"

"Wallahi ba zan buɗe ba taimako ɗaya zan iya yi maka"

Ta juya ta nufi dining, ta ɗakko ragowar bredin safe, taje kitchen ta buɗe fridge ta ɗakko ruwan sanyi, Sadik ya zuba mata ido yaga me za tayi.

Ba kunya taje ta zura masa bredi da satchet water tace "ga shi nan, amma kar ka sake zuwa ka damemu"

Galala yabi bredin da kallo da tsananin baƙin ciki da takaici, Nana kuma ta kashe fitilar falon tai tafiyarta.

Ji yai tamkar ya karya ƙofar ya shaƙe Nana, yai mata dukan da seta kasa motsi.

Cike da ɓacin rai ya koma BQ, ya tarar dr. Na zaune yana waya, se wani kashe murya yake cike da tsantsar shauƙi da Soyayya.

Sadik ya kalleshi ya ɗanyi guntun tsaki, ya wuce ya duba fridge ya samo cake, da lemo ya koma ya zauna akan 3seater, yana tura cake ɗin nan kamar ze fashe da kuka.

Gefe guda kuma Usaman na sake ƙular da shi, yadda ya nannaɗe murya yana zuba taɓara a waya, duk haushi ya cika shi, se tsaki yake yana hararar Usman, wanda be san me Sadik ɗin yake ba.

"Jeddaty, kamar in janyo Ranar Auren nan haka nake ji, zuciya ta ta kasa nutsuwa da samun sukuni, am about to loose control fa"

"Na fika ƙaguwa Nurain, sedai kayi haƙuri mu jira lokaci, kamar yaune zaka ga yazo, duk abu in dai an sama sa lokaci yanzu zaka ga yazo"

"Hakane Baby na, are you not sleepy?"

"No am not, when am with you, i keep everything aside, kai kaɗai zuciyar take kallo"

"Hmm Beb, yakamata ki kwanta dare ya fara yi fa, But are you on bed?"

"Yeah"

"Are you sure?"

"Quite sure Dear"

"So how do you dressed up, for today's night"

"I just wear my night gound"

"Ok am going to my room now, let me have a 1picture of you with the night dress, so that I can sleep well"

"Ohhk my Baby, as you wish"

Duk wannan wayar da Usman yake a gaban Sadik yake yin ta ba kunya ba Komai, Sadik ya dinga binsa da kallo, harya ta shi ya bar falon gaba ɗaya.

Ji yai ya dena jin ɗanɗanon cake ɗin, dama cin da yake na dole ne, ya miƙe shima ya koma ɗakinsa, ya nemi guri ya kwanta, sedai ya shiga tunani me zurfi, da kwaɗaituwar son yaga hoton da za'a turawa Usman ɗin.

Ina ma Farhan na da waya, da ko ba komai idan yaji muryarta ze ji daɗi a ransa, amma dai yasan ko kusa Farhan ba zata turo masa hotonta a kayan bacci ba, duk da ba mace a gidansu, amma yasan kayan Bacci na mata ba wasu kayan Kirki bane suke sawa, dan mafi akasari kayan baccin yana bayyanar da wani sashi na jikin su ne.

Take zuciyarsa ta cigaba da azalzalar sa, da ƙawata masa abubuwa daban daban, mussaman Farhan ɗin sa, ina ma ko sau ɗaya shima yaga hoton ta a night gound, ko yaya yana son ganin wani sashi na jikinta, a cikin kyakykyawar fatarta me ɗaukar ido.

Rumtse idonsa yai sosai yana sauke ajiyar zuciya, a hankali ya furta Farhan, yai ruf da ciki ya rirriƙe pillow ɗin da yake kai, a hankali ya dinga faɗin "Subhanallahi wabi hamdihi, subhanallahil azeem"

A haka bacci yai awon gaba da shi, sedai kasancewar ya saka abun a ransa, se ga Farhan a cikin baccin sa, a yanayi me wuyar fassara.

Yadda ya kwanta da wannan matsanancin tunanin, haka ya dinga mafarkai barkatai har Asuba, kiran farko ya buɗe idon sa, ya jiƙe sharkaf da gumi, duk da A.C da ke ɗakin nasa.

Tashi yai yayi shiru yana tunanin mafarkin da yai, jinsa yai somehow abnormal.

Tunani ya shiga yi yanzu se yayi wanka kenan? Amma ai mafarki ne kawai, shiru ya kuma yi yana tunani, ya ɗakko wayarsa ya shiga yai searching, tabbas wanka ya kama shi since he has a dreams.

Tsaki ya ɗanyi, ya sakko daga kan gadon, a gurguje ya shiga banɗaki yai wanka yai alawala, ya fito ya zura rigarsa, sedai yana gamawa sega Faruk ya shigo ɗakin nasa, ya kalli Sadik yace "Au ashe ka tashi? Sarkin nauyin bacci, yau anyi abun arziki, dama Daddy ne yayo waya, amma ya nake ganin kanka kamar a jiƙe?"

Tsaki Sadik yai yace "Alwala nayi fa"

"Alwalar ce ka ke a jiƙe haka, kalli jallabiyar taka fa duk ruwa"

Banza Sadik yai masa, ya ɗau turare ya fesa a jikinsa, ya saka hullar tashi ka fiye naci.

Faruk ya kwashe da dariya yace "inyee, Su Auta an girma, iyee sekace wani magidanci wanka da Asuba haka, Lallai ka girma ka isa Aure, na yarda da batunka na cewa da kake ka isa Aure"

Haɗe rai Sadik yai yaƙi cewa uffan, a falo suka haɗu da Usman shima ya fito, suka fito suka tafi masallaci, sedai suna tafe Faruk yana tsokanar Sadik, Sadik ya ƙulu matuƙar ƙulewa, amma yaƙi cewa komai dan kar Daddy ya fuskanci wani abu.

Da suka dawo daga sallar ma Sadik be koma bacci ba, ya nemi guri ya zauna yana ta tunani kala kala daban daban a zuciyar sa.

Haka ya zauna har gari yai haske, ya shirya ya fice dan tafiya makaranta, ba tare da ya shiga ko cikin gidan ba balle ya karya yai musu sallama, direbansa ya fara jan motar kenan ya hango Nana ta fito, se yanzu ya tuna abunda tai masa daren jiya, tabbas ba dan ya riga ya shiga mota ba da Allah kaɗai ze iya raba shi da ita yau, se kuma ya tuna yana taɓata ze sha tujara a gurin kakarsa, kuma Daddy ma ze masa faɗa, ƙwafa yayi dan ko me za'ai sedai ayi amma se yai maganin ta.

Haka ya tafi makaranta yana ƙananun sambatu.

Farhan ta shirya tsaf cikin Uniform ɗinta, sedai a jikinta tana jin tana ƙara ƙiba, dan skirt ɗin da ta sa tana jin yadda ya matse ta sosai, ta juya ta juya ta ƙarewa kanta kallo a madubi, ji take kamar ta cire shi ta canza wani, amma ɗaya skirt ɗin ba a goge yake va gashi ta makara sosai.

Ta ɗakko ƙaton hijjabin ta ta ɗora akan Uniform ɗin sannan ta fito tsakar gida, ta kalli Ummanta da ke kaiwa tana komowa a tsakar gida tace "Umma na tafi"

Ba ta kalli in da Farhan take ba tace "Allah ya kiyaye" cikin yanayin sanyin halin ta, ta wuce ɗakin mahaifinta, se da tai sallama akai mata izinin shiga sannan ta shiga.

Tace "Abba ina kwana"

"Lafiya ƙalau Farhan, za'a tafi makarantar ne?"

"Eh Abba zan tafi"

Ya saka hannu a aljihunsa ya ɗakko Naira ɗari ya bata yace "ga kuɗin makarantar ki, Allah ya tsare kin karya dai ko?"

"Eh Abba na karya"

"To shikenan, Allah ya kiyaye hanya, ki kula da kanki ki kula da addinin ki da mutuncinki kinji Farhan"

"To Abba insha Allah, nagode Sosai"

Ta miƙe ta fito, a soro ta tsaya ta buɗe jakarta ta ɗakko turaren da ta siya da kuɗin da Sadik ya bata, ta shashshafa a jikinta, dan tana matuƙar son ƙamshi a rayuwarta, sedai ummanta bata damu da ta ɗorata a hanya da yadda zatai amfani da kayan gyaran jiki ba, ko da yake yaushe ma ta kulata balle ta koya mata wani abu makamancin haka.

Ta gama shafawa ta maida shi jakarta, sannan ta fita ta nufi titi.

Gaba ɗaya Sadik yau kamar mara lafiya haka yake jinsa, yama rasa gaba ɗaya meke masa daɗi, duk yadda abokansa suka so jansa da surutu amma yaƙi magana, ƙyaleshi su kai, dan sun san haka yake yi wasu lokutan.

Ana ta shirye shiryen fara jarrabawa a makarantar, wasu malaman duk sun ƙarƙare darususskan su, wasu sunyi teses ɗin da duka zasu yiwa ɗalibai, zasu fara jarrabawa.

Farhan ta kasa fita daga ajinsu ma, gani take kamar ita za'a dinga kallo idan ta fita saboda yadda skirt ɗinta ya matse ta sosai, gashi bironta ya ƙare tana son siyan wani, haka ta daure ta fita siyan biron, sedai shop ɗin a kulle yake.

Kawai ta yanke shawarar zuwa gurin Prince ta karɓi aron nasa.

Ta ɗau littafinta ta fita, taje ajin nasu sedai tana shiga ta duba gurin zamansa ta ga baya nan, ita ba iya sakewa take da 'yan ajinsu ba, dan haka ta nemi guri kawai ta zauna tana jiran dawowar Prince ɗin.

Gudu gudu sauru sauri take hawowa step ɗin benen, jacket ɗinta na riƙe a hannunta ɗaya, ɗaya hannun kuma na riƙe da jarkar youghurt, yana daga saman benen a cikin malamai yake hangota tana hawowa, ilahirin jikinta na rawa, kanta a ƙasa ba tsammani tai karo da shi a tsaye yana kallonta.

Ƙoƙarin kaucewa tayi amma yaƙi ba ta hanya, yace "What did I told you last day?"

Kallon hannunta tai da ta riƙe jacket ɗinta, ta kalli jikinta ta ɗan yatsuna fuska tace "sir zafi nake ji shine fa na cire ta"

"Shut up! Bance karki sake cire jacket ɗinki ki tafi haka ba?"

Ta yatsuna Fuska tace "kace"

"Shine kika cire rigar kike yawo da ita a hannu dan rashin kunya ko?"

Shiru tayi tana zumɓura baki taƙi Magana, yace "oya wear it back"

Tana harararsa ta gefe haka ta maida rigar, sannan ya batta ta tafi.

Tana barin gurin tace "ɗan rainin hankali kawai" ta sake cire rigar ta tafi aji.

Corper Nura yace "Nayi matuƙar mamakin ganin irin wannan dress code ɗin na student, a garin Kano"

Nazir yace "ai ba kai kaɗai ba, abun da mamaki kam kamar ba garin musulmi ba, kalli yadda suke yawo kamar ba musulmai ba, kuma babban abun takaicin an rasa me musu magana akan wannan shigar ta yaran, kuma su kansu iyayen suna kallo amma sun yi shiru"

Nura yace "amma hakan be dace ba, ze iya buɗe ƙofar ɓarna a tsakanin malami da kuma ɗaliban kansu"

Nazir yace "ai kai kaga haka, su ba wannan ne a gabansu ba, su makarantar burinsu yadda zasu samu kuɗi, su kuma iyayen burinsu ace yaransu na makaranta me tsada, amma ɓarna kam a makarantar nan sedai ai shiru kawai"

"Subhanallah, Allah ya kyauta"

Nazir ya amsa da "Ameen"

Farhan kuwa gajiya tai da zaman jiran Prince, ga shi 'yan ajin se fitsara suke kala kala a gabanta, dan haka ta tashi zata bar ajin, harta fito taji yace "See me here"

Ta waiga taga yana tahowa a hankali kamar mara lafiya, tai murmushi tace "ina ka tafi ne na daɗe ina jiranka fa"

"Naje cin Abinci ne ina jin yunwa, kuma nasan idan nazo ma

Please Login or Register in order to submit comment