Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

     

SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN. 






                         27_28

Tsoro ne da fargaba suka ziyarci Farhan, jin wannan ihun haka, ba tare da tayi fitsarin ba a razane ta leƙo, aikuwa ta ga jini na zuba sosai a jikin Nasreen, wadda ta riga ta haɗa uban gumi kamar tayi gudu.

Take Farhan ta sake birkicewa, ta tsorata ainun ganin wannan uban jini, kamar an yanka rago.

"Ke da kin san baki iya abun ba kika je kika fara, gobe ma kya kuma ai, se ki shiga taitayinki, in kin san zaki yawon ki, seki ɗau mataki ba ki bari abu ya faru haka ba"

Suka cigaba da caccakarta suna mata mita, ita kuwa Nasreen se jujjuya kai kawai take, ita kaɗai ta san azabar da take sha.

Can wata tace "seki gode Allah, tunda Allah ya rabaki da wahala cikin ya faɗi"

Gaban Farhan yai mummunar faɗuwa,  Suf Farhan ta silale ta bar banɗakin jikinta yana tsuma, gaba ɗaya ta birkice, ba ta taɓa ganin jini me yawan haka ba.
Abunda ya sake ɗaure mata kai, be wuce yadda taji ana cikin ya faɗi ba, to ciki ya faɗi kamar yaya? Ta yaya cikin mutum ze faɗi?.

Jikinta se tsuma yake ta tafi ajinsu, ta nemi guri ta zauna ta kifa kanta a benci, tana jin yadda zuciyarta ke wani irin lugude kamar zata faso ƙirjinta ta fito.

Haseena ta kalli in da Farhan take ta ja uban tsaki, tace "Idan za'ai taro na 'yan makarantar nan be kamata a dinga gayyato 'yan alfarma ba, ga bikin yayan Prince da mukaje, yadda wata taje yarkace yarkace kamar wata 'yar ƙauye, taɓɗijan Ni wallahi da bikin gidanmu ne ta zo korarta zanyi wallahi"

Gaban Farhan farhan ta ji wani dumm a ƙirjinta, dan ta san tabbas da ita Haseena take, taji zafin Abinda Haseena ta faɗa amma ba ta damu ba sosai, sakamakon tasan eh dagaske ita ɗin ba 'yar kowa bace akan su. Ita abunda ta gani yau yafi komai ɗaga mata hankali nesa ba kusa ba.

Yauma Meena lesson kawai ake, amma ba wani ganewa take ba, dan tunda ta zo take maye, ƙwayar da ta sha daren jiya ba ta gama sakinta ba.

Taslim ta kalleta tace "Ke Meena, ki dena shan abun nan in zaki zo school, so kike se an fara ganewa tukuna? Kinga abunda kike yi kuwa? Idonki duk ya juye"

"Taslim ya zanyi, idan ba sha nai ba sam ba na jina yadda nake so, idan na sha nafi jin daɗi"

"Aikuwa za'a ganoki a gida da wuri, ki dinga bari se dare in ba haka ba kuma Asirin ki ya tonu ba ruwana"

Meena tace "Insha Allah baze tonu ba ba, kuma ma fa daddaren nake sha, kawai sakina ne ba tayi fa wuri"

Jakar Taslim Meena ta ɗauka, tana dubawa ko zata samu chewangum, ta samu ta ɗan tauna amma da mamakimta se ta ga maganin planing a jakar ta ta.

Ta kalli Taslim tace "beb what is this?"

Taslim tace "meye na tambaya, maganina ne"

"Amma wannan ai maganin hana ɗaukar ciki ne"

Taslim ta kalleta tace "ke a gidan ubanwa kika sani?"

"Naga Yaya Amra na sha ne, tace na planing ne kullum tana sha"

Taslim tace "ni ban san yadda akai ma na sa shi a jakata ba, ɓare shi nake daga satchet ɗin, in bar shi a haka ba wanda yasan meye"

Meena tace "Amma Taslim me kike da maganin hana ɗaukar ciki ke ba Aure ba?"

"Naga kamar baki fahimci amfanin maganin nan ba, bature beyi wannan maganin dan masu Aure kawai ba, yayi shi ne dan mabuƙata"

"Kenan kema kina cikin mabuƙatan?"

Taslim tace "ƙwarai, ina amfani da shi ne dan hana ɗaukar ciki"

Zare ido Meeena tayi tace "Taslim, it means you are not virgin fa"

"Yes of course, amma ai ba abun mamaki bane"

"Kamar ya ba abun mamaki bane? Kenan fa ke ba budurwa bace kina bin maza kenan"

Taslim tace "Ina ke shaye shaye kike yi? Shike ba ki nustuwa da kwanciyar hankali?"

"Amma Taslim shaye shaye daban, wannan da kike Magana daban, maganin hana ɗaukar ciki fa"

Taslim tace "to ke da da kike ƙoƙarin jan hankalin sir Nuradeen, me kike so yai miki?"

Meena tace "kawai ina son muyi soyaya ne na school, kuma ni iya abuna ba na wuce Romance, amma naga ke naki babba ne"

Taslim tai wani murmushi tace "Meena, ni dake kusan abu ɗaya ne, ke da ni budurwa ce ta ya zan dinga duk wani rashin mutunci da Mubarak Babba, ko dayake virgins ɗin ma nayi, amma yadda kike romancing da namiji, wataran zaki abunda nayin nima, nima da fari ba'a san raina ba, soyayya ce ta jani ta kaini ga wannan matakin, ina ƙoƙarin in dena, amma na riga na saba ba yadda na iya, ki manta kawai kiyi kamar ba kiga komai ba" Taslim ta ƙare maganar tana kallon idon Meena ta na mata murmushi.

Galala Meena ta cigaba da bin Taslim da kallo, Taslim tace "Meena ki dena kallo na a haka, kamar kinga wata baƙuwar halitta mana, nifa mutum ce, kuma kema mutum ce kin san me ake ji a irin wannan shekarun, so stop pretending"

Duk iya shegen Meena, Taslim ta dameta, dan bata taɓa tunanin gawurtar Taslim ta kai haka ba.

Sadik kam a gurin zamansa ya zauna, yana duba wani Keypoint na Physics, sega su Nas sun shigo ajin, sedai tun shigowar su yaji suna ƙauri.

Nas yace "Baba yane, zamu fita muka nemeka muka rasa ina kayi ne?"

Amin yace "kai seka tambaye shi ma? Yana cam gurin waccan ƙwailar da ba ta san ta tsinana masa komai ba sedai shi yai mata"

Nas yace "bar wannan batun kar yaji haushin ka, kasan shi baya son gaskiya"

Sadik be ce mus uffan ba ya cigaba da duba abunda ke hannun sa, Nasir ya zauna a kusa da Sadik amma Sadik ya dube shi yace "malam leave my place please"

Nas yace "meyasa kake korata?"

"Kai ba ka jin yadda kuke warin sigari ne, banzaye dalla tashi kar ka sani amai"

"Amma wallahi Sadik ka ɗan wahala ne, yau ka fara jin warin sigari da kake batun zata saka amai, naga har shisha kana sha ai"

"Shisha sigari ce? Dalla ku barmin seat"

Amin yace "Wallahi Shisha da sigari ba wani banbanci, tunda duk hayaƙi muke sha" ya ƙarasa Maganar yana miƙewa daga seat ɗin Sadik ɗin.

Farhan abun duniya ya isheta, gashi haka nan tun da taga wannan jinin ta tsorata taji cikinta ya ƙara tsananta mata ciwo, tun tana basarwa harta kasa jurewa ta fara zubar da hawaye,ba tare da kowa ya gane halin da take ciki ba.

Ganin an tashi kowa na fita, amma ita tana zaune yasa Lilly ƙarasawa gurinta, ta taɓa ta tace "Farhan an tashi fa"

Shiru Farhan tayi ba ta ɗago ba, kuma ba tace komai ba.

Sadik yana fitowa daga ajinsu ya tafi gurin Farhan, sedai ya tarar da ita ta kifa kanta, ba ta da alamar tashi daga gurin zamanta, ga Lilly a tsaye a kanta.

Sadik ya ƙaraso da sauri yace "lafiya kuwa?"

Lilly tace "wallahi ban san meya sameta ba, na mata magana amma taƙi tashi"

"Princess menene? What's wrong with you?"

Ɗago kai tayi a hankali, hawaye ya wanke mata fuska.

Yace "Ya Salam, menene?"

"cikina ne kemin ciwo".

A hankali ya durƙuso yace "Baki je Asibitin da nace ba ko? Tashi muje Clinic a duba ki"

"Um um ni bazanje ba, gida zan tafi" ta haɗa gumi sosai, ga hawaye na bin fuskarta. He just wish he can hug her and wipe her tears.

Yace "ba zaki A dubamin ke ɗin ba kenan?"

"Ni gida kawai" tai maganar tana jujjuya kai saboda ciwo.

Yace "ok tashi muje mota" ita kam Lilly gaba ɗaya burgeta sukayi, yadda yake nuna damuwarsa akan ta.

Sadik ya miƙa hannu ya riƙo hannunta, Lilly ta kama ɗaya hannun suna tafe tana durƙushewa, Sadik yace "Farhan, bari in ɗauke ki kawai in kaiki mota, tunda tafiyar ta gagara"

Da sauri ta sake fashewa da kuka tace ba ta yadda ba.

Da ƙyar suka ƙarasa mota, makaranta duk an watse.

Nazir yana bene na biyu, a Office yana ƙoƙarin tashi, ta window ya hango Lilly da Sadik sun riƙo Farhan, tana durƙushewa, ya girgiza kai ya nemi guri ya zauna, dan abunda tunanin sa ke kawo masa akan su daban ne"

Tare da Lilly Sadik suka tafi kai Farhan gida, Lilly na rungume da Farhan.

Da sukaje gidan ma, Sadik na mota Lilly ce ta kama Farhan Zuwa cikin layinsu.
Hakan yai daidai da fitowar Abban Farhan ze tafi masallaci, a kiɗime ya ƙarasa in da Su Lilly suke yace "lafiya kuwa? Meya sameta?"

Lilly tace "ba ta da lafiya ciwon ciki take"

Da Sauri Abba ya riƙota yana mata Sannu, Lilly ta juya zata tafi yace "Yarinya zo muje ko ruwa ki sha a gidan"

Lilly tace "A'a Nagode, zan tafi gida kar a ga na daɗe"

Abba yaita mata godiya yana sa mata albarka.

Sadik na bakin layin yana kallonsu, sedai be ƙarasa ba, da Lilly ta dawo seda suka kaita har gida sannan suka tafi.

Umma ma ta tsorata da ganin Farhan a haka, amma ta kasa nuna damuwarta sosai, Abba ya ɗebo ruwa yai tai mata tofi, ya bata ta sha.

Da ƙyar aka samu bacci ya ɗauke ta.

Sadik kam tunda ya koma gida kasa sukuni yai, yana ta tunanin halin da Farhan ke ciki, dan ya tsorata da halin da ya ganta a ciki.

Tunda Farhan ta fara bacci ba ta tashi ba, se la'asar kuma ta tashi da sauƙi da sosai, ƙannenta suka dinga jera mata Sannu.

Umma anyi abun kai ta kaiwa Farhan ruwa tace taje ta watsa, Farhan taji daɗin hakan sosai.

Sedai bayan tayi fitsari taga kamar jini a cikin fitsarin, basarwa tai dan bata kawo daga jikinta bane, dan haryanzu ta kasa manta abunda ta gani, lokaci lokaci ta kanji gabanta ya faɗi idan ta tuna.

Wankanta ta cigaba dayi, ta kammala tai Alwala ta miƙe kawai taga jini na bin ƙafarta.

Ihu ta buɗe baki zatai, tai saurin saka hannu ta tsohe bakinta, nan ta shiga zazzare idanu a banɗakin.
Kawai ta hasko abunda ya faru da Nasreen ta ss3 shine itama ya sameta, ta dinga rusa kuka a banɗaki.
Se da tai me isarta sannan ta sake wanke jikinta ta fito.

Ta dinga ƙoƙarin ɓoye hawayen da takeyi, ta shiga ɗakinta, ta tarar Umma ta ajiye mata shayi a ɗakin nata.

Kasa sha tai ta nemi Guri ta zauna ta cigaba da kukanta, can ta kalli ƙafarta ta ga yadda wani jinin ke cigaba da binta, nan ta sake rikicewa ta cigaba da kuka ta koma banɗaki da sauri ta sake wankewa.

Umma ta biyo ta ɗaki da magani a hannunta tace "ga magani nan, Na aika gidan Nurse ɗin nan, tace ki sha wannan"
  Sedai Umma taga kamar Farhan hankalinta baya kanta, nan ta lura da hawayen dake kwance a idonta.

"Ke lafiya kuwa?"

Cikin kuka Farhan tace "Umma mutuwa zanyi"

Cikin rashin fahimta Umma tace "ke bana son shirme, cikin ne yake miki ciwo haryanzu?"

"A'a fitsarin jini nake yi, kuma ko banje nayi fitsarin ba se inga ya zubo"

Gaban Umma me yai mummunar faɗuwa, ba ta taɓa kawowa Farhan yin Al'ada a Yanzu ba, saboda ƙananan shekarunta"

Jiki a sanyaye Umma ta bar ɗakin, ba ta daɗe ba ta dawo ta miƙawa Farhan pad tace "ki dena wannan kukan, jinin al'ada ne, ga wannan da shi ake amfani" Umma tai maganar ko haɗa ido ba ta san yi da Farhan, tana bata tai waje.

Mamaki ne ya kama Farhan, menstruation fa kenan, shikenan ta shiga uku itama za'a fara rubuta mata zunubi.

Jin tana ƙoƙarin sake ɓaci ne yasa, tabi direction ɗin yadda ake amfani da pad ɗin da ke rubuce a jiki ta saka, dan ba wani bayani da Umma tai mata, akan yadda zata dinga kula da kanta, da abunda ba'a so tayi.

Ita Umma hankalinta ne yai ƙololuwar tashi, duk wasu alamu na girma sun gama bayyana a jikin Farhan ɗin.
Duk da ƙanƙantar shekarunta, alamun girma kam yanzu babu wanda babu a tare da ita.

Farhan kuwa kukanta ta cigaba da rerawa, kamar wata ƙaramar yarinya, ko wadda wani bala'i ya faru da ita.

Bayan sallar magariba Abba ya dawo gida, ya siyowa Farhan kayan marmari, ko zata iya ci.

Yace Umma ta kira masa Farhan.

Ba jimawa sega Farhan ta zo, fuskarta duk ta kumbura saboda kuka, da ƙyar take tafiya, ko ƙwaƙwƙwaran motsi ba ta son tayi.

Abba ya kalli Farhan, Sannan ya kalli Umma yace "yarinyar nan ko dai mu tafi Asibiti ne?"

Umma tace "A'a base munje Asibiti ba"

"To ai naganta haryanzu wani iri ne"

Farhan tace "A'a Abba ai na samu sauƙi"

Abba yai ajiyar zuciya yace "shikenan, ga wannan ledar ki ɗauka kije ki samu kici, Allah ya sawwake"

Tace "Ameen Abba Nagode sosai"

Ta tashi ta bar ɗakin, Umma ta kalli Abba tace "Yarinyar nan fa, Al'ada ta fara"

Abba yace "to ciwon cikin kenan dama, lallai Farhan an girma, to Allah ya sawwake"

Cikin damuwa Umma tace "Nifa ina cikin damuwa, Farhan tayi ƙanƙanta, haryanzu fa ba shekarunta goma sha uku, tayi ƙanƙanta"

Abba yace "to banda abunki zamu hana Allah ikonsa ne akanta?"

"A'a, amma a tsorace nake, yarinya ce ƙarama amma kalli yanayin jikinta, anya ba za'a haƙura da bokon nan ba a Aurar da ita, ina jin tsoron wannan zamanin da muke ciki"

"A'a ki kwantar da hankalinki, ai Allah shi ke ds zamani, kuma kowacce yarinya da irin halittar da Allah yai mata, kiyi haƙuri ki yi mata Addu'a kawai"

Jiki a sanyaye Umma tace "to Allah ya tsare"

Har Dare yayi Sadik ya kasa bacci, yana son sanin halin da Farhan ke ciki amma ba damar sanin hakan.

Da safe da wuri Ya shirya ya tafi Makaranta, amma har aka tashi Farhan ba ta zo ba.

Abun ya sake ɗaga masa hankali, da aka tashi ya koma gida da yamma, yaje ya ɗakko Khairat yace mata zata rakashi gidan su Farhan ya duba ta.

Ba ta musa masa ba ta bishi, ya biya yai siyayya, suka tafi gidan su Farhan ɗin. da sukaje layin ya bata kayan dubiyar yace in ta shiga ze kirata ta haɗa shi da Farhan.

Khairat har Mamaki take akan yadda Sadik rawar jiki akan wannan 'yar mistilar Yarinyar.

Yauma Umma ta karrama Khairat sosai, Farhan na ganin Khairat ta san tare suke da Sadik.

Suka shiga ɗakin Farhan suka gaisa, Khairat ta kalleta tace "ya jiki?"

"Alhamdilillah na samu sauƙi"

"Bari in kira shi a waya, yace in haɗaku ku ze miki ya jiki"

Farhan ta jinjina kai, Khairat ta kira Sadik a waya ta bawa Farhan.

Sedai kowannen su ya kasa Magana, can Sadii ya katse shirun ta hanyar cewa "ya jikin naki?"

"Naji sauƙi Alhamdilillah"

"Kunje Asibitin ne?"

"Eh munje" ta bashi amsa.

"To shikenan, ki kula sosai dan Allah ki sha magungunan da aka baki kinji Babyna"

Murmushi tai tace "to insha Allah"

Su kai sallama ta katse wayar, Khairat ta miƙe tace "to shikenan Allah ya ƙara sauƙi, zan tafi"

Iya tsakar gida kawai Farhan ta iya raka Khairat, saboda gani take da tayi kyakyawan motsi, za'a gane halin da take ciki.

Wasa wasa seda Farhan ta shafe kwana biyar cif, sannan ta koma makaranta lokacin ta koma normal.
Lokacin da ta gama period ɗin ma tayi amfani da karatun Islamiyyar ta ne gurin yin wanka, da gane ɗaukewar jinin, dan in ta Umman ta ne sedai ta zauna a haka ba zata gaya mata ba, dan tunda Farhan ta fara period ma kamar sake janye mata tayi.

Ranar da ta koma makaranta Sadik ji yai kamar ya rungumeta saboda farinciki, tayi haske gau, amma fuskarta ta faɗa sosai.

"Princess, kin rame da yawa fa"

Murmushi kawai tai ta ɗauke kai ba tace masa komai ba.

"Da kuka je Asibitin ba suce miki komai akan ciwon cikin naki ba?"

Gabanta ne ya faɗi, ta maze tace "kawai ciwon ciki ne kuma na warke ai"

Yace "to Alhamdilillah, Allah ya ƙara mana lafiya"

Ta Amsa da "Ameen"

Tun dawowarta makaranta, kullum idan aka fita break su Lilly ba su da aiki se karanta litattatafai masu ɗauke da zunzurutun batsa, wadda ta kasance barazana ga ƙwaƙwalwar ƙanan yaran.

Da an fita break, Farhan ke tattara kayanta ta tafi ajin su Sadik, sedai can ɗin ma da nasu kalar watsewar, ga Mubarak Babba da ke cigaba da takura mata, wani rashin mutuncin ma se sunga tazo ajin suke fara yin sa.

Haka nan take jin zaman makarantar ya isheta, mutum ɗaya ke bata farinciki a makarantar Shine Sadik.

Kasancewar ta tare da shi ne kawai ke bata nishaɗi da ɗebe mata kewa, amma duk lamuran ɗaliban har malaman sun ishe ta.


Nana ke zaune a gefen Hakimi ta na ta zuba masa surutu kala kala, yayin da yake kashingiɗe yana sauraronta, fuskarsa na bayyanar da tarin murmushi.

"Kaga Baba Alaji, da mukaje bikin nan kawuna ya tambaye ni me nake son na zama idan na girma"

"To ke me kika ce masa?"

"Ai ni kasan 'yar jarida nake son zama, me karatu da turanci, irin na turawan nan ina son inga na iya turanci sosai da sosai fa"

Hakimi yai murmushi yace "Ai Yanzun ma kin iya, tunda in anyi kina ji"

"Taɓ me na iya, ai idan ina ƙauyen nan na fi iya turanci, da mukaje birni duk se naji ba turancin, kaji irin turancin da suke kuwa kamar Turawa, ni bama na gane irin nasu turancin wallahi"

Hakimi yai murmushi yace "to Allah ya ida nufi, ya nuna mana kammala karatun naki"

Nana ta gyara zama tace "ina ga fa nima ƙasar wajen ze kaini, inyi karatun fa"

"Ba Gidan uban da zaki, kina gama Sakandire Aure za'ai miki, kya yi karatun a can, dama ba Jamilin Gidan me unguwa bane yake biyo ki idan na aike ki ba, da kin gama makaranta za'a ace ya fito"  Inna ce take wannan bayanin a ƙofar ɗakinta.

Kwaɓe fuska Nana tayi tace "ni wallahi ba saurayina bane, dan Allah ki barni in karatu, wallahi ban isa Aure ba, kefa kike cewa Ni yarinya ce"

"Eh ke yarinya ce a yanzu ba, amma kan lokacin ai kin ƙara girma"

Nana ta kalli Hakimi tace "dan Allah ka sa baki, nima a barni inje inga ƙasar wajen nan inyi karatu"

Inna tace "idan kika je ƙasar waje karatu, ba bu me Aurenki za'ace idonki ya buɗe"

"Wallahi za'a samu me Aure na, kinga lokacin na zama 'yar gayu sosai, dama ni ba zan Auri ɗan ƙauyen nan ba, se ɗan gayu, ɗan birni wanda ya iya turanci"

Hakimi yace "Banda abunki, shi wannan turancin in kinyi Auren shi zaki ci ne, ai mutum Nagari ake nema"

"Eh to nagarin, kamar dai Farukun Gidan kawu"

Hakimi yace "shi kike so kenan"

Kamar wadda ake ce tayi zunubi tai farat tace "A'a ba haka ba, taɓ kawai dai ya iya turanci, kuma yana da kirki sosai, ba kamar wannan dogon mara kunya ba"

"Waye kuma dogo mara kunya"

Nana ta ɗan keɓe baki tace "wannan Sadik mana, wallahi na tsane shi ba shi da kirki kwata kwata, kaga yadda ya shaƙeni zemin duk ranar dan na zuba masa miya ban sani ba, ni kuwa na ɗau wandonsa me tsada na sa a ruwan datti"

Hakimi ya ɗaga kai ya kalli Inna su kai ido huɗu, ya jinjina kai yace "Kar ki sake cewa kin tsani mutum, kuma kinga ai shi yayanki ne, karki sake"

"Baba Alhaji, yaro ne fa shi, tsawo kawai ya fini, dan haka ba wana bane,  Faruk ne Yayana, me Kirki yaita saimin abubuwa da muna gidan"

"To uwar son abun duniya, dama saboda yana sai miki abubuwa shiyasa kike ta rawar kai a kansa, tashi ki bar nan uwar surutu, ko gajiya ba kya yi, kamar an kwance ruwa ki ta zuba"

Nana ta tashi, sum sum ta bar tsakar gidan, Hakimi yace "da kin ƙyaleta, a hirar ta ta nake fuskantar wasu abubuwan"

Inna tace "Na sani, nima a haka nake bugun cikin ta nake jin abunda ke ranta, amma wasu lokutan surutunta yai yawa, idan ba'a taka mata birki, a waje ma zata iya zuwa tai hakan"


Prince ya riga yai registration ɗin jarrabawar ƙarshe da wanda zasu gama a shekarar, zeyi tsallaken aji guda, duk a ƙoƙarin cinma burinsa na ganin ya shiga jami'a da wuri, dan ya samu ya mallaki abunda zuciyar sa ke so.
Sedai ɓangare guda idan ya tuna da ze bar makarantar, yai nesa da Farhan gaba ɗaya se ya ji damuwa ta mamaye shi, yana matuƙar jin Farhan a ransa.

Kamar kullum, Nazir ya kammala koyarwar sa a ajin su Farhan na ranar, ya bawa Class rep Umarnin ya tattara masa litattafan 'yan ajin ya kai masa ze duba notes.

Yana fita Lilly tace "kan bala'i, wai dagaske gayen nan yake checking note zeyi? Aikuwa kashi na ya bushe dan ba na wani note wallahi"

Haseena tace "Ubanki ze ci la'ada waje wallahi, kin raina mutumin nan kowa na tsoron sa amma banda ke"

Lilly tace "ke bari kawai, wallahi nima ina tsoron sa, ko kallona ya fiye yi se inji hantar cikina ta kaɗa wallahi, ni yanzu ya zanyi?"

Yasmin tace "to ki sauri ki ksrɓa kiyi mana"

"Ke wallahi ba zan ba, note ɗin fa fa yawa, ba yi nake na Assignments ɗin sa ma bayi nake ba, sedai ya kashe ni ya huta kawai"

Class rep ɗin su yace "ba shakka kin shahara Lilly, mitumin nan ba raga miki ze ba"

"Aikuwa sedai ya kashe ni, ni bari ma in tattar maka litattafan, idan ka tashi sedai ka kai masa kawai"

"Aikuwa da kin kyauta"

Lilly ta tashi ta na karɓar litattafan 'yan aji, ta zo kan Farhan, ko littafin ba ta ɗakko ba.
Lilly tai murmushi tace "Sannu basarakiya matar Prince, a dole se an nuna mana sarauta, kina kallo ina haɗa litattatafai amma ko ɗakkowa baki ba"

Kunya ce ta kama Farhan, tai murmushi tace "Yi haƙuri, ba wata sarauta wallahi, hankalina ne yana wani gurin"

"Eh hankalinki na kan tunanin sa ko?"

Murmushi Farhan ta cigaba da yi, ta ɗakko littafin ta bawa Lilly.

Lilly ta karɓ ta fara buɗe littafin tace "Masha Allah, ke komai naki abun burgewa, kalli handwriting ɗinki me kyau kamar ke"

Murmushi ta cigaba da yai tana sunkuyar da kai, Lilly na cikin buɗe littafin ta tsinci takaddar haihuwar Farhan a ciki.

Farahn ba ta san takaddar ta na ciki ba, Lilly ta tsaya tana duba takaddar.

"Wow Masha Allah, Ashe akwai birthday me yaji a school ɗin nan, saura sati ɗaya birthday ɗin ki Ashe?"

Da sauri Farhan tace "A'a ni ba na wani birthday, ban ma san takaddar na ciki ba, bani in ajiye"

Lilly tace "ke kin isa, budurwar Prince guda ace ba za'ai celebrating birthday ɗin ta ba, wallahi dole ayi let me go and show him in case be sani ba"

Lilly tai waje da sauri da takaddar a hannunta, gaba ɗaya Farhan ta rasa abunyi, sam ba ta so abunda Lillyn ke shirin yi ba, meyasa za tai mata haka.

Cikin sa'a Lillyn na fita, ta hango squad ɗin su Sadik ɗin, suna tahowa da alama zasu fita ne, Sadik na maga duk sun bashi attention ɗin su.

Tun lokacin da Lilly ta bi Sadik, suka kai Farhan gida idan ya ganta ya kan ɗan sakar mata fuska, saɓanin da da ba ruwansa da su, hasali ma Juniors suna tsoron sa, kuma ta fanni guda ana son sa saboda yawan kyautarsa.

Ta ƙarasa in da suke, Sadik ya ɗan kalli Lilly, amma be ce komai ba.

Miƙa masa birth certificate ɗin tayi, ya karɓa yace "wannan na menene?"

Tai murmushi tace "nasan wataƙila ba ka sani ba, birth certificate ɗin Farhan ne, on 8th ne birthday ɗin ta, nasan maybe ka shirya wani abun"

Murmushi yai ya fara duba takaddar, yana bawa duk wani abu da ya shafi Farhan mahimmanci.

Ya shafi sumar kansa yace "Wow, naji daɗin wannan Albishir ɗin, nasan ba dan kin gayamin ba ba zata faɗan ba, dole ai celebrating, kina da kyautar wannan Albishir ɗin"

Lilly tace "godiya nake Allah ya raya mana Farhan, ya kaimu lokacin abun"

Sosai Sadik yai murmushi har seda haƙoransa suka fito yace "Ameen"

Ya kalli su Nas yace "guys kuyi gaba, let me go and see her first"

Aminu ne ya fara jan uban tsaki yace "what a shit! Wallahi tun fa Yarinyar nan ta zo school ɗin nan ka zama wani bita zai zai, ni na rasa uwar me

Please Login or Register in order to submit comment