Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.                   

                                30



Sosai Lilly take kokawa da numfashinta, dan ya dinga sauka cikin huhunta da sassan jikinta, amma abu ya gagara.

Sadik da ya taho daga ajinsu ne yai karo da ita a hanya a ƙasa.

"Subhanallah, ke meyafaru meya sameki haka?" Ya tsaya yana tambayar ta.

Ba ta iya magana, se numfashinta da ke tayin sama yana ƙasa.

Rasa abunyi Sadik yayi, ana haka sega su Nas, sun dawo daga inda suke zuwa shaye shayensu.

Nas yace "lafiya ita kuma wannan meya sameta take kwance a ƙasa?"

Sadik yace "nima ban sani ba, na taho ne kawai na ganta a kwance a nan"

Amin yace "to ai kamata yai ka ɗagata da ga ƙasan nan, ko Clinic ka kaita"

Sadik ya kalleshi yace "waye ze ɗagatan?"

"Kai mana" Nas y faɗa yana nunashi.

"Bana taɓa abunda ba nawa ba" Sadik ya basu amsa.

"Dallacan banza, ji wata ƙaryar wofi wai baya taɓa abunda ba nasa ba"

Sir Nazir ne ya sakko daga kan bene, hannunsa riƙe da litattafai alamar aji za shi, har ze tafi ya hangi su Sadik a tsaye a guri ɗaya.

Takawa yai ya ƙarasa in da suke tsaye, yaga Lilly a baje a gurin.

"Yasalam, meya sameta haka?"

Sadik ya ɗage kafaɗa alamar i don't know, ya ja da baya a hankali ya bar gurin.

Nazir yace "this is an emergency case, you are not supposed to stand just watching at her, what if her breath seize.

Be saurari me za suce ba, yasa hannu ya ɗagata yace suje ajinsu Lilly su kira masa mutum biyu a ƙawayenta, daga nan ya nufi Clinic da ita.

Ya samu gado ya kwantar da ita, sedai me kula da Clinic ɗin baya nan, yana kwantar da ita sega Haseena da Yasmin.
Suna zuwa suka zubawa Lilly ido, duk ta ɓata Uniform ɗinta, se ƙoƙarin tashi zaune take, amma Nazir ya riƙeta.

Ya kalle su Yace "maza ku zo ku riƙeta karta tashi, Sannan ku cire mata hijjabin jikinta"

Haka kuwa akayi, suka cire mata hijjabin jikinta, suka barta daga ita se long slip ɗin ta, ta ɓalle botir ɗin saman rigar, dan haka idonsa ya sauka fatar wuyanta zuwa ƙirjinta me matuƙar haske.

"Astagfirullah" yaita maimaitawa a zuciyar sa, ya kalli su Yasmeen yace "dama ta na da wani special case ne?"

Haseena tace "Eh dama tana da Asma, amma ba ta fiye tashi ba"

Yace "ke Haseena, jeki staff room, ki kiramin Madam Joy"

Da Sauri Haseenan ta fita daga ɗakin dan aiwatar da abunda yace.

Sedai numfashin Lilly ya cigaba da sarƙewa, Dan she's unconscious ba ta san meke faruwa ba.

Yace "ko a jakarta Babu inhaler, ko maganin da take sha?"

Yasmin tace "gasky babu, dan tana daɗewa sosai ba ta tashi ba, sedai idan tayi kuka sosai take tashi, dan har cewa take ta warke daga Asma"

Kasancewar Microbiology ya karanta, yasa yasan wasu daga cikin clinical skills ya kalli Yasmin yace "can You resustate her?"

Yasmin tace "Sir meke nan?"

"Ki bata artificial respiration"

"Wallahi sir ban iya ba"

Tsaki yayi, ya durƙusa daf da fuskar Lillyn da ƙirjinta ke ɗagawa yana sauka, numfashinta na fita da Wani irin sauti, wani lokacin ma ya ɗauke gaba ɗaya seta ɗan ɗau lokaci kan ya dawo.

Sedai yana kai fuskarsa yaji zuciyarsa tana bugawa da sauri da sauri, addu'a yai tayi sannan ya kai bakinsa na ta, yasa hannunsa ya matse hancinta, ya ɗaga haɓarta ta kalli sama sosai yasa bakinsa a nata ya shiga hura mata iskar bakinsa.

Sama ƙirjinta ya ɗaga amma ta kasa karɓar iskar, se hawaye dake bin gefen fuskarta.

Ya cigaba da ƙoƙarin ba ta artificial respiration, a hankali huhunta ya fara karɓar iskar, Yasmin kuwa ta zuba musu ido tana kallonshi.

Haseena ta shigo ita da Madam Joy, sedai ɗan turus Haseenan tai tana kallon ikon Allah, dan ba ta taɓa gani ba.

Madam joy ta ƙarasa da sauri tana tambayarsa meyafaru.

Nan yai mata bayani, tace to bari  Director magana, a aika a siyo inhaler ai mata amfani da shi.

Madam Joy duk tace su Haseena su koma aji.

Suna fitowa daga Clinic ɗin Haseena tace "ke Yasmin, kinga abunda na gani ko nika ɗai na gani?"

Yasmin tace "taɓ, ni da kika bari a gurin, ai ni yace in mata nace ban iya ba, shine yai mata da kansa"

Haseena tace "taɓ to Allah ya kyauta, kinga yadda ya wani naniƙeta?"

"Na gani mana, Allah ɗai yasan me yai mata ai daga Office ɗinsa take, tunda muke da ita sau ɗaya na taɓa ganin Asmarta ta tashi se yau"

Haseena tace "baiwar Allah, ga wahalar ciwo ga yawun ƙato, kai Allah ya bata lafiya akwai buduri yaseen"

Suka tafi ajinsu suna dariya.

Da aka tashi daga school, A harabar makarantar Farhan ta tsaya tana jiran fitowar Sadik.

Tana nan tsaye se gashi ya taho, yana tafiya a hankali, sedai shikaɗai ne ba abokan nasa.

"Yana ganka wani iri kamar mara lafiya?"

"Am ok, just tired"

"To Sannu" ta faɗa cike da kulawa.

"Yawwa matar, kinga da munyi Aure muna zuwa gida ki ban Abinci, ki rarrasheni inyi bacci"

Banza tai masa kamar ba ta ji ba.

Matsawa yai kusa da ita yace "kina jina fa, shine ki kaimin shiru?"

Sunkuyar da kai tayi taƙi kallonsa, kuma taƙi Magana"

"Hmm, lalallai Yarinyar nan kin raina ni, shikenan mu tafi"

"Ni ba binku zan ba Napep zan hau"

Yace "Akan wani dalilin?"

"Ni tsoro nake ji, kar a gayawa Abbana kawoni ake gida a mota"

Sadik ya fuskanci yau rigima take ji, hannu yasa ya ƙwace jakarta da take ƙoƙarin goyawa yace "in kinga dama kizo mu tafi, in ba haka ba wallahi na tafi da jakar nan sedai ki bini gidanmu ki karɓa"

Zare ido tai jin yace wallahi, ta ina zata fara zuwa gidansu karɓar jaka? Ba shiri ta bishi da sauri zuwa motarsu.

Sedai se cika take tana batsewa, tana hura hanci, suna tafe a Motar taƙi kulashi.

Shima ya shareta sedai yana satar kallonta.

"Wash Allah" ta faɗa a marairaice.

Ya kalleta yace "lafiya kuwa"

"Lafiayata ƙalau" ta bashi amsa.

"Ok na gane, so kike dama in kulaki dan kinji nai miki shiru"

"Ni cikina ne yake ciwo"

"Waike wannan wane irin ciwon ciki ne?"

Shiru tai masa ta kashingiɗa a jikin seat ɗin motar, tana jin yadda mararta ke ɗan takura mata da ciwo.

Sadik yaita mata magana amma tai masa shiru, seda suka zo in da take sauka, sannan ta ɗau jakarta tacewa direban  "Baba nagode"

Direban yace "Yawwa bakomai"

Sadik yace "Nifa?" Murguɗa masa baki tai ta sauka, sedai tana sauka yaga inda ta tashi yai staining na jini, ga shi ƙasan baban hijjabin da take sawa ma ya ɗan ɓaci.

Kwanciya yai a jikin seat ɗin motar, ya ɗan shafi sumar kansa yace "Babyna ta girma ba labari, sedai yana ganin kamar tayi yarinta sosai da farawar"

Murmushi ya cigaba da yi, wanda shi kansa be san dalilin yin sa ba.

Suna zuwa gida ya kalli direbansa yace"A wanken motar nan"

Be jira amsar da ze bashi ba yai gaba abunsa ya nufi BQ.

Lilly kuwa seda aka haɗa mata da ƙarin ruwa da allurai sannan ta dawo hayyacinta gaba ɗaya, Sir Nazir yayi regrating Punishing ɗinta da yai har yai leading ɗinta ga Wannan condition ɗin.

Amma a zahiri ya dake ya nuna ko a jikinsa, seda ta gama farfaɗowa sannan aka ɗakko mata jakarta daga aji, Madam Joy ta riƙota ta kaita motar Makaranta, ta shiga dan raka Lillyn gida.

Seda Nazir ya tabattar komai ya daidaita, sannan ya koma ya tattara kayansa shima ya tafi gidan da yake zaune.

Sedai lokaci lokaci da ya tuna yadda ya kasance da Lillyn a ɗazu dan ceto ranta, se yaji wata irin mummunar faɗuwar gaba, ƙirjinsa kuma na bugawa da ƙarfin gaske.

Ya dinga maimaita 'Innalillahi, wa innalillahi raji'un"


A ƙauye kuwa Nana ce zaune a can ƙuryar ɗakin Inna, ta samu ƙatuwar 'yar tsanarta tana ta taje mata gashi, dan sam taƙi kula Inna, hakan ya kasance ɗabi'ar Nana, duk da shegen surutunta, amma lokuta da dama idan aka ɓata mata rai, se tai shiri ta dena maganar se abunda ya zama dole.
Sedai kan tai irin wannan fushin tana daɗewa.

"Nana" Inna ta kira sunanta, ba ta amsa ba sedai ta ɗago ta kalli Innan

"Ba zaki dena wannan fushin ba ko? Dani kike fushi ko Nana?"

Nana tace "A'a ni ba fushi nake ba fa"

"Ƙarya nai miki kenan, to dan ubanki wannan ba halin zuwa gidan miji bane, ba Namijin da ze ɗauki wannan iskancin da rashin mutuncin naki"

Nana tai shiru taƙi magana, can Innan ta kuma cewa "Nasan zakiga kamar ina takura miki akan wasu abubuwan, ba ina yine da cuzgunawa rayuwarki ba, ina yi ne dan ganin Rayuwar ki ta inganta.
Jiya duk hirar da ku kai da waɗanda suka zo gurin naki ina jinku.

Da sauri Nana ta kalli Inna, dan sam ba ta zaci taji hirar tasu ba.

"Ƙwarai kuwa, ko dan kinga na ƙyaleki? Naji suna gaya miki wani yana bakin layi yana jiranki, Nana ita rayuwa ba'a mata gaggawa, duk saurayin kirki da yake sonki saboda Allah, gidanku ze zo ya nemi izini, ba wai ya dinga laɓewa a bakin hanya yana tsare ki ba.
Nana ke yarinya ce, kina kan ganiyarki ta RUƊIN ƘURUCIYA, Shiyasa abubuwa da dama kike ganin kamar ina takuramiki.
Ba takura miki nake ba, so nake rayuwarki ta inganta, ki guji ƙawaye barkatai, idan kika fiye ƙawaye da yawa zaki zama baki da sirri, sannan ba kamun kai, dan zaki suffantu da ɗabi'u daban daban daga gurin su, masu kyau da marasa kyau.
Dan haka duk abunda ya shige miki duhu, wanda kike buƙatar ƙarin haske ni zaki samu ki gayawa, duk wata shawara da ƙawa zata baki, in dai zaki iya ɓoyewa ba zaki faɗa ba to ba shawarar Allah da Annabi bace, dan haka ki kiyaye kinji abunda nace miki?"

Nana ta jinjina kai alamar eh.

Inna tace "Yawwa".










Koda Madam Joy ta raka Lilly gida, ta gaya musu kawai ciwonta ne ya tashi, sun bata taimakon da ya dace a Clinic ɗin Makaranta.

Maman Lilly ta karɓe ta cikin girmamawa tare da yi mata godiya.

Mamanta se jera mata sannu take, yayinda zuciyar Lillyn fal take da jin haushin Sir Nazir, babban abunda ya ƙara ƙular da ita be wuce yadda tana buɗe ido ta kalleshi, ya wani haɗe rai ya bar Clinic ɗin ba.
Ba ta san lokacin da tai ƙwafa a fili ba.
Mamanta ta kalleta tace "Lillyna meke faruwa ne? Nifa nayi mamakin yadda a kai ciwon nan naki ya tashi, ko dai an miki wani abun ne kinyi kuka?"

Cikin taɓara Lilly tace "please Mamma allow me to rest, am still feeling pain in my chest"

"Ohh God, ko a kira Doctor Kaseem ne?"

"No am ok, i just need rest"

"Ok rest my dear, amma zuwa magariba insha Allah zamuje Asibiti, bana son mahaifinki yaji ciwon nan ya tashi, ban kaiki Asibiti ba yaita sababi"

Lilly ba ta sake Magana ba se gyara kwanciyarta da tai.

(Cikakken sunan Lilly Fatima, itace 'yar Auta a gidan su, su huɗu ne a gidansu, babanta Babban General ne na Sojoji, yana matuƙar ji da ita, kasancewar sunan mahaifiyarsa ya samata, shine suke ce mata little daga baya kuma suka koma cewa Lilly, hakan yasa ba kowa yasan sunanta na gaskiya ba).

Da magariba ba yadda maman Lilly ba tai da ita ba akan suje Asibiti amma taƙi, se ƙyaleta tai.



Sadik kam Kamar yadda ya saba duk dare, hotonta yake ta zooming yana ƙare mata kallo, kamar a lokacin ya fara ganinta, yana jin wani abu yana cigaba da shigarsa a kanta.
Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya kalli agogon wayarsa, ƙarfe ɗaya da rabi na dare, a hankali yai juyi tare da ƙanƙame wayar a jikinsa yana sauke numfashi.
"Allah ka amince min na mallaki Farhan"
Wani irin gumi ne yake tsatsafowa a goshinsa, a hankali ya ajiye wayar ya miƙe ya fito falon su.
Faruk ya tarar yana kallon wani Nigerian Film, kusancin jarumin da jarumar Film ɗin na nuna wani abu na shirin faruwa.
Tsakin da Sadik yai ne yasa Faruk ɗagowa ya kalli in da Sadik yake yace "kai kuma kai da waye?"
"Wannan shirmen da kake kallo mana Sadik ya bashi amsa yana buɗe fridge, ya ɗakko ruwa me sanyi.

"Ai seka tsaya ka gani kan ka yanke hukunci, tunda ba wani abun a kai ba"

Ɗan taɓe baki Sadik yai yace "Ni wannan ɗin ma shirme ne, mutum na zaman zamansa ya kallowa kansa damuwa"

Dariya Faruk yai yace "Allah nawan?"

Sadik ya zauna akan kujera one seater ya ɗora ƙafarsa, a kan ƙaramin teburin dake falon ya kalli Faruk yace "bro, am telling you the truth, wallahi bana iya jure kallon wannan fina finan, a simple Romance can put me in trouble, you understand what I mean"

Faruk yai murmushi yace "So, seka dena kallon Film gaba ɗaya ka koma cartoon"

"Ba zaka gane bane" Sadik ya faɗa yana shan ruwan da ya zuba a kofi.

"Ya zakace ba zan gane ba, i went through same situation as you, kawai Lokaci ne da jiki ke girma, da alamu na zama cikakken mutum shine kawai, amma nan da wani lokaci zaka koma normal"

Ɗan guntun tsaki Sadik yai yace "ni bana tunanin wannan yanayi ne da zan iya fita daga gareshi lokaci guda, duk kallace kallacen fina finai da nayi a baya, bana jin komai se haɗuwata da Wata yarinya a makarantar mu, i really fall for her, gaba ɗaya na kasa gane kaina, nayi ƙoƙarin nusar da Mother ni Aure nake so, amma se ta shareni koma taimin faɗa"

"Hmm ai dole tai maka faɗa, Sadik dudu guda nawa kake ne? Shekarun ka nawa a duniya da har zaka fara zancen Aure? Ni ban yi wannan zancen ba se kai, kasan Aƙidar Gidan nan ko? Boko first before anything"

"Aƙidar banza, ai ba dokar Allah bace, ni wallahi idan aka cigaba da tafiya a haka, ba zan iya wani karatu ba" yai maganar yana tsuke fuska.

Faruk ya tashi daga in da yake zaune, ya dawo kusa da Sadik ya zauna ya dafa kafaɗarsa yace "Sadik, ita yarinyar da kace sanadinta ne ka shiga wannan halin, ba wani abu bane face RUƊIN ƘURUCIYA, wanda yake faruwa a lokacin tashen balaga, wani abune na ɗan lokaci, kuma abun da kake ji kowa ma yaji, amma dannewa ake, kar ka sake wannan feelings ɗin yasa ka rusa Rayuwar ka, kayi ƙanƙanta dafara ɗaukar stress na marital life, just forget about her, focus on your life, da zarar ka samu abunda kake so zaka dena jin wannan son, dan haka ka kula"

Shiru Sadik yai yana sauraron Faruk, a hankali ya sauke ajiyar zuciya, ya ajiye kofin hannunsa, ya miƙe tafi bedroom ɗinsa ba tare da ya kuma cewa komai ba.

Safa da marwa ya shigayi, yana son tabattar da dagaske son da yakewa Farhan RUƊIN ƘURUCIYA ne? Ya rasa dalilin da yasa kowa yake ce masa ai Soyayyar su RUƊIN ƘURUCIYA ce kawai.
Sedai abunda yake ji akan Farhan ya wuce a kirashi RUƊIN ƘURUCIYA kawai, shikaɗai yasan meyake ji a kanta.

Da wannan tunanin ya kwanta, har bacci ya ɗauke shi.


Kwana biyu Lilly ba ta Zuwa school, se ana uku taje, lokacin ta warware sosai, aikuwa tana zuwa su Haseena suka dinga ihu suna rungumeta.

Ture su Lilly tai tace "dalla can marasa mutunci, ba wadda taje dubani a cikin ku"

Yasmin tace "Wallahi yau muke cewa zamuje dubaki, jiya mutumin ki yazo yana tambayar ko kin zo?"

Lilly tace "waye mutumina?"

"Sir Nazir mana" Haseena ta bata amsa.

"Uwar mutumina, ai gayen nan Allah ya sakamin kneel down fa ya sani, na dinga kuka ina roƙonsa amma yaƙi saurarata, seda ya ga dama yace in tafi aji, kawai na faɗi a hanya"

"Dama ya za'ai ya saurareki, ai shi wannan ciwon naki gaba ta kaishi, ya samu abunda yake so"

Da mamaki ta kallesu tace "kamar yaya?"

Yasmin tace "ai ni zan labarta miki, da aka kai ki Clinic ɗin nan, kin kasa numfashi bakinsa yasa a naki yana hura miki iska"

"What, dalla bana son ƙarya"

Haseena tace "to ubanwaye ze miki ƙaryar, Wallahi dagaske ne, ya sa aka cire miki hijjabi daga ke se Long sleep, yaita hura miki iska, a wayance kuma dai kamar dai ba iya hura iskar yake ba" ta ƙarasa maganar suna kwashewa da dariya, banda Lilly da ta haɗe rai kamar zata fashe.

"Allah ya isa na" ta faɗa tana jan tsaki.

Suka sata  a gaba suka ding tsokanar ta suna dariya.


Sunan zaune malamin da suke da shi ya shigo, yai lesson ɗinsa ya gama ya fita, yana fita sega ɗan aiken Sir Nazir yana kiran Fatima Hakeem.

Tsaki tayi, dan a lokacin saura mintuna bakwai a fita break, su Haseena kuwa dariya suka cigaba da yi mata, wanda hakan ba ƙaramin ƙular da ita yai ba.

Haka ta tashi ta tafi Office ɗinsa, sedai ko da taje kallo ɗaya yai mata ya ɗauke kansa.
Wani haushi ne ya sake mamayeta, ta tsaya a tsaye ƙiƙam taƙi Magana, shima ya cigaba da sabgar gabansa.

Jin ƙafafuwan ta na rawa ta gaji da tsaiwar ne yasa tace "Sir gani"

"Gaki, baki iya gaisuwa ba kenan ko?"

Kamar tayi masa tsaki, amma ta dake ta gaishe shi, be amsa yace "me nace miki ranar a Office ɗin nan?"

"Ai bani da lafiya"

"Will you shut up? Maza kije aji ki ɗakko littafinki kizo, in kin ga dama karki dawo"

Juyawa tai ta fita a matuƙar hasale, harda ƙwallar baƙin ciki.

Tana zuwa Class ta tarar da su suna karatun littafin watsewa da suka saba.

Tace "ke Yasmin shine kuka cigaba bana nan?"

"Ba dole mu cigaba ba, yaushe zamu tsaya jiranki?"

Suka cigaba da karatunsu, ta ɗauki littafinta tai waje, dan bata son dalilin da zesa Nazir ya kuma yi mata wulaƙanci.

Babban abunda ya bata haushi, be wuce yadda takasa faɗar abunda yai mata harta shiga halin rashin lafiya ba, da ko ba komai babanta yasa azo ai masa warning koma yasa a haɗa masa jikinsa.

Haka ta cigaba da Tunani, harta je Office ɗin.

Kujerar da ke facing ɗinsa ya nuna mata, ta nemi guri ta zauna.

Ya ɗakko wani littafi ya miƙa mata yace "maza ki duba daga in da kika tsaya da kwafar note ki fara kwafa yanzu Yanzu.

Kamar ta fasa kuka haka ta karɓa, tana jin haushin ajinsu ana can ana karatun Novel ɗin nan ba ita, ya kashe mata break ɗin ta.

Note ɗin da ake binta ba kaɗan bane, dan haka tasan ƙaryarta ta kammala shi a yau ɗin nan.

A hankali ta fara kwafa, sedai tun ba'aje ko ina ba ta gaji, ta fara tunanin me zatayi wanda zesa ya ƙyaleta ta tafi.

Ɗagowa tai ta kalleshi, shirt ce baƙa me gajeren hannu a jikinsa, damatsensa sun cika hannun rigar, sumar kansa zuwa sajensa se shining suke, ta kalli faffaɗan ƙirjinsa ta fara kamanta shi da jaruman da ake siffantawa a cikin book.

A ƙalla yana da kaso sittin cikin ɗari na yadda ake fasalta ƙirar jaruman littafi, ba shi da ƙaton baki ga gashi yaiwa haɓarsa ado. ƙirjinsa zuwa dantsensa ta cigaba da bi da kallo, she just imagine how will she feels if he hugs her?

Ta tuna yadda aka bata labarin yadda ya ɗauke ta da ta suma, da yadda ya bata artificial respiration, nan da nan ƙwaƙwalwarta ta shiga bata wasu lissafe lissafe da hasaso abunda suke karantawa a littafi game da malamin nata.

"Note ɗin zaki kwafa ko kallona zaki cigaba da yi?"

A ɗan kunyace ta dawo hankalinta, amma ta kwaɓe fuska cikin shagwaɓa tace "Am starve'

Ya ɗago ya kalleta yace "oya die here"

Kwaɓe fuska ta kumayi tace "Allah sir am hungry, let me go and eat food"

Drower gabansa ya janyo, ya ɗakko donut da drink, ya ajiye mata yace "oya kina ci kina rubutu"

Ta janyo donut ɗinta ta fara ci, sedai ƙwaƙwalwarta na mata saƙa a Mugun zare game da malamin nata.

A nasa ɓangaren shima yana basarwa ne, amma haka kurum yanzu da yaga yarinyar ƙirjinsa ke tsananta bugawa.

Seda aka koma class, Sannan ya bata damar tafiya, ta ɗau littafinta ta juya ta fara wata irin tafiya, wadda seda ya bita da ido harta fita.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, ya cigaba da aikin da yake.

Ko da ta koma aji har wani malamin ya shiga, dan haka kawai ta nemi Guri ta zauna, tana cigaba da tunanin Sir Nazir ɗin.

Sadik har yaje ya biya kuɗin ɗan maidaidacin hall ɗin da za'ai partyn, duk wani abu da za'a buƙata ya tanada, hatta rigar da Farhan zata saka ya siya. Sedai Farhan na ta fargabar yadda za'ai wannan lamari iyayenta basu sani ba, tana fargabar Idan Asirinta ya tonu da wani idon zata kalle su?.
      Har ƙanan invitation card ya bugo, ya bawa mutane ƙalilan, dan ba gayya yayi ba yadda za'ai komai a tsari ayi a gama.
Ya bawa Farhan invitations yace koda wanda zata gayyata, amma tace baby duk wanda ya gayyata shikenan.

Yau juma'a ta kama ranar da za'a gudanar da murnar zagayowar haihuwar Farhan, sedai gabanta nata faɗuwa ƙirjinta na ta bugawa, tabbas ba dan Sadii bane bijirewa wannan partyn za tai, dan haka nan taji ƙirjinta na bugawa da sauri da sauri da zarar ta tuna.

In da suka saba ajiye Farhan su kai parking, ya kalleta yace "Anjima su Taslim da Khairat zasu zo su ɗakkomin ke, kin riƙe abunda nace ki faɗa a gida ko?" Farhan ta jinjina masa kai jiki a sanyaye.

Yace "good, see you later"

A hankali tasa hannu ta buɗe motar ta fita, ta nufi layinsu tana ta saƙawa tana warwarewa.

Bayan an sakko daga masallaci, Abban Farhan ya dawo gida, taje ta same shi a ɗakinsa suka gaisa Sannan tace "Abba dama..dama maman malamin mu aka kwantar a Asibiti, anjima za'aje dubata shine nake son ka barni"

Abba yace "Farhan bana san yawan fitar nan da kike fa, kiyi masa Addu'a kawai ya isa"

"Ammm...Abba ai ba ni kaɗai zanje ba, a motar gidansu 'yar ajinmu za'aje su zasu zo mu tafi, su dawo dani gida"

"Nifa bana son yawan shishshsigewa 'yan ajin nan naku, kin san dai ba ƙarfinku ɗaya da iyayensu ba, shikenan Allah ya bashi lafiya, ki kula da kanki Allah ya tsare"

"To Abba nagode" ta tashi ta fito daga ɗakin nasa, sedai jikinta a matuƙar sanyaye saboda ƙaryar da tai Masa.

Shi ya sanar da Ummanta anjima za suje dubiya, ta gaya masa.

Ƙarfe uku da 'yan mintuna sega Taslim da Khairat ƙanwar Sadik, sun sha dogayen hijjabai, Taslim nata ƙarewa gidan kallo.

Farhan tai sallama da Umma cikin dogon hijjabi, tabi su Taslim suka fita daga gidan.


Kai tsaye in da za'ai partyn suka nufa, maimakon su shiga hall ɗin partyn, wani ɗaki suka nufa da ita a cikin gurin, Taslim ce take ƙoƙarin shiryata, ta ba ta wata doguwar gown dark blue tace ta shiga toilet ta saka.

Farhan ta dinga juya rigar nan kan ta saka, dan da gani rigar me tsada ce, rigar ta rufe mata ko ina na jikinta, sedai ta kamata tsam a jikinta.

Ta fito daga banɗakin tana kakkare jikinta, Taslim tasa comb ta taje mata gashin ta, ta kawo ribboms ta ɗaure mata shi, su kai mata simple make up, aka samata wata hula nan da nan Farhan ta sake haskawa, kamar ba ita ba tai kyau matuƙa, sedai ita duk a tsorace take.

Seda suka gama shiryata tsaf sannan suka nufi main hall ɗin da za'ai birthday.

Abun mamaki suna zuwa duk an gama hallara, an ƙawata gurin matuƙa, idonta ya sauka akan Mubarak Babba da yake binta da wani irin mayen kallo, take wani Mugun haushin sa da tsanarsa ya sake baibaye ta.

Haɗa ido sukai da Sadik yana waya, ya kashe mata ido ɗaya, ta sunkuyar da kai tana murmushi.

Duk kunya ta isheta, saboda kayan dake jikinta.

Kan a fara Komai Sadik yasa duk wanda ze shigo seya ajiye wayarsa a waje, dan yace be yadda ayi video ko ɗaukar hoto ba, se Camera ɗinsa da ya kawo.

Nan aka shiga shagalin ciye ciye da shaye shaye, amma banda Farhan da ta takure kamar ace ket ta zura da gudu dan fargaba da Zullumi.

Nas shine yake MC a gurin, ya ɗau mic yace  "Kafin mu cigaba da abunda ya taramu, wato taya abokiyar karatu, kuma wife to be ɗin abokin mu shagalin birthday ɗin ta, akwai wani game da za muyi Yanzu a gurin nan, Prince Sadik zan ajiye wasu papers, zaka fito kai da ita zaka zaɓi paper ɗaya, duk abunda ka ɗauka will be the birthday gift for your Beb"

Sadik yace "I already bought the

Please Login or Register in order to submit comment