Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

this year? Jumping zakayi kenan?"

Ya juyo ya fuskanceta sosai sannan Yace  'Khairat, jumping zanyi in kammala secondary School this year insha Allah, saboda Aure nakeso, Aure zanyi nan kusa"

Kwashewa Khairat tayi da dariya tace  'look at you, dan kaga kana da girman jiki? Secondary school fa zaka gama, Yaya Usman ma daza'ayi Aurensa Yanzu, seda yayi PHD, wakake tunanin ze maka wani aure yanzu?"

Ƙurawa khairat ido yayi sannan Yace "kina ganin nayi ƙanƙanta inyi auren ne?"

'ƙwarai kuwa, guda nawa kake zakayi zancen wani aure? Better build your future my friend, and stop talking this rubbish"

Tai maganar tana dariya, ta bar ɗakin.

Sadik ya daɗe a tsaye a gurin yana tunani, sannan ya ɗakko sallaya ya tada salla, bayan ya idar yaci Abincinsa ya kwanta.

Farhan ma harta koma gida, ta shirya ta tafi islamiyya, tunanin Sadik ɗinta ne a zuciyarta, tana tuna yadda yake yawan kyautata mata, amma abun tambayar anan shine, zasu iyayin aure kuwa ita da Sadik? Ita dai tana jin ƙaunarsa sosai a cikin ranta.

Se yamma sosai Sadik ya tashi, yai sallar la'asar sannan ya sakko ƙasa, har yanzu gidan da mutane sedai sun ragu ba kamar ɗazu ba, Yayyansa ne maza zaune tare da Yayar mahaifiyarsu, suna shirya atamfofi a cikin akwati, wanda za'a kaiwa Usman na lefe.

Sadik ya nemi guri ya zauna, yana bin kayan da kallo.

Mamansu Khairat ta kalli Sadik tace "dan ƙaniyarka ina maka magana ɗazu, amma kamin banza ko?"

Yai murmushi Yace 'na gajine, kaina na ciwo, gashi kuma an cika falon, shiyasa ban tsaya ba, wai wannan kayan duk na lefen ne?"

Maman Khairat tace  'eh gasu nan, jibi zamuje mu kai masa insha Allah"

Usman Yace "Autan mother Babu ko kara, ko 'yar sarƙa baka siya ka bani ba, a matsayin gudunmuwa"

Sadik Yace  "gaba ɗaya fa siyayyar nan kaɗan ce akayi maka a Nigeria, duk a waje aka yota, kowa yazo baka kuɗi kawai yake kaida Mummy, kuma kace Sena saimaka abu na  baka duk kuɗinka Bross"

Faruk Yace  'ji ɗan rainin hankali yaron nan dan Allah, duk gidan nan babu wanda ake sakarwa kuɗaɗe kamar ka fa"

Usman yace  "wallahi kuwa, yaron nan kuɗine dashi kamar banza a account bema san me zeyi dashi ba"

Sadik ya karkace ya gyara zamansa akan kujera yace  "aini na dena cin kuɗina, nima lefe zan fara tarawa, next year by now za'a kamin nawa lefen"

Maman khairat tace "Usman, dan Allah makemin mara Kunyan yaron nan"

Sadik yace "Nifa Mummy dagaske nake, aure zanyi nima, zamu yi magana da Daddy idan ya dawo gari, nifa banƙi a haɗa bikina dana Yaya Usman ba"

Umar ne ya kai masa duka Yace "yi mana shiru dan ubanka, mara kunya kawai, ubanwa ze maka auren? Ko dan kana ganinka ƙato haka? Better concentrate on your study, shikansa Bross Usy seda ya haɗa PHD ze aure balle Kai, da yanzu Balagar ta zo maka "

Harar Usman Sadik yayi Yace  "meye wani PHD?  Aure ze hanani karatune? Ai da sauƙi tunda balagara ta zo, Zan baku mamaki kwanan nan.

Ya miƙe yana zumɓura baki ya bar falon.




Ayshercool
07063065680
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨




RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_



                            Page2

Sadik na fita harabar gida, ya tarar abokansa sunzo wai zasu snuka, ya bisu suka fice dan yaje ya sarara.

Corper Nazir kuwa ya sha faɗa a gurin director, saboda ƙararsa da Sadik ya kai, ya dinga mamakin wannan lamari, shikenan dan yaran masu kuɗine baza'a basu tarbiyya ba? Yara duk ba ɗa'a? Ai makaranta ba iya gurin koyon karatu bane, hadda tarbiyya shikenan se a zuba musu ido su lalace, baza'a tsawatar musu ba dan kar iyayensu suji haushi?

Abun ya dameshi sosai, Tare da ganin rashin ma'anar wannan lamari akwai buƙatar a duba, idan bahaka ba rayuwar yaran zata ɓaci a banza.

Da wannan damuwar ya koma gidan daya kama, da yake ba'a camp yake a zaune ba, gida ya kama yake zaune a ciki.

Washegari ya shirya Domin zuwa makaranta, kamar kullum anyi assembly an gama, Farhan nata rarraba ido taga ta ina zata hango Sadik, sedai bata samu ganin nasa ba, ta duba inda yake tsayawa amma baya nan, duk setaji ta damu, haka aka sallamesu suka tafi azuzuwansu.

Sadik kam yau makara yayi sosai, corper Nazir yana harabar makarantar a tsaye yana zazzagawa, dan tabbatar da komai ya tafi daidai.

Motar gidansu Sadik ce ta kunno kai cikin makarantar, har Corper Nazir ze shiga cikin makaranta, yaga zuwan Sadik, dan haka ya tsaya.

Sadik ya fito daga mota, ya rufe motar ya saɓa jakarsa, ze shiga cikin makarantar.

Cikin shouting corper Nazir yace "hey come here'

Sadik ya juyo ya kalleshi, sama da ƙasa kamar kar yaje, sukuma yaje kiran, yana wani bossy walking yaje inda Nazir yake tsaye, Nazir ya kalleshi yace  "why are you just coming?"

Sadik ya kalleshi ya ɗauke kai.

"Check your watch, what's the time now?"

Sadik ya ɗauke kai kamar ba dashi ake magana ba, principal ne ya taho inda suke tsaye, yana faɗin"what's going on here?"

Nazir Yace  'Sir, wai Babu wani penalty na makara kowani laifi, idan yaran nan sun karya doka? Kalli lokacin da yazo makaranta, kuma na yiwa director magana akan haka amma ya nuna min is like you don't punish them"

Principal ya kalli Sadik yace  Yace  "Sadik, why are you late? Baka san lokacin da Yakamata kazo school bane?"

Tura baki Sadik ya shiga yi, yana hararar Nazir.

PC yace  "idan ka sake makara, sena baka punishment me wahala, ɗau jakarka ka bar gurin nan kafin in ci mutuncin ka"

Sadik ya ɗau jakarsa fuuu yai cikin makarantar, yana tunanin yadda ze koyawa Nazir hankali.

Principal ya kalli Nazir yace  "ka manta da director, duk abunda yakama na hukunci a hukuntasu, shi yana la'akari da yadda ze samu kuɗine kawai, shiyasa baya goyon bayan hukuntasu, kuma wasu daga yaran iyayensu nada kuɗi yanzun nan se su ɗaureka, amma dan dai punishment wanda zasu iya, in sunyi laifi kar a saurara musu"

Nan suka cigaba da tattaunawa akan matsalolin yaran.

Koda Sadik yaje ajinsu da malami a ciki Yana lesson, amma babu neman izinin shiga ko makamancin haka, ya kunna kai cikin ajin nasu, yaje gurin zamansa ya zauna, Tare da ajiye jakarsa, fuskar nan tasa a ɗaure yana ta jan tsaki.
Duk ajin suka waigo suna kallonsa, daga bisani malamin ya cigaba da Koyarwarsa.

Sadik be saurari me Malamin ke koyarwa ba, ya kifa kansa akan benci, zuciyarsa cike da jin haushn irin yadda Nazir ke zaƙewa da son cusawa hukumar makaranta wani ra'ayi na daban akansu, dole yayi maganin Nazir.

Malamin na fita su Amin suka zo inda Sadik yake, Nasir Yace"babban yaro ya dai? Meyafaru ne mun ganka Wani iri"

Sadik yayi tsaki Yace  "dan Allah ku rabu dani"

Amin yace "haba Sadik, Ya hakane? Mun tambayeka meyafaru kana wani cin magani"

Banza Sadik yayi musu, suka gama surutunsu 'yan matan class ɗin ma sukazo kan Sadik suna nasu surutun

"Babban yaro waye ya taɓo mana kaine?"

Kamar da Dutse suke Magana, yai musu shiru ƙarshe se haƙura suka yi suka ƙyaleshi.

Farhan kuwa gaba ɗaya ta kasa nutsuwa, ta kasa samun kwanciyar hankali saboda rashin ganin Sadik, ɗalibai kowa yana harkokinsa amma banda Farhan.

Ganin da tayi zaman baze fishsheta ba, yasa ta miƙe ta nufi hanyar ajinsu Sadik.

Tana zuwa gaba ɗaya ta kasa shiga, ta tsaya a waje tana leƙa ajin, ba zata iya shiga ajin ba, saboda na Seniors ɗintane, gashi bata san kowa a ajinba se Sadik, dan haka tana jin nauyi sosai.

Ta window ta tsaya, tana leƙawa dan taga ko zata hango Sadik ɗinta.

"What are you doing here?" Da sauri ta waiga dan ganin me Maganar, Nasir ne abokin Sadik, ya kalleta yace "ko kina Neman Sadik ne?"

Farhan ta ɗan sunkuyar da kai, cike da jin kunya.

Nasir ya ɗan tsaya yana ƙare mata kallo, da jinjinawa mugun jin kunya na Farhan, se dai babu mamaki irin wannan halayyar ga 'ya'yan talakawa, sam basu da wayewa.

Yace "to ki shiga mana, yana ciki ai"

Kamar wadda aka yiwa dole, ta shiga ajin can ta hango Sadik, zaune ya kifa kansa, gabanta ne ya faɗi tai tunanin ko bashi da lafiya ne?

Da ɗan hanzari ta ƙarasa bencin da yake zaune.
Jin mutum a kusa da shi ne yasa ya ɗago da sauri dan yiwa wanda yazo kusa da shi ɗin masifa, sedai kuma yayi tozali da fuskar Farhan.
Ajiyar zuciya ya sauke, bece komai ba.

A hankali tace "baka da lafiya ne?"

"No Farhan, lafiyata ƙalau"

"Amma ban ganka a gurin assembly ba?"

"Nazo a makare ne, kuma wancan corper ɗin ya ɓatamin rai, sena gyara masa zama tukuna"

Farhan tace "me yayi maka?"

"Yana min shishshigine, dan yana saka wannan koɗaɗɗun uniform ɗin na NYSC, idan be kiyayeni ba zan koya masa hankali"

Farhan tace  "kasan meyasa ya sani punishment jiya?"

Sadik ys girgiza mata kai, tace  "wai saboda kaje gurina, ya tambayeni meke tsakanina da kai, shine 'yan ajinmu suka faɗa masa, shine yaita min faɗa ya sani kneeldown"

Sadik ya daki benci yace "har akwai wani sakaran daze sawa soyayya ta ido a makarantar Nan? Wallahi idan mutumin nan be kiyayeni ba sena sa an karairayamin shi"  yai maganar a harzuƙe wanda seda hankalin 'yan ajin ya dawo kansu.

Aminu Yace  "wai kai Sadik meke damunka ne?"

"Wannan Nazirun ne, da gemu kamar soson wanka wallahi ya cigaba da shiga sabgata kota Farhan wallahi sena masa illa"

Farhan ta kwantar da murya tace  "dan Allah kayi haƙuri, dana sani ban gaya maka ba"

Wata cikin 'yan class ɗinsu Sadik me suna Amina amma suna cemata meenal ta taɓo ƙawarta tace  "Taslim, kina ganin wani abu kuwa, wannan budurwar Sadik ɗin akwai iya barikanci, kalleta saliha kuma yarinya amma ta dabaibaye zuciyar ɗan mutane ji yadda take masa magana"

Taslim tace "ke dai Bari, kina gani Tun ɗazu muke tambayarsa meya dameshi, yai banza damu amma tana zuwa ya ɗago kansa, na rasa meya ja ra'ayin Sadik akan yarinyar nan, kaf class ɗin nan Sadik bashi da budurwa,  ya rasa a inda zeyi budurwa se a Jss2, duk wannan iyayin nasa.

Meenal tace  "lallai ma ke ɗin nan, Sadik wayone da shi ya samo yarinya fresh, wadda bata san komai ba ya koya mata sonsa, zeyi tattalin kayarsa kuma ki ƙare mata kallo, yarinya ce amma me ƙirar manya, tana da zubin halitta me jan hankali sosai"

Suka cigaba da gulmarsu a gefe, Sadik kam se banbami yake akan Corper Nazir, Farhan tace  "ni ka dena wannan faɗan ko in tafi"

"Farhan ya bazanyi faɗa ba, yana nema ya kassaramin soyayya, ina ruwansa damu?"

Nasir Yace "Sorry Prince, ai komu ba zamu bari a kassara wannan soyayyar ba, wadda muke saka rana ta shiga kundin tarihi kamar ta su Laila majnun"

Kamar Farhan za tayi kuka tace"dana sani ban gaya maka ba, nace fa kayi haƙuri"

Sadik yai shiru yana cigaba da huci, Farhan tace  "kayi haƙuri mana, dan Allah ka dena fushi Kaji, ka ga malamnmu ne, koba komai ya koyar damu, ka dena zaginsa"

Sadik Yace "ke dalla ƙyaleni, na tsani mutumin nan wallahi"

Miƙewa Farhan tayi zata tafi, jin yadda yayi mata magana a tsawace, ya riƙo hannunta da sauri, wanda hakan ya haddasawa Farhan mummunar faɗuwar gaba, taga kamar kowa suyake kallo.

Tace "ka dena taɓani, meye haka?.

Sadik yace "am sorry, na dena amma dan Allah kiyi haƙuri, zauna"

Farhan ta nemi Guri ta zauna, yace "kiyi haƙuri bazan sake ba insha Allah"

Ta zauna tana ɗan tura baki, taƙi kulashi, ya sake kashe murya yace "haba na face kiyi haƙuri"

Tai murmushi tace  "Na haƙura ai"

Suka cigaba da hira ita da Sadik, yama  manta da maganar wani Nazir.

Har aka koma class Farhan bata sani ba, tana zaune tana hira da Sadik cike da nishaɗi, duk da mafi yawan hirar shi yake mata, ita murmushinta yafi yawa akan magana.

"Ke Farhan!" Sukaji muryar Sir Nazir.

A rikice Farhan ta waiga, dan ji tai an kira sunan nata tamakar saukar Aradu, Kamar yadda ta zata sir Nazir ne ba wani ba.

"What are you doing here? Is this your class?" Ya tambayeta yana zazzaro ido.

Cikin tsoro Farhan ta girgiza kai, alamar a'a  yayinda attention ɗin class gaba ɗaya ya dawo kansu, kowa ya zubo ido.

"Me kikeyi a kusa da namiji a zaune? Ajin ku ne nan? Tashi ki bar ajin nan ki koma ajinku"

Sadik ya fusata ze yi magana, Farhan ta girgiza masa kai, ta tashi da sauri ta fita, Sadik ya tsaya yana kallon kallo da Nazir.

Naziru yai ƙwafa ya fice, yana fita Sadik ya daki benci yana muzurai, Nasir Yace  "easy Prince, kayi haƙuri"

"Mutumin nan yana wuce gona da iri fa, zanyi masa kaca kaca a makarantar nan wallahi"

"Kayi haƙuri, zamu san matakin da zamu ɗauka a kai"

Farhan kam da Kusan gudu ta ƙarasa ajinsu, ai kuwa Nazir ya rufa mata baya, a gaban 'yan ajin ya shiga zazzaga mata bala'i.

"Ke wace irin yarinya ce ne? Abunda kike kin kyautawa kanki ko iyayenki? Gurin wannan ɗan iskan yaron aka turoki? Me kike zuwa gurinsa yi?" Yai maganar yana tsatstsareta da ido.

Farhan ta girgiza masa kai, alamar ba komai.

"Wallahi idan baki shiga hankalin ki ba sena haɗa miki assembly, kuma in kira mahaifinki in gaya masa abunda kike aikatawa, gara tun wuri ki fita harkar wannan ɗan iskan yaron, tun be lalata Rayuwar ki ba"

Farhan tana jin zafin cin mutuncin da Nazir yake mata, sedai jinsa kawai take dan bata tunanin zata iya rabuwa da Sadik,sum sum taje ta zauna a gurin zamanta tana sunkuyar da kai, Nazir na cigaba da zazzaga Mata cin mutunci.

"Irinku ne masu komawa iyayensu da ciki ,ku lalace tunda ƙuruciyarku, saboda RUƊIN ƘURUCIYA na ɗibarku, sun turo ki kiyi karatu amma kina biyewa 'yan iska, a haka gaki kamar saliha amma baki da hankali, in sake ganin kinje inda yake, sena zaneki a makarantar nan"

Farhan tai shiru, ta sunkuyar da Kai tana jin yadda maganganun nasa ke mata dirar mikiya a ƙirjinta, taji zafin yadda yake cin mutuncin ta a gaban 'yan ajinsu, dan seda tayi kuka, sedai sam maganganun nasa basuyi tasiri a zuciyarta ba, dan bata tunanin zata iya rabuwa da Sadik, tun da ita dai bata ga aibun Sadik ba, a barshii da zafin rai dai wasu lokutan da rashin son raini, amma yana da sauƙin kai sosai, sedai ta yanke shawarar zata yi duk me yuwuwa ta nesanta kanta da Sadik ko dan kaucewa cin mutuncin Sir Nazir da dizginsa da kuma gudun kar ya haɗa ta da mahaifinta, dan a duniya tana tsoron Allah, tana tsoron mahaifinta sosai.

Nazir ya gama faɗansa san ransa sannan ya shiga gabatar da lesson ɗinsa.

Har ya gama karatunsa Farhan kuka take yi, dan sam na ta fahimci komai ba har yai ya gama.

Bayan ya fita wata daga cikin'yan ajinsu wadda ake cewa Lilly tazo ta dafa kafaɗar Farhan, Farhan ta ɗago kanta ta kalli Lilly.

"Ki dena kuka ki rabu da wannan ɗan rainin hankalin kinji, ki dena kuka"

Farhan ta jinjina mata kai alamar to.

Koda aka tashi daga school, Farhan bata jira kowa ba ta silale ta tafi gida, Sadik yaita nemanta be ganta ba, haka ya haƙura ya tafi gida, yana mamakin yadda aka yi ta tafi basu haɗuba.

**********

Gudu gudu sauri-sauri haka ta faɗo makeken tsakar gidan, hannunta ɗauke da jakar makaranta, tana zuwa ba tayi wata wata ba, tai jifa da jakar a tsakar gida, ta faɗa banɗaki.
Dattijiwar dake zaune tana mulmula fura, ta kalli jakar makarantar da yarinyar ta jefar a tsakar gida, ta girgiza kai ta cigaba da aikinta, kusan mintuna biyar sannan ta fito daga banɗakin, ta tsaya a tsakar gida ta shafa cikinta tace  "wayyo Allah, fitsari idan ya matseka ba arziki, ina tafe a hanya kamar zanyi hauka, saboda yadda ya matseni"

Dattijuwar ta kalleta tace "zaki zo ki ɗauke wannan jakar da kikayi jifa da ita a tsakar gida, ko kuwa se nayi yaƙi da bakina"

Ɗan tura baki tayi, taje ta ɗauke jakar Tata, ta kai cikin  ɗaki ta ajiye, ta cire duk kayan jikinata, ya rage daga ita se dogon wandon makarantar ta, ta fito tsakar gida tana faɗin "Innarmu, wai yau me aka dafa ne?"

Inna ta ɗago zata yi magana, amma taci karo da yadda yarinyar ta fito tsakar gida.

"Nana waike wace irin sha3 ce ne haka? Kalli fa a yadda kika fito, kowane lokaci za'a iyayin sallama a shigo gidan nan, amma kika fito tsakar gida a haka"

Ummi ta ya mutsa fuska ta kalli kanta tace "to ni innarmu me nayi?"

"Dan ubanki baki san kin fara girma bane? Dubi ƙirjinki kin fara ƙigar dangi, amma kin fito a haka bako Kunya, ko 'yar shimi ba ki saka ba"

"Meye kuma ƙirgar dangi?" Ummi ta tambaya cike da wauta.

Inna tace "kin wuce kin nemi riga kin saka, ko sena taso na iskoki a gurin nan, gaɓuwa kawai ba kya ganin yadda ƙirjinki ya tasa? Amma kike yawo a haka? Karki adana su ki bari su fito a wulaƙance, naga alamar idan banyi dagaske ba, haka zakiyi budurci ba kintsi, 'yar butar uwa da kai kamar gwai gwai"

Ummi ta faɗa ɗaki, tana kumbura baki, dan bata son wannan faɗace faɗacen na Inna, Gashi idan ta tashi yi bata rufe komai, haka za tai ta sakin bayani, ko a gaban waye kuwa haka za tai ta sakin zance da sunan faɗa.

"Sarkin faɗa, ke da waye kuma da tsakar ranar nan kike faɗa haka?"

Cewar dattijon da yake shigowa, jikinsa sanye da Alkyabba.

"Dawa zanyi faɗa banda wannan yarinyar, duk gidan nan wake sani magana banda Nana, yarinya kamar ba'ace mata bari, taɓara da iya shege sinƙi sinƙi a cikinta"

Dattijon yai murmushi Yace "haba ke kuwa, takwarar taki guda, Ki dinga haƙuri da ita, yarinyace har yanzu ke kike ganin girmanta, amma yarinya ce ƙarama"

'ko da yarinta, harda iskancinta wani lokacin, bata taɓa jin daɗi idan bata sani magana ba"

Yai murmushi Yace  "to yanzu dai ba wannan ba, zuwa wani satin insha Allah, gidan Abdullahi  zasu kawo lefen Usman ɗin, ina fatan kina nan kina shiri?"

Inna tace "eh ina shiri, naji yace bikin bada tsawo za'a saka ba, ina ga idan suka kawo Kayan, zan bisu se kuma anyi biki, dan bana son yawan tafiyar motar nan"

But Nana dta fito daga ɗaki da ɗaurin ƙirji tace "Alhaji wai waye zeyi aure ne? Wai su wannan ɗin nan na birni?, wanda basa dariya sosai masu tara gashin nan kamar ƙabilu? 'ya'yan kawun nan?".

Dattijon Ya buɗe baki Yace "yayyen naki ne baki san sunansu ba? Se masu tara gashi?"

"Ni a ina zan san sunansu, bayan ba kula mutane suke ba, kuma ma ba zuwa gidan nan suke ba"

Alhaji ya jinjina kai Yace  "ikon Allah, lallai wannan abu bemin daɗi ba, Dole a tafi da Nana, kuyi kwanakin Tare, dan ta ga 'yan uwanta sosai"

Ummi tai tsalle tana faɗin "yee, zani birni inje asha bikin 'yan gayu dani"

Inna tai tsaki tace "mara hankali, ai idan kikaje ma kallon kwantacciya zasu yi miki, musamman matar Abdullahi, me wa mutane kallon banza"

Alhaji Yace "ai haka nan za'aje da Ita, rashin zumuncin yayi yawa, ace ba tama san sunayen su ba, shikenan ace yaran nan ko garin nan basa zuwa, balle su shaƙu da 'yar uwassu?"

Inna tace  "to ya zamuyi tunda uwarsu bata so? Nace a kai maka furar turakarka ne idan an dama?".

"Eh, a kawomin turaka, ina so idan na sha na ɗan huta, zanyi baƙi da yamma"

Inna tace "to shikenan, Allah ya baka yawan rai, zan kawo insha Allah"

Ya nufi hanyar ɗakinsa, Inna ta tashi, ta wanke hannunta, ta shiga ɗaki, ta tarar da Nana da ɗaurin ƙirji tana shirin Dutse"

"Nana kinyi salla kuwa?"

"Inna ai da sauran lokaci fa"

"To kuma kafin kiyi wanka, ba lokaci yayi ba?"

Nana ta zumɓura baki tace  "wai Inna ba nayi wankan nan da safe ba? Shikenan ni kullum cikin wanka kamar wata tarwaɗa?".

Inna tace "kyaci ubanki, lokaci na nan zuwa da za kiyi medalili, wanka ba wataran da asubar fari, koman sanyi haka zakiyi shi"

"Wankan?" Nana ta tambaya cike da mamaki.

Inna tace  "ƙwarai kuwa wankan da ki ke gudu, kuma dole ki koyi wanka da tsafta tun Yanzu kina gida, gaba nake jiye miki, kuma Yanzu ki ke girma kina kan tashen balaga, warin jikinki daban ze dinga fita, kuma duk wanda ki ka bari yaji wari a jikinki kin faɗo, ze dena ganin mutuncin ki, kuma dan ubanki na sake ganinki da ɗaurin ƙirji Sena makeki, idan baki alkinta abubuwan nan ba haka zasu fito ba tsari, kiyi 'yan matanci amma nono a zube, kizo kiyi aure ba zasu dinga birge miji ba"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, waike Innarmu kiyi ta faɗan magana ba kyajin kunya"

Inna tace  "Naƙi inji kunyar, idan ban gayamiki ba wani a waje zan jira ya gaya miki?, kin tashi kin tafi wankan ko sena zo inda kike? Na watsar da ke"

Nana ta tashi tana bubbuga ƙafa, da takaicin yadda Inna ke sata wanka ba gaura ba Dalili, ta ɗebi ruwa ta tafi banɗaki.

Bayan shigar Nana banɗaki, Inna tace "A kula idan za'ayi wanka, a wanke hammata da kyau, wuya da duk wani lingu....

'innalillahi Inna na haddace wallahi, na haddace ko karatune wannan na iya ke kullum sekin nanata min yadda ake wanka wai?"

'rufemin baki, gara in nanata miki ai, dan banƙi in zuba ruwa in wankeki da kaina ba,wani warin jikin yana faruwa ne daga rashin iya wanka tun a ƙuruciya, in kin gama wankan ga ruwan alumun nan da miski ki shafe jikinki dashi"

Nana ta yiwa Inna banza, dan wannan karatuttukan na Inna basa ƙarewa.

Inna ta damawa Hakimi furarsa, ta shiga kai masa, ta tarar dashi yana dariya, ta kalleshi tace  "lafiya naga kana dariya?"

Yai murmushi yace  "dariya nake miki keda jikar taki, kina takura yarinyar nan da yawa fa"

Inna tace  "a'a ba takura bace, gara in gaya mata ai, duk da Allah be taɓa bani 'ya mace ba, amma ni ban yadda se an sawa yarinya rana, sannan a dinga gaya mata ƙabali da ba'adi ba, tun tasowar yarinya ya kamata a dinga koya mata yadda zata kula da kanta, da yanayin Rayuwar Aure"

Hakimi yai murmushi yace "eh to hakane, amma ai Nana tayi ƙarama da yawa, da wannan karatuttukan naki"

"Taɓɗijan, kai kake ganin tayi ƙanƙanta, ba tayi ƙanƙanta ba, ba dan karatun boko ba, ai da yanzu idan ba'ayi aurenta ba, ana nan ana shirin hakan, kuma karkayi mamaki suna tattaunawa a junansu, yaran zamani ka kallesu kawai, gara in horata da nawa karatun, da wanda za'a karanta mata a waje ta ɗauka"

Hakimi ya jinjina kai yace "hakane kam, naga zasu yi hutun makaranta, shiyasa nace ki tafi da Ita bikin nan, wallahi ina jin banƙin cikin rashin raɓata da jikokina basa yi"

"Ka dena damun kanka fa, ita uwar yaran nata halin kenan, yaranta baza suzo ƙauye ba, dan haka ka haƙura ka bar mata yaranta, shi shine ɗanmu kuma yans zuwa inda muke, meye na damuwa dan yaransa basa zuwa?, Baga Ummi nan Allah ya baka ba"

Ya ɗanyi shiru Yace  "na tabatta da baban Ummi na raye ba yadda ze hana yaransa zuwa inda muke, kin sanni da ƙawa zucin yara, Allah be bani su da yawa ba, duk ya karɓe abunsa, ina ƙaunar yaran nan, irin son da nakewa mahaifinsu, haka nake sansu"

Inna tace "ni dai nace kayi haƙuri, ka maida komai ba komai ba, Ummin nan kawai in Allah ya bamu yawan rai, seka ga ta haysyyafa, ta cika mana gida da jikoki"

Hakimi ya jinjina kai Yace "wai, idan ba wani ikon Allah ba, ina ni ina ganin 'ya'yan Ummi, 'ya'yan jika fa?"

"Eh mana 'ya'yan jikan, ai abun na Allah ne, kai dai Allah ya baka tsawon kwana me amfani Saraki"

Yai murnushi, yana jin daɗin yadda matar tasa take masa addu'a, ko kuma yi masa kirari.

Inna na nan zaune tare da megari, seda ya kammala shan furarsa, ya kwanta sannan ta fito daga turakarsa, tana zuwa ɗaki ta tarar da mutuniyar tata, tana cin Abincin rana.

"Yawwa ta Nana, gaki nan fes dake

Please Login or Register in order to submit comment