Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Inna yace "Inna ba su da tarbiyya kuma?"

Cikin ƙwarin gwiwa, da nuna isa Inna tace "Ƙwarai kuwa, 'ya'yanka ba su da tarbiyya, mussaman me sunan Ƙarami ɗan Autan ka.

Allah ya sani ina ƙaunar yaranka fiye da yadda nake sonka, ka san yadda nake son jikokina duk da ba sa zuwa in da nake, amma hakan ba ze hanani faɗin gaskiya akan su ba.

Abdullahi ka sanya idanu akan tarbiyyar yaranka, kuɗi ba hauka bane ba, kafin kai dubun ka sunyi arziki kuma sun shuɗe babu su a duniyar nan, yana daga cikin sadaka me gudana bayan ran bawa, ya haifi ɗa na gari da ze dinga aikata aikin Alkhairi.

Kana tunanin wannan? Ko kuma neman kuɗin kawai ka saka a gaba, yau kana Habuja, gobe kana gurin wancan gwamana, jibi ka na waccan ƙasar, ka bar mace da tarbiyyar gidanka matar da ita kanta tana buƙatar tarbiyya, wannan ganganci ne haihuwa da damuna.

Ba ina kushe maka iyali bane, ko ƙoƙarin haddasa maka husuma a cikin gida ba, bulaliya nake maka, naga shekaranjiya, naga jiya gashi ana damawa da mu a yau, ko kai da kai boko ka zaga duniya, ba zaka gayamin sanin duniya da zamantakewa ba, bar ganina bagidajiya bafullatanar ƙauye, shekarun da nayi a duniya naga abubuwa da dama, kuma ina iya fahimtar abubuwa da dama.

Dan haka ka kula da iyalinka, ka sa ido akansu sosai ka kula da tarbiyyar su, ka barsu da ingantacciyar tarbiyya da kyakykyawar rayuwa yafi wannan kuɗin da kake tara musu, da basu san ciwonsu ba, sedai su ɗiba suyi ta bushasha"

Tun da Inna ta fara faɗan nan, ya sunkuyar da kai, bece uffan ba seda ta kammala, ya ja nannauyar ajiyar zuciya yace "Insha Allah Inna za'a kiyaye, in Allah ya yadda zan kula kamar yadda ki ka ce"

Inna tace "to Allah ya wuce mana gaba, ya kare dukkan zuriyar Annabi daga taɓarɓarewa da sharrin ƙarshen zamani"

Yace "Ameen ya Allah, Inna nagode Sosai"

Har ya miƙe ze fita tace "fita za kayi ne?"

Yace "eh Inna"

Tace "to zo in fesa maka turare"

Yai murmushi yazo gabanta ya durƙusa, ta ɗakko turare ta feffesa masa tace "yawwa duk da naji kana ƙamshin turare ai gara ka ƙara, ai ƙamshi rahama ne"

Yai murmushi yace "hakane Inna nagode"

Tai murmushi ta cigaba da laziminta.

Maganganun Inna sun damu Alhaji Abdullahi Sosai, duk d aba ta fito ta gayamasa ƙarara meyafaru ba, amma maganganun nata sun tsaye masa a rai sosai.

Se dare sannan aka din ga dawowa daga gurin kamun da aka tafi, wanda zasu kwana a gidan duk suka taho nan gidan, dan a tare motocin suka dinga dawowa.

Wajen ƙarfe sha ɗaya na dare, Mother tayi wanka ta canza kaya, ta nufi sashin Megidanta da coffee.

Tun da taje take zuba masa hira, tana nuna masa hotunan biki, sedai ta lura kamar yana tunanin wani abun ne.

"Yallaɓai ya na ganka wani iri ne? Kai da Yakamata ace kana farinciki zaka aurar da ɗanka na fari"

Kallonta yayi sannan yace "Akwai wani abu da Sadik yaiwa Inna ne na rashin kyautawa"

Haushi ne yakama Mother, wannan takurarraiyar tsohuwar ta isheta.

A fili tace "wani abun tace ya mata ne?"

"No, ba tace min yamata Komai ba, sedai tamin hannunka me sanda a cikin Magana, dan haka dan Allah idan ma da wani abu na rashin ɗa'a ko kyautawa da yake, ki ja masa kunne, nima zan masa magana bana son ranta ya dinga ɓaci akan wani abu"

Ajiyar zuciya Mother tai tace "ni dai iya sani na ba abunda yai mata, sedai kasan ba su fiye jituwa ba, amma zan masa magana insha Allah"

Yace "yayi"

Yana ɗauke kai ta dalla masa harara, gaba ɗaya haushin Inna take ji, ta fiye sa ido da son hanasu rawar gaban hantsi ita da 'ya'yanta.


Aka cigaba da gudanar da biki cikin bajinta, da kuma wadata.

Ranar Dinner Inna tace ba in da Nana za taje, wani irin bikine baza'a fara shi ba se dare dan watsewa, waye ze sa mata ido akanta.

Nana hadda kuka, tana son zuwa amma Inna ta hana.

Faruk ne ya shigo cikin shadda coffee colour, se sheƙi take kamar shine ango yayi kyau sosai.

Part ɗin Mother ze nufa, amma yaga Nana a zaune kusa da Inna tana kuka.

Ya dawo da baya yace "lafiya kuwa? Nana ana ta shirin tafiya gurin biki amma kina zaune kina kuka?"

Duk da tana shakkar Inna amma tace "Inna ce tace ba zani ba"

Ya kalli Inna yace "Inna meyasa ba zata ba?"

Inna tace "bana son abunda baza'ayi shi ido na ganin ido ba, wane irin biki ne za'a tafi wata uwa duniya ayi shi da daddare"

Faruk yace "haba Inna, aina lokaci ɗaya ne, yanzu kowa seya tafi a barta a gida, ai za taji ba daɗi, tashi ki sako kayanki mu tafi tare"

Inna tace "ki tashi daga nan kiga yadda zanyi dake"

Faruk ya ɗan marairaice yace "dan Allah Inna ki ƙyaleta, kinga kuka take fa"

"Ni bani da idon ganin kukan take ai, tayi kukan jini ma"

"Dan Allah Inna ki bari taje, kuka fa takeyi"

Inna tace "A'a yau naga ikon Allah, ka ƙyaleta tai ta kukan mana"

Faruk yace "wallahi Inna bana son inga mata suna kuka, kinga nan gidan bamu da ƙanwa mace, shiyasa idan naga yarinya ƙarama mace nake jin tausayin ta, dan Allah ki bari taje ko ta dena kukan nan"

Ɗan tsura masa ido Inna tayi, ta tuna haka mahaifinsa ma yake, ba ya son yaga mace a damuwa ko ta na kuka, da irin wannan damar Matarsa tai amfani se yadda tai da shi, ta lura Faruk shine me sanyin hali a cikin su, duk da ga irin sunansa amma ba shi da zafi sosai.

Inna tace "Naji, amma sedai muje tare, in sa ido akan ta"

Faruk yai dariya yace "Hajiya Inna agurin dinner"

"Bana wasa da yara, ka sani ƙaniyar ka zanci ni"

Yai murmushi tare da miƙewa tsaye.

Ba'a tafi gurin bikin nan ba se kusan ƙarfe tara na dare, Faruk ya ɗau Inna da Nana zuwa gurin bikin nan.

Inna ta sha mamakin irin tsukewar da 'yan mata da iyayensu sukai, ba bu batun mayafai dama, kowa sabgar gabansa kawai yake yi.

Ga zabga zabagan baligan samari, wanda suka kasance dangin Amarya da na Ango, suna shiga suna fita.

Inna ba ta ƙara tsinkewa da al'amarin ba, seda aka fara cashewa, ba iyaye ba 'ya'ya, ana ta liƙa kuɗi ana raye raye.

matashiyar 'yar galar nan me suna Gimbiya Ameeea ta nishaɗantar da su agurin, da kala kala samfur daban daban na rawa, cike da ƙwarewa da burge al'umma (Wanda be san labarin Amira ba, ya hanzarta neman littafin WUTA A MASAƘA) Daga bisani dj Sultan, ya sanar da zuwan, Maman Ango da Amarya.

Zuwansu ba daɗewa sega Amarya da Ango suma sun hallara.

Masha Allah, sunyi kyau matuƙa shi ya Sanya light blue ɗin shadda, ita kuma ta saka dark blue ɗin less.

Nan fa biki ya fara ɗaukar harama wajen ƙarfe goma saura na dare, gaba ɗaya zaman gurin ya ishi Inna, gashi ba ta san in da zata gano Faruku ba balle tace ya maida su gida ba, dan ba dan ya matasa ba ba abunda ze kawota gurin nan, dama ta zo ne saboda Nana, dan ba zata iya sakinta haka tazo wannan guri, ita kuma tana gida a zaune ba.

Tana cikin tunanin ne, taji ana wata shewa, ta ɗaga kai ta hango wasu gungun samari da 'yan mata sun shigo, suna ta faman iface iface.

Zuba ido tai sosai, ta hango Sadik a tsakiyar su, sanye da coffee ɗin shadda irin ta Faruk.

Mother da ke tsakiyar fili ta nawa Usman liƙi ta hango shigowar Sadik, tsayawa tai tana murmushi, yayin da Dj ya shiga koɗa Sadik ɗin yana masa kirari.

Da hanzari Sadik ɗin ya ƙaraso in da Mother ke tsaye, ya zura hannu a aljihun Rigar sa ya zaro bandir na kuɗi yana liƙa mata.

Juyi Mother ta dinga yi shima tana zuba masa kuɗin, ya rungumeta ana masa hotuna.

Inna kam tagumi tai tana kallon ikon Allah, can kuma aka sanar da cewa ana neman abokan Autan Hajiya Hauwwa,  akan stage dan yiwa abokinsu kara na zuwa bikin Yayansa.

Aikuwa nan da nan suka cika stage ɗin mazan su da matansu.

Ba kunyar iyaye ko manya da ke gurin, suka dinga tiƙa rawa ta fitsara a gurin nan, Taslim ta riƙo hannun Prince tana juya shi shikuma yana murmushi.

Rai a ɓace Inna ta kalli Nana da ta zubawa stage ɗin ido tana kallon ikon Allah, wanda ita kanta Nana a ranta abun da su Sadik ɗin keyi haushi yake bata, gaba ɗaya ba taga tsari ko dacewar Abun ba.

Inna tace "ke dan ubanki kin zura musu ido kina naɗar abunda suke ko? Wallahi ko da wasa naga makamancin wannan a tare da ke, se na shaƙe ki, ki mutu kowa ya huta"

Ɗan tura baki Nana  tayi tace "To Inna ni me nayi?"

"Rufen baki, tashi mu bar gurin nan"

Nana tace "mu bar nan Inna muje ina? Ba mu san hanya ba fa"

"Zaki ta shi ko se na make ki"

Nana ta miƙe suka fita daga cikin hall ɗin, Inna na cigaba da banbami kamar Nana ce tai mata laifin.

Ko fa suka fito sha ɗaya saura na dare, babu ababen hawa ma, nan Inna ta shiga rarraba ido, ta ga ta ina za ta hango Faruk, dan da ya shiga hall ɗin se ta neme shi ta rasa, saboda da alama shike ƙoƙarin sallamar abokan sa da na Usman.

Suna nan tsaye a in da akai parking ɗin motoci, sega Sadik ya fito shida abokan sa, suna hawa motocin da aka kawo su a ciki.

A hakan ma se rashin albarka suke.

Inna se girgiza kai kawai take, cikin sa'a kamar an jefo Faruku, se gashi ya nufo in da Su Inna suke.

Yace "Inna ba dai tafiya za kuyi ba?"

Inna tace "Aikam dan tun ɗazu kai nake nema, ka maida mu gida"

Faruk yace "to shikenan, bari in ɗakko motar"

Suna tafe a hanya, tunanin da Inna take daban har suka je gida.

Sadik kam kwana yai da ɗokin washegari Mother's evening, Farhan za ta zo, ze gabatar da ita a gurin Mother, sedai ayi duk wadda za'ayi.

Da safe yana ta ɗoki, yana son tabattar da zata samu zuwa ko kuwa?

Kasa haƙuri yai, ya ɗakko wayarsa ya kira lambar da Farhan ta kira shi da ita.

A daidai lokacin kuwa Huzaifa yana gidan su Farhan, kasamcewar cousin ɗin ta ne,  ɗan wan Abbanta ne.

Ɗaga wayar yayi tare da yin sallama.

Dumm Sadik yai jin muryar namiji, amma ya basar ya amsa sallamar yace "Amm Farhan nake nema ko tana kusa ka haɗani da ita?"

Huzaifa yace "wace Farhan ɗin?"

"Ta kirani da wannan layin shekaranjiya" Umma tsurawa Huzaifa ido tayi, tana sauraran abunda yake faɗa a wayar, ta ƙara saita nutsuwarta ne jin an ambaci Farhan ake nema.

Huzaifa yace "ok na tuna tayi waya kam, bari in kirata"

Huzaifa ya katse wayar, Umma ta kalleshi tace "ya akai ta karɓi wayarka ta kira wani?"

Huzaifa yace "Ai ban san wanda ta kira ba, kawai ta cemin za tai waya ne?"

Umma ta jinjina kai tace "kirawo ta"

Huzaifa ya miƙe ya kirawo Farhan, wadda ta duƙufa tana bitar Alƙur'ani.

Ta taso ta zo gaban Umma tace "gani"

"Waye yake kiranki a waya?" Umma ta tambayeta ta na kallon idon ta.

Farhan tace "Ni kuma?"

Huzaifa yace "wani ne ya kira wayata yace yana nemanki, wai kin kirashi a layina shekaranjiya"

Gaban Farhan ya faɗi amma ta dake tace "Yayan ƙawata ne, na kirata munyi magana ne, akan bikin da zamu anjima, ban san lambar wa ta bani ba"

Ba tare da ta kalli in da Farhan take ba Umm tace "tashi ki je"

Farhan ta tashi ta koma ɗaki, tana jin yadda wani irin gumi yake bin cinyoyin ta na Rashin gaskiya.

Ita kanta tayi mamakin yadda wannan idea tai saurin zuwa kanta.

Seda Farhan ta bari Umma ta tafi ɗakin Abba, sannan ta fito cikin sanɗa ta shiga ɗakin Umman ta ɗau wayar Umma, ta saka lambar Sadik ta kirashi.

Tai sa'a ya ɗauka, yana ɗagawa tace "call me"

Ba musu ya katse kiran, ya kirata ta ɗaga tare da yi masa sallama.

Ya amsa yace "Princess, kewarki ta dameni, na ƙagu in anjima, fatan dai zaki zo ɗin"

Tai ƙasa da muryarta sannan tace "Ka dena kirana se idan nice na kiraka, lambar da na kiraka ta Yayana ce, wannan kuma ta Umma ce, ka bari sena kira ka seka dinga kirana"

Sadik yace "ok i understand, yaya zaki zo ɗin?"

"Eh zan zo insha Allah, se anjima"

Tai maza ta kashe wayar, ta ajiye ta fita daga ɗakin da sauri.

Da ƙarfe huɗu da rabi na yamma, Farhan ta shirya cikin wani leshinta maroon me sauƙin kuɗi, ba wata kwalliya a fuskarta amma tayi kyau sosai.

Ta ɗakko ƙaton mayafi ta rufe jikinta, ta tafi ɗakin mahaifinta.

Ta tsaya a bakin ƙofa tai sallama, ya amsa mata sannan ta shiga, Umma ma na cikin ɗakin a zaune.

Tace "Abba na shirya zani gurin bikin nan"

Abba yace "Masha Allah, bari in baki kudin mota, sannan dan Allah kar ayi dare, ki kula da kanki kinji, kinga ban taɓa barinki zuwa guri irin wannan ba, ina jin nauyin yaran ne, sunzo hargida sun gayyaceki, kuma ko a Addinan ce babu kyau a gayyaceka walima kaƙi zuwa babu wani ƙwaƙwaran dalili, ki kiyaye kinji"

Farhan tace "to Abba, Insha Allah"

Ya bata ɗari biyu ta sa hannu biyu ta karɓa, ta kalli Umma tace "Umma na tafi"

Umma ba ta kalleta ba balle ta amsa mata, haka Farhan ta miƙe ta fita.

Abun takaicin ta na zuwa ƙarshen layinsu, se ga Sunusi da wani yadinsa, milk ne amma ya koma brown saboda ya dafe.

Yana ganinta ya washe baki yace "unguwa za'ane 'yar Malam"

Kamar tai masa banza amma tace "eh"

"To adawo lafiya"

A ciki tace "Allah yasa"

Ta miƙe ta nufi titi,tana addu'a akan Allah ya bata Sadik, in dai da Sadik kome za'ai ba abunda zatai da Sunusi.

Ko da taje gurin bikin babu wanda ta sani, duk se 'yan uwansu Sadik, ta samu guri gefe ɗaya ta zauna.

Tana nan zaune aka fara cika gurin, kasancewar wuni ne, tun huɗu ake ta zuwa  gurin bikin.

Yauma Inna tare da Nana Faruk ya kawo su.

Gaba ɗaya Farhan ta fara takura kasancewar ba ta san kowa agurin ba, gashi biyar ta wuce ta fara tunanin tafiya gida.

Khairat ce ta shigo hall ɗin, se rawar kai take tana kaiwa tana komowa.

Babu tsammani suka haɗa ido da Farhan, take ƙirjin Farhan ya buga da ƙarfin gaske, dan tuno da abunda ya gaya mata akan Khairat.

Khairat kam murmushi tai mata ta ƙarasa in da Farhan take, cikin iyayi tace "ashe za'a barki ki zo ɗin?"

Farhan ba tai Magana ba se murmushi da tayi.

Khairat tace "yana hanya ya kusa ƙarasowa, ya raka Mother gurin makeup ne" tana gama maganar tai gaba

Mamaki ya kama Farhan, jin wai ya raka mamansa gurin Kwalliya.

A lokaci ɗaya 'yan makarantar su suka shigo, sedai babu Sadik a cikin su, su Nasir ne da Taslim suka shigo.

Farhan ta shiga rarraba idanu dan ganin ta ina za ta ganshi.

Aminu ne ya fara taɓa Nasir yace "Baaba kalli mutuniyar Prince can"

Yana ɗaga kai ya hango Farhan zaune akan kujera.

Ya kwashe da dariya yace "dalla kalleta kamar wata ladaniya, se kace wata babba ga wani uban mayafi"

Suka kuma saka dariya, ka tsaye suka nufi in da Farhan ke zaune, suma suka zauna, suka sakata a tsakiyar su.

Ji tai kamar ƙasa ta tsage ta nutse, Amin yace "Matarmu kinyi kyau fa sosai, ya hutun?"

"Lafy ƙalau" ta faɗa tana sunkuyar da kai.

Miƙewa tsaye tayi, suka kalleta sukace "ina kuma zaki?"

"Gida zan tafi" ta faɗa cikin raunin murya.

Nasir yace "ai yanzu ze zo, ya faɗa yana wani ƙare mata kallo.

Ba ta kuma bi ta maganarsa ba, ta janye kujera ta nufi hanyar tafiya.

Hakan yai daidai da ƙarasowar Motar da Mother ke ciki ita da Sadik.

Ta cikin motar Sadik ya hangi Farhan, cikin hanzari yace "bari in sauka"

Mother tace "meyasa? Ka bari mu shiga mana"

Ai kan ta kuma Magana ya buɗe motar, wanda ya tilastawa direban tsayawa,yai waje da sauri.

"Farhan!"

Ya kira sunan ta da ƙarfi, tsayawa tai ta waigo ta kalli in da yake.

Da sauri ya ƙaraso in da take yace "ya zaki tafi da wuri haka?"

Kamar za tai kuka tace "na fa daɗe a nan, kuma za'aimin faɗa a gida"

Yace "ok am sorry, bari in maida ke gidan, muje ku gaisa da Mother tukuna"

Zaro ido tayi tace "ince me?"

"Ki gaisheta mana"

"Wallahi kunya nake ji" ta faɗa cikin tsoro.

Yai murmushi yace "karki damu, zan gabatar da ke ne a matsayin 'yar makarantar mu"

Ta amince da hakan suka koma hall ɗin, can ya hango Mother harta shiga cikin yamar jama'a, anata gaisawa ga sautin kiɗa da ke tashi.

Hannun Farhan Sadik ya riƙo ya shiga ratsawa da ita cikin mutane, gaba ɗaya se ta ɗan dirirce shikam ko a jikinsa.

Se da ya kaita gaban Mother tukuna, Yace "Mother ga sirikar ki na kawo miki"

Mother ba taji me Sadik ɗin yace ba, kasancewar hankalinta ya rarrabu ana mata Magana.

Cikin jin nauyi Farhan ta gaisheta, Mother ta sa hannu ta kamo na Farhan tace "Sannu 'yan mata, ya gida?"

"Lafy ƙalau" Farhan ta amsa cikin sunkuyar da kai.

Mother tace "mungode sosai kinji, Sadik ka duba motar Mummy ka bata kayan bikin"

Daɗi ne ya lulluɓe Sadik yadda Mother ta mutunta Farhan, nan da nan ya fara wani tunanin dabam, dan a zaton sa ta ji me yace mata.

Har zasu wuce Farhan ta ga Inna, wanda ko ba a gaya maka ba, kasan kakar su Sadik ce, saboda ta san hoton baban Sadik, kuma ta ga suna kamanni.

Durƙusawa tai tana gaida Inna, wadda sam shi Sadik be ma lura da Innar ba.

Inna ta amsa mata cikin sakin fuska, yayin da Nana kuma ta zuba mata ido.

Sadik be so Farhan ta kula Inna ba, dan yasanta da sharhi ƙil se ta tofa wani abun.

A kai sa'a dai Innar ba tace komai ba, su Amin ne suka fara ɗagowa Sadik hannu, amma yai musu alama yana zuwa, Sadik ya dinga nunawa familyn su Farhan.

Seda Farhan taji dama ba ta zo ba, dan wata kunya da ta mamayeta.

Ya je in da aka ajiye kayan biki, ya ɗebo mata fal, ya karɓi mukullin motar Mother a hannun direba, ya tafi maida ita gida.

Suna tafe a hanya, yana tai mata surutu da yadda yai missing ɗinta amma tai banza taƙi masa Magana.

Shima shiru yayi seda sukaje unguwar su, in da suka saba ajiyeta, ta sa hannu za ta buɗe motar, amma taji a rufe.

"Wai fushin me kike?"

"Ba kaine ba, kawai ka dinga nunawa mutane ni, kuma bayan ba haka mu kai da kai ba"

Dariya yai yace "to maza yi kuka, na iya rarrashi ai"

Zumɓura baki tayi tace "buɗe min, kar a ga na daɗe"

Maimakon ya buɗe mata se cewa yai "You look so beautiful" yai Maganar yana tsura mata idanun sa.

Nan ya fara gwagwarmaya da zuciyarsa da ke ta kissa masa wasu abubuwa, a hankali ya miƙa hannunsa da gargasa ta fara lulluɓewa, yatsunsa biyu ɗauke da manyan azurfa ga agogonsa me kyau, ya miƙa hannu ya riƙo na Farhan .

haka nan taji jikinta yai sanyi ta rasa dalilin hakan, kuma ta kasa yi masa magana, ta kasa zame hannunta, ga lokaci yana ƙurewa, kar a ga ta daɗe, amma ta kasa Magana saboda yadda yake binta da kallo, ga wani sihirtaccen ƙamshin druma da na kayan jikinsa ya gauraye motar, hakanan taji hannun nasa ya mata kyau!.



Me so daga farko ya duba AREWABOOKS KO KUMA WATPAD PLEASE.



Ayshercool
07963065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

     

SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.



                          23_24







A hankali Sadik ya sauke ajiyar zuciya, ya saki hannuanta  yace

"Farhan"

A hankali ta ɗago ido ta kalleshi, yai unlocking Motar yace "nagode Sosai da halartar bikin yayana, ki gaisarmin da Abba"

Ba tace masa komai ba, ta ɗau kayan da ya bata ta fita daga Motar, sedai gaba ɗaya taji jikinta yai sanyi.

Haka ta nufi layinsu dan kama hanyar gida.

Se da ta ƙule sannan Sadik ya kunna motar ya koma gurin taron bikin.

Yana komawa su Nas suka cigaba da tsokanar sa akan Farhan, su kai ta iya shegen su san ran su.

Sedai gaba ɗaya jikin Prince ɗin a sanyaye yake, ya dake ya ɓoye halin da ke damunsa, ya dinga biye musu.

Nas yace "Prince, wai ya batun movies ɗin da aka tura maka ne, ka kalla kuwa, kaga yadda ake madarar Love, ba irin wanda ku keyi ba, sekace masu wasan yara, dan Allah kai ba ka ji kunyar ka dinga nuna wannan Yarinyar kace budurwarka ce ba? Kalli kayan jikinta ta jibga uban mayafi kamar wadda zata ja salla....

Wani irin warning glance Prince yaiwa Nas, hakan ya sa Nas ɗin yin shiru.

Daf da magariba amma har a lokacin zuwa ake, har 'yan ajin su Farhan ma sun halarci taron bikin.

Sedai gaba ɗaya Haseena ta kasa sukuni, saboda kyan da Sadik yai a idonta, babban abunda yasa ta tsani Farhan bakomai bane illa kishi, gashi Sadik ɗin ba shi da fuskar da za tai masa shishshsigi, amma harga Allah yana matuƙar burgeta.

Yau ta ƙara tabattar da Sadik ƙyakyawa ne na gaske, dan ba ƙaramin cika ido da kwarjini yai a cikin manyan kaya ba, duk da ƙarancin shekarunsa, Allah yai masa ƙirar manya, dogo ne ga shi da jiki, wannan jikin ne ke ɓoye ainihin ƙuruciyar sa.

Yauma Inna ta ga taɓara kala kala, da rashin ta ido, wanda suka ƙara tsaye mata a zuciya.

Se wajen ƙarfe goma na dare, Sannan aka watse daga gurin bikin.

Farhan da ta koma gida, tayi zaton Umma za tai mata faɗan ta daɗe, amma ga mamakin ta ba abunda Umman tace mata.

Nan ta baje uban kayan da Sadik ya bata, ta bawa Umma, amma Umman taƙi ko kallon in da kayan yake, ƙarshe se bari tai da Abba ya dawo, ta kai masa ya sa albarka, yace suje su raba ita da ƙanen ta.

Ta rasa yadda za tai da ranta da wannan halin ko in kula da mahaifiyarta ke mata, kawai saboda tana 'yar fari, ita tafi danganta wannan abun da kawai ba ta santa ne, dan wannan abun ya wuce kawaici.

Tun da suka taho da Sadik, ta kasa gane me ke damunta, gaba ɗaya jinta take wani iri kamar ba ta da lafiya, ta rasa takaimeme meke damunta, ga Wani yanayi da ta tsinci kanta, tun shigarta motar Sadik duk da ba yau ta fara hawa ba, amma ta kasa tantance yanayin da ta shiga.

Ga shi ƙasan cikinta yana mata ciwo kaɗan kaɗan, amma babu wanda ta gayawa, to wa ma zata gayawa? Ummanta da ba ta son taje in da take? Ko kuma ƙannenta maza?.

Jin ciwon be takura mata bane, yasa ta cigaba da sabgogin ta.

Tun bayan sallar isha'i da tai, ta samu guri ta zauna ta shiga tunani daban daban, a baya ko bisa kuskure Sadik ya taɓa jikinta, se ta nuna masa taji haushi, amma haka nan yau ba ta ji haushin hakan ba, sema kasa manta hannun sa da tayi, da irin ƙamshin turarensa.

Nan ta lalace a gurin da Tunanin Sadik,ba ta taɓa sanin haka akeji a soyaya ba, Sadik ya koya mata son sa.

Ji tai tana son yi masa bangajiya, amma da wace wayar?
Nan ta shiga tunani, can wata dabar ta faɗo mata, ta tashi ta tafi ɗakin Umma, ta tarar da Umman na shirin kwanciya.

Cikin sanyin jiki tace "Umma, dan Allah aron

Please Login or Register in order to submit comment