Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya faru, kin barni wancan Nasir ɗin sun sani a gaba suna sake bani haushi, dan dai ban biye musu bane"

Farhan tace "am sorry, kayi haƙuri dan Allah"

Yai murmushi yace "bakomai, ai matata bata laifi"

Jin maganar tasa tayi wata uwar gundumemiya, wai matarsa ba ko kunya, shi baya jin kunyar wani yaji yana faɗar irin wannan maganganun sam.

Suka jera suka tafi har ajinsu Farhan, a can ya zauna suka dinga hira, yana bata labarin kayan da aka kaiwa yayansa na lefe yace "ji nai kamar in ƙwace kayan nan a kai gidanku, ace na aurenmu ne Ni da ke Farhan"

Shiruu tai ba tace Komai ba, kuma ba ta ɗago idonta ba.

"Farhan, wai meyasa a duk lokacin da nai miki irin wannan zancen kike yin shiru ne, ko dai ba kya sona ne?"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To meyasa ba kya son in miki Wannan zancen?

Tai shiru ba tace komai ba, ya gyara zama yace "Look Farhan, ina da kuɗin da zan iya yin Aure, kuma wallahi ni dagaske nake sonki Farhan, dan Allah ki dena doubting a kaina Please"

Ta sake jinjina masa kai yace "Yawwa,  zaki ci wani abun ne?"

Tace "A'a"

Ya zira hannu a aljihunsa ya ɗakko dubu biyu ya ajiye mata.

Zare ido tayi za tai Magana amma ya haɗe rai yace "shhhh" ya juya ya fita ta bi bayansa da kallo.

A varrender ajinsu Farhan, ya haɗu da Sir Nazir, Nazir ya tsaya ya bishi da ido, Sadik ya haɗe rai sosai, ko kallon inda Nazir yake be ba ya wuce.

Tunani Farhan ta shiga yi akan ya za tai da wannan kuɗin da ya bata?

Ba tai aune ba taji mutum a kanta, tana ɗaga ido ta ga Sir Nazir, yace "wato ba ki rabu da wannan yarn ba ko?"

Ɗan tura baki tai, ta sunkuyar da kai.

"Wai ke dan Allah da ma haka kike da taurin kai ne? Waima meyake gaya miki da ya sa kika liƙe masa haka? Ko kuma me kuke yi da yasa kullum se yazo in da kike?"

Ƙin ɗago kanta tayi da ga sunkuyar war da tayi.

"Kije ki cigaba da biye masa karki fasa, nan gaba idan ya gama morar ki, ze watsar da ke ne, a lokacin ne zaki nadama mara amfani, wannan yaron sam ba tarbiyya ce da shi ba, ɓata miki lokaci ze a banza"

Babban abunda yake ɓatawa Farhan rai be wuce duk wanda suke soyayya a makarantar nan ita kadai ya sawa  ido ba, kuma abun takaicin be wuce yadda yake dizgata a gaban kowa ba, saboda Prince.

Nazir na fita Yasmeen ta ja tsaki tace "nifa wannan mutumin ya fara ɓata min rai akan abunda yake wa Farhan, ya fiye sa ido da takura wallahi"

Lilly tace "ke bake kaɗai ba nima haka wallahi, ni yana burgeni yadda ya iya dressing ga shi kyakykyawa, sedai ya fiye shishshsigi, ni da ni yakewa haka wallahi da tuni nayi maganinsa dan ba zan ɗauka ba sam"

Ita dai Farhan ba tace musu komai ba, can Yasmeen tace "ku akwai labari fa"

Lilly tace "labarta mana muna jinki"

"Wallahi Sister na naji suna hirar Wani book, so romantic ina son in samo Book ɗin nan"

Hasina tace "haba dan Allah ki ɗakko mana mu karanta mana"

Yasmeen tace "dalla a wayarta ne fa, kuma ni ban san sunan littafin ba, amma yadda naji suna hirar littafin na manyan kai ne"

Lilly tace "ke dalla muma manyan kan ne, ki samo mana kawai"

"Ku bari zan ɗau wayar tata in duba mana"

Haseena tace "saura ki shanya mu, kiƙi nemo mana"

"Dalla ni na gaya muku fa, zan nemo mana shi"

Suka cigaba da taɗin su.

Kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki, haka Farhan ta koma gida, zuciyarta fal tunanin Prince, dan lokacin da aka tashi daga school, akwai Malami a ajinsu Prince, dan haka ta samu ta tafi gida.

A gidan ma kasa sukuni tayi, tana son samun wanda zata tatauna Maganar Prince da shi, amma babu ita ba me son yawan Magana bace, ba ta damu da yawan surutu ba, dan haka ko ƙawaye ba ta da su sedai 'yan makarantar su, suma ɗin ba kula su take ba, Ga mahaifiyarta ba ta sakar mata fuska sam, dan haka ba yadda za'ai ta tunkare ta da Maganar Sadik.

Tana son tabattar da waye me gaskiya tsakanin Prince da Nazir, dagaske RUƊIN ƘURUCIYA ce soyayyar da suke? Ko kuma soyayyar da Prince ke nuna mata gaskiya ce?

Gaba ɗaya ta rasa wane tunani ma Yakamata tayi, ta buɗe tsakiyar litattafan ta, ta saka 2k ɗin da Sadik ya bata, tana sake jin wani irin shauƙi yana fizgarta akan Sadik ɗin.

Yauma a gajiye Sadik ɗin ya koma gida, ya kwaso gajiya matuƙa idonsa har lunshewa yake saboda gajiya, gashi yau ne ranar da ustaz ɗin dake masa lesson ze zo.

Ya canza kaya kenan, sega kiran Mother a wayarsa, yana ɗaga wayar tace "Sadik wato seka janyo min zagi agurin wannan tsohuwar ko? Ba zaka zo ka gaisheta ba se raina ya ɓaci kenan?"

Seda ya tura baki Sannan yace "Yi haƙuri gani nan"

Ya ajiye wayar yana cigaba da kumbura baki.

Ya fito ya nufi cikin gidan yana tura baki, ya haɗu da Khairat.

Ya kalleta yace "ke wai kullum sekin zo mana gida ne?"

"Lallai daɗinta ma muma muna da gidan ai"

Murmushi yai ya janyota jikinsa yace "Sorry Sisto na, wasa nake miki fa"

Nana dake hango su ta window ta buɗe baki tace "taɓ ga 'yan iska, Allah yasa Inna ta gani, kut ya taɓa ta taɓɗijan, dama wannan yai kalar 'yan iska"

Inna na zaune a falon Sadik ya shigo, tun da ya shigo Inna ta ƙurawa Sadik ido, cikin majestic walk ɗinsa ya ƙaraso, ya ɗan durƙusa yace "Sannu ina wuni"

Inna ko ƙyafta idonta ba tayi ta kafe shi da ido, dan seda ya fara tsarguwa tace "Sannu Abubakar"

Ya shafi sumar kansa yace "yawaa an zo Lafiya?"

"Ban sani ba, tun jiya ina gidan duk 'yan uwanka sun zo sun gaida ni amma banda kai, kuma ance min kana nan"

"I was little bit busy that's why"

"Ni ba gane wannan Yaren nasaran nake ba ai, wannan wane irin aski ne haka a kanka?"

Ya shafi kan yace "suma ce kawai"

"Wannan uban gashin kamar ɗan daudu? Kai ko damunka baya yi, ni yaushe ka girma har ka tara wannan gashin haka ma? Rabona da kai yafi shekaru uku, uwarku ba zata zo ba kuma ba zaku zo in damuke ba ko?"

Mother tace "A'a ni bana hanansu zuwa, ya za'ai in hanasu Zuwa inda kuke?"

"Idan ba ki hana su zuwa ba ai baki koya musu zuwa ba ko?"

Sadik yace "wannan garin me uban sauro ga ruwan garin ɓata ciki yake ya za'ai mutum yazo"

Inna tace "ba shakka ba yadda za'ai a zo kam, be kamata azo ba kar ruwan garin ya kashe mutum"

Inna tai maganar cikin gatse.

Sadik ya sake cusa baki, Mother tana ta masa signing akan ya kintsa bakinsa.

Inna tace "kafin in bar garin nan ina son a rate wannan sumar ta kanka tunda kai ba mace bane, kuma ba kitso za kai ba"

"Inna wanan sunar na asketa ai ba kanta, wallahi kuɗin da nake kashe mata yafi kuɗin dokunan gidan Hakimi"

"Lallai kam naga alama, tashi kaje Allah ya shirya"

Ya miƙe ya juya abunsa ze fita, sedai sukai karo da Nana tana ƙoƙarin shigowa falon, ta zuba masa miya a riga.

Ya kalleta a Mugun fusace yace "ke! Wace irin dabba ce ke? Baki da hankali ne mahaukaciyar ina ce ke?"

"Kar ka sake cemin Mahaukaciya, kai baka gani ne, kana tafe kana kallon sama"

"Wai dan Allah wannan banzar 'yar waye, daga ina take? Waya kawo mana Mahaukaciya gida, wallahi na tsani ganin Yarinyar nan"

"To kasheni ka huta, fitsararre"

Inna na ƙoƙarin tashi ta ƙarasa inda suke, ya shaƙo hijjabin Nana!



Don't Miss this book wooo, akwai damalamalin cakwakiya 😂😂😂


Domin Sharhi gyara Ko shawara
Ayshercool
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa:     🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️











                            11_12


Tuni Sadik ya shaƙe Nana da hijjabinta, dan da ƙyar take iya numfashi ma, ta ware maƙogwaro ta dinga rafsa uban ihu.

Da hanzari Inna ta yo kansu, Mother ma ta taho da Sauri tana faɗin "Sadik meye haka? Baka da hankali ne?"

Inna tace "saketa kar ka kashe ta"

Zuciyar Sadik se tafasa take saboda takaici, ji yake kamar ya cigaba da shaƙeta seta suma tukuna.

Da ƙyar Sadik ya saki Nana, Inna tace "ba shakka ka kyauta, 'yar uwakka ka shaƙe haka kake cewa ka tsaneta, jinin ka ce fa kuma dan rashin kunya da rashin ta ido, a gaban nawa kake iƙrarin ka tsani 'yar uwaka, lallai ga illar rashin zumunci ai"

Saroro Sadik yai, se yanzu ya tuna in da yasan Nana ma, shi tun asali Nana ba tai masa ba, lokacin da ya santa tana yarinya sosai, tun tasowarta idan suka je ƙauye idan ya ganta haushi take bashi, mussaman yadda take shagwaɓaɓɓiya, ga tsiwar tsiya ga shegen ci, kuma ba'a isa a taɓata ba saboda son da Hakimi yake mata, amma yayi mamakin ganin girman da tai, tayi tsawo sedai halinta yana nan.

Mother tace "dan Allah kiyi haƙuri, wallahi Halin Sadik se a hankali, in kika bibiya be ganeta bane shiyasa"

"Eh ai dama baze ganeta ba, tunda tana ƙauye shikuma ba zuwa ƙauye yake ba, amma tabbas da dangin ki ce ba yadda za'ai yace be santa ba, yayi kyau"

Mother taja hannun Sadik suka fice daga falon.

Inna tace "ke kuma dan ubanki in rashin kunya abun yi ce gobe ma ki sake, se da nace ba zan taho da ke ba amma ya dage in taho da ke, kije ki cigaba da neman Magana da rashin nutsuwa ya illata ki a banza a wofi kan mu bar gidan nan"

Gefe Nana ta koma ta zauna ta na kuka, dan taji shaƙar da Sadik yai mata ba kaɗan ba.

Mother kuwa suna fitowa da Sadik tace  "Sadik meyasa ba ka gudun magana ne? Allah kaɗai yasan iya ɓacin ran da zaka jamin saboda abun da ka aikata, meyasa kake da baƙar zuciya ne kamar haka?"

Cikin takaici Sadik yace "Mother, kalli jikina fa kalli yadda ta ɓatani da miya, tun jiya na ga Yarinyar nan, take zagina ni na manta ma in da na taɓa ganinta se yanzu, gaba ɗayan ta Mahaukaciya ce"

Mother tace "Koma mece ce Ni dai ka lallaɓa mu rabu lafiya, karka jamin magana"

Sadik be kuma cewa Komai ba, ya wuce ya nufi ɓangaren su kamar ya fashe da kuka dan takaici.

Inna kuwa sosai ta cigaba da yiwa Nana faɗa, akan rashin nutsuwa da rashin zama guri ɗaya da ba tayi.

Inna tai faɗanta son ranta, Nana kuma ta ƙule Sosai ta ƙuduri aniyar se ta yiwa Sadik rashin mutunci ta rama abun da yai mata.

Khairat kuwa da akan idonta komai ya faru, ta fi jin haushin Nana, dan ta fuskanci Nanan ba dai rawar kai ba, ga iyayin tsiya.

Nana tana nan a gefen ƙafafuwan Inna, tai zuru tana kallon tv amma ba tv take kallo ba, tana son ta fita ta sha iska, amma tasan tana fita Inna zata zageta tsaf, koma tace zata daketa.

Har la'asar suna nan a Falo, Alhaji Abdullahi ya fito daga sashen sa, ya fito falon, yazo ya samun Inna cikin girmamawa yace "sannu da hutawa Inna"

"Yawwa sannunka"

Ya kalli Nana da tai tsuruu a bayan Inna yace "Mamana, ya na ganki a haka? Na ganki wani iri"

Inna tace "eh nina hanata fita"

'amma Inna meyasa, ko bari tai walwala mana gidansu ne fa nan"

"A'a ba dai gidan su ba, a gabana ba kunya ɗan autanka ya shaƙeta, wai shi be ma santa ba, Wannan rashin zumunci har ina Abdullahi, ace  'ya'yanka basu san ƙanwarsu ba, ko bayan ran mu wa take da su ban da kai da iyalinka?"

Mother kuwa wani takaici ne ya ƙuleta, anyi abun nan ta bawa Inna haƙuri amma ta zaunar da Daddy tana maida yadda akayi.

Daddy yace "subhanallah, Sadik ɗin ne yace be santa ba?"

"Zan masa ƙarya ne? Haka yace be santa ba, amma na tabbatar da a dangin mahaifiyar sa take baze ce be santa ba, gaskiya Abdullahi yana da kyau ka sake sa ido sosai akan iyalinka, wannan halin na Sadik sam be min ba, kun sangarta shi da yawa ba shi da ɗa'a sam"

"Ayi haƙuri Inna, insha Allah za'a gyara"

Ya kalli Nana yace "Amma ayimin afuwa, an takura Mamana da yawa, bari mu ɗan fita tare da ita"

Inna tace "sekun dawo"

Yai murmushi yace "taso Mamana"

Da murna Nana ta tashi, Daddy ya riƙo hannunta, suka fito harabar gidan.

"Mamana ajinki nawa ne?"

Nana tace "Ajina shida, daga wannan hutun zan shiga Sakandire"

"Masha Allah, Yarinya ta girma, Allah ya temaka"

"Ameen" ta amsa tana kalle kallenta.

Alhaji Abdullahi ya ɗakko wayarsa ya nemo lambar Sadik.

Sadik na ɗagawa Daddy yace "kana ina ne?"

Sadik yace "Ina BQ"

"Fito waje ina son ganinka"

Mintuna kaɗan sega Sadik na tahowa, sedai yana hango Nana a kusa da Daddy ya haɗe rai hadda hura hanci.

Ya ƙaraso yace "Daddy gani"

"Sadik, wai baka san Nana ba?"

Sadik ya galla mata harara yace "Eh amma na tuno ta daga baya"

"A gaskiya banji daɗin abunda ya faru ba, Inna ta yi min complain da kai Sadik, gaskiya ban ji daɗi ba"

"Daddy nifa ba abunda nayi, kawai kasan dama ni ta tsane ni, ba ta sona kawai, tana son Dr. Da Faruk amma ni ta tsaneni kuma wannan 'yar ai itama ba ta da kunya"

Daddy yace "ba wannan na kiraka ka gayamin ba, na kiraka ne in ƙara jadadda maka, Nana ƙanwarka ce kamar Yadda Khairat take ƙanwar ka, bana son sake jin kunyi rigima ko ka gayamata wani abu mara daɗi ka ji ko?"

Sadik fuska a cunkushe ya jinjina kai, sedai yana ɗago kai Nana tai masa gwalo, sannan a ɗan sanyaye tace "kuma ma da ya shaƙemin wuyan hijjabi na, seda na dena numfashi, wuyana ma Ni yanzu ciwo yake min, da ƙyar nake haɗiye miyau"

Daddy yace "Ya Salam, kiyi haƙuri ze dena insha Allah, dan Allah ku dena faɗa 'yan uwa ne ku"

Sadik A ransa yace "Allah ya kiyaye wannan me kama da cartoon ɗin ta zama 'yar uwata, shegen bakinta kamar ramin tsutsa'

Daddy yace "bari mu fita shan icecream tare, ku ƙara sanin juna a dena faɗa"

Sadik yace "Please Daddy, i scheduled to be with my friends by 5:00pm, if you don't mind i wanna be with them"

"We must go together!" Shine amsar da Daddy ya bashi.

Sadik kamar yai bindiga, haka yasa direba ya fito da mota suka fita tare, Sadik da Nana a baya, Daddy a gaban mota.

Suna tafe a hanya da ya waigo ya kalli Farhan, se wani baƙin ciki ya mamaye zuciyarsa, Nana kuma suna haɗa ido zata murguɗa masa baki hadda fari da ido.

Ji yake tamkar ya turata waje ta window kowa ma ya huta.

Daddy yace "Mamana, idan kin girma me kike son zama ne?"

Seda Nana tai wani ƙasaitaccen murmushi ta ɗanyi fari da ido sannan tace "Ina son in zama 'yar jarida, in din ga aiki a gidan Radio ina karanta labarai, ko in dinga hira da mutane, in dinga karanta labarai da turanci"

Daddy yace "wow masha Allah, Allah ya cika miki burin ki Mamana, da kin kammala sakandare insha Allah za'a samo tsadajjiyar jami'a kije kiyi karatun insha Allah"

Murmushi tayi tace "Kasan a wace gidan radion nake son in dinga karanta labaran?"

Yace "A'a"

"Ina wannan radion da Hakimi yake kaiwa yana ji da Asuba? Da kuma da rana rana haka"

"BBC ko America?" Abba ya tambayeta yana murmushi, dan ya san Hakimi da son jin BBC.

Tace "Yawwa BBC, kasan da Asuba suke hira da hausa, idan haka rana ta ɗanyi idan aka kunna sekaji suna turancin turawa, to irin wannan nake son nima in dingayi, in dinga labarai da turanci ina maƙale muryata"

Sadik ya ja wani uban tsaki, dan gaba ɗaya Nana ba ta gajiya da surutu, bakinta ko ciwo ba ya yi, tai ta zuba kamar wadda aka kunnawa ashana a ka.

A hankali Sadik yace "sedai aikin gidan radion jakai shi zaki, ba dai na masu hankali ba"

"Ai kai ne jakin" ta faɗa tana hararar Sadik.

Sadik yace "ke da wa kike?"

"Da kai nake, waye yace kace min Jaka?"

"Nike nace miki jakar?"

Daddy yace "A'a ya faɗa kuma a gabana? Ba yanzu na gama yi muku nasiha ba akan faɗan nan?"

Nana tace "cemin yai Jaka"

Sadik a buɗe baki yana kallon Nana, wato bayan hauka hadda makirci ma Nana ta iya, in ba haka ba yauhse yace mata Jaka.

Daddy yai ta musu faɗa, yayin da Nana ta cigaba da gallawa Prince harara hadda murguɗa baki.

Suka je wani babban store, Daddy ya saiwa Nana kayan ciye ciye, sannan suka nufi komawa gida, Sadik be kuma cewa komai ba, Nana ne da Daddy suke ta hirar su tana masa shirme kala kala yana biye mata.

Alhaji Abdullahi yana da son yara sosai, amma baya sha'awar ya tara su da yawa, sedai duk in da ya ga yaro ƙarami yana jansa a jiki ya kyautata masa.

Se daf da magariba sukaje gida, Nana ta rungumi kayan da aka siyo mata ta kasa da gudu.

Masaukin su ta nufa kasancewar ba ta ga Inna a falo ba, tun daga waje take ƙwalawa Innar kira, sedai tana shiga ɗakin kallon da Innar tai mata yasa ta nutsu.

"Gudun me kike yi haka?"

"Bakomai"

"Ban hanaki wannan guje gujen ba, a Wannan sakarcin naki kika zubawa wancan yaron miya a jiki, shine yanzu ma kike maimaitawa ko? Bari in sa a kira Hakimin ya turo a ɗauke ki a maida ke gida"

"Dan girman Allah kiyi haƙuri, na dena ba zan ƙara ba"

Inna tace "da dai halinki ne ban sani ba, kiran me kike min?"

Nana tace "kinga abunda aka saimin"

Inna tace "kince masa kin gode dai ko?"

"Eh na masa godiya"

"To amma dai ki dena wannan guje gujen"

"To na dena insha Allah"

Da magariba ma Daddy yasa Sadik a gaba sukaje masallaci su kai salla, suna tafe yana masa Nasiha akan haƙuri da son zumunci, yai masa faɗa sosai yace masa Inna ba tsanarsa tai ba, amma ya dinga zuwa yana gaida Inna.

Shi dai Sadik be ce komai ba, yai shiru yana sauraren Daddy, amma shi duk wani abu da ze haɗa shi da Inna ba so yake ba, saboda ta fiye ƙaƙalen abun da za tai faɗa.

Da safe ya shirya tsaf ze tafi Makaranta, ya tuna kashedin Daddy, ɗan gajeren tsaki yai ya ɗau jakarsa ya kai mota, sannan ya tafi cikin gida.

Ɗakin Mother ya fara zuwa, yaje ya gaisheta, ya zauna yai breakfast sannan ya fito, ya nufi ɗakin Inna.

Yana zuwa ba Sallama ya shiga ɗakin, ya tarar Inna tana lazimi, Nana kuma nata bacci akan gado.

"Ina kwana" shine abunda ya faɗa a taƙaice.

Inna ta ƙare masa kallo sannan tace "lafiya ƙalau"  tana amsawa ya  miƙe ya bar ɗakin ba tare da ya kuma cewa komai ba.

Yau ya makara sosai a makaranta, dan har an kammala assembly sannan yaje school ɗin, miƙewa yai da nufin ya tafi ajinsu, yaji an masa tsawa daga bayansa.

Tsayawa yai ya waiwaya yaga wane ke masa wannan ihun haka.

"Why are you always coming late ne?"

Sadik ya watsa masa harar ya gyara jakarsa, ya cigaba da bin Nazir da kallon banza.

"Am i talking to robot? Ba Magana nake maka ba?"

"To me kake so ince maka, nifa gaskiya kana takuramin, ina ruwanka dani ka bi ka samun ido ka addabeni, kamar nikaɗai ne ɗalibi a makarantar nan, gaskiya bana son haka ka fita a sabgata na gaya maka"

"Ni kake gayawa haka?"

"To waye kai da baza'a gaya maka ba?"

Yana gama maganar ya nufi ajinsu yana tsaki.

Nazir yabi Sadik da kallo yana jinjina rashin tarbiyya na ɗaliban makarantar.

Yana zuwa ajin nasu ya tarar ba malami a ajin, kowa se harkar gabansa yake, gaban aji kuwa Nas ne da wata 'yar SS3 suke wani dancing challenge ana musu video, se ihu ake ana musu tafi.

Sadik ya ajiye jakarsa ya zauna, yana kallon su Nas, Nas ya kalleshi yace "Prince, ranar bikin Brother ɗinka Akwai casu wallahi, gaskiya yakamata ka shirya mana special party iya na 'yan school ɗin nan"

Sadik yai murmushi yace "nayi wannan tunanin nima, dole ma ayi special party da za'a gyagije, kan kuzo Dinner bikin"

Amin yace "idan hakane kuwa, na ga tallan wasu wanduna, Yakamata muyi order ɗinsu latest crazy jeans masu kyan gaske"

Sadik yace "nunamin in gansu"

Nan suka zauna, Amin ya nuna musu wandunan, Sadik yace "gaskiya sunyi kyau, ni blue ɗin nan nake so ɗan 15k ɗin nan, ku kuma zan muku order na 10k ɗin nan kuyi ankon su"

Shewa suka ɗauka a gurin, Taslim tace "omo What do you mean? Mu ɗin kuma fa"

Sadik yace "in dai zaku sa se ayi order da ku"

Meena tace "mw ze hana? A siya damu"

"Shikenan duk wanda ze je partyn, a saka order da shi, zan sa a bugo riguna polo, amma kowa siyan riga ze dan ubanku"

Dariya su kai, Nas yace "nasan iya wuya ba tafi  5k ba, na saiwa mata goma riguna, amma fa se zafafa wanda suka cika mata, wadda idan ta saka kayan nan za'a ga kaya"

Taslim ta buga wani uban ihu tace "yeee ina cikin wanda za'a saiwa riga ko ba'a so, dan na kai mace wallahi"

Nas yace "ba ƙarya muma mun seda ai"

Shewarsu suka cigaba da yi, suna ihu, suna cigaba da tsara rashin jin da za suyi a gurin party.

Knocking ɗin ƙofar ajin akayi, Sannan aka shigo.

Director ne ya shigo, shida wasu 'yan bautar ƙasa, maza uku mata biyu, sedai matan kiristoci ne, dan kansu ya sha ƙarin gashi.

Tsit sukayi suka gayara zamansu, Director yace "my dearest And beloved student, can't you greet?"

Seda yai Maganar, sannan suka gaishe su gaba ɗaya.

Nan ya gabatar musu da 'yan bautar ƙasar nan, a matsayin sababbin malamai.

Nan suka gabatar da kansu ɗaya bayan ɗaya ga 'yan ajin, bayan sun gama gabatar da kan nasu ne, Director da kansa ya dinga gabatar musu da ɗaliban da kansa, kowanne ya gabatar da shi da matsayin mahaifinsa.

Seda suka kammala yai musu jawabin da ze musu, akan su bawa malaman haɗin kai, dan samun ilimin da ya dace.

Meena ce cikin harshen turanci da iyayi, ta wakilci 'yan ajin ta yi musu barka da zuwa, da tabattar musu da za su basu Dukkan haɗin kan da suke buƙata, dan gudanar da aikinsu.

Wani fari daga cikinsu wanda ya gabatar da kansa a matsayin Nura daga Kogi state, shima cikin harshen turanci ya wakilci 'yan uwansa, yai musu godiya da irin karɓar da a kai musu.

Daga nan kuma suka bi Director suka fita suka nufi wani ajin.

Suna fita Meena tai murmushi tace "Subhanallah"

Taslim tace "ke lafiyarki kuwa?"

Meena tai murmushi tace "Taslim kinga abunda na gani kuwa?"

"Me kika gani?"

"Wallahi I fall for that guy"

"Wane guy kuma?"

Taslim tai maganar tana kallon Meena.

"That fair and tall Man, Nura looking very beautiful and energetic, wallahi yai min"

"Ke bana son iskancin banza fa"

"Ke wallahi ba ƙarya nake ba, before nafi ganin kyan corper Nazir, Amma yanzu naga abunda zuciyata ke so wallahi"

Taslim tace "Nifa daɗina da ke 'yar bala'i ce ke, ki rage leƙe leƙe wallahi"

"Ba wani leƙe leƙe ƙyaleni kawai"

Nasir kuwa cigaba da batun bikin yayan Sadik sukayi.

Yau Farhan ba ta zo gurin sa ba, dan haka da kansa ya kuma tafiya nemanta, sedai ya tarar ta kifa kanta akan benci, kamar me bacci.

Ƙarasawa yai a hankali, ya ɗagota da ga kwanciyar da tayi.

Hakan ya firgita ta sosai, ta shiga rarraba ido amma ba tace komai ba, yace "Am sorry na miki laifi, na firgita ki gashi na taɓa ki ko?"

Ba ta masa ba, ya samu guri ya zauna daf da ita yace "Honey meke damunki ne? Naga idonki yai ja"

Ji tai kamar Sadik ya taɓo mata inda yake mata ƙaiƙayi, tana da damuwa But she has no one to discuss with, she's developing some changes in her

Please Login or Register in order to submit comment