Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

birthday gifts for her"

"Wannan ai kai da ita ne, wannan kuma game ne kawai"

Sadik yace shikenan ya taso shi da Farhan, Zuwa tsakiyar hall ɗin.

Aka zube takaddu da aka ninke a kan tebur akace Sadik ya zaɓa.

Yasa hannu ya ɗakko takadda ɗaya, Nas ya karɓi takaddar ya buɗe, take yai shouting "wow, this is an amazing Love game, Prince takaddar da ka ɗakko tace :you will kiss her for good 3minutes as her special lovely, birthday gift"

Ƙuuuu cikin Farhan ya kaɗa, ta fara gumi ta zubawa Sadik ido taga reaction ɗin sa.

Girgiza kai Sadik yai zeyi Magana, amma suka ƙi bashi dama, suka kaure da shewa da ihu.

Nas yace "zamu gani, as a young man abokin namu ya cika namiji ze iya kokuwa ragone haryanzu yaro ne? Ita ma beb ɗin zamuga can she sacrifice to make him happy, zata yadda dan ganin ba ta bashi kunya ba? Ko kuma zata sa yaji kunya a gaban abikansa, Yau dai zamu tabattar namijine ko kuma maza ya rako? Ya kai mutum ko kuwa haryanzu be wuce goyon Mother ba yaro ne"

Ire iren wannan maganganun na Nas, suka shiga tunzura Sadik, dan sosai yake jin haushin kalmar yaro da suke kiransa da shi wasu lokutan.
Dan haka kai tsaye ya fara takawa a hankali yana tunkarar in da Farhan take.
Nan da nan suka ɗau tafi da shewa a gurin.
Yayin da ita kuma ta shiga zazzare ido, tana jan numfashi da ƙyar!

Kome ze faru? Akwai cakwakiya da tarin darussa me yawan gaske, gefe ga Lilly da Sir Nazir, ga Nana da kakarta RUƊIN ƘURUCIYA karku bari a baku labari yanzu aka fara.

Da fari book1 naso in baku free kamar yadda mukai a AƘIDATA se ku sai 2, amma an maida ni gantalallliya, ina posting ba kwa Comment kuma kuna karantawa, dan haka zan cigaba da sawa a Arewabooks, me son cigaba ya siya a can, me buƙatar ƙarin bayani yai min magana ta lambata.

Iya wanda sukai payment tunda fari su zan cigaba da turawa ta what's app, nagode ina Alfahari da ku masoya a duk inda kuke.

Taku har kullum Ayshercool.

Domin gyara Sharhi ko shawara
07063065680.


Share please 🙏
[6/4, 9:58 PM] Jakadiyar Arewa: SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.                   



                              31

A hankali ya ƙaraso in da Farhan ke tsaye, yasa tattausan hannunsa ya riƙo nata, ya matse a hannunsa ya kalli cikin idonta. Hakan ya saukar mata da kasala ta sunkuyar da kai daga kallonsa saboda kwarjinin da yai mata.

A hankali cikin wata irin murya da ita kaɗai take jin meyake cewa yace "A karo na biyu bayan neman soyayyar ki, zan nemi Alfarma a gurinki Farhan, dan Allah ki amince na gaji da abunda suke min akanki Please Farhan"

Shiru tayi tana jin yadda zuciyarta ke wani irin bugawa, gumi keta keto mata kota ina, ba ta gama yanke hukunci ba, taji Sadik ya haɗata da jikinsa, ya haɗe bakinsa da nata.

Wata irin tsuma jikinta yake yi, ta rasa gane a wani yanayi take, tsoro ko kuma haushin Sadik, duk da yadda Sadik ɗin ya riƙeta gam, amma ji take tamkar zata faɗi ƙasa, dan haka ta sa hannu ta rirriƙe shi karta faɗi.

Wani irin ihu da shewa suka ɗauka a gurin nan Gaba ɗaya, seda mintuna uku suka cika cif sannan Sadik ya cika Farhan.

Idanunta sunyi rau rau kamar za tai kuka, se ajiyar zuciya take kamar wadda tai gudu.

Nan akaita tafa musu, Nas yace "Weldon gaskiya abokinmu da his wife to be, kun burge kun ƙayatar kuma ka tabattar mana da cewa kai....." Se kuma yaƙi ƙarasawa.

Aka yanka cake amma sam Farhan hankalinta baya jikinta, ji take tamkar ta aikata wani gagarumin zunubi da Allah baze yafe mata ba, take taji nadamar zuwa gurin partyn ta baibaye ta.

Da sauri ta silale ta tafi in da aka shiryata, ta cire rigar jikinta ta ɗau kayanta ta saka, wasu irin hawayen nadama suka shiga zarya a fuskarta.

Ta fito harabar gurin tana ƙoƙarin fita Sadik ya biyota yana ƙwala mata kira, amma taƙi tsayawa, cikin hanzari ya koma ya ɗakko mota, yaja ta da gudu yabi bayanta.

Su Nas kuwa dariyar mugunta suka dinga yi, Amin yace "wannan ne karonsa na farko da yayi, amma kamar ƙwararre dama can a matse yake, da haka da haka dai"

Babba yace "Aiku kuka ɓata abun da kuka hana ai amfani da ƙwayar nan wallahi"

"Dan ubanka idan anyi amfani da ƙwaya muyi yaya da su a gurin nan? Kuma ka san ba komai ake bashi ya karɓa ya ci ba, amma sannu a hankali se mun sa shi a layi"

Amin yace "hakane, Amma a hakan ma muny nasara ai"

Suka cigaba da dariyar mugunta.

Wani wawan parking Sadik yai a gaban Farhan, ya sakko yana faɗin "Farhan meye hakane kikeyi? Ki tsaya in maida ke gida mana"

Cikin kuka ta kalleshi tace "ba zan tsaya ɗin ba nika ƙyaleni"

"Ba zan ƙyalekin ba, ki wuce mu tafi"

"Bazan wuce ɗin ba"

Fizgota yai da ƙarfin gaske ya dannata a mota, yaja motar da gudun tsiya ya bar gurin.

Sosai Farhan take masa kuka iya ƙarfin ta, amma be saurareta ba, seda ya dangana da unguwarsu, sannaan yai parking.

Ya kalleta yace "Farhan me nai miki hakane?"

Wani irin mugun kallo tai masa, ta fara ƙoƙarin buɗe motar, amma yai saurin cewa "ok i understand, dan Allah kiyi haƙuri nayi kuskure amma hakan shine mafita kawai a gareni"

Buɗe motar tayi ta sauka, ta nufi lungun gidansu da sauri.

Sadik ya dafe kai ya jingina da motar yana dana sanin biyewa su Nas.

Ta samu guri ta zauna ta sha kukanta, kafin daga bisani ta goge hawayenta, ta tashi ta nufi gida, tan daf da shiga gidan sega Sunusi, yana ganinta ya washe baki yace "me sunan larabawa, daga ina haka?"

Ko saurararsa ba tayi ba, ta shige gida sedai tun a soro ƙirjinta ke bugawa, gani take tana shiga Asirinta ze tonu.

Ta daɗe a soron a tsaye sannan tayi sallama ta shiga, Umma na tsakar gida tana tankaɗe, ta ɗaga kai ta kalli Farhan, ta amsa sallamar ta maida kai ta cigaba da abunda take yi.

Dama hakan umman take mata tun a baya, amma wannan karon se ta tsargu ta ga kamar Umman na san karantar wani abu a tare da ita.

Ta daɗe a tsaye sannan ta shiga ɗakinta, tana shiga ta nemi Guri ta zauna ta cigaba da kuka, wai yau ita Sadik yasa bakinsa a nata a gaban jama'a ba kunya bakomai, shikenan ya zama ɗan iska itama yana son ya maida ita.

Duk da ta cire wancan kayan, amma natan ma da ta mayar ƙamshin turarensa suke, cikin hanzari ta tashi ta cire kayan, amma ta fuskanci ba iya kayan ne keyi ba, jikinta ne yake ƙamshin turaren nasa.

Addu'a ta dinga yi akan Allah yasa kar Asirin ta ya tonu, a gane in da taje da abunda ya faru.

Har zuwa dare, amma taƙi sakin jikinta ta kasa sukuni, ga damuwa da fargaba duk sun cikata.

Ko yunwa ba taji balle taci Abincin dare, haka taje ta kwanta, hakan be damu Ummanta ba balle taji ba'asin dalilin ƙin cin Abincin nata.

Sosai Sadik ya damu da yadda Farhan tai ta kuka, nadama duk ta bi ta lulluɓe shi da dana sanin biyewa abokai, ya dinga tunanin ko a wane hali take? Ko ta dena kukan Allah masani.

Sedai wani ɓangare na zuciyarsa ya kasa tantance nishaɗi yake ji ko kuwa? Abunda ya faru tsakanin su yai matuƙar tsaye masa a rai, he really enjoys it, abunda ya daɗe yana kwaɗayi ne dama, sedai damuwar da ya ganta a ciki ya hana shi sakewa yaji nishaɗin yadda yakamata.

'Auta yau ina ka shiga ne, for the whole day ban ganka ba, ba ka zo inda nake ba, rabona da kai tunda ka tafi school"

Beji shigowar Mother ba sam, se maganar ta da ya ji, a hankali ya ɗan gyara kwanciyarsa yace "bakomai Mother"

"But it seems like something is going wrong somewhere, na ganka wani iri"

"Bakomai kaina ne yake ɗan min ciwo, kuma na sha magani"

"Naga Abincin ku a falo, kaɗan aka taɓa kaci kuwa?"

"No, naje gurin friend ɗina bayan sallar juma'a a can nai lunch"

"Anyway shikenan, idan kan be dena ciwo ba se a tafi Asibiti"

Ya jinjina mata kai tare da lumshe idanunsa, ina ma ba weekend za'a shiga ba ya samu ya kuma ganin Farhan, ya rarrasheta.




A ɓangaren gidan dr. Kuwa wato ango sha guɗa Usman, Amarya ta fara fuskantar ƙalubale daga gareshi, duk da irin tarin soyaya da sukai a waje, ta kasa gane kansa yadda yakamata.

Usman wani irin mutum ne me murɗaɗɗen hali, gani take kamar ta dena burgeshi gaba ɗaya, da yawa wasu halayen bata san yana da su ba se yanzu, miskili ne na gasken gaske, idan har tai masa laifi ko zata mutu baze ce mata kin min laifi kaza ba, sedai tagavya canza gaba ɗaya ga zuciyar tsiya, nan da nan damuwa ta isheta, taga tamkar canza mata Ussyn a kai ba shine wanda sukai soyayya ba.

Wayarta ta ɗakko ta fito falo ta zauna, ta buɗe ta shiga contact ɗinta ta fara duba lambobi, tana zuwa kan wata lamba da aka saka my other half tai ajiyar zuciya da alama, lambar take nema.

Nan take ta dannan kira ta shiga sauraren a ɗau wayar.

"Salamu Alaikum"

Jidda tace "wa'laikum salam, ba dai bacci kike ba?"

"Wallahi ba bacci nake ba, nayi aikin gida ne na gaji, ya akayi ne Amarya?"

Jiki a sanyaye Jidda tace "Besty dama haka auren yake?

"Kai Jidds, yaushe a kai Auren da kike wannan zancen?"

"Besty na kasa gane kan dr. Gani nake kamar an canzamin shi, gaba ɗaya na dena burgeshi, duk rawar kan nan da yake a kaina babu, in yi kwalliya in tsuke, amma ko kallo ban isheshi ba na rasa meye matsalar" ta ƙarasa maganar cikin damuwa.

Wadda ta ke kira da besty ta gyara zama tace "Jidda kenan, lokacin da nake miki gargaɗi ina ɗoraki a hanya gani kuke Kamar ban waye ba, ban iya soyaya ba, ta yaya ba zaki gundure shi ba, bayan tun kuna waje kan kuyi Aure kin saba tura masa hotunan ki da ƙananan kaya, har video Call kuke da sleeping gown a jikinki, to me zaki da zako burgeshi kuma? Muna school idan yazo hugging ɗin sa kike, you even kisses his cheeks, idan nai Magana se kuce ni 'yar ustazai ce, to ga abunda nake gaya miki nan, abunda zeyi ɗokin kin gama nuna masa a waje, to what next kuma?"

Cikin sanyin jiki Jidda tace "hakane besty, wallna gani, kuskure dai na riga nayi shi, amma yanzu meye mafita, ke kaɗai na gayawa halin da nake ciki"

"Mafita ɗaya ce, ke dama ɗabi'arki ce zama da English wears kullum kamar 'yar turawa, tunda he's no more appropriating ita, ki koma masa ƙabilarki ta Hausa Fulani, ki duba kayan lefenki ki dinga masa wankan atamfa da leshi, idan yaso ki dinga saka English wears ɗin lokaci zuwa lokaci, Sannan shaƙuwar da ku kai a waje kar ta sa ki dinga kallonsa kamar mate ɗinki, ko ki dinga masa magana ba wani respect, no matter how close you are to each other, he deserves a respect from you shi namiji namji ne, ki dena wannan maganar taki cikin gadara, ki fara da jarraba wannan mu gani, se muga meye next abun yi"

"Ka besty i love You lodi lodi, ina yinki Sisyna, insha Allah zan jarraba Allah yasa a dace"

"Ameen Allah ya daidaita, kice ina gaishe shi"

"To zeji insha Allah"

Jidda ta fara tunanin maganganun bestyn ta, wato duk abun nan da suke a school suna ganin wayewa ce ashe yana da negative impact a gaba? Dama duk abun nan da take dan burge Usman kuma a kirata wayayyiya ze zo ya dena burgeshi? In Kuwa hakane Lallai a rayuwar ƙuruciya ana tafka shiirmen da ze zo ya zamewa mutum abun dana sani a gaba.




Daga Sadik har Farhan sukuku su kai Weekends ɗin, damuwar Sadik ɗaya kukan da suka rabu tana yi, ya dimga fatan Allah yasa karta rabu da shi a dalilin abunda ya faru.
Sedai baze iya misalta zallar nishaɗin da tsananin shauƙin soyayyar da ya shiga ba, a lokacin da yake sumbutar Farhan, wani abu ya dinga ji from no where yana ratsa ilahirin jikinsa, dan gaba ɗaya mantawa yai da batun wani ƙyanƙyami ko wani abu me kama da haka, hakan ya ƙara kwaɗaita masa son Auren Farhan, sabida wani irin sonta da ya ƙara shigarsa.
Amma ba ya jin ze kuma yadda ya aikata makamancin wannan kuskuren, dan shi kansa yayi nadamar biyewa su Nas ya aikata abunda be taɓa aikatawa ba a rayuwar sa.

Duk yadda ta so jin tsanar Sadik a ranta saboda abunda yai mata amma abu ya gagara, sam ba taji ta tsane shi a zuciyarta ba, mussaman idan tai la'akari da shima be san abunda su Nas suka shirya ba, sedai a jikinta tana jin abunda suka aikata ɗin ba daidai bane, kuma kasancewar sun aikata a gaban mutane, ba za'a taɓa dena kallon su da abun ba.

Ba zata iya misalta yanayin da ta shiga a lokacin da abun ya faru ba, dan Tamkar a mafarki haka ta dinga ganin lamarin, kuma ta kasa tantance halinda ta shiga, saboda taji wani abu da jikinta be taɓa bata ba a tsawon rayuwarta se a wannan karon da abunda ya faru ya faru, lokaci lokaci idan ta tuna abunda ya farun ta kanji ta tsani komai, sedai ƙarƙashin zuciyarta na hasaso mata wani yanayi ne me wuyar mantawa.


Ranar Monday kuwa Sadik shirin Makaranta yake, amma cike da zullumin yadda ze tunkari Farhan ta saurare shi.
Itama nata ɓangaren tunanin yadda zata shiga makarantar take tayi ido huɗu da wanda akai abun a gabansu, dan tana ji a jikinta ta rasa wata kima da daraja da take da ita a idon wasu daga cikin abokan karatun nata.
Jibtaka tamkar ta fasa zuwa makarantar, amma idan ta fasa tasan se a tambayi ba'asin hakan, dan haka jiki a sanyaye take aiwatar da shirin makarantar.

Seda aka gama Assembly sannan ta shiga makarantar, ta wuce ajinsu tana sussunkuyar da kai, duk wanda suka je gurin tsirarun mutane ne, dan a 'yan ajinsu Lilly ce kawai taje se wasu daga 'yan ajinsu Sadik se Khairat, du du du ba su fi su goma ba, amma gaba ɗaya ta rasa sukuni.

Sadik na shiga ajinsu suka hau yi masa ihu da shewa.

Be kula su ba yaje ya nemi guri ya zauna a mazauninsa, Nas da Amin sukaje suka zauna kusa da shi, Nas yace "Mazaa, ya ake ciki ne? Munyi ta kiran wayarka ba ta shiga, kuma ka barmu a gurin partyn ba ka dawo ba, ya kaji abun?"

Sadik ya ɗago idanunsa ya kalli Nas, kallon da Nas ɗin ya kasa tantance kallon meye.

Amin yace "wallahi you did it in the most passionate way, naji haushi da ka hana ɗaukar hotuna ku bada kala fa"

Nas yace "ai mun tabattar da namiji ne yanzu, yanzu zaka fara soyayyar morewa ba irin wadda kake yi ba da, ta ƙauyanci, nasan ko yanzu ka samu chance you want do it again ko ba haka ba?"

"Shut up!" Sadik ya faɗa da ƙarfi yana dukan benci.

"Dan Allah ku ƙyaleni inji fa abunda ya dameni, ku tashi ku ban guri"

Binsa su kai da kallon mamaki, meke damunsa hakane?

Kasa jurewa yayi, ya tashi ya nufi ajinsu Farhan amma ya tarar Madam Joy na ciki na musu lesson dan haka ya koma ajinsu.

Bayan fitar Madam Joy, Lilly taje in da Farhan ke zama ta zauna a kusa da ita tace "mutuniyar ya gajiyar taro?"

Wata ƙwalla ce ta zowa Farhan, da tuna a gaban Lilly Sadik yai kissing ɗinta, ta san maybe Zuwa yanzu duk ta gama bawa 'yan ajin labari.

Lilly tace "yana ga kamar zaki kuka? Meyafaru?"

Aikuwa maganar Lillyn tasa hawayen da Farhan ke maƙalewa ya gangaro kan kuncinta.

"Yasalam, Farhan menene?"

Cikin kuka Farhan tace "bakomai"

"Bakomai amma kike kuka?"

Farhan ta jinjina mata kai.

Lilly tace "anyway shikenan, bari in ƙyaleki kar in takura miki"

Har Lilly ta miƙe Farhan ta riƙo hannunta, ta dawo ta zauna tace "ya akayi?"

"Fatima dan Allah kin gayawa wani abunda ya faru agurin nan?"

Lilly ta riƙe hannun Farhan tace "i understand you ƙawata, karki damu ni ba wanda na gaywa, ni ba haka nake ba, and is something common in this school, no one will cares, amma duk da haka ni ban gayawa kowa ba, in abunda ya saki kuka kenan ki kwantar da hankalinki"

Farhan ta jinjina kai tace "Nagode sosai"

"Bakomai karki damu"

Ana haka, aka kaɗa jiniyar fita break, Lilly ba ta jira kowa ba ta ɗau littafinta, da kayan ciye ciyenta ta tafi ofishin malam Nazir, fan wata irin ƙishirwar ganinsa ke damunta, tun incident ɗin nan da yafaru, idan har bata sa shi a idonta ba, ba ta jin daɗi.

Kan tai sallama yaji ƙamshin turaren ta "Assalam Alaikum" tai Sallama.

Be ɗago ya kalleta ba ya amsa.

"Good morning Sir"

"Morning how are you?"

"Fine Alhamdilillah"

Ta ja kujerar da ta saba zama ta zauna, ta fara ƙoƙarin kwafar note ɗin ta, so take ko sau ɗaya su haɗa ido, amma yaƙi kallonta aikinsa kawai yake, wanda seda hakan ya ɗan bata haushi.

Sir Nazir kam yana sane yaƙi kallonta, saboda ya kasa gane kansa akan 'yar ƙaramar yarinyar nan.

Yayi rayuwar University cikin manya manyan 'yan manta, yai yawace ywacensa, amma be taɓa cin karo da wadda yake jin wannan bugun zuciyar akanta ba se wannan yarinyar me shegen iyayin tsiya.

Yayi mata kyau sosai, ji take tamkar ta gaya masa yayi kyau, amma tai shiri da bakinta tana tunanin me za tai wanda zesa ya kulata?

Can tai gyaran murya, tare da miƙa hannunta kusa da inda hannunsa yake ta ɗau biro.

Ɗagowa yai suka haɗa ido, ta ɗanyi luuu da nata idanun cikin wata irin murya tace masa "Nawa biron ya tsaya, shine na ɗauka aron naka"

A hankali ya jane idonsa daga nata, ya cigaba da abunda yake yi.

Wayarsa ce ta fara ringing, ya kalli wayar sannan yasa hannu ya ɗauka ya kai kunnensa.

"Assalam Alaikum" yai Sallama.

Lilly ba ta iya jiyo me ake cewa a wayar amma taji yace "like serious, congratulations my dear, am missing you, very soon zan shigo nima insha Allah"

Ya ɗanyi shiru Sannan yace "yadda kike so, idan ta idar ki bata wayar in kwashi gaisuwa"

Tunda ya fara wayar Lilly ta ƙura masa ido harya ƙare, gaba ɗaya Annurin fuskar ta ya ɗauke bata san lokacin da tace "Sir fa wa kake waya?"

"Da ƙaniyarki" ya bata amsa.

Sunkuyar da kai tayi ta cigaba da rubutunta, haka nan taji haushi ya kamata.

Mintuna kaɗan aka sake kiransa ya kuma ɗagawa, cikin wata nustuwa da girmamawa yace "Ina kwana Umma, duk kuna lafiya, ai insha Allah na kusa shigowa, Auta tace min ba ta da carryover a exam ɗinta, baki yaƙi rufuwa"

Murmushnsa ya faɗaɗa yana shafar gashin kansa yana wayar, wata nustuwa Lilly taji da ta fuskanci da 'yan gidansu yake waya.

Babban abunda ya bata mamaki da kusan dariya be wuce yadda yakewa Mamansa shagwaɓa a wayar ba, se taji ya wani ƙara burgeta sosai da sosai, ta dinga kallon sa tana murmushi.

Yana Ajiye wayar ta kalle shi tace "Sir is she your Mum?"

Ya jinjina mata kai alanar eh.

Tai murmushi tace "Amma Babba da kai kake shagwaɓa"

Murmushi ne ya ƙwace masa ya shafi gemunsa yace "Ai su iyaye ba a girma a gurinsu"

"Eh hakane, amma kai kayi girma da shagwaɓa"

Yace "Allah ko?"

"Eh mana, ai mata ne kawai suke shagwaɓa"

Murmushi yai ya cigaba da dannan System.

"Sir kana da ƙanne mata ne?"

"Eh ina da ƙanne mana, shiyasa bana don inga kuna rashin ji, idan na tuna da ƙanne na, bana jin daɗin ganinku kuja rashin ji, sedai ku kuma ba kwa son ace muku bari"

"Sir ba haka bane ba fa?"

"To yane Fati, ke kanki na san kina jin haushi na saboda hukunta ki da nayi ko?"

Lilly ba zata iya misalta farin cikin da ta shiga ba, kasancewar Sir Nazir yana mata Magana cikin nutsuwa ba hargowa da zare ido.

Ta ɗago idonta ta kalleshi, ta ga shima kallonta yake, ga wani cikar zati da kwarjini da ya sake yi masa ado.

A hankali ta sauke ajiyar zuciya, a ranta tace "ohhh God" ta fara tunanin ko ba duka ba za'a samu Sir Nazir da Mafi rinjayen siffofi da ake kamanta mazan littafi da shi, ba abunda yake tsole mata ido irin sajensa da wannan faffaɗan ƙirjin da yake da shi, she wish to hugs him even once, ta shafa wannan sajensa kamar yadda take karantawa a littafi.

"Fatima ya kira sunanta"

"Wani irin ɗagowa tai da idanunta, wanda sukai mata nauyi saboda jinta da take a gajimare, sheɗan na ta buga mata gangarsa a kwanyarta.

Kallon da tai masa ne yasa jin jikinsa yai wani irin sanyi, yaji gumi na karyo masa.

Kuma ta tsatsare shi da idanunta taƙi ɗaukewa.

Jin halin da yake shirin shiga ne yasa ya aro jarumta, ya haɗe rai yace "concentrate on what you are doing"

A hankali ta janye idanunta ta cigaba da note ɗin, amma lokaci lokaci idan ya ɗago ido se su haɗa ido tana masa wani irin shu'umin kallo da be san dame ze fassara kallon ba.

(Ƙalubale gareku iyaye da malamai, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya hana keɓancewa da mace wadda ba muharramarka ba, a yanzu muharraman ma se ana sa ido sosai, saboda muna zamani ne computer age, wannan kallace kallacen fina finan wanda ya dace da wanda be dace dui matasan mu kallo suke, ga uwa uba litattafai wanda wasu suke taka muhimmiyar rawa, gurin gurɓata tunanin Young adults ɗin mu.
Sannan mace duk in da take komai girmanta ko ƙanƙartarta duk girmanka duk ƙanƙantarka zata iya jefaka a bala'i, 'ya mace tana da hatsarin gaske, Allah yasa mu dace"


Farhan tai zuruu da ido, kamar agola a rabon gado, gaba ɗaya ta kasa sakewa. Gefe ga su Haseen suna ta karatun littafin su, da fari hankalinta baya kansu, tayi zurfi a cikin tunani, sedai jefi jefi kunnuwanta na ɗaukar wasu abubuwan.

Tana nan zaune aka tashi, kowa ya bar ajin amma ita tana zaune ba ta tashi ba.

"Farhan" taji muryar Sadik ta daki dodon kunnenta.

Haɗe rai tayi sosai ta ƙi kallonsa.

Matsawa yai kusa da Ita, tai saurin matsawa daga in da yake.

"Farhan meyasa kike guduna kuma? Fushin kike dani haryanzu?"

"Dan Allah ni ka ƙyaleni"

"Bazan iya ba Farhan, dan Allah kiyi haƙuri"

"Dan Allah ka ƙyaleni"

"Kema kin san ba abune me yuwuwa ba, tsautsayi ne baze sake faruwa ba insha Allah, ki tashi mu tafi gida Please kiyi haƙuri"

"Bazan haƙurin ba, kawai kasa nayi abunda ban taɓa yi ba"

"Nima ban taɓa yi ba, amma ai nace ba zan sake ba"

Tsaki tai masa ta ɗakko jakarta, ta raɓa shi zata wuce.

Riƙota yayi ya haɗata a bango yana kallonta, kamar yadda yaga anayi a Bollywood 🙄🙄🙄.

"Farhan nike baki haƙuri kina min wulaƙanci, nasan nayi miki laifi but am sorry, dan Allah kiyi haƙuri" ya ƙarasa maganar a sanyaye.

Kawai idanunta suka fara zubar da hawaye.

Hannu ya kai ze share mata hawayen, amma ta riƙe hannunsa.

"Shikenan na gane ba zan taɓaki ba, zo mu tafi"

"Ni ba zan bika ba"

"Baki haƙura ba kenan?" Ya tambayeta a marairaice.

Gaba ɗaya ta rasa dalilin da yasa ta kasa jin haushin Sadik, yadda yake marairaicewa ne yasa wani irin tausayinsa ya shige ta, kuma tasan idan ta dena kulashi, bata da wanda zata cigaba da raɓarsa tana jin daɗi, babu wanda zata dinga raha da shi tana jin daɗi.

Yasa hannu ya karɓi jakarta, yace "muje ko"

Tabi bayansa suka fito, a harabar in da ake parking ɗin motoci, suka haɗu da Mubarak Babba, ya kalli Farhan yana wani kashe ido yace "A'a yarinya ta zama 'yar hannu, delay ɗin na meye haka baku fito ba, ko dai ana tisa wancan karatun ne da a kai ran Friday".

A take Farhan taji wasu hawayen na silalowa daga idanunta.

Sadik ya kalli Babba yace "Mubarak, ka sanni na sanka, ni da kai kar ta san kar ne, ko da wasa ba ruwanka dani da kuma

Please Login or Register in order to submit comment