Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙwaya na sha tun jiya take wahal dani, na kasa baccin na kasa komai ga jikina duk a mace, taƙi sakina gaba ɗaya, kuma bana son in koma gida a gane"

Taslim tace "calm down dear, nima farkon farawa ta haka naita fama wallahi, amma ki kwantar da hankalinki, ki matsa lemon tsami da yawa, ki zuba manja a kai ki sha, zan saka Mubarak ya kawo miki wadda zata dai-dai ta miki jikin naki, amma ki ƙwarara jikinki kiyi exams ɗin lafiya, kar a fuskanci wani abun"

Ta jinjinawa Taslim kai alamar to.

Haka invigilators suka shigo, suka fara arranging ɗinsu domin fara jarrabawa.

Sadik kam kusan rabin jarrabawar nan be san meya rubuta baz tunaninsa da hankalinsa na can kan wani abu daban.

Meenat kuwa duk da ta na cikin maye, amma taji daɗin ganin corper Nura a cikin invigilators ɗin nan.

Da sun haɗa ido zata masa wani killer smile tana lumshe ido, tun yana basarwa har ya ɗan fara dirircewa.

Murmushi tayi tace gayen nan ai dole ka shigo koma ta ko baka so.

Da ya zaga ya zagayo se yaga tana kallonsa, ba ya son dizgata a gaban ɗalibai dan haka ya ƙarasa gaban seat ɗinta yace mata "gani me kike buƙata"

Cikin kashe murya da magana ƙasa ƙasa tace "ni ba kiranka nai ba"

"Amma ki ke kallona"

"To sir dan kawai na kalleka, ni bani da lafiya ne"

"Eyya sorry, can You write the exam?"

"Yes am trying"

"Ok sorry, in kin gama kije Clinic a dubaki"

"Ok thank you sir"

Har ze juya ya tafi tace "oushh"

Ya juyo da sauri yace "ya dai cikin ne?"

Ta jinjina masa kai alamar eh, "eyya ko dai zaki je a fara baki magani?"

"No i will finish the exams first"

"Ok sorry dear"

Ta jinjina masa kai tana wani marairaice fuska.

Yana wucewa tabi bayansa da wani irin shegen murmushi, a ranta tace "da Wannan raunanniyar zuciyar ta ka zan damƙe ka ta wuya"

Ta sake sakin wani murmushi, tana cigaba da rubutu.

Da wuri Farhan ta gama exams ɗinta, saboda tayi mata sauƙi sosai da sosai, duk da zare ido da muzurai da sir Nazir ya dinga yi, sam hakan be damu Farhan ba dan nan da nan ta kammala, dan abunda sukai bita tare da Prince mostly su suka fito musu.

Tana gamawa ba ta jira Komai ba ta nufi hanyar fita, ta jiyo Sir Nazir yace "daga nan ki ɗau jakar ki ki tafi gida, idan kika kuskura na ganki a gurin yaron nan sena miki duka"

Seda gaban Farhan ya ɗan faɗi, dsn tabbas yanzu Sir Nazir yana hukunta mutum idan yayi laifi, har duka yake, makaranta kuma sun kasa dakatar da shi, saboda jaki work da yake musu, he is very hard-working teacher, yana da jajircewa sosai suyi ta jibga masa jaki work, kuma hakan baya damunsa.

Da akai masa Magana akan dukan da yake yace shi koyarwa ko duk Makarantar ne ze koyar, baze dameshi ba, amma baze dinga kashe energy ɗin sa yana koyar da yaran da basu san darajar Malami ba.

Rashin Nazir ze sama musu babban giɓi a makarantar, dan haka suka ja masa kunne kome zeyi ya dinga yi sama sama, banda punishment me wahala ko duka, idan ba haka ba uban wani ɗan ze iya kulle shi.

Ajiyar zuciya Farhan tayi da ta tuna da haka, tana fita wajen ajin taji maganar da yai ta shiga ta kunnen dama ta fita a na hagu, ajin su Prince taje ta tarar be fito ba, dan haka taje ta nemi guri ta zauna tana jiran fitowar tasa.

Gajiya tai da zaman ta miƙe tsaye tana ɗan leƙewa cikin ajin.

Ji tai an kama rigarta an janyota ta baya.

Da sauri ta waiga amma taga Mubarak Babba ne da Wannan aikin haka.

"Meye haka, me nai maka?" Ta faɗa a ɗan raunane.

"Sekin min wani abu zan taɓa ki, i just feel like to do so, naga jiya kin bar ajinsu Sadik saboda nai kissing Taslim, shiyasa kema nake so in kissing ɗinki, in gwada miki yadda ake soyaya ba kamar wadda kuke ke da wancan wawan Sadik ɗin ba"

Nema yake ya haɗata da jikinsa, kasancewar gurin ba kowa, kusan itace ɗaliba ta farko da fito daga ɗakin jarrabawa.

Ƙoƙarin ƙwacewa take, ta hana shi ya haɗa jikinsa da nata, ga wani warin hammata da yake, take zuciyarta ta fara tashi.

Abunda ko da wasa ba ta taɓa jin Prince ɗinta yana yi ba, abun mamaki ya bata ma, dama yaran masu kuɗi ma na warin jiki? Ga ƙamshin turare a jikinsa, amma warin daban ƙamshin daban.

Ganin da tai bata da mafita yasa ta ware murya ta shiga kiran sunan "Sadik"

Da sauri Babba ya ƙyaleta, dan yasan gamonsa da Sadik ba daɗi.

Ta arta da gudu ta bar harabar gurin, tai waje.

Sadik kuwa da Sauri yai submitting paper ɗin sa ya fito, dan tabbas yaji kururuwar Farhan.

Sedai yana fitowa yaga be ganta ba, ya dudduba amma bata nan, ya nufi ajinsu ya tarar da wanda suka fito ya tambaye su Farhan, suka ce masa ai ta fita tun ɗazu.

Haka yaita zaga makarantar ko ze ganta, amma be ganta ba nan ya dinga mamakin abunda ya sata wannan uban ihun haka, gashi ita ba waya ba balle ya kirata.

Haka ya wuce ya tafi gida yana tunani.

A gidanma abunda ba ya so, dan sati me kamawa za'a fara biki, masu rumfuna da kujeru duk sun kawo sun jibge a harabar gidan, wannan ya shiga wannan ya fita ita kanta Mother bata da lokaci, kusan kullum ba ta nan, ita ce nan ita ce can saboda hidima.

Yana kwance a part ɗinsa da yamma, Nasir ya kira shi yace kayan da akai order sunzo, sedai nasa wandon ne se cikin satin bikin ze iso.

Sadik yace "i hope dai za'a kawon kafin ranar partyn nan"

"Za'a kawo insha Allah, ga sauran nan naje na karɓo rigunan ma, naso in biyo in kawo maka ka gani, amma ba mota a gidanmu duk an fita da su, a babur naje"

"Ok shikenan, gobe in Allah ya kaimu seka zo dasu a bawa kowa nasa"

"To shikenan Allah ya kaimu goben"

"Ameen" ya katse wayar.

Yanzu Nana ba ta haɗuwa da Sadik, sedai kuma abun ya koma rigima tsakanin ta da Khairat, haka kurum da ta motsa se Khairat ɗin ta fara hantarar ta, tana zaginta ko da kuwa a gaban Inna ne, Inna ba ta cewa komai dan ba ta shiga faɗan yara, in ba gani tai za su cutar da junan su ba, ita kuma Nana na gudun faɗan Inna.

Amma Nana ta fara ƙuluwa da abunda Khairat ke mata, kuma babban abun takaicin ma shine, ba iya Khairat ke mata hakan ba, mahaifiyar Khairat ɗin itama haka take, matar gidan ma haka take mata mussaman idan ta ga babu idon Inna a gurin.

Hakan ya fara damun Nana sosai, taji ita gaba ɗaya ma zaman Gidan ya isheta, gara su koma ƙauye dan a can matsalarta ɗaya faɗan Inna, amma kuma ba tsangwama da hantara, dan bata jin daɗin yadda ake hantararta a gidan.

Duk gidan ba wanda take ɗasawa da shi sama da Daddy, se masu aikin gidan se kuma Faruk, yana da fara'a sosai yana da kirki, ba kamar dr. Ba, dan shima baya kula mutane ba ya Magana Sosai, shikuwa oga kwata kwata nasa yafi na kowa, ga rashin son mutane, ga wulaƙanci, ga zagi da hantara ga iya muzurai duk shi kaɗai, Faruk ne me halin Baban su ba ruwansa shi da wannan zafin kan.

Yanzu ma Nana tana cikin 'yan aikin, ana girkin rana, Nana akwai son aiki sosai, sedai ko a gida Inna ba ta fiye sata aiki ba, Se su bata ɓarar maggi, ko jajjage ko shara, dan su huta da hayyatarta na lallai se taya su aiki.

Aka kammala girki, aka zuzzubawa kowa nasa, Nana ta ɗauka ta dinga kaiwa kowa har inda yake.

Ta kaiwa Inna nata, Ta ɗau na Mother ta nufi ɗakinta, da sallama ta shiga ɗakin, ta tarar da Mother da Maman Khairat se Faruk da yake riƙe da kuɗi a hannunsa da alama aikensa za'ai.

Ta ajiye kulolin Abincin tace "wai ga Abinci"

Mother ta kalli Nana tace "waye yace ki shigo nan?"

"Ba kowa kawai kowa kai masa Abincin sa nake"

"To daga yau kar in sake ganinki a nan ɗakin, ki dinga tsayawa a can in da aka sauke ku, baki da hurumin zuwar min sashe, idan kika kuma zuwar min nan sena saɓa miki"

Turus Nana tai tana kallon Mother, tana tunanin meye a nan ɗin da dan ta shigo za'a dinga mata wannan kashedin haka, nan da nan ranta ya ɓaci.

Maman Khairat tace "ba Magana ake miki ba kina jin mutane? Maza ki wuce ki bar gurin nan, da haka yaro ke koyar munafurci, yaran ƙauye dama ba kan gado suka cika ba, yanzu zaki ji ta haɗa wani abun ta gayawa kakarta ta kunno miki wata wutar"

Jiki a sanyaye Faruk yace "haba Mother, meye a ciki dan ta shigo me aka ajiye a nan ɗin, naga Khairat ba ta da iyaka a shiga duk in da take so a gidan nan, hakan da kike mata ba zata ji daɗi ba, ba daɗi hantara"

Mummy tace "to uban mu gayamana abunda yakamata"

"Ba abunda yakamata zan gaya muku ba, amma idan bata zo ta ga abunda za ta je ta gayawa Inna ba, ai ta faɗa mata abunda a kai mata, na baƙaƙen maganganun da ku kai mata"

Ya juya ya fita yana takaicin abunda sukai, dan shikansa baya jin daɗin wasu daga halayen mahaifiyarsu, Akwai ta da wulaƙanta ɗan Adam mussaman talaka, kuma Mummy ce ke zigata, kuma ko zata ƙyamaci kowa be kamata ta ƙyamaci dangin mahaifinsu ba.

Yana fitowa harabar gidan ya hango Nana akan barands, tai shiru tana wasa da tsinke, da alama tana cikin damuwa akan abunda akai mata.

Ya ƙarasa in da take yace "Naana What are you doing here?"

Ɗaga kai tai ta kalleshi, ita ba ta fiye gane irin wannan turancin da suke ba, a dinga yin sa a wani harɗe, wata kalmar ma bata fita sosai, zuba mai ido kawai tai ba tace komai ba.

Yace "ok, jeki gurin su Binta, su baki namu Abincin ki kawo mana BQ"

"Ina ne BQ?"

"Wancan sashen me farar ƙofa"

Tura baki tayi tace "wannan ƙanin naka zagina yake, idan naje ze iya zagina"

"No ba ze zageki ba, aini na aike ki"

Ta tashi ta koma dan cika Umarnin sa.

Yabi bayata da kallo, kawai yaji ta bashi tausayi, tsangwama bata da daɗi sam.

Nana ta koma ciki, ta karɓo kwando ɗauke da kayan Abinci da plates, seda tai sallama sannan ta shiga, amma tana shiga taga Prince ya harɗe ƙafa yana video game.

Kallon ta yai, ya tashi zaune yace "me kika zo yi nan? Ban hanaki zuwa ɓangaren nan ba?"

"To ban hanu ba, se kai abunda za kai"


AIMIN AFUWA FOR THE VERY LATE POST, ABUBUWA SUN SHA KAINA SOSAI DA SOSAI, AIMIN AFUWA.

Gyara Sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa:     🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

     

TAƘABALLALAHU MINNA WA MINKUM, ALHAMDILILLAH ALA KULLI HALIN UBANGIJI ALLAH YA KARƁI IBADUNMU YA MAIMAITA MANA, INA 'YAN UWA MASOYA, MARUBUTA DA MAKARANTA MURNAR BARKA DA SALLA, UBANGIJI ALLAH YA MAIMAITA MANA.
BAYAN HUTUN AZUMI ALHAMDILILLAH, GANI NA DAWO MUKU DA CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA.
INA FATAN ZAKU BINI SANNU, DAN JIK ƊUMBIN SAƘONNIN DA LITTAFIN YA ƊAKKO, WANDA SUKE TAMKAR BULALIYA GA IYAYE.

SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.


                           17_18













A fusace Sadik yace "ke ni kike gayawa haka?"

Murguɗa masa baki tai tace "eh ɗin, na faɗa ɗin"

Faruk ne ya fito hannun sa riƙe da wayarsa yace "Sadik meyasa kake hakane? Hantarar mutum ba daɗi, nine mace ta kawo mana Abinci nan"

Sadik yace "Amma dai bani a Wannan Abincin da ta kawo?, dan ba zanci Abunda wannan ƙazamar ta taɓa ba"

Aikuwa Nana ranta ya ɓaci sosai tace "wallahi ni ba ƙazama bace, kaje ka nemi ƙazama a can amma bani ba"

Ta dire kwandon Abincin, zuciyarta na mata zafi, yace "in kinyi zuciya ki tattara ki bar mana gida yau, kun zo kun cika mana gida kun hana mutane sakewa"

"Sadik meyasa kake hakane? She's lyk sister to you, be kamata ka dinga hantarar ta haka ba babu daɗi, yanzu ma fa daga gurin Mother take suna ta kyarar ta, ba bu daɗi hakan, kyarar ɗan Adam ba shi da wani Amfani ko rana"

Yatsune baki Sadik yai ya koma ya kwanta yana cigaba da video game ɗin sa.




Washegari a school kuwa, bayan fitowa daga exams aka kawo kayan nan da sukai order, wasu irin tsadaddun crazy jeans da riguna.

Ana ta ɗaɗɗaga kayan ana bawa kowa nasa, ana shewa da lissafin in da ya kamata a kama na partyn, amma hankalin Prince yana kan rashin ganin Farhan da beyi a ajin nasu ba yau.

Miƙewa yai tsaye yace musu yana Zuwa, ya fita da sauri ya tafi ajinsu Farhan, amma bata ajin, Library ya tafi ya tarar da ita a can tana karatu.

Sadik ya ja kujera ya zauna yana kallonta, ta ɗaga ido ta kalleshi tace "good morning"

"Naƙi in amsa gaisuwar taki, ba an gama exams ba, me ki ke a library kuma?"

Cikin sanyin halinta tace "Ai clubs suna rehasals yau, dan haka ance ba me tafiya se lokacin tashi yayi, shiyasa na taho nan kawai"

"Amma meyasa baki zo ajinmu ba?"

"Bakomai" ta bashi amsa a taƙaice.

Yace "yawwa, jiya ina exams kamar ihun ki naji kina kiran sunana"

Ɗan kallonsa tai tana zare ido, ta dake tace "bani bace"

"Kamar ya ba ke bace? Muryarki fa naji"

"Am serious ba ni bace"

"Ok shikenan, ta so muje class ɗin mu kiga kayan da zamu sa ranar bikin Brother na"

Ɗan noƙe masa kafaɗa tayi alamar ba zata ba.

"Baby meyasa?"

"Bakomai"

Sadik yace "kefa kin fiye mulki wasu lokutan, yau kuma ajin namu ne ba zaki ba?"

Ta ɗaga masa kai alamar eh.

"Nagane, saboda abunda su Taslim su kayi ne ranar ko? Na musu magana ba zasu sake ba"

"Ni dai kawai yau ba zani ba"

"Ko wani abun suke miki a ajin namu"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

Yace "shikenan ni na tafi"

Ya miƙe ze tafi, da sauri tace "nace ba"

Be juyo ba yace "ki ka ce me?"

"I want to talk to you please"

Juyowa yai ya kalleta, ya dawo ya zauna yace "am all ears"

Cikin jin nauyi tace "dan Allah ka zauna a nan"

Yace "Why?"

"Kawai mu zauna a nan"

Tai maganar kamar wadda take furta saɓo saboda jin nauyinsa.

Wani ƙasaitaccen murmushi yai mata me cike da ma'anoni da yawa, yace "kina so in zauna?"

Ta gyaɗa masa kai.

Yace "Da sharaɗi gaskiya"

"Sharaɗi kuma?"

"Eh mana" ya faɗa yana kwaikwayon ta.

Tai murmushi tace "meye sharaɗin"?

Yace "Look up" ta ɗago ta kalleshi tai saurin sauke idonta, dan ji tai ba zata iya tsawaita kallon nasa ba.

"Kice ki na sona dan Allah"

Ba tare da ta kalleshi ba ta ɗan zaro ido tace 'taɓ'

"Ba zaki iya ba kenan?"

Shiru tai ba tace komai ba.

Sadik yace "Farhan kenan, kedai wannan fulatancin naki yayi yawa, shikenan tun da kince in zauna yadda kika ce ai haka za'ayi gimbiyar mata"

Yana zama kuma wata kunyar ta sake baibaiyeta tana mamakin kanta, wai ita ce ke cewa namiji ya zauna kar ya tafi, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, farin ciki na ratsata kasancewar ga Prince a kusa da ita"

Haka shiru ya wanzu a tsakanin su, Prince ya katse shirun ta hanyar ɗakko mata hirarraki, a haka ta saki jiki suka cigaba da hirar tare.

Seda aka kaɗa bell, sannan suka baro Library ɗin tare.

Aka kammala jarabbawa, aka shiga shagulgula daban daban a makarantar, kullum akwai abunda za'ayi na nishaɗi, ko dai Quiz, Debate, inter House competitions, da dai games kala kala.

Farhan ta so tai zamanta a gida ta dena zuwa tun da hutu za'ayi, amma idan ta zauna a gidan a takure take ga damuwa, dan haka take zuwa school ko ba komai tana ganin abun ƙaunarta tana jin daɗi.

************

"Meena, wai anya lafiyar ki ƙalau kuwa?"

"Mum why are you asking? Me kika gani?"

"Gaba ɗaya kin ɗashe, se wata uwar rama da kike yi, ga wani uban bacci wanda na kasa gane miki gaba ɗaya"

"Am ok fa, kawai weather nan ce is not compostable to me, yau zafi gobe sanyi, and I have no appetite bana iya cin Abinci, shiyasa nake rama But i will be ok insha Allah"

"To shikenan, idan kuma ba hali muje Asibiti a duba ki"

"No don't mind Mum, sena dawo"

"Ok safe journey"

Meena ta amsa da "Thank you" sannan tai waje.

An taru sosai a gurin hall ɗin makarantar, dan kallon fafatwar da za'ai na Debate, ɗalibai 'yan kallo suna cakuɗe maza da mata, ana kallon fafatawar.

Farhan na kusa da Prince, ya bata wayarsa tana kallon pictures ɗin 'yan gidansu, yanayin hotunan nasu ya tabbatar mata da Lallai Prince ɗinta ɗan hutu ne, sannan da alamun akwai kyakkyawar alaƙa da shaƙuwa a tsakanin su.

Farhan ta kalli hoton Mother tace "she's Your Mum ko?"

"Eh mana, in law ɗinki ce, ai zaku haɗu agurin bikin Brother na, i will introduce you to my Family"

Zare ido tai tace "ni dai a'a gaskiya, se ace munyi rashin kunya ai"

"Meye wani rashin kunya, gara su sani tunda wuri ai, ko kin manta ina processing yadda zamuyi Aure ne? Gara su san da Maganar tunda wuri"

Shiru tai jikinta yai sanyi, duk da maganar Auren da yai yasa jikinta yai sanyi, amma a wani ɓangaren tana fatan Allah ya amince, yasa ta Auri Prince, First love ɗinta kenan, ba ta jin daga kansa zata kuma son wani namiji haka.

Ta cigaba da kallon hotunan ta, Sadik ya jiya yana magana da su Nas, yaji suna zancen wani Film.

"Nas, kune sarakan kallon series Films, dan Allah in mun bar nan System ɗina na mota, zaku turamin fina finai masu kyau sosai"

Amin yace "Allah mutumina, ka shigo layin kenan?"

Sadik yace "wani layin kenan?"

Nas yace "layin eh mana"

Sadik yai tsaki yace "Malam ba wannan haukan nace ba, just normal films nake so na Soyayya, za'ai hutu bayan bikin nan ina so zan kalla, ina son wanda ake soyaya sosai a ciki"

Amin yace "ji shi wai wani na Soyayya, se kace soyayyar suka iya, banda ƙauyanci da soyayyar yara ba abunda suke"

Farhan ta ɗago ta kalli su Amin, ta ja ƙaramin tsaki wanda Sadik ne kawai yaji, yai murmushi yace "don't mind them Baby, kar su mayar min da ke mafaɗaciya, i love Your silent character"

Farhan tace "ai ni ba faɗa zan ba"

"Ai tunda kika fara tsaki, nasan faɗan ma zakiyi ne"

Tai shiru ta cigaba da abunda take.

Sadik yace "Nasir zaku turamin ko kuwa?"

Nasir ya kashe ido ɗaya yace "meze hana a turamaka ranka ya daɗe, akwai korean, indian, American Chinese and many hot Love series, depending on which you wish to watch"

Sadik yace "Kawai me kyau nake so"

"Shikenan, bari a tashi daga nan ɗin, za'a tura maka Insha Allah"

Suna cikin maganar sega Babba ya nufo su, yana tunkaro gurin Farhan ta haɗe rai, jikinta ya hau tsuma, saboda yanzu a Duniya ta tsani ko ganin Mubarak.

Ya faki idon Sadik ya kashe mata ido, ta galla masa harara ta ɗauke kanta.

Ya zauna kusa da su Sadik ya miƙa musu hannu, su kai musabiha, miƙewa Farhan tayi zata bar gurin, Sadik ya kalleta yace "ina zaki kuma?"

Ɗan yatsuna fuska tayi tace "can zan koma"

Sadik yace "ok as you wish my love"

Tai masa guntun murmushi, ta koma cikin 'yan ajinsu mata, da suke ta zuba hira, gefen su kuma 'yan ajinsu Sadik ne, su Taslim da Meenal.

Can kuma ana can ana ta faman Debate, amma hankalin su ba'a akan abunda ake yake ba.

Su Lilly kam banda hirar litattafan da suke karantawa a Online ba abunda suke yi.

Taslim ta dubi su Lilly tace "Lilly, me kuke Magana a kai ne?"

Lilly tace "bakomai fa"

"A'a naji kamar kuna hirar romantic book ne na hausa"

A ɗan tsiwace Lilly tace "eh"

"Dama akwai romantic books na Hausa?" Taslim ta tambaya

Lilly tace "eh, akwai masu zafi ma kuwa"

Nan Taslim ta dinga lallaɓa su Lilly, suna bata labarin litattafn da suke karantawa a Online.

Gaba ɗaya hirar tasu ta gunduri Farhan, su gaba ɗaya makarantar daga mazan har matan tunanin su iri ɗaya ne, duk wata harka ta watsewa su ita suke so.

Haushi ne ya kuma kama Farhan, ta Tashi ta bar hall ɗin gaba ɗaya ta fito, zagayen ta ta shiga yi a makarantar, tana 'yan leƙe leƙen ta, makarantar shiru kamar ba kowa duk suna hall ɗin da ake gabatar da Debate ɗin.

Katsam idonta ya sauka akan corper George a cikin wani aji, abunda idanuwan ta su kai katarin gani ne ya kiɗimata, wanda har ya kusa awon gaba da nutsuwar ta na wani ɗan lokaci, a very deep Romance with his ss3 student, she don't even know the name of the lady, ta san dai shine class mastern finalist student ɗin.

Jikinta ne ya hau wata irin tsuma, kuma ta kasa motsi daga gurin, se idanunta da take ta faman jujjuyawa kamar taiwa Sarki ƙarya.

Ba tsammani George ya waigo ya ga Farhan tai musu ƙuri da ido, da sauri ya cika Nasreen, ɗalibar da suke watsewa taren, yana ƙoƙarin tattaro nutsuwarsa ya daidai ta.

Ganin da Farhan tayi sun ganta Ya bata ƙwarin gwiwar, fizgo kuzarin da ta rasa na wani ɗan lokaci, cikin sassarfa ta ja da baya cikin hanzari ta nufi hanyar da ta sauka daga kan benen.

Kana ganin ta kasan a firgice take, kamar wadda ke shirin zarewa, ba zato ba tsammani tai karo da Sir Nazir yana ƙoƙarin hawowa kan benan.

Cak ta tsaya tana cigaba da rarraba ido, kamar mara gaskiya.

Kallon tuhuma ya bi ta da shi, yana ƙare mata kallo yana son gano me ya razanata haka, fuskarta take bayyanar da alamun rashin gaskiya?

Hanya ta bashi, dan ya wuce sannan ita ma ta wuce, amma ya tsyaa kyam yana cigaba da kallon ta.

Ba tsammani taji muryarsa yace "me kike yi a nan?"

Girgiza masa kai tayi tare da faɗin "Nothing sir"

"Nothing as how? Ke da waye a saman gurin nan, bayan ba kowa duk ana hall ɗin da ake Debate?"

Rasa amsar da zata ba shi tai, ta cigaba da tsatstasare shi da ido.

"Ke da wannan shashashan yaron ne a saman ko?"

A razane ta kalli Sir Nazir, tana son tabattar da abunda yake faɗa.

Ganin Farham taƙi magana ta cigaba da bin sa da idanu ya sa ya ji zargin sa na neman zama gaskiya.

"You Are Much more than stupid Farhan, ki cigaba da biyewa RUƊIN ƘURUCIYA, Kina rusa Rayuwar ki, nan gaba se kin yi kuka da idonki, a lokacin da kuskuren da ki kai ba ze gyaru ba, ki cigaba da ba shi damar keɓewa da ke, sheɗan na buga muku ganga, nan gaba zaki gane shayi ruwa ne stupid girl"

Maimakon ya hau saman benen, se ya fasa ya juya ya sauka, zuciyarsa na ƙuna, ganin yadda rayuwar yara mata masu ƙananun shekaru, ke lalacewa saboda RUƊIN ƘURUCIYA.

Farhan kuwa kasa matsawa ta yi daga in da take, maganganun sir Nazir suka cigaba da sukar zuciyarta, yana zarginta da wani abu, wanda ba shi da tabbas a kai, dan duk wannan masifar da yake a yanzu, bashi da wata hujja da ze kafa, akan ta, amma ya sa mata ido yana binta da miyagun maganganu, tabbas duk da ƙanƙantar shekarunta, tasan idan har aka zarge ka da keɓewa da wani namiji, to kuna aikata wani abune da be kamata ba, take ta tuno abunda ta gani yanzu a saman benen, kenan da irin abun Nazir yake

Please Login or Register in order to submit comment