Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'Yar uwartace gidansu kusan 'dayane dan iyayansu sunyi xaman gaskiya da amana hakanne yasa suka kasance tamkar 'yan Uwa
YUSUF inasan yarinyar nan dan haka kawai tunda namata kallo 'day Naji qaunarta tashigeni ina Santa

YUSUF ya sauke sanyayyiyar ajiyar xuciya danjin LABEEBAH dai ba MATAR Yayan nasa KAMAL bace yakalli momy ahankali yace xanje in kwanta Tace toh atashi lpy katuromin Salim Yace Toh

Yana fitowa daga 'dakin Momy shashin KAMAL yayi da sallama Amma ina samun Yayan nasa yayi rungume da XARAH Yana leman bakinta
Da sauri ya komah baya Yace umm hmm hello
KAMAL yasaki XARAH ahankali Yace yes come.......
Bai qarasa furucin nashi bah YUSUF yashiga Yace gun Auntyna naxo
KAMAL yayi Murmushi da kallan XARAH Yace gatanan
YUSUF ya'dan sosa qeya yana qumbiya qumbiya
Yaba KAMAL dariya dan haka Yace ko sirrine abun
YUSUF aa
Cikin bet room KAMAL yayi Yana cewa bari inje in shiryΓ  kayanmu kafinnan kungama Sirrin komadai miye indai TEEMAH nace xata gayamin
XARAH tayi dariya tace hakane My luv
Murmushi YUSUF yayi da zama kan hannun kujera ya fuskanci XARAH xaiyi magana tarigashi da cewa. tunda mukaxo banga Sadeeq bah sai Aliyu ya haka
Yace hmm yana can saudi iyayan maman nasune suka roqi alfarmar abar musu shi kinsan dama maman nasu ita ka'daice dasu kuma gashi ta tafi shiyasa momy tace abarmusu shi kawai
XARAH tace ayya Allah yaji qanta
Yace AmEEn Nagode. Am dama labarin LABEEBAH nakesan kiban
Tace saika biya
Yace fa'di konawane Xan biya Tace toh gyara xama kasha labari
Yace nagyara

Tsaf XARAH taba YUSUF labarin LABEEBAH har San datakema KAMAL


Shuru YUSUF yayi can Yace a xan canki idan nafahimta ranar da kuka ha'du da Ya KAMAL aranar itama LABEEBAH taha'du da KAMAL 'dinta
Ko shakka babu XARAH tabashi
Murmushi yayi tare da gya'da kai dan yagane sarai nawani bane KAMAL 'dinda LABEEBAH takeso fa ce Yayansa. Nan take kishin yayan nasa ya dirtsu aransa .........

KAMAL ne ya katse mishi tunanin nasa tawajan fitowa daga bet room Yana cewa imma ka kamu da santa ne toh kasani Jameel ya rigaka da ita
Tashi YUSUF yayi Yana Murmushi sanda ya kusan fita Yace haba Yayana ai ban gama warwarewa ba tukunna koxan yi soyayyah sainan gabah yana gama fa'din haka baijira cewarsa bah. Ya fitta abinsa......

KAMAL ya kalli XARAH Yace kinga mutafi gidanmu tunkam Momy takoremu
Tace ina😳
aini anan xanyi xamana
Yawota jikinsa yayi Yace kokin xauna bashi xaisa naqi kar6ar hakkina bah
Tace kai My luv agidan Momy fah muke
Xura hanunsa yayi Cikin rigarta Yana cewa bara na tabbatar miki da agidan Momyn muke...................


YUSUF ko Yana fitowa suka da'da cin karo
Atare ko suka dafe goshinsu
Ya galla mata hararah tare da cewa biyoni
LABEEBAH tabishi tana tunanin KAMAL ne ko YUSUF
Han cintane ya bata amsa. Wajan bambamce mata shamshinsu
A Falansa ya tsaya itama tsayawa tayi tana kallansa
Yajuyo karab suka ha'da ido
Wani MASEEFAR SOONTA ne yataso mishi
Yace dan Allah meyasa kikama xuciyata mummunan illah haka

Tawaro ido Tace me namaka
Yace da alama ke muguwace
LABEEBAH tayi larai-larai da ido Tace muguwa kuma

Yace eh mana dan 'daxu kinci xalina yanxuma kinkuma ci
Bama wannan bah meyasa kike qoqarin cin amanar 'Yar uwarki XARAH


A furgice Tace ban gane bah
Ya galla mata harara Yace meyasa xaki SOO mata Miji
Kin tsaya kina raina mata hankali wajan San mijinta.
Tunaninta da gaske kina da KAMAL 'dinki. batasan mijinta kikeso bah
Dama har yanxu akwai irinku maciya amana
Akan me xakiso mijinta kije kinemi nakiman
Kalleki dan Allah ko kunya baki jibah kinasan mijin 'Yar uwarki............

Kuka LABEEBAH ta6arke mai dashi baqin cikinta yanda ya gaya mata baqaqen kalamai
Tace waya gama Ya KAMAL nakeso. Duk wandΓ  ya gayama qarya yake min.
taqarashe maganar da qara rushemai da kuka
Da'di Yakama YUSUF
Yace kinga malama denamin kukan gulmah Ni 'dinnan na hangode son ya KAMAL a idanki xaki qaryata nine. Yanxu inje in gayama XARAH komai

Da sauri takalleshi tare da qarasawa gabanshi ta durqusa tana kallan nasa tace dan Allah karka fa'da mata Dan Allah Wlhi nadena sanshi

Ya cije baki dajin da'din yanda xai sarrafata yanda yakeso
Yace tashi.
ba musu Tatashi
Yace daga yau naqara ganin soyayyar Ya KAMAL a idanki Wlhi Wlhi Wlhi saina miki dukan tsiya
Taqa kafeshe da ido tare da gya'da mishi kai
Yace gobe da safe Xan dingaya miki dokoki akan Ya KAMAL
kina jinah
Tace eh
Yace toh jeki......
Har takai 'kofa Yace tsaya
Nan tajuyo da tsayawa cak
Yaqaraso da xaro hankicif a ajjihunsa bawani shayi Yakama fuskarta ya goge mata hawayanta tsaf Sannan yasaki fuskar tata. Aiko tafice da sauri
Wani tsalle YUSUF ya daka ya dire a kujera dare da cewa gudβœ… Allah karabani da MASEEFAR SOO




Sam LABEEBAH bata koma gun XARAH bah. Dan direct 'dikin da momy taware musu ita da Sumayya tayi
Nan tasamu Sumayya dasu Safna
Batayi gigin kallansu bah ta wacce can qarshen gado takwanta abinta dan tasan Suna ha'da ido xasu tambayi meyasami idanta
Sagna Tace Aunty LABEEBAH bacci xakiyi tun yanxu Tace eh kainane yakemin ciwo. Atare dukkan Su ukun sukace ayya Allah yabaki lpy Tace AmEEn
Bara inkawo miki magani cewar Safna Tace toh
Taje takawo mata ta qar6a tasha Sannan tayi toilet tayi Alwala tagabatar da magriba da isha'ii da shafa'i da wuturi Sannan takwanta tana tunanin gamuwarta da YUSUF

Da gaske kannata ciwo yake mata dan tabbas YUSUF ya rikitata
Bata ankaraba taji hawaye na xubar mata.
Ashe duk yanda take 6oye soyayyar KAMAL aranta wani xai iya gane hakan
Jitayi tana San ganin Ya Usman 'dinta da Rukayya da Innah
Tasan da bata xoba ba.
da YUSUF bai hango soyayyar da takema KAMAL 'dinba.
Sagna CE takatse mata tuninta tawajan cemata aunty LABEEBAH kitashi muyi hira dan Allah karkiyi bacci.
Lumshe idanta tayi dan nuna alamun tayi bacci adole
Ganin tayi shuru Sumayya Tace tayi bacci ai
Aikowa cewar Sagna

KAMAL ne yashigo Yana cewa ina suke.
Safna tace Aunty LABEEBAH da Sumayya. Yace eh
Sagna Tace Aunty LABEEBAH tayi bacci Sumayya ko tashiga toilet
Yace OK in tatashi kuce musu mumun tafi gobe kwa rakusu Safna Tace toh yayah saida safe
Yace Allah tashemu lpy ya ficce

LABEEBAH taqara gimshe ido tana shaqar qamshin KAMAL
Ahaka bacci yayi awan Gaba da ita
Cikin caccin natane taji wayanta tana qara taduba taga ba Suna
Tsarin number yasata xubama wayar ido.....
Ya YUSUF ne Yace inbashi number-ki. Sagna ta katse mata tunaninta da fa'din hakan
Waro ido LABEEBAH tayi ta kalleta. Tako gya'da mata kai alamun tabbatarwa.
Tace ok ya naganki ke 'daya. Tace Safna sunyi gun Momy itada Sumayya.. Tace OK
Kara wayan tayi akunnanta da sallama gabanta na fa'duwa dan ba qaramin tsoran shi YUSUF 'din tajiba
Dai-dai nan Sagna tafita
Kamilalliyar muryarshi CE ta isar da sakwanta akunnan nata
Yace meya saki kuka bayan nagoge na'daxo
Tace nifa banyi kuka bah.

YUSUF ya lumshe ido tare da gyara kunciyarsa kallo 'daya xakamai kagano farincin da yake ciki awannan lokacin
Idan kuma kaqarema fuskarsa kallo kagano kishi da rikici kala kala a kwayar idansa

Yace 'daxo mexai kaiki gun Ya KAMAL.
LABEEBAH ta 6ata fuska kamar Yana gabanta Cikin shagwa6a Tace nifah gun XARAH xanje ba gunshi bah
Shuru yayi mata kamar ya sauka akan wayar
Har ta dubah koya kashene sai taga sa6anin haka
Shurun itama tayi tana jiran cewarshi
Ke da waye a 'dakin. Ya jefu mata tambayar
Taqarema 'dakin kallo tace ni 'dayace
Kashe wayan yayi yayinda tabi wayan da kallo tana tunanin shikuma wannan wane irin mutum ne.......
Bata ankareba takai kallantw 'kofah aiko saita ganshi a kofar 'dakin
Gabanta yafa'di
Yace naxone na miki saida safe tunda ke baki iyabah
Taturo baki Tace toh saida safam
Ya harareta Yace mutashi lpy Yana fa'din haka ya 6acema ganinta
Zuciyarsa cike dajin da'di dama yaxone kawai dan yaqara ganinta dan xuciyar tashice ta buqaci hakan


Ita ko Sam bata samu bacci yanda ya kamata ba dan xuciyar tata da fargaban YUSUF takwana

Washe gari bayan gari yayi haske Su Sagna sukayi skull
Dadynsu ya fitta
Yarage daga Momy sai Su LABEEBAH da YUSUF
Momy takalli LABEEBAH Cikin so da qauna Tace kuje kuyi breakfast mana ranah nayi
Tace toh
Nan sukayi dining ita da Sumayya suka cika cikinsu. Bayan sun dawo falanne YUSUF ya fitoh idanshi ya sauka akan LABEEBAH da take kusa da Momy
Gabanta yafa'di
Yace gudMrning my mom Tace Mrning my son da fatan katashi lafiya
Yace lafiya lau
Sumayya CE tafara gaisheshi kana LABEEBAH
Ya amsa Cikin kulawa kan yajah bakinsa yayi shuru
Ga mamakinsu sai ganin Momy sukayi taje dining ta ha'da mishi breakfast takawo mishi
Sanda ya bafara ci Yace tnx my mom Allah yabarni dake
Tace AmEEn my son
Bayan taxaunane takira darebansu Safna a waya Tace inasan xuwa anjima kakaimin wasu yarana gidan KAMAL. Yace toh ranki yada'de. Takashe wayan idanta akan YUSUF
Yace mexai hana insun gama in kaisu dan Xanyi tagun
Tace Yauwa mah


Sha biyu saura suka gama shirinsu tsaf tare da yima Momy sallama
Tace kwana biyu xaku mata fah. kodawo Ku qarashemin kwanakin naku
LABEEBAH tayi Murmushi Tace toh Momy
Sumayya Tace Su Sagna xasu xoko
Momy Tace eh kai xaku gansu
YUSUF Yace toh muje
Nan suka shiga motartashi duk kansu agidan baya suka xauna
Haka yajasu Sumayya nata xubah YUSUF na'dan biye mata
LABEEBAH dai binta take da eh ko aa
Yana yin fakin suka fara ciki kicin bu'de kofar Amma taqi bu'duwa
Fitowa yayi ya bu'dema Sumayya tafitoh Yace Auntyn naki xata rakani anguwa.
Sumayya tayi Murmushi Tace toh sai kundawo
Yace Yauwa qanwata Aunty XARAH
Tace toh
LABEEBAH najin haka tafitoh da sauri Tace niba inda xan rakaka. Tafa'di hakan da niyar bin Sumayya Cikin gidan
Ganin haka yasa yayi saurin riqo hannunta da sauri Sannan ya 'dagama Sumayya hannu alamun saisun dawo ta gya'da mishi kai.

🌡🌡🌹🌹🌡🌡
*MASEEFAR SOO*
🌡🌡🌹🌹🌡🌡


Sanda ya tabbatar da shigan Sumayya gidan Sannan ya kalli LABEEBAH da wani mugun kallo tare da sake mata hannunta ya bu'de mata gidan gaba cikin 'daure fuska Yace shiga mu tafi
Cikin tsoro tashiga kamar tarushe da kuka. Sannan shima ya shiga yajah motar
Awani gun shaqatawa yayi parking
Asan nanne ya kalleta Yace saboda kina xumu'din San ganin Ya KAMAL shine yasaki qin San binah
Ta kalleshi ka'dan Tace ni bashi nakesan gani ba
Yace maqaryacciya abin nan naban mamaki. Akanme xaki SOO Ya KAMAL Yana mijin 'Yar uwarki
Nima ban sani ba. Tabashi amsa cikin jin haushi
Yace dokokin daxan dinga miki shine
Wlhi naga ko da wasa kin kalli Ya KAMAL saina mugun 6ata miki Wlhi
Ke barima kiji namiki gwari-gwari daga yau banaso naqara ganinki da shi. Ko hanya ce taha'daku toh kicanja hanya. Sam karna kuskura naga kinyi sanadin daxaku ha'du da juna
Inba hakaba saina gayama XARAH cin amanar da kika mata nasan mijinta

Kuka LABEEBAH tafashe dashi mecin rai tayi da nasanin xuwa Abuja
Imin shuru kafin in maqureki anan
Shuru tayi
Yaci gaba da cewa dafatan kinji me nace miki
Cikin shagwa6a Tace naji
Yace gud my baby toh share hawayan ko banasan kukan.
Jitayi kamar ta sheqa mishi mari dan takaicinsa
Ya sata kuka kuma ya lallasheta
Saka bayan hannunta tayi tana goge hawayan
Ganin haka yasashi janyota jikinsa ya ha'data da qerjinsa Yana goge mata da hankicif 'dinsa ahankali
Itako lumshe ido tayi danjin da'din turaransa
Yace am sorry babyna xaki sha ice-cream
Ta'daga mai kai tayi ahankali



Yace. Toh bari na kar6o miki ko. Yafa'da yana me xareta daga jikinsa
Sannan ya fitta daga motar
Shuru LABEEBAH tayi tana tunanin shi
Tana kallo ya siyi biyu nashi da nata.
Ya shigo motar ahankali ya rufe tare da kallanta.
Ya gyara xamansa sosai yana fuskantarta. Tare da bu'de ice-cream 'din Yace toh bu'de bakinki
Ta kalleshi qasa qasa Tace xansha da kaina
Yace no nusuwata bu'de in baki. Taturo baki Tace nifah da Kaina xansha
Wani kallo yajefeta dashi. Bashiri ta bu'de bakinta yabata
Haka ya dinga bata tana Sha ha'de da lumshe ido dan da'di
Gareshi ko hakan ya fara jefashi cikin wani hali
Dan haka ya fara bata da sauri
Sanda takusa shanyewa tace ta'koshi
Bai matsa mataba yabu'de nashi yasaka mata kan cinyarta yace na baki dan haka nima saiki ban
Tawaro ido Tace banta6a bah atututan mutum abu bah
Yayi Murmushi Yace habah nutsuwata nine qatu. Yafa'da shima da waro idon
Tagya'da mishi kai alamun tabbaci
Yace bani dan Allah
Ta kalleshi ka'dan xatayi magana ya 'dan harareta
Murmushi tayi tafara bashi ahankali ahankali. Duk lokacin da xata bashi saiya wurga mata kallan SOO. Saitaji wani iri
Sam bata gane bah dan damuwarta shine yakaita gun XARAH. Ahaka dai yasha da'dan dama. Kana kallansu kaga masoya a xahiri Amma a ba'dili LABEEBAH batasan hakaba hasalima dagaske 'daxu xumu'din San ganin KAMAL 'dinne yaso hanata binsa kamar ya fa'di

Yauwa nutsuwata yanxu muje innuna miki garin abujah kafin mukoma ko
Tace toh dan Wlhi tsoran shine yake shigarta. Dan batajin xata iya mishi musu akan Komai
Haka YUSUF ya dinga yawo da ita yana jin da'di
Tabbas garin abujah ta ha'du iyakar ha'duwa hakan ne yasa LABEEBAH sakewa dan tanasan rayuwar yawo. Musamman tawannan tabu'de ido

Sun biya ta supermarket yasiya mata kayan xaqi da sauransu

Ahan yar Su tada wowane tana shan sweet Yana kallanta cikin SOO da kauna.
Yace nutsuwata
Takalleshi Tace meyasa kake kirana da hakan. Yace haka kawai dan kindace da sunanne. Shuru tayi
Shima shurun yayi........
Ta dubah wayanta ga mamakinta taganta akashe Tace la wayata tamutu bayan acike take da chaji. Tafa'da tana me kunna wayan. Sai taga ta kawo
Yace nina kasheta
Tace meyasa
Kai tsaye Yace saboda banasan XARAH da Ya KAMAL Su damemu
Tace Amma hakan yadace dan hankalinsu sai tashi kuma Wlhi inasan ganin........

Ya KAMAL
Ya katseta da fa'din hakan
Kobashi kikesan gani bah
Cikin wani yanayi Tace XARAH nakesan cewa fah
Yace gud niba qaramin yaro bane
Tace Wlhi XARAH xance......
Tsayawa yayi da motar agefan titin ya fuskanceta sosai Yace baxa kiga XARAH da Ya KAMAL bah. Dan yanxu haka gidan Momy xan maidake
Afurgice takalle shi tare dayin larai-larai da ido. Hawaye nasan xubowa
Ya gallah mata harara Yace Wlhi kika sake hawayannan ya xubu saina tsinkeki da mari.
Aituni tamai dashi tana 'kifta ido
Yajah qarimin tsaki dajan motar. Haka motar ta'dau shuru har suka iso gidan Momy xata fitta ne Yace kinga malama ban sallameki bah
Bata kalle shibah Amma tafasa ficewar
Yace idan Momy tatambayeki yasu XARAH kinuna mata kamar acan kika ini
Sannan idan XARAH takiraki kikawomin wayar ninasan abinda xan gaya mata.
kinji nutsuwata. Yaqarashe da lallashi

Tattaro jarumta LABEEBAH tayi tagallah masa harara Tace idan naqifah.
Yayi Murmushi Yace xaneki xanyi
Tace sai kace wata 'dalibarka
Yace lah😳
Aike yanxu kinxama 'yar rainona kinga bana saki asahun la'dibai naba
Dan kinsan shi 'dalibi malami yakan 'dan rangwanta masa. Amma 'yar raino bata buqatar rangunci
Ta kawar da kallanta daga kansa Tace kai xaka gane wannan karatun naka koko ince xauranci
Ya 'dan janyota jikinsa da muryar lallashi Yace kwarai da gaske Amma dan Allah kiyi abinda Nace miki plx kitemaken
Qara langwa6emai tayi tare da 'dago fuskarta xuwa kallansa Tace nima katemaken naga XARAH
Yace namiki alqawarin gobe xaki ganta da yardar Allah
Tace ko
Cikin marairaice mata Yace Allah da gaske
Yafa'da daniyar kai mata kiss πŸ’‹A mma ya fasa........
Xatayi magana kenan kiran wayan KAMAL ya shigo. takalli YUSUF ka'dan a'dan tsorace...



Da shagwa6a Tace Ya KAMAL ne in 'dauka
Cije le6e YUSUF yayi tare da qara maqaleta. ya kai bakinsa kunnanta Yace banaso ki'dauka Amma tunda kinaso 'dauka
Aiko da sauri ta'dauka tare dasan raba jikinta da nashi Amma yaqi yarda da hakan
Yaqara maqaleta
Tace hello Ya KAMAL................
Wani burkitaccen kiss YUSUF yakai mata awiya me shiga cikin jikin mutum batare da ya ankareba
Ai LABEEBAH batasan lokacin da tasaki wayan Tafa'di a gefanta bai. batir 'din ya fita
Mai makwan tabi wayan saita kwantar da kanta a qirjin YUSUF tabi wayan da kallo
shiko YUSUF abinda yake so kenan dan haka ya 'dago ha6arta
Yace yadai taturo baki kallo 'daya xaka mata kasan jikinta ya mutu. Da shagwa6a Tace wayan tafa'di
Cikin kwai kwayan Muryarta Yace toh me kikeso namiki
Tace nidai kakira min shi naji mexaice
Yace wlhi baxan iyaba nutsuwata
Saita fashemai da kuka tana cewa nidai gaskiya kakira shi
Shuru YUSUF yayi
Can Yace kinasan na kira miki shi ko
Ta'dagamai kai
Yace toh kibari anjima saina kira miki shi
Tace nidai.......
Ya katse da cewa xakiyi biyu babu in Kika matsamin
Shuru tayi
Shima shuru yayi

🌡🌡🌹🌹🌡🌡
*MASEEFAR SOO*🌹
🌡🌡🌹🌹🌡🌡

Sun 'dauki minti biyar 5 ahaka shuru mabai magana. Saima da'da langwa6emai da tayi
Ganin haka yafara shiga wani yanayi yasashi xareta daga jikinsa xaiyi magana kenan suka hango Safna da Sagna sun fitoh
Da kalleshi Tace dan Allah bu'demin Ya YUSUF plx
Saurin goge mata hawaye yayi da hankicif 'dinsa Yace plx kisan me xakice
Murmushi tayi tace kanasan koya min qarya.
Yace kare kanki xakiyi dan sunsan bana duka bare suyi tunanin ko na dakekine kanta tayi magana sun iso
Ya xuge gilashin motar suka leqo da kansu
Sagna Tace lah Aunty LABEEBAH yanxu fah muke shirin xuwa
Ta qaqalo Murmushi Tace eh gashi Ya YUSUF ya dawo dani
Tayi dariya Tace Yauwa gwanda dama kinga saimuyi kitsammu ko
Safna Tace hakane gobe maje
Ya yadanna gefan motar saiga kofar tabu'de da sauri LABEEBAH tafita tana cewa muje inyi Sallah saimu fara ko
Aiko Sagna da Safna suka bi bayanta Suna cewa bakiyi bah
Tace eh Wlhi

YUSUF yashafah kansa tare da sauke ajiyar xuciya dan ganin tamanta da wayarta ya 'dauka yajefa ajjihunsa Yace godiya gareka Allah
Na roqeka karkasa Yayana ya ankare da wannan baiwa taka
Idan Santa alkairine agareni kamallaka min ita
Yana fa'din haka yajuya kan motarsa daniyar yin masallaci.


Momy Tace yana ganki 'Yata
Ta'dan rufe ido cikin kunya Tace hmm inasan xama kusa dake ne Momy
Cikin jin da'di Momy ta rungumeta Tace ayya Nagode sosai 'yata ina tare dake.

LABEEBAH jin sanyi tayi aranta koba Komai tanada Masoya Innah Ya Usman XARAH Sumayya ga Momy mah. Kuma tana hangen tausayinta a idan KAMAL
Tagode ma Allah daya barta dasu

Haka tayi Sallah tayarfema Sagna da Safna Kansu da kitso Wanda kallo 'daya xakama kannasu kayi tunanin injinne ya xane kan dan tsabar kyau dakan da yayi

7:00pm nayi sai ganin Sumayya da YUSUF LABEEBAH tayi
Sanda suka ke6e Tace ya haka
Tace hmm Aunty LABEEBAH kedai bare Ya YUSUF akwai tsari bansan me yagama Aunty XARAH bah kawai sai cewa yayi inxo mu tafi tace ingaishe mata dake

Tace hmm namanta wayata a motarsa
Sumayya Tace nako ganta agunsa


8:30pm na dare ne Suna hirarsu me da'di a'dakin Momy. Momynma tana 'dakin Dady
YUSUF yashigo Yana cewa nutsuwata
Duk suka sura mishi ido
Sagna CE Tatashi tace Ya YUSUF kayi budurwane Yace me kika gani Tace Naji ka'ambaci nutsuwata ne
Ya saci kallan LABEEBAH tare da ta6e baki Yace share kawai xokiji
Tace toh tabishi
Safna takalli LABEEBAH qasaqasa batadai ce Komai
Sumayya ko taji meyace Amma tunaninta ko waya yagamayi shine yashigo da qarashen Kalmar a bakinsa.

LABEEBAH ko dama tasan da ita yake.......
Sagna CE tashigo da murnarta Tace Aunty LABEEBAH Momy nakira
Da sauri LABEEBAH Tace toh tana ina Tace tanacan falan mu
Toh Tace tafitta

🌡🌹🌡🌹🌡
*MASEEFAR SOO*
🌹🌡🌹🌡🌹

Waige wage tahauyi dan bata hango kowa bah
Ruffffff
Taji an rufe mata ido ta baya
Tajah numfashi dan tagane waye Tace Ya YUSUF.......
Yace na'am nutsuwata. Yafa'di hakan da xagayowa gabanta
Tace Kaine Momyn Yace eh
Tace toh miye
Yace kafin muxogun ya akayi kika gane nine
Kawar da kanta tayi daga kallan fuskarsa tace qamshinka ne ya ganar dani kai
Yace watoh kenan kinma qamshin turaran Ya KAMAL farin sani
Takalleshi ka'dan. Nan tahango rikici da futuna acikin idan nashi

_ai har duniya tana'de nayima turaran Ya KAMAL farin sani. Eh qamshinsa Yana sani nutsuwa. Tafa'di hakan aranta_

Afiliko cewa tayi aa banta6a riqe qamshin waniba sai naka
Yace gud
Dama kwalliyarki CE tamin kyau shine nakisan 'daukan ki photo
Taqare mishi kallo Tace kayi kyau kaima sosai
Yayi Murmushi Yace aisaimu mu'dauka tare in ba damuwa
Tace mexai kawota
Yace Mene
Tace damuwar
Matsowa yayi kusa da ita suka jera tare da seta wayanshi ya haskesu da hotuna
Haka yadinga 'daukarta Sannan Yace yunwa nakeji nutsuwata
Tace toh kaci abinci man
Ya kalleta da wurga mata mata wani shegen kallo. Wanda yasata sunkuyar da kanta da sauri dan taga irin abinda yake fitowa daga cikin KAMAL Wanda yake shiga idan ta shinetoh yake qoqarin shiga idan nata yanxu
Ya 'dago ha6arta Suna kallan juna Yace plx ki fanshi Momy dan Allah kiciyar dani yanxu
Da'da ware ido tayi Tace meyasa saini

Yaqara kusanta kanshi gareta kamar xai rungumeta Yace saboda natsinci kaina cikin farin ciki 'daxo da kikaban ice-cream plx gobema xaki qaraban. Yaqarashe da shagwa6e mata.
Ba qaramin rikicewa LABEEBAH tayi bah
cikin sauri Tace eh Allah ya kaimu
Murmushi ya sakar mata kana ya'dan nesanta kanshi da ita Yace muje ko
Cikin sanyi Tace xuwa inah
Yace Wlhi indai yanxu mah baki ciyar danibah baxan iya bacci bah kuma baxanci bah
Jan numfashi tayi Tace gaskiya kana da futuna Ya YUSUF
yayi Murmushi tare da kama hannunta sukayi dining Yana cewa Hakka abinxai kasance in raineki kema Ki rainan

Please Login or Register in order to submit comment