Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bawanda take gani sai hotan fuskar KAMAL
Yarikita mata ganinta tarasa yanda xatayi me kenan
Tafaru taqare
Dallacan kindameni da motsi tun 'daxo kin hanani bacci sai kijuyanan kijuyacan saikace me tattare da damuwa...
Zarah CE maima Labibah wannan furucin
Tace yi hakuri nakasa baccinne
Tace toh kitashi kiyi sallah man Ni bacci bakeji
Sam Labibah bataqi ta Zarah ba Tatashi tayi dayo Alwala tafara nafula......

Washe gari ta'dan jita garau
Zarah taxubah mata ido Tace lafiyanki ko naganki haka
Labibah takalli kanta amirro taga idanta ya'dan fa'da Tace mekika gani
Tace jikinki yayi sanyi da yawa
Tace nima haka kawai najini yau
da nayi tunanin baxan iya komaiba Amma naga harna'iya aikin gida
Tace damuwata dai ina lafiyanki lau. Labibah tayi Murmushi ha'de da riqe hannun Zarah Tace lpy nake 'Yar uwata Tace toh madallah



Kyakkyawan saurayine ajin farko fari tas. Kallo xakamai kasan ya ha'du tawajan ku'di ilimi nutsuwa hankali wayayye kuma karufe kallan naka daga gareshi da miskili ne me sanyin hali. KAMAL kenan

Misalin qarfe 5 da mintuna dareban daya 'dauko KAMAL daga airport ya saka hancin motarsa agidansu KAMAL 'din
Cikin nutsuwa ya fitoh yana qarema gidan kallo kamar yau yafara ganin gidan.
Yalla6ai shikenan ba wani abu ko. Direba ya fa'di hakanga KAMAL Cikin girnamawa
Yace no ba Komai yayi Cikin falon
Yayinda direba yayi gunyin parking dan ajiye motar

Hajjiya Anisa wacce suke kira da Momy mahaiyarsu tana zaune kan kujera tana danna waye. Mace kyakkawa taqarshe 'Yar duma duma
Da sauri KAMAL yaje Yakama hannunta ya sunbata Yace i miss u Momy
Cikin farin ciki Tace nima nayi missing 'dinka KAMAL. Ya kabaro min kakah
Tana lafiya tacema agaisheki. Toh ina amsawa
Yace yanaji gidan shuru bakowa
Momy tayi Murmushi Tace sunajinka suka shige aiki
Yace da kina famah dasuko
Eh wallahi bakaga yanda nadinga cewa sutashi suyiba Amma sukamin kunnan Uwar shegu
Yace hmm Salim fah. Tace Yana gun dadynku office 'dinsu wai suna lissafi akan fudda zakka Yace oho hakane fah danni kannaje kano nafitar da tawa
Tace madallah Allah ya qara bu'di. Kaje kayi wanka ga abincinka nan anjera maka Komai
Yatashi yana cewa AmEEn da shigewa shashinsa.

Yasami komai tsaf kamar yanda taxata. Nan yayi wanka ya canja kaya yana niyar fita saiga qannansa biyu Safna da Sagna
Suka durkusa suna gaidashi da mai sannu da xuwa
Cikin kulawa Yace Yauwa nasameku lafiya
Sukace qalau yayah ya kakah
Tana gaidaku
Muna amsawa
Suka fitoh atare.
Direct kan dining yayi.
Momy taxubamai abincin yafaci yana cewa yau nasamo miki sirika momy......
Saura ka'dan tasake cup 'din dake hannunta Tace KAMAL mekace
Yace dagaske Momy nasamo miki sirika Fatima-zarah
Zama tayi Cikin farin ciki da annushuwa ta'daga hannu sama tana kwarara addu yau tasamu labarin da takesanji
Tace a ina take kuma 'yar waye
Yace ba 'yar kowa bace dan iyayanta talakawane lis.
Tananan unguwarsu Auwal
Tace toh Allah ya tabbatar da alkairi Yace AmEEn Momyna.....
Dadyn shine yashigo shida Salim
Yace my soon kadawo Yace nadawo dady dafatan nasameku lafiya Yace qalau my soon dama inasan magana dakai inkagama kasaman Yace angama dadyna
Murmushi yayi yayi Cikin 'dakinsa ko ince shashinsa
Salim Yace sannu brother kadawo lafiya Yace lau lau ina maryam
Yasosa qeya Yace aitafi qarfina yayah shiyasa kawai narabu da ita. Yace ko
Yace da gaske
Momy tayi Murmushi Tace hmmm yaudai yayanka yaxomin da xance me da'di yayomin sirika
Da sauri Salim yakalleshi Yace kako kyauta yayah Allah yasa ayi damu
Yace AmEEn

Shin suwaye Bayin Allan nan


Alhaji Sale da Alhaji Nasir uwarsu 'daya ubansu 'daya Mahaifinsu yarasu tunsuna yara
Tun tasowarsu sun bu'di ido da ku'di dan haka su'din tun asulinsu masu dashine mahaifiyarsu hajiya Saude nanan da ranta
Itace suke kira da Hajjiya
Baqaramin so suke mataba. Itama tana sansu

Alhaji Sale da Alhaji Nasir suna San junansu
Sana'ar iri 'dayace watoh Su 'yan canjin ku'dine
Sannan basu tsaya ananba suna ta6a kasuwanci sosai
Shiyasa sukeda ku'di bana wasaba

Sunada mataye 'dad'dai
Alhaji Sale yana zama garin Abuja shida matarsa Hajjiya Anisa balarabiyace 'yar usuli dan acan Saudi Alhaji Sale ya Aurota
Mace mekyan hali dasan mutane Sam abin hannunta bai rufe mata ido bah. Dan kan tasamu sheda tagari
Sunada yara 4
KAMAL
Yusuf
Safna & Sagna
KAMAL shine Babba sai Yusuf Wanda ayanxu yake qasar Saudi da xama shida Matarsa 'yarcan dan iyayanta sunqi yarjemai yaxo musu da ita Nigeria Kasan cewarta ita ka'dai garesu
Toh dama shi Yusuf 'danba ruwansa ne. Dan yasaba da Saudi shiyasa baiwani damuba saboda yana ganin 'yan uwan momynshi
Dan haka aka musu Aure da Matarsa Mufeedat. Sunada 'yayansu biyu Sadeeq da Aliyu
Yusuf dai sana'ar saida gwala gawalai yake anan Saudiyan

Sai KAMAL wanda yake cikakken doctor nasalin ciwuka daban daban
KAMAL yasan kan aikinsa
Duk wani matashin doctor dayakejin kansa agarin abuja saidai yakoma Bayan KAMAL
Dan manyan qasarnan nasansa saboda kwarewarsa akan aikinsa
Suna girmamashi
KAMAL yataka matsayi babba danshi'din na musammanne

Doctor KAMAL waraka shine sunan da manyan doctors 'din kasarnan suke kiransa dashi
A England yayi karatunsa cibiyar bokan duniya

Gashi qaramin yaro Amma sai aiki
Dan Allah yabashi

Shekarun KAMAL ishirin da tara cif 29 Amma sai baiwar ilimi da sanin aikinshi

Wasu doctors suna mamakin aikinsa idan suka duba shekarunsa


KAMAL yayi ku'di bana wasaba
Saidai yanada zuciyar sadaka da kyauta shiyasa yakeda tarin Masoya

KAMAL yanada wani hali shidai bayasan hayaniya shiyasa baicika magana bah
Amma yanayi da wa'yanda yasani

SAIDAI FAH 😳 'DAN LUV NE 👈🏻

Yanasan soyayya Amma baisamu wacce tadace dashiba sai Fatima-zarah

Tunda Yusuf yayi Aure Momy da Dady suka sakashi agaba wai sai shima yayi

Shiyasa daya kawo musu xancan Fatima-zarah zuciyoyinsu suka cika da farin ciki

Tunda KAMAL yadawo daga karatu yakasance a Kano naniqe da Hajjiya kakah. Tsowuwar da take sanshi kamar ranta. bataso KAMAL yayi nisa da ita koka'dan
Shiyasa daya fara aikinsa Abuja yake xuwa duk qarshen. Wata yana dubata
Yakanyi kwana biyu haka. saiya komah
Bashakka Hajjiya kakana najin da'di

Yanxu ko jin da'dinta xaifi nada tunda yaxo mata da xancan Fatima-zarah
Ta'udurce aranta xata saka KAMAL yaqarasa gininsa nanan kusa da inda take yasaka Fatima-zarah aciki

Safna da Sagna ko sune 'yan autar Momyn KAMAL
'Yan biyune.
Masu bambancin ra'ayi
Itadai Safna yarinyace mehankali da nutsuwa Sam magana bata dameta bah
Shiyasa KAMAL yake shiri da ita


Yayinda Sagna takasance maraji da San shige shigen yawo da surutu
Ga 'dan rashin kunya dasan raini idan kasake mata
Amma tasan wa'yanda takema rashin kunyar tata.
Dan aduniya bawanda take jin tsoro kamar KAMAL dan baya mata da wasa Sam
Shine yake gyara mata xama

Ayanxu dai ita da Safna suna aji shidda na secondary Bayan dama sun kusa sauke alqur'ani da sanin wasu takaddun addini

Alhaji Nasir ko yanada Kano da xama inda Hajjiya kakah Mahaifiyarsu Tace baxasu watse Su barta ba.
Ba Alhaji Sale bashi baxai yuhuba
Dan haka yaxauna a Kano shida Matarsa Hajjiya Zainab
Yanada yara goma cif
Kuma "dayane dansa namiji watoh Salim
Ya aurar da mata hu'du4 saura biyar5 wayanda suke karatu uku kansu 'daya dasu Safna biyu kuma qannansu ne
Salim Yana harkar kasuwancinsa da Dadyn KAMAL.

Wannan sune asalinsu KAMAL
〰〰〰〰〰〰〰

Hira sosai KAMAL yakeyi da Momy Yana bata labarin Su Fatima-zarah
Yace kinsan wani abu.
Tace aa Yace dana ha'da ido da 'yar uwarta Aisha-Labibah sainaji gabana yafa'di
Momy tagyara xama Tace toh ita FATEEMA bakaji fa'duwar gaban agareta bah
Yayi Murmushi Yace banji komai ba illa sanda da qaunarta dayama xuciyata shigar baxata tanada kyau sosai ina Santa
Tace ita AISHA ba kyakkyawa bace
Yawaro ido Yace wow tanada kyau Momy sosai gatada da'din murya
Wallahi Momy inasan jin muryarta dan gaskiya tafi FATEEMA da'din murya
Murmushi kawai Momy tayi.


Washe gari KAMAL ya tashi ya kintsa kansa da shiga irin tasu ta likitoci doctor sai Qamshin turaransa yake
Yafitoh kenan daga part 'dinsa kamar ance yakalli window. Aiko yaga Sagna ta falle Ado meba fulayoyi ruwa da mari
KAMAL ya bu'de window da mamaki yaji tana xaxxagama Ado masifah wai dan tsabar iskanci Yana galinta xata wucce yawani watsa mata ruwan da yakeba fulayoyi
Yace Wlhi saginiyatu banganki bah
Ran Sagna yaqara 6aci dan tatsani yacemata saginiyatu dan haka taqara falleshi da mari Tace wai waye saginiyatu. Kullun saika kirani da sunannan wai Sagna ne baxaka iya fa'daba dan qauyanci
Ado yayi shuru yana ganin rashin mutunci irinnan Sagna. Sam bata ganin girman manya aqallah ya bata Kusan shekara shidda Amma hakan baisa ta raga mishi bah
Yace toh kiyi hakuri.......
Takaici ne yasa KAMAL wuccewa xuwa dining yana kuma mamakin Sagna Ashe rashin kunyar tata tawucce inda yake tsammani

Dady da Momy da Salim Safna suka kalleshi da mamakin 6acin randa yake fuskarsa Safna da Salim suka gaisheshi ya amsa. Sannan yagaida Su Momy
Dady Yace yanaga kamar ranka a6ace lafiyadai ko
Yace no is ok
Yafara break 'dinsa kenan Sagna tashigo falan fuskarta a 'daure.........

Ganin mugun kallan da KAMAL yawatsama yasa jikinta yafara rawa
Momy takalleta tata6e baki dan tasan babanxaba KAMAL yabita da mugun kallannan
Aiko Yace watoh kega 'Yar iska mara kunya ko
Shi Adon qanin ubankine daxaki falleshi da mari da haka

Tuni Sagna tarikice Tace dan Allah yayah kayi hakuri
Yace ko.
Tayi shuru.
Tashi yayi yabata mugayan marika biyu wa'yanda suka gigitata Sannan yayi boll da ita Yace duk ranar danaqara ganin kin 'daga hannu kin mari Wanda ya girmeki Wlhi ranar saina miki dukan mutuwa

Cikin kuka Tace Wlhi baxan qaraba
Cikin tsawa Yace jekibashi hakuri yanxu
Da sauri tatashi xataje yabi da qafah
Aiko takwasa a guje tana kuka

Yajah tsaki da 'daukar jakar laptop da wayoyinsa
Yace Momy Dady natafi
Xasuka mishi fatan alkairi yafito yashige motarsa sai hospital....

Cikin kukako Sagna takebama Ado hakuri
Baiyi mamakiba dan yaga futan KAMAL yana jifanta da harara
Yace karki damu saginiya.......
Baiqarasa ba tagallamai harara Yace yi hakuri Sagna
Kwafah tayi tayi falo

Momy mah harararta tayi Tace mutuniyar banxa aigwara yadinga gyara miki zama kokya kintsu
Dady Yace shashasha ba. kedai bakiyi hali mekyau ba dan albasa batayi halin ruwa Yana fa'din haka yafita shida Salim
Momy mah tashi tayi tabar falan
Aiko Sagna taqara fashewa da kuka gani take kowa ya tsaneta bamai Santa sai yayanta Yusuf dake Saudi
Tausayinta Yakama Safna Tace kidena kuka kinji
Kikuma tashi mutafi lokaci natafiya
Tsaki tajah tasa6i yakar skull 'dinta tafita batare da tacema Safna komai bah
Itama Safna nan 'daukar jakarta tayi tabi bayanta
Direban Su yajasu xuwa skull



KAMAL ko yana xuwa asibitin nasu yadinga kar6ar gaisuwa agun doctors da ma'aikatan gun
Dan dai KAMAL shina mutanene
Sakina 'daya daga Cikin ma'akatan itada Nafisat wa'yanda suke bala'in San KAMAL kuma qawaye ne Amma kowacce taqi yarda da manufar 'yar uwarta haka suke tafiya acewarsu kowacce tata tafish sheta
Suka gaida KAMAL Cikin girmamawa ha'de mai kwarkwasa
Yaxuba musu ido dan yada'de da harbu jirginsu. Nan take yatuno da Fatima-zarah yayi Murmushi yashige office 'din

Murna tacika su atunanin kowacce acikinsu ko yafara santa ne


KAMAL kam yau aiki kawai yake yana tumanin FATEEMA
Yayinda yake hasashen acikin satinnan xai koma Kano

〰〰〰〰〰〰

Suna tafiya Cikin nutsuwa dan xuwa gidan matan Bashir yayan Fatima-zarah dan kaimata 'dinkinta datasa FATEEMA takar6arnata
LABEEBAH Tace nidai naqagu mutumin nan yaqara dawowa
FATEEMA Tace wai meyasa kika damune Tace haka kawai dan naga ya cafki zuciyarki. Tayi Murmushi Tace ban 6oyemiki ba. Dan nafa'da miki tun shekaran jiya inamaji ajikina shi'din Mijina ne
Tace Allah yasa dan kundace da juna nidai fatana yadawo Wlhi hakan zaisani farin ciki
Tace naga alamar kinaso kifini 'dukin dawowarsa
Cikin tabbatarwa LABEEBAH takalli FATEEMA Tace kwarai Wlhi nafiki 'doki dan banaso wani yayi masa kwacanki
Cikin farin ciki Tace isiyaka yaruga shi fah
Dariya LABEEBAH tayi Tace harkin qara tunumin ranar da muka fara ha'duwa. Dan tsabar qarya kika wanice wai isiyaka ya rigashi
Wai wayema isiyakan
Cikin dariya FATEEMA Tace inafah nasanshi. Kawai bakina yafa'di hakanne
Tace Nasani ai
Dai-dai nan suka shiga gidan Bashir
Sunko taki sa'a Jamila nanan matarshi biyu dan aikwaita da yawo
Suka gaisar da Lami Uwar gida da take tsakar gida tana daka
Tace saiyau naga idanko LABEEBAH Tace hmm makaranta ne yake 6oyemu
Tace bawaninan islamiya kawai kuke xuwa.....
Kan taqarasa Jamila tafitoh tsakar gidan tana cema FATEEMA ina saqon nawa
Cikin rashin kulawa FATEEMA tabata dan taga tana wani yatsina.
Aiko tafusga takoma 'dinta
Lami tata6e Cikin 'daga murya Tace bagani Xanyi dakika wani shige afusace
Jamila talequ dakanta Tace Ai? Harkin xargi kanki. Mumafuka me shegen saka ido
Wai wai wai😳 Cikin 6acin Lami Tatashi xatayi 'dakin Jamila nan LABEEBAH taruqota
uwarkice munafuka mesa ido 'Yar gidan matsiyata
Lami tafa'da cike da 6acinrai.
Aiko Jamila tafitoh itama tafitoh tarama xaginda tamata. Nan fa'da yakaure daqer Su FATEEMA suka raba fa'dan Bayan sunjama Jamila kofarta




Xama sukayi a tsalar gidan suna kuma tausar Lami
ABEEBAH takalleta Tace Aunty Lami meyasa ko yaushe kuke Cikin fa'dene
Tace hmmm barni da ita Wlhi saina koya mata hankali 'yar iska ta Auremin Miji kuma tafini kishi akansa
LABEEBAH taqara gyara xama Tace wai miyene kishi
Lami takalleta gala gala Tace kishi. Bakisan kishi ba
Tagya'da mata kai Cikin tabbatarwa Tace bansanshi Amma koma ya yake nasan yana xuwane agun wa'yanda suka 'dau keshi da xafi
Dan Allah Aunty Lami kudena fa'dace fa'dacannan Sam Bashi da fa'ina. Kucire Komai aranku kuxauna lpy ko ya Bashir yasami kwanciyar hankali
Murmushi Lami tayi tana niyar magana FATEEMA tajah tsaki Tace hmm Ni tashi mutafi inkuma ba yanxu xaki tafiba kinga tafiyata.
Tana gama furucin taficce agidan
Cikin sauri LABEEBAH tabita tana yima Lami sallama


Da gudu tacin mata Tace wai meyasa bakyaba Su Aunty Lami damarki.
Na lura duk lokacin dasukayi fa'da bakya bada hakuri kodai kice wani Abu
Tace hmm haushi sukeban saisu dinga abu kamar wasu marasa hankali
Toh wai miye abun fa'dan dan Allah. Taqarashe kamar dajan tsaki
Shuru LABEEBAH tayi har sukaje gida

Mamah Tace kundawo. Cikin rashin walwala FATEEMA Tace eh.
Mamah takalli FATEEMAN tace kunsa mesu suna abinda suka saba ko
LABEEBAH Tace me kika gani mamah
Tace hmm naga fuskar FATEEMA ne a murtuqe
Murmushi LABEEBAH Tace Tace eh ai baxasu denaba
Yauwa mamah fa'damin menene kishi
Mamah tamaida kallanta kan LABEEBAH Tace kishi wani abune Wanda yake jikin kowane halitta kuma yarabu kashi biyu ne dana hankali dana rashin hankali
Na hankali shine Wanda kanajinshi Amma kake
Danneshi dan karya fito bare gangar jikinka yanuna
Na rashin hankaliko shine wanda Yana taso maka kake saurin baiyanashi har yasaka ka aikata abinda bai daceba

Ya mutun xaiji daxaran yataso masa.
FATEEMA CE tafa'di hakan

Mamah taqara gyara xama da kallanta Tace mutum yakanji ya tsani wanda abun kishin ya ha'dasu
Yakanji ranshi Yana 6aci idan yaga abin sansa yanasan wani
Hankalinsa natashi idan yagansu Cikin farin ciki
Saiya dinga rayawa aransa dama nine

Idanko ya kasance dama wanda yakeso zuciyarshi abin sannanshi biyune wato kubiyu
Toh idan yaga abin San nashi yakula 'dayan har yabashi wani dama suna Cikin farinci. Toh sai xuciyarshi ta tinxira tafara ganin kamar sunci mar fuskane ko yacimar fuska.

LABEEBAH tajah numfashi Tace toh Allah ya rabamu da ciwan kishi
Ananne FATEEMA tayi dariya Tace wato kishinne ciwo
Mamah takar6e da cewa kwarai kishi ciwone XARAH

Bayan kwana biyu ne. Xuciyar Aisha-Labibah. Tagama nisa Cikin soyayya da qaunar KAMAL
Wanda sanda kowa ya tambayeta miyene matsalarta me yake damunta
Shuru takeyi musu dan itakanta tarasa dalilin dayasa daga ganin mutum so 'daya Amma xuciyarta tacika da qaunarsa

Yanxu hakama xaune take Cikin dakinta kan 'Yar loluwar katifarta tana tunaninsa tana addu'ar Allah yasa taqara ganinsa ko xuciyarta tarage mata ra'dadin da take mata

FATEEMA tashigo da murnarta tana cewa ketashi Ashe har angama maganar Rukayya da ya Usman.......
Sam LABEEBAH batasan FATEEMA rashigoba sanda FATEEMAN ta ta6ata taqara da cewa wai wane irin tunani kikeyine LABEEBAH Wanda yake gusar miki da tunaninki
Me yake faruwane.

Cikin sanyin yanayi LABEEBAH Tace nima bansan me yake shirin faruwa daniba
Jinake idan bashi baxan iya rayuwa bah. Gashi ya 6oyema ganina yaxanyi FATEEMA plx kitemaken saiga hawaye.

Cikin rikicewa FATEEMA Tace mekenan LABEEBAH
Waye shi
A ina yake
Kalamanki sun nuna kinfa'da soyayya
Yaushe hakan tafaru bansani bah

Share hawayanta LABEEBAH tayi Tace wani saurayine yatafi da imanina.
Kallo 'daya namishi naji gabana yafa'di

Nagane sanshi nakeyi ne sako makwan kasa bacci da nakeyi

Ya rukitamin tunanina FATEEMA
Ya burkitamin kwakwalwata
Ya gur 6atamin tunanina da sanshi da qaunarsa.

Idan mukaje islamiya me makwan inyi karatu saikiga nafa'da tubaninsa

So 'daya nagansa. Amma yatafi ya barni da tunaninsa
Wlhi FATEEMA ba wani Abu wanda xai faran tamin rai ayanxu face ganinsa.
Taqarashe ta rushewa da kuke.

Jan ajiyar xuciya FATEEMA tayi tare da tausayinta ta guge mata hawayan nata
Kana Tace yaushe hakan tafaru kuma a ina
Tace ranar Jumma'a da yamma Bayan mundawo daga islamiya
Mamah ta aikeni shine nagansa yaxo huccewa
FATEEMA Tace rana 'daya kenan da muka ha'du da wannan mutumin dayace yana sona kin tuna
Da sauri LABEEBAH Tace eh ranar

Amma meyasa tun aranar baki gayamin bah
Tace hmm lokacin abin bai daman hakaba
Tace har yau kuma baki qara ganinsa bah
Tace eh ban qara ba

Meyasa xuciyarki takamu tasan wanda bata sanshi.
Meyasa tamiki wannan rashin adalcin

LABEEBAH tajah numfashi Tace duk iya tunanina narasa gano dalili

FATEEMA takalleta cike da tausayi Tace toh Allah ya bayyana miki shi
Tace AmEEn


FATEEMA tafitoh kenan daga gidansu LABEEBAH taga wata shegiyar mota ta faka a kofar gidansu. takalli me mallakin motar........
Waxata gani saurayin daya caki xuciyarta takejin xai xamo miji agareta

KAMAL yafitoh Cikin qasaita ya jingina da jikin motar.
Saiya bala'in yin kyau
Takawar da kallanta daga gareshi xata shiga gidansu Yace
Haba XARAH me nayi daxa'a nunamin rashin kulawa haka kamar ba'a sanniba
Takalleshi Tace dama ansanka ne
Yace eh mana.
Nasan ba'a manta da niba kawai xa'amin alayene
Tayi murmushi Tace kaga Malam idan tambaya xakayi kayi dan an hanani magana da maxah tunda akamin Miji........

Sam FATEEMA batasan ya akayiba sai ganinsa tayi agabanta
Yace Mene
kina nufin an miki Miji
Tace eh wani abune
Yace eh
Kitemaken kije kice bakisan wanda xa'a bakin plx
Yaqarashe da muryar shagwa6a kamar xaimata kuka.
Abinka dame tausayi. saitaga yabata tausayin. Dan tunaninta kuka zaisa mata
Tace wasa ne
Da sauri yasauke ajiyar xuciya
Yace nagodema Allah
Ina sanki XARAH kisoni plx
Tace hmmm matsamin nashige gida
Yawaro ido waje Yace haba my TEEMAH. Kiyi baqo Amma kidinga qoqarin raba kanki dashi

Ta kalleshi Tace me kakeso yanxu
Nuna mata kan dakalin qofar gidansu LABEEBAH yayi da hannu alamar suxauna
Ba musu taxauna shima yaxauna qamshin turaransa na bugarta Yace sunana KAMAL nidai doctor ne banda Aure
Momy na da Dady na suna raye
Ina da qanne uku Yusuf shine yake bina yanada mata sai mata masu binshi 'yan biyu
Safna da Sagnah

Da fatan kin gamsu dani kuma xaki soni kamar yanda nake sanki.
Tayimai fari da ido Tace Xan soka Amma sai 'yar uwata tayarda da hakan
Yace wacece kenan
Tace Aisha-Labibah
Yace OK nasan xata soni. Tace ko Yace gaske

Aisha-Labibah ko tana nan yanda FATEEMA tabarta Amma kuma saita tsinci kanta da dajin fa'duwar gaba.
Yayinda tadingajin qamshin turaran KAMAL yana bugarta.
Hankalinta sai yatashi.
Dan haka taxaro hijab dinta danufin fitowa. Danta tabbatar da xargin da xuciyarta takeyi

Ina xaki da sauri haka. Kamar me tashi sama
Mamah tafurta hakan idanta akan LABEEBAH

Tace bako ina xandai kar6i abu gun XARAH ne
Shuru mamah tayi tana qura mata ido
Candai Tace meyake damunki ne AISHA
Tace bafa Komai mamah kawai kainane yakemin ciwo kuma nasha magani

Shine yasaki kuka
Tace eh
Mamah cigaba tayi da aikinta Tace aishikenan

Da xafin nama LABEEBAH tayi hanyar waje. Amma kuma sai taci karo da XARAH
Tace Yauwa LABEEBAH
Wannan mutumin yaxo. Cikin farin ciki Tace kai haba. Tace Wlhi da gaske
Tace yayi dai dai muje in ganshi. Tace dama kenaxo kira.
Aiko LABEEBAH takama hannun XARAH suka fitta

Subhanallah. Aisha-Labibah Tace aranta. Sabuda wani kyau da KAMAL yaqara mata akaro na biyu na ganinta dashi
Cikin fara'a Yace lale marhaban da qanwata

Cikin sanyin murya da daidaita nutsuwa Tace barka da rana datafan kaxo lafiya
Yace lafiya qakau qanwata
XARAH Tace yaxo da Babban al Amari wai sai xuciyata tasoshi. shine nace saikin amince hakan tafaru

Tace daga ganinsa baxaiyi cutaba. Dan yayi kama da masu rike alqawari

Na hango sanki kwance mala mala kwayar idansa

Kisoshi plx dan Allah ina tayashi roqo dan tani na amince

Gud my qanwa kinyi kinha'du
Gaskiya da ana samun irinku Masu gyara so. Toh dako Masoya baxasu dinga shan wahala ba
Naji da'di axuciyata daga yau nabaki wani matsayi acikinta.
Nagode sosai

Cikin farin Cikin furucinsa Aisha-Labibah ta rufe fuskarta Cikin shagwa6a Tace ba godiya tsakanina dakai yayana. Dan abinda yadace kenan nayi
XARAH Tace hmm Lalle kaxo da qafar dama
LABEEBAH Tace ba mamaki kam. Toh ina muku fatan alkairi Tana fa'din haka tashige gidansu XARAN
KAMAL yabita da kallo kana ya maida da kallan nasa kan XARAH. Yajefa mata wani shu'amin kallo Cikin kwayar idanta. Wanda yasata sunkwai da kanta batare data shirya bah. Zuciyarta na mata da'di sanshi na shigarta
Xo gareni my luv plx yafa'di hakan da wata murya me da'di

Fa'dawa gadan Innah Aisha-Labibah tayi Cikin farin ciki ta rungumi fitoh
Wani da'dine yake xiyartar xuciyarta. Sai taji duk duniya ba abinda xaidinga sata farin ciki kamar tadinga kallan KAMAL ako yaushe kuma tadinga jin muryarsa. Me kashe mata jiki

Innah Tace meya miki da'di ne LABEEBAH yau naganki garau haka
In ban mantaba kinkai kwana biyar ban ganki cinkin sukuni da farin ciki haka ba.
Sumayya tace kwarai da gaske Innah yau farin cikin Aunty LABEEBAH na musam manne

Da murmushi Aisha-Labibah Tace hmm yau naga abinda yafimin Komai da'di a duniya Innah. Kuma har Cikin jinina da xuciyata 💗.
jina nake nafi kowa farin ciki yau

Innah Tace ikwan Allah wannan wane abune. Cikin sanyi kuma Tace wani abune wanda da alama xai wahalar dani kuma ba samun shi Xanyi bah
Innah tata6e baki Tace bidai ahankali dan in kika fa'da soyayya nice wacce Xan fara kwace miki mijin naki inga ya xakiyi
Simayya tayi dariya Tace wayaga idan Aunty LABEEBAH ranar
Duk sukasa dariya.
LABEEBAH Tace banso naxo asunan kakarki bah innah dan nasanki da riqe Miji kar6a Ki kwacemin shi da gaske
Tace aiko saidai in ban ganshi bah
Cikin dariya Tace baxan bari kiganshi bah...
Ahaka FATEEMA tadawo tagansu Cikin farin ciki taxauna jagab tana niyar magana Saiga wani yaro Yana shigowa da kaya. Sanda yagama tsaf. Innah Tace kai kayan waye haka Yace wanine Yace in kawomah Fatima-zarah wai ince KAMAL ne
Cikin wani yanayi LABEEBAH tamaimaita sunan abayyane Tace KAMAL
XARAH takalleta Tace ai sunanshi kenan
Tace abin mamaki
Tace namefah
LABEEBAH tagyara xama Tace sunansu 'daya
Da sauri XARAH Tace da Wanda yasace xuciyarki Tace eh Wlhi
Tajah numfashi Tace mun xama 'daya kenan

Innah Tace kuncikani da surutun dana kasa gane kansa
Shin waye KAMAL
Nan LABEEBAH Tace wani ne Yace yanasan XARAH tun ranar
Shine sai yau yadawo
Innah tabi kayan da yaran yashigo dasu da kallo Tace shine yaturo da kayannan LABEEBAH Tace eh
Innah tamiqe ta'dauki gyalanta taleqa waje. Aiko bataga kowa bah tadawo Tace yatafi Dana maida mai da kayansa

Sumayya Tatashi tajanyo kayan tana dubawa
Dogayan rigunane da takalma da hijabai acikin ledar farko
Da'yar nedar kuma kayan tie ne danginsu madara vombita da Milo suga bota dadai sauransu
Sai kudi bandir 'daya 'yan Dari bibbiyu

Kunsan Sumayya da kwa'dayi tuni tafara ha'diye yawo dan ganin madara da milo
Baban sune yashigo da sallama da ledar cefane a hannunsa
Innah talar6a tana amsa sallamar tasa
Yace kayan wayene haka
Innah takoromai Bayani. Yace Ayya KAMAL ne Ayya gabatarmin da kansa kanaki.
Amma ke

Please Login or Register in order to submit comment