Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mamakinta. Ga KAMAL ko jin shi yayi wani iri


Tsohuwace me kalar kamala da nutsuwa suka gani afalan tare da Momyn KAMAL har dasu 'yan biyu wato Safna da Sagna

Da murna sosai kakah ta tarbi su XARAH Tace lale barhaban da xuwanku jikokina
Auwal yayi dariya Yace waya gaya miki anama kishiya lale mar haban
Tace um um Auwalu wannan nayi shekara da shekaru ina jiranta sai yau Allah yayi
Cikin ladabi XARAH da LABEEBAH suka xauna a qasa suka gaisheta
Ta amsa da farin ciki. Safna da Sagna suka gaishesu
Sannan suka gaida Momy
Cikin wani irin *SOO* da qauna ta amsa tana cewa Sannunku 'yan albarka gaskiya naji da'din ganinku
Kakah Tace wacece kishiyar tawa. LABEEBAH tanuna XARAH
Momy Tace eh lallene sirikar tawa kyakkyawa CE
KAMAL Yace ai nagaya miki
Tayi Murmushi Tace ga 'Yar uwartama kyakkyawa
Yace hmm momy sai shagwa6a ta'ajiye
Tace ai da ganinta
Safna ce ta ajiye musu kayan marmari Sagna ta'ajiye abinci

Ganin kan XARAH aqasa yasa Safna Tace Aunty XARAH Ki 'dago kanki man naganki
Shuru tamata tana wasa da hanunta

Momy ta qurama LABEEBAH ido. haka kawai taji qaunarta nashigarta

KAMAL Yace yaushe kika xone Momy
Kakah Tace yan xun nan shigowarsu kenan sai gaku

Tashi Momy tayi. Tayi wani shashi na falan tana Murmushi xuciyarta cike da qaunarsu XARAH

Kakah tasake sai jansu take da hira LABEEBAH na biye mata
Al'amarin daya bah KAMAL da Auwal mamaki kenan ganin bata da'de da gama musu kukan shagwa6a bah

Can sukace xasu tafi. Nan take fuskar kakah ta sauya
Auwal Yace Xan da'da dawo miki dasu Tace toh Allah yasa Yace AmEEn kakale

Safna tagayama Momy xasu tafi nan tafitoh hannunta 'dauke da kayan kwalliya taba Sagna takai musu mota Sannan tamusu fatan alkairi
Kakah ko har Mota tarakasu tana samusu albarka. Suka tafi
Safna Tace kai Amma budurwar Ya KAMAL akwai kunya da kyau naji Santa Cikin raina da 'Yar uwarta
Tsaki Sagna tajah Tace hmm Ni 'Yar uwarta tafimin kyau kuma nafi Santa
Safna Tace eh tanada kyau Amma shi XARAN yagani saikije kice ya canja da ita
Tace kinga malama ba magana nanema bah. fa'dar ra'ayinki kikayi. Nima nafa'di nawa wani abune. Ta qarashe da mata kallan tuhuma.
Cikin takaici Safna tayi ciki batare da tace mata komai bah
Sagna tajah tsaki ha'da da kara wayarta akunnanta


Su XARAH ko suna xuwa gida LABEEBAH tayima kanta gata ta shige gida
Dan mutanan nata sunfara xaxxagama junansu kalaman *SOO*
Sai dai murnarta 'daya bataba KAMAL hankicif 'dinsa bah


Wannan dare baccin farin ciki LABEEBAH tayi
Dan kowane juyi tayi. To saita shaqi qamshin turaran dake jikin hankicif 'din KAMAL
Har washe gari XARAH Tace dama xaki tsaya ahaka mana
LABEEBAH Tace ban gane bah
Yanda kike Cikin farin Ciki yau dama kullun kike haka XARAH tace da ita hakan

Murmushi LABEEBAH tayi tace ba lefi nasamu wani abu na KAMAL wanda duk lokacin da naga abun jinake tamkar ina tare dashi
Ta6e baki XARAH tayi Tace hmmm qarya Allah dai yakawo miki sauqi *a MASEEFAR SOO.*
Cikin wani yanayi Tace nafa'da *MASEEFAR SOO*
Yaxanyi 'Yar uwata,
Xuciyata ta cuceni da taso wannan koda ya baiyana agareni baxan ta6a Auransa bah

Da nuna mamaki XARAH tadena game 'din da takeyi takalleta gami da cewa Me yasa.
Bayan kina sansa. Towaima me kenan kikayi
Ya baiyana agunki Amma kiqi auransa sabodame
_saboda ke. Xan'iya kishi da kowa Amma baxan iya dakeba. LABEEBAH tafa'di hakan aranta_
Afili ko cewa tayi. Haka kawai
Shuru XARAH tayi dan jinta kawai tayi


〰〰〰
Yau take jumma'a
Kuma yaune aka tashi ta tirqewar hadari a garin na kano
Tunda Allah ya wayi gari LABEEBAH take Cikin farin ciki dan sanda kowa yagane hakan
Dake yanxu 'yan gidan sunsa mata hawainiya me canja kala akowane lokaci shiyasa bawanda ya tambayeta farin Cikin me takeyi

Itako yau tashi tayi da MASEEFAR SON ganin KAMAL
Sai xuciyarta tabata hakuri dan ganin gobene ranar xuwansa
Sumayya ce takasa hakuri Tace mamah nifa ina ganin dan Aunty LABEEBAH taga hadari ya ha'dune shine take farin ciki
Da sauri mamah Tace kumafah gaskiyarki Sumayya
Dan gashi har tayi shirin tarbarsa
XARAH tayi dariya Tace Allah LABEEBAH yau Karki shiga ruwa kin manta shakaran jiya yanda kika kwana hanci a tushe
Tace kudai kunkasa ganewa ne. dan ba'abinda yafi farin ciki kamar anayin ruwa mutum yashiga yana juyi aciki.
Wow Wlhi ina tsintar Kaina cikin farin ciki. Kunga nayi kofar gida. Bata jira cewarsu bah tayi kofar gida abinta

XARAH tagyara kwanciyarta tace da Sumayya yanxu ruwa xai tsinke
Tace aikowa dai

LABEEBAH na fitta taga wata lafiyai yiyar motar tayi faking a kofar gidansu
Tabbas gabanta yafa'di dan har tayi tunanin ko KAMAL ne
Tuni xuciyarta tabata bashi bane dan baicika xuwa awa'dannan ranakun bah
Gilashin motar me duhune dan haka bata gane wanda yake ciki bah

Shaaaaaaaaaaaaaaa
Ruwan sama ya yanke kamar da bakin kwarya
Ai tuni LABEEBAH tayi 'dan kwanan da take tsayawa idan hakan tafaru
Ruwa ne ake zab gawa sosai
Yanda yake sauka a qasa haka yake sauka akan LABEEBAH
Sai tsalle take tana murna tana 'daga kai sama tare da lumshe ido tana Murmushi
Lokaci lokaci kuma take 'dan juyi
Kallo 'daya xaka mata kagane tana Cikin farin ciki

Mamaki da Al'ajabi gami da Takaici suka cika KAMAL
Dama shine a motar. Kuma tunda aka fara ruwan idanshi yake kanta
Eh tabashi sha'awa
Amma shi mutum ne mesan yaga mutum na tattalin kansa. Kodan gujema kamuwa da ciwuka
Shuru yayi yana naxarinta. Watoh itadai Sam bata da damuwa. yarinta na damunta. bata da matsala

Zuwa can cak ruwan ya 'dauke
Aiko taturo baki irin bataso haka bah
Yaxatayi dole tafitoh daga gun daniyar shiga gida
Xuge gilashin motar yayi. Yace Laveeba.......
Tun daga tsikiyar kanta taji wani xirrrrr har xuwa babban 'danya tsanta na qafah jitayi wani sanyi ya shigeta ha'de da birki cewa
Ya lura da birkicewarta
Ta juyo ahankali. Karaf suka ha'da ido. Ya ko dallah mata harara. Tayi saurin sun kwiyar da kanta
Zonan Yace da ita
Ahankali taje gunsan jiki shaqaf
Yace bakyasan lafiyarki ne
Ta girgixamai kai. Alamar aa
Baki da bakine
Takalleshi tare da qara girgixamai kai
Cikin fusata Yace baxakiyi magana bah
Cikin sanyi ha'de da nuna tsuro tace xanyi fah
Yaqara galla mata harara Yace xan qara ganinki ne
Taturo baki Tace waitoh menayi
Quqarin bu'de motar yakeyi dan fitowa
Aiko tafalle da gudu tashige gida
Abin yabashi dariya
Abaiyane Yace wannan mijinki yanada aiki

In kaine yaxakayi
Xuciyarshi tatambayeshi
Innine maqure xan dinga yi. inyi maganin shagwa6arta.......
Da sauri yayima kansa dariya ha'de da cewa abaiyane. Toh bama nibane.
Tanada aibine
Xuciyarshi taqara tambayarshi
aa
Yabata amsa still abaiyane

Mamakin kansa yafarayi ganin xuciyarshi na mishi wasu tambayoyo masu kama da Wanda yakesan fa'dawa wani yanayi
Na me kenan
Na SOO
Xuciyar tabashi amsa da sauri
Ga bansane ya bala'in fa'duwa.
Yayinda yayi saurin kawar da tunanin Yana murmushin tsoro
Fatima-zarah & Aisha-Labibah
Yace abaiyane
Tuni yakori tunanin xuciyarsa ya 'dauko soyayyar TEEMAN Sa yasaka agaba hankalinsa kwance


Kun gani ko taje ta jiqe shaqaf. Cewar Sumayya
Mamah ta galla mata harara Tace Naji kince min kanki namiki ciwo ko mura na damunki
XARAH ma harararta tayi taqara da cewa kokuma ta'ishe mutane da jan hanci bah

Shuru ta musu dan jikinta ya mutu mu'dus ba abinda takeso ayanxu kamar taka'daice tayi tunanin masoyin nata KAMAL

Ana kiranki awajefah tafurtama XARAH hakan kamar xata fashe dakuka
Sumayya tayi dariya Tace dan an'dauke ruwanne kikesan kiyi kuka
Ta harareta Tace ban saniba
Wa yake kira na
KAMAL tabata amsa Cikin sauri
Kan XARAH taqara magana wayanta ya 'dau ruri
My luv ganinan gareka masoyinah
Haka kawai Tace Tatashi ta ficce
LABEEBAH ta shige 'dakin mamah tana xubar da hawaye
Wane irin soh nake maka KAMAL
Duk lokacin dana ganka saika sani kuka ha'de da burkitani
Take fa'dar hakan axuciyarta
Wayarta ce tafara ringing tana 'dagawa taga KAMAL ne
Nan take mamaki ya kamata. Ta'dauka
Kitemaka kiyi gaggawar canjah kaya dan Allah Yace da ita hakan
Murmushi tayi Tace toh
Yace ban jiba
Tace cewa nayi toh

Kashe wayar KAMAL yayi yamaida kallansa kan XARAH asanyaye
Ya rasa dalilin dayasa yake bala'in jin da'din muryar LABEEBAH
Ashe awayama tana da'di haka
Kaji shuru my Luv kana kallona kamar ka shiga tunani
Yayi saurin kawar da kansa Yace kyanki nake wara gani Wanda yake hanani bacci maye sirrinne
Tayi dariyar jin da'di Tace bawani Sirri my luv
Yace da gaske yanxu LABEEBA baxata canjah kayan jikinta yanxu bah
Tace karka damu tasaba Amma tunda kamata magana xata canjah
Yace kice inada darajah sosai haka
Tace kaima kamanta ne. sunanka 'dayafah da KAMAL 'dinta. Ai ina ganin idan aka cire iyayanmu xakafi kowa daraja a idanta
Yayi Murmushi


Xuciya da abinda takeso ai ko minti 'daya LABEEBAH bata qaraba ta canja kayan jikinta tana 'dan Murmushi dan kulawar da KAMAL yabata tamata da'di hakan ne ya kori kukan da takeyi











MASEEFAR SOO
〰〰〰〰〰〰
Rayuwa kenan
Yau taxo maka da da'di gobe taxo maka sa6anin hakan
Haka watanni suka shu'de masu XARAH da KAMAL & LABEEBAH

Toh yau Allah yayi saura sati biyu bikin XARAH-da-KAMAL
Tun yanxu suka cika da shagalul lukan biki

'Din kunane baje akan gadan Innah na XARAH da LABEEBAH Wanda KAMAL yakawo musu
Ko wacce kala goma goma

Shiri suke dan tafiya sweet-faty
Sanyi kyau sosai Cikin shigarsu ta doguwar Riga ta materiyal jah me ratsin ash Colo sunyi kyau sosai
dan kam kallo 'daya xakama shigarsu kagane sunyi shigar alfarma dan tsadar kayan
Aikin KAMAL ne

Qawayansu na islamiya dana skull ne sunkai Su ashirin kuma kowacce tayi shiga takerema sa'a

Jamila 'daya daga cikinsuTace kai habah LABEEBAH lokaci na tafiya yaushe kukaje make-up kuka dawo har mutafi

Au namanta anqara awa 'daya ban fa'damiki ba. LABEEBAH tace da ita hakan

Sumayya Tace kunga kutashi mufara gaba tunda dama daga canne xasu hucce
Sukace toh sukayi can

Su XARAH na fitowa Auwal Yace 'yan gatanka sunfito
Cikin sauri yakai kallansa Kan XARAH nanko suka ha'da ido tasakarmai Murmushi
Yace wow. Kyau haka tunkan ayi make-up ya dire kallan nashi akan LABEEBAH
Wacce tunfarko tayi qasa da kanta tana wasa da xoban hannunta
Tace toh munji. Yanxu dai muje mutane sunfara qorafi
Yace aikowa dan muma yanxu muka gama bada hakuri dan haka ku shiga da sauri


Hiyana make-up beauty sukaje
Nan tagyara amarya XARAH tsaf ha'de da LABEEBAH
Duk iya hangenka qaryane kagane wacece amarya tsakanin XARAH da LABEEBAH
Tun amota KAMAL yaketa satar kallansu
Wani abokinsa Jameel Yace dan Allah XARAH kiban 'yar uwan nan taki plx dan Allah
Tace wa ni😳
Rabani da LABEEBAH karkasa saidai inga tana yima wasu dariya bani
Da mamaki Yace ban gane bah
Shuru tamishi
Yayinda LABEEBAH tayi fuska kamar ba akanta ake maganar bah
Jameel ya maida kallansa kan KAMAL kamar xaiyi kuka Yace tayimin shuru
KAMAL yayi Murmushi yace wacce acikinsu
Yace XARAH da ita 'din mana
KAMAL Yace hmm. ai indai MATAR KAMAL CE baxaka ta6ajin ta bakinta bah
My XARAH ko bata da abin cewane shiyasa yin shuru
Cikin sauri yace MATAR KAMAL. Kana nufin ita'din matar Aure ce. kuma mijinta ya barta haka
KAMAL Yace aa fah. Ba haka nake nufiba
Sunan saurayin natane KAMAL me sunana

Jameel ya ta6e baki danuna kishi Yace yabada sadakine
Bana tunanin hakan Amma ban saniba. KAMAL yabashi amsa ataqaice
Yace wow Allah Nagode mah dani xa'ayi
Cikin sauri XARAH Tace hmm Allah yasa
Shima da saurin Yace AmEEn
LABEEBAH najinsu ita jin da'dinta 'daya yau XARAH da KAMAL sunkulle bakinsu basuyi kalaman so ba bare susa mata damuwa da tashin hankali

Wajan shaqatawane qayataççe Jameel abokin KAMAL ya paka motarsa
Kallo 'daya XARAH da LABEEBAH sukama wajan gun ya basu sha’awa

Kowa idansa akan motar. sunasan ganin fitowar ango da amarya
LABEEBAH ce tafara fitowa aiko masu photo suka fara 'daukarta tunaninsu amaryarçe

Ganin haka yasata saurin bu'dema XARAH kofah
Yayinda Jameel ya bu'de KAMAL
Aiko suka jera abin sha'awa.

Kamar yanda suka dace da juna. haka xanso ki'daga idanki ki kalleni Wlhi ni dake mun dace da juna. Jameel yace da LABEEBAH hakan Cikin sanyayyiyar.
Tace ko
Yace gaske
Ba mamaki kai kaga hakan. Tafa'da tana mesan wucce shi
Cikin sauri yasha gabanta

Yace haba LABEEBAH bakyau wulaqanta mutum fah
Tace toh na wulaqan taka ne
Yace Kwarai kowa dan kema kinsan hakan. ina sanki LABEEBAH. Wlhi ba KAMAL ba koma waye baxan ta6a bar mishi keba
Tayi murmushin daya qara mata kyau. Tace Ka ha'du. Ka iya wanka. Kana da kyau. Ba macan daxata ganka ta qika. dan kayi tako ta ina
Amma gareni banga hakan ba. Dan matsalar 'daya CE
Kai ba KAMAL bane. Baka da wani abu takaxo dashi irin nasa.
Da ace xaka kasance kome irin qamshinsa ne dako na soka.....
Tana kaiwa nan tashige shi abinta
Shuru Jameel yayi xanci kanta na yawo akunnansa
Duk sai yaji kansa namasa ciwo. Dan haka sai kawai ya koma Cikin motarsa
LABEEBAH ko bayan taxauna duk sai idan maxan gun ya dinga sauka akanta. Taji takasa sukuni. Hakadai ta'daure ha'de dayin fuska tana kallan XARAH da KAMAL tana kissima abubuwa da dama aranta

Ki'de kidene suka ji ha'de da ciye ciye dashan kayan Su drink dasu fruit abindai ya qayatar. Dan kallo 'daya xakama duk wanda yake gun kagane yana Cikin farin ciki
Allah Allah LABEEBAH takeyi atashi dan xuciyarta tafara mata xafi qirjinta ko ciwo ya fara mata dan irin soyayyar da KAMAL yake nunama XARAH awajan
Hankalinta ya farah tashi ba 'dan ka'dan ba
Bama wannan ba. Gani tayi kowacce mace agun jifan KAMAL take da wani fitinannan kallan wanda kallo 'daya xakama kallan nasu kagane na sone
Ni ka'dai nalura da hakan
Xuciyar LABEEBAH tatambayeta
Nan take. Tabata amsar eh kai. Dan kinfi kowa sansa ne
Hawaye ne yanemi xubo mata tayi saurin mayar dashi. Lokacin kuma yaxo dai-dai data ha'da ido da XARAH
Cikin wani yanayi tasakar mata murmushin yaqe
Ba'awani da'deba aka tashi. Kowa Yakama gabansa
Qawayan Su suka dinga yabah taron. Hadai aka watse Al'amarin daya yima LABEEBAH da'di kenan dan tana qara cigaba da ganin KAMAL da XARAH ne. Qirjinta namata xafi.


Tun amota XARAH take tambayar LABEEBAH lafiyanta qalau kowa
Tace lafiya lau kaina ne ya kemin ciwo
Cikin muryar qasa qasa XARAH Tace kodai soyayyar KAMAL ne
Murmushi LABEEBAH tayi Tace ko 'daya
Toh Allah yasa XARAH tace hakan
LABEEBA tace AmEEn
Haka suka dawo gida.

Ga mamakin LABEEBAH ko shine tun awajan sweet faty da qirjinta yafara mata ciwo har yanxu bai dena bah
Tunaninta ko ganin XARAH da KAMAL ne. To yanxu dabata ganin ciwan ya 'dauke man
Kuma Data rintse ido saita dinga ganin hoton XARAH da KAMAL Suna dariya a wajan sweet faty 'dinnan
Saiko hankalinta yaqara tashi

Abu kamar wasa saida taxo kwanciya dan hutawa
Bacci Yace baisan xancan bah. Dan qirjinta ciwo yafara mata yayinda xuciyarta tacika dasan ganin KAMAL
Kuka take sosai tana Allah wadai da xuciyarta data so Wanda yake San XARAN ta
Ban yima kaina adalci bah tunda nasoka KAMAL
Allah katemaken kaciremin soyayyar KAMAL
Haka taketa fa'da a baiyane tana dafe girji
Kallan agogo tayi taga 11:00pm na dare. Tamaida kallanta gun Sumayya da XARAH da suke bacci hankani kwance
Kuka ya da'da kubce mata. Numfashinta yafara fitta sama sama. Nan hanakalinta yanemi fitta daga gareta.
Al'amarin daya tashi XARAH kenan taganta Cikin wannan halin
Cikin tashin hankali Tace lafiya me yake damunki innalillahi meyasa meki
Cikin wani yanayi Tace qirjina XARAH qirjina temakeni Xan mutu
Kwalla qara XARAH tayi tana kiran mamah Cikin tashin hankali
Mamah tafitoh daga 'dakinta da sauri tana tambayar lafiya
Nan tanuna mata LABEEBAH tana cewa kinga mamah xata mutu wayyo Allah mukaita Asibity
Itama mamah Cikin rikicewa Tace me yasa meta haka
Wlhi ban sanibah najidai tace qirjinta na ciwo wai xata mutu
Mamah taje tagayama Malam Sanih shima Cikin wani hali yace muje asibity kunga tasume mah Subhanallahi
Aiko nan XARAH da Sumayya wacce tafarka itama suka 'dagata mamah tatemaka musu suka fitoh waje
Xarah Tace mamah bari atashi ya Usman saiya kaita a ababur 'dinsa mu sai mushiga adaidaita sahu
Malam Sanih Yace Yauwa kinkawo shawara.
nan Usman suka fitoh da XARAH Yana cewa meya sameta. Wai qirji mamah Tace dashi
Nan Cikin sauri mamah da XARAH suka sata kan babur 'dinsa Sumayya taxauna abaya dan riqeta sai Asibity

XARAH ta kulle gidan mamah tafitoh daga gidansu dan tagayama Innah sukayi titi dan binsu


Da sauri nurse suka kar6i LABEEBAH dan bata temakwan gaggawa
Duk iya binciken doctor ya gane damuwa CE da saka abu arai yayima LABEEBAH yawa
Cikin wani yanayi ya kalli Malam Sanih da mamah Yace kutemaki 'yarku kubata abinda takeso inba haka bah xaku rasata dan xuciyarta tafara kumbura
Cikin tashin hankali suka ce xuciyarta ta fara kunbura Yace yes
Cikin mamaki mamah Tace a'iya sanina LABEEBAH bata Cikin damuwa dan ba'abinda tarasa
Doctor Yace akwai. Lurane bakiyi da yanayinta bah
Ki saka ido akanta xakice nace miki
Da mamaki da damuwa suka fitoh daga office 'dinsa
Cikin sauri Usman da XARAH suke tambayarsu me doctor Yace
Nan suka gaya musu
Usman yashiga damuwa. Yayinda XARAH take kissimawa aranta tabbas MASEEFAR SOON KAMAL ne yafara ta6a xuciyarta ba wani abu bah


Washe gari da qarfe goma sha biyu na ranah XARAH ta kira KAMAL tagaya mai Komai
Cikin tashin hankali da damuwa Yace what. Xuciyarta tafara kumbura
Cikin damuwa XARAH Tace eh haka Yace
KAMAL Yace akwai matsala my TEEMAH. Dole asan yanda xa'ayi dan gaskiya xa'a iya rasata Tace yanxu kana inane Yace ina abujah yauxu dan ko minti ishirin banyiba da shigowa gida
Tawaro ido kamar Yana ganinta Tace abuja fah kace
Eh Wlhi. wani kiran gaggawa nasamu gun Dadyna shiyani bin jirgi naxo
Tace aikowa sai aikin jirgi
yanxu dai bara na Barka ka huta mayi magana anjima
Yace toh my TEEMAH luv u Tace me 2.


Kwana biyu LABEEBAH ta'dauka a Asibityn. Ba lefi ta'dan samu sauqi yau tunda har tana iya magana Cikin hankalinta Amma bata cin abinci sai ruwan da ake qara mata
Yan xuma Mamah CE tasata a gaba wai saitaci abinci dan bayan da doctor dasu nurse basuyi da ita bah akan taci taqi ci dan Ita bajin yunwa take bah. aa ganin KAMAL take sanyi.
Ga ninshi shine kwanciyar hankalinta. Tatabbatar mah kanta tana ganinsa ciwanta ya warke

Ta kalli mamah Cikin xubar hawaye Tace Allah mamah banajin yunwa
Tace toh meyasa LABEEBAH Tace hakka dai. Innah Tace ki daure kici kinji
Tace Wlhi banajin yunwa.
Shuru sukayi Suna mata kallan tausayi
Can mamah takalli Innah Tace muje gida mubarta da Sumayya dan bake bani ai baiyiba
Innah taja numfashi Tace hakane XARAH mah ta dawo da matar Suleiman ko ta Bashir
Mamah Tace gaskiya kam dan hakan shiyafi
Suntashi xasu tafi kenan doctor da KAMAL suka shigo
Cikin ladabi KAMAL da doctor suka gaishesu. Suma suka amsa Cikin kulawa
Doctor Yace D KAMAL narasa yanda Xanyi da yarinyar nan.
KAMAL ya kalli LABEEBAH data juya musu qeya Yace metayi Yace taqicin Komai Wlhi.
Da sauri KAMAL ya waro ido Yace what 2 days bataci Komai bah
Yes doctor ya tabbatar masa tare da qarawa da cewa ranar kabata wani da kaxo ne
Yace eh tasha tie Sumayya ha'da mata.
Sumaiya Tace Allah Ya KAMAL ko anha'da mata baci xatayi bah....
Mamah Tace Hakka nayi fama da ita kinga innansu xomu tafi
Innah Tace toh Amma dan Allah kusakata taci wani abu
KAMAL Yace toh innah insha Allah
Suka fitta Sumayya tabisu tana cewa bari in rakaku bakin titi mamah
Tace toh xomuje sukayi gaba
Doctor ya kalli KAMAL Yace ina xuwa Allah yasa kanna dawo kacika mata ciki danni nayi nayi abin yaci tura
KAMAL Yace bakadai San yanda xakayi bane
Yace Allah ko. Toh ai gaka gata Allah yasa tabaka kunya
Dariya sukayi doctor ya fitta

KAMAL yaja kujera ya zauna Yace nasan darajar KAMAL xanci kamar yaumah atemaken kar aban kunya kici abinci dan Allah
Tace banajin yun......
Yayi saurin katseta da cewa kijuyo kikallan inyaso saikimin qaryar
Allah ba qarya....
Bakiji me naceba kenan ya qara katseta

Wayyo Allah masoyayina karka takura xuciyata akan kallanka. Xaka tafi kabarta Cikin tunaninka
Inasan KAMAL dan Allah kasoni ko sau 'dayane. Duk da nasan ko kasoni baxamu ta6a kasan cewa tare bah
LABEEBAH ce me fa'din hakan aranta. Yayinda hawaye ke xuba mata.

Kitemaka dan Allah kici
Goge hawayanta tayi tajuyo karab suka ha'da ido
Al'amarin yafaru biyu wato bugun xuciyarsu.
LABEEBAH tasaba da hakan. Yayinda shi ako da yau she yake tambayar kansa meyasa hakan take faruwa dashi akanta

Toh fa'damin yace da ita
Bana jin yunwa tafa'di hakan cikin sanyayyiyar murya
Shuru yamata yamiqa mata abincin da yasa mata
Batayi musu bah takar6a. shinkafa da miya ce dai.

taxubama abincin ido tana mamakin kanta dan sai yanxu taji wani bala'in yunwa. Wato dai ya tabbata KAMAL ne farin Cikin ruhinta

Shiko Cikin jin da'di Yace Yauwa koke fah.
Yi maxa kici
Tayi shuru ita bataci bah kuma taxuba mishi ido
Ganin haka yasashi tashi yasama

Please Login or Register in order to submit comment