Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata hanya
Yarage sauran tasha ice-cream
kinga sai jibi inkai mata har gida tana sha bame futar da ita sai Allah

Kilishi ta sheqe da dariya Tace kai Amma ke muguwace Turai harna hango idan XARAH a gaban oga.
Sai suka sheqe da dariyar rashin imani
Turai tace angaya miki qawance dani alkairine ai naranshe miki XARAH tashige saita fimu matsayi dan shegiyar kantace

Amma in dama tariqe alqur'ani toh ba shakka tashiga farraqamu xatayi

Kilishi Tace ta babbakamu mushiga uku

Turai Tace damuwata SAUBAN ya shigo hannuna
Kilishi Tace ke kika sani danni wannan ban'dauke shi damuwa ba. Kinga maxa mu kammala wannan abun kafin taxo tasamemu
Haka suka gama tsaface tsafacensu suka maida kayansu mekyau lokacin yayi dai-dai da xuwan XARAH. Ta xube kan kujera
Turai takalleta cikin sha'awa na kwa'dayinsu na'yan lesbian talashe baki da matsowa kusa da ita kamar mesan shige mata ciki Tace banganki da SAUBAN bah
Tace eh yana gun LABEEBAH
Cikin fusata Turai Tace wai itace ta haifar miki shine daxata dinga maqale miki 'da plx lokaci yayi daxaki kar6i 'danki kijanyo shi jikinki
XARAH tagirgixa kai Tace baxan iya kar6e SAUBAN agun LABEEBAH baxan iyaba. Kibarsu kawai kin san ni ba damuwa nayi da yaraba. Dan kona kar6eshi baxai sami kulawa daga gareni bah Gaskiya

Turai tacije baki tare da bu'de mata MALTINA tabata
Ba Bismillahir-rahmanurrahim XARAH tasha jini me ha'de da sirkin MALTINA
Turai ta ha'da ido da Kilishi suka qifta ido kilishi Tace saura ice-cream Turai Tace aiko dai
Tunda XARAH tasha wannan MALTINAN shikenan taji jikinta yayi mata 'dauyi taji wani abuna yawo acikin jikinta saitaji tanasan taqara sha.

Can taji kanta yafara juyawa mata saita kamo hannun Turai tafara lasan hannun nata tana banqarewa fa'di take qaramin

Turai tayi murmushin mugunta tacirema XARAH gyalanta tafara cire mata riga.
Cikin kalar maye XARAH tariqe hannunta Tace cewa nayi ki qaramin me xakiyi da rigata
[4:46PM, 14/10/2016] Rahamat Nalele💋: Turai takai mah bakinta kiss Tace nada'de ina sanki XARAH nada'de ina san kasan cewa dake
Na da'de ina jiran wannan ranar daxamu kasance tare da juna
XARAH sha'awarki tana San illatani
Ina sanki plx kiyarda in xama mijinki. Kixama matata
Harkar tana da da'di. Na rantse miki kika fara baxaki qara sha'awar 'da namiji bah
Tana kaiwa nan takai bakinta kan dukiyar fulaninta tana tsotsa
XARAH ta lumshe ido cikin maye takama kan Turai da 'dago da kanta idannan nata yayi jawur Tace dagaske ke 'yar lesbian CE
Turai ta'daga matakai
XARAH tamiqe tana bangarewa tanayin wani abu wani iri haka kamar xata xube qasa ta'dau gwangwanin MALTINAN nan takai bakinta tana San Sha Amma babu
Tahau xaxxagewa a hannunta tana lashewa
Can tayar da gwangwanin da fashewa da kuka ta'dane kan cinyar Turai da kamo furkarta Tace xan mutu inhar baki qaramin ba
Turai takalli kilishi Tace naso nayi amfani da ita awannan lokacin Amma saidai Sirrin oga ya caf keta da yawa
Kilishi Tace wayaga saban shiga kawai ki maida ita gida kafin tafi haka haukacewa kinsan yanxu ko jini tagani 'dauka xatayi tasha inhar ba baccin nan tayi bah
Turai Tace kuma fah
Nan tagyara mata rigarta tana lasan harshe dan taga dukiyar fulaninta
Suka sakata amotar sukayi kurna

A'kofar gidan sukayi parking Turai tafitoh da XARAH da tarota wacce xuwa lokacin tafara bacci sukayi gidannasu
Innah Tace lafiya naganku haka Turai Tace Wlhi wai cikintane yake mata ciwo shine mukaje Asibity suka dubata da bata allura
Ina ganin itace ta hargitsata haka yanxu dai bacci take buqata tana tashi garau xakiganta

Innah Tace to to to kukwantar da ita agado
Suka kwantar da ita sukayima innah sallama suka tafi


Tun qarfe biyar dasu Turai da suka dawo da XARAH bata barka daga baccin bah sanda takai washe gari da qarfe bakwai
Innah taga maseefa dan tunda take XARAH bata ta6a yin bacci irin wannan bah
Dan tatashe ta sallar magriba da isha'i Sam XARAH taqi motsawa
Haka da Asuba mah. Tashin duniyarnan Sumayya da Innah summa XARAH Amma shuru kakeji
Da badan sunajin numfashinta ba da cewa xasu tamutune

Innah Tace keko wane allura doctor 'din yamiki haka ta bacci
XARAH takalleta cikin rashin fahimta Tace doctor kuma
LABEEBAH Tace shi mana bajiya Turai takawo ki ranga ranga wai cikinki na miki ciwo bah
XARAH tadafe kai tanasan tuno me yafaru da ita
Aiko nan tatuno komai Amma abun yana mata wasi wasi anya hakane ko ba haka bane
Tadai kalli inna Tace nima basan wacce allura bace Amma dama Yace xanyi bacci Sosai
Innah tajah numfashi Tace toh saiki tashi kije kibiya sallar magriba da isha'i da kuma Asubah
Tawaro ido Tace banyi bah
Innah Tace eh kai



Qasar Armiyaniya
MALUDDEEN ne gaban Sarki Suna xantawa duk akan harkar kasuwanci
Sarki ya kalleshi Yace ya kamata kayi Aure
Gaban MALUDDEEN yafa'di Yace toh BABAH Xanyi
Yace kaxa6i 'daya acikin qannan naka KHADIJA da Halima
MALUDDEEN ya sunkuyar dakai Yace toh aban lokaci
Sarki yayi Murmushi Yace ambaka

Yayi shashin nasa kenan Khadija taxo gareshi
Yace yadai Tace naxo in gankane
Yace kiyimin me
Tayi shuru
Shima shurun yayi yana bin hotan LABEEBAH da kallo
Tace Ya MALUDDEEN wacece wannan
Yayi Murmushi Yace itace farin cikina
Da sauri ta kaqara tsaida idanta akanshi ta marairaice Tace tayimin inasanta dama taxama Aunty na
Yayi Murmushi kuma atake yaji santa ya kamashi Amma ba irin na Masoya ba Yace xata xama auntynki insha Allah
xatayi magana
Yace jeki xan nemiki anjima
Tafita tana waiwayansa
Anan taci garo da Halima xata shigo itama
Sukayi kallan kallo Khadija tawucce Halima tashigo

MALUDDEEN ya kalleta ka'dan Tace ina wini Yayana Yace lafiya
Sai kuma tayi shuru
MALUDDEEN Yace yadai Tace Wlhi yayana bansan yaushene bah nakamu da MASEEFAR SONKA dan Allah ka soni Wlhi nime qaunarkace
dan Allah karkayi sanadin da xan afka tarkwan ~MASEEFAR SOO~
Taqarashe da xubu da hawaye
MALUDDEEN ya rumtse ido
Dan shi yasan menene ~*MASEEFAR SOO*~
Ya bu'de idanshi ya nuna mata hotan LABEEBAH Yace Wlhi duk duniya bani da mata sai ita
Ina Santa Halima ina qaunarta
Baxan iya xaman Aure da wata mace inba itaba
Idan kuma wata tayi gangancin aurena na rantse miki baxataji da'di naba
Laveevah itace farin cikina
Itace nutsuwata
Itace haskena
Itace hankalina
Duk abinda na mallaka ajikina natane
Banajin xan ha'data taraiya da wata 'ya mace aduniyar nan alqawarine na 'daukarma xuciyata
Dan haka plx jeki
Cikin kuka wiwi Halima tafita daga falan

MALUDDEEN ya rintse ido axahiri yaji tausayinta dan *ciwan soo maseefane*
Wayarshi tayi qara. Ya 'Dauka dan ganin mutanan nasa ne
Yace yadai
Can 6angaran Yace oga XARAH tana shan ice-cream 'dinnan fah😳 shikenan tashiga kwingiyarsu

MALUDDEEN yayi Murmushi Yace idan na temaketa banyima kaina adalci bah
Dan haka kubarta kawai

Ina dai jiran ganin komai
Yace angama ranka ya da'de
MALUDDEEN ya ajiye waya Yace am sorry TEEMAH.....


Gida🏘
Misalin qarfe 4:00pm Hajjiya Turai tana tsakar gidan Su XARAH Suna hira
XARAH tajuya ganin Innah tashiga bayi
Tace da Turai niko maiya faru danine shekaran jiya nakira numbarki jiya bata tafiya
Turai tayi dariya Tace aranta idan kinada qarfin kwakwalwa xaki iya tunawa Amma abun xai dinga miki wasi wasi
Idan kuma bakida qarfin kwakwalwar ba'abinda xaki tuna

Afali ko cewa tayi namanta wani abune
XARAH Tace eh toh Komai dai yanamin wasi wasi haka
Turai tasheqe da dariya Tace kishare kawai bakomai

Kinga ice-cream na kawo miki kisha. Nasha nawa a hanya

XARAH takar6a tasa gefah Tace aiko yanxu innayi Sallah xansha

Turai tatashi Tace nina tafi amma naso ganin SAUBAN saidai Allah bai yiba XARAH tata6e baki tace yanagun uwarsa
Haka Turai tatafi tana cewa in Innah tafitoh kice natafi
Tace toh

XARAH ta kinkimi ice-cream 'din Tace bara nakaima LABEEBAH tasha saita ragemin

Haka tashiga gidansu LABEEBAH tamiqa mata ice-cream 'din Tace kisha kiragemin nawa
LABEEBAH takar6a tabu'de cikin murna tana ha'diye yawu dandai tana San ice-cream arayuwarta
Dai-dai nan XARAH tashige bayi
LABEEBAH tagyara xama xatasha sai kuma ta ajiye gefe tatashi tashiga 'dakinta daniyar 'dauko SAUBAN dan susha tare


Armiyaniya
Dai dai video na MALUDDEEN ya tsaya aiko ya saki wani ihu tare da tashi afurgice
Yace no no no baby karkisha plx kitemaken plx no.......
my baby karkisha
Agigice yafara kiran numbanta wacce dama mutanan nasa sunda'de da bashi kirantane dai bai ta6ayi bah
Nanko tafara ruri

Saidai bata 'dauka bah. MALUDDEEN kamar xaiyi hauka haka yadinga kiran wayan LABEEBAH bata 'dauka bah
Yakira mutanan nasa suma shuru numbar tasu taqi shiga
Saiya xauna ya dafe kansa ya fa'da tunanin yanxu babyn tashi tasha ya xaiyi

Gida🏘
LABEEBAH ko 'dauko SAUBAN tayi suka fito daniyar shan ice-cream. Amma me😳
Sai neman ice-cream 'din sukayi sama ko qasa. LABEEBAH tafara lemanshi harda 'daga turmi
XARAH tafitoh daga bayi takalleta Tace me kike nema Tace ice-cream 'din da kikaban
Kinga daga shiga 'daki nafitoh Kinga babushi sama ko qasa
Rukayya tafito daga 'dakinta Tace nidai ina Sallah naji 'dan motsi qila almarine yaxo bara ganinshi yasa ya 'dauke yayi gaba abinsa. Ta qarashe maganar da dariya
XARAH Tace ba mamaki kam. Sai tafara alwalarta.
LABEEBAH tajah tsaki Tace naso Sha Wlhi Amma ba damuwa.
Rukayya ta kalli LABEEBAH Tace Naji wayanki na ringing
LABEEBAH tajah tsaki Tace share kawai

A Armiyaniya ko MALUDDEEN ya shafe awa axaune yana tunani
Can yaji wayansa tafara ringing aiko ya 'dauka da sauri Ganin mutanan nasa ne. Kuma dama a ankare yake
NIGO sunan ogan nasu yayi qasa da murya Yace afuwa ranka ya da'de
Cikin buqata MALUDDEEN Yace tasha ko
Yace haba oga ai shiganta 'daki nasa Yarona yaje ya 'dauke gaskiya an auna sa'a dan Kasan ba xama muke bah. Allah yayi dai ranar Yarona yaje gyara camera ne dan matar Yayan nata Rukayya takauce mana shi
Yace gud inaso yanxu kudinga Kasan cewa da ita ina buqatarta cikin nutsuwarta
Yace angama oga
Suka ajiye waye xuciyar MALUDDEEN tayi haske
Yace dole na gaggauta xuwa gareki my baby.......
Marwan ne ya shigo Yace yadai 'dan uwana
Yace kaidai bari na kusan rasa nutsuwata 'daxu😔
Yace meya faru
Yace dole inje Nigeria kwanan nan
Yayi Murmushi Yace toh maje tare Amma kafin nan dama naxo in gayama ne nashirya mana komawa Dubai gobe
Yace OK Allah ya kaimu. Yace AmEEn


Gida🏘

Bayan kwana biyu Hajjiya Turai CE da qawarta kilishi xaune Suna tattauna yanda xasu 6alloma XARAH
Lamarin daya basu mamaki. Dan ogansu ya tabbatar musu XARAH batasha ice-cream 'dinnan ba
Kilishi takalli Turai rai 6ace Tace lamarinki yafara ban haushi
Tayaya xa'ayi XARAH da 'danta Su gagareki......
Turai ma cikin fusata takatseta da cewa nagaya miki yaran nan ba qaramin tsoro yake dashi bah
LABEEBAH toh feshi take da addu'a safe da yamma
Sannan awaje matakan tsoro suna aikinsu
Kilishi tajah tsaki Tace toh ita XARAH fah
Tace nayanke shawarar yau xan fitoh mata a asalina. Kedai kisaurari xuwan dare kawai
Kilishi tata6e baki Tace qaramin aiki yana neman caja miki kwakwalwa. Taqarashe dajan tsaki


Xaune XARAH da LABEEBAH suke Suna hira LABEEBAH Tace ina Ganin ya kamata mukoma islamiya da xaman ban xan nan da muke
XARAH Tace kuma fah dan yafi xaman kam....
SAUBAN ne ya shigo hannunshi yanke sai kuka yake ya tsanshi na fidda jinii
LABEEBAH ta kama shi tana cewa ya akayi kayanke
Kan yayi magana Sumayya tashigo tana cewa ai maganinka kenan bakai ta6e ta6e bah. Daga ajiye reza sai ya 'dauka wai xai yanke farce sai ya yanke hannun

Xurama hannun SAUBAN ido XARAH tayi sai taji tanasan shan jinin😳
Saita fara ha'diye yawu tana matsowa jinkin LABEEBAH
Aiko saita kawo SAUBAN tasaka 'dan ya tsan daya yanke abakinta tafara tsotsa jinin kamar tasamo sweet.......
Duk binta da kallo sukayi suna mamakin wannan abu
SAUBAN daya dena kukan nasa saiya xuba mata ido kawai
XARAH ko da gaske tsakaninta da Allah xuqar jinin take tana lumshe ido
Can Sumayya ta janye SAUBAN tana cewa Aunty XARAH miye haka
Dafe kanta tayi da saurin ankarewa Tace ai yaro nane. Danya yanke ai baxan bar jininsa yatafi a iskaba......
Kan Sumayya tayi magana Rukayya da take saqa Tace haka naga wasu sukeyi Amma ni baxan iya ba
LABEEBAH ta sauke ajiyar xuciya Tace Wlhi koni baxan iyaba sai kace wata mayya
Tashi XARAH tayi tafitta hankalinta tashe dan ganin har xuwa lokacin jinin SAUBAN bai dena fitowa bah. Gashi taji aduniya ba abinda takesan Sha sai jini 🤔
Taje takwanta tayi lamo tana tunanin ya xatayi tajanyo SAUBAN taqara shan jinin

Bari tayi kusan awa 'daya sai takoma gidansu LABEEBAH
Bata ganshi a tsakar gida bah Tace SAUBAN yayi baccine
Sumayya Tace eh Yana 'daki
Xama tayi na tsawan minti biyu.
Xuwa can tayi wuf tashige 'dakin.
Saidai LABEEBAH tasa mishi kalanxir jinin ya tsaya Amma akwai sauran ka'dan daya bushe
Tayi saurin cafkar hannun xatakai bakinta SAUBAN ya tsandara ihu aiko da sauri tasaki hannun LABEEBAH Tace yadai
Cikin Takaici XARAH tafitoh Tace xan kwanta ban sani bah na'dan take hannun ciwan
LABEEBAH ta harareta tayi 'dakin dan lallashinsa

XARAH ko data koma 'dakin innah kuka tasake tana ji inhar batasha jini bah mutuwa xatayi. Wai me yake shirin faruwa da ita
Innah tafitoh daga kitchen Tace lafiya dai
Tace ba Komai
Innah ta kalleta sheqeqe Tace ban gane ba Komai ba kike kuka
Tace bafah Komai
Innah tafita Tace iyya dameki kya fa'damin
Shuru XARAH tayi tare da lumshe ido tana ganin hotan hannun SAUBAN tanajin takaici


Cikin daran ranar misalin qarfe 1:00am XARAH tana bacci saiji tayi ana tashinta
Tatashi tana mustsike ido da sauke ganinta akan Hajjiya Turai
Tuni tawaro ido tana qaremata mata kallo
Baqar rigace ajinkinta bakinta ja6ale jabale da jini. Kanta 'daure da Jan 'yalle ga wani ruwa ahannunta
Cikin bala'in tsoro XARAH Tace Turai.....
Aiko Turai tawatse mata wan nan ruwan afuskarta tayi saurin rufe fuskarta
Turai tayi murmushin mugunta
XARAH tabu'de idan nata. Basai taganta a wani falo babba bah
Ga mutane kusan ashirin dukkansu da shiga irinta Turai Maza da mata
Iya furgicewa XARAH ta furgice
Turai Tace bari namiki gwari gwari XARAH yanda xaki gane
Dukkanmu nan 'yan shan jinine kuma matsafah
XARAH tagwalalo ido Tace wayyo Allah nah meyasa xakiyimin haka Turai..........
Wata tsawa XARAH taji andaka mata cikin muryar raxana taji ana cewa karki qara kiramana Allah anan
Sai taga Turai ta dur'kusa qasa tayi wani doro tace ina Neman mata afuwa shugaba.
Sai taji ansheqe da wata mahaukaciyar dariya wacce taji tana mata kurwa akunne uku uku
Ai XARAH batasan lokacin data sake xawo bah 😳
Iya tashin hankali XARAH tashiga
Kanta ankare saiganin Alhaji Nura tayi wani shahararran me ku'di alayinsu ya dire mata kwaryar jini agaba
Aiko XARAH taga abinda tunda yamma take kwa'dayin sha
Nan takafah kai tashanye jininnan tsaf
aiko saita fara banqarewa tana wani irin ihu tanajin wani qarfi yana shigarta
Taxaro ido tare da fashewa da kuka takama hannun Alhaji Nura Tace babah qaramin
Shuru yayi mata tare da komawa wajan da yake ya daskare kamar yanda sauran suke
Turai ma ganinta tayi a daskaran
Saita juya bayanta anan taga wani qatan mutum kan kujera da qatuwar kwarya agabansa yace xonan
Ba musu XARAH taje gareshi. Saiya watsa mata wani abu
Saboda tsabar xafin da jikin XARAH yayi bata san lokacin data
kurma wani uban ihu baTace wayyo Allah na A'uxubillahi na mutu

Iya 6acin rai ogansu ya shiga danme xata kira sunan Allah harda cewa A'uxubillahi
Ogan nasu yatashi ranshi 6ace Yace Turai
Da sauri Turai ta amsa Yace maxa fitarmin da ita daga nan kinsan da sauran tsari ajikinta kika kawomin ita
Tace eh nadai barta tana Sallah
Yace saina 'dau mummunan mataki akanki kinyi kuskure na 'daya narashin kawomin yaranta na barki wannanko saikin kar6i hukunci
Maxa futarmin da ita
Tamkar qif tawa da bismillah haka XARAH taganta a kan gadansu ita da Sumayya
Turai tanunata da 'dan ya tsa
Tace sai kinyi babbar nadama atayuwarki tunda kika jaxamin matsala
Tana fa'din haka ta6ace.

XARAH ta'dora hannu aka ta kurma wani uban ihu
Nan Sumayya tatashi afurgice Tace innalillahi menene Aunty XARAH
Shuru XARAH tayi mata
Sumayya takai hannunta jikinta nan XARAH ta jirkice alamar tasume


Sai Sumayya tabita da kallo tana tunanin qila ba itace tayi wannan ihunba
Kuma dama qila bacci tayi a haka
Saita gyara mata kwanciya xata kwanta kenan Innah tafara kwankwa kofar tana cewa lafiya
Sumayya Tace eh ba anan ihun yake bah
Innah da babah sukace toh suka bar kofar


.
[11:36PM, 17/10/2016] Rahamat Nalele💋: Da Asuba Sumayya tatashi XARAH Amma taji shuru
Data tsaida tunaninta akanta saita gane bata motsi numfashi baya fitta daga gareta
Nan taje ta gayama Innah da babah. Cikin tashin hankali sukayi kanta nan suka tabbatar da furucin Sumayya. Amma jikinta bai sake irin na mamaci bah

Ba shiri suka kira Usman suka gayamai Yace toh akaita asubity. Nan sukayi asibitin Sumayya kuka LABEEBAH kuka


Bincike ya nuna XARAH dai suma tayi yanda aka bata temako yasa doctor Yace xata farfa'do akowane lokaci

Lokacin da XARAH ta farka ba kowa a'dakin
Saiko Hajjiya Turai tabayyana agareta tawajan 6ullo mata ta bango
XARAH tawaro ido xata kwalla qara Tace dakata karki soma

Aikin gamu da maseefa har qarshen rayuwarki
Tunda kika jaxamin matsala da oganmu Wlhi ba abinda xai hana in 6ata miki nutsuwarki.
Kuma ako ina kikaga jini sai kin sha hankalinki xai kwanta wannan alqawarine

Tana fa'din haka sai XARAH taga ta xama qatan xaki
Aiko XARAH ta kwalla qara

Cikin sauri LABEEBAH Innah ya Usman Rukayya Sumayya sukayi 'dakin.
Suna Tambayar lafiya
XARAH tadinga nuna musu Turai da taxama xaki. Innnnna Su basuga Komai ba
XARAH tafashe da kuka ta qamqame ya Usman tana wani rin kuka. Tana nunamai ita Yace A'uxubillahi ai nantake XARAH tadena ganin Turai Tace na shiga uku ni XARAH na jawoma kaina ruwan dafah Kaina. NAYI NADAMA niyi da nasanin yarda da Turai......
Ta tucuceni taha'inceni ga shi tajefani cikin maseefa na mutu.......

Tambayar duniyar nan LABEEBAH Innah Usman Sumayya Rukayya summa XARAH Amma taqi gaya musu me yasata furucin nan

A washe garin ranar aka sallamesu


Al'amarin XARAH fah ya rikice dan tahana kowa xama cikin kwanciyar hankali ba ga ranah baga dare ba

Dan cikin dare alqawarine sai Turai ta bayyana agareta ta tsoratar da ita tawajan canjah kalarta

Da rana ko in tabayyana agareta saita sake mata tsaka🐊 ko 6era🐀 danginsu dai qananan halittunnan haka XARAH xatata furgita ta dinga ihu Sam mantawa take da addu'a.
Kowa tausayin XARAH yake dan tabbas taxama abin tausayi yanxu
Ta fige ta lalace tamkar ba XARAH bah. Kallo 'daya xaka mata kaji tausayinta

Ita kuka LABEEBAH kuka
Kowa yanxu ya xuba mata ido. Watoh na mujiya dan har yanxu taqi fa'da musu Komai


( toke Aunty Rahamat Ki fa'da musu damuwar ta mana😔. Cewar MUFULEEDA qanwar ga HAYATUDDEEN. NASRIN Tace indai KAMAL baifa'dafa musu bah bana tunanin XARAH xata fa'da musu. Ni Rahamat nayi Murmushi Nace mexai hana inyi garin Dubai Gaskiya Naji tausayin XARAH. Hamida qanwar HAYATUDDEEN Tace ko tausayi bata ban bah. saura Ki ha'da da KAMAL. Nace ai mijintane duk suka waro ido. HAYATUDDEEN Yace plx Auntyna kiyi saurin gama wasan salan soyyayar MASEEFAR SOO. Ki bama 'yan DUNIYAR MARUBUTA labarina......
Wasa ne😂😂😂😂)



Yanxu haka XARAH tana xaune Gidansu LABEEBAH tana kukan nata daya xame mata jiki yanxu
LABEEBAH xaune akusa da ita tana tayata abin tausayi
Turai ta hargitsa tunanin ta
LABEEBAH Tace kima Allah XARAH Ki fa'damin me yake damunki Kinga yanxu anyanke shawarar kaiki gun Malam Harisu. Kinsan bulala xakisha inhar ba aljanun bane suke ta6aki kigayamin me yake damunki
Taqarashe da xubo da hawaye
XARAH Tace nidai baxan iya cewa Komai bah Amma nafi buqatar akaini gunsan.....
Usman ne ya shigo
Ya harari XARAH yace waike wane irin taurin Kaine dake hakah
Kifa'di damuwarki amiki maganinta kinqi kinbar Mutane cikin damuwa da tashin hankali
XARAH tayimai shuru
Yajah tsaki da shigewa 'daki

LABEEBAH ta rungumeta Tace Allah ya fidda ke daga kowane kunci XARAH




Dubai🌃
MALUDDEEN ture laptop 'dinsa yayi da Murmushi akan fuskarsa ya kalli NIGO ogan mutanan nasa Yace aikinka nayin kyau
Yace oga XARAH na cikin wani hali fah
Kujerar da MALUDDEEN ke kai tafara juyawa Yace Sosai kam
Amma ni ba wannan bane damuwata. Kasan damuwata
NIGO ya girgixa kai Yace saika fa'da oga
MALUDDEEN ya tashi ahankali yaje jikin wani hotan LABEEBAH ya shafa fuskarta Yace abinda ya damen shine yanda tahar gitsamin Babyna
Ta hanata xama lafiya
Kullun a tayata kuka take gashi duk duniya ba kukan macan dayake tafarfasa xuciyata kamar na laveevah
NIGO Yace toh oga ya xa'ayi yanxu
Yace abinda xa'ayi shine Ku rubuta abinda yajefa XARAH cikin wannan halin tsaf ku bama Usman
Nasan xai karanta daga nan saisu lema nama magani da addu'o'i koya kagani.
NIGO ya 'dan duqa Yace hakan yayi
MALUDDEEN Yace muma a cikin satinnan xamuyi Nigeria
NIGO Yayi dariya Yace xakaga madam kenan Yace eh Amma ina tsoran ta sume min. Yafa'da da Murmushi akan fuskarsa
NIGO ya 'daga mishi hannu ya fitta.
MALUDDEEN Yace gani gareki my baby YUSUF ya tafi baxai dawoba KAMAL ya tafi KAMAL ya dawo




Gida🏘 Nigeria
Komai ya ca6e dan Usman yaxo da labarin abinda yadami XARAH.........

Basu Innah bah hatta XARAH tayi mamakin yanda akayi Usman ya San Turai 'yar shan jinice da kuma yanda akayi yasan hartanemi jefata cikin kwingiyar tasu
Iya tashin hankali kowa ya shiga
Suka tasa XARAH agaba Suna tambayarta da gaske yanxu intaga jini xatasha
Da sauri XARAH ta'daga kai da cewa eh
Kowa salati ya 'dauka BABAH Yace toh akaita gun Malam Harisu ya rabata da wannan maseefa


Haka ko akayi nan akayi gun Malam Harisu da XARAH
Ya qare mata kallo Yace ba shakka abin haka yake

Dama ance duk cutar da take damun mutum idan ya rasa maganinta a Qur'ani toko ba shakka baxai samu yanda yake so bah
Dan ba abinda Qur'ani ya bari
Yaxo mana da komai bai ragemu da Komai bah
Ni da ke da kai muje mu riqe Qur'ani hanyar gaskiya. Muso Allah da manxansa mu rabauta.
Muso sahabbansa muyi koyi dasu mu dace

Toh Madallah tunda Malam ya fara karantu mah XARAH suratun baqara inda ya shafi kowane cuta tafara wani amai Baqi tanayi tamkar xata mutu.
Ahaka ta sume ya ya yayyafa mata ruwa tare da tofeta da addu'o'i nan tasamu bacci
Ya kalli babah Yace tada'de tana cin abubuwan tsafin nasu. Bata sani bah shiyasa da tasha jinin farko lamarin nasu yayi saurin cafkarta
Amma yanxu Tatashi insha Allah Komai ya wucce

Aiko haka akayi XARAH tashafe awa uku tana bacci can ta farka
Madallah Tatashi garau 'dinta malam ya 'dan yanki hannunsa da rexa Yace XARAH ga jini
Saitayi saurin girgixa kai Tace mexanyi dashi.
Yiya Murmushi Yace bakyajin kina sha'awar ki sha
Tace aa Wlhi







Komai ya dawoma XARAH daidai tadena Ganin Hajjiya Turai
Kowa yayi farin cikin da hakan
Toh sai dai me 😳



Yau LABEEBAH sun fitoh ita SAUBAN dinta dan xuwa supermarket jifatu ba wani abu bane ya kaisu sai siyan Su chocolate danginsu xaqi dan SAUBAN yasata agaba yanaso
Sanda suka shiga taji tanasan siyansu kayan make-up
Dan haka ta shagala da kallan wani turare SAUBAN yayi wani shashi yana kalle kalle.
MALUDDEEN tayake ganinsu yabi SAUBAN Yace wow my boy me sunanka SAUBAN ya kallesa Sosai da waro ido Yace lah😳 Dadyn Momyna
MALUDDEEN ya 'danyi jim ka'dan can Yaje ya rage tsawanshi yanda xasuyi daidai da dafashi Yace ka sanni ne
Yace eh Kullun in nakar6e wayan Momyna xanyi game saina ganka ajiki wayan
Kuma tacemin kai Dady nane kuma Dadyn ta
MALUDDEEN yayi Murmushi Yace hakane ni Dadyn kane kana sonah
Yace eh Amma me yasa baka xuwa guna
Ya kai mishi kiss a goshi Yace nadawo gareku my boy yanxu Xan dinga xuwa kaji
Yace toh
MALUDDEEN ya miqa mishi wata Leda Yace kaba momyn ka ko
SAUBAN Yace toh harya fara tafiya saiya dawo Yace Dady Momyna guda biyu ne
Akwai momyna akwai kuma Momy wacce xan bama.
MALUDDEEN yayi Murmushi da shafa fuskarsa Yace kabama wacce kafi SOO
Da murmushi yace toh xan bama momyna
MALUDDEEN Yace gud.
Nan SAUBAN yayi inda ya fitoh
MALUDDEEN yayi Murmushi Yace i luv u my boy

LABEEBAH tagigice da neman inda SAUBAN yayi
Tayo wata kwana kenan taga ganshi yana tawowa
Ta tsaya tana cika tana batsewa ganin hakan yasa SAUBAN yin wani shashi wai anufinshi

Please Login or Register in order to submit comment