Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kigayamai daga yau karya qara kashe kudinsa haka kuma Ku ajiye kudin idan yasake dawowa abashi abinsa
Yafa'da Yana mai kallan XARAH
Tace toh Babah
Innah Tace toh madallah tunda kasanshi mah da Sauqi.

Mamah ce tayi sallama da Kaya niqi niqi Tace Kaya wani yaro yashigo dashi wai inji KAMAL a ajiyema Aisha-Labibah
Tafa'da tana mai bu'dewa

Komaidai iri 'dayane dana Fatima-zarah har ku'din KAMAL bai bambanta bah

Inna Tace kinga mah na XARAH nan yanxu muke tattaunawa Malam Yace ya shedashi danya gabatar da kansa agunshi
Malam Sallau Yace hakane Karku damu
Mamah Tace Amma amaida mai da ku'dinsa Ko
Malam Sallau Yace abinda Nace yanxu kenan koya kuka gani
Mamah Tace hakan shiyafi.
Nan tabashi ku'din ya ha'da dana Fatima-zarah Yace xai tsamayi xuwanshi gobe


Koda Malam Sanih yadawo mahaifin Aisha-Labibah mamah takoramai Bayani. Kayan da KAMAL yakawo musu baqaramin mamaki yayiba
Yadinga sanya mishi albarka Yace gaskiyane gwara amaidamai da ku'dinsa.

A ranar baccin farin ciki LABEEBAH tayi.
Dan tariga tasa aranta ganin KAMAL kojin muryarsa kojin qamshinsa shine farin cikine agareta.
XARAH Tace sai murna kike lafita Tace lau lau Tace toh Allah yasa



Washe gari da KAMAL yadawo. malam Sallau da malam Sanih sunci sa'a suna gida. Dan Yana xuwa suna fitowa dan xuwa Kasuwa
Dan haka Malam Sallau yakoma gida ya 'dauko kudin KAMAL ya danqama mai
Amma Sam KAMAL yaqi kar6a Yace Wlhi Babah munfara kenan
Haka nake da bayarwa bana gajiya
Bare kuma Ku baxan iya in bakuba koda kowa ranku xai 6aci. Haka xaku kaqura dan bana dawowa na kar6i abinda nariga na bayar.

Bayanda Malam Sallau da Malam Sanih basuyiba akan KAMAL ya kar6a Amma yaqi saima nuna musu da yakeyi mah yanxu yafara bayarwa
Haka suka hakura suna samai albarka suka tafi

KAMAL ya kalli XARAH Yace my TEEMAH kinfi jiya kyau
Takalli shigarta
Duguwar rigar atamface sai hijab 'dinta da 'dan takalminta mekyau
Tace ina kyan yake my luv kawai kaso xolayane
Yace da gaske nake
Tace toh naji yanxu dai bani labari
Yace namefah.

Kata6ayin budurwa.
Tafa'da tana me kafeshi da ido Yace eh aa
Tace ban ganeba
Yace inada masu sona Amma ba wacce tadace da xa6ina kamarki da fatan xaki riqeni amana.......

Hmmm
Allah sarki LABEEBAH tana jinsu dake akan dakalin kofar gidansu suke hirar wanda dakalin yayi 'dan kwana yanda mutun na fitowa xaici arba dasu
Dan haka taxauna a jikin katangar da suke dama da bishiya agun kuma lokaci lokaci tana xama agun dan shan iska
Toh yaudai abin ba haka yakeba. Dan tanajin muryar KAMAL har Cikin xuciyarta
Hankankk na mata da'di. Sai Murmushi take ita ka'dan tana addu'ar Allah yasa karya tafi da wuri dan bata qoshi dajin muryarsa ba me da'din dauraro da kashe jiki

Tajah numfashi taleqa tajikin wani huji daya 6ule Wanda yabata damar ganin KAMAL 'din nata hankali kwance
Tako quramai ido ko qiftawa batayi dan idan tana kallansa manta kanta take


Tayi nisa acikin kallan nasane. Sai taji ranta na 6aci kuma😳
Xuciyarta na soya. Hankalinta yafara tashi
Can kuma taji zuciyarta namata zafi. Saka makwan jin wasu kalmomi da masoyan suke gayama juna

Inda KAMAL Yace banta6a soyayyaba. Amma tunda Allah ya ha'dani dake namiki kallo 'daya qaunarki da soyayyarki suka caki xuciyata. Ina sanki
XARAH tayi dariya Cikin jin da'di Tace dama haka so yake.
Yakan shiga xuciyar mutum batare daya shiryaba

Nima na soka sosai
Yace ban gani bah

Akwai wani abu da kakesan namaka dan katabbatar da hakan
Yace eh kai. Sunanan da yawama
Tace toh fa'desu dan har naqagu najisu
Yace baxan fa'da miki ba. Danke yadace ki ganosu da kanki

Tace toh
Karka damu badai muna tarebah
Yace yah mutu ka raba takalmin kaxa inji....
Da dariya XARAH Tace inji yara
Yace gud
Inasan akoda yaushe idinga ganin dariyarki.
Tasun kwiyar da kanta qasa Tace gashi ban cika yintaba.

Nina yima mamakin yanda nake maka dan gaskiya bancika dariya bah
Yace sone ya kusan toni shiyasa komaima xakimin batare da saninki ba......


Juyowa LABEEBAH tayi da kallanta tsakar gidansu hawaye naxuba daga fuskarta.
Meyasa yau taji tsanar XARAH. meyasa yau takejin xuciyarta na mata xafi

Waime yake shirin faruwa da kene LABEEBAH
Akan wane dalili xakiji tsanar XARAH
Shin kin manta itace qawarki 'yar uwarki
Me baki shawara kema kibata
Shin kinmanta keda ita kunxama tamkar ciki 'daya kuka fitoh

Xuciyar LABEEBAH CE take mata wannan tambayoyin

Tashi tayi anutse tayi 'daki tasaka sakata tarisgi kuka San ranta kana tayi bacci tana rokwan Allah ya rabata da MASIFAR SOO

Sai kusan biyar 5:00pm tatashi
Tabu'de 'dakin tare dayin kicin ( kitchen) inda mamah take girkin dare

Tace mamah kawo intemaka miki
Tace aa kibarshi keda bakijin da'di
Tace naware fah

Juyowa mamah tayi da kyau taxuma mata ido dan taji muryarta tacanja tamata alamun tawanda yayi kuka Tace LABEEBAH meyasaki kuka.
Tayi saurin qaqalo yaqe Tace ba Komai fah me kika gani
inbaki fa'da yanxuba kya fa'da gaba
Mamah tayi furucin da 6acin rai

Cikin 'dan Murmushi Tace hmmm ciwan idonane yatashi fah.
Kawai banasan in ba'da mikine

Da sauri mamah tamaida kallanta kanta Cikin tausayawa Tace Ayya shine
Tace eh shine
Tace toh aini lamarin ciwan idan nakine yaqijin magani yaxamuyine

Tace hmn addu'a mamah karma kisamomin wani magani kibarshi kawai zaidena
Mamah Tace toh bari muganidai
Kedai kina shan jarabtar ciwuka. Ga ciwan Mara ga ciwan ido.
Fitowa tayi daga kicin (kitchen) 'din ta'dauko taburma taje gindin bishiyar gidan nasu tashinfi'da taxauna tana cewa mamah XARAH bata shigoba lokacin da nake bacci
Mamah Tace af namanta taxo. Ciduba 'dakina ta ajiye miki wasu Kaya da KAMAL yabata da naki harda ku'dima inkin ganshi kyayimai godiya

LABEEBAH tamiqe tayi 'dakin da gudu

Aiko waro ido tayi tana kallan kayan
Atamface guda biyar les biyu
Sai takalmi da gyale
Gyefe kuma turarukane da kayan kwalliya (make-up)

Nan tashiga shinshina turarukan tana addu'ar Allah yasa da irin turaransa aciki
Sai dai kash........
Duk iya shinshinanta bata shin shino irin qamshin KAMAL bah

MASIFA
Nan kuma hankalinta yatashi taji aduniya qamshin turaran KAMAL takesanji.
Cikin sauri tafitoh tsakar gida tana waigen inda tasaka hiyabinta. Aiko tahango shi kan igiya nan tasaka tayi waje

Kan dakalin da XARAH da KAMAL suka xauna nan taje taxauna dai-dai inda KAMAL yaxauna..........
Tasauke wata sanyayyiyar ajiyar xuciya saka makwan qamshin turaran nasa dataji

Tayi shuru tana jan numfashi akai akai dan ganinta qamshin yanasan barin gun gashi tanajin da'din hakan. bataso taga yatafi qamshin

Akallah Aisha-Labibah ta'dauki awa 'daya gun tana shaqar qamshin KAMAL agun
Tana kuma mamakin wannan wane shegen turarene daya kasa barin 'dan gurin nasu. Komadai wane irine itadai batajin xata tashi agun
wani abin da'di. Bawanda yayo tagun bare yaganta xaune ya tambayi me take agun

Tana Cikin wannan halinne saiga XARAH tafito daga gidansu daniyar shiga gidansu LABEEBAN

Mexata gani
LABEEBAH xaune kan dakali tana shinshinar bango
Taqaraso tana cewa wani saban salan iskanci ne kuma yau agunki da shinshinar bango
Bama wannan ba. Asanyinnan kike xaune anan

Cikin fa'duwar gaba Tace yanxu fah nafito kuma naji qamshin qasane jikin bangwan shiyasani shinshinawa
Tace aikowa Amma meyasami idanki Allah dai yasa ba
Ciwan idankin bane yadawo

Meqewa LABEEBAH tayi da alamun tafara gajiya da tambayoyin XARAH. Kuma yakaicinta 'daya xata rabata da qamshin KAMAL da take shaqa.
Tace shine

Cikin tausayawa Tace Ayya sorry sannu kinji Allah yasa ya tafi da wuri
Tace AmEEn
Naga kayafah muje muqara gani
XARAH tayi dariya Tace hmm gaskiya KAMAL yayi
Dan qarshene shi
Ina sanshi LABEEBAH kitayani da addu'a kar Allah ya jarabceni da son da nake masa yafiwanda yakemin

Cikin Murmushi Tace toh

Nan suka shiga gidan sunamasu qara ganin kayan suna yabawa mamah na tayasu
har axuciyar Aisha-Labibah taji da'din kayan tayi murna sosai Cikin ranta tana ganin kayan tamkar KAMAL nagun











Tafiya tayi tafiya hardai mamah da Usman da XARAH da Innah suka saka LABEEBAH wai sai tagaya musu meyake damunta. Dan kallo 'daya xaka mata Kasan tafuta daga hankalinta kuma ba tambaya akwai abinda yake damunta

Amma LABEEBAH takafe akan itabah abinda yake damunta
Haka Su mamah suka rabu da ita. Amma XARAH tanace saita gaya mata dumuwarta
LABEEBAH takalleta Tace Wlhi XARAH ba abinda yake damuna sai MASIFAR SOON KAMAL
Ina sanshi ina qaunarsa.
Yana burkitana.
Tunaninsa yafara cutardani
Kuma gashi koxan mutu akan qaunarsa baxan sameshiga

Cikin bala'in tausayi XARAH tafara share mata hawayanta Tace ina jin tausayinki LABEEBAH
Kinfa'da Cikin fa'da Cikin MASIFAR SOO
Abin takaicin shiwanda kikeyi danshi bakisan wayeba
Bakisan daga ina yakeba
Bakisan a ina xaki samoshi bah
Shin tunda kika mishi ganin farko kinqara masa

Cikin kuka LABEEBAH Tace aa banqara ganinsaba

Tace toh kiyi hakuri muta addu 'a Allah ya baiyanasa

Shuru LABEEBAH tamata tana tausayin kanta dajin haushin xuciyarta da takamu dasan Wanda har abada ko sanshi da qaunarshi xasuka kasheta baxata ta6a auransa bah


Awannan ranar Sam XARAH rasa sukuni tayi har da KAMAL yaxo gunta yake tambayarta lafiya yaganta hakah

Kuka tasamai tana labartamai ciwan San da 'Yar uwarta LABEEBAH take ciki. Taqara dacemai yanxu hakama tana kwance batajin da'di
Yace subhanallahi waye yayi gigin shigewa xuciyar qanwata harya haifar mata da ciwo 💘 haka
XARAH tata6e baki Tace hmm sunanshi KAMAL

Yawaro ido Yana cewa no no no plx kicanjamai suna dan baidace yaxo da sunanaba dan ya aikata Babban lefi
Tace Allah sunanshi KAMAL my luv

KAMAL ya girgixa kai taredajan tsaki Yace Wlhi my TEEMAH banso sunanshi ya kasance KAMAL ba..
Dan da gaske nabama LABEEBAH wani matsayi axuciyata
Banso me sunana ne yake wahalar da itaba
Shuru XARAH tayi tanaci gaba da kuka
Daqer ya lallasheta Yana cewa taje tagayama mamah xaishigo ya dubu LABEEBAH.
Nan ko tagayama mamah
Mamah Tace yashigo

Yashigo Cikin nutsuwa suka gaisa da mamah tana yaba kyau da tsari da nushuwa irinna KAMAL

Nan LABEEBAH tafitoh suka gaisa Yace ya jiki. Cikin sanyi Tace da sauqi tana mejin kunyarsa
Cikin murya qasa qasa Yace bama xuciyarki hakuri my qanwa insha Allah xaki kuma ganin KAMAL akaro nabiyu.
Kuma xakisha mamakin yanda xaixo miki da Kalmar SOO

Cikin tsoro LABEEBAH takalleshi Tace waya gayama asirin xuciyata iye Ya KAMAL
Yayi Murmushi cikin jin da'din muryarta Yace me qaunarkice tagayamin XARAH dan natayaki da addu'a ko bakyaso

Saurin girgixa kai tayi Tace inaso. Kuma dan Allah idan xakamin addu'ar ka roqimin Allah yaciremin qaunarsa acikin xuciyata kwata kwata......

Saiyanxu ta ha'da ido dashi. Aiko wani dafin sanshi yafito daga idansa yacaki nata idan
Nan take tasaukar da idanta qasa tare da xubar da hawaye

KAMAL Yace toh Xanyi yanda kikace MATAR KAMAL...........

Da sauri takalleshi takuma kawar da kallannata daga kallansa

Xuciyartace tabuga dam
Tabbas bata ta6ajin kalma meda'di kamar yanda yakira da MATAR KAMAL bah
Tajah numfashi tare da sauke ajiyar xuciya

Shiko KAMAL ganin hawayanta yasashi tabbatarwa tana Cikin MASIFAR SOO
Ya girgixakai da dumbun tausayinta
Yace plx kar kibari San KAMAL ya haifar miki da ciwan xuciya dan Allah

Daurewa tayi tace toh xankiyaye
dan muryarshi kashe mata jiki take tare qamshinsa

Ahaka yatafi yanamaijin tausayinta. Yayinda ita kuma baqin Cikin tafiyarshi yaxiyarci xuciyata kai hatta da gangar jikinta








🌹MASIFAR SOO.....🌹

Bayan wata uku LABEEBAH tashiga tashin hankali dajin da'di kala kala
Dan duk qarshen sati sai KAMAL yaxo. Kuma idan yaxo kwana biyu yakeyi yake komawa Abuja

Yanxu LABEEBAH tagane ganin KAMAL da XARAH baqaramin bala'i da MASIFA bane agareta

Dan yanxu tagane kishin XARAH ne yake damunta tare da qarin MASIFAR SOON KAMAL da take 'dawainiya dashi

Dan haka idan yaxo saita xauna na minti biyar tana leqansa tajikin hujin ginin gidansu tanajin da'di da sanyi aranta tare dajin tsanar XARAH da kuma takaicin xuciyarta
Daga nan saita Koma dakinta tariski kuka sanranta saita kulle kofah tanajin XARAH tana nemanta insun gama xance. Amma saitama kunnan uwar shegu daxuwan bacci take

XARAH nayin gida saita fitoh tayi gun xaman KAMAL tata shaqar qamshinsa tana sauke ajiyar xuciya

〰〰〰〰〰〰〰〰〰
Toh yau KAMAL yaxoma XARAH da babbar magana
Wai xai toro iyayansa asaka ranar bikinsu



Ta kalle shi da alamar 'Yar tsorata agareta. Tace aa kabari sainan gaba
Yace Mene
Tace nasan kaji my luv
Bana san. Nayi Aure LABEEBAH batayiba.
Yace idan nagane xanxanki baxaki xama mallakina bah. harsai 'Yar uwarki tasamu miji amuku Auren tare
Tace eh haka nake nufi. Amma dan Allah kayi hakuri
Yace no karki damu xanyi tunani



Yau LABEEBAH Tatashi da masifaffan menstruation ciwan ciki na al'ada.
Toh
Dama haka yake mata kuma idan yatashi baya mata Nada'di dan jitake kamar xata mutu

Nishi take tana hawaye daka ganta Saita baka tausayi
Innah Tace sannu AISHA Allah yabaki lafiya
Mamah Tace AmEEn
Ni Malam yabani wani magani nabata. Kinga nanemeshi sama ko qasa narasa
Innah tajah numfashi Tace nidai lamarin ciwan nan nata Yana 'dagamin hankali Wlhi. har banaso wata yaqare
XARAH Tace mukaita asibity karta suma kunsani idan hakan tafaru bata farfa'dawa tada'di

Mamah Tatashi ta'dauki gyalanta. Tana cewa kuma gaskiyarki FATEEMA

Innah ta'dagata tana cewa Allah ya rabaki da wannan kiwo kihuta
Sunfitoh daga gidan kenan saiga KAMAL yafaka motarsa
Da sauri yafitoh yana cewa Subhanallahi meya sameta
Mamah tagayamai
Cikin sauri ko yabu'de mota Yace kushiga muje asibity
XARAH Tace kamarko Kasan nan xamu


Bawani bane yadubata a Asibityn Aminu kano fa ce KAMAL
Ya tausaya mata sosai dan sanda tasuma sau biyu. Cikin tausayawa yaxauna yaxuba mata ido Yana naxarinta.
Yau kwananta 'daya kenan batasan wanda yake kantaba

Qura mata ido sosai KAMAL yayi
Fa'di yake aransa
Tabbas baxata rabu da ciwan nan bah har sai tayi Aure.
Yayi shiru Yana kissimawa aransa shidai beta6a ganinta da saurayiba. Gashi yanda yakeji aransa saiso ace tayi Aure nan kusa.
Dan ba qaramin tausayinta yaji ba.Sam jiyayi bayasan takai wani month 'din....
Mustafah ne ya katseshi daga tunanin da ya keyi tawajan shigowa da yayi
Bayan yaxaunane Yace yau qarfi da yaji ka kwacema ANAS aikinsa
Wai wacece ita agunka ko amaryace
KAMAL yayi Murmushi Yace nasan daxaka shigo kaga wata beauty baby
Yace eh naganta
KAMAL ya kalleshi dakyau Yace toh da ita xa'asha bikin
Da dariya sosai Mustafah Yace Amma natayaka murna Allah yasa nan kusa xa'ayi
Cikin wani yanayi KAMAL Yace ina buqatar iyali nan kusa Mustafah. Amma Tace sai wannan tasamu miji Sannan xatayi Auren. Yaqarashe da nuna LABEEBAH da ido
Cikin nuna damuwa Mustafah Yace halin mata saisu. Banda haka yaxa Tace haka
Wannan ai na Allah ne
Kuma shiyasan lokacin kowa
KAMAL Ya'dan ta6e baki Yace Xanyi tunani dan sanin yanda Xanyi
Da wasa Mustafah Yace Kasan Allah tayimin. Wlhi tunda kuka kawota zuciyata tacika da soyayyarta.
Xuciyata sai bugawa takeyi ina addu'ar Allah yasa ba budurwarka bace
Da farin ciki KAMAL yadafah kafa'dansa Yace Amma naji da'di
Plx kafito da wuri. Dan Naqagu naganni da baby
Dariya sosai Mustafah yayi. kana Yace naxama katangarka.......
KAMAL xaiyi magana wayan Mustafa tayi qara
Nan ya 'dauka yana cewa ganinan.
Yamiqe. Bari naje gun doctoh ANAS in ka6i Abu
Toh KAMAL Yace mai Sannan yafita.

Bu'de ido LABEEBAH tayi karab suka ha'da ido da KAMAL
Cikin sauri tajuyar da fuskarta
Dam xuciyar KAMAL tabuga. Shiya rasa dalilin dayasa yake tsintar fa'duwar gabah da xaran ya ha'da ido da ita
Sannu MATAR KAMAL Allah yabaki lafiya Yace da ita
Daqer ta iya furta Kalmar AmEEn. Shima ahankali
Badan kunnansa sun kafa dukar 'daukar duk wata bagana tataba da baxaiji metace bah

Itako LABEEBAH kuka take mara sauti dan yanxu ko magana KAMAL yayi da ita ko da wani tofah ji take tana mata yawi ajikinta kamar yanda jininta ke yawo ajikinta
Wannan wane irin soyayya takema KAMAL wacce takeji aranta duk duniya baxata ta6a Aure bah har sai tasamu me yanayin KAMAL
da Komai nasa. Wannan alqawari ta'daukarma xuciyarta.

Ya kikayi shuru KAMAL Yace da ita
Aiko kamar jira take tarushe da kuka. Ba taso yadinga mata magana da sanyin muryar nan nashi hakan na haifar mata da mutuwar jiki da taso mata da MASIFAR SOON shi

Ayya sorry qanwata insha Allah xakiji sauqi kinji
Shuru tayi
Shima bai qara magana bah ya ha'da mata tie kakkaura.
Tashi kisha
Banajin yunwa
Wannan xai temaka miki wajan saka maganin daxaki Sha yanxu yayi aiki yanda yadace
Dan Allah Ya KAMAL kabarni haka banajin yunwa
Xako muyi fa'da dake Wlhi. in baki shabah
toh Xan Sha tafa'da Cikin wani yanayi me saka namiji jin wani filing
Tajuyo ahankali tare da tashi Amma Sam batayi gigin kallansa bah takar6a
Ka'dan ka'dan takesha. KAMAL nabinta da kallo Cikin sha'awa
Suna Cikin haka Usman ya shigo shida XARAH
Cikin farin ciki Usman Yace a jiki yayi kyau.
XARAH Tace mekabata haka
Yakalleta da Murmushi baice Komai
LABEEBAH Tace Naji Sauqi Ya Usman mutafi gida
KAMAL yawaro ido Yace ina. aisai gobe. Taturo baki dasan yin kuka Tace naji Sauqi fah
Abin yabashi sha'awa yanasan mace 'yar shagwa6a me yanayin yarinta shiyasa yakejin wani yanayi idan Aisha-Labibah na magana kodako badashi bane
Yace plx kibari sai gobe a sallameki
Him um kakasheni kenan da salanka tace aranta
Afili ko kuka tafashe dashi
Usman yace aa yi hakuri yau xamu tafi
Dan Allah Ya Usman mutafi Wlhi baxan kwana ba
Tafa'da da miqewa
Toh shikenan bara inkar6ar muku sallama KAMAL Yace tare da ficcewa.
XARAH ta harare tah
Wlhi muka koma gidah kika damemu da ciki na ciwo sai kinsha mari
Yan zune dariya taxoma LABEEBAH Tace gaskiya kin rainani kidinga tuna cewa awa uku kikaban a aihuwa
Ko minti 'daya nabaki nice dai sama dake. Kuma dole idan kikayi lefi inmiki hukunci
LABEEBAH Tace hmm kibari nasamu sauqi sosai bakina yabu'de kisha mamaki
Murmushi Usman yayi Yace XARAH dasan girma LABEEBAH da tsiwa da surutu. Nidai inasan caftarnan taku

KAMAL ne ya shigo hannunshi 'dauke da magunguna.
Yace muje angama Komai
Usman Yace sannu fah da qoqari Allah yabiya
Yace no karka damu
Yace Ni Kasuwa ma Xan hucce
KAMAL Tace toh sukayi masa baha

Amota ne KAMAL yasamu damar da Yace qanwata ki temaken XARAH taxama tawa nan kusa gabanta LABEEBAH ya fa'da Cikin rawar murya Tace haba Ya KAMAL ai XARAH takace
Yace a ina.......
Cewa fah tayi baxata auran bah har sai kin fitoh da Miji ayi tare
Da sauri LABEEBAH takalli XARAH Tace me hakan yake nufi
Tab xaki danqare dan Wlhi baxanyi aurebah har sai naga KAMAL

Baki da hankali. Wai har sai yaushe xaki gane Annabi yakafu. a ina xakiga KAMAL. kinga malama inxaki tsaya kigane hanyar me 6ellewa toh kitsaya kifitar da wani KAMAL aranki dan baisan kinayiba. Kitsaya kixa6i 'daya daga Cikin Masu sanki muyi Aure tare. Dan baxan iya yin Aure nabarki bah
XARAH CE me wannan furucin Cikin 6acin rai

Nayima xuciyata alqawarin baxan ta6a Aure ba. har sai nasamu me yanayin KAMAL
Me qamshinsa me muryarsa
Kada san rai yasaki cutar da Ya KAMAL kibashi dama ya turo maga batansa
LABEEBAH nafa'din haka tayi yunkurin fitta daga motar KAMAL Wanda yayi faking 'dinta yanxu dai-dai kofar gidan nasu......
KAMAL Yace gud qanwata yanxu ke my luv saiki sakemin Mara inyi futsari tunda wacce kikayi furucin dominta tabaki dama.

Cikin yanayin tausayin LABEEBAH
XARAH Tace shikenan Allah ya tabbatar da alkairi
Dai-dai nan LABEEBAH tasaka kanta Cikin gidansu xuciyarta na bugawa


Tana shiga taci karo da mamah. Cike da mamaki mamah tasaki kayan hannunta tarungumeta Tace yanxu muke shirin tahowa da innanku ashe jikin da sauqi ke dawa kuka tawo
Cikin shagwa6a LABEEBAH Tace naji Sauqi dan farkawa nayi kawai najini garau. Nida XARAH da KAMAL ne
Cikin farin ciki mamah tajata xuwa 'daki sun xauna kenan Innah tashigo da farin ciki
Tace eh gaskiyane jiki yayi kyau. Mamah Tace kinganta nan muna qoqarin xuwa saigasu
Tace aikowa jiki yayi kyau kome suka bata oho......
XARAH CE tashigo da magunguna ahannunta Tace gashi injishi wai dan Allah kidaure kisha zakiga Komai arubuce
Tace toh takar6a
Mamah Tace Allah ya saka mishi da alkairi. Duk sukace AmEEn

Kwana biyu ta warware dan kam batayi sawa dashan magungunan bah


Mustafah Yaxo ga LABEEBAH da gaskiyar xan cansa nasan Auranta
Amma tarufe ido Tace bata san shi.
Abinda ya baqanta ran XARAH kenan har tace ixuwa yanxu nafara tsanar KAMAL 'dinnan ke nama tsaneshi
Cikin 6acin ran meyasa xatace tatsaneshi LABEEBAH Tace dama kindena dan abin sanki ne



KAMAL ya turo da magabatansa ga Mahaifin XARAH kuma sunyi bincike sun tabbatar KAMAL daga gidan mutunci yafito
Dan haka take Su manyan suka bada sadaki da saka ranah nanda wata takwas. Asha biki


KAMAL da Auwal a kofar gidansu XARAH. Fa'di Auwal yake plx kakira 'daya daga cikinsu mana lokaci na tafiya.
KAMAL yayi Murmushi toh agogo sarkin aiki. Inban mantaba yanxu muka dawo daga wajan siya musu waya koka mantane
Auwal ya dafe goshi Yace ya Allah
Wlhi namanta shaff...
Bai qarasa furucinsa bah Su XARAH suka fitoh
Sunyi kyau sosai Cikin shigar dogayan riguna kamar kasacesu kagudu

_Zuciyar Auwal fa'di take sarki ya tabbata daga Allah yake LABEEBAH sarauniyar kyawawa. shidai gani yake Aisha-Labibah tafi Fatima-zarah kyau Yayinda xuciyar KAMAL take qaryata hakan danta shagaltu da soyayyar TEEMANSA_

Tatuqi yake Cikin gwanin cewa
Ga wayoyunku 'yan gatan KAMAL. Auwal yafa'di hakan da dariya
Suma dariyar sukayi
Wayoyin sunyi kyau duk *LG* ne kuma iri 'daya
Cikin farin ciki sukamai godiya Yace no karku damu
XARAH takashe mai ido 'daya da cewa
Kanaji damu my luv gaskiya inajin da'din hakan Allah yabarni da sahibina
Kunfi haka TEEMANAH kuma inbanji da kuba dawa xanji
Kinkasance masoyiyata abin alfaharina ina sanki TEEMAH plx kiqara sonah
Nayi rantsuwa xan soka har qarashen rayuwata Xan kyautata maka har sai kace ya'isa Xan bika har qarshen numfashina. Amma inajin tsoron kar wata rana kaqini kaso wata ka wulaqantani..........

Parking yayi a Cikin gidan kakarsa inda dama sunxo gaisheta ne
kallanta yayi Cikin kulawa tare da kafeta da wani mirgi 'dad'dan kallo Yace xuciyata tacika dam da qaunarki. bawata *'YA* *MACE* daxanso bayanki
Karkiyi kokwanto balle shakka. kisaka axuciyarki narike miki alkawari dan Allah kiyarda dani sannan kicire xargin... hakan axuciyarki
Itama Cikin nata kalan kallan takalleshi Tace karka damu ko 'daya baxargi acikin xuciyata. nayarda dakai sosai

Da wani shegen kallo Yace Allah yabarni dake
Sam KAMAL-da XARAH sun manta da LABEEBAH da Auwal acikin motar sukaci gaba da hirar soyayyarsu

Ixuwa lokacin ko LABEEBAH takai maqura dan haka batasan lokacin data da qarqare ba. Ta fashe da kuka tana rayawa aranta KAMAL da XARAH xasu kasheta kwananta beqareba

Nan suka farga da inda suke. Cikin mamaki da Al'ajabi Su uku sukace lafiya LABEEBAH me ya faru
Cikin kuka sosai ha'de da shagwa6a Tace kai... Nane.... Yake... Min ciwo.. Muyi sauri mukoma gida

KAMAL ya kalli Auwal shima Auwal 'din kallansa yayi
Yace my TEEMAH haka MATAR KAMAL ta ke
XARAH tajah numfashi Tace hmm haka take da shegen shagwa6a musamman agun mamah da innah. Kai ga kowama na gidanmu
Amma nalura ha'duwarta da KAMAL yaqara ta6ara mana ita
Auwal Yace ikwan Allah kenan. toh yi shuru yanxu xamu koma

Cikin wani yanayi KAMAL yamiqa mata hankicif Yace sorry ko. Ga wannan ki goge fiskarki
Kar6a tayi tagoge fuskar tata tana cewa a _axuciyarta ko Ba komai dai na katsemuku soyayyarku 'yan rainin hankali_

Haka suka fitoh Suna

Please Login or Register in order to submit comment