Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya gudu karta kamashi aiko tabishi yana gudu tana binshi abin gwanin sha'awa.
Can ta ritsashi Tace wana kama
Yace yi hakuri Momyna baxan qara bah Tace toh ina kaje
Yace gun Dadyna....
Waro ido LABEEBAH tayi Tace oho a ina ka ganshi Yace acan gashima Yace inbaki
Da sauri LABEEBAH kar6i ledar tabu'dewa.
wata fulawa CE mekyau sai handkerchief da turare da 'dan wani not a paper ka'dan
Tayi saurin bu'dewa.

_nadawo gareki my baby_

Gaban LABEEBAH yayi wani bala'in bugawa ba shakka wannan qamshin KAMAL ne a handkerchief 'dinnan me hakan yake nufi
Nan ta waroma SAUBAN ido Tace a ina yabaka Yace acan. Yafa'da yana me nuna mata bayanta
Nan tajah hannunsa suyican suyi nan
Ko ina SAUBAN nuna mata yake Yace anan yaga Dadyn nashi
Can dai da tagaji taje ta 'dauki abinda takeso na kayan make-up da kayan xaqinsu tayi gaba
Awajan biyan ku'di mah cemata sukayi taje anbiya mata Tace Waye sukace MALUDDEEN
LABEEBAH tacika da mamaki ahaka suka dawo gida take bama XARAH labari
Dariya XARAH tayi Tace qila na saudiya ne ya biyoki.
LABEEBAH tayi tsaki Tace koma Waye plx yayi saurin bayyana agareni naxa'ku in gansa Wlhi
Rukayya Tace kiyidai ahankali kar yana 'kofah yajiki yajah miki aji
Tace ni ina mace banjah masa ajibah saishi
XARAH Tace ai indai agarekine qamshinsa wannan ka'dai baxai barki kija mai ajibah
LABEEBAH tajuya idanta Tace xan baku mamaki ne


Washe gari da misalin qarfe goma Bayan LABEEBAH takai SAUBAN skull
Tana xaune agidansu XARAH tana karanta wani littafi wai shi *K@ULAT D@ ALHAXAWAN ABUJAH*
Daga ita sai XARAH ne agidan dan innah taje kantin kwari siyayya
Wani yaro ya shigo Yace ana sallama da LABEEBAH
Tace kaje kace waye yaran Yace wai inji MALUDDEEN
Cikin sauri LABEEBAH Tatashi Tace kace ina xuwa. Yace toh
Dake XARAH na bayi
Sai kawai taxari gyalanta ta tafitoh wajen dan dama a kin tsanta take


.
[12:09PM, 18/10/2016] Rahamat Nalele💋: Wani baqin mutum tagani jingine a jikin mota Yana binta da Murmushi Yace sannu Ko Tace Yauwa
Yace dama yaran da kika kai skull 'daxone matsala ta meshi plx xaki iya binmu kiga halin da yake ciki
Da sauri LABEEBAH Tace eh dan Allah meya sameshi
tafa'da kamar xatasa kuka
Shiga motar yayi da Bu'de mata yana cewa muje ki gani
Aiko LABEEBAH tashige harda saurin rufe 'kofar shiko ya figgi motar da sauri
Juyo wannan da LABEEBAH xatayi idanta ya sauka akan MALUDDEEN.
Habawa aiko tasaki wani ihu yayi saurin rufe mata baki da hannunsa.
Ta waro mishi ido abala'in tsorace Yace Ki nutsu my baby
Aiko sai LABEEBAH tayi luuu taxube sumammiya.
MALUDDEEN ya janyota jikinsa
Marwan dake gidan gabah Yace tab😳
'dan Uwa ta sume fah
Yace nasan xa'ayi hakan

Wani kata faran gida NIGO yayi parking a cikinsa.
MALUDDEEN ya 'dauke bai direta ako inaba sai a falan gidan kan kujera
Ya xauna kusa da ita da yayyafa mata ruwa
Nan LABEEBAH ta farfa'do
Ai tana qara ha'da ido dashi taqara sumewa
Ya dafe kai da qata yayyafa mata ruwa
Nan taqara farfa'dowa
Wannan karan fashewa tayi da kuka tana dan Allah dan Annabi aljani karabu dani
Ya kai hannunsa gefan fuskarta nan taji wani shock tayi saurin lumshe idanta gabanta na fa'duwa Yace plx my baby Ki nutsu kuma kiyimin shuru da kukannan
Tsit LABEEBAH tayi dan itadai har ga Allah tasa aranta MALUDDEEN aljanine
Yace Yauwa toh tashi
Tatashi da jingina ajikin kujerar tana addu'ar neman tsari da aljanu Sannan idanta aqasa
ya xubah mata ido can yayi Murmushi Yace niba aljani bane da kike neman tsari dani
Tabi qafarshi da kallo nan taga irin ta mutanece
Takalleshi Cikin shagwa6a Tace toh kai Waye kuma meyasaka kawoni nan
Ya kalleta ka'dan Wato har yanxu ga shi dai baxata dena yimai shagwa6a ba
Yace ni sunana MALUDDEEN......
Tayi saurin katse shi da cewa toh kasaka KA afarkwan sunan naka mana kaga saiya bakah KAMALUDDEEN
Yace dakyau my baby haka sunan yake
LABEEBAH taqara furgita Tace qamshinka 'daya dashi fuskarku 'daya jikinku 'daya muryarku 'daya Komai naku 'daya meyasa haka xata faru bayan ba'a mutuwa adawo. Kawai dai kai aljanine
Yace naji ni aljanine kuma Auran Ki nakeso nayi
Tawaro ido Tace aiba'a Aure tsakanin bil'adama da Aljani
Yace xa'a fara daga kaina Yafa'da dakai bakinsa goshinta yayi mata kiss
Yaci gaba da cewa natsanci kaina acikin farin ciki yau ina tare da baby na
Kuka LABEEBAH tasa mai
Yace shuru
Shurun tayi
Yace xan dingaya miki shara'do'di biyu
Na Farko xan dinga kiranki awaya munayin hira
Na biyu Xan dinga xuwa gareki kuma kifitoh
Ta bala'in marairaicewa Tace dan Allah karabu dani Yace Wlhi baxan rabu dake bah. Kuma idan kika bah qawarki XARAH labarin nan saina hukuntaki
LABEEBAH taxuba mai Tace toh mai dani gida dan Allah
Xan mai dake Amma sakin bani breakfast dan banyi bah. Yafa'da yana nuna mata kan table inda kayan break 'din suke
Tace meyasa saini xan baka. Yace saboda ke kike da alhakin 'daukar hakan
LABEEBAH tagya'da kai

Haka tanaji tana gani tadinga bah aljanin nata abinci yanaci yana qare mata kallo
Ita kuma tana kukan xuci

Can Yace oya tashi namaida ke gida ko Babyna Bayan KAMAL babyn MALUDDEEN babyn aljani babyn YUSU.......
Sai suka ha'da ido ya sakarmata Murmushi
Da sauri tatashi ko gyalanta ba 'dauka bah tafara yin hanyar waje
Yace kinga
Tatsaya cak
Ya qaraso gareta da yafah mata gyalan nata. Ya'dago ha6arta tarumtse idonta. Saiya kai bakinsa kan nata yayi mata qaramin kiss tabu'de idan nata ka'dan saiya janyota jikinsa ya rungumeta
Na tsawan minti 'daya ya sauke ajiyar xuciya kana Ya kama hannun suka fitoh
Wannan motar dai dasuka sato ta acewarta ita suka shiga. Ya jasu

LABEEBAH dai tunda ta sunkuyar da kanta qasa bata 'dago bah dan itadai addu'arta "daya taganta agida
Shiko MALUDDEEN kallanta yake jifah jifah xuciyarsa cike da santa da qaunarta

Itadai taji sun tsaya dan haka ta'dago ahankali takalli inda suke nan taga qofar gidansu ne
murna tacika tayi yingurin fitta nan taji 'kofar akulle
Tajuyo ahankali takallesa Tace aljani budemin tohhhhh
Yace kalleni
Ahankali.tatsaida idanta akansa.
Nan xuciyarta tafara bugawa dan Wlhi gani take wannan KAMAL ne
Yasa hannunsa ahankali ya janyota jikinsa tare dasa handkerchief 'dinsa yana goge mata fuskarta LABEEBAH tayi lub a qirjinsa yayi Murmushi Yace kar kiyimin bacci
Da sauri tajanye kanta daga gareki
Yafita daga motar yaje ya bu'de mata
Nan tafitoh tayi hanyar gidan nasu. Sanda takai 'kofar gida tajuyo tana kallansa
Suit CE ajikinsa sky blue tayi mishi kyau Sosai
Ta shagala da qare mishi kallo ya 'daga mata gira dayi mata nuna da ido alamun lafiya
Har tana bige goshi wanjan yin saurin shigewa gidan nasu
MALUDDEEN yayi saurin runtse idanshi da bu'dewa yanajin tamkar shine ya bige
Haka yajah motarsa yana tuna babyn tasa

LABEEBAH ko tana shiga gidannan nasu taxauna akan turmi ta xubah uban tagumi
Tunani takeyi yanxu XARAH tarabu da 'yan shan jini gashi ita kuma ta ha'du da aljanu


Har yamma LABEEBAH rasa nutsuwarta tayi. Har kowa ya lura da sauyin nata
Suka tambaye ko lafiya Tace Bakomai
XARAH Tace da Komai LABEEBAH tunda kikace 'daxo naje na 'dauko SAUBAN a skull nasan akwai abinda yake damunki
Dan ko ciwo kike saikin je 'daukosa
LABEEBAH Tace bafah Komai.
XARAH tata6e baki Tace Allah yasa

Kusan qarfe tara wayan LABEEBAH tafara ringing
Data 'dauka saitaji muryar KAMAL Yace my baby
Aida sauri tagyara xama da cewa innalillahi
Yace wa'inna'ilalhirraji'un
Cikin sarewa da shagwa6a Tace toh Me nene kuma
Yace fa'damin
Tace mene
Yace me kike cema YUSUF idan kika kasance dashi
LABEEBAH tawaro ido eh Lalle lamarin aljanu sai Su har yasan YUSUF
Tace na manta
Yayi Murmushi Yace Ki tuno
Tace Wlhi na manta
Yace kosai na tunomiki
Tace aa me toh Kake san ji Yace so nake Naji me yafara birgeki dashi har kikaji kina sanshi
LABEEBAH tayi shuru tana tunani can Tace kaga yana da kirki kuma yana sonah.....
Sai tayi shuru
Shima shurun yayi can Yace shikenan
Tayi saurin 'daga mai kai kamar yana gabanta da cewa eh
Cikin sanyin murya Yace bansan wane irin so nake miki ba my baby kowa yanada wacce yakeso ni dai ke naso kuma xanci gabah da sanki har qarshen rayuwata
LABEEBAH tajah numfashi cikin sanyin kuka tace nima ina sanka
Yace kar kiyimin kuka
Rufe bakinta tayi da hannu hawaye ya xubu mata.
Yace plx kiss me
Wataro ido 😳

Yayi murmushi yace in baxa kiyi min bah nixan na6ullo ta bango inyi miki
Da sauri LABEEBAH tayima wayar kiss hannunta na rawa
Yace toh kiyi bacci da mafarkaina kinji
Toh Tace mai da kashe wayar
XARAH tata6ata nanta tsorata
Tace Waye ya furgitaki haka
Hawaye ya xubuma LABEEBAH Tace wani ne Wlhi yajefah soyayyarsa axuciyata daga xuwa dare ya hargitsa min nutsuwata
XARAH Tace tab salan soyayyarsa ya bani sha'awa kalli yanda yasaki kuka lokaci 'daya
LABEEBAH takwanta da jawo SAUBAN jikinta batace mata Komai bah


Washe gari kusan qarfe hu'du XARAH da LABEEBAH ne suke tawowa gida dan sunje gidan Ya Bashir Innah CE ta aikesu fa'da masu aihuwar wata makwaf ciyarsu
Xasu shugo layin nasune XARAH taga Alhaji Nura wannan me ku'din unguwar tasu takalleshi ya kalleta Tace A'uxubillahi
Sai yayi saurin wuccesu
LABEEBAH Tace yadai
Tace hmm masu ku'dinnan 'dai-'dai kune ku'din nasu na Allah da Annabi
LABEEBAH Tace meyasaki fa'din haka Tace hmm share kawai.........
Kan LABEEBAH tayi magana wata shegiyar mota me xafi da 'daukar hankali tayi parking agabansu
MALUDDEEN ya leqo da kansa Yace jimana 'yan mata dan Allah ku'dan jini ka'dan tambayarku Xanyi
_jimana 'yan mata dan Allah karku shareni ina tambaya ne_
XARAH LABEEBAH suka tuno da wanda yayi musu wannan furucin ashekarun baya
Gabaki 'dayansu xubah mishi ido sukayi XARAH tagigice ta furgice Tafara nunashi da yatsa Tace KAMAL.......
MALUDDEEN ya ta6e baki yace MALUDDEEN saikin
Sannan ya maida kallansa ga LABEEBAH Yace dama sunanki xan tambaya my luv
_dama sunanki xan tambaya my luv_
LABEEBAH tatuno da Kalmar da KAMAL ya gayama XARAH tun farkwan ha'duwarsu dashi.
Sai tayi murmushin yaqe ta'dan kalli XARAH ka'dan tare da qarema gun kallo tatabbatar tarihine xai maimaita kansa me makwan akan XARAH sai taga akanta lamarin yakesan juyewa ita da ALJANIN nata
saita qarayin murmushin yaqe wai kafi kuka ciwo
Tatsaida idanta akanshi da kyau Tace ayya banda sunah. Yace yayi murmushin jin da'di dan ganin xata biyema wasan nashi Yace kice ke 'Yar baiwace. Tace ba mamaki kam yayana
Sauri muke kaga baifi taku hamsin xamuyi ba mushiga gidanmu. Dan haka kasamu damar daxaka iya tambayar cikakken gaskiyar xancanka nabaka minti 'daya.
Yace gaskiyar xancan shine tunda na'dora ido akanki xuciyata takamu da soyayyarki ina sanka my luv
Lamarin fah yafaraba LABEEBAH tsoro Amma ta dake tasa aranta saitaga abinda ya turema buxu na'di
Dan haka tagyara tsayuwa da kyau
Tace tab kamakara dan isiyaku ya rigaka shiga Birnin soyayyata dan haka sai anjima..........

Luuuuuuuu XARAH taxube aqasa sumammiya
LABEEBAH ta kalleta Sannan takalli MALUDDEEN tata6e baki xata rushemai da kuka yayi saurin katseta da cewa idan kika min kuka Wlhi saikin sani
Shuru tayi saita kalleshi ta kalli XARAH data sume...
Shima maida kallansa yayi ga XARAH yana murmushin mugunta Sannan Yace temaka mata mana kin barta axube
LABEEBAH ta xubamai ido





Tare da kalar tausayi Tace ai baxan iyaba ni 'daya bah Yace OK inje in kira miki Sumayya ne. Yafa'da da kwaikwayan ta.

Ta kallesa da kyau Tace me yasa saika kirata bayan gaka kawai ka temaka min
Yace wa ni😳
Saiya girgixa kai da 'dauko wani ruwa daya ke gefansa
ya miqa mata Yace yayyafah mata idan tatashi kice mata takwantar da hankalinta kar tayi sanadin daxaki rasata
Yana fa'din haka yajah motarsa
LABEEBAH tabishi da kallo lallema aljaninnan bashi da mutunci da tausayi.

ta dai xubama XARAH ruwan amma shuru XARAH bata farfa'do bah
Gashi har yara sunfara taruwa
Can saiga Ya Usman kamar anjefushi Yace Subhanallah meya same ta
LABEEBAH tayi shuru
Baijira cewar taba ya kinkimi XARAH yayi gidan nasu da ita
Akan taburma ya direta cikin tashin hankali yake tambayar LABEEBAH waime ya sameta ne
Tace wani tagani me kama da KAMAL
Yace ikwan Allah nan ya dinga yayyafah mata ruwa
Can ta farfa'do
Aiko ta qamqame hannun LABEEBAH Tace Wlhi ko kaffara baxanyi bah LABEEBAH
KAMAL ne wannan mutumin .
LABEEBAH ta girgixa mata kai Tace bashi bane aljani ne

XARAH ta gallah mata harara Tace Wlhi ba aljani bane mutum ne kuma KAMAL ne

Ya akayi haka. dama bai mutu bah
LABEEBAH Tace nagaya miki aljanine
XARAH tajah tsaki da fashewa da kuka Tace Allah ya isa Turai Allah ya isa
Kin cutar dani kin ha'in ceni.....
Usman ya katseta da cewa kinga dakata
Yan xuma tana shirin maida ke cikinsu ne

XARAH Tace aa Ya Usman kawai dai ta cutar dani ne
Bata ban shawara ta gari ba
Nayi nadamar saninta
Ba wacce na tsana a duniya kamar ta..
Usman yajah numfashi Yace toh Madallah tunda abinda nayi xato bashi bane
Yana fa'din haka ya bargun
XARAH ko taciga da sambatunta tayi tana kuka
Fa'di take aranta indai wannan bawan Allan KAMAL ne itakam ta mutu ta lalace.
Idan kuma aljanine tabakin LABEEBAH tabbas tayi gamo da MASEEFAR SON SA😳

LABEEBAH ta xuba mata ido kawai sai kayi tunanin XARAN take kallo nanko tunanin aljanin saurayin nata take
Ita dai kam ta kashe wayanta dan bataso ya kirata ya hargitsa mata kwanya



Har Washe gari
XARAH fah😳 tashiga tashin hankali ba'dan ka'dan ba.
Idan ta rumtse idanta fuskar MALUDDEEN take gani
Ko kaffara tace baxa tayi ba KAMAL ne

Gashi yanxu ba ita bah Hajjiya Turai bare takirata ta tambayeta ya abin yake
Can tayi tunanin takira Su Musa jage mana
Aiko takirasu tana tambayarsu dama KAMAL bai mutu bane
Musa jage Yace me kika gani
Tace wani ne ya bayyana agaremu Komai nasa na KAMAL ne
Yace toh Gaskiya yanda kika kashe shi haka muka ya dashi a ruwa yanda kika umarcemu
Kashe wayan tayi tana tunanin ya abin yake


A abujah ko abinda ya faru shine motoci sunkai biyar wa'yanda sukayi parking a cikin gidansu Momy
MALUDDEEN ne fitto daga 'daya daga cikin wa'yannan motocin ya'dan tsaya ka'dan yana shaqar shamshin gidan. Kana yayi Murmushi ya 'dagama Marwan hannu Yace xomu shiga tare ko
Nan Marwan mah ya fitto suka shiga cikin falan gidan.........
Dake Dady yana gidan Kasan cewar lahadi Safna da Sagna basa nan Suna gidan wata qawarsu
Gidan yarage daga ma'aikatan gidan sai Momy da Dady

Dady yana dining da jarida ahannunsa shi bacin abinci yake ba Amma daka gansa xakasan yayi shirin cine

Gaban dady ya fa'di dan jin muryar da har ya mutu baxai manta da ita ba.
ya juyo ahankali idanshi ya sauka akan MALUDDEEN
Kasan cewar shi na Miji kusan Allah ya horema wasunsu nutsuwa
Yayi tasbihi ga Allah xuciyarsa tana bugawa
Yayi qarfen halin nuna MALUDDEEN da hannunsa Yace KAMAL
MALUDDEEN yayi mai shuru
Saiga hawaye ya xubuma Dady Yace nasan gixan da idanona yasaba munne

Hawayan ne ya xubuma MALUDDEEN KAMAL
Yace Dady ba gixo idanka yayi maka bah. Nine KAMAL 'dinka
Da sauri dady yayi cilli da jaridar hannunsa ya tashi ya iso ga KAMAL tare da ta6ashi
KAMAL ya rungumesa cikin kuka Yace nine KAMAL Dady KAMAL ne
Dady qamqameshi yayi Sosai yana cewa Kaine Kaine KAMAL dama baka mutu bah

Momy tafitoh idan akan dining tana cewa ayya Dady na barka shuru
Tun a kitchen nakejin qamshin turaran KAMAL.
Ganin datayi Dady baya dining tajuyo da kallanta inda taji motsi ai cak Momy tatsaya ta qurama KAMAL 'dinta ido tana cewa KAMAL
Yace na'am Momyna
Aiko sai ganinta sukayi a qasa tasume


Bayan da kamar 10 minutes Momy ta farfa'do KAMAL ya fara dacewa
Wanine yaxo min akan anturo shi ya 'dauke
Banyi wani tunani ba na shiga motar tasu aiko wani daga cikinsu ya fesamin abu
Abin mamaki Momy Dady ban tashi tsintar kaina ba sai agun Sarki Yayan maman saurayinnan
Ya qarashe xancan nasa da nuna musu Marwan

Nan take Momy da Dady suka shafa kansa cikin farin ciki suke godema Sarki....
KAMAL ya qara da fa'da musu yanda Sarkin ya tsincesa
Momy da dady sunyi mamakin yanda KAMAL ya lulaqa qasar Armiyaniya
(Toh ai ba'a mamaki da lamarin ubangiji )

Da kanta Momy Tatashi ta gyarama KAMAL part 'dinsa na gidan
Murna tacika xukatansu
Sai waya da waya Momy da dady suke Suna gayama Mutane bayyanar KAMAL
Kan kace kabo KAMAL ya fara amsa xan cikan mutane na murna da bayyanarsa

KAMAL ya sallami mutanan nasa daya manta dasu a farfajiyar gidan nasu Yace sai sun ha'du kawai

Sagna da Safna sundawo daga gidan qawar tasu
Suna saka qafarsu afalan nasu suka ha'da ido da KAMAL kwalla qara sukayi dan ganin Yayan nasu
Momy taje taqaraso dasu cikin falan nan tagaya musu abinda yace musu

.
[6:00PM, 19/10/2016] Rahamat Nalele💋: Aiko suka rungume Yayan nasu murna cike a ransu
Sagna Tace bara na kira Aunty XARAH da Aunty LABEEBAH
KAMAL ya lumshe idansa dan jin takira LABEEBAH
Momy CE tayi saurin cewa Karki kirasu ki bari jibi xan ka'da mai walimar murnar bayyanarsa kinga gobe sai in sa a kawo minsu nan in musu baxata. Saidai kawai sugansa
Safna Tace kuma gwara ayi haka
KAMAL yayi Murmushi yana cewa aransa sun rugaku ganina momy. Musamman my baby


Kusan qarfe tara KAMAL ne a shashinsa shida Marwan suna hira
Marwan Yace abinda ka fa'dama Sarki da ban
abinda kacema Su Momy da ban
Ni kuma ka fa'damin Komai
KAMAL Yace banta6a qaryaba Amma sanda XARAH tasani yi
Na fa'dama Sarki hakane dan kar yayi yunkurin sadani da iyayena awannan lokacin
Saboda banga amfanin bayyanata agaresu awannan lokacin ba
Sannan na gayama Su Momy hakane dan banasan hankalinsu ya tashi da XARAH Su tsaneta kamar yanda na tsaneta kaga in haka tafaru baxan sami ha'din kansu yanda nakeso akan mallakar LABEEBAH da nakesan yi ba
Dan xasuyi tunanin ai XARAH da LABEEBAH haka suke dan haka dole LABEEBAH ta'ibi wasu halaiyar XARAH
Kaga idan sukayi wannan tunanin na rasa LABEEBAH kenan har abada

Kai kuma na gayama gaskiyane dan kawai ra'ayin kaina

Marwan Yace tunaninka Yayanah yana jaaaa
Allah ya karemin kai Yace AmEEn
Nan MALUDDEEN wanda ya koma KAMAL ya dinga kiran wayan LABEEBAH shuru
Marwan Yace da mutananka har yanxu Suna aikinsu da kaga dalilin rashin samunta da bakayi bah
Yayi Murmushi Yace watoh Marwan inama LABEEBAH wani SOO wanda yafi qarfin ~*MASEEFAR SOO*~
Fatana taxama jarumata dan nalura xatayi ragwanta
Marwan Yace ba daga nan take ba Yayanah Amma ina maka fatan samunta yanda kakeso
KAMAL yatashi yana cewa Nagode
Saidai nayi maka shish shigi
Marwan Yace namefah. Yace nayi maka mata
Marwan ya waro ido cikin dariya Yace ayya Yayanah kamin afuwa dan naga wata xanka'da xeeeya😳💃🏼

KAMAL yayi Murmushi Yace Safna ko Sagna
Tace itoh medai rawar kannan haka.
Yafa'da da ta6e baki
KAMAL Yace nasoka da Sumayya
Amma ba damuwa tunda Sagna tatafi da xuciyar taka ba wani abu
Yafa'da yana me ficcewa daga 'dakin

Direct gun Momy ya nufah Yace Momy tasakar mai Murmushi
Yace nayi Babban rashi Tace hmm har mu mah
Yayi Murmushi Yace Allah kaji qan YUSUF
Tace AmEEn
Ya gyara xama Yace Wlhi momy nadawo da ~MASEEFAR SON~ 'yarki LABEEBAH
Ta kalleshi ka'dan dayi masa Murmushi Tace ainayi mata Miji
Da sauri KAMAL ya kama hannun Momy Yace haba Momy kituna mana
Tunfarkwan soyayyata da XARAH nace miki banajin wani filing akan sai akan LABEEBAH
Kin tuna😄
har nace miki idan na ha'da ido da ita tsintar Kaina nake a fa'duwar gaba
Kin tambayeni banajin hakan ga XARAH nace miki eh
Pls my Momy idan ban auri LABEEBAH bah mutuwa xanyi Wlhi
Tace KAMAL ka nutsu katsaya ka maida matarka XARAH
Yayi saurin waro ido😳 Yace wa ni😳 inaaa
Na gama Auran XARAH har abada
Momy Tace meyasa Yace Wlhi Momy baxan qara rayuwar Aure da XARAH bah. Dan tayimin lefin da inhar nabari taqara xama mata agareni toko baxan ta6a yima kaina adalci ba
Kuma baxan yafe ma kaina bah
Sannan baxan ta6a yimata adalci bah
A taqaice dai na tsaneta baxan qara yarda taxama mata agareni ba
Momy taja numfashi Tace ka gayamin dalilinka
Yace ba dalili momy
Tace ka gayamin Gaskiya toh
Ya qara kama hannunta Yace kishare kawai Momy kibar batunta ki Auramin LABEEBAH kawai idan kina san farin cikina
Momy ta jinjina kai Tace OK Allah ya shige mana gabah
Yace Yauwa Momy kin bani 'Yar taki
Tace nabaka idan ita 'din tayi na'am da kai
Ya tashi yana Murmushi Yace ai duk duniya ba wa'yanda suka dace da juna sai ni da LABEEBAH tayi na'am dani Momy Nagode miki goodnyt....

Momy tabishi da kallo cikin Murmushi
ta sani YUSUF yaso LABEEBAH Amma tayi mamakin yanda har ya mutu bai kusanceta bah
Abin ya bata mamaki Sosai



A *kano* ko
LABEEBAH CE xaune da wayarta ahannunta sai juyata takeyi tana wasi wasin kunnata saboda fargabarta da aljanin nata

XARAH na gefanta ta xabga uban tagumi tana tunanin wannan bawan Allan da taji LABEEBAH ta ambata da aljani.
MASEEFAR😳 SON shi takeji har cikin ruhinta😳

Sumayya na xaune da SAUBAN tana buga game yana cewa taba shi ya buga dan tabuga game over da yawa tadena mishi wayo
Tayi dariya Tace Lalle yaran nan kanada kwakwalwa

Rukayya na xaune kan turmi jiki asanyaye dan yanxu tagama amai dan ciki ya kusantuta😄

Innah tashigo da waya ahannu kallo 'daya duk suka mata sukasan tana cikin farin ciki da murna
Tace toh yaran Momy gobe da safe direba xaixo ya kwasheku ya kaiku garin na Abuja dan tana ha'da wani walima bayyanar abinda basuyi xatoba dan haka tanasan ganinku agun
LABEEBAH da XARAH sukace toh
Duk da Innah talura yaran nata na cikin damuwa Amma batayi gigin tambayarsu bah
Dan tasan ko tace miye cewa xasuyi ba Komai
Mu samman ma XARAH da jiya tana kallanta cikin dare tana riskar kuka dan a 'dakinta suka kwana BABAH yaje qauyan garin babba nanan kano wajan wani amininsa acan ya kwana
Tajuya ta fitta
Sumayya takwashe da dariya Tace ai xuwa Abuja danine

Rukayya Tace hmm bakiga mutanan naki duk Suna cikin damuwa bane
Sumayya Tace eh nagani ai nadena damuwa da damuwarsu tunda sun xa6i subarta acikinsu ai shikenan

LABEEBAH taja numfashi tayi shaha'da ta kunna wayar tata
Aiko ko 2 minutes batayi bah saiga wayan KAMAL aljanin nata ya shigo
Aiko saita rushe da kuka kowa ya xuba mata ido tayi saurin shanye kukan ta'dauka da cewa hello
Yace waya ta6amin babyna
Taturo baki kamar tana gabansa Tace kaine mana
Dan Allah a ina kata6a jin anyi Aure tsakanin aljani da mutum

Murmushi KAMAL yayi Yana kwance akan gadan shi
Marwan na kujera yana kallan wani film na mutuniyar tawa Rahama Sadau👯 waishi JININ JIKINA😄.



Yace toh ya xanyi Babyna Allah ya jarab ceni da MASEEFAR SONKI. Akaina xa'afara wannan Auran

LABEEBAH tagyara muryar xatayi kuka
Yace Kinsan Allah kika yimin kuka alokacinnan da nake buqatar farin ciki
Saina 6ullo miki yanxu na maqureki da tsotsan wannan munafukin bakin nan naki daya ke cewa wayyo aljanina kaxo gareni naxaqu inganka axuci Amma baki yana cewa dan Allah karabu dani
Hakane ko ba haka bah. Yafa'da tasan tabashi amsa
LABEEBAH takalli Su XARAH da suka xuba mata na mujiya (ido) ta marairaice Tace ba haka bane fah😳
_ba haka bane fah_
Ya maimaita mata furucin nata da cewa xaki fa'damin gaskiya ko saina 6ullo yanxu.......

Tayi saurin cewa hakane da fashemai da kuka Yace ya salam
Cikin shashsheqa Tace dan Allah karka 6ullo nayi shuru
Yace ai ina kallanki goge hawayan ko na goge miki
Da sauri tagoge hawayan Tace toh nagoge
Yace nayi missing 'dinki babyna xanji da'din ganinki gobe
Tace a ina xaka ganni
Yace ba naja xakuxo abuja bah
LABEEBAH tawaro ido Tace harcan xaka Bini
Yace mexai hanani binki Bayan mu iska kawai muke Bi. Kanki qifta ido munje bangwan duniya fah😝

LABEEBAH tajah numfashi. Tace hmm ina sanka
Yace nasani Babyna kici gaba da suna kinji
Ta 'dagamai kai kamar yana gabanta Tace toh

Kiss💋 ya sakar mata tare da kashe wayan
Marwan Yace naga alamar kanajin da'din jin kukan Auntyna
KAMAL Yace haka take
Sam in batayi bah. hankalinta baya kwantawa
Amma kukan yana tafarfasa xuciyata

Marwan Yace toh kadena sata mana
Yace ko ban sata

Please Login or Register in order to submit comment