Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani abun mamaki
Dan kamar ancema Sarki kalli can......
Aiko yaga mutum gefan ruwa ya kunbura.
Cikin tashin hankaliy yayi kan wannan mutumin
Fadawansa sukace Allah ya temake ka karka ta6ashi
Baibi tatasuba ya ta6a wannan bawan Allah
Yace maxa kukai min shi gida
Nan suka bi umarninshi suka kai wannan bawan Allah gida
Yakira masu maganin gargajiya sukayi aune aunansu
Nan suka gano mutumin bai mutu bah
Dan haka xa'a xuqe ruwan daya Sha acire harsashin jikinsa aga abin Allah xaiyi yi akansa
Sarki Yace toh akaisa asibiti
Nan aka kaisa asibiti sukayi gwaje gwajansu yanuna musu dagaske da ransa kuma sunxuqe ruwan daya Sha. Saidai yasami buguwa a akan Wanda idan ya dawo hayyacinsa baxai iya tuna Komai arayuwarsa bah
Saidai yasan rayuwar daxai fuskanta nan gabah
Iya tashin hankali da tausayin wannan bawan Allah Sarki ya shiga
A'kalla wannan bawan Allan ya kai wata biyu kafin ya dawo hayyacinsa

Ahaka Sarki yaxage ya nunama wannan bawan Allan rayuwa
Ya tsaidashi akan ibada tare da koya mishi sanin Allah da ladabi da sanin rayuwa ya take. Sannan ya ra'da mishi Suna Shamsu

Toh Alhamdulillah ya kasance yanda sarkin yakeso
Saidai Sarki yayi Abu 'daya
Shine iyalansa kawai ya ya fa'dama tsintar Shamsu yayi
Amma banda mutanan gari
Dan yajah kunnan fadawansa Yace bayaso jama'ar gari Susan tsintar shi yayi


Toh shidai Shamsu bai cika magana bah
Dan inkaga yana magana toko da Sarki ne
Shiyasa jama'ar gari suke fa'din Sarki ya samu wani miskilin mutum Sam baya wul'da da Mutane kuma idan xaka kashe ka binne agabansa baxai 'daga kai ya kalleba bare Yace ga abinda yagani

Abokinsa 'daya ne Marwan 'dan qanwar Sarki
Dashi kadai Shamsu yake ma'amala

Wannan shine labarin wa'yan nan mutanan

********
'Daya daga cikin fadawan Sarki Yace Allah ya qarama nisan kwana naga kashiga tunani
Sarki ya numfasa Yace
Naxa'ku Shamsu ya dawo tunaninsa isan Waye shi daga wata qasa ya fitoh 'dan Waye shi
Duk fadawan suka ha'da baki wajan cewa Allah xai dawo mishi da tunaninsa insha Allah cikin lokaci qanqani

Sarki yajah numfashi Yace toh Allah yasa
Amma inasan amana shirin Komai gobe
dan jibe inasan muje 'kasar India aduba min shi
Ni dashi da Marwan
Sukace angama ranka ya da'de

Sarki ya 'daga wayarshi ya kira Shamsu Yace kafara shiri dan xamuyi tafiya xuwa India jibi
Shamsu Yace toh Allah ya kaimu

Wannan kenan


.
[6:37PM, 10/10/2016] Rahamat Nalele💋: Gida Nigeria
XARAH kuka take ba nawasa ba.
LABEEBAH ko bata farka bah

Iya damuwa Momy da Dady sunshiga damuwa da tashin hankali
Dan Dr Aryan ya tabbatar musu da cewa akwai abinda ya gani ko yaji Wanda yasa hankalinsa tashi
Sai kuma baqin ciki yayi saurin caf kar xuciyarsa
Yanxu haka ma yana qara shiga irin wannan halin xuciyarsa bugawa xatayi kuma sun rasashi kenan

Me yaji haka Wanda yaja mishi wannan matsalar
Meya gani wanda ya tarwatsa tunaninshi yasashi cikin wannan matsalar
Tambayar da Momy da Dady sukema xuciyoyinsu kenan

Hawaye baibar xuba a ida nuwansu bah
Tunsninsu sun rasa KAMAL
suka rasa YUSUF basusan ya xasuyi bah

Washe gari LABEEBAH tafarfa'do
Aiko tatashi da kuka macin rai
Ganin YUSUF akwance kamar gawa
Kukanta ya qara qaruwa Tace har yaushe Xanyi farin ciki ni LABEEBAH
Har yaushe xan dena shiga tashin hankali
Narasa KAMAL gashi kaima kanasan barina
Na roqeka da Allah YUSUF karka tafi kabarni dan Allah. Ina sanka ina qaunarka.....
Sai taqara rushewa

Momy taji tausayinta Amma tafijin tausayin kansu ita da Dady
Su Sagna ma binta da kukan suke
XARAH ko wani haushin LABEEBAH ne ya kamata. Gani take akwai wani abunda tama YUSUF shiyasa ya kirata awaya
Tayi kwafah tana addu'ar yasa ya tashi suji gaskiyar me yajefashi cikin wannan halin
Ta 'dau al'kawari in har LABEEBAH ce sanadi Wlhi saita gane kuranta



Lamarin YUSUF yaqi xuwa musu yanda sukeso
Dan yau kwananshi biyu baisan aduniyar da yake ciki ba
Dady ya shirya musu tafiya xuwa india dan su duba mishi YUSUF 'dinsa
Gani yake Su doctor Aryan basu San aikinsu bah. Basa ma wani 'ko'kari

Tafiyar takama da XARAH da LABEEBAH sai Dadyn da Momy da Salim.

Washe gari ko suka 'dauka xuwa qasar India
Xuwansu asibitin yaxo dai-dai da xuwan Su Sarki da Shamsu da Marwan

Allah ko ya dubesu sun samu yanda suke so dan kwana 'daya YUSUF yayi ahannun manyan doctors 'din aka sami kanshi. Dan sun bada tabbacin xuwa yau da yamma xai farfa'do ko dare


~*MASEEFAR SOO*~

Can 6angaran da Sarki suke ko. Bayan doctoh yayima Shamsu wata allura nan yafara binciken kwakwal warshi
Sanda ya gama tsaf yafitoh daga 'dakin yayi office 'dinshi

Kallan doctoh Sarkin yayi Yace Dr is dia notin could b done
Dr ya numfasa Yace this problem has 2 be followed according 2 my prescription.else d problem may deteriorated,or better still com wit sum1 he might recognized,dat may help alot in regaining back his memory,
Sarkin yayi shuru. Toh a ina xaiga wanda yasani bare har tunanin nashi ya dawo.
Allah yasan dasu
Haka sukayima doctor sallama sukayi masau kinsu
Marwan ne ya tsaya jiran tashin Shamsu
Amma me baccine mai qarfi ya 'dauke Marwan
Yayinda Shamsu ya farfa'do
Ya da'de xaune kafin ya tashi yayo harabar Asibityn yana naxarin wajan

.
[8:55PM, 10/10/2016] Rahamat Nalele💋: Lokacin yayi dai-dai da farkawar YUSUF
Wata nurse ta shigo ganinsa ya farka tayi Murmushi tafita da sauri xuwa wani 'daki tana addu'ar Allah yasa 'yan uwanshi sun idar da ibadunsu (Sallah) tabasu labarin farkawar tashi.

YUSUF ko takura kansa da tunani yayi akan me ya kawoshi asibiti
Aiko saurin dafe xuciyarshi yayi dan xafin data mishi saka makwan tuna komai da yayi
Hawaye ya xubu mishi.

A hankali ya kai kalansa window.....
Aiko wayo😳 idansa yayi ya tashi agigice tare da tsinke igiyoyin da aka mammaqala mishi
Yaqara bu'de idanshi da kyau.

Nima Rahamat maida hankalina nayi da kyau agun inda YUSUF yake kallo Wanda kallan ya gigitashi haka harya sashi dawoma da kansa ciwa baya
Nidai Shamsun Sarki nagani ya na'de hannunshi yana kallan farfajiyar asibitin

Aiko sai ganin YUSUF nayi ya fita da sauri jini na fito mishi ta hanci yaje ya ta6a Shamsu
Nan ya juyo da kallansa ga YUSUF
Cikin in ina YUSUF Yace YA KAMAL......

Cikin wani yanayi Shamsu ya fara nunashi da yatsa lokaci 'daya kuma yayi saurin riqe kansa danjin yanda yake juya mishi yafara yin kalar hajijiya nan yafa'di sumamme

YUSUF ya dafe bango jini yana fitoh mishi ta hanci ta baki
ya fara lumshe ido yana jah da baya hannunshi dafe a qirjinsa
Sai gani nayi shima ya xube qasa

Kan nayi wani kyakkyawan motsi sai ganin docton daya duba Shamsu nayi yafitoh daga office 'dinsa idansa ko ya sauka akan Shamsu da YUSUF
Nan cikin gigicewa yakira norse suka shiga da Shamsu 'dakin da yafitoh
Kana doctor 'din ya fara Tambayar daga wane 'daki YUSUF ya fitoh
Wata nouse tanumai dan taga fitowar shi YUSUF 'din
Nan shima aka maidashi 'dakin daya fitoh da fara bashi temakwan gaggawa

Shamsu ma shima doctor tsayawa yayi akansa yana duba shi da tunanin me yasashi sumewa haka
Kuma yaga kama tsakaninshi da wancan yaran
Murmushi doctor 'din yayi dan wani tunani daya cafki kwakwalwar shi yanxu
nan yafara addu'ar Allah yasa 'dan uwansa ne shi kenan tunaninsa ya dawo


Cikin farin ciki Momy XARAH LABEEBAH suka nufo 'dakin da YUSUF yake
Wasu Norse suka tsai dasu suna mai CE musu doctors na ciki Suna dubashi
Momy Tace ina ya farfa'do sukace eh dan Yar ya fitoh Amma asume aka ganshi
Hankalinsu ya da'da tashi

Can doctors 'din suka fitoh sunama su Norse din maseefa akan me xasu barshi ya fita sukace suma doctor shankar ne ya kirasu basusan ya fitoh bah.

Maida hankalinsu sukayi gasu Momy Suna basu hakuri da cewa xai qara far mfa'dowa xuwa tara na dare
Ananne hankalinsu ya 'dan kwanta


Sai qarfe goma YUSUF ya qara farfa'dowa
Aiko yasauke idanshi akan LABEEBAH da XARAH
Aiko sukayi kansa da murna
XARAH na fa'din dama nasan baxaka mutu kabarni bah
LABEEBAH Tace Alhamdulillah nagode Allah daya tashi kafa'darka

Kallan window yayi koxai qara ganin Shamsu Wanda ya kira da KAMAL sai yaga Momy da Dadyn da Salim ne Suke magana cikin damuwa
Ya dawo da kallansa ga matan nasa yana hawaye
Ya tsaida idanshi akan LABEEBAH Yace insha Allah xakiji da'di arayuwarki fiye da kowa
Xaki sami farinci fiye da tunaninki
Sannan ina rokwan Allah yasa kixama matata agidan aljanna

Na ganshi da idona LABEEBAH Wlhi shine shine
ko kaffara baxan yiba shine shine
Dama dashi kika dace ba daniba
Nasani xai baki kulawa fiye da wacce nashirya baki
Kimin alqawarin baxaki Auri kowa bah sai Ya KAMAL......

LABEEBAH tashare hawaye Tace kana cikin xafin ciwone MeeNi
shiyasa fa'din wa'yannan kalmomin.
Ya YUSUF Wanda ya mutu baya dawowa
Kadena maganar banaso....
Ina maka addu'ar tashi inbaka ice-cream me da'di mugina rayuwa me da'di.
Sannan na maka alqawarin faranta maka har qarshen rayuwarka

Yayi Murmushi da kama hannunta yayi mata kiss cikin xubar hawaye
Yace ina sanki
Ta shere mai hawayansa Tace nima ina sanka
Sai suka fashe da kuka atare
Cikin sanyin murya Yace ke👈🏻
kidena kuka bayan ina tare dake.
Ta girgixa kai Tace kaima kai👈🏻
kadena kuka Bayan ina ina tare dakai
Ya qara xubo da hawaye Yace xakisha ice-cream
Ta'daga mai kai Tace eh inhar kai xakaban...............

XARAH Tace YUSUF baka ganni bane.....
Ya juyo gareta ahankali Yace aduniya ba wacce na tsana sama dake XARAH
Naji Komai agun Jameel
XARAH kin tucemu
Kin tarwa mana farin cikin mu kin hanamu fuskantar rayuwa mekyau
Amma Karki damu kije duniya CE. na sakeki saki uku Allah ya Isa tsakanina dake
Sai dai kinsami galaba akaina Amma baki sami galabah akan abinda ki kayi a baya bah.

Araxane XARAH Tatashi hankalinta yayi mummunan tashi tafashe da kuka......

Momy da Dady Salim ne suka shigo
Ganin YUSUF ya farka yasasu qarasawa gareshi da sauri Suna hawayan farin ciki
Yace ina sanku iyayena Amma dole kuyi hakuri dani dan baxan qara rayuwar daku kuke so bah
Lokacin daxan tafi lokacin Allah ya dubeku ya dawo muku da Ya KAMAL
Cikin sarewa Dady Yace kadena fa'din haka Wanda ya mutu baya dawowa YUSUF
ko kana cikin xafin ciwone
Ya girgixa kai da maida kallinsa kan LABEEBAH Yace ina sanki matata kuma Karki manta alqawarin da nace kiyimin idan Ya KAMAL ya baiyana agareki Ki Aureshi

Sannan yajah numfashi yaci gaba da cewa.

Ga amanar LABEEBAH nabaki Momy dan Allah Ki 'dauketa kamarni
Kidinga kallanta kamar ni
Ki sota fiye dani

Dady kasa ran ganin Ya KAMAL
Idan Sadeeq da Aliyu sun girma kafa'da musu ina musu fatan alkarri......
Yana fa'din haka yayi kalmar shahada tare da kallan sama hannunshi na cikin na LABEEBAH

Me kenan 😳
XARAH ta tsaida kukanta cak
Kowa ya qurama YUSUF ido jikinsu asanyaye
Tsoro ya kamasu
Da sauri Salim ya damqi hannun YUSUF 'din...........
Hankali tashe




Ya 'daga hannun. Nan yaji hannun yasake
Alamar rai yayi halinsa
Momy na miqewa taxube qasa sumammiya
Dady ya dafe girji yasaki wani qaramin kuka mara sauti
LABEEBAH tashi tayi tana girgixa kai Tace ina ba mutuwa yayi ba.
Kar kamin haka dan Allah. Dama maganar da kake min wasiyace
Nan tafarajah da baya sai ganinta sukayi qasa tasume

XARAH taje ahankali takama hannun YUSUF ta'daga. Yanda ta'daga haka tasauke
Aiko ta kwalla wata furgitacciyar qara taxube qasa itama sumammiya
Qarar da tayi ita janyo hankalin ma'akatan asibitin sukayo 'dakin da sauri


Nan ko Doctors suka fara aikinsu nasan cetoh rayuwar LABEEBAH Momy XARAH

Momy dai tasamu kanta daqer
Haka XARAH
Saidai lamarin LABEEBAH sai ahankali
Dan taqi farfa'dowa


Acan 'dakin su Shamsu ko. Doctor ya gama bashi temakwan daya dace
Ya kalli Marwan daya ke ta shaqar Baccin Sa hankali kwance
sai yayi Murmushi yakira wata Norse Yace takula da shi dan xai iya samun kansa akowane lokaci Tace toh.

Sai Washe gari kusan bakwai LABEEBAH ta farfa'do
Kuma kunsan bakinta ba shuru xaiyiba haka idanta ba dena xubar hawaye xaiyi bah awannan lokacin

Haka suka tafi da gawar YUSUF masaukinsu da niyar gobe sutawo gida Nigeria

Wani ikwan Allah sanda doctorn daya duba Shamsu yaxo Washe gari Sannan Shamsu ya dawo tunaninsa

Yayi shuru yana bin Sarki da Marwan da doctorn da kallo
Can cikin sanyin murya Yace nan inane
Da sauri sauki ya 'daga hannu yayi godiya ga Allah daya dawo da tunanin Shamsu
Sannan ya kallesa Yace da farko dai me sunanka awane qasa kake
me kuma ya kaika cikin ruwa da harsashi biyu a jikinka.
Sarki yafa'di hakan cikin xakuwa dasan jin kalmomin Shamsu

Shuru yayi kwakwal warshi ta'dau aiki nan ya tuno da kansa
Ya tashi ya jinjina jikin gadan da yake
Yace a Nigeria nake garin Abujah
sunana MALUDDEEN
Abinda yakaini ruwa ko shine. Ni marayane. Allah ya albarkaceni da arxiqi me tarin yawa Kasan cewata doctor
Ranar xanje garin Kano muka ha'du da 'yan fashi. Toh garin guje musu ne nida abokina mukayi daji
Anan suka sami galabar harbin mu. Daga lokacin bansan meya qara faruwa ba.
MALUDDEEN ya qara she xancan nasa da Tambayar tsawan wane lokaci ya 'dauka a hannun Sarkin

Nan shima Sarki ya gabatar mishi kansa da bashi labarin Komai na yanda ya sameshi cikin ruwa.
Kuma da rokwanshi da Allah ya yarda ya xama 'danshi karya guje mishi


MALUDDEEN yayi mamaki mutuqa. Lalle ruwa ba inda baxai kai mutum bah.
Ban da ikwan Allah ya akayi yaje har qasar Armiyaniya

Ya kalli Sarki da Murmushi Yace karka damu har yanxu kai BABANA ne
Koda xan barka bayanxu bah

Doctor yayi Murmushi Yace naga wani me kama dakai a cikin asibitin nan namu
Kuma abin mamaki kamar shi yasa tunaninka dawowa
MALUDDEEN Yace Kasan haka yana faruwa arayuwa kasami mutum me kamarka.
Ya fa'di hakan da San kaucema xancan nashi
Shima Doctorn bai matsa masa bah Yace haka ne

( _Ni ko Rahamat qurama MALUDDEEN ido nayi na shagaltu da kallan sosai_
_me kyau ne_
_Me haske ne irin na nafiyayyun mutanannan_
_Ga wayewa da nutsuwa. Komai dai yayi agareshi. duk da ance 'dan adam Tara yake bai cika gama ba. Toh nidai MALUDDEEN ya kai 'dari 💯 cif_
_Amma saidai yana yimin kama da wani. Ko waye 🤔. Dole in gano_
Sarki Yace yanxu miye burinka arayuwa
MALUDDEEN yajah numfashi Yace yanxu dai inasan aikina ya dawo min
Sarki yace inhar kanasan komawa aikinka toh saidai da takaddunka.
Yace Hakkane Amma tunda nadawo nutsuwata wannan baxai kasance matsala xansan yanda xanyi
Sarki Yace karka damu dan nima nayi wani yanxu. Fatan mu kawai Allah yasa muje gida lafiya
Marwan Yace AmEEn



Su momy ko kwana 'daya suka qara suka duro gida Nigeria
Annan koke koke ya 6arke na rashin YUSUF da sukayi

Kakah ta gigice da lamarin itada qanin Dady Alhaji Nasir
Haka Su Ya Usman da Su innah
(Toya xasuyi muma jiranta mukeyi)




Anawa ganin XARAH tafi kowa shiga tashin hankali na mutuwar YUSUF
Dan yau akayi arba'in duk da mutuwar tadawowa kowa sabuwa.
Amma yanda XARAH tanuna damuwarta saida kowa ya tausaya mata

Wata sabowar rayuwa suka farayi LABEEBAH da XARAH
Sam LABEEBAH ta canja ma XARAH
Bata shiga harkarta
Idan kaga LABEEBAH na Murmushi toko da Rukayya ne ko Sumayya ko Innah da yayanta Usman
Abin ya dami XARAH sosai dan bataso agane yanxu basa jituwa
Wani tunani tayi Wanda take ganin in tabi LABEEBAH xata sauko mata kamar yanda suke



.
[2:25PM, 12/10/2016] Rahamat Nalele💋: A qasar Armiyaniya ko kamar yanda shashin MALUDDEEN yake daban. Yanxu ko saiqarama shashin nasa armashi da Sarki yasa ayi.

Rana ta biyu da dawowarsu Sarki ya kira MALUDDEEN Yake shaida mishi yanada wani company a England cikin garin Dubai wanda suka qirqiri Sim na waya.
Ya gaya mishi turawa yasa akan harkar saidai yansu da Allah ya kawo mishi shi ya 'dorashi akan harkar. Dan yana San ya xama sugabansu
Marwan xai nuna mishi Komai akan harkar

MALUDDEEN yajah numfashi Yace BABAH kenan kana ganin xan iya wannan har kar
Yace mai xai hana kaidai banaso kayimin musu.
MALUDDEEN yayi Murmushi Yace toh Allah ya shige mana gaba

Yafitoh daga gun Sarkin kenan suka ha'du da KHADIJA
Tace Ya Shamsu
Harya wacce tah. Ya 'dan dawo ka'dan fuskarshi ba yabo ba fallasa Yace MALUDDEEN dai ko
Tace toh aini da ya Shamsu na sanka. Taqarashe da 'dan shagwa6a
Yayi Murmushi ka'dan dan ganin yanda tayi maganar. Ta tuno mishi da wata babyn shi.
Yace indai agidan nan kike kuma Kinsan da xamana nasan Kinsan da 'daukewar tunanina.
Tace eh nasani
Yace toh yanxu Allah ya dawowamin dashi ba Shamsu nake bah MALUDDEEN nake
Yana fa'din haka ya wucceta
Yayinda tabishi da kallo
Tafiya yake Cikin nutsuwa qamshinsa me narkar da xuciya itadai tunda taganshi a gidansu take sanshi


Shiko shashinsa ya koma anan ya tarar da Halima. Ya kalleta da mamaki
Amma dake 'dan iya wane sai ya shareta Yana niyar barin falan Tace dan Allah Ya Shamsu katsaya
Ya salam MALUDDEEN Yace
Tace dama nasami labarin dawowarka ne shine naxo immaka barka da dawowar tunaninka
Yace Sunana MALUDDEEN ba Shamsu bah. Plx Ki kiyaye hakan
Kuma Nagode da kulawarki.
Kantayi magana saiga Marwan yashigo Yace ansami me xanan 'dan uwana
Yace gud aikinka yayi kyau kace ya shigo mana
Nan wani me xane ya shigo
Aiko MALUDDEEN yaxauna yadinga suffantu mishi kamannin yarinyar daya kesan a xana mishi

Xuciyarshi cika tayi da murna fam lokacin dame xalan ya gama
Yace kayimin abunda yafi Komai yimin da'dai aduniya.
Ya maida kallanshi ga Marwan Yace abashi kyautar da xata gigitashi
Yace angama "dan uwana
Halima Tace Ya MALUDDEEN wannan 'din wacece ita
Ya kalleta da Murmushi ya nuna xalin da hannunshi Yace xaki Santa
Tace yanxu fah
Yace bani da lokaci
Tace Amma Naji haushinta dan da alama tatatafi da tunaninka
'Daure fuska yayi ya tashi da 'daukar xanan hotan LABEEBAH dani Rahamat nagani yayi bet room 'dinsa.
Halima tasake baki galala
Tasani tana MASEEFAR sanshi shiyasa taji tsanar wannan yarinyar da aka xana mishi ita. Tajah tsaki tabar falan da Takaici

Sati biyu da faruwan hakan MALUDDEEN ya gane sababbin qannan nasa sun kamu da MASEEFAR SON shi
Amma saiya dinga basarwa yaqi basu damar da xasu fito da maitarsu
Iyayan nasu matan sunsan da haka
Kuma kowacce tayarda da 'yartata taxama mata ga MALUDDEEN

MALUDDEEN yanxu haka yana qasar Dubai inda aka 'dorashi akan harkar kasuwancin memartaba Sarki Azeed

Dake shi MALUDDEEN wayayyene kuma me ilimi da kuma aiki dashi nan yagane kasuwancin nasu.
Shida Marwan ne jagaban kasuwancin
Allah ya 'dora MALUDDEEN akan turawan companyn sanshi suke kamar me
Dan baya nuna musu gadarar shine shugaba shidai barshi da muskilancinsa


Yana xaune a qayataccan office 'din nasa. Ya xubama hoton LABEEBAH ido ko qif tawa baya yi Marwan ya shigo cikin shigar ma'aikata
Yace 'dan uwana ga mutanan sunxo.
Kan yayi magana saiga wasu mutane su shidda kallo 'daya xaka musu gano su black American ne
Amma sun watatu da ilimi sosai.

MALUDDEEN ya kallesu ka'dan sukace barka dai me gida
Da mamaki MALUDDEEN ya kalli Marwan dan jin sunyi mishi magana da hausa Yace ya sukejin yaranmu
Marwan yayi Murmushi Yace ai musulmai ne. Kuma sunsan HAUSA fiye da tunaninka
Yace gud da nuna musu hotan LABEEBAH Yace tana Nigeria cikin garin kano unguwar kurna inasan in dinga sanin duk wani mutsinta banaso inyi missing 'din komai nata
'Daya daga cikinsu Yace Koda wanka ta shiga tanayi
Ya girgixa kai Yace shine abunda banasan gani
Sukace angama ranka ya da'de
Yayi Murmushi Yace shine abunda xai sani farin ciki
Kufara da bincikomin tariyin rayuwarta Sannan daganan ina so yaxama kamar a gabana take rayuwa
Suka ha'da baki wannan cewa karka damu oga Komai xaixu maka yanda kakeso
Yace nagode
Yana fa'din haka suka fitta
Marwan yayi Murmushi shidai yana bala'in San MALUDDEEN yana qaunarshi sosai
Kuma yana addu'ar Allah yasa shima ya soshi kamar yanda yake sanshi.


Gida Nigeria
Yau gidan nasu LABEEBAH ba kowa Aunty Rukayya taje sunan qanwarta
Sumayya ko tana islamiya
Haka Innah ma batanan yanda Sumayya ta fa'dama LABEEBAH wai taje gidan rasuwa tun safe
Gidan ya rage daga LABEEBAH sai SAUBAN 'dinta
Shima bata da'de da 'dauko daga skull bah

dake ya fara xuwa har islamiya
LABEEBAH CE me xuwa kaishi. In lokacin tashinsu yayi taje ta'dauko shi.
Haka islamiya mah
Momy tasa mammishi direba dan ya dinga kaishi yana dawowa dashi
Amma LABEEBAH Tace ita xata dinga yi
Haka Momy tabarta badan tasoba

Da gaske SAUBAN bai 'dauki kowa da mahimmanci arayuwarshi bah kamar LABEEBAH. Ita yake gani uwarsa yanasan LABEEBAH Sosai kamar yanda itama take qaunarsa

XARAH CE tashigo gidan da sallama.
Batare da LABEEBAH ta kalleta bah ta amsa sallamartata
XARAH taxaune gefan taburmar jiki asanyaye
Tace nasan da ciwo kimanta abinda namiki.
Nayi nadama LABEEBAH
Wlhi sharrin she'danne yasani aikata miki Komai
Nikaina nayi mamakin kaina
Duk abinda na miki Wlhi da qaunarki acikin xuciyata.
Dan Allah kiya femin
Na roqeki. Na miki alqawarin hakan baxata qara faruwa bah
Plx mudawo yanda muke da dan narasa duk wani farin cikina
Ke ka'dai kika ragemin plx Karki juyamin baya Wlhi ina sanki
Saita fashe da kuka

LABEEBAH tayi shuru tana tuna abinda tayi mata gidan YUSUF.
Dake xuciyarta atsarkake take saitaji tausayinta ya kamata

Cikin xubar da hawaye Tace nayi mamakinki XARAH
Kinyi min abinda banyi xatoba. Kuma banyi tunaniba
Nice na rasa duk wani farin cikina bake bah
Ba Uwa ba ubah
Ba masoyin da xuciyata tafara so
Ba wanda ya kasance Miji agareni
Sannan bake danake matuqar qauna
Haka rayuwa take XARAH.
Hmmm. Har yanxu ina qaunarki
Saidai baxan iya sakewa dakeba
Dan kin tsoratar dani yarda da kowa
Wlhi tsoran mutum nake yanxu.
Dama KAMAL ya ta6a gayamin karna yarda da kowa ciki ko harda ke
Naso na 'dauki xan cansa Amma daga baya na watsar da xancan saboda na duba qaunar da mukema juna
Ashe ko xanyi nadamar bujirema wannan umarnin nashi

Na yafe miki XARAH
Ya kuma rage naki yanxu kiyi abinda xan qara yarda dake
Tana gama fa'din haka ta jawo SAUBAN jikinta ta rungumeshi wanda ya fara bacci hawaye na xubo mata. Taci gaba da cewa
KAMAL 'dinki shine KAMAL 'din da xuciyata tarayu da sanshi da qaunarsa
Na soshi na qaunaceshi kuma har abada baxan so wani kamarsa bah
Duk yanda nasan xanyi dan karki sani sanda nayi
Saboda banasan 6araka ta shiga tsakanina dake
Banasan cin amanarki Amma ke sanda kikaci tawa
Dan Allah na roqeki kar wata xuciyar ta raya miki kirabani da SAUBAN......
Idan kikayi haka agareni shine abinda baxan iya yafe miki bah
Dan natabbata baxan iya rayuwa bah
Ina kallanshi tamkar mahaifinsa
Dan Allah Karki rabani dashi na roqeki saita fashe da kuka me sauti. Tare da qara qanqame SAUBAN tamkar XARAH tace xata kwaceshi alokacin.



Tashi XARAH tayi tana kuka wannan Karan ba kukan munafunci takeba kukan gaskiya takeyi
Tayi Allah wadai da rayuwarta saiyanxu ta tuna wacece LABEEBAH. Da rayuwar da sukayi
Da kuka tafita daga gidan


Akan gadan Innah tafa'da tayi kuka tayi kuka har tagaji. Daga bisani takira number Hajjiya Turai Tace nayi nadamar abinda nayima LABEEBAH
Tace kai habah tunyanxu
XARAH ta goge hawaye Tace eh nayi dana sani
Tace ke da Allah share kinyi abunda ya dacene
Kinbi San xuciyarki kuma ba lefi bane plx kar xuciyarki ta karaya
Ki share kawai.
Dan yanxu rayuwar haka take. Kowa kansa yasani.
Shuru XARAH tayi tana San yarda da xancan Turai kuma tana tunanin karta yarda da hakan
Ganin tayi shuru yasa Turai cigaba da cewa
Wlhi kina Ganin LABEEBAN nan munafukace ta'iya munafunci
Saita dingayin kalar sanyi da tausayi nanko bom CE
Kema dan Allah yana sallakar dakene akan makircinta shiyasa baki ta6a fa'dawa tarkwanta bah
Dake xuciyar XARAH batayi nisa a nadamar tataba sai xancikar Turai yafara tasiri akanta nan ta watsar da lamarin da yanxu ya faru ita da LABEEBAH
Amma duk da haka tasa aranta baxata qara cutar da ita bah dan tagaske soyayyarta ta'dan motsa mata yanxu
Sanda Turai tagama cusa mata ra'ayin tsiya Sannan sukayi sallama



Dubai 🌌
MALUDDEEN ne xaune ya yana duba wasu takaddu
Saiga 'daya daga cikin wa'yanda ya tura Nigeria ya shigo da wata baqal Leda ya dire a gabansa cikin girmamawa Yace oga bin cike ya nuna mana
Sunan yarinyar Aisha-Labibah tana da qawa ko 'Yar uwace Fatima-zarah
Tare suka tashi da San junansu yayinda Fatima-zarah tayi wani saurayi KAMAL saidai Aisha-Labibah tagamo da sanshi wannan KAMAL 'din
Bai baisani bah har ya auri

Please Login or Register in order to submit comment