Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kanka mana ko bakwan kane yanxu gidan
Yakanyi Murmushi Yace hmmm MASIFAR SON da nakema XARAH bata kai nan ba nutsuwata.
kema kyayimin fa'da haka kawai nashiga ga sirikata
Ko kin manta yanxu innah suruka tace

LABEEBAH takanyi shuru dan yanxu YUSUF ya canja mata gani takeyi ya dena Santa XARAH ya keso. Hakanko yana sawa taqara jin haushin ~*XARAH*~










*Bayan shekara biyu da watanni*

Haka rayuwar tasu taketa tafiya yau taxo ma LABEEBAH da da'di gobe kuma 6anin haka. ga kowa mah aduniya rayuwar da yakeyi kenan .

XARAH ko sai abinda yaci gabah ita da Hajjiya Turai.

Inda ita Turai 'din tafara nunama XARAH toh fah lokaci yayi daxaki fara aiki da maka manki XARAH

XARAH ta girgixa qafah Tace tunda na yayaye SAUBAN bah

Turai Tace madallah kinga yanda kike kuwa. Wlhi kamar bakiyi Aure kin haife SAUBAN bah

Kinga kayan nan maganin matane na haqiqa na mallaka awajan wani hamshaqin malami na kar6o dan kaf magungunansa bana banxa duk tsiyar namiji ya kusan ceki ya rufe shafin wata mace kenan.
Wlhi ina tabbatar miki idan kikayi amfani da wa'yan nan narantse miki YUSUF baxai kalli LABEEBAH ba
Dan kin tarwatsa soyayyarta axuciyarsa har abada
Musumman inya kusanceta kin san Allah yabar kusantar kowace 'ya mace aduniya in ba kebah
Ace shi mebin matane to daga ranar ya barsu har abada
Dan kallansu xaiyi tamkar maxa 'yan uwansa

*XARAH tasheqe da wata shegiyar dariya suka tafah*
*Tace an gaya miki ni wawiya ce da xan bari YUSUF yasan LABEEBAH.*
*inaaaaaaa.*
*ta girgixa kai*
*Taqarashe da cewa Wlhi Matarsa mah* *Allah ya 'dauketa ne dan in mallakeshi Ni 'daya*

*Kawai xan so ya Aureta ne saboda surutun Mutane karsuga abayi mata adalci bah*

*Idan muka kasance matansa ko tayayane saina rabata dashi ita dashi saidai ido👀*

Kinga idan na 'dan 'dana mata axabar sanshi datayi saina San yanda Xanyi insashi ya rabu da ita Jameel ya Aureta Kinsan wannan yana cikin game 'dinmu nida shi.
Turai ta waro 😳 Tace kin Allah na manta dashi
XARAH Tace niko ina xan manta dashi
Turai tajah numfashi Tace danayi wani tunani mexai hana kibarta da Jameel sai musan yanda xamuyi kisami YUSUF ke 'daya
XARAH ta gyara xama Tace har yanxu kin kasa fahimta
Auran LABEEBAH da YUSUF tamkar ba Aure bane
Dan xan bari ta Aure shine saboda mutane
Kuma ba abinda Auranta dashi xai taremin.
Saimani daxan tare mata shi

Ina tabbatar miki kan aje ko ina xata nemi ya saketa
Ni kuma Xanyi ammafani da wannan damar in ingixa xuciyarshi ya rabu da ita Jameel ya samu

Turai ta 'daka mata duka Tace gaskiya XARAH baki da alqawari. Xuciyarki abushe take. Dan imanin naki ya tafi. Ixuwa yanxu har nafara tausayin LABEEBAH Wlhi

Bakiyi halin *Nana Fatima* bah
Macan da babu kamarta aduk duniya
Macen da bata da mugunta macen da.........

XARAH tayi saurin katseta da cewa Allah ya bamu albarkacinta

Eh inada nawa halin Amma kome nayi ke kika 'dorani akan hanya
Amma kinnasan cewa wani......

Turai itama ta katseta da cewa naji abin baikai nan bah koma me kikayi MASEEFAR SONE yaja miki haka

Yanxu saura wata 'daya bikin naku baki ban labarin yanda aka karke da Innah bah
[12:41PM, 06/10/2016] Rahamat Nalele💋: XARAH Tace hmm Wlhi da har nayi tunanin ko Innah ba sona takeba

Turai Tace meyasa
Tace yanda tanuna Allah ya karta ya binne baxan auri YUSUF ba dan na LABEEBAH ne
Baban mu ya biye mata ko
Ita kuma shegiyar taxo tasaka Su agaba da kuka da magiya akan ita taji tagani ya Auremu mu biyu batasan rabuwa da nine
Bu'dar bakin innah Kinsan me tace mata
Turai ta girgixa kai
XARAH taciga da cewa
Cewa tayi wai tarufe mata baki ita bata da hankali
Akanme xata CE YUSUF ya Aure Ni
LABEEBAH tagyara xama tadinga jero mata misalai akan batasan ta rasani kusa da ita muna san junanmu dan Allah tah bari ayi auran

Momyn YUSUF nagun akayi Komai daqer da si'din gashi Innah tayarda

Kinsan Allah agun sanda soyayyar LABEEBAH ta motsamin Santa ya manayemin xuciyata
Amma da YUSUF yakira awaje dan suta6a ta'di nan take tsanarta ta dawomin


Turai tayi dariya da cewa yanxu innah ta yarda kenan
XARAH Tace eh kai ba dole bah
Dan LABEEBAN da Momyn YUSUF ne suka sukata a gabah da magiyar har tayarda
Washe garin ranar iyayan YUSUF suka kawo sadakina.
Toh kinji Komai

Turai Tace toh madallah
Yanxu dai yau xaki fara amfani da magungunan nan
Dama na wata 'daya kinga duk ranar da YUSUF yayi gangancin ta6aki ko uwarsa qarya take ta rabaki da shi






Al'amarin auran nasu yaxo da salo
Yau saura sati 'daya.....☝🏻jal

Amma XARAH ta nunama LABEEBAH karsuyi Komai
Yayinda LABEEBAH Tace ko walima baxa muyi ba
XARAH Tace toh duk yanda kikace haka xa'ayi
LABEEBAH ta girgirxa kai Tace aa karmiyi Komai 'din

Sumayya najinsu
Itadai tarasa dalilin da yasa. Talejin haushin 'Yar Uwar tata XARAH
Gani takeyi ta cutar da LABEEBAH
Akanme xata yarda da ha'din da LABEEBAN tayi bata tirjeba
Sai kawai ta tsinci kanta da jan tsaki
Rukayya tata6e baki
XARAH da LABEEBAH suka bisu da kallo
XARAH takasa hakuri Tace wai meyake damunki ne Sumayya kwana kinnan kin canja daga kijah tsaki saiki dinga hararata
Rukayya Tace qila kinyi abinda bai dace bane
Tace menayi Aunty Rukayya fa'damin
Tashi tayi tana shanya Tace inaxan sani XARAH gaki ga Sumayyan ita xaki tambaya ai
Saitajah tsaki Tace banyi Komai ba. Inadai ganin iskancine kawai yake sata haka
Rukayya tace hmmm ba mamaki


Da yammar ranar ne
Rukayya tayi qoqari wajan tursasa LABEEBAH shan tsumi na mata da abinda baxa'a rasabah
Fa'di take Kinga XARAH tayi Aure tasan me yafi da'di a Aure da abinda yake kawo matsala
Ba xama xatayi YUSUF yajita salam bah
Dan haka kema kidage da shan kayan marmari da wannan tsumin
Toh LABEEBAH Tace mata dan tun safe barartace take mata ciwo ka'dan ka'dan

Abin bai caf keta da kyau bah sai gab magriba
Nan ta nemi sumewa Usman ya furgita dan yasan yanda ciwan nata take
Ya shiga 'dakinsa dan tuna wani magani da wani me magani yabashi Yace insha Allah inya tashi mata tajiqa tasha xata samu lafiya
Cikin sauri Rukayya ta ji'ka maganin suka bata tasha. Nan bacci yayi awan gaba da ita
Bata farkaba sai kusan asubah takoga al'adar

Sumayya tayi mata sannu Tace kina buqatar wani abune
Tace aa
Nan tatashi sai tajita garau sumul
Saidai tana 'danjin ciwan ka'dan
Da tayi karin safe Usman ya qara bata tasha.
Rukayya Sumayya Innah XARAH duk sata sukayi agaba Suna yimata kallan tausani

SAUBAN na maqale da ita fa'di yake cikin gwarancinsa yana cewa me yasameki momyna
Ta shafah kansa Tace bani da lafiya SAUBAN Amma na samu Sauqi
Saiya kwanatar da kansa a qirjinta yayi lamo

Innah taja numfashi da kallan Usman Tace aiko tunda yayi mata magani ka qara kar6o mata ta ajiye saboda wata ranah
Yace akwai da yawa nama bata. dan me maganin baya xama yau yana wannan gari gobe yana wannacan
Innah Tace Allah mah ya rabata dashi gabaki 'daya
AmEEn duk sukace

Da yamma Momy ta aiko wasu attajirai mata da kayan Auran LABEEBAH dana XARAH Komai iri 'daya Kaya masu kyau da inganci da sha'awa



🌵🌵🌹🌹🌵🌵
~*MASEEFAR SOO*~🌹
🌵🌵🌹🌹🌵🌵


Toh yau dai alqawarin ya cika
*An 'daura Auran YUSUF da LABEEBAH & XARAH*

Me xai faru 😳
Bayan Amare sunsha nasiya sunsha kuka

'yan kaisu sun luluqa dasu Abuja inda suka diresu a gidan Momy suka Sha nasiyarta sai suka kwashesu suka kaisu tangamemen gidan inda yaba mutane sha'awa
Dan part 'din XARAH daban na LABEEBAH daban saidai akwai wani falo atsakaninsu Wanda xai sadasu da juna in sunso

Wannan aikin Dadyn YUSUF ne dan shi yasa aka Komai tunda yaji maganar 'dan nasa Su biyu xai aura yasa aka hau gini ahankali har aka gama Komai


Haka Mutane suka musu addu'ar xaman lafiya sukayi gidan Momy acan xasu kwana
[1:28PM, 06/10/2016] Rahamat Nalele💋: YUSUF ko yana tsakiyar abo kana yansa. yayi musu shuru yanajin tsiyar da suke masa yau xai qara angwancewa
Salim 'dan uwansa Yace toh 'dakin waxai fara shiga oho
Yace LABEEBAH bah
'Daya daga cikinsu Yace habah dai kasani tunda akayi maganarka da XARAH batakayi gigin da kasake ha'duwa da itaba ko ka ganta kanta ankare da kai kakeyin fuska
Yace hmm kunga xaku rakani ne ko in tafi da Kaina

Sukace wane mu sai munje munga kwul Uwar dakah


XARAH safa da marwa daketayi cikin bet room 'dinta jiki ya jiqa da magani yana buqatar maxa
Fa'di take aranta Allah yasa yafara shiga gun LABEEBAH yana xuwa gunta ta rufe kofah shikenan baxai koma gun LABEEBAH bah. A sannan in Komai ya wakana ta tarwatsa tsakanishi da LABEEBAH


LABEEBAH ko tsoro ne ya shigeta hankalinta yatashi tasani ba makawa YUSUF agunta xai kwana tana tsoran mexai biyo baya itadai batasan ya abin yake bah Amma acan baya XARAH ta ta6a gaya mata ba da'di har sumewa mutum yake
Dariyace ta kamata data tuna tanamah period me xai mata mah tana cikin jini
Wata xuciyar tace mata ba gobe xaki gama bah
Abayyane Tace ba gama XARAH bah.......

Shugowar YUSUF ne ya katseta da xama kusa da ita Yace iye kaga Uwar gidana
Ta harareshi
Yajawo ta jikinsa Yace yau kin xama tawa nutsuwata. yau xan bu'de miki wata rayuwa. Baxaki qara ciwan marar da kikeyi bah
Shuru tayi mishi
Shima shurun yayi can Yace nabar mutane a Babban falo tashi muje Su muku Nasiha
Ta'dan bugi qirjinsa takai harda kai
'Dago fuskarta yayi yakai bakinsa cikin nata ya hau yimata kiss baji ba gani.....
Can wayarsa tayi qara. Hakan yasashi barinta
tako langwa6emai ajiki
Ya 'dauki wayan idanshi alumshe
Salim Yace xamu tafi kasa in kira XARAH ka kuma shanyamu kamar kayan wanki

Xare LABEEBAH yayi daga jikinsa ya miqe da riqo hannunta Yace muje
Ahaka sukaje har falan hannunshi Cikin nata taxauna kusa da XARAH
Nan abokanaye suka hau addu'o'e dayi musu fatan alkairi dasu xauna lafiya
Sannan suka ajiye musu kaji da madara suka tafi
YUSUF yadawo da kulle falan bayan ya rakasu

XARAH Tatashi tana cema LABEEBAH saida safe
Bata jira cewar LABEEBAN bah tayi part 'dinta YUSUF ya bita da kallo
LABEEBAH ta kalleshi ka'dan ya kashe mata ido 'daya Yace bara inje imma XARAH saida safe sai inxo ko
'daga mai kai tayi
Ya qaraso da saka hannunsa ya shafi fuskarta ka'dan Sannan yayi part 'din XARAH
Ita kuma tayi part 'dinta

.
[2:55PM, 06/10/2016] Rahamat Nalele💋: Abune wannan bai saba dashi bah
Abune Wanda yake tunanin ta ina xai fara yinshi
Shiyasa da ya shiga bet room 'din XARAH ya xauna gyefan gadanta yayi shuru
Itama da take kan gadan shuru tayi xuciyarta nayi mata xafi yanda 'daxo yaje ya da'de a 'dakin LABEEBAH Uwar me ya tsayayi

Can dataga shurun yayi yawa saita fashe mai da kuka wiwi
Hankalin YUSUF yatashi sai yarasa yama xaiyi da ita
Yasani in LABEEBAH namai kuka saurin ha'data yakeyi da jikinsa nan xata mishi shuru
Amma XARAH dako hannunta bai ta6a riqewa ba ya xai mata
Tashi yayi yadafe kansa Yace kiyi shuru dan Allah
Aiko taqara rushewa da kuka.......

Shikansa tsintar kansa yayi agabanta ya rungumeta still bata dena kukan bah
Ciro hankicif 'dinsa yayi yana gige mata hawayan
Yace plx XARAH kiyi shuru meya faru Tace meyasa baka sonah
Jin Kalmar yayi tamkar saukar aradu da kah
Yace ina sanki mana Tace ban yarda bah dan kafisan LABEEBAH dani
Shuru YUSUF yayi yarasa me xaice mata
Itako taxare jikinta daga nasa taci gaba da kukanta
Yaqara dafe kansa yana kiran sunan Allah Yace yanxu me kikeso na miki na nuna miki ina sanki
Tace sonake ka kwana anan dan ina bala'in furgita inna kwana ni 'daya ni bakamar LABEEBAH bace da bani tsoro
Da sauri ya kalleta kana yajah numfashi yayi shuru kawai yana kallan qasa
Can Yace toh bari nafa'dama LABEEBAN saina dawo
Matsowa jikinsa tayi tashige mishi ta fara kuka tana cewa Wlhi LABEEBAH ba Komai xatace bah tasan halin tsorona plx karka futa in ka fita sumewa xanyi dan hakama 'daxo naga kamar mciji ya wucce
Shuru YUSUF yayi danjin wani furgitatcan qamshi dayake shaqa daga gareta wanda yasa yafarajin kanka na juyewa wani maseefaffan filing na na sha'awa na kusantoshi.
Sai tsintar kanshi yayi da rungumarta yafara kissing 'dinta tako ta ina
Sanda ya samu nutsuwa na kiss 'din Sannan ya rabata da jikinsa yayi toilet dayin wanka da alwala
Bayan yafitoh Yace itama taje tayi
Kafin ta fito ya canja Kaya
Dake tunkan suxo tayi wanka sai kawai ta'dauro alqala suka hau lafula raka'a biyu dayin Addu'a Sannan ya 'dauko mata kaxarta da madara yasa a gaba sukaci ka'dan yanata mamakin kansa da ita.
Bayan sun gama XARAH tayi gado
Ba wani nuqu nuqu YUSUF yabita

Ya rabata da Komai nata ya hau sarrafata kamar injin
YUSUF yaga bala'i da MASEEFA ganin idansa ya kasa gajiya da XARAH Sam
Yi yake Amma yaqi barinta

Itako sumewa tayi dan batayi tunanin aika aikan da tayi xaikaita hakaba
Can YUSUF ya fashe da kuka danjin wani MASEEFAR SON XARAH daya cafki xuciyarsa
Badan yaso ba ya barta dan karya illata kansa
Xuba mata ido yayi kawai yana kallanta SOONTA na shigarsa



LABEEBAH fah😳
Gani tayi shuru YUSUF bai dawo bah taje tayi wanka tasaka kayan bacci tayi addu'a da kwantawa abinta sai bacci yayi awan gabah da ita
Ta cikin baccin natane tayi mafarkin KAMAL


_cikin wani ni'iman taccan gida me kyau_
_Yana wajan furanni Sai qamshin furannin ne me tashi agun_
_KAMAL yana xaune kan sallaya yana addu'a Amma batasan me yake cewa bah_
_Ya juyo ahankali suka ha'da ido_
_Wannan abun dayake fitowa a idansa ya shiga nata idan shi yafitoh daga idan nasa ya shiga natan_
_Ta lumshe ido Tace Ya KAMAL wata duniyace wannan._
_Yayi Murmushi ya nuna mata wani gu da hannunshi. Tabi gun da kallo_
_XARAH tagani da YUSUF maqale da juna. Amma hankalin YUSUF nakanta dan sai miqo mata hannu yake alamar daje gare shi yana hawaye still yana rungume da XARAH_

_Saiko ta maqale kafa'da cikin tsoro Tace baxan xo bah_

_KAMAL yayi Murmushi da girgixa kai Yace plx Babyna kibarsu ahaka Karki shiga rayuwarsu_ _kijirani kiriqemin alkawarin kanki_


_Nufu shi tafayi. Saidai wani xare me qarfi yayi mata katanga da_ _KAMAL Tace dan Allah Ya KAMAL kaxo kayanke igiyarnan kar Ya YUSUF ya kamani_
_Yace bani da damar yanke igiyar_....


Furgigit LABEEBAH tafarka lokacin yayi dai-dai da qala kiran sallar asubah.


🤔 Amma fah kumin afuwa masu xagina Nagode
Sai dai inasan kusani baxan canja tsarin littafina bah



Fa'di take aranta nariqe maka alqawari Ya KAMAL
Sannan kuma kar in shiga rayuwar XARAH YUSUF
In jiraka
Me hakan yake nufi
Shuru tayi xuwacan xuciyarta tacemata kishare kawai karki sakama kanki damuwa ai mafarki ba gaskiya bane

Aiko tatashi tayi toilet ta gyara jikinta dayin wanka kana ta share falan nata duk da bawani datti bane dashi
Ta fesa turara. Sannan. Ta koma ta kwanta tana tuna YUSUF daga cewa bari yayima XARAH saida safe Amma shuru


Bayan YUSUF ya tsaftace kansa yafitoh ya'dan yarfama XARAH ruwa
Aiko nan ta farfa'do da jan numfashi
Ya xauna gyefan gadan yana kallanta Yace in 'daukeki in miki wankan ne ko Yah

Ta harareshi tare da tashi tayi toilet ahankali dan ta 'dan 'dana ko'darta

YUSUF yayi Murmushi Yace yanxu aka fara

Koda tagama tsaftace nata jikin xama tayi a toilet 'din tana rayawa aranta eh Lalle YUSUF bashi da imani
Tun take da KAMAL bai ta6a bata wahala irin yanda YUSUF ya bata yau bah

Shurun yayi yawa inji xuciyar YUSUF
Dan haka sai kawai yafa'da toilet 'din
Aiko ganinta yayi cikin tunanin
Yace Kinga malama ke nake jira
Tace Menene
Dariya yayi dan Ganin yanda ta tsorata
Ya qarasa shiga toilet da kamota suka fitoh da kwantawa
Nan ya rungume abinsa
XARAH dai Tace tayi kwanan farin ciki
Yayinda YUSUF yayi na Mamakin kansa da ita
Farkawar YUSUF yayi dai-dai da farkawar LABEEBAH da Asuba haka yatashi XARAH sukayi Sallah

Washe gari kusan qarfe takwai Momy ta tauro musu su Sagna da Safna da breakfast

Shashin LABEEBAH suka farayi. Dake kofar abu'de take sai suka shiga kawai
Nan suka ganta kwance tana bacci hankali kwançe
SAUBAN ya saki hannun Safna yayi kan gadan da gudu ya 'dane da hawa kanta yana dariya
Ai nan LABEEBAH Tatashi da sakar musu Murmushi
Tace yaushe kukaxo
Suka gaisheta Sagna Tace yanxu mukaxo
Safna Tace kinsan kukan da yarannan yamana agida kowa
Sagna Tace Wlhi hanamu bacci yayi
Wai shidai mamansa akaisa gun mamansa
Aiko Momy Tace mutawo dashi ya xauna gun wacce batada da Ya YUSUF
LABEEBAH taqara rungumarsa Tace ai kun kyautamin da kuka kawoshi ina kayansa Sagna Tace yana falo
Tace Yauwa da kama fuskarshi Suna wasa

Safna Tace breakfast muka kawo
LABEEBAH Tace toh Sannunku.
Nan suka ta6a hira kana sukayi part 'din XARAH dan gaisar da ita
Da sallama suka shiga falan shukaji shuru
Sagna Tace mushiga bet room ko itama baccin take
Safna Tace baki dakai bakiga bamuga ya YUSUF a 'dakin Aunty LABEEBAH qila anan ya kwana
Sagna Tace anya mudai shiga. Safna tayi waje tana cewa Wlhi baxan shigaba
Aiko Sagna ta leqa ta windan Bet room 'din
Nan taga XARAH maqale ajikin YUSUF Suna bacci hankali kwance
Futuwa tayi itama Tace mah Safna dagaske Suna tare Wlhi xoki gansu Safna tace bacci suke
Tace eh
Nan itama Safna taje taleqasu
Suka fito Suna dariya dayin gun LABEEBAH sukace Ashe basu tashiba
LABEEBAH Tace suwa Sagna Tace Ya YUSUF da Aunty XARAH man mun leqasu sai bacci sukeyi hankali kwance
Gaban LABEEBAH ya tsinke ya fa'di dammm
Tayi saurin qaqalo Murmushi da kallan agogo ganin takwas da rabi Tace yanxu xasu tashi
Safna tace mu xamu tafi Aunty tace mungode kugaida momy suka toh xataji dayi mata sai anjima suka tafi

Akan hanyarsu ne Safna Tace Wlhi naxaci ya YUSUF agun Aunty LABEEBAH xai kwana
Sagna Tace nima nayi tunanin haka Amma kamar baidace abinda yayibah
Safna Tace ina ruwanki kika sani ko ita Aunty LABEEBAN CE Tace yaje guntan kin santa da gwaninta
Sagna Tace aikowa akwaita da gwanintar Allah yasa karya xame mata matsala dan Wlhi Aunty XARAH tafita wayo kuma Kinga shi namiji kamar kwallo yake duk wacce ta iya cillashi itace dashi
Safna Tace toh malamar soyayya kice Aminu har yanda xaki mallakeshi ya koyar dake
Sagna Tace eh aimu xaman Auran mu da kallo
Safna Tace xa'asha kalle kalle ba kallo bah
Sagna tajah tsaki


LABEEBAH tashiryama SAUBAN kayansa tsaf a durowa
Sannan. Suka baje sulayi breakfast 'dinsu kana taje Babban falo tajera sauran a dining Sannan suka dawo suka da'da bajewa itada SAUBAN 'dinta tadinga biyema shirmansa.
Amma hankalinta yana kan XARAH da YUSUF abin ya bata mamaki yanda taji Su Sagna sunce wai har yanxu bacci suke basu tashi bah.
Me hakan yake nufi
Yana nufin anan ya kwana abinsa. Xuciyata tabata amsa


YUSUF da XARAH sai xuwa goma suka tashi
Sukayi wanka
YUSUF yafitoh falo yanata mamakin Kasan cewarsa da XARAH
Can tabiyoshi falan tagaidashi idanta a qasa
Ya amsa da kulawa sai kuma sukayi shuru
Dake YUSUF yasan kan tamace tashi yayi yaxo gabanta ya durkusa Yace farin cikina kisoni plx kamar yanda nasoki na qaunaceki adaran jiya
Fashewa da kuka tayi Tace inasanka YUSUF son da wata mace bata ta6ayi maka shiba
Nafa'da ~*MASEEFAR SONKA*~ saidai xan kasance cikin damuwa da tashin hankali ha'de da baqin ciki
Ya share mata hawayanta Yace fa'damin me xai yawo miki haka
Tace kishinka ne xai jawomin haka
Inasan 'Yar uwata LABEEBAH Amma akan kishinka xamu samu babbar matsala da ita dan baxan iya jure kaje gareta Sannan kaxo gareni ba
Xuciyata xata iya bugawa
Taqarashe da rushemai da kuka
[8:19PM, 08/10/2016] Rahamat Nalele💋: --------------
Ba qaramin bugawa xuciyar YUSUF tayiba. atake hankalinshi yatashi. Sam ya manta da LABEEBAH tunda ya shiga 'dinkin XARAH jiya
Tashi yayi ya dafe kai Yace innalillahi.......
XARAH Tace wani abune
Ya kalleta har xaiyi magana saiya fasa ya nufi part 'din LABEEBAH
Ganinta yayi a falo tanata taya SAUBAN wasa
Ta kalleshi ya sakar mata Murmushi ta mayar mishi
Ya qaraso da xama kusa da ita Yace am sorry nutsuwata Wlhi XARAH CE Tace tana da tsoro wai bata iya kwana ita 'daya bah shiyasa baki ganni ba
Shuru LABEEBAH tayi dan axahiri itace matsoraciya mejin tsoro ba XARAH bah Amma meyasa Tace mishi tanajin tsoro.
Ganin tayi shuru yasashi cewa dan Allah kiyi.........
Bata bari ya qarasa ba Tace ina kwana da fatan kuntashi lafiya

Yace lafiya lau Amma baxan qara kar6ar wannan gaisuwar ba. Dan ba ita nake buqata bah
Tace toh wacce kake buqata
Ya kama fuskarta ya manna mata kiss a goshi da hanci da baki Yace xaki iya rungumata kiyi min kamar yanda namiki yanxu plx kar kice Komai
Tace bin umarninka shine numfashina
Karka damu xamma yanda kakeso
Nagode sosai
Tace ya kwanan XARAH.
Ananne ya Sosa qeya ka'dan yace lafiya
Tace haka akeso ga breakfast can Momy ta aiko tun'daxo
Ya 'dan waro ido da kallan agogo Yace kai ya akayi lokaci ya qure haka.
Sai yanxu takaicinsa ya kamata Tace gaskiyane ka huta da yawa shiyasa lokaci ya maka baxata

Tashi yayi yana cewa aransa yarinyar nan neman magana take
Amma afili cewa yayi toh muje kiban mana
Tace toh bara in kira XARAH ko
Yace no bari na kirata
Yafa'da da sake SAUBAN wanda tun shigowar shi ya maqale mai

Toh LABEEBAH Tace mai kawai da binshi da kallo

Yana komawa falan XARAH ya ganta tana kuka wiwi
Cikin tashin hankali yayi kanta da tambayar lafiya Tace watoh dan LABEEBAH tafini darajah agunka shine ina ambatarta kayi gunta
YUSUF ya dafe kai
Yace toh yi hakuri ba haka bane ke da LABEEBAH 'dayane aguna plx Ki fahimceni
Cigaba tayi da kukanta. Ya rungumeta yana lallashinta
Can dai tayi shuru tana sauke ajiyar xuciya
Yace Yauwa.tashi toh muje muyi breakfast

Tace nidai saidai kaxauna anan in kawo mana Komai nan
Bayanda YUSUF xaiyi sai gya'da mata kai da yayi ta ficce
Direct part 'din LABEEBAH tayi suka gaisa Sannan ta tambayeta breakfast 'din
Tace yana can falan
XARAH tayi Murmushi Tace gaskiya hankalina yayi gunki banda haka yaci ace naci karo da shi kafin in qaraso nan
LABEEBAH ma tayi murmushin Tace Hakkane Amma me yasami fuskarki kamar kinyi kuka
Tace haka kawai natashi da ciwan ido ina addu'ar Allah yasa karnah xama ke
Tace ayya sannu ciwan ido ba da'di
Tace ina xuwa
Tace toh
SAUBAN wasanshi yake Sam be waniyi 'daukin Ganin maman nashi XARAH ba

Kamar ance LABEEBAH leqa Babban falo aiko Tatashi ta leqa nan taga ba YUSUF ba dalilinsa haka ba XARAH da abincin da tajera
Tadawo ahankali tana tunanin wai me yake shirin faruwa ne
can dai ta'daga kafa'da takori tunanin xuciyar tata

Abinda yabata mamaki shine yanda taga YUSUF da XARAH sun fitoh Suna dariya da kagansu kaga Masoya YUSUF ya kama hannun XARAH batasan me yake CE mataba ya shige mota ta 'dagamai hannu ya ficce
Saita XARAH Koma part 'dinta

Shuru LABEEBAH tayi kawai taqi 'dauke idanta a window dan tafa'da wani birkitaccen tunani


Da yamma ne LABEEBAH tana kitchen tana ha'da musu abinci dan taga Komai na buqata a kitchen 'din akwai harsu nama kifi gasunan a refrigerator shi yasata San yin girkin. Kuma takira Momy Tace karta turo musu da Komai sai kayan gwari
Aiko taturo musu harda Su kayan Qamshi

XARAH ta shigo kitchen 'din tana qare mishi kallo Komai yayi daidai saikace yaran sarauta ko 'yayan shugaban qasa.
Tace wow gaskiyane kitchen din yayi kyau
LABEEBAH Tace eh Momy tayi qoqari Allah ya biyata Tace AmEEn
Bara natayaki
Nan sukayi girkinsu me da'di da rai da lafiya. sukaci

Wajan 6:00pm YUSUF ya shigo gidan.
Tabbas part 'din LABEEBAH yayi niyar shiga duk dako ya dawo da buqatar San Ganin XARAH
Saidai me😳

Yana fitowa daga motar XARAH tafitoh tariqe mai hannu Tace Wlcm my luv da fatan kadawo lafiya
Farin ciki ya cika xuciyar YUSUF musamman data Sha wankan Riga da wando tayi kyau sosai kamar ya sataceta ya gudu
Yakai bakinsa Cikin nata ya tsotsa ka'dan kana yajata part 'dinta
Anan suka baje suka fara aikawa junansu sakwanni luvvvvv


Hawaye ne

Please Login or Register in order to submit comment