Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsorata Tace waifah aunty XARAH CE tace tanasan ganin Aunty LABEEBAH shine yaxo 'daukarta yakai mata ita
Atare suka sauke ajiyar xuciya

LABEEBAH ko tunda Sumayya ta ambaci KAMAL jikinta yamutu. Tuni xuciyarta takwa'daitu dasan taganshi

Dan haka dasauri tafa'da 'daki tahau shiryawa.
Mamah na cewa kiyi sauri karki barshi yagaji da jira danke shirinki daban yake dana mutane
Innah tayi dariya Tace ai AISHA akwai da'dewa wanjan fante fanten fuska yanxu bari kiga tafitoh tamkar sarauniya xata xama


Wata jar shadda tasa riga da siket 'dinkin ya kar6i jikinta dan ba qaramin kyau tayi bah
Tasaka gyalanta mekyau da takalminta me'dan tudu
'Daurinta irinna wayayyun matan nanne watoh ture kaga tsiya. Sai xubah qamshi take. Sumayya Tace kai Amma fah kinyi kyau bah 'dan ka'dan bah
Tace Nagode
Haka tafitoh tayima Su Innah sallama tafitta


Tunda tafitoh idan KAMAL yake kanta har ta'dan duqa tagaisheshi bai 'dauke idansa akanta bah
Bayan tashiga motarne sunfara tafiya Yace kinyi kyau sosai.

Ji tayi wani da'di yacika xuciyarta Tace Nagode
_Nagode_
ya akwai kwayi muryarta. Duk sukayi dariya
Tace inafatan 'Yar uwata tana lafiya
Yace ina kika ta6agin aikai amarya 'dakin mijinta da kwana 'daya ace lafiyarta qalau
Cikin tsoro LABEEBAH tawaro ido hankalinta a'dan tashe Tace toh me yasa meta
Ka'dan yarage KAMAL bai fashe da dariya ba Yace nima ban sani bah
Taturo baki gabah. qiris take jira ta6arke da kuka Tace dan Allah dan Annabi Ya KAMAL kagayamin me yasa meta hankalina ya tashi me yafaru da ita. Taqarashe maganar dasan fashewa da kuka
Tamkar ya ankare yayi saurin cewa wasafah nake miki karkimin kuka kisani ka'de mutane dan rikicewa
Jan ajiyar xuciya tayi tare da sake fuskartata Tace harnaji dadi
Da Murmushi ya kalleta baice komaiba. Itama shuru tayi tana jin farin ciki aranta yanda take shaqar qamshinsa ahaka suka isa gidan
Yana faking ta ficce da sauri dan ganin XARANTA
Murmushi KAMAL yayi yajuya motarsa ya qara ficcewa
XARAH ko na kwance nan na'de agado. 'dan ciwan Kaine yake damunta kuma KAMAL yabata magani Amma ciwan bai barta bah
Ganin LABEEBAH yasata miqewa da sauri ta rungumeta Tace Ashe haka Aure yake LABEEBAH Ashe KAMAL mugune Mara tausayi saita fashe da kuka
Yayinda hakalin labeebah ya tashi cikin wani hali Tace meya faru fa'damin dan Allah
Nan XARAH tagaya mata yamata kaca kaca narashin tausayi sam bai mata da Sauqi bah. dan haka baxata qara yarda dashi ba
Yanxu LABEEBAH tagane Komai tadinga lallashinta da nuna mata hakkin shine dole tayarda dashi inba hakabah taha'du da tsinuwar mala'iku
Daqer dai da si'din goshi LABEEBAH tashawo kanta
Dan haka XARAH tasake har tanemi ciwan kan tarasa
LABEEBAH Tace kinje kin gaida Momyn shi da kakah
XARAH Tace eh kai tare dashi mukaje
Bakiga yanda suka kar6eni bah Wlhi Cikin farin ciki da kulawa
LABEEBAH Tace gud hakan yayi kyau yanxu akwai abinda Xan miki ne
Tace ba Komai dama wanke kayan da mukayi breakfast ne 'daxo kuma qanwarshi Safna tayimin sai nayi shara kawai
LABEEBAH Tace yanxu dai ba wani aiki Tace eh kam babu..........
Sallama sukaji anatayi dan haka LABEEBAH taleqa. Safna CE da Sagna Cikin fara'a Tace la Sannunku kushigo
Nan suka shiga. Sagna taxauna gefan gado yayinda Safna take tsaye suka gaishesu XARAH da LABEEBAH suka amsa da kulawa

Sagna sai wani 'daure fuska take wai adole batasan LABEEBAH da XARAH surainata dan taga ba wasu masu shi bane
Ita ko LABEEBAH tanace saita kula Sagna tun Sagnan na sharewa hardai tasake da LABEEBAH
Safna ko ba ruwanta dan bata nuna musu Komai bah
Ganin haka yasa XARAH tafi sakewa da ita Safna
Haka suka dinga hira abinsu can suka tafi

XARAH takalli LABEEBAH Tace nalura Sagna 'yar jin kaice. LABEEBAH tawaro ido Tace kai habah ni ban gani bah Tace Allah Safna tafita sauqin kai
LABEEBAH tata6e baki Tace tun yanxu kin fara qorafi. kimata uxiri ila wani abunne yake damunta ne
XARAH tajah tsaki Tace bawani ni bana san rai nine
Shuru LABEEBAH tayi dan tasan XARAH sarai basan raini takeba toh koya xasu Kaya da Sagna oho

Natuna gobe xaku Yola ko. XARAH tatambayi LABEEBAH
Eh Amma nida Innah da Ya Usman saijibi xaimu. Tace-da'ita
Allah ya kaimu naso aje dani. XARAH taqara fa'din hakan
LABEEBAH tatashi tayafah gyalanta Tace Allah baiyi ba toh. Ki xauna a'dakinki mungode. Barah naje nagaidaisu kakah daga nan saina wacce tashi muje
Kamar XARAH xatayi kukah Tace haba dan Allah tafiya yanxu
LABEEBAH Tace xanjefah gidan Aunty Zainab Kinsan ta kuma dasa mutum aiki bai xama Lalle tabarni nakoma gida da wuribah taqarashe maganar da ficcewa nan tabita tana cewa da wannan dan wannan

A harabar gidanta XARAH tatsaya yayinda LABEEBAH tashige shashin su kakah
Tako same ta afalo taje kusa da ita tagaisheta.
kakah tadafa kanta ta'amsa Cikin farin ciki
Kana Tatashi tamata sallama xata fitone kakar tace ga momynku na wanka dakun gaisa
LABEEBAH tayi murmushi Tace LA Bakomai agaisheta
Tace toh xataji Nagode sosai 'Yar kirki
Murmushi tayi tafito

XARAH Tace toh kigai shemin dasu mamah kice xanxo da daddare. LABEEBAH ta harareta Tace agarin jakuna xakixo ko
XARAH Tace Allah da gaske
LABEEBAH Tace hmm ba mamaki kam dan naga xafin luv 'din jiya bai barki bah. Tana fa'din haka taficce tana dariya tare da qarawa da cewa Allah yasa yauma ya qara
Sanda gaban XARAH yafa'di Tace ta Allah ba takiba



LABEEBAH taje gidan Zainab bata sameta bah
Akan han yarta taxuwa gidane taga wani makawo da alama yanasan atsallakar dashi titine dan haka taje takama hannunsa ta tsallakar dashi yanata samata albarka Tace ya Isa godiyar haka Babah tabu'de jakarta tabashi laira 'dari biyun da takesan hawa adai-daita sahu tabashi
Sannan tayi gaba abinta
duk abinda ya faru akan idan KAMAL ya faru dan danja na tsaida shi ya xuge gilashin motar tasa dan yaga kamar LABEEBAH
yako tabbatar da ita 'dince. Ahaka yaga abinda yafaru.

Itako LABEEBAH Sam bata gansa bah haka kawai takesan tafiyar qafah yau dan sai tafiyarta take hankali kwance Cikin nutsuwa

Jimana 'yan mata KAMAL yace da ita
Cak tatsaya dan har abada muryar KAMAL baxata ta6a 6ace mata bah


Ahankali tajuyo ta xuba mai ido. Ya 'daga mata gira da cewa kin tsaya kina kallona kina 6atamin lokaci kixo mu tafiko
Murmushi tayi tabu'de motar tashiga Sannan takulle
Tace barka da yamma. Batare da ya kalleta bah Yace Barka dai
da fatan kinsha tafiyar qafah lafiya
Lau Tace dashi
Meyasa baki bari nadawo na maidake gidaba
Tace dan xanje gidan yayana ne shiyasa kuma mah ai bai can canta nasaka wahala bah
Xan can ki bai gamsar daniba nafi yarda da kawai kina sanne ko xakiga KAMAL 'dinki. Dan in amota ne ko mashin bai xama lalle Ki gan sabah. Ya qarashe da kallanta
Murmushi tayi Tace lallema Ya KAMAL waya gayama. Yace aiba sai angaya min bah gani nayi a kwayar idanki
Lalle ko idan nawa ya nuna maka qarya Tace da shi
Ko ya bata amsa
Da sjagwa6a Tace Allah da gaske
Ganin xata fara yimishi shagwa6a yasashi batar da xancan da cewa
Yauwa namanta Auwal Yace min am muku rasuwa wai gobe xaku mah Yola ko
Tace eh
Allah yaji qansa ya gafarta masa
Tace AmEEn Nagode sosai
Batare da ya amsa godiyarta ba Yace
In tambayeki man
Kallansa tayi Tace Allah yasa nasani
Faking yayi a kofar gidan nasu ya kalleta Yace meyasa muryarki take yimin da'di
A'dan tsorace ta kalleshi Tace banji bah
Yace nasan kinjini
Inasan muryarki Laveeva. Wanda idan kina magana banasan kidena. Ya qatashe da sanyin murya da kuma jefah mata wani shu'umin kallan da yasa jikinta mutuwa lokaci 'daya. Batare da yasan ya mata shibah
Cikin wani yanayi Tace nima ban sani bah.
_nima ban sani bah_ shima yafa'da da kwai kwayan muryarta ashagwa6e

Dariya tayi Tace Allah Ya KAMAL kadena bana so tafa'da a shagwa6en
Ni kuma inaso. Ya bata amsa tare da kafeta da ido
Ya salam LABEEBAH Tace axuciyarta wannan mutumin nasan kasheta lokacinta baiyi bah
Jan yo duk wata jarumta tata tayi wacce tarasata yanxu Tace toh ka gai shemin da XARAH tafa'da dasan ficcewa
Yayi saurin cewa baxan fa'daba.
Tajuyo da kallan sa Tace meyasa. Yace saboda ban gama jin muryarki bah.
Tace toh aikai ba KAMAL 'dina bane kai KAMAL 'din XARAH ne. Kamar yanda Komai namu yaxo 'daya ni da ita haka mah muryo yunmu 'daya ne
Yayi Murmushi dan ya raina wayanta Yace hmm ai XARAH tafiki da'din murya idan tana magana bawanda yake gajiya da ita wasa nake miki bakida da'din murya

Aiko tarkwanshi ya 'danu dan turo baki tayi kamar xatayi kuka Tace toh ina ruwana koma tafini ai nida ita 'daya. Taqarashe da harararsa
Gimtse dariyarsa yayi Yace To miye na turomin baki kamar xakiyimin kuka in hakan ne me yasaki 6ata fuska
Harararsa tayi taficce daga motar sanda takai 'kofar gidan nasune tajuyo ta kallesa
Shiko ya 'daga mata hannu anamar bye bye....
Gya'da mai kai tayi kana tashige gida
Shiko ya jah motarsa xuciyarsa na tuno mishi da ita
Yayi gidansa gun XARAN Sa

LABEEBAH ko bata samu kowa a tsakar gida ba. dan haka Cikin san'da tashige 'dakinta da kwantawa kan yaloliyar katifarta dan bataso wani ya katse mata tunanin da xakeyi yanxu..

Nu tsuwa tayi sosai tana tunanin KAMAL. Meyasa Yace mata yanajin da'din muryarta. Ita harwata murya me da'di take da ita
Ajema a haka. Amma kallan da yake mata fah. Yayi kama da wanda yake yima XARAH
Idan ko hakane me yake nufi
Shuru tayi tana neman amsa Amma kaf tunaninta yakasa bata amsar
Mararta ce ta'dan mur'da mata
Cikin tsoro tatashi xaune tana ta6a marar tana kuma xaro ido
Jiki asanyaye tafara lissafin yau kwananta talatin
Wato dai al'adarta CE xataxo mamah
Kuka tafara tana kiran sunan Allah yau kuma wahalarta taxo kenan
Cikin sauri talalli gyfanta inda take ajiye magungunan da KAMAL yake kawo mata duk qarshan wata tabu'de tana addu'ar Allah yasa akwai saura
Addu'arta taci dan taga sauran sha 'daya
Dan haka ta6alle jiki na rawa rawatsa a baki takora da ruwa Sannan takwanta tana addu'ar Allah yasa karta Sha wahala a ciwan
Da haka bacci ya 'daketa me tattare da mafarkin KAMAL

Kiran sallar magriba ne ya tasheta tana tashin taga ko al'adar taxo mata
fitowa tayi tsakar gida mamah da take alwala takalleta da mamaki.
Yaushe kika dawo
Tace 'daxo
Amma banji shigowarki bah
Eh nadawo agajiyene kuma ban ganki a tsakar gida bah shiyasa nashige 'daki na kwanta
Amma ko kinada shirme har Sumayya tashigo Nace baki dawoba
Yi hakuri toh mamah
Nayi toh. Mamah tabata amsa Cikin murmusawa. Tare da cewa ya XARAH Tace lafiyanta qalau tacema agaisheku
Muna amsawa Zainab fah
Naje na same ta bata nan
Toh ba damuwa mijinta xaixo an jima ai
LABEEBAH tagyara tsayuwa Tace
A kwai wani abunda Xan miki ne
aa je kiyi wanka kiyo alwala kiyi Sallah na gama Komai
Tace ina fashi 'daxo yaxo
Gaban mamah yafa'di cikin tsoro Tace yaxo 'daxo fah kikace Tace eh na'danji ciwan ka'dan 'daxo
Shuru mamah tayi taqarasa alwalarta tana addu'ar Allah yasa karya wahalar mata da ita
LABEEBAH ko bayi tayi ta tsaf tace jikinta tsaf tayi wanka Sannan tadawo 'daki.
Bayan tasaka kayane Sumayya tashigo Tace yanxu kika dawo
Tace aa tun 'daxo Amma bacci nayi mamah mah batasan nadawo ba. Wai harkin shigo tace miki ban dawo bah ko
Eh hakane ya Aunty XARAH dai
Lpy yanta qalau tanamah gaisheki
Ina amsawa Sumayya tace
LABEEBAH tace 'danjeki kicin ki ibo mana abinci dan Allah Tace toh

Bayan sunci abincinne ne Suleiman da Usman suka shigo tagai dasu
Tace mah Suleiman Yayah naje gidanka 'daxo Aunty Zainab batanan ai
Yace eh wai taje suna ne
Tace aiko........
wayarta CE tayi qara. Koda taduba sai taga Jameel ne.
da 6acin rai a fuskarta ta'dauka da sallama

Yace ran gimbiyata ya da'de dafatan xan sami ganinki yanxu ina kofar gidanku
Shuru tayi.
Yace dan Allah karki qi fitowa Wlhi xuciyata xata iya bugawa.
Tausayinsa ne ya kamata dan har abada baxata so shiba KAMAL ne aranta
Tace toh ganinan takashe wayan.

Qara feshe jikinta da turare tayi Sannan tagayama mamah tafitta

Jameel ya runtse ido Yace qamshin kine ya sanar dani xuwanki gimbiyata.
Tace Hmmm toh Barka da dare
Yace barka da fatan nasa meki lpy
Tace lafiya lau nake ya har kokin yau da kullun
Yace lafiya Amma akan soyayyarki Wlhi bana cikin lafiya
Tace toh naji yanxu me ya kawoka
Yace idan masoyi yaxo gun budurwa me yake akawo shi gunta
SOO
Tabashi amsa Cikin sauri Yace toh nima so ne ya kawoni.
Shuru tayi. Shima shurun yayi
Can takatse shurun da cewa banaso na yaudare ka. kayi hakuri kanemi wata dan Allah
Yace LABEEBAH kenan tsoran mekike
Plx kibani dama in shiga birnin xuciyarki in saka miki qaunata.
Na miki alqarin saikin manta da wani KAMAL
Ina San KAMAL so na haqiqa
Baxan iya ha'da sanshi dana kowa bah
Kadena ha'da kanka dashi
Wlhi xuciyata tayi nisa a soyayyarsa
Son sah ya xamemin MASEEFAR SOO
Banasan mu gina rayuwarmu nida kai ta farnin yaudara
Plx dan Allah ba danni bah ka hakura dani. LABEEBAH Tace dashi hakan

Yayi Murmushi yace idan na hakura dake inyi yaya kenan
Gaskiya baxan iyaba
Idan har kika bani dama. Nagaya miki saikin soni fiye da KAMAL din
Toh wai waye shi

Sanin koshi waye bashine abu me mahimmanci agareka bah
Rabuwa dani shine yafi dacewa dakai
Kaina na min ciwo dan haka saida safe. Tace dashi hakan tare da shigewa gida batare da taji cewarsa bah
Shima jinjina kai yayi yashige motarsa Yana cewa aransa Wlhi baxan bar kiba Sannan yajah motarsa

Ita ko tana shiga gida Bayan taxauna ciwan marah yace salamu'alekum
Nan tafara juyi ka'dan ka'dan.......
Sumayya ta miqa mata wayarta dacewa ana kiranki Ya KAMAL
Da sauri takar6a tana cije baki Yace
Me kikeyi Tace banajin da'dine.
Yace ya salam dama nakawo miki maganinki ne gani a kofar gida
Tace Yauwa nagode dan 'daxuma yaqare
Yace shaf na manta kituro wani ya kar6ar miki plx dan bana so yafara wahalar dake
Tace ga Sumayya nan Nagode
Yace Karki damu. Yana fa'din haka ya kashe wayan
Nan tagayama Sumayya takar6o mata
Komai arubuce yake dan haka duk tashasu batare da 6ata lokaci bah

Cikin ikwan Allah ko. Ko rabin awah bata yibah taji ciwan ya'dan 'dauke
Mamah Tace Allah yasakama KAMAL da alkairi tunda yasan ciwan nannata baita6a mantawa da kwanakin watanba
Sumayya Tace AmEEn ai Yana kirki sosai
Shuru LABEEBAH tayi dan qara son shi take ba'dan ka'dan bah
Da gaske dai ciwan bai takura mah LABEEBAH kamar yanda yasaba bah. Tayi dai baccin nutsuwa. Yayinda abin ya kasance ga KAMAL ba haka bah



Yana rungume da Matarsa XARAH wacce ta amince ne da hakan idan baxai mata Komai bah. Yayi Murmushi Yace habah my TEEMAH wannan fah hakkinane Naji dai baxan miki Komai bah shikenan. Ta'dagamai kai
Nan ya jawota jikinsa Yana shafata har tayi bacci.
_Toh nashi baccin ne yaga wasu kyawawan yara sunkai 6 awajan shaqatawa_
_Gyefansu LABEEBAH CE tana danna laptop tana hawaye ya shigo gun_
_Yaran sukaxo da gudu suka rungumeshi Cikin farinci da annushuwa suke. Hakama shi_
_Nan ya dinga sumbatarsu yana godiya ga Allah daya bashisu_
_Can ya kalli LABEEBAH Yace me kike ganine a laptop 'din_
_'Daya da ga Cikin yaran Tace Dady hotan nan take kallo meyasa Momy take santa_
_Bayan ita kuma bata Santa tunda ta iya tafiya tabarta_
_Yayi Murmushi ya shafi fuskar yarinyar Yace qaddarace yasata barinmu_
_Tace qaddara menene qaddara_
_Yace o momyna kincika tambaya jeku qarasa wasanku_
_duk suka sakeshi suka koma gun wasansu_
_Shi kuma yaxo gunta yana kallan fuskar laptop din_ _XARAH yagani_
_Sai kawai ya rufe laptop din yamaida kallansa kanta Yace nagaji da hanaki kuka akanta_
_kuma nafa tunanin saita kaiki wutta akan na._
_agigice takalle shi yako gya'da mata kai_
_Cikin kuka Tace kayi hakuri dan Allah_
_Ya ta6e baki Yace ai kullun a hakuri nake dauke._
_yanxu dai tashi Ki kula dani nadawo da MASEEFAR SONKI_ _gya'da kai tayi ya rungumeta Cikin so da qauna_..........


Agigice KAMAL ya farka daga wannan mafarki. Yayi shuru
Ayanda dai ya gansa da LABEEBAH ba shakka matarsa ce.
Toh ya abin xai kasance innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un me xai faru dani ni KAMAL
Abaiyane Yaketa furta cewa LABEEBAH LABEEBAH LABEEBAH
Cikin mamaki XARAH data farka tace metayi metayi my luv menene
Cikin murmushin yaqe Yace Bakomai
Tace ban yarda bah ka gayamin menene dan Allah
Xuba mata ido yayi na minti 'daya kana Yace mafarki kikeyi shine naji kina ambatar LABEEBAH
Shine nima na furta hakan kikaji
Dafatan dai ba mugun mafarki kikayiba
Tayi Murmushi Tace tab Ni Wlhi ban san ma ina ambatar sunantaba
Kuma kasan wani abu. Ya girgixa mata kai alamar a'a
Taci gabah. bana mafarki kuma koma nayi mantawa nake dan Wlhi yanxuma bansan nayi mafarkinta bama harnake ambatarta
Yace hakane Allah yasa mudace Tace AmEEn
Sannan yatashi yayi Alwala yayi Sallah raka'a goma Sha biyu ya ruqi Allah akan ya bashi haske akan lamarin shi da LABEEBAH ya kuma bashi fahimtar abunda yake faruwa ya kuma sah albarka acikin lamarin.


Washe gari ko mamah da Malam Sanih da Suleiman da Matarsa Zainab da yaranta kaf suka loloqa birnin Yalo

😭😭😭😭😭😭😭
Hatsarin ya faru ne lokacin da motarsu take gaf da shiga Yola
Rai yayi halinsa
Dan wata babbar motace tabugi tasu motar nan take takama da wuta
Amma anyi nasarar fitar dasu. Saidai inba kasansu ba. Baxaka ganesu bah
Toh Malam Sanih da mamah da Suleiman da Zainab da yaranta kaf duk sun rasu rai yayi halinsa
Harda wasu tsirarru da direban motar

Wani ne yalura da wayar da take jikin Malam sani shine ya 'dauka duk da ta 'kone Amma haka yacire sim 'din yasa a wayarsa
Nan sunan mutane takwas ya baiyana
Wato innansu LABEEBAH KAMAL XARAH Suleiman Usman Malam Sallau Bashir
Sai kawai ya tsinci kansa da kiran KAMAL
Amma har tagama ringing ba'a'dauka bah
Dan haka sai yakira Malam Sallau ringing 'daya ya'dauka yanacewa kunsauka lafiya
Mutumin Yace kayi hakuri bawan Allah Amma rai yayi halinsa kaf Cikin motar sun mace sakamakwan hatsarin daya afku dasu Suna daf da shiga Yalo...............




Kasan cewar wayar tashi baji yake bah dan haka yaqara volume tunda ya 'daga wayan
Toh dama Innah na gyefanshi a tsaye tanajin komai
Dan haka da mutumin yagama xancan atare suka xu6e qasa. Inna ta sume yayinda shi kuma yaxuma mata ido hankalinsa amatuqar tashe


ya fito daga wanka kenan yaga wayan tashi da miss call sai yaji gabansa ya fa'di ganin BABA 2 watoh mahaifin LABEEBAH dan haka da sauri yakira number Yana cewa BABA Barka da safiya
Murumin daya 'dauka Yace Bashi bane tare da gaya mishi hatsarin daya faru
😳Iya gigicewa KAMAL ya gigice Yace what kana nufin sun mutu gabaki 'daya
Cike da tabbaci mutumin ya bashi amsa ha'di da rarrashi. Dai-dai nan XARAH tashigo 'dakin ganinshi hankali tashe ga waya akunne yasata kafeshi da ido Tace yadai naganka haka lafiya. Sake wayar tasa yayi a qasa tabi wayan da kallo shima yabi wayan da kallo. Atare kuma suka kalli junansu
.





Shuru nawani 'dan lokaci Suke kallan junan nasu. Can dai XARAH ta'aro jarumta taje ta'dauki wayar tashi tasa a gado Tace my luv ka........
Yayi saurin katseta da cewa Karki tambayeni plx👏🏻
Tace meyasa
Yace Hakka kawai
Tace OK dama naxo gaya maka ne anturo mana da abinci nd is so delicious
Yace dat is luvly I will be wit u in a short while.
Tace OK. Sai tafuta
Shuru KAMAL yayi Yana Cikin furgicin lamarin. Xama yayi gyefan gado yana tunani ya'da kansa yakalli agogo ya nuna mishi 6:00pm
Can kamar an muntsineshi yatashi Cikin sauri ya kasa kayansa ha'de da 'daukar wayarsa da keey 'din motarsa yafito falan
Nan yaganta a dining

Please Login or Register in order to submit comment