Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magana YUSUF ya shigo
Ya gaida Yayan nashi
XARAH takafeshi da ido tana cewa kabari direva ya kaisu man
Ya gallah mata harara
Momy tayi Murmushi
Sagna da Safna suka fitoh daga 'dakinsu
Safna Tace gaskiya banji da'din tafiyar nan taku da xakuyi bah Aunty LABEEBAH
Sagna takama hannunta Tace Xanyi missing 'dinki
LABEEBAH Tace karku damu bayan muna tare
Haka suka loda musu kayan Su amotar YUSUF Wanda Momy ta shirya musu shatara ta arxiqi
sukayi sallama wa juna Sannan suka cale garin na Kano


Ko amotar soyayya sosai YUSUF ya bu'de mah LABEEBAH shafinta
Sumayya tanajin Su cikin sha'awa tana Murmushi
LABEEBAH ko tun tana biye mishi har tadawo tadena biye mishi bacci yayi awan gaba da ita

Ahaka suka iso lafiya hankali kwance
Innah da ya Usman saiganin Su kawai sukayi wayyo murna kamar suyi yaya
Innah fa'da take kunyi kyau sosai yaran kirki musamman ke LABEEBAH

Haka Rukayya ta damama YUSUF fura da nono mesanyi Innah takawomai abinci irin na gida dambu

Nan YUSUF yaci ya 'koshi ya kora da nono

Sannan suka ke6e
Shida da LABEEBAH Tace yanxu sai gidan Kakah ya 'dauka ko Yace eh Xanyi mata kwana biyu kinga jibi sai in tafi. Tace toh kaishemin da ita
Yace har yanxu xan qara roqarki abu
Tace inajinka Yace kimin alqawarin baxaki yarda ya KAMAL ya ganki bah dukko xuqanda xaiyi Karki fitoh gareshi Tace namaka alqawarin shi kenan Yace hmm
Kallansa tayi takyau Lalle kishin YUSUF ya fara damunta
Tace kanada kishi ya YUSUF
Yace idan banyi kishinki bah kishin waxanyi
Yafa'di hakan a fusace
Sunkwai dakan ta tayi



Abuja
🌡🌹🌡

Koda YUSUF ya koma bai xame ko ina bah sai office 'din KAMAL
Yasameshi ko Yana aikin tunanin LABEEBAH Yace sannu da aiki Yayana Yace Yauwa dafatan kadawo lafiya Yace qalau Kakah na gaida kai sosai wai yaushe xakaje
KAMAL yayi Murmushi Yace Kakah ko rikici
Shuru suka 'dauka nawani 'dan lokaci candai YUSUF yashi daniyar tafiya
KAMAL ya kirashi
Da sanyi yadawo ya xaunah
Yace nalura akwai abinda yake damunka plx kafa'damin
Sosa qeya YUSUF yayi Yace hmm Bakomai
KAMAL Yace dan Allah kafa'damin banasan damuwarka
YUSUF yajah numfashi ya sunkwai da kansa Yace Wlhi Yaya bansan yaushene nakamu da Santa ba.
Plx yayah katenaken dan Allah
dan Allah katemaken
Saiga hawaye
KAMAL ya qura mishi ido gabansa na fa'duwa ya ta6a fuskar YUSUF da dangwalo hawayansa Yace yau kai kake kuka YUSUF
Yace Wlhi Yayah kusan kullun sai nayi akanta
Yace wacece
YUSUF ya kalleshi ka'dan Yace Aisha-Labibah
Rumtse ido KAMAL yayi ha'de da dafe kanshi tashin hankali ya baiyana qarara agare shi
YUSUF ya lura da hakan dan haka yaqara cewa Wlhi Yayah santa yajefani cikin tunani damuwa tashin hankali katemaken Yayah xan iya mutuwa akanta Wlhi.

_xuciyarta tawace Ni ka'dai. idan nabar maka LABEEBAH baxakaji da'dinta bah har abada. nine dulmiye aranta xaka mallaki gangar jikinta ne qanina Amma banda xuciyarta. Ina sanka xan iya sadaukarma da soyayyar LABEEBAH koda Ni xan rasa nawa ran_
KAMAL ya fa'di hakab aransa xiciyarsa namasa xafi hankalinsa tashe
Da hawaye ya kalli YUSUF Yace kaje qanina nabar maka LABEEBAH sai kayi qoqarin neman xuciyarta
Da murna YUSUF yatashi ya rungumi Yayan nasa Yace ina sanka Yayana Allah yabarmin kai
Ya gya'da mishi kai YUSUF ya fitta





Hmmm Ni Rahamat Nace tab anya hakan xaiyuhu
Hmm ba ruwana kudai biyoni
Karku damu xuwa dare xan yo muku wani post 'din juhuta lpy



KAMAL yabishi da kallo dagaske yaji da'di aransa
Yanda yaga farin cikin qaninnasa

Kasa aikin nashi yayi haka ya dawo gida yanasan yin jinyar kansa

Koda XARAH tashigo bet room nashi ganinsa tayi cikin xaxxafan xaxxa6i
Arikice take tambayarsa meya jawo mishi wannan xaxxa6in
Tafa'da tamai bashi maganin xaxxa6in
Kar6a yayi yasha
Yace na rasata TEEMAH na rasata....
Tace wacece
Yace AISHA
Tace au dama sunanta kenan
Yace eh kuma na rasata har abada
Da xaro ido Tace yanxu kana nufin ka sadaukar ma wani ita
Yace eh
gamama kinsa sai yaga tatsaya cak tafa'da tunani
Yace yadai
Saurin gyara kanta tayi Tace hmm Bakomai. Yanxu dai kafasa auran naka
Ya rumtse ido Yace eh
Xama tayi agyfansa kawai tana kallansa.


YUSUF ansamu abinda akeso sai murna yake yaudai yayi maganin matsalarsa
Momy takallesa Tace nakwana biyu banga farin cikinka irin nayau bah
Yace eh Wlhi Momy yaudai nayi maganin matsalata
Tace miye matsalar taka
Yace nasa mam miki sirika
Takalleshi da mamaki Tace wacece wannan Yace AISHA LABEEBAH 'yarki
Cikin wani farin ciki Tace kai Amma naji da'di ka biyani YUSUF kuma kodama bakaxomin da wannan vatun bah nayi alkawarin aura maka ita
Yace toh gashi naxo miki da batun saiki bani tukwaici.








🌡🌡🌹🌹🌡🌡
Bayan watanni hu'du da kwanaki
Tundaga ranar da KAMAL ya sadaukarma YUSUF soyayyarsa da LABEEBAH baiyi gigin kiran wayanta ba

Allah sarki yayi dan gana ga Allah ya bama Allah amanar kansa
Duk wani abu daxaiyi dan ya kori soyayar LABEEBAH aransa yayi yayi Amma abin yaci tira
Saiyaga kamar qara mishi MASEEFAR SONTA akemai
Lokaci lokaci yakan kulle kansa yayi kuka sosai ya lallashi xuciyarsa
XARAH na kallansa saidai tabishi da na mujiya
Amma duk da haka bai manta da ranakun al'adar LABEEBAN tashi bah
Dan yanaba YUSUF maganin nata

YUSUF xirga xirga tasashi agaba. Dan kusan kullun Yana kan hanyar garin na Kano
Yana quqari sosai wajan ganin ya cire soyayyar KAMAL a baxuciyar LABEEBAH
Yasani duk alaye take masa wajan nuna yanxu shi takeso
Amma yasan har ixuwa yanxun yasan Yayan nasane aranta


Momy tayima dadynsu KAMAL maganar soyayyar YUSUF da LABEEBAH kuma dasan akai ku'din Aure da saka ranah
Abin ya mishi da'di sosai
Dan haka yatada 'dan uwansa na kano Yace yanasan sujega gidansu LABEEBAH

Hakako akayi nan Baban XARAH da Ya Usman sukayi na'am da batun
Musamman da aka tambayi LABEEBAH Tace eh tana San YUSUF
Dan haka aka saka ranar Aure wata biyu masu xuwa.

Al'amarin daya hautsina KAMAL da LABEEBAH kenan
Wanda awannan ranah basuyi bacci bah
Sai tunanin junansu da suke
LABEEBAH takasa jure tunanin dan haka kawai ta6are baki ta riski kukanta San ranta


Washe gari sai tatsinci kanta da kiran KAMAL. Yana 'dauka tarushemai da kuka sosai
Yana jinta yamata shuru candai da Kukan nata yafara qoqarin saka mishi ciwo yayi saurin cewa me ya farune baby
Tace yanxu ya YUSUF shine xai xamo Miji agareni
Yace eh
Tace haba mana Ya KAMAL kace wani abu mana xuciyata namin xafi
Yace plx my baby ki temaken ki kasance cikin nutsuwarki
Tashin hankalinki shine tashin hankalina
Kiyi addu'a Allah ya fiddamu daga wannan MASIFAR
Cikin sanyi Tace toh
Yace Yauwa babyna iyi dariya Naji
Tace saidai Murmushi
Yace ko shine kiyi Naji da'di plxxxxxxx
Tayi murmushin cikin kuka. Yace Yauwa Babyna
albishirinki
Tace goro
Yace saikin share hawayanki xan fa'da miki
Aiko da sauri tashare hawayan kamar tana gabansa
Yace yanxun nan 'Yar uwarki XARAH ta aihu.....
Da sauri Tace dan Allah
Yace da gaske Tace wayyo da'di kasheni me aka samu Yace namiji
Tace dawa yayi kama
Yace kicanka
Tace toh tsaya inyi tunani
Yayi Murmushi Yace axaune nake mah my baby
Tace xanso yayi kama dakai Yace toh kamarmu mah 'daya kincanka
Har aransa yaji dariyarta
Yace my baby........
Taji sunan har ranta Tace na'am Yace wane suna kikesan asa mishi
Tace Ni kuma Ya KAMAL Yace eh kee
ina cikin office 'dina yanxu haka
Ita kuma tanacan tana hutawa baby Yana hannunsu Momy
Xanji da'din yanda nasamu nutsuwa awannan lokacin kifa'di ra'ayinki akan babyn nan
Wlhi my baby ra'ayinki shine nawa

Tajah numfashi Tace toh asa mishi MUHAMMED-SAUBAN
Yace yayi
Yayi my baby
Tace toh yanxu ya xa'ayi xuwanmu
Yace ya kikeso my baby
Tace xataxo wankan gidane
Yace hmm in yau kikesan suxo garin Kano Wlhi yau xasuxo
Tace toh suyi kwana uku sai suxo
Yace angama shikenan Tace eh Amma...... Saitayi shuru
Ya gyara xamansa Yace Amma me
Plx dan Allah kar kiqi fa'da
Tace toh dama inasan in ganka ne......
Taqarashe da sanyin murya
Shuru yayi
Tace Amma.....
Yayi saurin katsata da cewa yaushe kikesan ganin nawa
Ta lumshe ido
Xuciyarta na cewa kice yanxu Amma ganin rashin dacewar hakan yasata cewa. Inasan Ranar da xasuxo ya kasance inganka

Yayi Murmushi dan yagane fa'din hakan kawai tayi Amma ba hakan bane Cikin ranta.
Yace toh Allah ya kaimu
Tace AmEEn
Suka ajiye waya jiki asanyaye

Rukayya Tace dawa kike waya Tace da ya KAMAL ne
Tace Naji kina murna kamar XARAH ta aihu
Tace eh ta aihu namiji ta aifah mah
da murna Rukayya Tace kai Amma Allah ya raya
Tashi tayi taxari gyale daniyar xuwa gayama inna Tace AmEEn
[9:47PM, 30/09/2016] Rahamat NaleleπŸ’‹: 🌡🌡🌡



Kwana ukun ko nayi Su XARAH suka diro kano harda Momy agidanta tasauka Su Momy ko shashin Kakah

Aiko ko minti biyar LABEEBAH da Sumayya basu yiba dukayi gidan

Jariri na hannun LABEEBAH taqi bama kowa
Sagna da Safna mah suna maqale da ita fa'di suke yau gamu gaki Aunty LABEEBAH
Tace eh nayi missing 'dinku sosai

YUSUF ya shigo da waro ido Yace eh lallene da gaske tunda gaku
LABEEBAH Tace me yafaru
Ya harareta Yace watoh nace miki hardani akan hanya kuma gareki xan fara xuwa shine kika gudo nan dan xumu'di
Tace ayya MeeNi kayi hakuri kasan baxan iya ba
baxan iya qara ko minti 'daya bane wajan xuwa gun baby
Yace hmm ai kinganshi saiki tashi muje dan nadawo da 'daukin ganinki da San hirarki
Kai Ya YUSUF ban gama ganinshi bafah
Ya miqa mata hannu alamar tabashi babyn
Da turo baki ta bashi
Aiko direct kan cinyar XARAH ya ajiye babyn
Yace kiji dashi dan nutsuwata taji dani nimah
Mugun kallo XARAH tajefeshi dashi bai lura bah yajah hannun LABEEBAH suka ficce
Su Sagna suka sheqe da dariya

Wajan shaqatawar gidan yayi da ita nan sukasha soyayyarsu
Amma xuciyar LABEEBAH na muradinga San ganin KAMAL

Saidai taji da Sumayya take tambayar XARAH shi
Taji XARAN Tace mata baisami xuwa bah dan ayau 'din yatashi bayajin da'di
Tana ganinma sai bayan Suna xaixo
LABEEBAH tayi saq dan da gaske hankalinta yatashi

Aiko ke6ewa tayi
takira number nashi taji akulle
Kiran duniya yaqi shiga




πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―
Yau asabar Yakama kuma yaune suna dan haka akasha Suna aka ra6ashe
Abin sha'awa da jin da'di. Gaskiyane duk yanda kaso ganin sunan ya xarce tunaninka. Mejego tasamu kaya na nunama sa'a
Yaro yaci Suna MUHAMMED-SAUBAN


Yau kwana biyu dayin Suna Amma har yau LABEEBAH taqi jin KAMAL awaya
Kuma abinda ya bata mamaki XARAH bata wani damu

Yanxu haka Suna tare LABEEBAH da XARAH
LABEEBAH Tace niko lafiya Ya KAMAL shuru.
XARAH tayi Murmushi Tace Yana lafiya dan 'daxu muka gama waya wai Yana kan hanya mah
Kinga yanxu qarfe uku inaga xuwa 4 xai sauka.
Ko ba komai Hankalin LABEEBAH ya kwanta
Amma me yasami numbar tashi da take dashi yadena amfani da itane
Wannan tambayar bata da amsa inba agun XARAH bah
Ita kuma baxata iya tambayar tabah

XARAH Tatashi tana kallan agogo Tace kinga xan kar6i wani Abu agidan wata qawata dataxo nan kano kuma har na gayama KAMAL
ya kamata inje yanxu kafin ya qaraso
LABEEBAH Tace bai dace kifitaba kimin kwatancan gidan inje in kar6o miki
Kinga kar wani yaxo ganinki bakyanan

Tace saikice musu na shiga wanka.
Kuma baxata baki bah dole saidai Ni
Kuma kinga gobe ne tafiyata gida wankan gida Kinsan kuma Innah baxata barni fittaba

Dan haka plx dan Allah Kikula da SAUBAN kuma Karki bari Momy tasan bana nan
Da kallo LABEEBAH tabita har tafita





Hmmmmmmm
Al'amarin ya farune lokacin da KAMAL ya iso kano
Yana jiran direban Kakah yaxo ya 'dauke shi sai yaga wata motah ta faka a gabansa wani 'dan saurayi ya fitoh da fara'a Yace yalla6ai muje ko
KAMAL yamai kallan raini Yace waya turoka
Yace XARAH CE ta turoni wai dereban Kakah yabajin da'di
Cike da yarda KAMAL yashiga motar.
Aiko Yana shiga wani ta bayansa ya rufe mishi hanci da baki
Nan take KAMAL ya sume
Sai me😳

Tsintar kanshi yayi a wani fanta meman gida
Ya bu'de idanshi ahankali kana ya sauke akan mutunan

Su biyar ne manyan qatti masuji da qarfi kallo 'daya xaka musu kagano rashin imaninsu
Kan yayi magana yaga 'daya daga cikinsu yaje je da gudu ya bu'de get 'din gidan wata mota ta shigo

sai yaga wata qatuwar mata tabu'de 'kofar ta fito
Qurama matar ido yayi yana tuna inda ya santa........
Saidai kan ya tuna XARAH tabiyo matar wajan fitowa
Jameel ya biyo Bayan tah
KAMAL ya murje idan Sa da kyau aiko yaga XARAN shice cikin shigar riga da siket tayi kyau sosai taci tabarau saikace ba kwananta Tara da aihuwa bah

Ta qaraso gareshi ta xare tabarau 'din tana tafah hannu
Sannan takalli wa'yannan qartin Tace wow aikinku yayi kyau
Sannan taqaraso daf da KAMAL

Tace kayi mamaki ko ba mamaki idan kayi mamakin.

KAMAL kenan
Da XARAH kake ba gixo idanka yake maka ba
Kasan dalilin dayasa nasaka aka kawoka nan
Xubah mata yayi baice Komai bah

Hmm nasaka an kawokane dan na kashe kah

KAMAL ranah ta biyu da xuwana Abujah ranar da mukaje dasu LABEEBAH

A ranar na kamu da MASEEFAR SOON qaninka YUSUF

Sai narasa yanda Xanyi da raina dan Ni matar kace

Sai ya kasance akoyaushe inasan naga YUSUF
Hankalina ya tashi dan tuna har abada baxan mallaki YUSUF ba

Ina cikin wannan saiga Hajjiya turai makwaf ciyarmu gata. Tanunamai wannan qatuwar mata
Tace taxone taxama aminiyata dan talura ni sabowar zuwace
Niko Nayarda da batunta dan naga tadace da taxama aminiyar tawa
Inba ka mantaba ina nagaya maka xan shiga gunta
Dake kana ganinta aguna saika lamince akan inje gareta

To sai dai me
Ranar taxo taganni cikin tagumi da damuwa
Tatambayeni matsalata niko nagaya mata

Kasan inda Wanda xan gayama matsala toh LABEEBAH CE
Amma Kasan ko karan haukane ya cixan baxan tun kareta da wannan batu bah

Anan nida Hajjiya Turai muka shirya kasheka
Amman saina aihu
Dan inci riba biyu
Tafarko idan nakasheka xan sami YUSUF
Na biyu duk wata dukiyarka taxama tawa danna aihu dakai

Tajah numfashi anan Sannan taci gaba da cewa

In gaya maka wasan da kada'de kana bugawa tunaninka ban saniba

Shine soyayyarka da LABEEBAH

Akwai wata rana dana cema LABEEBAH nifah ixuwa yanxu nafara tsanar KAMAL 'dinnan
Ina nufin wanda take so
Bu'dar bakinta Kasan metace min
Hmmm
Gwarama kidena dan abin sankine
Tun daga ranar nafara bin tunaninta da yanayinda nakane kaine KAMAL 'dinta

Sai dai awannan lokacin baxan iya bar mata kaiba
Saboda kayi tako ta ina duk Wanda Yace baka iya luv bah yayi qarya
Kai gwanine musamman dana kasance matarka Nagano abubuwa da damah agame dakai

Amma meyasa nakamu dasan qaninka YUSUF


Kana wani maganar kakamu da MASEEFAR SON LABEEBAH
YUSUF Yana cewa ya kamu da MASEEFAR SONTA
Tana cewa ta kamu da MASEEFAR SONKA

Ni kuma fah meca'a kirani kenan. Ina matar Aure
Kaga sai ace na kamu da babbar MASEEFAR SOO dan taxarce taku
Tasan wani ba Mijina bah. Kuma wanin qaninka

Ni XARAH Ni yadace da akira da nafa'da ~MASEEFAR SOO~

Ayanxu ba abinda natsana kamar LABEEBAH tsana ko me muni
Tunda Wanda nakeso ita yake so

Baxan kasheta bah
Dan tana sona
Musamman yanda ta6oye soyayyar da take maka soboda Ni

Lokacin da ka ankare da son da take maka ban damu bah
Saboda mun rika mun gamah shirinmu
Amma da kaxo min da batun kasadaukar da soyayyarka nadamu
Dan hakan Yana nufin YUSUF xai samu LABEEBAH


Duk wannan kukan da nake maka duk na gwajine dan Naga wane irin kisa xan maka
Kidan kanuna tausayina in maka mutuwar sauki indan kuma ban baka tausayiba in maka mutuwar rashin imani


Xan auri YUSUF dan nawane Ni 'daya
San nan tare xai Aure mu Ni da LABEEBAH dan tahakan ne xan gasata san raina
Lefinta ko shine na yanda ta yarda da auran YUSUF
Baxan ta6a barin YUSUF ya Santa bah
Dan baxan iya jure wannan bah

Xan axab tar da ita sosai cikin makirci
idan kuma takawo min matsala sai in kasheta


Ta kalli Jameel Tace bani bindigar nan
Aiko Jameel ya miqa mata bindiga
Yana cewa karkayi mamakin ganini KAMAL haka rayuwa take. Kasan ina MASEEFAR son LABEEBAH Amma katake kafara Santa
Na ha'de da XARAH ne akan wannan cin amanar da kamin

XARAH Tace baxan ta6a samun YUSUF bah har sai ka mutu KAMAL
Xan maka wata alfarma shine......
Taxaro wayarsa a gaban rigarsa ta qarashe da cewa xan kira maka LABEEBAH ka gaya mata kalmomi uku na soyayya
Dai-dai nan numbar LABEEBAH tashiga

LABEEBAH naxaune da jariri ahannunta yana qananun kuka Tace ko a ina XARAH ta tsaya oho tajah saki
Sai taji wayarta na ringin tana dubawa taga KAMAL aiko da sauri ta'dauka Tace hello Ya KAMAL

KAMAL yayi Murmushi me ciwo Yace na'am Babyna

XARAH ta'daga mishi yatsa 'daya alamar saura mishi kalmomi biyu

BABEEBAH Tace nayi fushi dakai tunda kaqi xuwa tun ran uku
Yaqara yin Murmushi

Yace I LUV U

Sannan yajah numfashi yaqara cewa
Karki yarda da kowa arayuwarki cikiko harda ~XARAH~

Gaban LABEEBAH ya fa'di Tace meyasa kace haka
Shuru taji wayan tayi tana dubawa taga ankashe
Tayi saqalo da wayan tana kallo

A canko XARAH CE ta'amshe wayan sanda taka she Sannan Tace kalmominka sunqare sai kuma acan
Karka damu nasan ka aikata kyakkyawa arayuwarka dan haka ina maka fatan alkairi

Aiko jikake fas... fas....
XARAH ta sakarma KAMAL harsashi biyu 'daya a qirji 'daya a cikinsa
Nan KAMAL ya riqe cikinsa da qirjinsa
Tace karka damu *~MASEEFAR SOO~* ne yajah maka haka
Suna kallo har yadena motsi sannan takalli qartannan Tace kusan yanda xakuyi kujefar min shi a babban rafi Wanda abubuwan ruwa xasu cinyesa yanda bawanda xai gansa

Kudauko wannan gawar data dagargaje kusaka wannan fuskar da aka ha'da tasa akan ta mutumin. Kuyi yanda baxa'a gane bah Sannan kuxo Ku ajiyeshi 'kofar gidana
Da 'dayanku ya tsaya dan fa'dar shuru mu

Sukace an gama ranki ya da'de

Jameel Yace naji basira Allah yajah da xamaninki XARAH
Tayi Murmushi da cewa muje ko

Haka suka shige motar da sukaxo suka ficce

Su kuma qartan nan suka saka KAMAL a motarsu suma suka ficce dan aiwatar da abinda XARAH ta umarcesu dashi



LABEEBAH ko saqalo tayi da waya ahannunta tana tuna me KAMAL Yace mata
Nan take jikinta yayi sanyi saitaji hankalinta ya tashi. Kuma sai jitake gabanta na fa'duwa

Taxauna gyefan gado tana tunani
batasan adadin da ta'dauka tana tunanin ba . Saiji tayi XARAH ta dafata
A'dan furgice ta kalleta
Keko mexaisa saki shiga tunani haka bayan nabarki lpy

LABEEBAH tajah numfashi Tace hmm haka kawai naji gabana na fa'duwa
XARAH tayi Murmushi Tace ki kama salati xaki dena ji
Ai nama 'dauka tunanin KAMAL 'dinki kike
Tace eh harda tunaninshi
XARAH Tace koda Naji

Am ba wanda yaxo nemana
Eh babu saidai SAUBAN ya 'danyi kuka ka'dan LABEEBAH tace da ita hakan tare da miqa mata shi
Xama XARAH tayi takar6e shi da jan tsaki Tace toh mezan mishi
LABEEBAH Tace ban gane mexa Ki mishi vah kibashi nono man
Tace Tab ai daga yau nayanke bashi nono. Dan banaso na tsufah
Cikin tsoran furucin nata da xaro ido LABEEBAH Tace me kenan kike nufi
Kina nufin yau kin yanke ba shi nono saboda banxan tunaninki
Cikin fusata XARAH Tace eh haka nake nufi baxan qara bashi nono bah dan banasan suxube in tsufa da wari......
Kan LABEEBAH tayi magana saiganin Sagna da Safna sukayi sun shigo agigice suna kuka. Cewa suke Aunty XARAH Aunty XARAH aunty LABEEBAH
Munrasa Ya KAMAL ya KAMAL yayi hatsari ya mutu ya da gargaje ya mutu
Atare LABEEBAH da XARAH suka kalli juna. Aiko XARAH tatashi gabaki 'daya saiji kake tim SAUBAN Tafa'di qasa
Qararsa tayi dai dai da 'dora hannun XARAH akaπŸ™†πŸΌ ta kurma wani uban ihu Wanda duk Wanda yake makwaf taka da ita toka yaji wannan ihun
Tarushe da kuka me qara tare da fallewa da gudu waje Safna tabita. Yayinda Sagna ta'dauki SAUBAN dan ba qaramin kuka yake bah
LABEEBAH ko gabanta yabala'in vada dummm cikinta ya 'duru ruwa
Tasaka aranta ba KAMAL bane ya mutu
Dan haka XARAH na shekawa aguje itana tabita
Saidai me 😳
Tana xuwa farfajiyar gidan taga Momy axube YUSUF axube da alama sumewa sukayi.
Yamaida kallanta ga XARAH wacee taketa xabga kuka tana surutai. Nan taga gawar mutum fuskarshi ta KAMAL sak
Ahankali taqarasa aiko KAMAL ne fuskarsa kawai xaka gane Kasan shine

Jijjigashi XARAH takeyi tana kuka tana fa"din meyasa kamin haka KAMAL me yasa me yasa Kasan in bakai baxan iya rayuwa bah
Na shiga uku ni XARAH Wlhi binka Xanyi KAMAL binka Xanyi wayyo Allah
Duk wa'yanda suke gun saida suka tausayama XARAH
Salim ya goge hawaye yajata Yana cewa kiyi hakuri XARAH

Luuuuuuuuuu.....
Suka ga LABEEBAH taxube a qasa ba tambaya kasan sumewa tayi.......

Duk Su ukun akasa amota sai asibity




Wasa gaske KAMAL ne yayi hatsari ya mutu
Garin yayah
Me yakai ya KAMAL hawa motar haya
Bayan munyi waya dashi Yace min xai shiga jirgi kenan
Meyasa yafasa bin jirgi yabi motar haya
Da har 6arayi suka taresu. Ganin hakan yasa direbansu yin daji lamarin yafaru

Salim ya dafah YUSUF Yace duk wa'yannan tambayoyin naka shine xai baka amsarsu. Kuma kaga yanxu Bashi dan ya rigamu gidan gaskiya

YUSUF wanda ya riga Momy da LABEEBAH farfa'dowa Ya share hawayansa Yace yanxu kana nufin ya KAMAL ya mutu ya barni yabar Momy da Dady da kowa
Shuru Salim yayimai dan ya fara Ganin alamun hankalin 'dan uwan nasa yafara fitta daga gareshi

Momy mah batafi rabin awabah ta farfa'do
Aiko sai kuka take tana ambatar KAMAL ne ya mutu jama'a ya mutu

Dadyn su KAMAL mah shima da yaji lamarin yanke jiki yayi yafa'di daqer aka samu ya farfa'do

Lamarin XARAH ko abin tausayi dan duk me hankali idan ya ganta saiyaji tausayinta

Ahaka akakai gawar KAMAL gidanshi na gaskiya


LABEEBAH fah😳
Har Bayan uku bata farfa'doba
Al amarin da yasa YUSUF dasu Momy Su Innah shiga tashin hankali kenan
Nan hankalinsu ya koma kanta.
Akwana na biyarne tafarfa'do lokacin ba kowa dan Sumayya ta shiga toilet
Aiko LABEEBAH tafashe da kuka sosai tayi tayi tayi San ranta.
Sumayya tayi mata lallashin duniya Sam LABEEBAH taqi sauraronta. Itadai kukanta take tana tuna kalmomin da KAMAL ya fa'da mata
YUSUF da Ya Usman suka shigo
Xuwa lokacin tadena kukan dan tuna wani Abu da tayi
YUSUF Yace am sorry
Ta sake mishi murmushin yaqe batace Komai bah


Bayan wata uku
XARAH taqara kyau sosai sai kace ba wacce mijinta ya mutu bah
Komai yinsa takeyi cikin jin da'di
SAUBAN yayi wayo saidai ya rasa nonon Uwa dan Sam XARAH bata Bashi nono
Sai aikin 'dirka mishi madara da takeyi
Ita kuma sai magunguna da takesha. Dan suqara yin tsaf

Innah ko bata ganewa
Dan idan Yana kuka tace tabashi nono saita

Please Login or Register in order to submit comment