Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bah sai tasa kanta

LABEEBAH ko na ajiye waya tayi shuru kawai tafa'da tunani
XARAH Tace hmm da aljanin kikayi waya
LABEEBAH ta kalleta Tace eh
XARAH tayi murmushin yaqe dayin shuru
Sumayya tayi Murmushi Tace kudai bakwa rabo da matsala
Wannan na fitta daga nan wancan xata 'dauka
Rukayya tace kiji wai aljani
Ke yanxu da aljani kike soyayya
LABEEBAH Tace eh
atare Rukayya da Sumayya sukayi dariya
Rukayya Tace wannan ai story ne.
Sumayya Tace babbama kuwa

Shuru LABEEBAH tayi musu da Qara kashe wayanta.

Washe gari tun qarfe tara direba yaxo ya kwashi LABEEBAH da XARAH Sumayya xuwa garin na Abuja

A gajiye suka Isa
murna tacika Momy Safna da Sagna Dady
Kowa yayi murna da xuwansu
Hajjiya Zainab matar Alhaji Nasir qani ga Dadynsu KAMAL tadinga yaba LABEEBAH da XARAH tana masha Allah
Kakah mah tayi murna Sosai da ganinsu

Bayan sun huta sunci sun sha LABEEBAH Tace hmm nagaji bari na'dan kwanta
Sumayya tayi gunsu Sagna
XARAH ko xagawa tayi Bayan gidan tana buqatar ka'daicewa......
Saidai me😳
Tana xuwa tahangi KAMAL da Marwan Suna hira cikin nisha'di
Gabanta ya tsinke ya fa'di. Nan nutsuwa tabayyana agareta
Hawaye ya xubo mata
Tabbas KAMAL ne wannan dan tatabbatar ma kanta shine tun ganin da tamasa a kano
Aiko tarushe da kuka wiwi
KAMAL ya kalleta ka'dan. Shiko Marwan xuba mata ido yayi kawai xuciyarsa tatafi tunaninta
Ya rinya kyakkyawa da ita gata kalan tausayi Amma ta aikata wannan aika aikam
Bai Ankareba ya ganta durqushe gaban KAMAL tana wani kuka me ban tausayi Tace nayi nadama nayi dana sani nayi Allah wadai da rayuwata nayi asarar da har in mutu baxan maida itaba
Na sani Kai KAMAL ne
Dan Allah dan Annabi karufamin asiri Karki tona wannan abin Allah wadai dana aikata maka.......
Ta qarashe da rushewa da kuka
Wani abune ya muntsini xuciyar KAMAL Wanda ya Haifar mai da tausayinta
Sai kawai ya tashi ya bar gun
Taqara rushewa da kuka
Marwan bai 'dauke idansa akantaba yayi Murmushi Yace XARAH ko
Ta kalleshi ka'dan tare da 'dauke kallan nata tacigaba da kukanta Yace Kinga malama baxafah Ki takuramin bah
Ki tashi kibar nan dan Allah
inajin kukanki har cikin xuciyata
Plx dan Allah temakeni kibar nan gurin
XARAH tatashi da jifan shi da harara Tace baxan bari bah kai katashi mana
A rayuwar Marwan yana San mace me tsiwa da rawar kai
Shiyasa Sagna tayi saurin shiga xuciyarsa. Wannan ra'ayinsa kenan
Yayi Murmushi Yace wow gaskiya ne in bakiyi tsiwa bah a tambayeki
Irin wannan harara haka. Kinga bacewa nayi ina sanki ba. Daxa kimin hararar Masoya
Ya ta6e baki ka'dan yaci gaba da cewa Kumama ni matsoracine koda kin soni aranki baxan aureki bah. Dan ina tsoran kar na Aureki wata ranah kiga qanina Ki kashe ni kice shi kikeso ..........

Tun da ya fara magana XARAH tasaki baki da hanci ido tana kallansa da mamakinsa
Akanme daga ganinta xai mata sharrin tana sanshi daga harara saiya juya mata manufah
Lokacin da yaxo furucinsa naqarshe abin ya 'kona xuciyarta tafashe da kuka me ban tausayi
Ya kalleta ka'dan da murmushin mugunta ha'de da tausayinta Yace am sorry......

Tafiya tafarayi tana cigaba da kukanta
Yace na'danji sanki ka'dan
Tajuyo ahankali takallesa sai taga ba ita yake kallo ba wata fulawa yake kallo.
Ya juyo ahankali ya kalleta Yace ina san Sagna Sannan ina 'dan sonki shin ya ha'din xai kasance
Cikin fusata XARAH taqara kai mishi harara Tace bana sanka bana sanka bana sanka
Yace da gaske naji sanki ka'dan. Amma Wlhi soyayyar da nakema Sagna taninka taki so dubu. Kina wani maganar baki sona keyanxu idan da xa'aji abinda kika aikata waxai aureki da wannan mummunar xuciyar taki. wacce Sam ba Allah acikinta. Wlhi tausayinki naji kuma nasan baxa kiqi na'am da soyayyata ba. Saidai kitsaya wani alaye. Gashi kuma inda xakiyin baxai ta6a tasiri ba. kawai ki share dan nima qarfin hali nayi kawai nayi dan nasan da wahala na Aureki bakiyi min abinda kikama yayanah KAMAL bah

XARAH takece da wani kuka Tace natsaneka
Tana fa'din hakan tafice daga gun
Marwan yayi Murmushi yace story kenan. banji sanki bah XARAH Amma xan dinga binki da kalamai har sai nadamarki tafi haka

XARAH 'dakin Momy taje takwanta tana tuno kalaman Marwan. Wanda talura baqar magana ya gaya mata

KAMAL ko part 'dansa yayi ya kwanta yana tunanin rayuwa
Can yaji yanasan Ganin LABEEBAH saiya kira Safna awaya. cikin sauri ta'dauka Tace Yayah
Yace inasan kigano min me LABEEBAH takeyi
Tace bacci take Yaya
Yace. A ina
Tace tana 'dakinmu
Yace OK saiya kashe wayan. Ya tashi direct part 'dinsu Sagna yayi ananko yaga LABEEBAH tana bacci hankali kwance yayi Murmushi da qare mata kallo.
Ya da'de yana kallanta ahaka kafin ya koma part 'dinsa batare data sani ba

Marwan Yace mai gata kyakkyawa XARAH Saidai ta6ata wayanta
KAMAL ya kalleshi ka'dan yayi murmushi yace kar kayi wani alaye idan tsuntsun ya koma kan tane kagayamin in baka ita karka duba abinda tamin dan kasameta xakaji da'dinta.
Marwan yayi Murmushi Yace aa Wlhi Yayanah kawai dai nafa'di abinda yakef hakane. Da ace nafara ganinta kannaga Sagna ba shakka da tayi Babban nasarar sace xuciyata
Amma maganar gaskiya son da nakema Sagna yafi Wanda naji yanxu araina
Kawai kashare
KAMAL ya dafa kafa'darsa Yace kayi dai tunani duk wacce takwanta maka nayi alqawarin baka ita
Marwan yayi Murmushi Yace toh Sagna
KAMAL Yace tunani Nace kayi . Yace toh Yayanah Xanyi


.
[1:47PM, 23/10/2016] Rahamat Nalele💋: LABEEBAH ko bata tashi ba sanda ta'dauki kusan awa 'daya
XARAH ma bacci tasha abinta. Saidai bana kwanciyar hankali bane kamar na LABEEBAH


Mexai faru 😳
Bayan isha'i sunci abinci XARAH Sam takasa cin Komai duk tawani hargitse lokaci 'daya
Sagna da Safna sun tambayeta me ya hargitsa ta haka Tace ba Komai
Sumayya tajah numfashi Tace toh Allah yasa ba Komai 'din
LABEEBAH ko tunani tayi qila har yanxu tunanin wannan aljanin nata takeyi Wanda ta'dauka KAMAL ne

KAMAL yakira Momy awaya Yace plx my Momy 'dan turomin 'Yar taki man
Momy tayi Murmushi Tace naqi baxa'amin hira agida bah
Yace ayya momyna dan Allah kituromin ita magana 'daya xan gaya mata
Tace toh naji. Takashe wayan tana Murmushi

Can takira Sagna Tace mata taturo mata LABEEBAH
Nan ko LABEEBAH taxo
Momy takalleta da Murmushi Tace ga abinci nan inaso ki kai part 'din KAMAL
toh Momy. LABEEBAH tafa'da da 'daukar abincin

Tunda ta doshi part din gabanta yake fa'duwa danjin qamshin turaran KAMAL
Tayi sallama tashiga falan da ajiye abincin kan table
Juyo wannan da xatayi sai taga KAMAL xaune akan kujera yana danna waya
Marwan na gefanshi yana kallanta
Taje kusa da Marwan Tace dan Allah kaima kana ganin aljanin nan
Yace eh Sosai mah
Tace ko kaima aljaninne
Yace aa ni mutum ne kamarki Yana fa'din haka ya fitta daga falan yana mata dariya

LABEEBAH xatayi saurin bin bayansa sai taji kawai KAMAL ya rige mata hannu
Yace xauna
Ba musu taxauna a kusa dashi inda ya buqata
Ya tattara hankalinsa da nutsuwarshi waje 'daya ya kama hannayanta dukka biyu yana kallanta ido cikin ido Yace lokacin da na sauka a jirgi. Na tsaya jiran direban Kakah yaxo ya 'daukeni Amma abin mamaki sai wani yaxo akan wai anturo shi ya 'daukeni
Ba musu nashiga motar tasu
Ashe rayuwata suke nema my baby. Dan ban tashi tsintar kaina bah sai a wani gida wanda baxan iya cewa ga inda mukabi mukaje wannan gidanba
Sai ogansu ya harbeni harbi biyu. Sannan yasa yaransa suka jefar dani a ruwa
Daga nan sai tsintar kaina nayi a qasar Armiyaniya. Nafa'da hannun sarkin garin

Shiya bani temakwan gaggawa
Har nasami matsalar 'daukewar tunani.
Daga baya tunanina ya dawo
Sarkin ya nunamin qaunah Sosai my baby ya 'dorani akan wani business 'dinsa da yake qasar England garin Dubai
Ni ba aljani bane my baby
Ni KAMAL 'dinki ne

LABEEBAH ta kura mishi ido Tace toh me yasa da aka kawoka mugaka fuskarka akan kaine wanda ka mutu. Yace duk shirin mutanan ne ban san dalilinsu nayin hakan ba
Tace yanxu kai Ya KAMAL ne
Tashi yayi ya buqaci Tatashi
Nanko Tatashi ya ware hannunsa Yace rungumeni Ki gane
Ahankali taje ta rungumesa
Nan ta lumshe ido Tace gaskiyane kaine kai Ya KAMAL.....

Ya rabata da jikinsa da qura mata ido Yace xaki Aure ni.......
Hawaye ya xubu mata Tace ina sanka Ya KAMAL ina sanka Wlhi ina sanka ina qaunarka. Amma ya xanyi da XARAH tana sanka. Kuma baxan iya kishi da ita bah
Ni kam na haqura da kai kawai
Ka maida matarka kawai
Yace ko
Ta'daga mai kai
Yace shi kenan
Ta qara 'daga mai kai
yaja numfashi. magana ta gaskiya Baxan maida Auran XARAH ba
Idan har ban Aure kiba Wlhi baxanyi Aure bah
Kuma nayima xuciyata alkawarin Auranki. Baxan ta6a barinki ba my baby
Yana fa'din hakan ya manna mata kiss a baki da nuna mata hanyar 'kofah
Ta kalleshi
Yace jiki dan Allah
Sai kawai ta rungumeshi tarushe mai da kuka

A duniya KAMAL bayasan kukan LABEEBAH daurewa kawai yake
Ya 'dago da fuskarta data rimtse idanta. Yace ki temaken dan Allah kidena kukannan yana ta6a xuciyata plx karkisa na aikata miki abinda baidace ba yanxu

Ta bu'de idan nata da 'dauke sautin kukan Amma hawaye bai bar xuba mata
cikin shagwa6a Tace meyasa baxan rayu cikin farin ciki bah
Yayi Murmushi Yace xakiyi rayuwa taban mamaki me da'di da gar'di da laushi da Santsi idan kikabi Komai asannu
Cikin kuka ta raba jikinta da nashi tafita daga falan.
KAMAL yayi Murmushi Yace bana san matsala tadawo min Wlhi
Ya 'daga kansa dama
Allah ka dubeni dan darajar Manzanka Annabinmu

LABEEBAH kare fuskarta tayi daga mutane tashige 'dakinsu Sagna
Anan taga XARAH duk jiki amace dan kallo 'daya xaka mata ka tabbatar a hargitse take

Aiko sai LABEEBAH bu'de shafin kuka
XARAH na kallanta
Tace meya saki kuka LABEEBAH
Shuru LABEEBAH tayi mata
XARAH tayi Murmushi Tace kinga Aljanin naki yace miki shi KAMAL ne ko
Da sauri LABEEBAH ta kalleta
Na gaya miki tun farko KAMAL ne kika musamin da aljanine
Na ganshi 'daxo ai. Hakanne ya qara tabbatar min da cewa shine
Toh mai xai dameki Bayan kinsami abinda kikeso.
Ya dawo gareki da muradin Auranki
Kibashi ha'dinkai kawai.
kuma kishare Komai aranki. Karki dubeni bare kiyi yunkurin aikata abinda ko xaki mutu baxai yuhuba
XARAH na kaiwa nan ta kece da kuka. Fa'di take na cuci Kaina LABEEBAH na aikata abinda har namutu baxai dena damuna ba
Na rasa KAMAL rasawa irinna har abada
Na aikata mishi abinda Ku xan mutu baxai qara maidani matsayin matarsa bah
Hajjiya Turai ta cuceni tasakani na aikata abinda in jama'a sukaji xasuyi Allah wadai dani
Ba xan rufe miba LABEEBAH ayan duk duniya ba abinda yake damun xuciyata kamar MASEEFAR SON KAMAL
Saidai baxan qara Kasan cewa Matarsa bah

LABEEBAH tayi shuru kawai tana jinta tana hawaye
Haka suka Kasan CE XARAH na kuka LABEEBAH na kuka

Washe gari walima
XARAH da LABEEBAH sunyi kyau Sosai cikin shigar dogajan riguna da Momy tabasu Tace shi xasusa

XARAH da LABEEBAH sunyi mamakin Cikan da akayi.
Duk wani abokin KAMAL sanda ya halacci gun
Haka kowa na Momy da Dady sanda suka bayyana kowa nuna farin Cikinsa yake na bayyanar KAMAL

Dake harabar gidan irin babbar nance. anan akayi Komai akagama
anci asha abin dai sai Wanda yagani
Haka taro ya watse cikin jin da'di
Hajjiya Kakah da Hajjiya Zainab ne sai Su LABEEBAH ne wa'yanda suka rage
Suma gobe xasu cilla garin nasu na kano
Momy ta kalli Kakah Tace ai tare dani xamu Kanon dan maganar shi KAMAL 'din da LABEEBAH.
Kakah Tace toh Allah ya kaimu
Hajjiya Zainab Tace AmEEn. Aiko gwara ayi saurin mishi wannan gatan
Momy tayi Murmushi

KAMAL ne yayo shashin Momy dan yana San kar6ar Abu agunta. Yayi kyau Sosai Cikin shigar suit dan yanxu duk shigarsa haka take
Aiko sukaci karo da XARAH gaf
Nan ta durkusa qasa takama qafarsa takece da kuka
Tace dan Allah ka yafe min dan Allah na roqeka dan soyayyarka da Allah kamin rai nayi nadama nayi nadama nayi nadama ka rufamin asiri
Dur 'kusawa agabanta yayi shima Yace XARAH kenan.
Hmmm Kinga rayuwa ko
Haka take daman tunda ba ahannun mutum takeba
Na yafe miki har abada bawanda xaiji wannan batu.
Mutum 'daya nema wanda na gayama
shine kuma Marwan Namiki alqawarin ba nabiyunsa aji
Temako 'daya xakimin Ki birgeni shine inaso idan Momy taxo gidanku da maganar Aurena da LABEEBAH inaso kice na nemi kikoma gidana kece kikaqi
Idan antambayeki dalilin dayasa kikaqi hakan kice............

Saurin katseshi XARAH tayi cikin kuka Tace karka damu da wannan nasan abinda xance musu
Ni fatana kayarda da tubana kuma kayarda ayanxu duk duniya ba Wanda nake MASEEFAR SOO sai kai ina SONKA ina QAUNARKA
Saita qara fashewa da kuka mai ban tausayi
Yayi Murmushi Yace watoh XARAH SO maseefa ne SO balaqine SO damuwa ne. SO ba da'di bane. nayarda da hakan dan nagani akan MASEEFAR SAN da nakema LABEEBAH ina santa ina QAUNARTA duk duniya ba wata macen da xatasha gabanta aguna
Yana fa'din haka ya tashi ya barta nan xaune cikin kuka

LABEEBAH taji Komai da suka tattauna dan itama 'dakin Momyn tanufa dan baxata iya jure shu'umin Kullan da KAMAL yake jifanta dashi ba
Dan haka tana ganin yabar inda suke tace bari tayo 'dakin Momy
Toh saitayi gamo da XARAH da KAMAL tanajin tafiyarshi yanda yanajin kukan XARAH yayi burus da ita shiyasata sulalewa ta xube aqasa tana hawaye. To wai wane lefi XARAH tayi mishi hakane

Ita dai tana San XARAH tanasan farin cikinta gashi farin cikin nata ya bayyana agareta Saidai yaqi yarda ta ra6eshi Sam

Gashi ita kuma abinda takeso shine farin cikinsu dukka ita da XARAN
tanasan KAMAL Amma baxata iya Auransa XARAH tana gani bah
Ta kece da kuka ta'dora hannu aka Tace wai har sai yaushe xan dena shiga matsala asoyayya har sai yaushe
Haba soyayya meyasa baxa kimin adalci bah
Meyasa kike tarwatsa nutsuwata
Meyasa in nan ya toshe saiki 6ullomin tawani gun
Wai KAMAL ne ka'dai namiji aduniya. Daxaki nace mishi xuciyata.
Haba haba haba xuciyata meyasa kikesan KAMAL
Sam banyi dace da soyayyaba

Na tsina kaina na tsani kaina taqara rushewa da kuka

XARAH najinta tatashi taxo lungun da take takama hannunta Cikin xubar da hawaye Tace KAMAL nakine LABEEBAH tun farko
Tabbas nayarda da qaunar da kikemin Amma kisani idan MASEEFAR SON KAMAL xata kasheni baxan kumama Auransa ba har abada
Nabar miki KAMAL

LABEEBAH Tace banyi mah kaina adalci ba XARAH natsani Kaina KAMAL shika'dai namiji da xuciyata xata nace sai shi
Na rasa wanda xanso sai mijinki
XARAH tafara goge mata hawaye duk da nata ba dena xuba mata yayi ba.
Tace kimanta abinda namiki akan YUSUF ne
Kin manta irin budurcin dana miki akansa
Kin manta cewa banji tausayinki ba akansa
Toh mexaisa kidamu dan KAMAL ya bayyana agareki
Yana sanki LABEEBAH tun ranar Farko
Ki temaken ki rama abinda namiki mana akan YUSUF
LABEEBAH Tace kishare wannan XARAH yarigada ya wucce. Ki fahimceni yanxu .

ina ina ina baxan iya Auran KAMAL kina kallo bah
XARAH Tace hmm ni kuma nayi miki alqawarin sai kin Aure KAMAL ina kallo dan KAMAL baxai ta6a barinki bah

In gaya miki wani sirri Wanda idan kaka jure a Auran KAMAL xaisa ya qara sanki
LABEEBAH ta girgixa mata kai Tace aa Karki gayamin komai
dan ke xaki koma 'dakinki mijinki
XARAH ta miqe Tace ko kiso ko karkiso LABEEBAH sai kin xama MATAR KAMAL......



XARAH tayi tafiyarta
LABEEBAH tabita da kallo
Wannan ranah kowa yasan XARAH da LABEEBAH basa cikin nutsuwarsu
KAMAL yakira LABEEBAH awaya
taqi amsa kiransa
Murmushi yayi dan yasan abinda takeso dai bamai yuhuwa bane


Washe gari haka Su LABEEBAH da Momy kakah Hajjiya Zainab Safna Sagna Su salima 'ya'yan Hajjiya Zainab suka garyatu garin na kano
Sun sauka lafiya
Inda direba ya kai su LABEEBAH Gidansu
Su innah sunyi da murnar dawowarsu ba kamar SAUBAN daya maqale maman nasa LABEEBAH
Bayan sun huta LABEEBAH tafa'da tunanin yanda suka wanye da KAMAL harya rikita mata kwanya

Abin da ya faru ko shine
Bayan sun tashi da safe KAMAL yaje ya marairai cema Momy Yace plx momy xanyi ganawar qarshe da 'yarki kafin sutafi
Tayi Murmushi Tace hmm dakayi hakuri tare damu ni da Dadynka xamu Kanon dan maganar Auran naka da ita
Da sauri ya kama hannun Momyn cikin murna Yace naji da'di momy dan kin rufamin asiri dan Wlhi 'Yar taki ta har gitsamin tunanina
Tace yanxu dai ina bakayi breakfast ba Yace eh Tace kaje xan turo maka ita. Yace Yauwa momyna

Yana fitta ko Momy takira LABEEBAH Tace takaima KAMAL breakfast 'dinshi
LABEEBAH dai toh tace mata Amma xahiri bata so ba

Da sallama tashiga falan nashi ta ajiye Komai kan table.
Marwan ya kalleta Yace gdmning my Aunty da fatan kintashi lafiya
Tace lafiya lau. Sannan Ta kalli KAMAL ka'dan Tace ina kwana Ya KAMAL
Yace daban kwanaba zakiganni
Tace atunanina banyi lefiba.........
Marwan ne ya fitta dan basu guri
KAMAL ya kalleta da kyau. Sai tayi saurin sunkuyar da kanta
Tace akwai abinda kake buqatane dan.....

Katseta yayi wajan tashi ya nufeta.
Yace jiya lefin menayi kikaqi 'daukar wayata
lumshe ido tayi dan jin qamshin sweet 'din bakinsa Tace wayan fah bata gurinane
Yace tana gurin waye
Tace Sumayya.
Yace yaushe kika fara qarya
Taqara lumshe ido dan qamshin sweet 'din yana neman takura mata dan jinshi take kamar ita takesha
Yayi Murmushi Yace xaki Sha ne
Tabu'de idanta ahankali bata san lokacin data 'daga mai kai bah
Ya qarayin Murmushi xaiyi magana XARAH tashogo falan duk suka bita da kallo
Ta koyi saurin runtse idanta dan baqaramin mummunan gani tayi ba
Dan xuwa lokacin da tashigo falan hannayan KAMAL Suna kan qugun LABEEBAH yayinda fuskarsu ka'dan ta rage ta ha'de da juna dan kusanci
Cikin saurin XARAH tamaida kanta qasa takasa cewa Komai danta manta abinda ya kawota mah tayi
KAMAL ya maida Kallansa ga LABEEBAH cikin 'daure fuska yayi furucin nashi ahankali yace bu'de bakinki tayi narai narai da ido tanasan xubo da hawaye. Yaqara 'daure fuska
Aiba shiri LABEEBAH tabu'de bakinta yasaka mata sauran sweet 'din da yake bakinsa tare da manna mata wani shu'umin kiss a wiya. Nan tasaki wata qaramar qara
wani Abu ya caki xuciyar XARAH hawaye ya xubo mata nan taficce da gudu batare da tayi abinda ya kawota ba.

Hawaye ya xubuma LABEEBAH cikin kuka Tace Ya KAMAL........
Yayi katseta da cewa ke kike da damar mallakarsa
Tayi shuru
Yaci gaba da fa'din
Wlhi daga yau kika qara min xancan XARAH ko ina tare dake kika ganta kika wani Sha jinin jikinki kin san Allah ba abinda xai hanani hukuntaki
Cikin shagwa6a tace to ya Xanyi. Yace wannan kuma ke kika sani
Tace ai matarkace koka manta kata6a Auranta harda arxiqin 'da.......
Cikin jin haushinta da maseefa ya raba kansa daga gareta ya nunata da yatsa Yace Wlhi daga yanxu kika qaramin manarta saina miki dukan tsiya
Tace toh meyasa baxa duba halin son ka da yake damunta kayi mata afuwa sai ka maida ita gidan.......
Wani wawan mari ya sakar mata wanda tunda take ba'a ta6a yimata irinshi bah
Dan haka cikin sauri ta durkushe agabansa tarushe da kuka

KAMAL ya yabi hannunsa da kallo tare dajan wani shegen tsaki. Yakama kansa cikin takaicin abinda ya aikata Yace am sorry
Tashi LABEEBAH tayi daniyar fitta daga falan yace kitemaken ki yafemin my baby.
Tayi banxa dashi. Ganin haka yasashi saurin jawota jikinsa cikin sanyin yanayi yana shafa bayanta cikin lallashi Yace am sorry
Cikin sanyin itama LABEEBAH Tace dan Nace kamaida.......
kanta qarasa yayi saurin katseta da cewa idan kika qarasa saina sharara miki marin dayafi wannan yanxu wlhi
Shuru tayi kana taraba kanta dashi sannan ta fitta daga falan
Ya bita da kallan Takaici da harara

XARAH ko dama Hajjiya Zainab CE tasata kiran LABEEBAH dan shirinta ne yarage musu
Qaddara tasata amsawa dabin umarninta
Tafitoh falo ne Sagna Tace naga tayi shashin Ya KAMAL 'daxo
gaban XARAH yafa'di har xatace Sagnan ta kirata sai kuma tafasa
Ashe da raban xatayi mummunan gani
Tafashe da kuka tanajin wani MASEEFAR SON mijin nata ga qaddarar mummunan halinta tayi mata yankan qauna.
Cikin kukan Tace Turai kin cuceni......
Sumayya dake kallanta Tace hmm Allah ya kyauta
XARAH ta galla mata harara da ficce daga 'dakin



Koda LABEEBAH taje 'dakinsu Sagna bataga XARAN ba
Nan takafa tagumin me xatace mata
Aiko tana cikin tunaninne XARAH tashigo 'dakin
Sai dai LABEEBAH ta tsinci kanta da basarwa tayi kamar basuyi Komai da KAMAL 'din a gabanta bah......

SAUBAN ne ya katse mata tunaninta da cewa menene momyna me yake damunki kikayi shuru
Tashafah kansa tare da kai masa kiss agoshi Tace Dadynka ne yake damuna SAUBAN
Yace toh meya miki. Waro ido tayi danjin ashe a bayyane tayi furucin
tayi Murmushi Tace kanajin bacci Yace eh
Tace toh xumu kwanta haka ko suka kwanta abinsu
Sai dai kuma Suna kwantawae taji sa'ko ya shiga wayarta
Nan ta 'daubah da dubawa
_momy xata baki maganinki dan a lissafina yau saura kwana uku al'adarki taxo miki plx kitemaken kifara Sha goben pls my baby_
[10:13PM, 27/10/2016] Rahamat Nalele💋: Tayi Murmushi tace abayyane Ya KAMAL
Cikin sauri tarubuta mai
_Baxan shaba_😔
Sakwan na isa ga KAMAL yayi Murmushi ya mayar mata da _ai baki isa ba. Kina sone Ki hargitsani inrasa tunanina da nutsuwata_
_tace hmm fuskata fah ta kunbura_
KAMAL ya waro ido. Cikin sauri ya kirata
Ashagwa6e tace hello
Yace am sorry my baby pls Ki kiyaye gaba banasan kiramin xancan XARAH plx
Tace to Amma......
Ya katseta da fa'din Ya salam
Cikin sauri Tace toh kayi hakuri nadena
Yace gud kin temaki kanki. Yanxu dai bani labari kina inane me kikeyi me yake faruwa
Taturo baki tamkar tana gabansa Tace ina kwance nida SAUBAN muna San muyi bacci
Yace da kyau babyna kuhuta lafiya. Am gobe xani qasar Armiyaniya ina buqatar addu'ar Ki
Tace Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lpy Yace AmEEn AmEEn
Tace Ya KAMAL......
Yace ke kike da damar mallakarsa
Tayi Murmushi Tace dama inasan sanin duk xamanka a qasar baka ta6ayin budurwa bah
Yace hmmm fa'da miki ne banyi bah. inada mata acan.
Tayi saurin tashi cikin wani yanayi Tace yanxu kana da mata kuma kakesan mallakata.
Yayi Murmushi Yace karfa Ki damu my baby tana sanki ba 'dan ka'danba
Dan Kullun xan canta gareni yaushe xata ganki. Fa'di take ina San Aunty Laveevah dan Allah kakaini gunta
Nakan ce mata xan kawota gunki.........
Cikin wani yanayi LABEEBAH ta katseshi da cewa Wlhi qarya take dan ba matar da takesan budurwar mijinta.
KAMAL ya gyara xama Yace aa fah😳 da gaske khadi take tana sanki
Cikin maseefa tace toni bana santa kuma baxan sota ba danna tsaneta...... Tana fa'din haka takashe wayan gabaki 'daya
KAMAL yayi Murmushi axuci yake fa'din bawacce xata qara gigin mallakata saike my baby ina matuqar sanki

LABEEBAH kuka tafashe dashi tsakaninta da Allah tanayi SAUBAN na tayata dan ganin kukan da take ba nawasa bane

Daqir KAMAL yasamu kanta da daddare Bayan ya qaryata kansa dace mata wasa yake mata


Washe gari XARAH na xaune agidansu takalli Innah da baba da suke karin kumallo
Tace BABA
Yace na'am
Tace dama KAMAL ne yakesan LABEEBAH
Babah da Innah fuskarsu tacika da fara'a atare sukace kai Amma ko munji da'di Kinga sai ya ha'daku tunda bakwa tare da matsala
XARAH tagirgixa kai
Tace xan cutar da LABEEBAH tabbas inna qara kasan cewa da KAMAL kamar yanda nacutar da ita a gidan YUSUF
Kuma kafin KAMAL ya 6ata na aikata mishi wani lefin da baxan iya komawa gidansa ba
Koda ko ya buqaci hakan
Innah tayi sak hakama BABAH
Candai BABA Yace toh keko XARAH wane lefi kika aikata mishi haka
Hawaye ya xubu mata tace Wlhi Babban lefine mummuna
Kuma baxan iya gaya muku ba. Dan sirrine tsakanina dashi
Ni dai ina roqarku da Allah karku saka wani abu aranku dan gane da Auransa da LABEEBAH
Cutace dai na cuci Kaina
Dan Allah ya ha'dani da hatsabibiyar qawa wacce takasa bani shawara tagari
KAMAL yayi min halacci tunda ya iya 6oye abinda namasa. Hakan yasa nima baxan iya furtama kowa ba.
Innah Tace tomu kigaya mana mana.........
Babah ya katseta da cewa aa Karki matsa

Please Login or Register in order to submit comment