Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Basu sadakar dariya abin ya bashi a fili ya Furta wonder shall never end, wannan yarinyar karfi gareta,Bai Gama tunaninsa ba yaga ta karkade jikinta tare da daukan speaker ta fara tallan maganin, yau Yaga abinda Bai taba gani ba a duniya mace ta Ware tana shararo karya maganin gargajiya,Kuma yarinya Haka har tasan su maganin sanyi Bai Gama Shan mamaki ba sai da yaji tace Kina mace bakya gamsar da mijinki sai da ya toshe kunnensa da sauri sabo da shi kunya ma yaji.
Su sukeyi shi yake Jin kunya,a idonsa yaga Khairat tana talla Kuma ta fashe da kuka sosai a titi tana tafiya idan tayi Shuru sai yaga Makahon Yana dukanta da Sandarsa,Shi dai yasan ba wani tausayi ne dashi ba Amma yaji tausayin Khairat sosai,Hanya ta gyaru Nan suka ja motocinsu sukayi gaba abinsu.

Yau Kuma Talatu ta yiwa Khairat dukan tsiya ta kwace dubu gomanta da Mutumin ya Bata,washe gari kuwa da zazzabi ta tashi me zafin gaske Amma da kanta ta lallaba taje ta siyo magani tasha,.
Sati na zagayowa sai ga Hammad ya zo da sabuwar waya Infinix me tsada ya kawowa Khairat,yau ma Haka suka gyara gidan tare da Bata kayan Zainab me kyau tasa,ita kuwa Khairat da ya Bata waya taki karba ya damu ta karba taki Karba sabo da tasan ma Su Zainab ne zasu kwace,Amma daya takura sai ta karba a kofar gida ta Shiga makwaftansu ta bayar da ajiya a sirri,Kudi ya Bata dubu Hamsim taki karba,Gashi yau Bai bawa su Talatu sisi ba,sai suka ga Khairat ta dawo ba ko sisi,Talatu tace tsinanniyar tayi halinta na bakin ciki,Khairat tace kwarai kuwa Dole sai da Sa Hannuna zaku samu to daga yau na hanashi sisi baza kuci ba.

Hmm kawai Talatu tace tana saka mugunta a ranta,Haka Hammad ya sake zuwa Bayan 4,days Bayan Nan yaci gaba da zuwa dake ya iya kalamai sai ya fara siye zuciyar Khairat ta fara sonsa abin sai gaba gaba yakeyi,ganin Haka Talatu Bata samun sisi sai tace da Usy Wanda Khairat ta tsana ya turo da iyayensa zasu aura Masa Khairat.
Kawai sai Labari taji har an kawo kudin aurenta tare da Usy, sai shirye shiryen bikinta sukeyi,ita Kuma tuni ta tsara barin gidan Baki daya,Amma abinda ya daure Mata Kai sai taga Hammad yanzu wajen Zainab yake zuwa suyi Hira ya tafi,sai daga baya taji ai Zainab ce zata auri Hammad ita Kuma za a hadata da Usy, Khairat tayi ta Rusa kuka sabo da tsakani da Allah ta fara son Hammad, Kwalar Zainab taci tana kuka tace me nayi muku?me nayi muku...me na tare muku?..kun San bakwa kaunata ku kaini gidan rainon Yara mana,..ta jijjiga Zainab sannan tace wlh duk abinda Kuka min bazan yafe Muku ba,Kuma sai Allah ya bi min hakkina,kun San hakane Zainab zaku bashi ku hadasu tun farko Mana,ta Kara fashewa da Kuka ta Gama haukace musu da karfi ta kara shake Zainab me yasa Kuka Bari na fara sonsa,why..why...sai da kuka Bari muka shaku...kuka ta fashe dashi sosai tace Kuma kun San bana son Usy ba mutumin kirki bane shine sabo da kun tsaneni zaku daura Mana aure? Me kika fadawa Hammad ya daina ko kallo na? Zainab taji Shaka tace Munce ke Yar shege ce kiyi hakuri...kauu....kake ji Khairat ta kwadawa Zainab Maruka har Uku kafin kace me kumatunta ya kumbura, Khairat ta haukace ta fara daukan duk abinda ta gani tana farfasawa tana jifa da komai,Ammar Soja dama ya zo hutu karnukansa suka Fara Haushi Khairat tasa kafa ta daki bakin Karen iya Karfinta sai ga bakin Kare ya murgude ya koma Bari daya.
Kawu ne ya fito da Sandarsa zai daki Khairat ta rike sandarsa tare da fisgeta Kawu ya tafi taka taka ya Fadi dabar,Tazo tayi jifa Da Sandar lokacin Kuma Talatu a fusace ta bude Baki zatayi magana kenan Sandar ta daki hakoranta na gaba dama wasu cako cako ne Aiko Nan take guda uku Hakoran gaba suka rushe tare da zubewa kasa Hakoran Talatu.jini yayi tsartuwa,Jin Talatu tana ta zubar min da hakora,jini...Kawu yace Khairat bar min gida bani bake Kuma na cire Hannuna a kanki,tsaki Khairat ta ja tace ka cire har kafar taka ba Hannu ba.
Dakinta ta fada ta kwaso kayanta a Leda Viva ta fito daga gidan,Zainab Kuma suka dauki Talatu sai Asibiti.
Soja ya fita yawo sai dawowa yayi yaga Uwarsa ba hakora aka bashi labari,a fusace yace duk ranar Dana ganta wlh na rantse sai na lalata Mata rayuwa daga yau Zan fara neman inda take Ido na idon Khairat sai nayi Raping dinta nayi kaca kaca da rayuwarta abinda zanyi kenan na huce.

Khairat kuwa tuni ta Shiga Makwaftansu ta karbi ajiyar kudadenta da take Tarawa idan Hammad ya Bata, sannan ta karbi wayarta sabuwa daya siya Mata Infinix ta fito ta shige Napep Bata San Ina zata nufa ba,sai zage gari ake da ita har suka zo Bakar number irin wajen gari suke a Kano ma daga su ba gida gaba ba gida Baya sai Daji.

A Nan ta sauka ta rasa Ina zata nufa sai tayi hanyar Daji tayi nisa taji kukan yarinya karama a dajin,inda take Jin kukan ta nufa a tsorace sai ko ta iske wata yarinya za tayi 3yrs wata Kyakyawa da ita Fara Tasha Kaya masu kyau da tsada sai kamshi takeyi,Yarinya sai Mama take Kira tana kuka,Tausayinta ya Kama Khairat ta rike yarinyar tace Mama ce ta tafi ta barki?, Yarinya ta daga Kai,daukanta tayi tare da goyata a bayanta,yarinya tayi Shuru kuwa ta rasa ya zatayi da yarinya,gashi taki yarda Khairat ta ajiyeta, giftawar wata mace ta gani taci wanka Yar gayu ta shige motarta me tsada ta bar wajen da gudu,Yarinya ta kwalla Kara ganin matar ta tafi ta dinga nuna motar tana Mama...Mama hakan yasa Lallai Khairat ta gane uwar yarinyarce ta jefar da yarta kuma ta tsaya ganin Wanda zai dauke ta, Gidan Mai Unguwa ta nema taje ta sanar aka fara bincike Amma ba a San Yar waye ba gashi ta nacewa Khairat kamar jela,Me unguwa da Police suka ce to za a bada sanarwa Amma Dole Khairat ta zauna da yarinyar a gidan Mai gari har na sati daya, Me unguwa yace tunda har taga uwar yarinyar ta gudu to tana sani kawai a rike yarinyar Uwarta zata nemeta da kanta.

Me Unguwa dai akwai karamci da kirki Haka matansa ma,Khairat ta Zama uwar Dole ita take yiwa yarinyar komai,Ana gobe sati daya taji me Unguwa Yana neman Wanda zai bawa hayar karamin gidansa dake Gwammaja, me daki biyu da Toilet sai kitchen gidan toilet ne kawai da tiles sai kitchen Amma siminti ne ko Ina,Khairat tace wlh Me unguwa dama Ina neman hayar gida,tayi karya Ni karatu ya kawoni Kano Yar Taraba ce,Yarinya kinyi Dace kuwa domin gidan Yana da shago a kofar gida wani Dattijo ne ya Kama shagon Yana Kasuwanci Kinga Namiji a kusa dake Security ne ba Yan iskan da zasu shigar Miki gida da niyyar cutarwa.

Murna ta kamata tace nawa ne kudin Haya na Shekara? Me Unguwa yace dubu Sabain ne Amma Dan kece Yar makaranta nayi miki sauki Nan take ta biya kudinta cash na Shekara guda,sannan ta Goya Yarinyar data tsinta taje kasuwa ta siyi katifa da resho sai bedsheet da tukane kayan cin abinci da carpet Kato tasa daya a Palo daya Kuma ba cikin bedroom dinta,ta shirya kitchen ma,da sauran kayan bukata na rayuwa duk ta siya,wayar Tata ta siyar dubu Arbain da biyar ta siyi karama ta dubu hudu tecno da layinta sabo tasa Number ta me Unguwa da number Baba Isyaku Wanda ke haya a shagon gidan data kama,cikin kudin ta ajiye wasu sannan ta siyi kayan Abinci da komai dai dai talaka,ta siyawa yarinyar data tsinta Kaya kala hudu masu araha,ta siya Mata Pampers gidan guda da panties masu araha,ta siya Mata takalmi Dana fita unguwa da slifas Dan karami,itama ta siyawa kanta panties da vest harda Atamfa Leda kala biyu ta bada dinki sai Kuma taje wajen Yan gwanjo ta zabo kayan gwanjo Riga da skert kala hudu da dogayen riguna guda uku,ta siyo mayafenta kala uku,da Hijab kala biyu masu hannu,sai ta siyi takalmin roba kala biyu da slifas na tsakar gida,Haka dai ta samu ta rage zafi,kayanta dasu ka kode ta wanke su tas, Wanda Bai yage ba ta ajiye Wanda suka yage Kuma ta watsar dasu,duk inda zata da Meenal yarinyar suke tafiya. dama Bata sa bra Bata dameta ba Amma duk da Haka ta siyi kala biyu sannan tazo ta gyara gida neat ko Ina Kal Kal.washe gari ya cika sati daya Amma ba a gano iyayen yarinyar ba.

Ranar Khairat zata koma Gwammaja da Zama gidan data Kama,ta tafi ta bar yarinya hannun me gari yarinyar ta dinga ihun kuka Dole me gari yace ta tafi da ita ta rike ta a hannunta zasu ci gaba da bincike har a gano iyayenta.
Gashi an tambayi yarinyar sunanta tace Meenal Bata San sauran ba Bata da wayon ko Sunan uwarta Bata sani ba.

Kamar yarta Haka Khairat suka Shiga gidansu Bayan ta gaisa da Isyaku dattijon daya Kama shagon kofar gida ta sanar Masa itace ta Kama ciki yace Alhmdllh Allah ya taimaka,Isyaku mutumin kirki ne matuka.
Bayan sun huta Khairat ta mike ta dafa musu ruwan wanka tace Alhmdllh na rabu da kazanta da tallan Magani,wanka tayi tayiwa Meenal suka shirya cikin kayan gwanjonsu data wanke da ruwan zafi,Zama tayi ta gyara kayan cefanenta da ta yo tayi miyar jajjagenta da kifi ta zuba musu tare da Meenal dinta suka ci tana Bata a Baki har ta koshi Bayan sunci sun Sha sai ta hau katifarta data Sha gyara luf luf ta daura Meenal a gefenta suka kwanta bacci ya kwashe Meenal ita Kuma Khairat ta fara tunanin duniya,yanzu wacce Sana'a zata yi.
Fitowa kofar gida tayi wurin Isyaku me kanti Wanda kuma a ciki yake siyar da kayayyakin kanti kuma ciki yake kwana, Zama tayi tace Baba Dan Allah a unguwar Nan wacce Sana'a kake ganin zanyi na Samu kudin da Zan rike kaina da yata kaga na kusa sata a schl Nan da 1yr ta Kara wayo Dole na nemi kudi domin inganta rayuwata data yata,.
Baba Isyaku yace Wai Wai Yar Nan wlh ban sani ba Kuma kudin sanaar Siyar da Kayayyaki kamar kayan Miya Baki da jarin yinsu Wanda har Zaki samu kudin sa yarki a makaranta da Kuma cinku shanku da sitira,aiki ne ya kamaceki Wanda za a dinga biyanki albashi,a kwai kamfononuwa da dama da suke daukan masu shara da goge goge ko Restaurant ki nemi irinsu ko Zaki samu Kinga sai ki Kara Kuma da Sanaar siyar da kayan Miya Haka su barkono,kanwa,citta,kaninfari etc,hakane Baba naji dadin shawararka Kuma na gode,Baba yayi Murmushi yace Kije Zan bincika Miki inda suke neman masu aikin shara da goge goge tunda Baki da takardun makaranta.

Washe gari da wuri na Shirya naje na Saro irin kayan da Baba ya bani Shawara na Rika siyarwa su kayan kamshi da sauran tarkace dai,a littafi na rubuta komai har ribar da Zan samu sannan na Shiga makwafta kaf na dinga sanarwa Ina siyar da kaza da kaza etc,ai kuwa Alhmdllh aka fara zuwa Ana siya.

Bayan kwana biyar tsakani Baba ya kirawoni ya sanar min Restaurant da kamfani a kalla zasu Kai biyar Wanda suke neman me goge goge da Shara.
Ranar Monday na karbo dinkunan Dana Kai na atamfa Leda dake taji dinki me kyau sai na fito das ka rantse me tsada nasa ita kuma na sa Mata Pampers da kana Nan kayanta masu kyau Wanda na tsinceta da su.
Daukanta nayi tana son ita Wai sai na sauketa,muna tafiya tana min gwarancinta Ina biye Mata kuwa muna dariya muka Isa Resturant na farko da Baba ya bani Address naje.









AsmaBaffa
[10/18, 2:49 PM] Sis Asma: 🦚🦚ME MAGANI🦚🦚







4








Official







By
AsmaBaffa






Oum Naufal,Oum Zara,Maman Khalifa,Xeee Gwanda,Khadija A Hamza,Humaira,Ameera page dinku ne.







Isar Su Restaurant kenan ta nemi shugabansu mace ce tace Nan bama bukatar me Yara,bama daukan me Yara aiki,ba tace komai ba ta fito ta tafi daya restaurant din shima suka ce basa bukata taje musu da yarinya wuri ta Kori customers dinsu da kuka, sai ta hakura ta wuce Company dake da mugun Nisa shima bata Dace ba,taje dayan ma bata Dace ba,wani katafaren Building taje abin kallo da birgewa a fili tace yanzu Naga Company me kyau, gaba daya kusan turawa da Yan China ne a ciki suke ta shige da fice,ga leburori bakaken mu Ana ta hada hada gaskiya ya Tsaru karshe ita kanta ta daga sama taga An rubuta BIN MAHMOOD KUWAIT.
Wata motace me azabar kyau ta wuce ta gaban ta suuuu...cikin Company din itama ta Shiga Securities suka taso kanta suna tambayarta me ya kawoki?tace Ogane ya daukeni aikin Shara,zatonsu da gaske ne sai suka barta ta Shiga ciki,Koda ta Shiga sai ta rasa hanyar da Zata bi ta fara wuri wuri,Wani Kyakyawan matashi ne ya fito yasha kyau ya Gama haduwa cikin Shadda Yar gaske chocolate ne me haske gaskiya guy din yayi,gaba daya Naga Ana ta girmamashi kamar za ayi Masa sujjada,shi Kuma sai wani Shan kamshi yake Yana wulakanta mutane,ganin Haka sai kharat tace wan can ne me Company din kawai,da sauri ta Karasa gabansa,kamshinsa ya bugeta me Dadi,a hankali ta rusuna a gabansa Ina kwana ranka ya Dade abinka da ta Saba talla a Tasha da kasuwanni,magana Bata wuya a wajenta,Wani tsaki yaja Yana wani toshe hanci Bayan uban wankan da kwalliyar Data ci,ko uban waye yasan kamshi yake ba wari ba,dama can rashin Sabulun wanka da wanki ne yanzu kuma tana da shi.
Tsawa ya daka mata Wanda ya jawo Meenal ta barke da kuka,kunnensa ya Dafe har ta lallasheta tayi Shuru tayi matukar fusata,yace ke kazama kun cikani da wari uban me kuka zo yi Nan? Daurewa tayi tace aiki nazo nema, what????ya furta a tsawace, sai da ta firgita Amma Haka ta durkusa a kasa tace Dan darajar Allah ko shara da goge goge ce zanyi, yawu ya tofa Mata a fuska yace God forbid bama daukan irinki dabba mahaukaciya,mu Nan masu ilmi muke dauka ko masu shara ne to sai suna da takardu,Allah yasa Khairat tana da zuciya ta mike a fusace ta ajiye Meenal dinta a gefe ta cafki rigarsa.

sannan ta goge yawun daya tofa Mata a saitin goshinta,ta goge tas Yana kallon ikon Allah sannan Taci kwalarsa tare da tsarge Masa Riga gida biyu,tace ba a haifeka ba,wlh kayi kadan, Kuma Kaine dabba jahili duk abinda suke akan idon ainihin me Company din,yazo da jerin motocinsa kusan guda biyar rantsatsun gaske,Khairat ta nuna shi da yatsa tace Kai kayi kadan baka Isa ba Kuma ba a haifeka ba, who do you think you are? I wl definitely teach ur a Good lesson Wanda mace ma sai ka tsaneta,Yar Tasha ce Ni bani da mutunci wlh yanzu Zan tozartaka a idon duniya dakiki, Mutanen leburori sun cika suna kallo farin ciki ya cika musu zuciya,dama ya Addabesu Company ba nasa ba Dan kawai an bashi Secretary shike Nan yake ciwa kowa mutunci.

Azababen Handsome guy ne ya fito kamar balarabe ga kyau ga sura gashi fari har wani Jaja yakeyi,hutu da Naira sun ratsashi, ga iya taku duk inda kake neman me kyau ya Kai,Mamaki ya kamashi daya ga ya San yarinyar ma Me Magani ce wacce ya taba bawa Sadaqa tana fada da Babanta,ya tabbatar zata aikata Bata da mutunci tunda yaga ta danne Makahon babanta Akan kudi Kuma talla takeyi da speaker na batsa ai ta Gama cika sharudan rashin tarbiya, yasan abokin nasa bashi da mutunci,Bai San darajar Dan Adam ba Amma wannan yarinyar ta fishi tashanci Yana zuwa wurin ya dauke Khairat da mari,Meenal ta tsage da kuka,Musaf je ka saita kanka kana gani Ana kallonka jikinka a waje mace tayi ma Haka kana tsaye Nonsense,A fusace Musaf yace sai na ga karshenki a duniya sai na wulakanta ki sai na sa kin tsani zuwanki ta duniya,Khairat tace ka Dade bakayi ba,Allah nake tsoro ba Kai ba,Kai din banza me ka Isa kayi min,Wanda aka Kira da Musaf Yace mu zuba Ni da ke,ya juyo ya kalli Handsome yace Hunaif Bin Mahmood idan ka daukeni abokinka na kwarai ka bawa yarinyar Nan aiki a Nan tana goge mana Office da Shara,duk Office dake Building din Nan ta dinga goge su,Hunaif Me kyau yace Ni na tsaneta wlh cewar Hunaif, Musaf yace Kawai kayi min wannan abinda nake so kenan sai na nuna Mata waye Musaf.

Khairat tana tsaye Bata Jin me suke fada domin kasa kasa suke maganganunsu,Khairat ga kuma fa Ammar Soja na nemanki wanted kin zubarwa da uwarsa hakora gashi kin hadu da Musaf duk Baki San mugun nufinsu ba.,
Musaf ya juyo ya kalli Khairat yace Zanyi maganinki,da karfi Khairat tace ka Dade baka yi ba,in ka fasa baka kaunar Allah, Ido suka hada da Hunaif gabanta ya Fadi Haka kawai take Jin tsoronsa Amma duk da Haka ta fara kuri a wajen tace ni zai rainawa hankali Akan ya ganni a sadaka wani wurin nema na akeyi da kudi ma ba a samu ba kamata Ni Khairat Muaz Wanda ya zauna lafiya shi yaso yawwa a tsaye nake Kar nake kallon kowa ehe.

Dariyace ta kusa kwacewa Hunaif Handsome yanda take tsokalo Dan mitsilin bakinta, gobe kizo ki fara aikin 9am zuwa 5 ake tashi,albashinki 15k a wata.
Farin ciki ya kamata Jin har dubu Sha biyar,tave shegu masu restaurant ku rike abinku naku ma dubu biyar a wata to gashi Allah ya kawoni inda ya linka naku sau uku,harda wani Wai basa son kukan Yara waye waye.... Yan..Yan...Yan..kina da yarinya bla...bla..bla...stupid people,shi dai Hunaif Yana jinta abinda takeyi dariya abin yake bashi,sai ko yaji ta fara koro Masa adduaointa daya Fara ji lokacin da ya Bata sadaka,Fari me farar Aniya kaga Wanda ya gaji arziki ba taka haye ba Musaf talaka,Allah ya Kara budi ubangiji Allah ya Kara lfy da nisan kwana,me arziki Bai gaji tsiya ba,Allah yasa ka rabu da iyayenka lfy,yanda ka taimakemu Allah ya taimakeka,farin gani farin Alheri,shi kuwa Hunaif dadin kirarin Nan yake ji yarinyar Nan ta Gama gogewa a Tasha da tallan magani Haka yake furtawa a ransa.

Musaf Yana labe Yana jinta yaja kwafa ya koma Office dinsa Riga a fece,leburori su kansu dariya take Basu yarinya da iya dadin Baki Kuma ta samu dai dai ita ogan nasu Hunaif akwai son girma akwai son a girmamashi,a yabe shi sannan akwai son ayi Masa Addua ga yarinya ta Gama ganoshi.
Lifter ya Shiga ya haura sama inda Office dinsa yake,ita Kuma Khairat ta fito tare da Shiga Napep tayi gida abinta tana dauke da yarta ta tsintuwa Meenal.

Tana kan hanyarta ta komawa gida ta iske mutane Sunyi dandazo kusa da gidansu Ana lekawa, wajen taje sai taga Wani yaro ne Kyakyawa fari dashi Amma ba can ba,da Alama an yayeshi ne ta karfi Yana ta uban kuka an rasa me shi,Ga mutane kowa yace bazai dauka ba,Police ne suka zo aka nemi Me unguwar unguwar suna tattauna yanda za ayi cigiya ko za a samu me shi,Khairat kuwa wajen police taje tace Dan Allah idan ba a samu iyayensa ba zanyi signing na daukeshi Ina so Zan rikeshi tsakani da Allah ga gidana can sannan Ina da kwakwaran aiki a Company,Dpo yace gaskiya kina da imani idan ba a ga iyayensa ba za a Baki sannan hukuma zata dinga bibiyar rayuwar yaron.
Da sauri Khairat tana Murmushi ta Furta ba komai hakan Yana da kyau,Yan Sanda suka tafi da yaro tare da me Unguwa, Khairat Kuma ta Shiga gidanta lokacin Meenal tayi bacci.

Kwantar da ita tayi ta fara kici kicin dafa Abinci ta Gama ta Kara gyara gidanta sannan tayi wanka ta mikawa Baba Isyaku Abinci ya karba kuwa Yana ta Godiya yaji dadin girkin a ransa sai Santi yakeyi a fili yace tunda yarinyar Nan ta sauka kullum kamshin girkinta sai ya cika min ciki.
Khairat tana zaune tana bitar karatun Quraninta Meenal ta tashi tana cewa Mama..Mama Khairat tace gani Nan ta dauketa sannan ta hada ruwa tayi Mata wanka tare da shafeta da mai Vaseline ta Sa Mata Yar vest ta Shan iska da wando Dan shot sannan ta zauna ta Bata Abinci da ruwa da kanta har ta koshi sannan ta zauna tayi Mata kalaba me kyau da beat yarinyar Tasha kyau dama gata da Gashi dama.
Karatun Qurani take koya Mata yarinyar ga brain ga wayo.

Washe gari da wuri Khairat ta shirya kanta tare da Meenal 9:00am tana Company zata Fara aikinta.
Tana shiga wani Aminu Wanda shine ke kula da tsaftar Company ya tare ta da faraarsa yace sannu,yawwa Ina kwana ta gaidashi da faraa sannan ya zaga ko Ina da ita wurin Maaikata maza da Mata suka gyaisa tare introducing kanta, Meenal tana baccinta Aminu yace kawo Yar taki na tayaki daukanta,da faraa ta Mika Masa ita ya sabata a kafada,iya shara da gogenki ko wanne Office ne Banda compound ko wani waje,Office uku kawai Zaki wanke musu har toilet sauran Office din akwai masu yi,Office din Hunaif me Company din kenan,sai na Manager,da Secretary Musaf Wanda kuka yi fada jiya,Ok Khairat tace,Bazan boye Miki ba Khairat jiya kin burge mutane da kika yiwa Musaf Haka Amma yanzu Shawara kibi a hankali bashi da Imani ko kadan,Baya kaunar Hunaif Amma Hunaif yaki ganewa,duk wannan Company da kike gani duk abinda Musaf yace shi akeyi,ko cewa yayi Hunaif ya kori wasu korarsu akeyi,abokinsa ne kut da kut ma Kuma Yana Masifar kaunar Musaf,sai abinda Musaf yake so sabo da Haka ki kiyaye Musaf idan ya rasa Abinda zai Miki kiji haushi to wlh ko mene ne zai iya yanda zai tarwatsa rayuwarki.
Tsoro ya kama Khairat tace to Ni dai Bari na fada maka gaskiya ban San Hakuri ba idan aka zalunceni ba mutunci na sani ba,bana iya controlling Anger Dina ban San sanda nake ramawa ba,Kuma Ni nafi Jin Tsoron Hunaif Akan Musaf Amma tunda kace Haka zanyi kokari na danne zuciyata ko yayane iya karkari idan ya zalunceni da yawa na Dan Masa zagi ko biyar ne ai yayi hakan ko?
Aminu ya kwashe da dariya yace tab wlh da ki zagi mutum gwara ki Duke shi,ai na iya kokawa,Aminu yace so kike ki rasa Mijin aure kina fada da maza? Khairat tayi Murmushinta Wanda ya tafi da Imanin Aminu ya tsaya tare da kafe ta da ido kuriii,Khairat ce ta katse Masa tunani da Ni wa zai so ni a Haka,yanda muke talakawa Marasa galihu,ba wata kwalliya na iya ba,me neman irinmu ya aura ai sai irin masu gadi ko masu Dako,shi yasa ma ban damu da nayiwa kowa kirki ba,ko wani na Zama nutsatsiya saliha ban ko damu ba sabo da ba Miji nake nema ba,bama na neman a aureni,Baki bude Aminu yace to Haka Zaki Kare rayuwarki? Yafiye min Dadi ta Furta da sauri,Shi ya rakata kowanne Office ta share tare da gogewa Neat,Office din duk sun canja tsari sun Sha uban kyau kamar me sai kyalli ko Ina yake musamman Office din Oga Hunaif, Aminu ya Mika Mata keys din yace ga naki ki rike kullum dasu Zaki dinga zuwa da kinzo sai ki fara aikinki yau na rakaki kinyi na farko,sai kije ki huta

Please Login or Register in order to submit comment