Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa idan ya Matsu yazo gidansu tayi Masa Amma baza ta dinga zuwa gidan namijin da ba muharraminta ba,sannan ita Bata da aji ne da zai na kiranta taje in ya Matsu yazo wajenta.
Ladi tace kinyi dai dai Yar Nan,Tayi tunanin bazai zo ba,5pm sai gashi a Tasha wurin sanaarsu,Khairat tayi mamaki ta bude motarsa ta Shiga suka tafi gidansu kamar gidansa ya wani shige Palo shine a gaba,ya zauna a kujera,ita Kuma ta Shiga kitchen abinta, zo ki kunna min tv, Khairat ta fito tana cika tana batsewa ta kunna Masa tv sai ta Kai Masa Chanel na cartoon tayi tafiyarta,canja Chanel yayi Yana kallon Ball,tana kitchen tana girkinta.

Kankanin lokaci tayi masa me shegen Dadi tasan Yana son Kwai da su tumatir ta yanka komai yayi kyau ta fito ta ajiye Flask da plate a gabansa tare da kawo fork dasu Yaji da mai,.
Serving Nasa tayi yanda yake so yayi mamakin da tasan Yana son Danwake da kwai dafaffe,Ya kalleta da mamaki yace Dan Allah munyi soyayya Haka? Na taba cin girkinki? Kina min Danwake Haka? Taya Kika san abinda nake so?
Khairat mamaki ya kamata itafa gaskiya mutumin nan Yana Raina Mata hankali,Harararsa tayi tace ae munyi zaka aureni ma ka yaudareni ka fasa,Murmushi ya saki yace Ni din? Kamarki yarinya Haka dake me zaki iya na zaman aure?
Fushi Khairat tayi ta shareshi Yana cin danwakensa Yana Santi yace Ke a Ina kika koyi girki Haka? Khairat tace a gidan iyayena,wannan fa? Ladi Antynki ce? Khairat tace kafa San komai nawa sau nawa Zan baka labarin tarihina,wannan kawai haduwa mukayi nake tayata aiki tana bani Abinci da wurin kwana,Me ya kawoki Abuja? Khairat ta kalleshi tace a Kano nake Karuwanci aka kawo Ni na gudu,Dariya Hunaif yayi yace uhm Yar yarinya dake wa zai kulaki a karuwancin? Khairat tace kai yaro wlh baka ga yanda ake rubibina ba amma Ni ba Yar iska bace na gudu,Samari ne Dani ko Ina Baja baja,kawai Ni bana son kowa ne Amma da tuni Ina da Yara kamar biyu ko Uku,dariya ta Kama Hunaif.
Serious ya Zama yace Ina so Zan fada Miki wata magana,Khairat ta nutsu tace Ina jinka,Yace na Samu matsala bana iya tuna abinda ya faru last yrs zuwa yanzu Yana fadin Haka sai yayi Shuru ya kasa tsayawa yayi Mata bayani cikakke,Khairat kawai sai tayi tunanin rainin hankali zai Mata tace to Allah yaye ma matsalar Amma Bata yarda ba.

Bayan ya Gama ci ya zaro kudi da Bai San ko nawa bane ya mikawa Khairat Kai ta girgiza tare da cewa na gode kyauta na maka,yayi yayi ta karba Amma taki Dole ya hakura ta rakoshi sun jera suna tafiya yace Kinga me kyau kin nace min,da sauri ta kalleshi dama Dan ya tsokaneta ya fada,tace yanzu Ni na biyoka gida ko kaine,? Sai Kuma tace kayi hakuri fa mu Nan bamu da giya ka Gama cin Abinci baka Sha ba,da na sani na siyo wiwi na maka shayinta.
Da sauri ya Kalli Khairat ya akayi tasan da Yana Shan giya da Shayin Wiwi? Yanzu tunda ya samu matsala Sam ya daina Sha ya tuba ga Allah baya Shan komai,Amma da yasan Yana Sha,a Nan ya tabbatar Khairat ta Masa farin sani,wata mota ce ta shararo tare da dalle musu Ido da haske.

Da Sauri Hunaif ya dafe kansa kwakwalwarsa na juyawa yuuuuu.....sai ya tuno farkon ganinsa da Khairat tana tallan magani ya Basu Sadaqa,sai da taje Office nasu neman aiki,sai rayuwar da sukayi a Company, daga Nan ya tsaya a tunaninsa,Bai tuna yace zai aureta ba, da Kuma zuwa gidan Khairat da yayi.
Khairat ta tsorata Jin Yana Nishi ya dafe Kai,tace lfy? Yace lfy Lau Bari na Baki labarin me ya sameni,Tiryan tiryan ya bawa Khairat labarin Hatsarinsa da abinda ya sameshi baya iya tuna abinda ya faru na last year,sannan Memory nasa baya ajiye komai,yace yanzu na tuna na taba Baki sadaka kina Tallan magani da Kawunki,kinje Office dinmu neman aiki,sannan munyi aiki tare, Kuna yawan fada da Mus'af frnd na.

Khairat taji tausayinsa Hawaye ya zubo mata ta matsa kusa dashi tace sannu kayi hakuri Dana kasa Fahimta,Baki da laifi Inshallah Zan koma normal.
Allah yasa cewar Khairat tana murmushi yanzu ko ba komai ta daina Jin Haushinsa,Bayan ya tafi ta koma gida cike da tausayin Hunaif.

Washe gari Khairat da wuri ta Kira Hunaif lokacin Yana Office tare da Mus'af tace kana ina? Yace Office,Ina son ganinka yanzu idan ba damuwa idan da matsala Kuma watarana...no Ina Free kizo ya Furta da sauri Kar ta fasa zuwa,wata macece ta shigo Office din tayi magana Khairat kishi ya taso Mata Jin Muryar mace na magana da Hunaif dinta,Tace wace wannan?budurwarka ce? Murmushi ya saki yace secretary nace, idan kana busy....ya katse ta da no bana busy kizo ko nazo?kina Ina? Gani zanzo Office naka yanzu,ok sai kinzo yace Mata.

Mus'af yaja tsaki Wai wace kake wani rawar jiki a kanta Haka,jiba yanda kake zubar da kimarka kana wani azarbabin tazo? Haushi Kuma Musa'af ya bawa Hunaif Akan me zai na wani Jin haushin Khairat,shi Akan Haka zasu Bata da ko waye. Khairat kuwa Office din ta Shiga bako knocking ta Shiga da Sallama,Hannunta dauke da Leda Fara me kyau.
Mus'af ganin Khairat ce sai yaji kamar yayi hauka,gashi wani son Khairat yake ji,Khairat ganin Musaaf sai taji tsoro sabo da rannan ta Masa rashin kunya da kyar ta dake ta Karasa gaban Hunaif Yana kujerarsa.

Ina wuni? Ta furta,Hunaif ya amsa kawai, Mus'af Kuma Bai kulata ba itama Bata ko kalleshi ba ta mikawa Hunaif ledar,yace Mene a ciki? Murmushi tayi tace Gift ne naka ne,da sauri ya bude ledar tare da dakko Katon kwali guda biyu ya bude babban Riga t-shirt ya Ciro Fara Kar me tambarin Sky blue a gaban rigar,ta hadu sosai me tsada ce ta Kai dubu Bakwai,Murmushi yakeyi kawai,sannan ya bude na buyu yaga zoben azurfa me shegen kyau na maza,gefe Kuma Perfume ne Gucci, dagowa yayi suka hada Ido da sauri tayi kasa da kanta tana Murmushinta me tsada.

Yace Thank you so much,you are welcome ta Furta tana Wasa da yatsunta,oya zo ki saka min ring din da hannunki,Kishi ya Gama kashe Mus'af kansa ya sadda kasa Baya so ma ya gani,Khairat ta rike Hannun Hunaif tare da Sa Masa ring din a babban yatsansa ya Masa Masifar Kyau. Ya Kara Furta tnx,tace na tafi,Tsaya na rakaki suka fice tare da Hunaif Mus'af takaici ya dameshi dama shi ta bawa Rigar da ring din,Yana bakin ciki Hunaif yasa kyautar Khairat kawai sai ya sace Gift din Baki daya,Ring ne kawai dake Yana Hannun Hunaif,a motarsa ya jefa Gift din ya dawo Office din yaci gaba da Jiran Hunaif.

Hunaif kuwa Suna tare da Khairat baya so ma su rabu da juna duk da cewar yasan Kawai mutunci sukeyi ba soyayya ba, a gefen titi suka tsaya suna Hira,ya kalli Khairat yace me kika fi so a yanzu? Karatun boko,naga Yan uwan Mamata da Abba na, Nayi aure..Hmmm yace kawai,taci gaba sannan Na siyi katuwar mota Ina yanga, sannan gidan Mijina na dauki Yan aiki Ina bada doka da Order,sannan Nima na dinga aiki a katon Office me ac da kamshi.
Yace banji kina lissafo biyayyar da Zaki wa mijinki ba, tab Namiji ai ba Dan goyo bane,duk wacce Naga ma ta Goya Namiji sai na sata ta saukeshi ta sakeshi ya kwala kansa da kasa,dariya Hunaif ya Shiga yi,tace Yana daka min tsawa Zan daka Masa shima na zare Masa ido,Me mazan suka iya a zamanin Nan sai a auri mace a kasa ci da ita,Ni fa bazan Bata lokacina Ina lallaba miji ba,Ko wani waye waye,Kuma ba mutunci ba daga kafa jambaki sai ya siya,Kuma bazan Bari ayi mini gara ba Dan kar ma zuciyarsa ta mutu, gara tana karewa ya sakeni,Wanda kika Raina zakiwa ya kyaleki yarinya,Amma idan nine ko tari baza ki iya ba abinda nace zakiyi,Khairat ta tafi tunani tace ba sai na dinga Addua ba kullum na mallakeka, nifa Nan daka ganni mutunci Bai wadaceni ba,Ina bacci aka raba mutunci,sai da safe Dana tashi aka ce ya Kare,Dariya Hunaif yayi tare da cewa ke kurin banza ne dake bakya iya komai sai tsoron tsiya,wlh Kika yi Wasa sai na aureki Naga iya karshen rashin Mutuncin naki da kike fada,Khairat tace to idan ba tsoro ba ka aureni a gani, Hunaif yace an Gama ki bani Nan da 2mnths,Yayi nisa Ina laifin 3wks ma a daura,yace to an Gama yarinya,Khairat Bata yi tunanin Hunaif da gaske yake ba Sam Wasa take Masa ita.

Mus'af ne ya fito da motarsa zai tafi ya gaji da jiran Hunaif Yana Fitowa ya iskesu gefen titi sai dariya suke suna Hira,Glass na motarsa ya sauke yace kaji kunya da wannan kazamar ka tsaya a titi ana kallonka,Khairat ta Kalli Mus'af sai ta Masa Dakuwa (Ambola) tace kaga ta tuwo kaga ta Miya kaga ta tattasai da tumatir who are you?
Mus'af maimakon ta bashi haushi sai dariya ma data bashi wannan zagin nata tun suna Yara yasanshi.

A taxi Hunaif ya sata tare da biyan Drop sannan ya koma Office,Yana Shiga yaga ba gift tabbas yasan Mus'af ne ya sace,ran Hunaif yayi Masifar baci, Akan ka taba kayan Khairat gwara ka cinye Masa milliyoyin kudi,mota ya Shiga a fusace yabi Bayan Mus'af Wanda tuni Yana Palon Ummi,Yana Shiga bako sallama ya shaki wuyan Mus'af sosai ba Wasa idonsa yayi jajir yace ina abinda Khairat ta bani? Mus'af yayi Masifar mamakin Hunaif da fushi haka,rabon da yaga Hunaif a irin wannan Hali tun mutuwar Abbinsa,Tsoro ne ya Kama Mus'af yace Yana motata dama dakko maka nayi Zan kawo maka gida na Adana maka su.
Hunaif yasan karya yake a hasale yace bani kawai karka Kara taba min Abu wlh Akan Haka zamu Bata har abada.

Dadi Ummi taji da Hunaif ya fara gano Halin Musa'af,Ummi tace haba Hunaif Kai da kake me hakuri me ya hadaku?
Ummi Kinga shine Baya son zaman lfy,Ina ruwansa da yarinya tunda ya ganta ya tsaneta kullum Yana zaginta kawai fa Ina sanin me nake domin ko Mene indai akanta ne bana mantawa,ya ganmu tare Kuma ya damu yarinya,da dama Yana min Abubuwa kawai kyaleshi nakeyi.
To kayi hakuri ga kayanka Nan ma ya dakko maka cewar Ummi,fisge ledar Hunaif yayi daga hannun Mus'af, ya Haura Samansa a matukar Hasale.
Mus'af kuwa wani mugun kallo yake bin Hunaif dashi tare da Ummi,shi kadai yasan irin muguntar da yake hadawa.

Talatu Ana titi tare da kawu a kasar Kenya Ana zuba bara wata Trailer ta kwace driver Yana bacci ta taho Kan mutane saura kadan ta talitse su Kawu Amma duk da Haka ta fyallar dasu sun daki wata Taxi daga Nan Basu sake sanin inda suke ba,sai ji Talatu tayi Ana kwanta karki tashi cikin harshen turanci,Tana bude Ido ta ganta saman gadon asibiti tare da kawu shima a nasa gadon,kudin da suka Dade suna Tarawa ta duba taga Babu ko sisi barayi sun sace lokacin da basa hayyacinsu,kawai sai gani Nurses sukayi Talatu ta rushe da kuka,Tunaninsu Zafin ciwo ne,ai tuni suka Danna Mata Allurar bacci,Kawu kuwa Makaho Yana farkawa ya fara Khairat Allahumma Tafatsinini a kanki,Shima aka tsira Masa karfen nasara sai Shuru kake ji Sunyi baccin Dole.
Da yamma Talatu ta farka tana tashi ta koma kamar mahaukaciya ta Fara Kenya Allah ya tsine muku,Mutanen Kenya Allah wadaranku,Kenya tsinannen gari,wayyo gwara na Mutu na huta,Da kyar aka samu Talatu tayi Shuru,Kawu Yana farkawa tace an sace Mana kudi ta rushe da kuka, Nurses suna Bata hakuri da yaren Kenya Talatu tace kunci ubanku tsinannu bakaken Banza, Kawu Kuma cewa yake ku kyaleta tayi Kuka,Talatu Yi kuka kinji ko kyaji sanyi,Nima kukan zanyi yanzu, wlh da a Hannuna Kahon busa tashin Alkiyama yake da tuni na hura shi kowa ya mutu a tashi duniya a huta,Talatu tana kuka tace ai wuta zamu Shiga,Khairat Bata yafe Mana ba,hakkinta ne yake binmu da halayenmu Marasa kyau,Kawu yace ah na tuna bana Hura kaho ba..Harara Talatu ta zuba Masa tace maza kayi sabo Masifar da muke ciki ta karu.

Talatu kullum suna asibiti Yan Kenya sun rasa wanne yare takeyi Amma zasu ji tana Allah tarwatsa kasar Kenya ya tsine musu,sai dai suyi ta Basu hakuri da turanci,Ana kawo musu bill na asibiti Nan take Talatu ta yayyaga takardar ta cafki wuyan Nurse din da kyar aka raba su,Masifar Talatu tasa Dole suka sallamesu kyauta ba tare da sun biya sisin asibiti ba.
Tunda suka ci gaba da bara ganin Yan Kenya basa Jin Hausa sai Talatu ta koma wakar bara da Allah ya tsine muku Yan Kenya....Kenya Allah ya tsine muku Yan Kenya ..Haka take ta rerawa tana langabewa, tunanin Kowa Addua takeyi da wani yaren tana roko,sai suyi ta Basu sadaka Talatu suna caskar Naira.
Wani Dattijo Dan Kenya yayiwa Talatu magana da yarensu Wai Yan Nigeria ne? Talatu da sauri tayi gwari gwarin turancinta tace yes yes mu from Nigeria can Kano stase (state), Mutumin yace Uhmmm,Dan Talatu ta birgeshi ya taimaka musu sai Kawu yace kice yazo mu tafi Nigeria yaci abinci me dadi.
Talatu kuwa tace mu damu da Kai You muje to Nigeria eat shinkafa da wake,Dankali,da rogo eat Food Dadi, mutumin Bai gane me Talatu take nufi ba,ganin yanda take wani washe bakinta ba hakoran gaba sai ya harareta yayi tafiyarsa.
Sabiu yace shashaSha Haka ake turancin duk kin damalmale da Hausa me zai gane,Ni Bari mu hadu da wani a hanya kiji yanda ake turanci.
Talatu tana sani Dan ta kure Kawu sai ta tare wani Dan matashi,tace bismillah Kawu Sabiu Nemo Mana taimako ga yaro Dan Kenya, kace yasa a maidamu Nigeria da harshen turanci tunda ka fini iyawa. Kawu ya gyara tsaiwarsa tare da yin gyaran murya ehem..ehem....







Jinjina gareku masu Sharhi akai akai kun wuce kyautar page,Allah ya biya.
Maman Nauwal
Precious Baiwar
Aisha Saleh
Mmn Khairat
Farida yusuf Bashir
Hafsy
Khadija A Hamza
Momy Suraj
Maryam Babu gumel.







AsmaBaffa
[10/18, 2:52 PM] Sis Asma: 🦚🦚ME MAGANI🦚🦚









46-50









Official








By
AsmaBaffa








Fans din kwarai Ina godiya
CHOICE,MRS ABDULWAHAB,BALKISU,HINDA ABUBAKAR,FARIDASULAIMAN 130,RAHMA ADAM UMAR,MAMAN ABDALLAH,KHADIJA GIDADO,ZAINAB BAYERO,ACERYER LAME,HAFSAT SOKOTO,AMINA SADA(MAMAN JIDDA).



Page naku be

DR HUMAIDA,BALKISU ISHAQ,MRS FAROOQ,FATEE BENI,MRS BAKARI,MMN WAHEEDA,FAUXEEY, and FATEEMA XARA.








Kawu yace Ehem...we Devil enter car come Kenya, so yake yace sun hau motar Aljanu an kawosu Kenya,Matashin tsaki yaja yayi tafiyarsa,Talatu tana ta dariya tace wlh gara Ni ai Kanka,ba abinda ka iya ai Kaine Devil din.
Suna Tafiya suna bara katsam sai Talatu taji wani Yana waya da yaren Hausa,da sauri taje wajensa tace sannu Malam Kai bahaushe ne Dan Nigeria,mutumin yace ae Dan Kaduna ne Ni sunana Ibrahim,Talatu ta fashe Masa da kuka tace bawan Allah ka taimakemu Nan ta bashi labarin yanda suka zo Kenya,yayi mamaki nyace Ina passport naku? Talatu ta nuna Masa,yace to kuzo muje wurin police na tiryan Ibrahim ya Kai su Wurin Police akayi musu shige da fice sannan aka kaisu wurin Shiga jirgin ruwa zuwa Lagos.
Murna kamar zasuyi ihu,suka dinga godewa Ibrahim ba adadi,dala dari ya Basu yace idan kunje Nigeria ku canja doller dari din sai ku Shiga motar kano.
Talatu sai Godiya takeyi suka Shiga jirgin ruwa suka taho Nigeria,Kawu yace Makkah Amma ko jirgin sama bamu gani ba daga mota sai jirgin ruwa,Khairat kwai muguwa.
Talatu tace ka godewa Allah wlh Tam.


Kwana biyu Khairat Bata siyar wa da Ladi Kati sabo da yanda Hunaif ya hanata sakat kullum ya kirata a waya,ko yazo su hadu suyi fada suyi Hira.
Kamar Wasa Hunaif suna tare da Khairat a jikin motarsa unguwarsu sai kansa ya Sara ya rike kansa sai ya fara tuna baya tsakaninsa da Khairat,har sanda ruwa ya taso ta Shiga motarsa,da zuwa gidanta da yayi,tare da yaran Nan Mohd da Meenal,har shirye shiryen auresu kaf ba abinda Bai dawo Masa ba Amma iya abinda ya shafi Khairat da shi,sauran abubuwan baya tunawa, farin ciki ne ya mamayeshi Wanda har ya kasa dannewa sai Murmushi yakeyi ya riko hannun Khairat ba zato,yace Kece Khairat wadda naje gidanki har naci Danwake,nace Zan aureki,na Baki takardar Rules,sannan na dauki Meenal da Mohd na kaiwa Ummi,Ummi Kuma ta bawa sister nata yaran sabo da matsalar Dana samu,Khairat farin ciki ya kamata da ya tuno da komai yanzu,da sauri ya rungume Khairat Kam a jikinsa tare da kissing nata a lips,da kyar ta kwace kanta badan ta so hakan ba,ya kalleta still Yana rike da hannunta yace Address din danginku da Kawu ya bani Yana Nan Zan dakko muje garin naku ki shirya muje Saturday,Kuma aurenmu Yana Nan baza a fasa ba duk da cewa ba soyayya muke ba,Zan aureki in kin Amince? Khairat tace na Amince,Khairat a ranta tace muje zuwa.

Saturday da wuri suka shirya ya turo Driver ya dauki Khairat ya kaita Aairport zasu wuce Taraba state, wasu Arabian Riga da skert ya bawa yaronsa Usman ya kawowa Khairat masu Masifar tsada,sai Kaya kala uku Suma ready made sun hadu Wai tayi Shirin tafiya,Murna wajen Khairat ba a magana,kicif ta shirya Yar Jakar daya Aiko Mata ta Yan gayu komai na bukata ta zuba, ta shirya cikin Arabian Riga da skert tayi bala'in kyau sosai light blue and black color,Haka takalmi da jaka ma same color Wanda Hunaif ya kawo,Ladi tana ta kodata gaskiya kinyi kyau Khairat karfa ki zautar da yaro,dariya tayi kawai sukayi sallama da Ladi ta Shiga rantsatsiyar motar Hunaif da Driver yazo daukanta.

Tana zuwa Airport ta hango Hunaif da ruwa Eva Yana Sha Yana Danna waya,gefensa Yar karamar Jakar maza ce ta manyan Yara ya hade cikin Shadda light blue da takalmi Baki agogonsa Baki dama Bai fiye sa wata hula ba,Suma taci kudi sai sheki yakeyi,Khairat wani nishadi take ji sai wani fara'a takeyi,ji take kamar tafi ko wacce mace duniya,Nan kanta ya Kara girma,ta Fara yanga da gadara tana taku dai dai kamar wacce zata tafi England,tun kafin ta karaso wajensa da kyar ya gane Khairat sabo da tsananin kyan data yi, kamar balarabiya,sai yaji ta Kara birgeshi Bai taba ganinta da kwalliya Haka ba sai yau.
Murmushi yake saki shi kadai tana karasowa ya sunkuyo tare da leka Fuskarta Yana dariya yace kwalliya Kika yi min? Gaskiya na iya zaben Kaya,Khairat tayi Murmushi tace ai wacce tasa kayan ita ce me kyan ba kayan ba,dadina dake kuri da yabon Kai cewar Hunaif,yarinya kinyi dacen miji Dan Umminsa, kafin ya rufe Baki tace kaima kayi dacen mace Khairat marainiyar Allah zankadedediya son kowa kin Wanda ya rasa,Murmushi ya saki suka tafi aka musu Screening tare da shigewa jirgi,Khairat gata ga Hunaif sit dinsu su kadai,Kamshi kawai suke musamman Hunaif sarkin kamshi,Khairat an Shiga jirgi yau harda zaro Qurani a jaka ta Fara karance karancen adduoi Allah ya saukesu lfy,Hunaif ya kalleta ta birgeshi Yana son mutum me addini da yawan addua.

Mintuna kadan sai gasu a Taraba,Ashe tuni Hunaif yasa an shirya Masa lafiyayyar mota tare da driver Dan garin Taraba Wanda yasan lungu da sako a garin, Khairat ta kalleshi a ranta tace kudi masu gidan nara,ko me kake so indai da kudi an Gama, ita kanta abar motar abar kallo ce,baya ta shige kusa Da Hunaif sabo da kamshi da sanyin dake motar a fili Khairat tace Naira maganin masifa da Jarabar duniya,Naira masu gidan nara.
Hannu ya Mika ta tare da Furta bani Address note din naki uwar surutu.

Yar takardar data rubuta Address din da Kawu ya Basu ta Mika Masa shi Kuma ya mikawa Driver,Ido Driver ya zaro yace tab Kauye ne sosai kafin muje kauyen sai munyi kusan 4hrs,nisa ne da garin,idan zaku ci Abinci ma ya kamata kuci tun muna cikin gari,Hunaif yace muje kawai bama Jin yunwa, a'a nifa bana jure yunwa Allah ya gani sai naci na koshi nake iya tafiya cewar Khairat, Dole aka tsaya a wani eatery na manyan yara suka yi take away sannan suka dauki hanya.

Daji ne sosai suka Shiga abin tsoro,Khairat tsoro ma takeyi Kar matsala ta samesu a Dajin,suna tafiya Sunyi rabi Motar tasu Haka kawai ta mutu a Dajin,Karfen nasara ba tabbas,Tsoro ya Kama Khairat Amma Driver da Hunaif ko a jikinsu,anyi anyi motar ta tashi Taki,Hunaif Yana fita Khairat ta fice da gudu ta makale kusa dashi kafa ya motsa sai ta motsa,Driver yace mota sabuwa dal kawai ta mutu karfen nasara,suna ta gyara Driver da Hunaif Amma taki ko motsi har Magrib ta wuce,a wurin sukayi Alwala da salloli sannan suka ci take away nasu.

Sallaya Hunaif ya dakko tare da Shimfida musu shida Khairat a gindin bishiya ko Ina koren ciyayi luf luf fresh air na kadawa,Driver Yana can jikin mota Yana fama ta tashi taki.
Dare yayi 8pm Bayan Sunyi sallar Isha Tsoro da bacci ya Kama Khairat tana gyangyadi Hunaif na gefenta Yana latsa waya sai ji yayi ta Fado jikinsa,dama ya Santa da bacci duk inda ya kamata a Nan zatayi,Murmushi yayi Yana karewa kyakyawar Fuskarta kallo,kwanciyarta ya gyara Mata tayi matashi da cinyarsa baccinta takeyi sosai sai da ya gaji yaga Allah ba Wasa ba Driver ya shige mota yayi kwanciyarsa Yana bacci,shi kanshi Hunaif yanzu tsoron Dajin ne ya kamashi,ba shiri ya zame Kan Khairat daga cinyarsa a hankali,ya Dan matsa can karshen katuwar carpet din ya kwanta Yana so shima yayi bacci,idonsa ya rufe ruf.

Cinnaka ne ya sadado ya ciji Khairat ta mike a firgice tana Sosa wajen,Daji ga duhu ko Ina Tsoron Aljanu ya Kama Khairat ta Matsa jikin Hunaif ta kwakwume shi,Yana jinta shima tsoron yake ji baya so ya bude idonsa.
Kukan wani Abu sukaji Khairat tace wayyo namun daji ne ga kukan Damusa can,Hunaif da sauri yace Allah? Wani Abu yayi wani Gurnani,Hunaif ya juyo tare da rungume Khairat sosai itama ta shige jikinsa tana cewa fada sukeyi da Zaki da Damusa wancan kukan Zaki ne,Innalillahi cewar Hunaif mu koma cikin mota,da sauri suka tashi suka tafi wurin motar da sauri,Driver ya farka a tsorace shima yace lfy? Hunaif yace Dabbobin daji ne harda su Damusa gasu can suna ta kuka,Driver ya koma gaba da sauri,Khairat da Hunaif suna Bayan mota,Abin mamaki Driver na gwada tashin mota sai kawai sukaji mota ta tashi lafiya Lau,farin ciki ya kamasu,yaja mota suka ci gaba da tafiya,Khairat da Hunaif bacci sukeyi sosai,har Allah ya taimakesu suka kusa zuwa garin daga Nan suka dauki Hanyar kauyen,lokacin 12am, Saida Driver ya kawosu lfy cikin garin sannan ya samu wuri yayi parking motar ganin darene Bai tashi Hunaif ba,shima sai ya gyara kwanciya ya fara baccinsa.
Basu farka ba sai Asuba Kiran sallah ya tashesu, da ruwansu Na roba sukayi Alwala sannan Hunaif da Driver suka tafi masallaci,Khairat ta Shimfida sallaya jikin mota tayi Sallah da azkhar sannan ta koma motar taci gaba da baccinta, Hunaif ma dawowa yayi yaci gaba da bacci,Driver kuwa ya bazama garin abinsa.
Tunda suke bacci sai sha daya suka tashi,Lokacin Driver tuni yaje table din me shayi yayi hadin kauri ya karya abinsa.
Khairat ta Kalli Hunaif,shima ya kalleta suka sakarwa juna Murmushi,Driver yace Hajiya

Please Login or Register in order to submit comment