Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taba min jakata, Sai da Khairat ta Hadiye na bakinta da take ci tace Babu komai Kaine dai kawai hancinka yake jiye maka ba abinda ya faru.

Bayan sun Karasa gida kuwa Talatu ta bude kifi da Kwai daga ita sai yaranta da Kawu suka ci ko kula Khairat basuyi ba aiki kawai take ta faman yi daga wannan sai wannan ko a jikinta dama ta Saba da halinsu Kuma taci ba tare da Kawu ya sani ba.

Da dare Khairat yau ba Makaranta tana zaune Dogs din Soja suna kwance sun wani baje a gefenta wani Almajiri ya shigo Yana bara Wahidin...Iya Ni ban samu ba,Iya yunwa Bata da Hankali...ko Dan kanzo...takaici ya Kama Kawu sarkin rowa ya fito daga daki Yana dauke da sandarsa yace Kai Almajiri Ubanka Yana Ina?ko akwai kasonka a gidana?ko nauyinka a kaina yake?nace ka rataya a wuyana?ko hakki nane ciyar da Kai,ina ubanka ko uwarka ka kirasu a waya a kansu hakkinka yake,,Almajiri yace Baba Ni Maraya ne a taimaka min .
Tsagal Talatu ta Nuna Khairat da yatsa wannan ma Marainiyace a hannun kanin babanta take ai kana da dangi ka tafi wajensu shegen yaro me suffar Yan ruwa.
Almajirin Khairat ta kalla yaro karami ya bata tausayi tace Yi Hakuri ka tafi kaji,Rahinatu wacce Bata fi 15yrs ba ta gallawa Khairat Harara tare da cewa Iyayin banza.

Khairat tace wlh sai na mike na Miki dukan tsiya ko Ni saarki ce Dan uwarki? Karki ga Ina kyaleki wlh Dan yarinya ce ke da sai na fasa Miki bak...tas Kake ji Soja Ammar ya buge bakin Khairat tare da cewa kafin ki fasa Mata Ni Bari nayi maganinki shegiya kodaddiyar banza, takaici yasa ta mike taje kofar dakinta sannan tace Kai Kuma Duna Dan Baki sari daddawa Baki wuluk da Kai sai kayan Muni jiki duk Dirty Wai Kai saurayi,wace zata so Ka kana tsami an cuci soja,tana Gama fadin Haka ta fada dakinta tare da Sa sakata ta kulle, Ammar Soja ya dinga bugun kofa kamar Zaki Yana yau sai na kasheki har lahira,Talatu tace kyaleta Dan Ubanta gobe zata fito ai,Kawu Makaho yace an cire Mata tallafin Abinci na sati guda shegiyar yarinya.

Talatu tace wannan yarinyar da dama ta samu sai ta taka mu to Allah yasa munfi karfinta dama indai ta gaji uwarta sai Addua.
Washe gari kuwa tana Fitowa da Asuba Soja ya mata shegen duka kamar zai kasheta ko Bari barinta tayi Sallah Bai yi ba,Haka suka je yawon talla kauyuka da kyar take motsi ga zafin dukan Rana tana Sha ga yunwa kamar ta mutu.
Suna jikin wata bishiya a kauyen Kumbotso kawai ta bingire a Nan ta fara baccinta data saba,Kawu Babu tashin da Bai Mata ba yasan baza ta tashi ba kawai ya kyaleta yaci gaba da cinikin maganinsa.

Sai da ta gaji da bacci ta tashi lokacin Ana sallar Azahar tayi Alwala tare da Shimfida Dankwalinta tayi sallah abinta sannan tace Kawu Bari naje wancan gidan nayi Fitsari,cike da masifa yace to kiyi sauri ki dawo,Tana Shiga gidan ta iske an sauke shinkafa da wake Ana rabawa yaran gidan,Suka gaisa da matar gida tace Dan Allah Zanyi fitsari,mutanen kauyen sunga bakuwa daga birni amma gwara na kauye da ita, Nan fa suka ji tausayinta suka nuna Mata Bayan tayi ta fito Matar tace baiwar Allah zauna a zuba Miki Abinci kici Mana, dama abinda ya kawota kenan kwadayin abinci,ai kuwa ta zauna aka cika Mata wata katuwar Siver ta cinye tas tare da kwankwadar ruwan rijiyarsu me sanyi ta musu Godiya sannan ta tafi,Suma kansu na kauye sunga rashin gata a jikin yarinyar.

Yau ta koshi ko kula Kawu batayi ba kan ya siya Mata Abinci Haka da suka koma gida ma ko a jikinta tayi aikace aikacenta.
Su kansu su Talatu Sunyi mamaki Basu bata Abinci ba Amma suka ganta lafiya Lau,da misalin 8 na dare sai ga yaro an Aiko yace Wai Khairat tazo inji Usy.
Talatu tace Usy dai anyi asara ya rasa wurin wacce zai zo sai wata Khairat,Khairat Kuma Bata kaunar taji Namiji ya Kira ta zance,ta tsani maza su zo zance ganinta nawa take yarinya da ita za Ana damunta,duk wahalar da take Sha ya fiye Mata ta zauna Don har yau tana sa ran zata yi karatu,Kuma Usy ma wani gara dashi gaja kamar daga kauye yazo Haka yake ba Wanda zaice Dan birni ne sabo da a kauye ma akwai Dan birni a birni akwai Dan kauye, Talatu tace tashi kije shegiya wa zai soki in ba irin su Usy dinba,Hakan ma ai ke kika yi dacen miji kamar Usy,Rahinatu da Shahid suka sheke da dariya tare da cewa Usy hhhhh.
Kawu yace jeki ko Zaki samo Mana Yan kudi Dole suka Kora Khairat ta tafi zance wajen Usy.

A fusace Khairat ta fita wurin Usy tace Salamu alaykum gani ya akayi? Usy ya washe Baki sannan yace Sannu tawan,Khairat tace Fadi me ya kawoka? Usy yace shegen yaron Nan Muazu dana Aiko ya Kira min ke Amma sai da yace na bashi ashirin kudin Kira,takaici ya Kama Khairat sai tayi tunanin Usy Babanta Muaz daya rasu yake zagi a wayance,Sai itama tasan Sunan Baban Usy Kabiru tace Wlh kuwa kasan Kabiru makwafcinmu yaron Nan na can gidan Haka rannan na aikeshi ya kaimin shara yaki duk ranar Dana kamashi sai naci Uwar Kabiru,Dan uban Kabiru Ni zaiwa Haka,Tsam Usy ya Shiga tunani sai ya gano Babansa take zagi Akan ya Fadi Sunan babanta Bai sani ba,sai yanzu ya tuna Ashe Sunan Baban Khairat Muaz,ba shiri yace kutmar au da Babana kike?iyye....Khairat Ni din? Kwarai kuwa gobe ma ka Kara zagin me Sunan ubana ka gani idan ban zagi naka ba.

Koda Khairat ta dawo gida Kawu yaga Bata samo ko sisi ba sai yace shegiya yanzu Haka ta koreshi,Rahinatu tace wlh Ina jinta Abba tana zagin iyayen Usy,Wai Dan yace Muazu..to Muazu an fada, da sauri Khairat tace Sabiu..Sabiu..na Kuma cewa Sabiu.
Baki bude suke kallon Khairat Talatu tace lallai yar Nan Bata da mutunci Amma zanyi maganinki,Tuni Khairat ta gudu dakinta ta kulle ta window ta leko tana Talatuwa Yar Talatuwa me a daure a dinga wanka.

Wace ce Khairat?

Khairat Muaz Fulani cikakken sunanta,Yan Asalin Fulanin Taraba state ne, kasuwanci ya kawo Muaz Fulani Kano,Su biyu ne wajen iyayensu Wanda sun Dade da Rasuwa,Muaz sai da Ya auri Hauwau Babar Khairat kenan sannan ya dawo Kano Yana kasuwanci har Allah yasa arzikinsa ya bunkasa Bayan Matarsa Hauwau da yake matukar so ta Haifi Kyakyawan yarta Khairat ya jawo Dan Uwansa Kawu Sabiu Wanda dama tun Yana yaro yaje ya hau wata bishiyar kuka Aiko Aljanu suka makantar dashi hannunsa daya ya shanye magani ba inda ba aje ba Amma ba a Dace ba har ya girma ya Riga Muaz aure sosai ya Auri Matarsa Harira wacce ake Kira da Talatu itama Yar kauyensu na Taraba ce, tausayin Dan uwa yasa Muaz ya dauko Kawu Sabiu ya Gina Masa gidan da suke ciki a yanzu,tun asali Kawu Sabiu ba wani mutunci garesu ba daga shi har Matarsa,dake Muaz me dan kudi ne na rufin asiri sai Kawu yake Masa biyayya shi Kuma yaji Dadi yake Masa ko me yake so,sannan duk yaransa shine ya dauki nauyin Karatunsu har Ammar Soja da Zainab suka Gama secondary.

Muaz ya Dade Bai samu Haihuwa ba kafin Allah yasa Hauwa ta samu ciki ta Haifi Khairat,ta taso cikin gata da Jin Dadi har aka yaye ta,Lokacin Hauwa ta sake samun wani cikin tazo Haihuwa Allah ya Mata Rasuwa,Muaz yasha bakin ciki sabo da Yana son Matarsa lokacin Kuma suna zamansu lfy da Kawu duk inda zasuje ko ziyarar dangi can Taraba tare zaka gansu Muaz Yana Masa jagora,sosai Shakuwa ce me karfi tsakaninsu, sabo da bacin Rai na rashin Matarsa Hawan jini ya kamashi da karfi Amma a Haka shi yake wa Khairat komai Yana rainonta ko shagon Kasuwa zaije da Khairat yake tafiya ga yarinya Fara Kyakyawa tayo babarta Hauwau tafi ma Babar Tata komai,Kawu sabo da rashin Imani ko Talatu Bata ce a Bata Khairat ta rike ba kafin Muaz ya sake aure,shi yaci fitsarin Khairat da kashinta.

Bayan Shekara biyar Muaz Hawan jininsa ya tashi ya Shiga bayi zaiyi wanka ya Fadi dam, shike Nan ya sankame an kaishi asibiti Allah ya Masa rasuwa dattijon arziki,lokacin kuma Fafur Talatu tace baza ta rike Dan wani ba,Kawu kuma Allah ya Dora Masa son kansa sai abinda Matarsa da yaransa suka ce,mutanen Unguwar Gwale cikin birnin Kano suka Fara zagin Kawu da Matarsa ganin Khairat kullum tana makwafta wata Mata ta dauketa tace idan basa so ita tana so da na kowane, sai Kawu ya lallashi Talatu da ta daure ta dauki Khairat ta riketa idan ta girma sai ta zamar musu Yar aiki.
Talatu tace Sam sai dai a siyar da gadon Khairat kaf data gada a Bata a matsayin kudin rainonta,baza tayi a banza ba,ba a aikin banza a Kano.

Kawu ya hada komai har gonakinsu na gado na Taraba state ya siyar suka bude bushasha a matsayin kudin rainon Khairat.
Dama Basu da iyaye sai Yan uwa na Taraba wasu sunji labarin me ya faru sai suka zo daukan Khairat Talatu da Kawu suka musu dadin Baki ai yarmu ce Kawu harda kuka Wai an nuna Masa Bai iya ba,kamar Dan uwansa ya kasa rike Masa ya daya Allah ya kiyaye.
Bayan dangi sun tafi Sai Talatu tace mutanen Unguwa sun Sa musu Ido a siyar da gidan na Gwale su koma Sheka can kusa da Zooroad, suka siyi wani tsohon gida Wanda kaf layin ma an San talakawa ne kukut a cikin wajen.

Suna cinye dukiyar Khairat har ta Kare tas lokacin Khairat na karama ba irin azabar da Talatu Bata yi Mata watarana ma sai Su Zainab suyi ta mintsininta,dake tafi su karfi sai su cijeta mugunta iri iri,shi kanshi Kawu watarana mintsinin Yar yarinya yake,Talatu Kuma tayi Mata duka da carbi ko tsinkaken tsintsiyar kwakwa, tun Bata gane basa kaunarta har ta gane komai, tana Shiga jss2 suka cireta a schl Wai kudin rainonta sun Kare Kuma Hakan ma Primary kawai tayi Private Amma jss1-2 government schl tayi.
Daga Nan Talatu take daura Mata talla iri iri har da kayan Miya etc.
Kudin gadonta sun Kare nan Talauci ya addabi Kawu.

Kawu yaje bara wasu wuraren Amma gaba daya kamar ya zagi sama ba Wanda ke bashi sadaka,sai ya tuna babansu kafin ya rasu Yana hada magungunan gargajiya Kuma yasan wasu da dama,shine yake Shiga daji cikin kauyukan Kano ya samo ganyayyaki da jijiyoyin bishiyu iri iri wasu ya hada dai dai wasu kuma shirmensa yake hadawa.

Dansa Soja Ammar shi ke rakashi gonakin kauye ya samo tare da tambayar mutanen kauyen wannan itace bishiya kaza ne? Haka har su samo iri iri su dawo,tunda Khairat ta Gama jss2 yake tasa keyarta suje daji,su Kuma yaransa suna makaranta Yana so su Gama su Samu aiki su dinga rike gidan shi Kuma ya huta.
Haka idan ya hada magani zasu bawa Khairat wasu ta Shiga gidajen mutane a samu ciniki Kuma,shine karshe ya siyi speaker ya dauki Khairat Yana sata Dole tayi tallan magani.

Kawu da Talatu son Kudi ne dasu,ga son kayan wani,rowa harda rowar Abinci sannan yaransu kawai sune Yaya sune dolensu, basa hangen na kowa, Akan muguntar da suke yiwa Khairat ta Zama me Saurin fushi,zuciya da rashin barin ko ta kwana kullum a shirye take kana yi Mata zata maka,su Kawu sun zubar da girmansu Bata ganinsu da daraja ko kadan.
Yaran Kawu biyar a duniya Talatu ta daina Haihuwa tana tsarin iyali,Ammar Soja shine Babba 28yrs sai Zainab 23yrs,sai Shahid 19yrs,Rahinatu 15yrs sai Ummi auta 12yrs.
Kawu ya manta da abinda Muaz ya Masa yaci Amanarsa ya daya tal ya kasa rikewa sun cinye Mata gado Kuma suna azabtar da ita,ko sutura basa dinka Mata sai dai su Bata kwancen Zainab ko Rahinatu.
Allah ya bawa Khairat farin jini kowa ya ganta sai ta birgeshi shi duk da kazantarta ta Dole domin basa Bata Sabulun wanka bare na wanki sabo da tsananin kyawunta da kyan diri,gashinta har gadon baya Baki sidik,idonta kadai ya Isa ya birgeka kamar Madara gasu Dara Dara kamar tana jin bacci fadin kyawunta zai cinye Mana time ma duk inda kuke zaton kyau to Khairat ta Kai,Hancinta ba me tsini bane can sannan round face gare ta gata da Masifar kyan diri ita ba ramammiya ba Kuma ba me kiba ba,sannan tana da tsayi Amma dai dai normal na dirarriyar mace duk da wahalar data ke Sha Bai Hana fatarta laushi ba,gata da son Tsafta Amma ba dama.
Talatuwa kuwa duk yaranta munana ne shi yasa suke kishin Khairat.gwara ma Zainab tana shafe shafen sai ta Zama Fara shine ta danfi dama dama Kuma tana kwalliya sosai Yar wanka ce.
Wannan kenan.

Yau ma da dare kamar yanda Samari suka Saba yiwa Khairat tururuwa Haka Bata kulasu ko ta fita sai ta Kori mutum,a boye Talatu taga Dan gidan Kawarta Laure takarice a Makkah take rayuwa tana turo kudi ta siyi filaye ta bawa danta Hammad Kudi me yawa yake business Yana juyawa ya Zama me kudi,Talatu tasan bazai taba son yayanta ba,sai ta nemi Haj Lauren da tasa danta yazo yaga Khairat ya aureta sai ta samu kudi ta Nan sabo da kwadayi.
Ai kuwa yau Laure ta bugawa Talatu waya cewar Yarta ta shirya Hammad zaizo ya ganta idan tayi Masa sai ya aura,Haj Lauratu duk tunaninta sabo da Allah take son hada alaka da ita sannan tayi Mata karyar cewa yarta ce ta cikinta,saura kwana Uku Hammad yazo Talatu ta zage tare dasu Zainab sukayi kwalima suka gyara gidan fes gida ya dawo kamar sabo,lokacin Soja Kuma ya koma schl tare da karnukansa Babu ko daya bare su Bata gidan sabo da schl yake kaisu su hade da karnukan makaranta masu gadi,kullum sai an gyara gida an kunna turaren wuta gida ya fito kamar ba shi ba,duk Kaya masu Dirty an wanke tare da killicewa,sannan Kuma kullum sai Zainab ta Kai Khairat Saloon an wanke Mata gashi fresh sabo da bako me kudi zaizo,Khairat Kam tana Jin dadin harkar Nan tuni ta Kara kyau ta fito tsaf Amma ko kadan Bata son Namiji ace ma tana da saurayi ko zata tsaya dashi zance.

Yaune Hammad zaizo ganin Khairat,yau Kuma Talatu da kanta ta mike tace ai Khairat bakya wanke jikinki ya fita da kaina Zan Miki wanka,Khairat ta bude Dan bakinta tace wlh Ni bazan yarda ba Zaki jawo wlh idan yazo na zageshi ta uwa ta uba,Jin zata cucesu Zainab
tace kyaleta tayi da kanta Ni dai burina na Samu kudin registration ta silar Khairat,Dan Allah Khairat ki taimake mu Za a rufe registration banyi ba zanyi asarar shekarata,Rahinatu tace muma wlh jibi za a Fara Kora Kuma ba a biya Mana schl fees ba,Dan Allah Khairat karki koreshi,Allah sarki Khairat sai suka Bata Tausayi duk da ita Bata karatun sai tace to idan ya bani Zan karba tunda kun San Ni bana karbar kudin samari in bana sonsa bazan karba ba,Amma wannan idan ya bani Zan karba sabo daku, murna ta Kama Talatu tace me kudine Khairat sosai,Khairat tace bazan roka ba Amma in ya bani Zan karba na baku.

Suka dinga lallaba Khairat ta yarda da suka koma daki Kuma sai suka Fara zaginta shegiya tsinanniya mu lallaba dai ta karbo Mana kun San Bata da mutunci.
Da yamma Zainab ta karbo sabon dinkin da suka yiwa Khairat Atamfa me kyau taji dinki Riga da skert Bayan tayi wanka ta shafa Mai me kamshi suka Bata,ta Sa subhannah kamar a jikinta aka tsara dinkin,Zainab da kanta ta tsantsarawa Khairat kwalliya ta kafa Mata dauri kamar Amarya suka Bata sabon mayafi da takalmi dai dai talaka irin kayanta tare da fesa Mata turare.

Suna zaune suka ji Dirin mota,Zainab ta leka ta wata Yar kafa ta hango Kyakyawan matashi hutu ya ratsashi chocolate color dogo yasha shadda Yana zuba kamshi,Zainab taji Ina ma wajenta yazo da wlh sai ta aureshi wannan Kyakyawa Haka,ga kudi motarsa wata katuwa ta ba million biyar baya,a ranta tace ai kuwa Khairat Baki Isa na bar Miki wannan ba kina Gama Mana aiki Zan aureshi. Talatu ta tura Ummi da tayi Masa iso zuwa palonsu Wanda yake malale da carpet yasha gyara.

Bayan sun gaisa da Talatu a mutunce sai ko Zainab ta Kai Masa ruwa da lemo tare da cewa tana Zuwa Khairat din,Yana Danna waya me tsada yace ok,Khairat ce ta shugo a nutse dauke da Sallama ya amsa Mata Yana Kare Mata kallo,wani dam gabansa ya buga sabo da tsananin kyan Khairat,tun a lokacin a ransa yace tayi ma wannan dai dai nice dama irinta nake nema a duniya Allah ya bani a ransa yace da kudi Zan siyesu a aura min ita da wuri,Matan yanzu da ka saki kudi sai su aureka ,durkusawa Khairat tayi tare da gaidashi ya amsa yana sakar Mata Murmushinsa me tsada,ita kanta Khairat Bata taba Jin Wanda ya Dan birgeta ba kadan sai Hammad.
Magana ya fara da nasan kin San komai ma tunda Ummata da Ummanki sun Gama magana, Alhmdllh na ganki kuma na yaba kwarai da tarbiyarki da komai naki ma yayi min, Khairat sai kunya take ji tana boye fuska shi Kuma hakan ya Kara birgeshi Bayan sun danyi Hira sama sama yace sai Allah ya kaimu Nan da sati daya idan na Samu time Zan zo,ga wayata sa min number dinki Bayan na tafi zamu na gaisawa.

Bani da waya Ni sai ko Nan gaba,kamarki Baki da waya idan Zan dawo Zan kawo Miki inshallah Khairat tace a'a na gode Kawu yace zai siya min,Dole sai na kawo Miki a kyale Kawu ya huta nauyin ya Masa yawa,Shuru tayi kawai tana jinsa ya zaro rafar dubu Hamsim ya ajiye Mata,Koda ya fito zai tafi sai ya bawa Talatu Dubu goma tausayin Kawu Makaho yaji ya bashi dubu Ashirin shima.
Har kofar gida Khairat ta rakashi mukayi sallama.
Lokacin sun cika gidan da ihun murna,dubu Hamsim din daya Bata ta mikawa Talatu gashi Nan kuyi abinda kuke so dasu,dubu daya kacal Talatu ta ciro tare da Miko wa Khairat tana hade fuska tace ga rabonki kayan sawa Kuma an bar Miki sabo da kokarin da kika yi kin biya a cikin kudinki,Baki Khairat ta tabe ta wullawa Talatu dubu dayan tace bana bukata bazan auri mutum ba bana sonsa ba ruwana da kudinsa,dan ku nayi sabo da masu komawa makaranta Kar su Samu matsala,Ni Ina da Imani,zuciyata Bata mutu ba kamar ku,Allah ya bani wadatar zuci,sannan Bari har kayan sawarku Zan baku dama badan Allah kuka yi min ba,Ni Kuma Dan Allah nayi Kuma sharrinku kanku zai koma,Nandai Khairat sarkin zuciya ta shige dakinta Wanda ake Tara kayan wanki ta cire kayan jikinta kaf da suka bata ta watso musu ta window tare da maida jemammiyar atamfarta.

Shewa da ihu sukayi suka kwashe kayansu washe gari da Kudin Zainab ta biya kudin makaranta,Haka su Rahinatu ma,ragowar Kuma Suka dinga cin kayan Dadi iri iri,Khairat kuwa sai aikin tallan Magani suke zuwa da Kawu.







AsmaBaffa
[10/18, 2:48 PM] Sis Asma: 🦚🦚ME MAGANI🦚🦚







3







Official







By
AsmaBaffa






Fancy Honey,Raliya Nura Lawal,Agas,Queen kk, Amatullah and Maman Ameer ga page naku.









Washe gari kuwa Kawu yace Hutawa zaiyi sai munyi sati guda bamu fita ba,kudi sun samu sai sun Kare an ciye sannan mu koma,Talatu tace uhm Khairat an washe Baki za a huta to wlh Baki Isa ba kullum sai kin fita kuma da speaker har kasuwa kina tallan maganinki,Kawu yace ai Akan ta huta ma gwara na fasa Hutawa mu fita Dan ubanki tashi ki min jagora yau cikin manyan GRA zamu Shiga unguwar masu kudi tashi mu tafi,Kuka Khairat ta fashe da shi, ta kife a Nan tana ta Rusa uban kuka talla ai gwara a kauye Amma birni kowa Yana kallonta da ace tasan a Taraba Ina danginsu suke na uwa Dana uba da taje Amma Kawu yaki fada Mata,ita Kuma lokacin da iyayenta suka rasu Bata da wayo,sai hotonsu kawai take dashi kala kala,ba yanda ta iya Haka ta mike suka tafi Fara tallansu.

Katafariyar GRA Khairat taje Kawu suka tafi fuskar Nan Tata kamar hadari yayi bakikirin Tana goge kwallar da take cika Mata ido Kawu ya fara dukan kanta kwas kwas ki fara Mana ya banji kina Tallan ba? Speaker katuwa ta Sa saitin bakinta murya na rawar Kuka tace...ku tashi ku nemi lfy... ,sai da Lafiya ake neman Duniya da lahira..,da lfy ake karatun Qurani....,ba sai na rantse muku ba sai kun gwada maganin zaku ga aiki...idan karya nake bance ku tsine min ba Amma akwai ranar da zamu tsaya a gaban Allah zamu tashi tsirara,Kawu na tsirara Kuma Haka....Allah muka roka ya bamu baiwar magani,Maganin Ulcer,Basir,sanyi,amosani,Ciwon Mara mace idan tana yawan Ciwon Mara Azo ga Magani,wani titi suka biyo Wanda Goslow ya Hadu sosai Karar jiniya suka ji kamar Gomna ne zai wuce motoci kusan guda shida ne rantsatsun gaske ba ta kasa da 20million.
Ketowa sukayi Amma Goslow wata babbar motace ta mutu a tsakiyar titi,Kawu cewa yake kutsa ciki kiyi talla, Aiko ganin ba sarki sai Allah ta Ware murya tana tallanta ta jikin shegun motocin Nan tazo zata wuce kawai taga suuuuuu Glass din motar data fi kowacce kyau cikin jerin motocin Nan masu jiniya sunsha tint wani Kyakyawan hannu ne fari Kar Kar kamar na balarabene dan Khairat cewa tayi Kawu ga Balarabe ya Miko Mana sadaka, Kawu yace karki karba Dan mafiya ne yaje ya sace Ni,Mutumin da ya zuro hannu ne ya Miko musu kudi ya gaji da jira basu karba ba,Gajiya yayi tare da Jan tsaki ya leko da kansa kadan kan uba kamar aljani cewar Khairat sabo da kyawunsa,wani kamshi ya cika wajen, tace Kawu Balarabe ne Ni dai Bari na karba Kuma wlh idan na karbo sisi bazan baka ba,Jikin motar ta Karasa tare da Sa hannu ta karba tana angode Allah ya Kara budi Allah ya biya maka bukatunka, Allah ya saka a Aljanna firdausi uban giji yasa kasha ruwan alkausara,in Allah ya yarda baza ka tabe ba a duniya da lahira,Allah ya rufa ma asiri duniya da lahira,Allah ya baka mace ta gari idan Kuma kana da ita Allah ya Kara dankon kauna ya Baku Yara masu albarka,Jin yanda yarinyar ta iya surutu Haka da yanda take ta faman Masa Addua me Dadi Haka wacce ba a taba Masa irinta ba a duniya sai yau.

Hakan shi yaja hankalinsa ya bar karatun Magazine dinsa da yakeyi ya leko da kansa Dan ya ga wace wannan Haka,Abin mamaki sai yanzu ya kula ma yarinya ce karama ga Makaho Nan ko babanta ne oho ya furta ransa ita kuwa tuni tayi wajen Kawunta tana murna tace kawu wlh dubu goma ya bamu.
Wayo kawun ya Mata yace laaa muji na taba su Aiko ta Sa Masa a hannu ya fisge da karfi yace Naira Hamsim Zan baki,takaici ya Kama Khairat ta jefar da speaker a kasa ta cakumi Kawu suka Fadi rigija,ta danne Kawu Iya karfinta suna kokawa Yana ihun neman agaji Amma Khairat sai da ta kwace kudin Nan,duk abinda sukeyi Akan idon Balaraben da ya

Please Login or Register in order to submit comment