Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kuma sai mutane sun zo Sannan zakina Shiga duk Bayan 3hrs ki duba idan da dirty ki gyara wajen,sai Kuma idan wani ya nemeki,Kar kiyi nisa.
Wurin da aka tanada na hutawa taje ta zauna tana hutawa Lokacin Meenal ta tashi sai gwarancinta take mata tana saurara suna hirarsu.

Musaf ne ya fara zuwa Office yau sai Manager Ogan kuwa Bai shigo ba yau ya tafi Abuja duba wasu kamfanonin nasa sannan Yana da meeting a Rivers State.
Musaf ne ya nemi ganin Khairat.
Babu ko tsoro a ranta taja Meenal dinta suka tafi,Bata iya Shiga lifter ba tabi steps taje tana knocking sai da ta Dade yace Come in,Auzubillah ta Furta ganin katuwar Plasma dinsa ya Kama tashar XXX Yana ta kalla a nutse Yana Shan tea,ko a jikinsa Volume ma ya karo sai yi suke suna ihu,ganin Haka yasa ta fitar da Meenal waje take karki kiyi kuka tsaya a Nan Zan Shiga na fito,Allah ya kawo Aminu kawai ya dauki Meenal suka tafi Office dinsa ita Kuma Khairat ta Shiga tana matukar Jin tsanar Musaf a ranta,Bata ko kalli TV dinsa ba tace gani fa nazo baka ce komai ba,da yatsa ya Mata alamar ta matso tana matsowa ya mike tare da sharara Mata uban Mari,Fuskar ta tayi jajir sannan yatsunsa rada rada a jiki.
Ta daure ko kwalla Babu kuma Bata ce komai ba,yace sai ta sake shara da wankin Toilet,ba gajiyawa tayi Masa,yace Ina Nan Akan kudira ban Fara daukan mataki ba a kanki,wannan Yar taki da kika fi so zakiga me Zan mata sai kin kwammace Baki haifeta ba,dama daga gani Yar cikin shege ce.

Bata ce komai ba sai ga Aminu ya kawo Mata Meenal tana kuka taki zama a wajensu,Takaici ya Kama Musaf Nan take ya mike tsaye Yana Zubawa Aminu masifa sai na Kore ka daga aiki,u r very stupid Kar ka sake ka ajiye min wannan tsinanniyar yarinyar a Office Dina,Khairat taji haushi tana huci zata Fara masifarta Aminu ya Mata signa da Ido,Musaf Yana kallon abinda sukeyi yace da Aminu na sallameka daga aiki daga yau,Khairat tace jeka Aminu Zan sa Oga Hunaif ya dawo da Kai,Zan sa Wanda ya gaji arziki ya dawo da Kai bakin aikinka,fari me farar aniya Dan Kyakyawa ba kyan kame kame ba,kishin Hunaif ya tasowa Musaf komai shi baza a yabeshi ba sai Hunaif,Mata Hunaif,kudi Hunaif komai Hunaif,Kara Jin Tsanar Hunaif yayi a ransa Jin Khairat tana yabonsa,a fusace ya mike Khairat ta dauki Meenal da sauri zasu gudu ya samu ya tankadasu suka Fadi rijif,Meenal bakinta ya fashe jini na zuba,Aminu kuwa tuni ya bar ma Building Baki daya.

Zuwa Khairat tayi famfon da suke wanke hannu a can baya Garden ta wankewa Meenal bakinta tana Kiyi hakuri kinji,yi Shuru Allah zai saka miki tana jijjigata tayi Shuru kuwa.
Yinin yau Sunyi shi ba Dadi Khairat ji take ma ta tsani aikin,Amma ba yanda ta iya Haka zata hakura dole karfe biyar na yamma tayi tafiyarta gida ta dafa musu abinci suka ci sukayi Wanka sannan ta kwanta tana huce gajiya ita kuma Meenal tana Wasanta a tsakar daki.
Tunanin rayuwarta takeyi kawai musamman Meenal da take riketa ganganci tayi ta karbi yarinyar gashi ta Shiga ranta baza ta iya Kai ta gidan Raino ba.

Da dare Khairat Bata iya wani baccin kirki ba sabo da tunanin wulakanci da Musaf ya Mata, washe gari ma Haka suka shirya cikin kayansu na gwanjo,Khairat Bata yi wani baccin kirki ba suka tafi Company ta Fara aikinta tana Office din karshe na Musaf bacci ya takura Mata,ita Kuma tun farko Haka take daga taji bacci a wajen zata kwanta,Meenal tana Wasanta Khairat ta kwanta a kasan tiles ta fara baccinta,ko minti goma Bata yi ba Musaf ya shigo ya dau shegen wanka,mamaki da takaicin Khairat ya kamashi ya watsa Mata ruwan Robar dake hannunsa gaba daya ya juye Mata a jikinta,Amma ko a jikinta baccinta takeyi,Baki bude yake kallonta,Meenal Kuma tana dariya ta Kama rigarsa tana Mika Masa hannu ya dauketa,Babu Imani Wai ta Bata Masa Kaya Sunyi Dirty,yayi ball da Yarinyar ta Fadi goshinta ya fashe,lebenta na sama ya tsage kadan Yana jini,ta kwala uban kuka,ba shiri Khairat ta farka taga abinda yake faruwa,itama Khairat sai ta dauki Meenal ta fashe da kuka suka zauna a wajen suna ta yin abinsu,Musaf ko a gefen rigarsa sai ma takaici da ya sani Bai sa Hunaif ya Bata aiki ba zasu kashe Masa dodon kunne,Khairat Kuma tunani tayi da wani banza ya ci ma mutunci gwara Dan uwa,Gidan Kawu Sabiu ya fiye Mata wannan wulakancin,A tsawace Musaf ya koresu daga Office dinsa,jiki na rawa Khairat ta fito Meenal tana kafadarta suka Shiga lifter Bata kula ba ta fada ciki,wani kamshi ya ratsasu na musamman,garam tayi Karo da Hunaif a lifter zai je Office nasa,yasha kana Nan Kaya kamar a England yayi kyau ya gaji,duk macen data ganshi sai ta zauce.

Da sauri Khairat tace Morning sir ita a Dole maaikaciya,Hannu kawai ya daga musu ya kallesu yasan aikin Musaf ne ko a jikinsa,da sauri Khairat tace Sir Dan Allah Ni dai a cire min aikina zuwa Office din Musaf ko kudina na albashi na yarda ka rage,Dariya ce ta kusa kwace masa sabo da yanda a farko ta dinga kuri sai gashi just 2days tayi laushi,a fili ko kala Bai ce ba ya fita abinsa ya bar lifter zuwa Office dinsa.
Khairat tace Kai kaga mutum Lallai sai na gyara musu Zama Naga Alama,tana zaune wurin 12pm Bayan ta Kai Meenal chemist ta dawo bakin aikinta,Aminu yazo yace kije Sir Hunaif na nemanki, yace Kinga Alhmdllh Hunaif yace Kar na tafi ya barni nayi aikina, murna Khairat tayi tace Alhmdllh Musaf sai ya mutu, da sauri ta mike da Meenal dinta a kafada ta tafi Office,tana yin knocking yace Shigo,Yana Shan tea Yana rubuce rubucensa tace gani Sir, ba tare da ya Dago kansa ba yace ke Ina iyayenki suke? Tace sun rasu Sir Baki daya,wannan Makahon fa da kuke tallan magani? Kanin Baba nane same father and Mother,Blood daya,wannan yarinyar kuma fa?tace 'yata ce,cikin shege kikayi ko aure? a'a ko daya tsintarta nayi sabo da ita ma nake wannan aikin Zan kaita schl tunda ta fara wayo kaf ta bashi labarin tsintar yarinyar,wayarta ce tayi Kara kirrrrr....ta daukota da Sauri taga Baba Isyaku,tana dagawa yace an kawo Miki yaron Nan daya Bata ba a ga iyayensa ba,anyi bincike an gaji nace musu nine mijinki nayi signing da komai yaro gashi a wajena idan kin dawo kizo ki tafi dashi,Ok to ya Sunan yaron? Hmm yaron da baya wata magana kawai ki rada Masa Mohd, Khairat tace to ba damuwa.
Hunaif Yana ji Yana aikinsa yace bazan iya hanaki aiki a Office din Musaf ba,sabo dashi ma na Baki aikin Nan domin shi yace na Baki yana da nufinsa,,Amma Kai dolo ne Sir, Baki bude Hunaif ya kalleta, gaka a Haka kamar Namiji tsayayye Ashe ba Haka bane wlh Mijin tace za ayi a Nan.







AsmaBaffa
[10/18, 2:49 PM] Sis Asma: 🦚🦚ME MAGANI🦚🦚








5





Official






By
AsmaBaffa







H B K,AISHA HUMAIRA,AEESH A SALIM,MAMAN YUSEEF ,MR MUBARAQ,MN SADIQ and HAFSAT.
Ths page is for u.






Common be a Man ace just a normal frnd Yana juyaka a company dinka ur sweat guminka wannan ba Dan Allah yake Zama da Kai ba,don inda mutunci yake ma Bai sani ba Kuma na tabbata ba wani kaunarka yakeyi,who the Hell are u kizo Office dina kina fada min shit,kina Yar shara leave my Office before I slap u idiot.
Baki bude Khairat take kallonsa Bai ma iya fada ba a hankali yakeyi kamar ba fada ba,Amma yanzu tsakani da Allah kana gani yanda ya daki yata baka Masa fada ba Kuma....get out ya daka Mata tsawa ta fita ba shiri tana mamakin Halayensu Sam Basu yi ba.
Meenal tayi bacci lokacin,Khairat ta koma wurin su Aminu can a Garden Bayan Compound suna zaune itama ta zauna suna hirarsu tana jinsu Bata ce komai ba,ganin ta Gama aikinta ta fita sai gida yaron data rada Masa Mohd tazo ta ganshi wurin Baba Isyaku Yana ta wasansa.

Baba yace ai dazu na siya Masa abinci yaci Kuma Bai Dade da tashi daga bacci ba,Murmushi tayi ta rike hannunsa suka Shiga gida,tana aikinta suna wasansu da Meenal har sun Saba,Tana zaune sai ga Dpo ya shigo Mata da buhun shinkafa Yar Gomnati daya,Taliya, Macaroni, couscous,buhun semo, Indomie,kayan tea da sauran tarkacen kayan Abinci su mangyada man ja etc ya Bata dubu ashirin kudin cefane yace chairman na local government ne yace a kawo mata sabo da ta birgeshi data iya daukan dan wani zata rike irinsu kasa take so.
Farin ciki ya Kama Khairat dama kudinta saura dari biyar kacal na Napep zuwa wajen aiki,sai gashi Allah ya kawo Mata Mafita,dama shi Allah shine ke ci da mutum, kuma ba zai Bari mutum ya tabe ba,washe gari kuma Baba Isyaku ya siyowa Mohd kana Nan Kaya masu kyau dai dai shi kala biyar da Takalma,da Pampers da yawa,Khairat ta hada Yara biyu,Meenal tafi Mohd Girma da wayo sabo da ta girmeshi.
Haka Khairat take koya musu Karatun boko Dana Qurani suna gwarancinsu,suyi Wasa tare kamar yaranta sun shaku ma sosai.

Khairat ta kwashe 2wks tana aiki a Company Amma kullum Da irin muguntar da Musaf yake Mata tare da yaranta,musamman Mohd ya tsani yaron Haka kawai,yayi ta tsine musu Yana aibata su,ganin Haka yasa Khairat take bawa Baba Isyaku su kafin ta dawo,ko ta kaisu gidan wata Sadiya me kirki da son Yara sabo da Bata taba Haihuwa ba makwaftansu ce.
Sai dai dai kun Rana take tafiya dasu,shi Hunaif baya Shiga harkar kowa kuma bazai taba yiwa Musaf fada ba,Khairat tana mamakin wanne so yake wa Musaf Haka.
Hunaif shi baya Zama kullum Yana zirga zirgar kasashe Business dinsa.

Yau dai bataje da yaro ko daya ba,Office din Hunaif shine na karshe tana zuwa ta murda Handle kullum baya Nan yau da mamaki ta ganshi yazo da wuri yasha kana Nan Kaya kamar kullum kyan da suke Masa sun baci, Good morning Sir,Kai kawai ya daga mata yanda ya Saba amsa gaisuwarsa, aikinta ta fara ya mike da sauri yace kina batamin jiki da Dirty,Babu Dirtyn komai kawai iyayinsu ne da suka Saba da Musaf kullum suce Ana Bata musu sutura,jikin Window ya koma ya tsaya Yana shakar Fresh air, Wata kwalabar Giya ya dauko a fridge me tsadar gaske yana zubawa a glass cup Yana korawa,mamaki ya kama Khairat,Saman lafiyayyar Kujera ya zauna ya nitse a ciki Yana Kora giyarsa, Chewgum ya dauko a aljihunsa ya jefa a Bakinsa sannan ya Sa me dafa musu tea yace ta kawo Masa shayin wiwi,dama ta Saba da halinsu, Hunaif Shayin wiwi yake Sha Shi kuma Musaf hayakinta yake bulbula, Christain Chimaroke ta kawo Shayin Wiwi dama aikinta kenan, Yana korawa,Baki bude Khairat take kallonsa ta kasa motsi a wajen,muryarsa ta tsinta yace Zaki Sha ne? Da sauri taci gaba da aikinta ta fuske.
Tana mopping taji knocking cikin muryarsa me Dadi yace come in,wata tsaleliyar budurwa ce kamar Baturiya Haka take Tasha kana Nan Kaya da Alama Christain ce,takalmi me uban tsini tasa,tana zuwa ta fada saman kujera a gajiye tare da kwantar da kanta a Kirjinsa,Janye jikinsa yayi cikin harshen turanci yace yaushe kika zo kasar Nan? Tace uhm last wk, Ina Abuja naji kawai nayi missing naka na zo Kano just to see u,bakinsa madaidaici me kyau pink ya tabe yace I can See that Yana Mika Mata Giyarsa ta karba tace Ina son kalar wannan ta fara korawa itama,ta dakko Wata Allura ta kwaya ta zuki ruwanta tare da tsirawa kanta ta Gama ta maida Jakarta,Hunaif yace har yau kina wannan Allurar kwayar,idan banyi ba bana Jin dadin duniya Sam,ta Furta,Baram Musaf ya bude kofa ya Shigo,ganin Lidia me kyau Haka ta nacewa Hunaif tun suna England shi ko kulashi Bata yi sai bakin ciki ya kamashi ya tsani Lidia,Harara ya watsa musu a wayance Wanda Khairat ce kadai ta kula da hakan.

Garin Mopping Khairat ta gogo kafar Lidia kadan,Musaf Dan mugunta kamar kafarsa sai ya hankade Khairat ta Fadi sosai ta kasa tashi a fusace ya bar Office din,Lidia tana Masa magana ko kulata baiyi ba,shi kuwa Hunaif Mikewa yayi Yana mika,Lidia tace ka bani driver daya da mota ta zaga gari,Ina Tahir guest palace,Waya yayi sannan ya Mika Mata wani key na mota,yace Driver Yana gate.
Tafita ya koma kujerarsa ya fara aikinsa Amma Shuru yaga Khairat Bata tashi ba Tunda Musaf ya hankadeta,Bai San Khairat tuni bacci takeyi ba abinta.
Kanta yazo Yana Jan tsaki ya Dan zunguri kafarta da tasa kafar tun Yana yi a hankali har ya koma tashinta da karfi sai ya Ankara bacci takeyi abinta mamaki yayi kawai ya kyaleta a nan Yana aikinsa tana sheka bacci.

Mafarki ta fara yi tana Furta Kawu wayyo..Talatu zata kasheni,Dan Baku Kuka haifeni ba,wayyo Babana Ina ma kana duniya kaga yanda nake Shan wahala,tana baccin ta take ta surutai iri iri, Yana aiki Yana jinta banbanci su da Musaf shi ba azzalumi bane,sannan baya Shiga sabgar wani,Yana aikinsa har ya mike yayi Sallar Azahar tana ta baccinta Bai tashe ta ba,tana bacci har kusan 4pm sannan tayi mafarkinta na karshe ta hada zufa ta kwala ihun daya tsorata Hunaif ta farka zumbur jikinta na rawa tana hakki kamar wacce tayi gudu,a hankali ta nutsu ta kalli Hunaif tayi matukar firgita ta mike zumbur tace I'm sorry Sir taci gaba da aikinta tunaninta safiyace ma,sai da ta kalli agogon wayarta da sauri ta Karasa ta tafi Masallacin dake cikin wurin tayi Sallar Azahar da laasar sannan kawai ta fita ta tafi gefen Titi zata Shiga Napep sai ga motar Musaf zai wuce gida shima.

Yana zuwa saitinta ya sauke glass ya watsa Mata ruwan lemo,lokacin Hunaif ya fito da jerin motocinsa zai wuce ta bashi tausayi abinda Musaf ya Mata yaji ba Dadi Bai kyauta ba,Yana kallonta tana kakkabe kayanta,Driver dinsa yace tsaya ka dauko waccan mu kaita gida, Driver Sunyi mamakinsa Dan ba uban Wanda yake Shiga motocin Hunaif sai Mamansa sai Musaf, Amma yau har motar daya ke ciki wata zata Shiga,ganin Hunaif yasa Khairat ta Shiga motar tare da rakubewa a gefe tana kallon kofa ba Wanda ya kula wani har ta musu kwatancen gidanta suka kaita har can tace na Gode Allah ya saka ta fita ,sai ga Meenal da Mohd sun rugo da gudunsu ganinta suka fada jikinta ta dauki Mohd a daya barin Haka ma Meenal ta dauketa a daya barin,Tana tambayar Meenal kunci Abinci? Kai ta daga tana nuna Mata Baba Isyaku ne ya siyo musu.
Gida suka shige shi Kuma Hunaif suka bar layin tuni.

Washe gari 9am yau Khairat da yaranta ta taho aiki tana Sauka sukayi Ido hudu da Ammar Soja Yana tabbatarwa Khairat ce Amma a Ina ta samo Yara? Kawai ya fara binta a baya da gudu ta dauki Meenal da Mohd suka shige Company din,Soja yaje zai Shiga Security suka koreshi, a fili yace ba komai zamu hadu ne da ke Zan kamaki ai Naga Ina kike zuwa zanyi maganinki.

Kawu Sabiu tunda Khairat ta bar gidansa gaba daya komai ya lalace Masa,ga yaransa Bai Isa dasu ba Talatu baza ta Bari suyi tallan magani ba,sai schl suke zuwa duk yanda za ayi su biya schl fees sai Sunyi,Haka shi kanshi Makahon baya so yaransa dama suyi tallan, sabo da Haka sai Zainab da Rahinatu suke damfarar samari suna ciyar da gidan tare da sutura,Wata katuwar kawaliya Hajiya ce suka hadu da Zainab take hada Zainab da manyan Yan siyasa da masu kudi suna mashaa Ana biyanta kudi,Hammad kuwa a bangarensa sai yanzu ya gane halin su Zainab sun cuceshi sun rabashi da wacce take me tarbiya Yana sonta Amma Sunyi Mata sharri sabo da Haka yaga Zainab ta Zama babbar yarinya ta gaske ta koma Fara kwal na Mai,tayi kiba Tasha kwayar kiba Kuma tayi kyau,sosai take gyara jikinta ka rantse Yar attajiri ce,kawayenta daga Yan Film sai manyan Yan iska.zainab ita kadai take daukan nauyin gidansu da komai,gashi tana Schl dinta,Talatu da Sabiu Makaho Alfahari suke da Zainab,Haka ma Ammar Soja Zainab ke biya Masa kudin schl.

Yau ma suna zaune Wani Alhaji ya bugowa Zainab waya ta fito ga Driver dinsa ne ya turo ya dauko Masa ita zasu hadu a Hotel,shiri tayi kamar zata fadar shugaban kasa tace Kawu Zan tafi sai dare,yace ki dawo da wuri fa ni ban San Ina kike zuwa ba Zainab Wai a Ina kike samo kudi haka? da Sauri Talatu tace ai aiki ta samu a wata Maaikata ta Agriculture,murmushi Kawu yayi yace to a dawo lfy Allah ya kiyaye,Talatu tace naso ace kawun Yara kana gani kaga yanda Zainab tayi kyau da kiba gaskiya Allah ya bamu yarinya me kyau,Kawu yayi Murmushi tare da cewa Kai kice kawai Ni Tayo? Talatu tace Kai Dan baka sanni bane kamar balarabiya Haka nake Dan kawai Kai Makaho ne baka sanni ba aka daura ma aure Dani,dariya su Rahinatu sukeyi Jin karyar babarsu Talatu data shararo ganin Kawu baya gani,da ace yasan yanda munin Talatu yake da ko a kafa aka daura Masa ita bazai karba ba.

Ammar Soja ne ya shigo ko Zama Bai yi ba yace Kawu Naga Khairat wlh da Yara biyu a hannunta yaran da gani jinin kudi ne watakil aiki take a gidan masu kudi tana musu rainon Yara,na ganta ta Shiga wani Company,tana ganina ta kwashe da gudu, Talatu tace Amma ka kyaleta ai kamota zaka yi ka fawo Mana da ita Dan Ubanta,baka ganin yanzu halin da muke ciki na rashinta bamu da Yar aiki,duk wahalar aiki ya isheni sanda tana Nan ita take komai,Kawu ne yayi magana gashi yanzu kana gani fita ta gagareni bana sanaar komai sabo da ba Khairat,da kuwa kullim cikin samun kudi nake Danma Allah ya taimakeni Zainab tana aiki yanzu,Soja yace wanne aikin Zainab take Kawu Banda Karuwanci,Karya kake cewar Talatu aiki ta samu a Maaikatar harkar noma.
Shuru Soja yayi kawai yace idan na sake ganin Khairat sai na dawo da ita ta karfi taci Ubanta na tsani yarinyar Nan,Talatu ta cafke zancen ko Dan aiki ai ta dawo Mana.

Khairat kuwa data Shiga Comp din da gudu kicibis sukayi da Musaf zai shige Office dinsa,ya kalleta shekeke yace wannan shegun yaran naki karki shugo min dasu Office kizo ki gyara min Office kuma,Wata Dattijuwa dake siyar da fura a building din tana siyarwa leburori ta Kai Mata su Meenal ajiya sannan ta Fara aikinta tana Mopping taji Musaf ya kamo tashar Xxx videos Yana kalla sai Ihu sukeyi shi Kuma Yana kallo ya nutse a kujera,zumbur ya mike Yana Kiran wata a waya yace Wanne Hotel zamu hadu? Tace Horizon Hotel yace ok zai fita Yana sani ya takawa Khairat kafa da takalminsa ya murza Kara ta kwalla tare da tsugunawa a wajen Ina kuka sabo da zafi,gashi skin Dina Bata da karfi Nan take wurin yayi ja wani wurin ma ya fashe Yana jini,ko kallo bata isheshi ba yayi gaba abinsa.
Bayan taci kukanta Haka na Karasa naje Office din Hunaif yau shine na karshe Ina kuka Ina yi,sai gashi yazo Office din kallo daya yayi mata ya wuce abinsa, itama bata kulashi ba tana kukanta har ta Gama,Zata fita kenan Allah ya Kai idonsa Kan kafarta ya ga yanda jini ke fita,Muryarsa me Masifar Dadi taji yace me ya sameki Kuma? Musaf ne kawai ta iya furtawa,Bai ce komai ba,yace tsaya to,tsayawa yayi taga ya dakko Wata Yar box ta kayan aikin asibiti,longslip shirt dinsa Fara ya nade hannun rigar tasa yace zauna a kujerar can ta koma inda aka tanadi lafiyayyun kujeru ta zauna saman one seater,tsugunawa yayi a kasa saitin kafafunta,ya bude Box din,ya dakko kayan aiki yasa auduga tare da dangwalo ruwan spirit ya fara wanke mata wajen,wani azabar zafi ya ratsata Wanda jikinta har rawa yakeyi,idonta na bulbulo da hawaye,fuskarta ya kalla abin ma dariya ya bashi yayi Murmushi kawai,ya sake saka wani kalar wanda ba zafi sannan yasa plaster ya manne mata wurin,uban gashin kansa take kallo da Dan sajensa kadan,ga gemunsa Dan dai dai kamar balarabe kyan da yake dashi ya tsine a duniya,tunani takeyi a Ranta ko dai aljanine Haka,ga mugun iya daukan wanka,bata taba ganinsa da manyan kayaba,kanana yake sawa masu tsadar masifa kamar wani Dan turawa Haka yake,ko waye ya kalleshi sai ya tafi dashi,Kamshinsa na daban ne,Shima Musaf Haka yake da kyansa ga wanka Amma ko kafar Hunaif Bai kama ba.
Muryarsa ce ta katse ta da tashi ki tafi ga yaranki can suna kuka,ki tafi gida na sallameki yau,farin ciki ya kama ta dama so take taje Kasuwa zata yi cefane.
Tana washe Dan bakinta tace Allah da gaske kake?Kai ya daga mata Yana kallonta,ta Kara cewa ko Musaf ne yace na dawo Kar na dawo? Nan ma ya daga mata Kai Yana murmushinsa Mai tafiya da ruhin mutum,tace Tam na gode wlh kuwa Ina ganinsa a hanya yace na dawo bazan dawo ba tayi waje tana Murna.

Tana fita yaranta suka rugo da gudu wajenta tana dingishi ta dauki Mohd shine karami sannan ta rike hannun Khairat suka Shiga Napep sai kasuwa,sabo da kudin da chairman ya Bata tayi cefane iri iri na talaka,ta siyi naman rago da kifi me Dan yawa,sannan ta siyi Danyar kaza guda suka dawo gida.
Zagewa tayi tayi miyar Egusi Tasha Naman rago tuwon Danyar shinkafa,sai ta soya naman daban,ta soya kazar ma daban ta ajiye musu zasu dinga cin abinci dasu kullum, kifi Kuma tayi musu farfesun sa sai da ta kaiwa Baba Isyaku da makwafciyarsu Sadiya.
Khairat Ita da yaranta suka kwashi dadinsu tayi wanki ta musu wanka itama tayi ta shirya suka zauna tana koya musu karatu suna wasansu.
Meenal wayo ne da ita ga Saurin girma ya Dace ace ma an kaita Schl zamanin yanzu.

Yau Sunday Khairat ba aiki da yamma lis ta fita siyowa Yaranta Madara da take hada musu Oat,Su Kuma ta barsu wurin Baba Isyaku,tana can kasuwa Hadari ya hada ya taso gashi ta bar kasuwa tabi hanyar titi ta mike tana sauri ba Taxi ba Napep,ruwa ya tsuge kuwa tana ta tafiya Haka ta jike ga ruwan me karfi,ta danyi nisa taga Mota fyaleliyar gaske yawan ruwan da ake yasa sun kasa tafiya suka gangare gefe tare da tsayawa,kawai tana zuwa ta kwankwasa glass ba Wanda ya kulata,motar Tasha tint gata baka, handle ta murfin motar ta ja Aiko mota ta bude ta fada gidan baya abinta tana karkarwa ga madararta a Leda a hannunta.
Wani kamshin Dadi ne ya ratsata ga motar dumi,gefenta ta kalla kawai tayi mutuwar tsaye ganin Hunaif ya hade cikin Shadda Fara fadin kyan da yayi Bata Baki ne.
Kallon jikinta tayi sanye take cikin doguwar rigarta Yar kanti da mayafinta Wanda karami ne,ruwan daya daketa yasa rigar ta manne a jikinta ta fito da surarta me matukar kyau,sannan gashinta duk ya kwanto a goshinta yalala dashi Yana digar da ruwa.Da sauri ta gyara mayafinta ta bude mota a tsorace zata fita tana bashi hakuri ka..kayi hakuri.

Ta yunkura zata fita taji muryarsa yace zauna,Ana wannan ruwan Zaki fita bakya son lafiyarki ne? Shuru tayi ta zauna gabanta na faduwa ita kam tsoron Hunaif takeyi Yana Mata

Please Login or Register in order to submit comment