Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tsakiyar gogoron aka fito dashi tare da sakinsa a bayan Khairat aka Masa wani style na daban Wanda ya bada ma'ana,Sarka me kyau black and white me tsadar gaske aka sawa Khairat da Dan kunne,sai bangles a hannu daya,da Agogo fari,fadar yanda Khairat ta hadu Bata Baki ne,Takalmi me Dan tsini kadan tasa da pose hadaddiya,duk same color kamar Diamond.
Kowa yaga Khairat sai dai yace mashaallah.

Frnds tuni sun cika wurin da za ayi Event din maza da Mata Ana can Ana ta shagali,Suma su Zainab Sunyi gaba abinsu,har su Ladi gidan ba kowa daga Amarya sai Sadiya,suna fesa turaruka Kiran Hunaif ya shigo wayar Khairat,Sadiya ce ta Daga wayar yace ku fito gamu munzo muna gate.
Wata mota sabuwa dal me azabar kyau Fara kwal Motar kowa ya ganta sai ya koka,Tasha adon flowers a jikinta da gani kasan ta Amarya ce gata Tasha tint.
A nutse Khairat suke Tafiya,Sadiya ma ta dau wankan kure adaka, Mus'af Dan kar duniya ta zageshi sai ya danne zuciyarsa ya koma suka shirya da Hunaif sabo yaga idan Yana nesa dasu bazai taba cin nasara ba,gwara ya dawo jikinsu yanda zai samu Nasara cikin sauki.
Munafuki sai gashi shine Driver cikin sabuwar Motar Hunaif fara,Hunaif ya lafe a baya Yana jiran Amarya ta Shiga,Farouq Kuma shima ya tsaya da cadediyar motarsa ya dauki Sadiya sun wuce, Mus'af sabo da munafunci da kansa ya fito Yana fara'ar Dole ya budewa Khairat mota kusa da Hunaif ta Shiga ya rufe sannan ya Shiga tare da jansu suka bar wajen zuciyarsa na suya.

Hunaif Kallon Khairat yake ba ko kyafta ido Yana mamakin yanda ta Kara haduwa Haka,ta gefen Ido tasan Yana kallonta sai duk taji ba Dadi kunya ta rufe ta,juyo wa tayi kadan ta Dan kalleshi,ai da sauri ta dauke kanta yanda gabanta ya buga ganin irin tsaruwa da haduwar da Hunaif yayi kamar wani Aljani, wata arniyar suit yasha black and white,harda wata Yar flower a saitin Kirjinsa a manne,dai dai jikinsa fitted sosai normal,sumar Nan ta Sha gyara,Kai Babu Wanda zai ga Hunaif bai Kara kallonsa ba,Khairat a wayance take ta kalleshi ba tare da ya gane ba,shima Haka yake ta faman aikin kallonta.
Har suka je wurin Basu San sunje ba kowannensu na kallon Dan uwansa,Musa'af ne ya musu magana ku fa ake jira, yayin da a ransa tsinewa Hunaif kawai yakeyi.

Kawayen Amarya aka jera wasu,sai Frnds na Ango tare da danginsa Larabawa da Kuma na Ummi Yan Nigeria,Khairat ma dasu Zainab sai kawaye aka tarbesu an Shimfida Wani carpet fari ta Kai Ango da Amarya ke takawa a hankali an sasu a tsakiya sannan Ana fesa musu Golden Buzzer me kyallin fari da Baki,Hannun Khairat Hunaif ya rike Wanda sai da suka ji Masifar shock,Har Wurin zamansu aka rakasu suka zauna kidan soyayya na tashi na turawa,Yan biki sai yabon Ango da Amarya sukeyi kowannensu na ji da kyau.

Mc ne ya fara jawabi tare da Kiran Uwar Ango Ummi Kan ta fito ta bude taro da Addua, Ummi ta fito cike da Jin Dadi,cikin Shiga ta Alfarma kamar matar sarki,Addua tayi aka bude taro sannan Mc ya Kira babbar kawar Amarya Sadiya a takaice ta bada tarihin Amarya da turanci,Haka ta dinga zubar da turanci,Sai Farouq ya mike ya bada Dana Ango shi Kuma da Yare biyu yayi farko ya fara zubar da larabci sannan Turanci, Mus'af yaji Haushi Akan ba shi aka bawa babban abokin Ango ba.
Daga Nan aka Dan Sha kida masu rawa suna yi Ana barin Naira.

Amarya da Ango aka Kira Kan zasu yanka cake, suka yanka ya fara yankowa tare da sawa Amarya a Baki,tafi akayi Ana dariya sabo da yanda Khairat ta bada show Ango ya kawo zai saka Mata a Baki sai ta shagwabe fuska sannan ta makale kafada Wai Taki,wasu harda Ihu akeyi ta kayatar,Yankowa tayi itama Tazo zata sawa Ango ya karba sai Hunaif shi Kuma ya rike Hannunta tare da hadewa da yatsunta,Yar Kara ta saki aka dauki tafi da sowa,Ummi a kafada ta daki Dan nata da Wasa.
Bayan Nan aka Kara Shan kida da liki,sannan kowa yaje ya Devi Abinci kalar Wanda yake son ci,Bayan an lafa aka ci gaba da ragargazar rawa ba ji ba gani Ana ruwan Naira,ranar ansha kallo,Dinner ya kayatar matuka,tun 7pm aka fara sai 1am aka tashi.
a mota Amarya har ta fara gyangyadi sabo da gajiya,shi kuwa Hunaif dadin baccin nata yaji domin ya samu damar kallonta da yawa,a kujerar ta mike ta kwanta sosai tare da yin matashi da cinyar Hunaif,har suka kaita gida lokacin bacci takeyi sosai,motar ya bude a hankali ya fito, Musa'af Yana kallonsu ransa na Kara baci sai yaga Hunaif ya dakko Khairat kamar jaririya tare da komai nata Bag etc ya kaita har gida,Ladi tace kaima da biye Mata sauketa, Khairat tana magagin bacci ta Karasa dakinta inda su Zainab ke Hira su da sauran kawaye,Khairat ta kwanta ko kayan Bata cire ba,shima Hunaif tuni sun tafi gida.

Washe gari da wuri Yan Matan Amarya sukayi Shirin tafiya Kano tare da Yan Daurin aure za a daura.Ango dai da Amarya ba wani shiri sukeyi ba,Hunaif anyi fushi sabo da yaga Mus'af wurin Khairat,ita Kuma Khairat ta kyale Hunaif Bata bashi Hakuri bsannan ta Gaza fada Masa me ya faru.

Hunaif Already ya turo da motoci za a kaisu Airport,Jirgin Karfe 9 na safe suka bi tare da tafiya kafin angwaye suzo,wacce Bata taba Shiga jirgi ba yau ta Shiga,Su Zainab sai Selfie akeyi da Amarya a jirgi,Haka Bayan Sun Isa Kano, Farouq tuni an shirya masu daukansu zuwa gidan Kawu,Suna zuwa ba Bata Lokaci sukayi wanka ko wacce ta cakare,Khairat Shadda tasa dinkin Senegal Sea blue me adon Silver color tayi azabar kyau, Talatu sai kaiwa da kawowa akeyi cikin danginsu.
Suna zaune Khairat kanta har ciwo yake sabo da zirga zirga,gashi duk tsoro take ta faman ji,Soja da su Kawu an dau wanka Ana hada hada,Haka ma Kawu Sabiu.

10:30am Angwaye da danginsu maza da wasu Matan jirginsu ya sauka a Kano,Bayan sun karaso gidan Kawu sai suka wuce Katon Masallaci na unguwar Wanda a Nan za a daura aure,ba karamin Dan Adam aka Tara a wajen ba,mutane manya manyan masu kudi sun halarta ga Larabawa da turawa duk a wajen.
11:30am aka fara khudubar daurin Aure,ga walliyan Amarya gana Ango fa nan aka daura auren HUNAIF da KHAIRAT Akan sadaki dubu Dari uku cash sannan tare da tabbatar da Takardar asibiti na Medical check up kowa cikinsu lafiyayye ne Babu cuta waccce mutum zai dauka ta cutar da Dan uwansa.
Speaker Ana ta sanarwa,Maroka da makada suna ta aikinsu, Hunaif yau harda Babbar riga shadda ce ta bugawa a Jarida Sea blue shima da wata Yar hularsa me tsada kalar shaddar yayi Mata sawar samarin zamani,baya Kuma sumarsa ce luf luf tana sheki,takalmin ma Haka abin kallo,kowa yaga Hunaif sai ya girgiza da kyawunsa sai ka rantse baya Jin Hausa balarabe ne.
Hotuna aka fara dauka kala kala Ana ta Yi ba ji ba gani,Daga Nan suka Shiga gaisar da iyayen Amarya, Khairat kuwa tana Jin an daura ta sauke Ajiyar zuciya tare da Furta Alhmdllh ruwa ta sha, ta mike tsaye tana wani Murmushin Jin Dadi,Zainab tana an daura su Khairat an Zama manya ayyiriri,Sadiya ta Fara yiwa Khairat kida da Baki ai kuwa sai Khairat ta Fara taka rawa.

Angwaye sai neman Amare sukeyi su fito ayi pics,Hunaif sai nishadi da warkajaminsa yakeji Yana farin cikin da Bai taba yin irinsa ba,yau ba a fushi da Khairat tana Fitowa ya jawo hannunta ta dawo kusa dashi gefensa, Yan Mata suka fito sai hotuna kyas kyas ake ta faman yi,Sadiya da Farouq sai hirarsu sukeyi.
Bayan komai ya lafa angwaye suka wuce reception anci ansha a lafiyayyen wuri kida na tashi sannan suka bi jirgi tare da komawa Abuja.

Dangin Ango Mata su Uku suna Nan zasu dauki Amarya,Ladi tuni ta koma Abuja an Gama kaiwa Khairat kayanta Na sawa Wanda ta dauka tana so Yan kadan sauran duk ta bawa Rahinatu da Zainab,Lefenta duk an Kai gidan mijinta.
Sun Kara gyara part din ko Ina Yana zuba kamshi,Amarya kawai ake jira,Kawu Sabiu da sauran Dangi sun yiwa Amarya Nasiha sosai Sannan aka dauki Amarya zuwa Abuja,Gidan Ladi suka kaita ta sake sabon shiri cikin material na India Riga da skert ready made ne black and dark blue Tasha kyau,Ladi ma da Yan uwa sai Nasiha akeyi,cikin masu Kai Amarya harda Talatu,Hunaif ya kawo Motoci aka kwashi Amarya da dangi tare da kawaye sai katafaren Gidan Hunaif,Ummi Kuma tace ita baza ta zauna gida Daya da suruka ba,gwara tana nesa yafi mutunci,gidan da Hunaif ya kaita idan an Gama biki ta dawo fafur tace ita gidan ya burgeta a Nan Zata zauna,cikin danginta ta dauki wata yarinya Yar 11yrs Khausar da wani matashi Dan 16yrs Ameer wai zata rikesu su zauna tare.

Hunaif ba yanda baiyi da Ummi ba Kan ta koma Gidan takiya,dama wayo tayi Masa,gidan ma ba nisa layi daya ne dana Amarya Yar tafiya kadan ce a kafa.
Khairat ko kuka Bata yi ba,sabo da ta Saba dama da barin gida ba wani Kuka sai kwalla da tayi na sabo da Ladi tare dasu Talatu,sai tunanin Kuma rayuwar auren da zatayi da Hunaif tunda Bai damu da ita ba a ganinta.
Ana Kai Amarya sai santin gidan akeyi,Bayan 15mnt Ladi ta hada Kan Yan Taraba Dangin Amarya maza da Mata aka kaisu Airport suka tafi gida lfy,Na Kano ma har su Zainab aka tattarasu a jirgi suka tafi Kano lfy,Haka Dangin Ummi,Dangin Ango na Uba,Yan Uwan Ladi dana Talatu kaf kowa ya tafi gida,duk Hunaif ya dauki nauyin komai suka koma lfy,sabo da bikin Yan gayu akayi Babu wasu Baki da zasu zo su tare a wuri Suki tafiya komai a tsari akayi shi kowa ya huta.
Abin kokarin Da Kawu yayi harda Gara yayiwa Khairat me yawa,duk da cewa Store Ango ya cika abinsa da Abinci sai da Kawu yayiwa Khairat gara,Wanda hakan ya farantawa Khairat Rai sosai.

8pm Baki tuni sun koma gida lfy an musu ban gajiya,Yan aiki ke gyare gyaren inda aka Bata bangare Amarya da Kuma gidan Ango,Ladi ma tana can tana gyara inda ya Baci,su Zainab ma haka.
Mus'af Yana can Hotel Zazzabi ya lullubeshi Ciwon Son Khairat,Hassada da bakin ciki ya jawo Masa zazzabi,Ana ta nemansa za a raka Ango 10pm gidansa Amma ba labarinsa,Daga Farouq sai Hunaif suka tafi gidan Amarya abinsu,Khairat tana zaune tsakiyar bed ta rufe kanta da mayafi me shara shara tayi Shuru tana sake sakenta da tunani.
Sallamar Hunaif ta Fara ji gabanta ya Fadi Ras,Farouq iya karsa bakin gate ya sauke Ango ya juya da motarsa ya tafi Hotel Room dinsa zai kwanta ya huta.
Khairat tana Kallon Hunaif ta gyalenta.

Gefen Bed ya zauna sanye yake cikin wani yadi me laushi shara shara milk color yayi kyau matuka,Khairat tayi Shuru shima Angon Bai ce komai ba ya matsa kusa da Khairat daf da ita,a hankali yace bude fuskar Mana malama,sabo da ya Saba da matansa duk da yake aura duk fetsararru ne su suke nace Masa suna shakoshi saman bed Dan ya kusancesu,Har Ameera da yake tunanin Me hankali ce itama Saida ta nuna zalamarta a kansa,Amma Khairat Sam ko damuwa dashi Bata yi ba Anya kuwa kalau take ba aljanune suka auretašŸ¤£ kunji Hunaif Akan ba a kwamushe shi ba a saman Bed.

Ta cikin Mayafin Khairat tace Kai Wai Haka akeyi ne Kaine fa zaka bude min fuskar,Bude Ina jirinka ko nayi zuciya na kwanciya ta a Haka,Kallonta Hunaif yayi Yana Murmushi yace Zaki kwana ashe ba a budeki ba Ni nace ki rufe kanki ki komai sai kinyi al'adun Bahaushe.
Ganin da gaske baza ta bude Mayafin ba yasa hannunsa daya tare da fisge Mayafin fitttt..ya jefar saman bed Yana cewa yarinya sai tsiwa ai sai ki tashi,Khairat tace ai daukan Amarya akeyi komai Bata yi da kanta fa,Ina zan kaiki? Toilet Mana muyi Alwala da Sallah,to ai na sani Amma Ni banji labarin ana daukan mutum ba,Da kanta ta sakko kasa tare da kallon ledar kajin daya ajiye ta hadiyi yawu sannan ta fasa tafiya ta zauna gefensa,Murmushi ya saki da gani yasan yunwa take ji,jeki dakko plate,Khairat tace Ina Amaryar zaka aikeni salon ka Tara min wanke wanke da safe nayi ta aiki,Ni dai muci a ledar.
Ido ya zaro wannan kuya gare ta ya furta,A ledar kuwa suka ci abinda suke so suka Sha Madara da lemuka sannan Khairat ta fada toilet tayi Brush tare da wanka ta fito sanye da katon Hijab sai ta Iske Hunaif tuni yayi tafiyarsa Room dinsa,a nutse ta shirya cikin kayan baccinta me kyau Riga me siririn hannu ta Kai gwiwa me laushi,ta Mata kyau sosi, Zani ta daura tare da Sa Hijab,Sai ga Hunaif ya shigo sanye da jallabiya Fara da Alama shima wanka yayi,Sallah ya jasu sukayi Nafeela rakaa biyu tare da adduoi na sunna sannan Khairat ta cire Hijab da Zanin tare da linkewa ta adanasu ta haura saman bed sabo da ta gaji bacci take ji.
Hunaif shi Kuma sai yayi tunanin Khairat ba kalau take ba,ko damuwa dashi batayi ba sabanin matansa na da masu makale Masa.

Kallo ya Kare Mata yace ko bakin Aljani ne da ita,Yana kallo tayi baccinta,a hankali ya lallaba ya fara karata mata Ayatulkursiyu maganin Aljanu,Wai ko zata tashi ta makaleshi suyi bacci, Shuru ko motsi Khairat Bata yi ba,Harara ya watsa Mata tare da Furta ko Abinci Bata bani a Baki ba Amma duk sauran Wanda na aura sune suka dinga bani a Baki,wannan yarinyar ko kyawuna Bata gani tsaki yaja kadan ya fita abinsa tare da komawa Bedroom nasa.šŸ¤£Dan rainin hankali Ashe ma shine Amaryar ko ya kuka ce fans.

Da kyar ya samu bacci ya kwashe shi,da Asuba Khairat ta farka ta ganta cikin Barko Hunaif ne ya dawo ya dubata cikin dare ya lullubeta tare da kashe Mata light.
Murmushi tayi kana ta mike ta Shiga Toilet tayi Alwala tare da Sallah ta zauna tana Azkhar ta kusa gamawa ta tuna da cewar ya taba fada cewar Ummi ke tashin sa da Asuba,Shirmen Khairat Wai sai ta fada Toilet ta fesa wanka tare da Brush,tazo ta zauna ta ci kwalliya kamar wacce zata je Party cikin Atamfa Orange and Green,tayi kyau dinkin cas a jikinta Riga da skert kamar a jikinta aka dinka,tana zuba Kamshi ta Shiga Bedroom dinsa dauke da Sallama a bakinta,lokacin Rana tayi, saman Sallaya ta hangoshi Yana bacci hankalinsa kwance,ganinsa tasan yayi Sallah ma Amma sai ta gwada tashinsa ko baiyi ba shaawar kwanciya yayi a kasa.
Yatsansa Babba ta Kama tare da Dan ja kadan,a hankali ya bude idonsa masu kyau ya kalleta Yana wani Murmushi sabo da
Birgeshi da tayi da Sassafe har tayi kwalliya sabanin matansa na da,sannan a zamanin Nan ba kowacce mace zaka samu tana kwalliya da safe Haka ba,ko ta Fara na Amarci ne dainawa sukeyi.
Idonsa ya lumshe ba zato ya jawo hannunta ta fada kansa,Rungumeta yayi a jikinsa sosai kamshinsa ya hanata sakewa,tana so ta kwace Amma kamshinsa me Dadi ya hanata hakan,a kunne ya rada Mata Babu gaisuwa,Murmushi tayi me Sauti kana tace kayi Sallah ne?
Yaushe zanyi Sallah kiyi? Ya Mata habaici,Allah baka hakuri ba nufina kenan ba.
Saukar min jikina kin makale min,ba ruwana Ni Kaine fa ka rikeni ka sakeni Mana ka gani.
Sakinta yayi ta mike da sauri,ya tashi tare da Shiga Toilet zaiyi wanka.

Mus'af tun jiya Bai runtsa ba,Yana tunanin Yanzu Hunaif ya dandana zumar Khairat,da kyar ya mike yayi wanka tare da shiryawa sannan yayi Sallah ya zari key din mota da sauri sai Hospital ganin Doctor,Bayan an duba shi tare da bashi Magunguna sai ya tsaya a mota ya Kira sabon Malaminsa,Malam yace kafin ka Shiga gidan ka saka wannan kwallin Dana baka idan kaje ka tabbatar kunyi Ido hudu da Amarya,sannan kamar yanzu da safe zaka je ka kalleta.
Ai ko sai ya dauke Hanya ya tafi gidan Hunaif tare da tsayawa a bakin Gate yasa tozalinsa.

Lokacin Hunaif ya fesa uban wanka cikin Shadda Silver color ya Hadu karshe,Yana fesa turare yaji mota Me gadi ya bude Gate,tunaninsa ma Ummi ce ta Aiko musu da Breakfast sabo da tace sai Sunyi sati Khairat zata Fara girki.
Ta window ya leka ya Hango Mus'af ya fito a firgice,mamaki ya Kama Hunaif ko ba lfy ba Taya Mus'af da ko bacci sai 10am yake tashi Amma gashi Haka yazo da Sassafe.
Door bell ya dannan kirrrrrr, Khairat tana Palo ta mike tare da bude Kofa,kamar ta sani ta sadda Kai kasa Bata ko kalleshi ba taji Muryarsa tasan shegen ne yazo,Gashi Taki kallonsa yace Amarya barka da Asuba,ya Amarci ya Furta da fara'a Dan ta kalleshi,Khairat ta Dago da kanta Amma sai ta kalli jikin bango, Mus'af har da wani zaro Ido waje Dan ta kalleshi Amma Khairat sabo da Tsanar data Masa fuskarsa ma Bata kaunar gani.

Alhmdllh tace fuska ba Rahma ta Haura saman Hunaif ta Shiga dakinsa tana fushi cike da Shagwaba tace ka fito kayi min waje da wannan mutumin bana kaunar ganinsa Ni Allah,Shagwabar ta birge Hunaif yace Mus'af din? Ae Ni dai tsakani da Allah ance Musulmi yaso musulmi Ni dai bana sonsa komai musuluncinsa,Murmushi ya saki to me yasa Baki fada Masa ba? Ai Dan karka ji Haushi nane Amma kadan ne daga aikina na koreshi.
Gatse Hunaif ya Mata yace to jeki koreshi,Bai San Khairat a kwai kuruciya ba sannan idan suka Kulla da mutum ba ruwanta ubansa zata ci,tace na gode matukar baza kaji haushi na ba,Amma muje na saka a gaba a gabanka zanyi komai taje jikin Hunaif tare da sakala hannunta a nasa tana cewa kayi kyau muje,suka jera zuwa kasa wurin Mus'af,Sunyi kyau,suna kamshi Kuma sun Dace da juna, Mus'af ji yayi kamar ya cakawa Hunaif wuka ya mutu,da kyar ya iya dannewa Yana so Khairat ta kalleshi su hada Ido sai yaga Hunaif take ta kallo kamar zata cinyeshi sabo da ya Mata kyau da yawa.

Harara Hunaif ya watsa Mata da Wasa tace sai dai kayi ta fushinka sai na kalla na more wa yace ka biya sadaki,dariya yayi ba shiri, Mus'af huci yake Yana Jin zafi a zuciyarsa,Gashi bukatarsa Bata biya ba ga Kuma Yana ta kallon takaici da idonsa,Bai Gama kwasan bacin Rai ba sai da yaji furuncin Khairat Malam Mus'af ka daki gurbi,Ina ka taba Jin Ana zuwa gidan Amare da safe haka? Oh kallo kazo ka gani na tashi lfy ko Ina tafiya? Tana magana ta Bata fuska idonta a rufe ruf sabo da rashin kunyarta ta motsa,Hunaif ta Nuna tace wannan da kake Gani Expert ne ya iya harka lfy Lau muka ji dadinmu,yanzu da Sassafe Kuma kazo zaka Shiga Hakkinmu,fitar min a gida Malam yanzu nice me gidan uwar yayansa sabo da Haka baka samu karbuwa ba,Da Sauri Hunaif yace Khairat Mene ne Haka? Kaifa kace baka da lokacin ganinsa kana da kamata Me zakayi da Mus'af,sannan ka bani labarin irin tuggun da yake hada maka na korar maka Mata sannan ya zage ya auresu.
Mus'af ya mike a fusace wato Hunaif Kaine kasa tayi min Haka ko? Ni Musa'af Ni Baku Isa ku wulakantani ba wlh,Akan ka auri wannan Abun? Khairat ta bude Baki zatayi magana Hunaif ya jawota jikinsa tare da rungumeta zatayi magana ya hade bakin su wuri daya Yana tsotsa tun yanayi Don Kar ta sake yiwa Mus'af rashin kunya har ya koma na soyayya Bai ma San da wani Musa'af ba ya Gama rudewa,Khairat ma ta wani dage kafafu tare da sakalo wuyansa da hannayenta tana maida martani, a fili Mus'af Yace kun jawowa kanku,wlh na daina sonki yanzu fadan Makiya zai Fara,sai na wargazaku,Hunaif sama sama yaji Furucin Mus'af da yayi niyyar ya bashi hakuri Amma jin yace son Khairat dinsa yake sai yace Mus'af dama matar tawa Dana ke aure kake so? Mus'af ya juyo yace kwarai tun kafin aurenku Kuma wlh sai kasan Ni ka wulakanta,Hunaif yayi Murmushi yace Ina zuba Ido.
Khairat Kuma tace a sannu sai nasa ka tsani kanka,sai na nuna ma Khairat ta daban ce,yanzu Hunaif ya auri ingantacciyar mace.
Barin gidan yayi a fusace Yana faman Danna Horn a bude Masa Kofa,kafin Gateman ya bude Mus'af ya fito a motar ya samu Dattijo me gadi ya fesa Masa maruka har Uku sannan ya bude Gate da kansa yayi waje,daga Nan Bai tsaya ba sai kauyensu ya tafi sake sabon shiri yanda zai dawo ya tarwatsa Khairat da Hunaif tare da Ummi ya karasata.

Tunda Musa'af ya fita su Khairat suke faman tsotsar lips din juna sai da kyar ta dawo Hayyacinta ta kwace kanta da kyar,suna Haki kamar Wanda sukayi Tseren gudu... Khairat ta Kalli Hunaif kunya ta kamata ta boye fuskarta cikin Cinyoyinta,Murmushi yayi me Sauti,ba tare data Dago ba tace yaushe Wai ya akayi na iya wannan Abun ne? Taya na koya? Hunaif yayi dariya ba shiri sannan yace me kikayi ya zauna kusa da ita,tace uhm....wannan Abun Mana Abun Yan Iska Nan da mukayi yanzu fa.
Wai abun Yan iska See you abin masu aure ake cewa,Khairat ta Dago da kanta da sauri tace kai wlh sanda Zainab ta Zama Yar iska Bata da aure fa Naga suna ta Yi a mota da saurayinta,kaima watarana ka taba yimin kadan sannan yanzu zaka ce abun masu aure to harda samari da Yan Mata yanzu Yi sukeyi,Murmushi yayi Yana me dariya yace to uwar surutu ki Fadi gaskiya tsakani da Allah da Dadi ko ba Dadi? Khairat ta daga Kai cike da kunya tace dadinma harda na masifa,Wanda ka taba yi min kaga dai Dan kadan ne ko kafin muyi aure? Hunaif yace ae, tace to kullum sai nayi ta tunanowa.
Ai Dan kina so nane shi yasa Kika ji Dadi,Khairat tace yaushe nace Ina sonka? Gashi kina min kallon so kuwa,Khairat tace to Kaine baka ganewa kallonfa kiyayya ne nake maka.
Dariya Hunaif yayi suka ji Karar Door bell,Khairat tace maybe Musa'af ne Lallai watan cin ubansa ne ya tsaya kawai, Hunaif ya kalleta tare da furta karki sake Masa rashin kunya frnd Dina ne, Hmm Kai Wai ko kishina baka yine nifa yace Yana so,sanda ka ganshi a gidanmu wurina yazo zance zai kwace maka Ni Amma Kai kullum baka ganin laifinsa,to Ni Allah maganinsa zanyi,idan Kuma kaci gaba da biye Masa sai na koma na soshin kawai tunda Haka kake so,da sauri Hunaif ya kalleta Yana me hade fuska cikin fushi ya Furta ki soshi fa kika ce?kina matar tawa? To ba Haka kake so ba,Amma Kai kullum ka zama Namiji ka kasa sai kana wani sanyi,Shike Nan indai Zaki iya ki min maganinsa na Baki dama,Khairat ta kyalkyale da dariya tare da kwanciya a kafadar Hunaif tace harna gama kulla muguntar da Zan masa.
Mikewa Hunaif yayi Yana Murmushi a duniya komai Khairat tayi Kyau yake Mata,gata da iya Shagwaba,idan tana taba Masa ko hannu ne wani Dadi yake ji yanzu data kwanta a jikinsa kamar su dawwama a Haka,yau Kam ya rantse tare zasu kwana ko Bata zo inda yake ba zai je wurinta,ga iya Hira ga kuruciya,gata da abin dariya.

Karar Bell suka

Please Login or Register in order to submit comment