Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aure daga Dangin Mahaifinsa,Farouq frnd nasa,Ummi sai dangin Khairat, Mus'af ya cuci kansa ya tare a Hotel Akan Yana Jin Haushin Ummi yaki Zama a gidan Bai San me akeyi ba,Haka Hunaif Bai ko neme shi ba ganin Mus'af Yana wani share shi, Ana Haka Biki sai karatowa yake,Yayin da Amarya ta Sha uban gyara ta ko ina,kyau ba a magana,ga Ladi Bata fiye barinta tana zuwa wajen Hunaif ba,ya Dade baya ganin Khairat har ma ya rabu da ita ya Shiga harkarsa,saura sati biyu biki Farouq ya bugo hadadden iv na gani na fada kowa ya kalli Iv din yasan na masu kudi Ne,na ango daban na Amarya daban,Khairat nata iya Wedding Dinner aka sa on Saturday 5pm event daya zata yi ba wahalar da Kai.

Hunaif Kuma Daurin Aure da Wedding Dinner aka sa a jiki kawai,Dinner Saturday,daurin aure Sunday Kuma a ranar za a Kai Amarya.

dangin Khairat na Kauye zasu wahalar da Yan Daurin Aure sai suka ce su zauna kawai zasu zo gidan Kawu Sabiu ayi komai a Nan,Sai Hunaif yace Yana da Masauki za a Basu a cikin Abuja kowa ya zauna cikin Jin Dadi aci a Sha a daura aure a Kai Amarya sai su tafi kawai,dangin Khairat sai Godiya suke,Nan Kuma Sadiya kawar Khairat tace Dole suyi gayyar frnds da yawa,Sadiya ta dinga kaiwa kawayenta schl mate nata Iv,Haka Khairat ma Wanda ta sani na unguwar duk da ba wani kawaye gareta ba domin Bata Shiga harkar kowa Amma ba laifi duk wacce suke mutunci ta gayyaceta,Sadiya kuwa a kawayen nata ma idan Baki hadu ba baza ta gayyaceki ba.
Saura Sati daya biki Ummi ta aiki Yaron Hunaif Usman Kano ya kaiwa Iyayen Mus'af Iv, tare da Yan uwa da abokan azirki na ko Ina dage Nigeria,da Kuma na kasashen ketare an tura through social media,gidajen radio,tv Ana ta sanarwa ko Ina an San da bikin abinka da me kudi,Lefe kuwa kawar Ummi Hajiya Bilki Yar kirki itace Yar kasuwa tana zaga kasashen duniya tana business itace aka bawa kwangilar Hado lefe,size na Khairat kawai ake fada Mata,ta hada akwatu set biyu guda goma Sha shida,ko wacce Tasha Kaya na alfarma,Babu abinda Babu a lefen kowa ya gani sai ya koka ya tafi da santin Kaya.
Ladi da kawayenta tare da Dangin Khairat wasu Mata da maza sunzo su Bakwai suka karbi lefe a gidan Ladi sannan suka koma sai Kuma biki,Ana ta tururuwar zuwa ganin lefe,Khairat kuwa takanas ta shirya ita da Sadiya Maman Sadiya ta Sa Driver ya kaisu Kano zasu gayyaci kawayen Khairat dake Kano Unguwar su Kawu,sannan zasu je wajen su Kawu Suma a gayyato su,Har sun tafi tasa Driver ya koma Office din Hunaif,waya ta Masa kana Ina pls?

Office ya Bata amsa,gani nazo zamuyi Sallama Kano Zan tafi kaiwa su Kawu Iv,a mota ta bar Sadiya ta Shiga Office din Hunaif,sai kallonta yakeyi yanda ta canja Baki daya tayi shegen kyau,sai kamshi da sheki takeyi,fuska a tamke yace sai yanzu Zaki wani tafi Kano,ko tsoron Tsautsayin Amarya bakya ji? Dariya ya Bata tace au Amarya har Tsautsayi gareta? Usman ya nema yace yaje ya yiwa Khairat da Sadiya Booking din jirgi from Abuja to Kano, Khairat ta kalleshi kawai tace da ka barshi mun tafi,banza ya Mata ya dakko envelope Wanda kudi ne dubu dari cash ya Mika mata Wai tayi Hidima dasu,Farouq Yana Kano zai zo airport ya daukeku duk inda kuke so Driver din Farouq zai kaiku,number Farouq ya bawa Khairat tayi saving,sannan ya turawa Farouq ta Khairat.
Godiya Khairat tayi,Usman yace an Gama komai ya mikawa Hunaif flight ticket nasu,Su Khairat Drivern su Sadiya Airport ya kaisu ya koma gida,Su Khairat sai Murna akeyi za a Shiga jirgi again.

Su Kawu sun Iso Kano mota ta tsaya a kwanar dawaki Tasha,Dole suka sauka suka Shiga Mota zuwa cikin Kano,a Dangi suka sauka tare da Shiga Napep zuwa gida,sai Murna sukeyi,Tun a Lagos Kawu ya tsaya ya siyi manja jarka daya Babba,da Doya guda shida,Sai Talatu ta siyowa su Zainab kwakwar manja,da Coconut,Kawu yace ya kamata suyiwa yaran abin arziki sabo da Haka sai Talatu ta zabowa Soja 3quarter da singlet daya,Yan yaran ma Haka mazan kowa 3quarter da singlet,Rahinatu Kuma ta siya Mata Glass Baki faskeke da Riga wata tsangalalliya ita ta wuce gwiwa Amma Bata Kai kasa ba irin ta arna masu Talla a titi.
Zainab kuwa ganin Yan Mata ce sai aka siya Mata t-shirt da Dan Skert me rawa,irin Wanda kana tafiya Yana rawa na masu gasa masara a titi, da an ga kayan an San wannan kayan sai talaka shi zai sa.

Sabo da Haka da suka sauka a Kano Kawu dauke da jarkar manja,Talatu ta riko ghana must go sai Doyarsu etc a buhun bacco.
a kofar gidansu Napep ya saukesu suka biya shi ya tafi,Don Kar a ganesu suji kunya sai Talatu ta rike Hannun Kawu kamar walkiya wukil suka fada cikin gida kamar Aljanu.
Lokacin Zainab ta fito tana kwashe girkin da ta gama na Rana katsam ba zato taga Su Kawu sun Fado gida da gudu ba sallama har suna bigewa,Da kyar ta iya ganesu sabo da wahalar da suka sha, ihu ta saki da tsalle tare da ihu, Rahinatu ta fito,Soja da sauran Yara suka yo waje,ai gaba daya duk Doyin da Talatu ke Yi Basu ji ba suka rungumesu suna Ihu da murna.

Bayan komai ya lafa Talatu ta kalli gida gaba daya ya canja yayi kyau sabo da Tsafta,Yara duk sun nutsu abin mamaki,Talatu tace ki fara bani labari me ya faru Bayan tafiyarmu,Nan Soja ya kwashe labari ya fadawa Talatu,yaran Nan sannu kunsha wahala kuyi hakuri da yanda muka raineku,bamu koya muku Abun Kirki ba,ku yafe mana mun gane kuskurenmu Allah ya kawo Khairat duk mu taru mu yafewa Juna,Suka hada baki wajen cewa Ameen,nanfa Talatu ta Fara Hawaye tana Basu labarin irin gwagwarmayyar da suka Sha tunda suka bar gida da niyya tafiyar Makkah, Rahinatu tace Khairat Bata da masaniyar Zaku Shiga wannan halin na tabbata .
Nanfa aka dinga Hira sai da suka huta suka ci abinci suka Sha ruwa sannan Talatu ta Shiga toilet ta dinga dirje jikinta,Bayan ta Gama yin wanka fes sai ta samu ta dinga Brush ba ji ba gani har gawayi da gishiri ta hada ta goge,Kawu ma Haka. gida Rahma sai gasu Talatu Ana bacci.

Su Zainab su dai abin mamaki ya Basu Jin su Kawu a Kenya sai abin ya Basu dariya,Amma Khairat ba karamar Yar iska bace,ga iyayensu Kamanninsu sun canja sabo da wahala,Abin dariya ma Bai kamasu ba sai da suka ga Kawu dauke da jarkar manja, ga Talatu da doya muku muku harda su kwakwar manja Yar Lagos,Sannan su 3qtr din da sauran tsarabar duk Babu na kirki.
Yanda suka basu labarin wahalar da suka Sha sun tausaya musu matuka,Sannan abinda ya burgesu yanda su Kawu Suma suka gane gaskiya suka tuba har suna neman a Nemo Khairat su Bata hakuri sannan ta dawo gida su zauna tare lfy.

Bayan kwanaki da dawowar Su Kawu sosai gida ya canja,rayuwa ta gyaru suna zaune lfy yayin da Soja ya dage da Sana'a Yana rike gidan,Mutanen Unguwa ana zaune lfy,duk tunaninsu Talatu sunje Makkah basusan Talatu boye Zancen tayi sabo da Makiya aka barsu kawai a sunje sun dawo,Yanzu ta karfi Kawu ya koma Alhaji Sabiu,Hajiya Talatu itama ake ta ce Mata,Basu San iyakarsu Niger,Kenya da Lagos ba.
Talatu ta dage da Tsafta tsaf,komai ya canja Khairat kawai suke neman Hanyar ganinta.

Talatu ta Kira Kawarta wacce ta Bata Khairat ta kaita Karuwanci Abuja, Talatu tace Khairat Dan Allah Ina kika kaita?ki dawo min da ita,Ni yanzu na tuba nabi Allah bazan sake zalinci ba,Kawar Talatu ta tamke fuska tace yo wa yasan inda take,wannan in Banda bala'i da ta jawo min ta jawowa Hajiya Baturiya me tayi Yar iskar yarinya marar mutunci,Talatu ta kalli Kawarta tare da cewa karki sake zaginta ai tayi min dai dai Khairat,To Bari kiji Talatu yarinyar Nan duk Saida ta jawo muka ci dukan tsiya da kwanaki a sail,Wani Senator da Baturiya ta hada Khairat dashi yarinyar Nan ta Masa aski ta tsaga Masa kirki shine yasa aka Kama Baturiya sannan aka kori Karuwan data ke Tarawa a gidanta kaf,ita Kuma Zancen da nake Miki an yankewa Baturiya hukuncin Shekara ashirin a gidan yari,muma da muke Kai Mata Yara anci tarar mu sannan munci duka daya Bayan daya Hajiya Baturiya tasa aka Nemo mu,Munsha wahala mu mun tuba,gidan Hajiya Baturiya ma Gomnati ta kwace ta rushe shi Baki daya yanzu Senetor din da kansa ya fara Gina katafaren masallaci a wurin.

Wannan Yar taku ko sati hudu batayi ba a gidan Baturiya ta gudu,yarinyar tana da hankali ga addini sannan wayayya ce,Ta sanadiyyar Khairat gashi yaran Baturiya da dama sun shiryu sun koma gaban iyayensu,Duk aikin Senetor ne Wanda Khairat ta Masa aski, Mudassiru yanzu aikin Allah yakeyi,Ban San inda Khairat ta Shiga ba,Talatu tace to Allah dawo Mana da ita,Ameen sannan suka yi sallama Kawar tata ta tafi gida.
Zainab tace ban San me yasa ba a samun Khairat a waya ba ko kadan da Kuma Kinga muna waya da ita,Kawu Yana daga dakinsa ya Furta Allah ya bayyana Mana Khairat mu ganta ko Dan mu roketa gafara ta yafe Mana.

Misalin 12am jirgin su Khairat yayi landing a Kano,suna Fitowa da jakarsu a hannu Farouq already Yana jiransu a airport,gaisar dashi sukayi Yana tsokanar Khairat da Amaryar next wk suna dariya suka Shiga Motarsa Khairat na baya Sadiya na gaba,Kwatance tayi Masa na gidan Kawu ya kaisu har Kofar gidan,Zainab ta dawo daga Shago ta siyo Sabulun wanki zatayi kawai taga dalleliyar mota Yar gaske a kofar gidansu,Wata hadaddiyar kafa ta gani sanye da takalmi me tsada High hill kamar kafar Yar Shugaban kasa,gata Fara tas,Khairat ce ta fito Baki daya daga motar,da kyar Zainab ta gane Khairat ce sabo da yanda Khairat ta waye,ta goge,tayi kyau da kiba,ga sutura me tsada,da gani a hutu take,Sadiya ma ta fito zukekiya da ita,Zainab a Nan ta Raina kanta har kunyar kanta taji ma,Amma hakan Bai Hana ta Karasa wajen Khairat da gudu gudu ba,ta rungume Khairat tana murna,Khairat ma tayi missing nasu murna take,Amma tayi mamakin canjawar halayen Zainab,sannan duk taga ta lalace ba irin da ba,Farouq ta gaisar ya amsa da fara'a sannan sukayi Sallama da Khairat yace sai Sunyi waya idan tana bukatar wani Abu.
Bayan yaja mota ya tafi Zainab tace Khairat wannan Kyakyawan saurayin fa? Ga kudi Ina kika sameshi ko shine saurayin da Zaki aura? Khairat tayi Murmushi tace bashi bane Wanda Zan Aura gobe zaizo da kansa shima ya gaida Kawu,Zainab ta daukar musu jakarsu tace ku zo mu shiga ciki.

Talatu sai Khairat ta gani katsam itama ta rude da yanda taga Khairat ta canja hutu ya Kama jikinta,Haka dukkan Yan gidan ma,Soja kuwa tuni a ransa yaji Khairat tafi karfinsa ta wuce ajinsa,matar manya ce,Talatu tace Khairat Ina kika buya Ana ta nemanki ko a waya bama samunki,Jin Khairat tazo Kawu ya fito har Yana tuntube,A katuwar Tabarma suka zauna Baki daya,Bayan gaisuwa aka fara Hira Talatu tace Khairat kinci gidanku,kin bamu wahala,nanfa Talatu ta bawa Khairat labarin tun barin Khairat gida har zuwa Niger, Kenya,da Lagos, da irin wahalhalu da shiryuwa da suka yi,itama Khairat ta Basu labari tun daga barinta gidansu,gidan data kama haya,tsintar su Meenal, zuwa Abuja,Har Hunaif labarinsa da aurensu da zasuyi ta Basu labari kaf,sai Murna suke Taya Khairat,Kawu yace ki yafe Mana Khairat mun San bamu kyauta ba mun zalunce ki,Khairat tace wlh ban rikeku a Raina ba na yafe muku ko Mene ma har gadona duk na yafe muku Nima ku yafe min ban San zaku Sha wahala Haka ba,Talatu tace kaddara ce ba laifinki bane mun yafe,Nan fa aka yafi juna sannan aka ci gaba da hirar duniya,Kawu yace ai zamu je muma Taraba mu fara zumunci sannan mun hutar da Angwaye muma sai muje Abuja ayi bikin damu tunda ya bada masauki ai yayi ko,Khairat tace a'a Kawu ku zauna Yan Taraba sai suzo Kano a daura auren a gidan ubana kawai ayi biki da komai ai yafi mutunci,dama rashinku yasa za ayi a Abuja Amma yanzu ai bazan koma ba zama zanyi,Talatu tace a'a tunda Ladi na gyaraki ki koma can idan anyi Dinner an Gama Ana gobe Daurin aure sai kuzo a daura a dauki Amarya a Nan a kaiki ko?
Sadiya tace hakane Kam Umma.amma dasu Zainab zamu tafi Abuja ayi Dinner dasu sai mu dawo Kano tare ko? Cewar Khairat,Zainab tace ko fa anko bamuyi ba,ai ga naku na siya muku kyauta,Nan Khairat ta bawa Talatu dinkunanta na biki kala uku lace,Atamfa,Shadda,a dinke dai dai Talatu,Zainab ma kala uku da takalmi da jaka kala biyu da mayafai,Haka Rahina ma same things,yaran ma kala Uku uku,Kawu ma shadda kala biyu da yard rantsatsu,Haka Soja ma,nanfa gida ya kacame da murna,Talatu tace Yar nan Ina kika samu kudi Haka? Khairat tace Hunaif Wanda ya taba zuwa gidan Nan kuka ce kun sanshi a tv da radio ai shine Mijin,Ihu suka dauka da tafi Suna Taya Khairat murna,Zainab tace Allah bamu I taku suka ce Ameen.
Dubu Darin da Hunaif ya bawa Khairat ita ta dauka kacokam ta mikawa Kawu tace gashi na hidimar biki da zirga zirga Kar ace dangina sun Gaza.
Talatu Nan aka fara lassafin yanda za a gudanar da biki lafiya.

Khairat a ranar Yan kawayenta ta na unguwa da abokan arziki suka raba katin biki,Har na maza an bawa Kawu da Soja Suma suna gayyatar nasu,Haka Talatu ma an gayyaci danginta da kawayenta,sai su Zainab Masu tarin kawaye Yan gayu sun gayyatosu.
Khairat ba Zama zirga zirga sukeyi tunda suka zo Kano tare dasu Zainab da Rahinatu,Zainab da Rahinatu har Talatu ta Basu kudin siyen kayan kwalliya na Mata iri iri sabo da suyi kyau kafin bikin yazo Kar abarsu a baya.
Saida Khairat suka Gama komai suka kwana daya sannan Hunaif yace ya fasa zuwa Yana da meeting idan sunzo daurin aure a hadu,Khairat waya a nuna musu lefenta dake gidan Ladi suna ta kallo sun haukace,Talatu tace a barshi acan a Kai Miki gidan miji Ana gobe za a Kai Amarya.
Jin dadinsu ga Hunaif ya dauki nauyin komai cokali baza a kaiwa Khairat ba sai iya kayan sawa.

Khairat kwanansu biyu suka Shiga jirgi suka koma Abuja aka ci gaba da shirye shiryen biki,Me magani fans sun Gama Shirin zuwa biki, AsmaBaffa fans club ma sun Gama shiryawa tsaf,House of Hausa Novels duk gasu Nan Ana ta shirye shiryen zuwa a bawa Ido Abinci.

Mus'af yana ta zirga zirga daga Hotel zuwa Hotel ya daina saurar Hunaif sabo da bakin ciki,gashi Bai San ma Hunaif zaiyi aure ba,Yana can Yana kulle kullen ya za ayi Khairat ta Zama Matarsa,Sannan Yana so yaga Bayan Ummi da Hunaif,Yana Hawa Online ya fara chart kenan Yaga sanarwa ta ko Ina da Iv na auren Hunaif da Khairat,Mikewa yayi zumbur,Ya Fara sallallami da Gurnani,zuciyarsa kamar zata fasa Kirjinsa ta fito,Nan take kamanninsa ya canja,komai nasa ya canja kala,ransa ya dugunzuma,Ummansa ya Kira a waya Dan ya tabbatar da gaskiyan abin,yace Umma an Aiko a kawo muku katin biki ko? Dama bazan samu zuwa Kano ba sai Ummi tace zata tura a kawo muku,Ae an kawo tun wancan satin ai Abu yayi kyau Haka ake so Hunaif zaiyi aure saura kaima ka dage ka Nemo Mana taka,Duf Mus'af ya kashe wayar baima Bari ya Karasa ji ba,a fili ya Furta na rantse da Allah da Hunaif ya auri Khairat gwara na Mutu,Dole ayi wacce za ayi Akan Hunaif ya auri Khairat Ni ban sameta ba gwara mutuwata,koma me zai faru ya faru wlh bazan kyaleshi Ina ji Ina gani ba, Nan Fa ya haukace Mus'af ya fito ya figi motarsa ya nufi gidan su Khairat Can Suleja Dama Already ya Dade da samo Address din.

Khairat ta fito kenan zata Shiga gidan su Sadiya kawai sai taga Mota ta Sha gabanta tare da cin wawan birki,idon Mus'af jajir sabo da bacin Rai Yana huci ya fito ya tsaya a gabanta, Khairat ta kalleshi sama da kasa tace lfy dai ko? Da yatsa ya nunata wlh kinji na rantse Baki Isa kin auri Hunaif ba,Dani Kika Dace,duk abinda zanyi na raba Baku sai nayi ko zan tafi tsirara,gwara ma ki hakura da aurensa Ni ki aureni tun wuri,tun kafin na muku illa Baki daya,Shekeke Khairat ta kalleshi tayi Murmushin takaici tace kalleni tsaf nayi Kama da matarka? Dai dai lokacin kuma Hunaif yazo wurin Khairat zai kawo Mata kayan Dinner da zata sa,ya hango Mus'af a wurinta suna Hira,ran Hunaif ya baci,kishi ya taso Masa Duk da cewar ba Wai wani soyayya suke da Khairat ba,aurenta zaiyi Dan farin cikin Umminsa Amma ya tsani Yana kula mace wani ya kulata.
Ransa ya baci tunaninsa Khairat hirar kirki suke da Mus'af.

Lokacin Kuma Khairat tace ja tsumman rayuwarka Dattijo nafi karfinka wlh duk tuggunka sai dai ka rainawa wasu hankali ba Khairat ba,Kuma aure inshaallah anyi an Gama mutu ka raba Ni da Hunaif,da munyi Shawara da Kai? a Haka ka gammu tare ,inba shishigi da Hassada ba mene hadina da kai,wlh idan baka kiyayeni ba sai nasa an canja maka kamanni,Kai rayuwarka Hassada kawai ka iya?shi yasa baza ka taba ci gaba ba a duniya,Allah ya shiryeka,ka tuba ga Allah.
Tana Gama fadin Haka tayi gaba ta danyi nisa ta juyo ta kalli Mus'af dake huci shi kadai tace Ni Khairat kwalelenka,babu rabonka a lafiyayyen jikina du na Hunaif ne.

Hunaif ne ya karaso ransa a bace,Khairat tana ganinsa ta juyo da fara'a ai kuwa sai ya juya a fusace ya bude mota ya dakko kayan auren ya Mika Mata ransa babu annuri ya juya baice kala ba ya shige mota yaja a fusace ya bar wajen, Mus'af ma ya juya kamar zai tashi sama ya shige mota ya tafi shima.

Khairat tsoro ya kamata yanda taga Hunaif Yana zarginta,cike da zullumi ta dauki ledar kayan ta shige gida kamar kwai ya fashe Mata a ciki,a ranta tana ta tunani to me tayiwa Hunaif Kuma?sai kawai ta fashe da kuka tana Mus'af ka cuceni tsinanne zai jawo ya fasa aurena.
Kuka takeyi ba ji ba gani,Ladi tayi tayi ta fada Mata Amma Khairat taki fada,sai Kawai Ladi ta dauki waya ta Kira Hunaif Bugu daya ganin Ladi ce dama Yana da number ta ya daga suka gaisa a mutunce,Ladi tace tofa Ango Amarya kuka take min me ya sameta ne ko ka sani? Hunaif yace Ki kyaleta kawai Aunty ita tasan me tayi,Akan me zata tsaya da wani tasan an kusa Mana aure,ba damuwa ki kyaleta ai an kusa bikin idan anyi ai ba Wanda zata gani bare ta kulashi,Talatu tace hakane Kam,Amma Khairat ba halinta bane akwai Dalilin tsayawarta da koma waye,na sani Aunty shi yasa ma bance Mata komai ba,Ka Dan Lallasheta Dan Allah ko ta samu tayi bacci,to kawai Hunaif yace,Amma Bayan sun Gama wayar Bai ko nemi Khairat ba.

Haka abin nasu ya kasance, Mus'af baya kula Hunaif,Hunaif ma haushinsa yake ji ya ganshi da Khairat dinsa suna zance ba Wanda ke kula wani ko a hanya suka hadu,Sannan Khairat ta rasa sukuni Bata ko saka Hunaif a idonta,Haka ya daina zuwa ba text ba waya,Amma duk abin shirye shiryen na auren Yana Aiko da Usman ya kawo Mata,ta Nan take Jin Dan sanyi tasan auren Yana Nan za ayishi .

Yau biki saura Kwana daya a Fara,duk abinda ya Dace ayi anyi shi,Yan uwan Khairat suna gidan Kawu a Kano acan za a dauro aure,Nan Kuma su Khairat da Bangaren Hunaif suna Abuja za ayi Dinner gagaruma ta gani ta fada,an kama wuri tsaddaje Wanda sai me kudin gaske ke Kama irin wajen,dangin Uban Hunaif sun sauka Larabawa,Haka dangin Umma kaf,frnds na Hunaif kasa kasa duk sun sauka Kuma masauki a lafiyayyun Hotel aka musu,Ana ta baragaza da Naira,yayin da Zainab da Rahinatu sun sauka a gidan Ladi sai anyi Dinner zasu tafi Kano daura aure har Khairat.
Abin ba acewa komai, Mus'af ya haukace sai Kora giya yakeyi a hotel kamar zai kashe kansa,Can kauyen Ummansa ya nemi wasu daya sani Kan a hadashi da malami zazzafa Wanda Sha yanzu magani yanzu yake son aikin,Amma Bai San ya rigada ya makara ba,Dole abinda Allah ya tsara sai ya faru boka ko Malam Bai Isa ya canja abinda Allah ya tsara ba.
Meenal da Mohd sun Kara girma da wayo yanzu sun manta ma da wata Khairat sai kanwar Ummi suka sani,sabo da basu Dade tare da Khairat ba.

Farouq shi yake komai ya shigewa Hunaif gaba ganin Hunaif Yana da lalura Bai wani Karasa warkewa ba,cutar mantuwarsa tana Nan Akan Khairat ne kadai baya manta Abu har gobe.
Gidansu ma an canja Masa fasali ya Kara bada wani haduwar daban, Komai yaji Ras,Sabo da a Nan za a kawo Amarya sai Hunaif ya dauke Ummi ya canja Mata gida Wanda zata zauna anan ta sauki baki da Yan Uwa har a Gama biki sabo da Kar Yan biki su Bata gidan tun ba a kawo Amarya ba.
Washe gari Saturday ranar Dinner Khairat tun jiya Tasha lalle na gani na fada gashi
Tasha gyara,yau Kuma gidan kwalliya zasu tafi daga can za a dauki Amarya a wuce wurin Biki,Hunaif ya rado hadadden aski na Yan birni wani style din daban,dansajensa da gemunsa yasha gyara sunci kudi,kowa ya kalli Hunaif bazai so ya dauke Ido ba,shi kanshi ba shi zai shirya kansa ba,wurin shirya maza yaje daban yaje zai dau wankan gaske.
Khairat Abu daya ke damunta Wanda Hunaif baya kulata,sannan ya daina Mata ko Murmushi,dama tasan ba wani sonta yake ba kawai zai aureta be Dan Farin cikin Umminsa ba Wai Dan Yana sonta ba.
Duk ta Zama silent da ita kadan take jira ta fashe da kuka duk ta tararrabe,ga zullumin auren duk tsoron auren takeji gashi ya Zama Dole.😝😝😝😝😝😝









Fans kuyi Hakuri kwana biyu ban baku page ba,Ina busy ne.




Wannan ma banyi Editing ba kuyi hakuri.












AsmaBaffa
[10/18, 2:54 PM] Sis Asma: 🦚🦚ME MAGANI🦚🦚









56-60









Official









By
AsmaBaffa







Suwaibag3,wasila,samee,Ummu Sa'ad.
Ga page naku tnx.








Khairat kawaye sun Kai su Goma sun cika dakinta Ana Shirin Zuwa Dinner,Ladi ta dauko kwararriyar me kwalliya tazo gidan da Yaranta tana ta shirya Mata,Khairat sai yaki akeyi da ita Kan taje tayi wanka Amma a banza Taki sai tunani takeyi,Sai da Zainab ta shugo tare da Rahinatu suka Sa Khairat a gaba tayi wanka tare da shafa tsadajjen body lotion wata arniyar Arabian Gown tasa itace wacce Hunaif ya kawo da zata sa,Fara ce kwal,saman ta Dame,kasa ta bude sannan anyita Daga baya ta Zobe tana Jan kasa Kaya guda,hannun rigar dogo ne Amma net ne shara shara,tun kafin ayi komai Khairat ta bada haske,me kwalliya ta zauna tana tsantsarawa Khairat kwalliya ta gani ta fada.

Sauran Yaran matar suna ta shirya frnds,Khairat ita kanta sai taga kamar ba ita ba,tayi azababben kyan da Bata taba yi ba,kowa ya hangame Baki Kawai Ana kallon Amarya, black head da shi aka nadawa Khairat gogoro a kanta gashinta natural me tsayin gaske kamar na Larabawa Wanda yasha gyara

Please Login or Register in order to submit comment