Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har Dining ta shirya Masa Already,Zama yayi yaci ya koshi sannan yayi wanka ya kwanta bacci ya kwashe shi sai kusan Magrib ya tashi baya baccin yamma sai Dole,ji yayi ba abinda yake bukata sai Khairat dinsa.
Khairat Kuma tana can gidan Ummi tana fushi ita Babu Wanda yake kaunarta a duniya,Talatu ma ko kiranta basa Yi a waya ba komai wlh itama ta daina kulasu.

Tana zaune Sadiya ta kirata a waya daga Cewa Khairat ta Hunaif kin Gama Mallake bawan Allah bazai iya Miki kishiya ba,shike Nan Khairat taji Haushi Wai Sadiya ta fada Mata bakar magana tana so mijinta ya Mata kishiya,a Palo ta samu Ummi tace Ummi kinji Sadiya Ashe badan Allah take so na ba,ba kawar kirki bace,har fata take min ayi min kishiya ba komai na daina kulata.

Ummi tasan cikin Khairat ne haka yake ta sata fada kowa haushinsa takeji,Sadiya yau ta jawowa kanta sai ta Kira Hunaif a waya Yana dagawa tace Mijin Khairat zaka iya yi min kishiya? Hunaif yace a'a na Isa ai ban Isa ba yanda nake sonki Ina Zan iya hadaki da wata,To Kaji Sadiya Banza Yar iska Wai fata take min ta Allah ba Tata ba.
A Nan Hunaif ya samu dama ya lallaba Khairat har ya samu tace yazo ya dauketa a gida zata kwana.

Haka yaje ya dakkota a mota,Ummi ta fito Palo sai gani tayi Babu Khairat Wai Hunaif yazo ya tafi da ita,me aiki ta fada Mata.
Haka cikin Khairat ya kasance kullum sai tace anyi Mata Abu,Hunaif yayi kokari da hakurin jurewa,Watarana har kokawa takeyi dashi harda cizo yasha wurin Khairat.
Har cikinta ya Shiga wata 9 cif Khairat yanzu Bata fiye neman fada ba sai dai kuka ba gaira ba dalili sai ta fashe da kuka sai tayi ta gaji,ko tace ita Dole sai an cire Mata ciki ko ta kashe kanta.
Hunaif sai ya Kira Ummi sannan ake samu ta hakura.

Yau ma tunda ta tashi take kukanta,Babu lallashin da Hunaif baiyi ba Taki yin shuru,ta kalleshi tace Mugu azzalumi kaki kaini a cire min cikin Nan na huta,Hunaif tausayi take bashi da Yana da iko wlh da cire Mata za ayi ta huta gashi yayi Kato ya hanata sakewa,Lallashinta yayi ta hakura da kyar tace zata haihu da kanta.

Shi Kam sai faman Kashe kudi yakeyi Akan cikin,ya Mata dinkuna na Alfarma Banda Wanda ba a dinka bama,readymade iri iri,kusan kayanta da nasa kaf ya canja musu sababbi, Haka jariri ma yasha siyayya tunda ance Mace ce a cikinta da aka auna.

Ummi da kanta tazo da dare ta tafi da Khairat wajenta,Hunaif Yana ta bakin ciki an raba shi da Matarsa,Ummi tace wlh bazan bar Yar mutane Babu me kula da ita ba ciki ya tsufa Haka baza a barta ita kadai ba.
Sosai Ummi ke bawa Khairat kulawa a gidanta,Hunaif shima a gidan ya tare kullum Yana can makale da Khairat ko Office ba kullum yake zuwa ba sabo da Wai ta haihu a gabansa.

Yau Monday yace zai leka Office Yana barin gidan Ummi,Khairat ta yunkura zata tashi kenan kafa ta rike,tayi tayi ta kasa,sai Ciwon baya Kuma,daga Nan sai Mara gadan gadan,Ummi tana kitchen sai Karar Khairat ta jiyo tana Wayyo Ummi,Ummi...marata Zan mutu,ai ko Ummi ta daka wani tsalle Tayo sufa waje ba ko gyale ta Kira Driver suka tafi da Khairat Asibiti,Khairat ta Hana driver tuki cikin jin Dadi Sai kwarototo takeyi,wayyo marata,gashi Nan Ummi Ciwon ta Nan wajen ya taho...ya tsaya a nan wajen,ta bayana wayyo Allah.

Ummi tace sannu addua akeyi ai,Khairat ta fashe da sabon kuka tace ni ban iya wata Addua ba,na manta...yiiii....Ni a Nemo min Mijina kowa baya kauna ta Ana gani Zan mutu,Dan Ubanka Driver kayi sauri Dan baka San daraja ta ba shi yasa kake tuki a hankali.

Ummi tace Nasan Yanzu idan Na fadawa Hunaif zai tashi hankalinsa Khairat a kyaleshi,yanzu zai iya hatsari ma a hanya sabo da Yanayinsa,Ni na mutu ko kenan? Sabo da Ni bake Kika haifeni ba kinfi son danki,Ni anfi so na Mutu shi lallabashi akeyi sabo da Ni daga sama na fado, Bayan shine ya jefa Ni a halin da nake ciki shi Yana can Yana Jin dadinsa Ni Zan mutu.

Tun Khairat na magana har tayi laushi ta kasa magana har suka Isa asibiti aka Basu daki,Ciwo idan ya taso gadan gadan Sai dai kawai Khairat tace Ni marainiyace Ya Allah....Marainiyace Ni...idan ma ta Fara Addua mantawa takeyi Bata iya karasawa,Ummi tace ko Fatiha ki karanta Mana Alhmdllhi rabbil alamin Arrahmanirrahim shike Nan abinda take fada ta dawo baya ko ta dauko karshe ta kawoshi Farko waladdualllin Arrahmanirrahim..Maliki...maliki...shike Nan sai ta koma suratul Iklas Kuma ta Karasa Fatiha da ita,Allahussamad Arrahmanirrahim....

Shegun likitoci Yan iska Haka Khairat take zagin Likitoci tana tsine musu Albarka,Tun safe Har 12pm Khairat na ciwon Nakuda sai 12:30 Allah ya taimaketa ta Haifo yarta mace katuwar gaske me kama da Hunaif sak kamar an tsaga Kara,Sai lokacin kuma Khairat ta dinga sheka Amai sosai ta Gama,Aka gyara ta fes dake private Hospital ne daki mutum daya,kamar Hotel Haka asibitin yake,Ummi tasa aka gogewa yarinyar jikinta da man Zaitun,sannan Khairat Bayan ta huta Ko ta Yar Tata Bata yi,sai da tayi wanka da kanta ta gasa jikinta har kuka tayi sabo da zafi tana gashin,Allah yasa sai da Nurses suka Sa machine suka kwashe Mata jinin dake mararta,yanzu kadan ne ke fita ba da yawa ba,Khairat ta Dade tana gashin Nan kamar zata kone gabanta,sannan ta dinga wanka ba ji ba gani da sabulu me kamshi dama Ummi ta tanadi komai na kayan da zasu bukata a Hospital.
Bayan ta Gama Wankan ta shirya kanta tsaf ta fito Ummi tace karfa zafin gashin yayiwa jikinki yawa,ki kula,Kai kawai Khairat ta daga Mata duk jikinta ba karfi kamar iska zata dauketa Haka take ji.

Yarinyar Ummi ta wanke Cikin Bahonsu na jariri da Ummi ta dakko sabo,Bayan an wanke yarinya Ummi ta shiryata cikin kayan sanyi designers masu kyau cikin Wanda Hunaif ya siyo farare tas,Khairat Doguwar arabiyan riga tasa ta,Ummi ce ta gyara Mata gashinta me tsayi ta Mata parking nasa tare da shafa Mata Vaseline cream a hannu da kafafu,ta fesa Mata turaruka masu dadin kamshi.
Khairat sai tsamtsamin kanta takeyi.

Ganin Haka Ummi tasa Aka canja musu daki na hutu,Khairat taci abincin da Yar aiki ta kawo ta koshi sannan Tasha Magunguna,suka Sa Mata drip da Allurai na karfin jiki.
Sai kallon Yar Tata takeyi tana Jin kunyar Ummi tana so tace a Bata Yar ta ganta tana Jin kunya Haka har bacci ya kwasheta,lokacin Ummi ta Kira Hunaif yazo da sauri ya shigo ya Iske Khairat dinsa lfy tana bacci,ajiyar zuciya ya saki Yana godewa Allah ya dauki Yar sa,ya Shiga kwarara Mata adduoi na sunna.







AsmaBaffa
[10/18, 3:01 PM] Sis Asma: 🦚🦚ME MAGANI🦚🦚








91-95








Official






By
AsmaBaffa







ASMABAFFA FANS, ASMABAFFA FANS CLUB,HOUSE OF HAUSA NOVELS,ME MAGANI FANS,TASKAR SURAYYARMS ETC.
PAGE DINKU NE,NA GODE DA SHARHI.


SAURAN GPS INA MATUKAR GODIYA DA SHARHI ALLAH YABAR KAUNA.

INA KAUNARKU MASOYA A DUK INDA KUKE KUMA INA JINJINA MUKU.




Daraf Hunaif ya zauna kusa da Khairat ya fara buge bugen waya Khairat ta haihu,Ummi ma Haka sai waya suke,Ladi ce ta farko data danno asibitin da wuri da shiryayyen farfesunta, tana murna Hunaif ya makale yarsa ya Hana kowa Wai shi Dole sai ta shaku dashi tun yanzu,Ladi ta kwace ta tana masifa ya hanata jaririya,Talatu kuwa tun daga Kano a waya tace da Ummi Ashe zamu Sha Illi gogoro zuwa Abuja,su Zainab su Sadiya sai Murna za a zo suna.
Khairat tana bacci Bata San me akeyi ba sai yamma lis ta tashi a bacci,Hunaif ta Fara gani ya rike Hannunta tare da kafeta da Ido.

Farin ciki ya Kama Khairat ta kalleshi kawai ta mike zaune,yace Sannu da jiki kinsha wahala ko? Khairat kunyar su Ummi take ji Shi Hunaif ba ruwansa ko a jikinsa,Ladi tace tunda ta tashi muje muyi Sallar laasar kafin a sallamemu,suka fice tare da Ummi,daga Khairat sai Hunaif,sai lokacin ta karbi jaririyar dake hannunsa tace Banfa dauketa ba Ina Jin kunyar Ummi sai yanzu,Hunaif yayi Murmushi yace da wahala ko Haihuwar?,Khairat ta rike Baki tace kaiiiiiiii bala'i ne kawai kaji kuwa? Ai ba a magana,Wai ba a kuka daurewa akeyi Ni wlh kasa dauriya nayi na dinga kwara ihu,Ummi tana Addua Ina ai tuni haddata ta goge ta Qurani Babu ko daya a lokacin,Wai Ummi baza a fada maka ba,sai ma fa na bawa Ummi Hakuri har rashin kunya nayi Mata nace tafi sonka Dani,Dariya Hunaif yayi Haba ai tasan zafin ciwo ne yasa Kika Fadi haka,muje Na Miki wankan cewar Hunaif.

Khairat ta bude Baki tace tab Kai kazanta zaka gani ban taba ji ba baza kayi min ba,Ni ba wanka ma zanyi ba,nayi dazu sai Munje gida Ladi zata Yi min,Amma dai ba wannan wankan na duka da ganye ba ko? Kai Khairat ta daga tace da towel zata min ai.
Ok to jeki ki fito,Bayan ta fito a toilet ta samu har an Basu sallama Bayan anyiwa yarinyar Allurar rigakafi ta Hypititis B suka tafi gidan Ummi Baki daya a Nan aka bawa Khairat daki guda,Ladi ce zata zauna da ita tana kula da ita a gidan Ummi kafin Talatu tazo suna ta karbi aikin.

Ranar Ummi sai ganin Hunaif tayi ya Haura Samansa shima ya zabi daki guda ya ajiye akwatin kayansa guda,Ummi ta bishi dakin tace me Zan gani Haka? To kazo ma ka koma gida baza ka tare Mana ba,Wlh Ummi ba abinda zan Mata kawai nafi so Ina kallon matata da 'yata zanfi samun kwanciyar hankali,Ummi kallonsa kawai takeyi tasan ba tafiya zaiyi ba,Ladi tace kyaleshi ai Talatu zata zo tayi maganinsa.
Khairat dai tana jinsu Bata ce komai ba,Kwana biyu a tsakani Yan uwa da abokan arziki Ana ta sintirin ganin jaririya,Yau kwanan Khairat Uku da Haihuwa ta samu karfi da lfy sosai sai uwar kwalliya take Sha kamar sabuwar Amarya,kullum sai tayi wanka sau uku ko hudu Kuma duk wanka kalar shigarsa daban cikin sababbin kayan da Hunaif ya sake musu,Ga Ladi da Ummi suna gyara ta suna kula da ita sai wani kyau takeyi da sheki gwanin birgewa,ita da jaririya suna cikin koshin lfy ga Hunaif Yana ji dasu yanzu ba fada tsakaninsa da Khairat sabo da dama Laulayin cikin ne ya jawo Khairat ke masifa kullum.

Hunaif kamar shi ya haihu Wai ya dauki hutu baya zuwa aiki Sai Bayan suna da sati daya zai koma,yau da dare Bayan Sallar Isha ya Shiga dakin Khairat ya isketa taci wanka iya wanka cikin wata fitted Gown Orange color sai sheki da kamshi takeyi,sun fito Mata da sura sosai,duk Wanda ya kalli surar Khairat sai ya Kara sabo da kyan data yi,hips ya fito sosai dama gata da abin, Hunaif ya hadiya yawu ta baya ya rungumeta tana linke kayan jaririya da aka wanke su,kasan dai Nan ba gidanmu bane,Ummi zata iya shugowa ta Kama mu,Shagwaba ya fara mata,Ni yanzu kin daina Sona ta Baby kawai kikeyi kin daina kula Dani sai ita,ko nazo sai ki dinga shareni,yaushe rabon naji dumin jikinki? 4days fa Dan Allah yau Zan kwana a Nan,wlh ba abinda Zan Miki kin sani ma.
Ummi zaka fadawa Da Ladi Kar suce Ni na nemoka,Lokacin Ummi zata Shiga dakin taji Maganar sama sama,Sai taga kamar an tauyewa Hunaif hakki,tunda Dole bazai wa Khairat komai ba tana jini Bai dauke ba,sannan an rabata da gidansa ya hakura to ya kamata a barshi yaji dumin Matarsa da Yarsa.
Shawara sukayi da Ladi yau Ladi baza ta kwana a dakin Khairat ba.

Abinci Ummi ta kawowa Khairat ta kwankwasa Hunaif ya bude Mata ta ajiye abincin tace Khairat ki kulle dakinki yau Ladi a dakina zata kwana sabo da zamuyi shirye shiryen suna,to Ummi ta Furta,Hunaif ya fara murna tare da gyara Zama,flask din abincin ya bude ya samu lafiyayyen tuwon shinkafa miyar kubewa danya Tasha manshanu da Kifi,sai wani tsumi na gyara Mata a Glass juck,gefe Kuma ga fruits salad a wani glass bowl.
Nayi Sha'awar tuwon Nan,Khairat tace Bari nazo muci ko na fara Bata nono Tasha?

Hunaif ya sakko kasa ya zauna Khairat ta daura pillow a kasa tare da Zama a kansa sabo da Ummi ta hanata Zama a kasa ba kujera ko Pillow ba.
Jaririya tana saman Cinyarta,Hunaif da Khaira sai kallon juna suke suna sakarwa Juna Murmushi cike da so Hunaif ya Furta Bata Nono Mana Zan Baki abincin a Baki,Zif din rigarta ta zuge ta zaro Dan madaidaicin Nononta me kyau Yana sheki fari tas,Kansa ta goge da wani ruwan na magani da aka Bata a asibiti,ba a so abawa jariri Nono ba tare da an goge Kan ba da Breast feeding spirit,Sai da ta cije lips da yarinyar ta Fara tsotsa sabo da zafi da take ji na rashin sabo.

Hunaif yace Sannu da zafi ko? Kai ta daga Masa tace Kaine ka jawo,da nayi me? Da baka Sha sosai ba lokacin Ina da ciki da bazan ji zafi Haka ba,Oh..Haka Kika ce? Dariya sukayi gaba daya yace zakiyi bayani ne,hannunsa ya wanke tare da Fara cin abincin ya bawa Khairat a Baki tana ci har suka Gama,sannan yayi wanka tare da Shirin bacci Khairat ma wankan musamman tayi tabi jikinta da turare masu dadin gaske tasa rigar baccinta normal me kyau me laushi,Jaririya da Rana Bata yi bacci ba,shi yasa da dare tuni tayi bacci da Tasha Nononta,Kaya Khairat ta canja Mata tare da kwantar da ita a saman Dan gadonta dake jikin na Khairat.
Hunaif yaje tare da tofeta da Adduoi sannan ya kwanta,Khairat tana jikin mirror ya Matsu tazo su kwanta zumudin Jin duminta yakeyi.

Wai Dan Allah me kikeyi ne Haka? Ribbom Dina nake nema,No..kyaleshi nafi son gashin a Haka,Khairat ta Fara Shagwaba tana dire diren kafafu tana Ni...Ni...nifa yau naje Saloon an gyara min shi zai hargitse ya lalace Kuma kasan da kyar Ummi ta Bari naje.
Ko kin saka cirewa zanyi gwarama ki hakura mu kwanta.

Zuwa tayi a Shagwabe ta kwanta a gabansa suna facing juna daf ba ko space a junansu,tace ya akayi ne,taga gaba daya Duk ya canja lokaci guda,Yace I'm in need of u,I Need u,I need to Feel u Matata,Khairat tace kasan no way sai idan a cinya za kayi?
Ae a cinyan ma is Ok,Kissing dinsa ta Fara tana Masa wasu salo,tana sarrafashi,tace karka min komai sabo da hankalina zai tashi kasan Kuma ba dama,Haka ta dinga jiyar dashi Dadi tana Sucking Masa Hajiyarsa, yace Bari nayi Mouth xxx sai gashi ma a iya yanda ta Masa abin ta bakinta kamar Yana babbar harka sai ko ya kawo ya samu nutsuwa ta gaske,yaji Dadi matuka,sai sawa Khairat albarka yakeyi.
Kuma yaji sonta kullum Karuwa yake a ransa,tana birgeshi yanda take iya sarrafashi yanda yake bukata.
Sabanin wasu idan suna period ko sun haihu shike Nan an ajiye miji a gefe baza a jiyar dashi dadi ta hanyar Romance ba,wannan ya halalta ki faranta Masa ko a tsakanin su cinyoyinki ne zai samu gamsuwa ba tare da ya shigeki ba.

Tana rungume a jikinsa Bayan ya tsarkake jikinsa bacci ya kwashe su Baki daya,sai tsakiyar dare jaririya yunwa ta farkar da ita ta Shiga kuka,
Hunaif ne ya fara farkawa ya daukota tare da tashin Khairat ta Bata Nono,Khairat tayi Mika tare da kwanciya a Bayan Hunaif tana magagin baccinta,tace pls Honey ka kyaleta na gaji.
Yana zaune saman Bed yace ki daure kinji,Yi hakuri ki bata tasha.
Haka Khairat ta hakura ta Bata Nono sannan Baby tayi Shuru tare da komawa baccinta,Hunaif ya kwantar da ita Suma suka koma baccinsu abinsu Shar Shar.

Wani Hadadden wuri Hunaif ya Kama Wanda a can za ayi suna,Babu wani suna a cikin gida abinka da harkar masu kudi Yan gayu,Zainab da Mus'af,Sadiya da Farouq,Sai su Talatu da Rahinatu sai kuma wasu daga Dangin Khairat Yan Taraba,sai na Ummi da Bangaren Hunaif Duk Ana gobe suna sun hallara Ana ta hada hada,Sadiya,Zainab da Rahinatu suna Dakin Khairat sai Hira suke zubawa.

Khairat ta Kalli Sadiya tana Mata tsiyar cikinta ya fito itama,Haka Zainab ma ciki gare ta,Talatu taci Gogoro kamar Dangin yoruba ta shigo dakin tace Iyayen Jaririya ku bani yarinya Zan Mata wanka,Khairat ta Mika Mata jaririya,Sannan tasa Yan aiki su shirya take away da za a raba a wurin,Hunaif ne ya shigo dakin Ya tsallake su Zainab ya Karasa kusa da Khairat tare da Rada Mata magana a kunne Wai zakizo dakina muyi bacci sai Su Sadiya su kwana anan? Khairat ta dafa kafadarsa suna tsaye tace itama cikin rada yau daya kayi hakuri,tun fa rannan sau daya su Ummi suka Bari mukayi bacci tare tunda Kika Haihu,Umma Talatu ta tare komai ba Daga kafa,dariya sukayi gaba daya Banda su Zainab sabo da Basu San me suke cewa ba,kus kus sukeyi ba aji sai dariyarsu, da kyar Khairat ta lallabashi ya hakura.

Dare yayi sai Hira sukeyi sun kasa bacci tsakanin Sadiya,Zainab da Khairat,Zainab ta zuge Jakarta ta kwaso tarkacen magungunan Mata tace Khairat tashi Dan Ubanki Kema Naga mijinki irin nawa ne wurin naci,Da sauri Khairat ta mike Zaune,Sadiya tace ke Zainab Nima Farouq baya daga kafa,Zainab tace na sani Amma wlh duk mazajenmu Basu Kama kafar na Khairat ba,wannan Hunaif baya gajiya da Alama,Khairat tace yo ai Alhmdllh tunda Nima irinsa ce Haka nake wlh mu abinmu Shar.

Zainab tace to Gashi Aswakin Mata ne kullum ki Dan gutsiri kadan ki cinye,ko ki hadashi da masoro tare da Yayan zogale ki daka su lukwi ki tankade su ki zuba a lafiyayyar zuba kullum ki dinga Shan Rabin spoon,matsi da Karin Niima yake sosai ga gyara gaban mace,kullum zai zauna tsab sosai yake aiki kala kala me amfani dashi zata ga aikinsa. Idan Nan gaba Zaki siya ki nema a Islamic chemist Zaki samu.
Nan Zainab ta fito dasu iri iri ta bawa Khairat,Sadiya kuwa tuni Zainab ta Bata sabo da gari daya suke Aure Kano.

Khairat Nan take ta Fara Amfani da wasu,bacci suka kwanta suna Hira sama sama,Farouq ya Kira Sahibarsa Sadiya tana magana tana kashe murya kasa kasa,ga Shagwaba tanayi,Zainab ma Mus'af ya kirata da uban Daren Nan Wai waya suke sha,.
Sadiya tace da Farouq Dearna I'm missing U,missed ur kisses,Missed ur everything Babyna.
Shima ta wayar yake antayo Mata kalamai,Zainab kuwa dake dama duk Yan duniya ne ita da Mus'af ba wani sakaya magana da sukeyi baro baro suke zubeta.

Khairat sun Hanata bacci Sam,sai tace Nima Bari na Kira nawa,ta dauki waya tare da Kiran Hunaif,Bugu daya ya dauka muryarsa ta bacci alamar bacci, I forget to tell u that I Love and I missed u,Murmushi me Sautin bacci ya sakar Mata,ganin bacci yakeyi ta Masa Sallama suka rabu,da kyar bacci ya kwashesu.

Washe gari kuwa a masallaci aka radawa Yarinya Sunan Ummi Fateema Raguna manyan gaske guda Hudu aka yanka, Khairat tace ana kiran jaririya da Noor,da yamma kuwa wanka suka dauka kamar Amare Haka suka Sha wanka aka wuce wurin da Hunaif ya Kama Mata da maza akayi suna can,anci ansha tare da Shan kida rawa da liki,sai wurin 12am na dare aka Gama shagalin suna tare da rabawa duk Wanda ya halacci Sunan Mata Atamfa Yar dubu biyar,maza Kuma Yardi me azabar kyau da tsada.
Anyi an Gama lfy yayin da bakin nesa washe gari kaf suka koma inda suka Fi wayo yanzu ya rage Daga Talatu wacce zata zauna da Khairat har tayi arbain,sai Ummi,sai Hunaif tare da Yan aiki gasu Nan suke Nan a gidan.
Kawu Sabiu Bai samu Zuwa suna ba sakamakon an kaishi gidan wani babban malamin Izala me fitar da aljannu ta hanyar adduoi can Borno state kamar yanda Hunaif yayi alkawarin za a gwada ko idonsa zai bude.

Bayan komai ya lafa anyi suna da sati biyu Khairat satinta Uku da Haihuwa tayi Masifar kyau da kiba Gashi tana ta gyara jikinta ko Ina kamar Sabuwar Amarya,Kawai kamshi take fitarwa,Yarsu Noor tayi kiba tare da wayo ka rantse balarabiya ce,Hunaif Yana zuwa Office idan ya dawo to Noor tana wajensa.

Zainab ce ta bugowa Talatu waya tana Ihun murna tazo Kawu ya warke idonsa ya bude,Aljanu sun sakeshi Mus'af kuwa a Jirgi yasa Kawu da kansa ya kawoshi Abuja,Kawu Yana ganin komai tas,kowa yayi Murna da farin ciki.

Yana zuwa yaga Khairat yace Lallai yayana ya Haifi ya me kyau,Talatu ta kalli Kawu yace Wohoho Nasan Za a rina,gaskiya Talatu yanzu a Haka aka aura min ke? Talatu tace yo Ina laifi Ni Dana taimakeka,lokacin da kake Makaho wace zata kulaka bare ta aureka idan bani ba,sannan Hakorana da Babu na gaba yarka ta zubar min dasu,Ummi da Hunaif tare da Mus'af dake Dauke da Noor Yana Mata wasa Dariyar su Kawu suke.
Iyayen Mus'af Suma Suma sunzo Suna har Abuja.
Kawu yaga jaririya Sannan Hunaif ya kaishi Gidansa yasha kallon sabuwar duniya,Kawu sai kauyanci yakeyi Yana mamakin Khairat ce a wannan gida Haka dankari.
Satin Kawu Guda tare da Mus'af
, Kawu ya goge duniya Saura kwana hudu Khairat tayi Arba'in Talatu,Kawu,tare da Mus'af surukinsu ya sasu a gaba cikin jirgi suka koma Kano Bayan Hunaif ya sauke Alkawarinsa na sawa Talatu Hakoran Roba,kuma an Sa Mata tayi kyau,kamar na gaske idan ba fada maka akayi ba baza ka gane ba.

Khairat ta Dade da Fara Sallah Amma Hunaif Romance kawai suke danyi jefi jefi sabo da Ummi ta hanashi Sakat da Khairat,Ummi suna zaune da Khairat tace ya kamata muje asibiti a sa Miki abin tsarin iyali a hannu sabo da ya Dace ace kin yaye Khairat kafin Allah ya Baki wani cikin,Yanzu Kwanikar Nan ba sonta akeyi ba,ko Dan sabo da lafiyarki data Noor,idan kin yayeta sai a cire Amma karki Bari kiyi kazamar Kwanikar Nan,Khairat tana Jin kunya tace Jiya da Doctor tazo yima Noor Rigakafi ta saka min,itama ta bani shawarwari shine ta saka min.
Alhmdllh cewar Ummi Amma Doctor Halima ta taimakemu ta hutar damu,sai ki fara shiri saura kwana biyu ki koma dakin mijinki sabo da Hunaif ya takura min kullum da nacin na rike Masa Mata.

Yau Khairat tayi Arba'in harda Karin kwana biyu,gidanta dama kullum Yan aiki suna zuwa su gyarashi Neat Amma wannan lokacin Hunaif Saida ya canja komai na gidan yasa new design,ba karamin kashe kudi yayi ba,hatta kwai na wuta sai da aka sake,komai na Khairat dake gidan Ummi ta maidashi gidanta,suka je da Yan aiki tare da kara kalkale gidan Yana sheki da kamshi.

Shiryawa tayi cikin sabuwar Shadda me tsadar gaske Tasha dinki na garari,Ummi Already ta shirya Noor sannan Suka shiga mota sai gidan Hunaif Ummi ta maida Khairat da kanta ta Kara Mata nasiha sannan ta dawo gidan,Hunaif ya dawo Office baiyi tunanin Khairat ta koma ba sabo da Basu sanar Masa ba,Gidan Ummi ya dawo kawai.









AsmaBaffa
[10/18, 3:02 PM] Sis Asma: 🦚🦚ME MAGANI🦚🦚










Please Login or Register in order to submit comment