Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fika kudi ko kana karkashinsa yace bazai ci Abinci da Kai ba,ko ya nuna maka kyama shi Sam ba Halinsa bane,shi yasa ba dai kaji Ana zaginsa ba sai dai yabonsa ko Ina.

Sai da Khairat tayi Sallar laasar sannan tayiwa Ummi Sallama tare da komawa Gida,tana komawa ta hada kayan maganin matanta na gyaran jiki Tasha tare da yin matsi da wasu,ta zauna tana kitchen ta danyi soye soyenta na abin marmari sabo da Mata da dama musamman Amare Ana kuskure,sai kaga mace Wai ita me iya girki baza tayi abincin da me gida zai iya ci ya koshi ba,sai tayi na turawa Wanda irin wannan ba a yiwa mutanenmu Hausawa suci su koshi ba dashi suka Saba ba,irin wannan da marmari ake yinsu yanda mutum irin kamar yunwar hantsi anci na safe ba a Gama na Rana ba,sai yamma anci na Rana ba a Gama na dare ba,ko Kuma da dare Haka kafin a kwanta a danci a marmarce,Amma sai a samu kawai ayi girkin Rana Wai na turawa sai kiga me gida ya kasa ci Haka Yara ma,a barki dashi ko miji yayi ta tsaki yayo cefane kin sarrafa ta inda Bai Dace ba bazai iya ci ba,ya kamata a gyara.mutum ya Saba cin su shinkafa da Miya dasu salat,jullof,waina,tuwo,etc Abinci dai normal na Hausawa kice ke Dole Haka zaici na turawa,duk girkin gayunki akwai inda ya Dace da lokacin daya kamata kiyi muku su kuci a dadin Rai ga mazajen Hausawa,idan kuma kin San na turawa yake so to sai kiyi Amma ba Kawai ace Dole sai yaci girkin Yan gayu na turawa ba Bayan Bai Saba dasu ba.
a kiyaye durawa miji maiko ba wasu girki ba Healthy food ba,sakamakon idan Yana da wata cuta wacce tana kwance ba a San da ita ba Ke kuma kina ta dura Masa abinda zai tashe ta sai ta tashi ta Masa illa ta Kara karfi a jikinsa ko naki ko yaranki.
A kiyaye abincin da za aci,Kar a durfafi Abu daya.

Kar kiga tarin Kwai available a kitchen sai kice ke Dole kullum sai kin sarrafa kwai ta fanni daban daban Kuna ta cin kwai a Dole masu shi,wlh wannan Yana kawo Illa a jiki matukar za durfafi Abu daya Ana cinsu,ko nama ai ke kullum komai sai da nama ku masu kudi to wlh ba birgewa bace,domin duk abinda zaka nace Masa da yawa sai ya cutar dakai,a kiyaye.

Tana gamawa a gurguje tayi wanka,tare da shiryawa cikin fitted Gown Red and Golden Material cikin kayan lefenta,Tasha kyau ta Gama Yar kwalliyarta tana kamshi,gashinta take sharcewa tana gyarashi saura kadan ya Karasa bushewa tasa Handdrier tana karasa busar dashi har ya bushe ta gyarashi sosai tare da shafeshi da mayuka masu kamshin gaske,ta gyara komai ta shirya sosai sannan ta gyara Fuskarta da powder tayi kyau, Wayarta ce tayi Kara tana Dagawa taji Muryar Ladi tana fada Mata jirginsu ya sauka dazu sun dawo daga kasa me tsarki.
Khairat tana murna tace saura su Umma Talatu kenan Suma suna tafe soon.

Karar motar Hunaif taji Tasha daurin ta me kyau kamar Amarya,shigowarsa taji dakinta Yana kiranta,I'm Home ya Furta tare da rungumeta gaba daya a jikinsa Yana I missed u, juyowa tayi tare da sakalo hannayenta ta wuyansa ta Fara kissing nasa,ya samu abinda yake so dama da bukatarta ya dawo,Zobo Drink data hada me sanyi ta cika Masa Glass cup yasha Ginger ta bashi a Baki ya shanye kuwa Yaji dadinsa sosai.daga Haka ya dauketa suka saman bed.

Romancing sukeyi sosai saman bed dinta suka fada ya fara rabata da kayan jikinta, Bata hanashi ba itama domin so takeyi, hadin Kai ta bashi yau wani sabon Salon style sukayi na daban Wanda yafi karfin furta shi,Ihun Sweet kawai suke yi,shi Kullum ji yake Khairat tana Kara Dadi na musamman,Kuma yaji ta Gam Gam a matse sabo da Bata Wasa da gyara kanta.
Tare sukayi wanka da komai yasa Jallabiya Fara ya fito a balarabensa itama ta canja cikin gown Yar karama me kyau iya gwiwa kamar Yar baturiya,girkin turawan data shirya musu,ta shirya musu baya son zuwa Dining yau, a Palo kasan center carpet suka baje tana makale a jikinsa kamar jela Haka suka ciyar da junansu cike da so da kaunar juna.

Bayan kwana Uku Hunaif ya Kai Khairat gidan Ladi suka Mata sannu da zuwa harda Basu tsaraba me yawa Khairat da Hunaif tare da Ummi ta Basu nasu na Musamman ne,Talatu kuwa sun dawo Hunaif yace zasu je Amma ba yanzu ba sai bikin Zainab da Mus'af.

Lokaci na ja Rayuwa na tafiya dai dai,Ana zaune lfy Ana zumunci sosai,Ango da Amarya sun wani Kara azabar kyau da Yar kiba,kowa ya gansu yasan suna Jin Dadi sosai ma kuwa.

Bikin Sadiya saura Sati daya,Haka bikin Zainab da Mus'af saura sati Biyu,Khairat da Hunaif sune komai manyan kawayen Ango da Amarya,Sunyi dinkin biki sababbin Kaya masu tsada na biki,Yau Sadiya da Sassafe tazo gidan Khairat lokacin Weekend Sunday suna bacci ko bacci Basu tashi ba,Suna Fitowa suka Iske Sadiya ce Wai tazo Dole Khairat sai ta rakata Shopping zata siyo wasu kayan kitchen da Bata Karasa siyowa ba.
Hunaif yace baiwar Allah sabo da Allah da safen Nan ko bacci Bai ishemu ba,Kuma kice wani Shopping ma Zaki janyeta ku tafi,ya Furta Yana Murmushi Yana tsokanar Sadiya, Iyye sabo da an baka ita kace Haka Mana,Ni Kam sai Munje da ita Dan dai yau ma daya ai ka bani aronta.
Mikewa yayi Yana dariya tare da cewa to sai ku tafi na gani ya Haura sama, Khairat tace ke Baki da hankali Sadiya ai bazai barni na fita yanzu ba,dama da yamma ne sai muje a gurguje mu dawo Amma yanzu yau weekend Yana gida ko motsi baya Bari nayi,Ke bacci fa Baya iyayinsa ko da Rana ne sai Ina kusa dashi, Sadiya tace wlh nifa ba ruwana sai kin rakani Ni a naku bikin Haka na muku? Sannan me kike bashi idan kun kwanta din Wanda bazai huta ba? Khairat tayi dariya tare da cewa baza a fada ba to.

Ke Khairat wlh kin lalace yanzu Baki da kunya ko kadan da kuwa ba Haka kike ba,Hunaif ya koya Miki, Khairat tace to karki dameshi yarinya Bari naje ko zai yarda, sama ta haura ta iskeshi yayi wanka tare da hadewa cikin kana Nan kayansa masu tsada,Khairat ta baya ta rungumeshi suna Kallon kansu a mudubi tace ka yarda na shirya na rakata?
Ae Mana na yarda kuje ku dawo Yanzu fa zanje wurin Ummi dama,Khairat ta Kara matseshi a jikinta tace na gode tare shigewa Toilet tana cikin wanka ya Shiga Toilet din yace na tafi, Khairat ta turo lips cike da Shagwaba,karasawa yayi tare da kissing nata jikinta du kumfa Amma sabo da naci sai daya shafa kyawawan Albarkatun kirjinta sannan ya tafi, tayi wanka da sauri ta fito ta shirya cikin Atamfa Super Green and black Tasha dinki Riga da skert ya zauna jikinta,ta yafa mayafinta a mutunce,ta dauki Jaka da wayarta ta fito da sauri tace tashi Sadiya Muyi sauri mu dawo nifa bana son yaga mun Dade ya min fada,Baki bude Sadiya take kallonta,ke yanzu Khairat komai miji,da anyi magana miji, ae wlh Dan kece Amma da bazai Bari ma na fita ba,Motar Sadiya suka Shiga suna hira,Sadiya na tukasu tace Khairat Wai me kike bawa mijinki ne ya damu dake Haka? Gaba daya kin mallakeshi ki fada min Nima nayiwa nawa idan anyi biki.
Murmushi Kawai Khairat tayi tace sai ranar bikin na Miki fada dariya sukayi Baki daya har suka je.
Khairat sai cewa takeyi muyi sauri Sadiya,kofa abinci banyi Masa ba,da kyar ta Bari aka Karasa siyayya suka zaba sai waya suke da Hunaif ta soyayya,Sadiya tace jarababbiya an Gama muje na sauke ki a gida.

Koda biki yazo kullum Hunaif da kansa yake Khairat ya koma ya dakkota,Gashi Abokin Ango Ana ta hada hada,Anyi rantsatsiyar Dinner sannan aka Kai Amarya Kano tsararen gidan Amarya,Hunaif dai Da Khairat Basu je Kano ba sunce sai anzo bikin Zainab zasuje su gani.
Khairat murna takeyi sun kusa tafiya Kano bikin Zainab,sai da bikin ya rage saura kwana daya a Fara suka shirya da Hunaif suka bi jirgi sai Kano State.

Zainab an Gama shirya komai domin Mus'af komai ya zuba a gidansa shima harkar girma kenan,Zainab ansha gyaran jiki lungu da sako tayi matukar kyau,Talatu Tasha murnar ganin Khairat da mijinta,Kawu ma Haka,Khairat sai kallon gidan takeyi gaba daya sabon gini aka canja,ko Ina tiles da tiles,Zainab tace ai Kawu da Ammar Soja ne sukayi hadin gwiwa suka gyara gidan,sabo da Ammar Yana karatu Kuma ya bude katon kanti yasa yaro a kantin Kuma Hunaif ne ya bashi jarin.
Hunaif kuwa tuni Ango Mus'af yazo ya daukeshi sun wuce Hotel da suke angwancinsu a Nan ake saukar frnds na nesa kaji masu abin.
Khairat tana cikin Yan Mata da ita ake komai,Hunaif ko a waya baya samunta ta samu dangi da Yan Mata ta shareshi kawai,Friday yau za ayi party,Tun safe Hunaif yake neman Khairat a waya tana ta ringing Bata dauka ta barta cikin jaka sabo da Lalle aka tsantsara Mata,sannan suka je Saloon gashi yaci kudi, Rahinatu ce taji Karar wayar yayi yawa ta daga tace ai sun tafi gidan kwalliya da Amarya,daga can zasu wuce Wurin event din.

5pm aka sa Amma sai 7pm aka fara,Khairat kyan data yi ba a magana,Hunaif ma Haka kamar shine Angon,Khairat ta fito a motar Farouq kenan tare da Sadiya Kawarta sai ga Hunaif yazo a lafiyayyar motarsa.
Tasan tayi laifi sabo da tasan zai nemeta ta kyale wayarta,Wurinsa ta karasa,Ya fito Yana ganinta bacin ransa ya gushe,yaji sanyi a ransa,Bai Mata fada ba ya rike Hannunta suka tafi ciki,kida na tashi I'm sorry na Shiga busy ne ta Furta masa, kiyaye gaba kawai cewar Hunaif.

Ansha rawa,an zubar da Naira,anci ansha Party yayi matuka,washe gari aka daura aure tare da Kai Amarya,Khairat ta zaga mutanen arziki na Kano Wanda suke mutunci da,taje gidan Sadiya,washe gari kuwa Hunaif yace tafiya gida zasuyi,Talatu itama ta Basu tsarabar makkah,Rahinatu ma ta samu Mijin aurenta wani matashin Doctor ne Amma Bai Gama gini ba yace a jirashi kadan.
Bayan Khairat sun koma gida da Sati daya ta Fara Laulayin ciki,zazzabi da Amai,sai da sukaje asibiti aka Bata Magunguna sannan Doctor ya Basu takardar cikinta Dan wata biyu.
Sunsha Murna,Haka Ummi ma sai Murna,Lokacin Kuma Hunaif ya maida Khairat schl ta zana waec da Neco sannan ya dakko Mata Irin copper me Mata karatu a gida.

Exam na Fitowa ya sata a private University me tsadar gaske a Abuja,Driver ke kaita ya dakko ta,watarana har Escort dinsa yake bata sabo da kula da lafiyarta,tuni makaranta ke tsoron Khairat matar Hamshaki ce.
Ta Kara gogewa da wayewa,ga frnds tayi wasu yaran mutunci.










AsmaBaffa.
[10/18, 3:00 PM] Sis Asma: 🦚🦚ME MAGANI🦚🦚









86-90








Official







By
AsmaBaffa









ALLAH KALAMUN CE ya kamata kisa name naki,Gashin Nan Kyautar page naki ne.

Jinjinar ban girma gareku Yan Amana,iyayen Sharhi
MAMAN NURIYYA,AISHA ZUBAIR,MAMAN RAHMA,UMMU HANEEF and AISHA BAYERO.










Yau Khairat Bata da lecture sai Monday Hunaif yafi kowa murna sabo da zai girgije,ko Office yau Friday yace bazai je ba Yana gida tare da Sahibarsa.
Yana bacci Khairat ta zare Albarkatun Kirjinta dake bakinsa kamar jariri,a hankali ta barshi tayi Dan aikace aikacenta data Saba duk da Cewa yanzu Ummi ta Bata me aiki Mace kullum tana zuwa ta yini tayiwa Khairat abinda takeso na aikin gida sai ta koma gidan Ummi Haka kullum suke aikinsu tare,yauma Haka sukayi ko Ina,har dakin Hunaif daya ke ciki Khairat ta gyara neat har toilet ko Ina Yana kamshi da Kyalli Kawai bed din Hunaif ne Bata gyara ba sabo da Yana bacci a kai, sai da suka shirya Dining sannan Khairat ta sallami me aikin da abincinta cikin Flask tace an Gama aikin yau ta koma gidan Ummi sai Kuma gobe.

Wanka Khairat tayi ta cakare cikin wani cotton material Brown Riga da skert Tasha kyau Dan dinkine na Yan gayu na gaske,Hunaif lokacin Yana toilet Yana wanka,Ta koma Bedroom dinta ta Gama gyara bed din,tana duba Ina ta Sa wayarta shi Kuma tuni ya shirya cikin Shadda light blue kamar zasu je gasa Haka ya hade shima,Yana kamshi ya fito Main Palo Yana Aiki a Laptop dinsa me tsadar gaske.
Khairat a Nan ta iskeshi ta Dauke System din tace Bari na duba wannan folder din Mene a ciki,tana dannawa zata bude Yana Murmushi yace Baki Isa ba me Zaki gani? Kokawa suka Fara suna dariya tace sai ta gani,da gudu ta koma Dining ta zauna tare da ajiye System a saman Dining din,Ta bude yazo ya kwace tare da dagawa sama da hannayensa biyu yace baza ki gani ba sai kinyi Hugging Dina Tight sai na Baki, Shagwabewa Khairat tayi tace to ai baka da gaskiya ka barni Mana na gani,Ido suka hada ta dauke idonta suna Murmushi wata Yar karama take tashi a Kan Hunaif,a hankali Ta rungumeshi sosai a jikinta tare da dago kanta tana kallonsa Cike da tabara tace pls ka bani na gani kaji ta Furta cikin salon shagwabarta.
Yana zuba Murmushi yace ok I give up Zan Baki gashi,Ta karba tare da Zama a kujerar Palon tana dubawa shi Kuma ya zauna kusa da ita.

Tana budewa ma duk pics dinta ne iri iri,Bayan ta Gama gani ta rufeta gefe,ta kalleshi da kyawawan idonta shima ita yake kallo Cike da nutsuwa yace akwai wani Abu Dana ke so ki bani pls,Khairat tace what? Yace Ur Heart ita nakeso,farin ciki ya sake shigarta tare da Tsantsan kaunar Mijin nata tace na baka tuni ma,Kawai ka cireta du,Fuskarta ya tallafa da hannayensa biyu a hankali yana matso da fuskarsa har ya hade bakinsu wuri daya suka shiga tsotsar bakin juna kamar sun samu Sweet, matsawa jikinsa Khairat tayi sosai kirjinsu ya hade,sun Dade kafin su kyale kansu Yana shafa Dan cikinta daya Fara tasawa yayi Dan tulele abinta.

Wannan Weekend din Outing suka fita shakatawa wuraren masu kudi na manyan Yara inda masoya ke zuwa,sai gidan Ummi da sukaje da dare sun Dade a can kafin su dawo tsarararren gidansu.
Sadiya da Zainab ma suna can cikin kwanciyar hankali Ana Shan love.
Talatu ta Kama Sana'a sosai take Business na siyar da atamfofi,dasu Inner wears.

Yau Khairat tana da schl Gashi ta tashi Bata da lfy sama sama take zazzabi,Hunaif ya kalleta tana rawar sanyi,ji yake kamar ya dawo da Ciwon jikinsa,ga ciki Dan ma Allah ya taimaketa Bata laulayi me zafi,tana jikinsa duk zafin da jikinta yayi Amma Baya jinsa,ta lafiyarta yake yace pls a hakura da Schl yau sai muje Hospital a dubaki tare da Baki Magunguna,Khairat fafur tace Ni Allah sai naje schl Muna da Test,Ba yanda Hunaif baiyi ba har ta bashi haushi yace to shike Nan sai kin dawo, Paracetamol ta Sha Kawai ta shirya Yana kallonta har kitchen ta shiga a Haka tana aiki tana kwanciya Amma sai da tayi kokarin hada musu chips da tea lafiyayye,Shi kuwa fushi yakeyi yace bazai ci ba,a hankali tace sabo da Kai fa nayi Dan Allah kaci,ga zazzabi na damunta ta saki masa kukan Shagwabarta data saba.

tausayi ta bashi yaci abincin sannan tace tunda Office zaka wuce ka saukeni a schl din,Tare suka fita yau shike driving da kansa ya kaita har schl,ya bude ya fita sannan ya zagayo tare da bude Mata kofa ta fito a hankali,Sai kallonsu akeyi anga Kyau na gugan Kyau,Frnds din Khairat da sauri suka zo wajenta Dan su kalle Mata miji sabo da sau daya suka taba ganin Hunaif,Dan munafunci suka fake da gaidashi sai kallonsa suke kamar zasu cinyeshi sunga Handsome.

Khairat tana kallonsu ta Bata fuska kishin mijinta ya rufeta ta riko Hannunsa tana Wasa da yatsunsa,Rungumeta yayi ta dage kafafunta yace basai kin wahalar da kanki ba,Tsaiwarta ta daidaita ta tsaya cak Hannayenta Yana kugunsa ta rike,rankwafowa yayi tare da Kara Mata kunnensa a kunnenta yace fada min Abinda kike so naji, a kunne ta rada Masa pls ka turo Driver ya daukeni Karka dawo schl dinnan wannan jiba kowa sai kalle min Kai sukeyi.
Murmushin Jin Dadi ya saki sannan shima ya rada Mata yanda Baki da lfy Babu Wanda Zan Bari yazo daukanki da kaina zanzo.
Shagwaba ta Fara ajiye Masa Amma yace shi zai dawo,Fushi tayi tace da frnds din kuzo mu wuce tana harararsu Cike da kishin mijinta.
Mota ya koma Yana Murmushi ya bar schl din.
Bayan Sunyi Test dinsu sun fito zazzabi ya sake Rufe Khairat ta dinga sheka Amai a Bayan Class Frnds nata ne suka dauki wayarta tare da Kiran Hunaif cewar yazo ya dauki Khairat tana ta Amai,yasan zaa rina,Minti kadan yazo tare da daukanta ya wuce da ita Hospital har ruwa aka Kara Mata sannan aka Basu Magunguna suka dawo gida.
Ya dinga Mata fada,kinga irin taurin kanki ko,an fada Miki magana bakya ji,ai Gashi Nan kinsha wahala a banza,Ana tausayinki ke bakya Jin tausayin kanki, ai Ni Dadi ma naji da Haka ta sameki Nan gaba sai ki kiyaye,Khairat tace Dama ai baka so na,Ni nace bana sonki? Ae Mana Gashi kace Allah ya Kara,dama Ciwon ya kashe Ni,sannan sai zagin iyayena kakeyi Akan naje schl,Dariya Hunaif yayi yace sharri Zaki min? Yaushe na zagi Iyayenki? Haka kawai Khairat ta kalawa Hunaif Sharri Wai ya zagi iyayenta Akan taje schl, taci gaba da cewa indai akan ka sani schl ne kake min Gori to ga schl dinka Nan na daina zuwa,sai ka Kai wacce kake so.

Ummi da tazo dubiya fada ta samesu suna tayi Ita Khairat Dole Hunaif Wai zaginta yayi taji Haushi,Ummi tace Kai mene Haka? Khairat tana Hawaye tace Haka kawai Ummi Dan naje schl cuta ta sameni shine yazo ya dinga Zagar min iyaye Yana ta min Gori Dan Yana biya min kudin schl,Ummi tasan Danta bazai Haka ba,kawai darun Khairat ne irin na masu ciki,domin wasu idan suna da ciki laulayinsu fada kawai suke takalowa ba a Zama lfy da miji,idan Mijin baiyi hakuri ba ya Kai zuciyarsa nesa ba sai aure ya lalace ko ayi ta tashin hankali.

Hunaif yace Ummi wlh karya take min,yanzu ko ya akayi Abu sai ta canja min magana tana takalata da fada,kullum neman fada takeyi.
Ummi tace Khairat jeki shirya mu tafi Gidana yau acan Zaki yini ki bar Masa gidan ya cinye abinsa.
Ta mike da murna tace ba sai ka cinye gidanka ba Bari na shirya Dan Allah Ummi zanyi sati daya,to Kawai Ummi tace mata,Khairat tana tafiya Shirin bin Ummi,Nan Ummi ta fayyacewa Hunaif halayen wasu masu ciki na takalar Miji fada,idan suna da ciki an dinga tashin hankali kenan,Suma ba kowanne ciki ba,Amma Ana samun Mata da yawa masu laulayi na neman fada,yanzu sai su canja Magana ayi ta fada.
Hunaif yace Ummi gwara da kika fada min nayi tunanin canja Hali tayi,ko Frnds ke zugata,kullum Bata Bari ayi zaman lfy sai ta San yanda tayi ta kaini bango tunda na yanzu na gane to na daina biye Mata.

Khairat harda shirya kayanta tabi Ummi suka tafi,Ummi tace da Hunaif ka kyaleta zata nemeka ne,Khairat Kuma ganin tabi Ummi Amma Bai nuna ya damu da ita ba ko hanata baiyi ba,sai tace ai dama ya daina sonta,dama maza Haka suke munafukai Da kin samu ciki sai su daina sonka su tsaneka,suna ma kallon ka tsufa, ita kadai ta Gama tunaninta sai sake sake takeyi harda suka je gidan Ummi ta Hana zuciyarta sukuni, Hunaif Kam shi bazai iya Zama ba Khairat ba ko Mai fadan da zasuyi yafi son Abarsa kusa dashi,Amma Dole ya Dan daure da abinda Ummi tace.
Khairat Kam jira take taga kiran Hunaif ko a waya Amma Shuru,Bai zo ya ganta ba,wani masifa ce da bakin ciki ke taso Mata a ranta kawai so take ta ganshi.

Wasa Wasa Har dare Shuru,sai ta tura Masa text ka manta Dani ko? Dama baka damu Dani ba na sani.
Shuru baiyi replying ba,sai ta samu Ummi tace nayi mantuwa a gida Ummi zanje na dauko,Ummi ta ganeta sai tace sai kin dawo.
Da sauri ta zurma Hijab fiya fiya tana sauri Hunaif sai ganinta yayi ta banko kofa a fusace ta shigo,Yana Palo Yana aiki a system,ta kalleshi kawai tace wato Dan cikin ba ajinka yake ba shine kake wulakantani kullum,Hunaif ya kalleta farin ciki ya kamashi ta kawo kanta,yace me nayi Kuma sabo da Allah?
Idan Ban Sha fiya-fiya na Mutu Baki daya ba kace ba sunana Khairat ba.
Jikinsa ya jawota ta zauna ya shafa cikinta yace gaskiya ko waye wannan Dan nawa Masifaffe za a Haifa,Yana magana ita Kuma sai kuka takeyi ta kalleshi tace Allah sai na kyastawa kaina wuta na kone du, dan Allah a cire min cikin Nan na huta.

Akan me za a cire? Hunaif ya tambaya,Sabo da ya jawo ka tsaneni yanzu ka daina so na,baka damu Dani ba,sai kayi ta min fada kana zagina, Hunaif sai ta bashi tausayi ya Shiga Lallashinta Yana lallabata tare da Furta Mata dadan kalamai Yana yabonta,Yana kodata,sai lokacin ya samu ta daina fushin zuciyarta tayi sanyi yace idan cikine ya dameki za a cire ki huta kwana Nan,Amma ki daina fada kinji? Ki daina masifa, Khairat tace ai na daina bazan Kara ba.
Nan ya dauketa suka koma Bedroom ya Shiga jiyar da ita Dadi ta Hanyar Sunna, sosai suka jiyar da juna Dadi,Wanda baza su manta da wannan Rana ba.

Washe gari kuwa tunda Khairat taje schl ta dawo da fushi ta dawo gida ta Gama tunaninta tace sabo da baya kauna ta Akan nace a cire min ciki shine ya yarda za a cire min, Dana Wanda nafi so za a kasheshi Lallai Hunaif baya kaunata Bari ya dawo daga Office.
Kasa jurewa tayi sai da ta turawa Hunaif text kamar haka:
dama nace baka kaunata gashi Nan Akan nace a cire min ciki gudan jinina ka yarda.

Tunda Hunaif yaga text abin ya bashi dariya sannan ya San Yana komawa Gida to fa akwai daru,sai daya tanaji kalmomin da zai tsara Khairat sannan Ya Shiga gidan,a main Palo ya iske ta sanye cikin doguwar rigar shadda Fara tayi kyau cikin Nan ya girma ta zauna a kasa tare da mike kafafu ta zube Green Apples a gabanta tana ta ci,kanta ba dankwali tayi kyau,Sallama kawai ta amsa Masa Amma Bata ko kulashi ba,haushinsa take ji yace za a cire Mata cikin ta.yace Ummi tace jiya Baki koma ba,ta bar Miki kofa a bude Amma Baki koma ba.

Khairat tace to ai cewa kawai zaka Yi na tashi na bar maka gidanka ka gaji Dani,fuuuuu ta mike ta dauki Hijab dinta sai gidan Ummi,Ummi sai ganin Khairat tayi ta dawo tace Ummi ya koreni daga Gidansa yace na taho nan sai ya neme Ni,Ummi tace to Lallai Abin na Hunaif ya fara fin karfina Yi zamanki karki koma,Khairat tace bazan koma ba ai.
Ta bude Fridge din Ummi ta ebo Apples dinta taci gaba da ci,Hunaif dai ya samu

Please Login or Register in order to submit comment