Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

To naji zanyi muku sarkin naci cewar Ummi,Wai Khairat din me ya sameta ne haka nasan yarinyar da kokari,Hunaif yace malaria ce Ummi kawai, ai Tasha zazzabi me zafi jiya da dare Allah sarki baiwar Allah shi yasa nake sonta Ummi, Ummi rankwashi ta zubawa Hunaif tana marar kunya,Kara ya saki Yana shafa wurin, harga Allah Ummi yarda tayi da Zancen Hunaif Malaria ke damun Khairat sabo da yanda ya zake yake ta Bata labarin Karya.
Yana kitchen ya zauna,Ummi na girkin daya sata,yake ta bawa Ummi labarin cutar Khairat,Yace Ummi jiya na tausaya mata Allah sarki gaskiya kasar Nan baza a taba ci gaba ba,Ummi tace wlh kuwa ai na lura kiyama haka Zata tsaya ba tare da Nigeria munci gaba ba,kullum mune koma baya a idon duniya,Hunaif yace ace common Malaria an kasa kawo karshenta a kasar Nan Allah yasa Ni ban Nigeria bane ba ruwana, Ummi tace Ina ji a radio suna babatun banza Wai rayuwar sauro data Zuma tare suke rayuwa idan aka kashe sauron kasar Nan shike Nan an daina samun Zuma a kasar Nan,masu noman Zuma shike Nan.

Hunaif yace to Dan Zuma sai a shigo Mana da ita daga wata kasar, Ummi tayi dariya tare da cewa kasar Nan baza muyi wani hankali ba gwara ma a saki kudi kowa ya huta, dariya Hunaif yayi tare da Furta tunda ke Ummi danki me kudi ne ai Baki da matsala, mikewa yayi tare da yiwa Ummi Sallama tana cewa kayi mata sannu zuwa dare Zan shigo na dubata,ok Ummi Zan fada mata ya tafi gida.
Khairat kuwa tuni ta gaji da bacci ta tashi ta gyara room din da Toilet sosai ko Ina ya dau kamshi itama ta fesa wanka tare da Kara gasa kanta sosai,maganin daya bata dazu yayi Mata magani sosai,kwalliya ta tsantsara sosai tasa doguwar rigar wani arnen Material Purpple and Maroon dinki ne na manyan Yara tasha kyau Bata daura dankwali ba Kawai gashinta me tsayi ta gyara tare da sakinsa kamar wata balarabiya Haka ta fito tana kamshi tako Ina.

Karar motar Hunaif taji ya shigo gida, Murmushi ta saki ta fito Palo tare da Hakimcewa a lafiyayyar kujera 2seater, tana latsa wayarta kawai tana kallon wani Film a Mbc2, Hunaif ya bude Kofa tunaninsa bacci takeyi har yanzu baisan Khairat tayi wanka har da gabatar da Sallar Azahar ba sabo 1:20 tayi shi yasa tayi sallarta ta azahar, Yana shigowa Kamshinta Dana Palon ya bigi hancinsa ya hango Dan lips din Nan yasha jambaki maroon,Ido suka hada kunya Khairat taji shi Kuma Murmushi yake sakar Mata ya karosawa gabanta yayi tare da sauke gwiwowinsa kasa ya daura kansa Saman Cinyarta,Wayar ta ajiye gefe tare da nutsa yatsunta a lafiyayyar Sumar sa tana shafa gashinsa tace Ina kaje ko Wurin Ummi kaje?

Ae mana tace tana Miki sannu da jiki ya Bata amsa,Baki bude Khairat take kallonsa idonta ya ciko da hawaye yanzu Ummi ka fadawa cutar da nakeyi yanzu ya zanyi da kunya? Dagowa yayi ya kalleta yace ke kin fiye Saurin kuka yanzu,da ba Haka kike ba kin Zama raguwa Malaria fa nace na damunki,tace da dare zata zo dubaki,Malaria nace karki kiyi kuka,Yanzu naji zance harka sa hantar cikina ta kada,Matsoraciya kawai Allah ya shiryeki.
Ameen Khairat ta furta,lokacin Hunaif ya dawo saman Kujera tare da daura kansa a saman Albarkatun kirjinta Yana tambayarta kinyi Sallah ko? Ae tace nayi,Nima a masallaci na tsaya nayi,yanzu za a kawo Abinci nasan zakiji yunwa ko? Khairat tace duk tarkacen daka zuba Mana a kitchen komai gashi Nan na ci da Sha ai bazan ji yunwa ba Tunda ga kayan ciye ciye Nan iri iri suna Haka sai ga Yar aiki Ummi ta aikota da katon basket girke girke ne iri iri sai ka zaba masu dadin gaske.

Khairat da dare sukayi waya dasu Talatu suna Bata labarin irin abin arzikin da Hunaif yayi musu sai Murna sukeyi,itama Khairat taji dadi sosai, Talatu tace ke Dan Ubanki Mijinki zai biyani Hakorana da kika rotse min su,Dariya Khairat tayi tace ai na hanashi,Uwaki Khairat zanzo Abuja ne ai wlh Dole sai ya biya, bashi Kika ci Masa.Harda kaimu mu Haye motar Aljanu to gashi jirgin sama zamu Dane,dariya ake tayi Ana Wasa da dariya gwanin sha'awa Kawu Yana cewa Allah yasa idona ya bude na Karo Miki kishiya Talatu budurwa Zan Aura suruki na zai min Aure,Khairat tace Ni Zan biya sadaki ma Kawu,Talatu ta waya ta Shiga aunawa Khairat zagi har Abuja zanzo naci ubanki Khairat,Ana ta dariya har su Zainab da Soja.
Mus'af da wuri yaje asibiti akace Typoid ce dashi aka bashi Magunguna,Bayan kwana biyu ya warke Har Hunaif yaje duba shi da sukayi waya.
Ranar kwana na Uku ne sai gashi yazo gidan Hunaif 11:30am lokacin Khairat tana kitchen taji maganganunsu da Hunaif,Fitowa tayi hannunta dauke da spoon tana ganin Musa'af ne da kyar ta gyada shi,tana fushi ta koma kitchen abinta,kamshin girkin Khairat ya cika Palon,sai Hadiyar yawu sukeyi suna Hira,Musa'af a ransa sai Jin haushi yakeyi Hunaif yayi dacen mace shi Bai samu ba.

Suka je masallaci tare da Hunaif Bayan sun idar Liman ya fara wa'azi akan masu Hassada da irin azabar da Allah ya tanadar musu,sannan ya karanto Hassada iri iri kowacce da azabarta,Mus'af yayi mukus Yanaji cikin Hassadar da aka lissafa Babu wacce Baya yin irinta,da sauran mugayen Halayensa, da cin Amanar da yayiwa Hunaif sai lokacin ya Shiga nazari da tunani,tsoro ya kamashi yasan halayensa Basu da kyau Amma yau tunatarwa tayi amfani domin yaji tsoron Allah ya shigeshi,Wanda sabo da Hassada! ba Halinsa bane neman malamai sai gashi Akan Hassada ya fada harkar shirka,sannan neman Mata da shaye shaye duk cin Amana da Hassada ya jefashi ciki,Babu Wanda Kuma yakewa Hassada sai Hunaif Wanda shine silar arzikinsa,Jin dadinsa Dana iyayensa,ga Hunaif Yana sonsa duk abinda yake Masa baya taba daga Kai ya kalleshi, sai Ummi yanda ta daukeshi da, tasan Bashi da Hali me kyau yanda yakewa danta data Fi kauna a duniya Abubuwa da yawa na cutarwa Amma Bata ko nuna Masa komai,Ga Matan Hunaif da ya Kora sannan ya auresu sai yanzu Nadama da tsoron Allah ya kama Mus'af yaga Sam Bai Dace da Zama abokin Hunaif ba,sannan da wanne Ido zai kalli Hunaif da Ummi ya Basu hakuri tare da fayyace musu Halayensa da mugayen abinda ya musu ba tare da sun sani ba, Liman Yana zazzaga waazi Mus'af Hawaye ya kwararo Masa,Liman yace wlh duk me Hassada bazai shiga Aljanna ba wannan fadar Allah ce,Allah yayiwa wani Niima kana bakin ciki ta gushe ta dawo kanka,ko kaima ka samu irinta, da me cin Amana da masu Shirka Ana bin malamai Akan biyan bukata ka manta Allah ke komai,Jama'a mu taru muyiwa kanmu fada,mu gyara halayenmu,Allah maji Rokon bayinsa ne, kofar tuba a bude take cewar liman bamu makara ba.

Kuna ganin har yau akwai lokaci ko? Kullum Ana kiyama ta kusa tashi gani akeyi kamar Wasa ne,wasu har cewa suke akwai saura ai kaza Bai bayyana ba sai kaza ya bayyana,wlh inda akaci gaba komai ya Gama bayyana manya ne suka rage kawai,je kasashen ketare ku gani komai ya bayyana cewar liman,Yaci gaba Allah yayi alkawarin Annabi bazaiyi Shekara dubu biyu a kasa ba face an tashi kiyama,Annabi bazai Yi Shekara Dubu biyu ba a kasa za a tashi kiyama,jama'a nawa yayi saura? Yanzu Shekara nawa muke a shekarar musulunci? Wlh ya kamata mu farga muji tsoron Allah,Ana Wai Wai Wai kiyama ta kusa tashi wlh watarana Ana tashi za a ga Rana ta hudo ta yamma,a Haka Ana gani kamar Wasa ne za a bude Ido kofar tuba ta rufe wa yasan yaushe ne? Ba sallama ko fada mana za ayi ba sai dai kawai aga Rana ta fito ta yamma,kurunkus,daga Nan Kuma da manyan sun bayyana ba za a Kara kwanaki Mai tsayi ba,sai dai da safe wannan masifa ta danno,anjima da Rana kaza ya bayyana,da yamma wancan yazo,Haka dare ga wani ma, kafin kace me an tashi kiyama.

Munanan ayyuka da muke aikatawa a kasa ya kamata kowa yayiwa kansa hisabi ya tuba ya daina tun da sauran lokaci,idan kana wani Abu marar kyau Kuma ka kasa dainawa Addua akeyi yaku alumma,kayi Addua kace Allah kasa na daina aikata maka laifi kaza kaza,Allah kasa na daina kaza Dana keyi,Allah ka yaye min, inshallah baza ka mutu ba Allah zai baka ikon dainawa ka tuba ka gyara halayenka.
Fans Dan Allah a dage da Addua duk abinda muke aikatawa muka kasa dainawa a roki Allah yasa a daina Yi, inshallah Allah zai sa a daina,komai sai da Addua Allah zai baka sa'a.
Liman yaci gaba da kawo Ayoyi da Hadisai Akan masu Hassada da shirka tare da cin Amana.

Yau Allah ya amsawa iyayen Mus'af adduarsu, tuni sun Dade sun Fahimci halayen dansu sai suka yi dabara suka dage Masa da Addua ba dare ba Rana Allah ya shiryeshi ya ganar dashi gaskiya,sun Dade sunayi sai yanzu Allah ya amsa,ko Dan uwanka,iyayenka,yaranka da miji etc duk Wanda ke Abu Bai Dace ba yan Uwa Addua ta Dace a dukufa Ana yiwa mutum Allah zai amsa.
Mus'af Mikewa yayi Yana goge Hawaye Imani ya ratsa zuciyarsa,Hunaif yayi mamakin ganin Mus'af yau yaji wa'azi harda Hawaye, gida suka koma Mus'af ya kasa komai abincinma da kyar ya ci kadan,Hunaif ya tambayeshi lfy? Yace zazzabi yake ji yayi karya,Mikewa yayi yace zaije ganin Doctor,Har mota Hunaif ya rakashi Yana Masa sannnu,Mus'af Yana fita ya koma Hotel ya sharbi kuka Yana Rokon Allah gafara sai ya kwaso tarkacen da malamai suka bashi ya watsar dasu Baki daya,ya shirya kayansa ya bi jirgin yamma sai gidansu wurin iyayensu,Gaba daya ya rasa sukuni ya hargitse ya rasa taya zai roki Hunaif Gafara da Ummi.
Kuka yake kullum a dakinsa ba dare ba Rana Yana tuba ga Allah,Ummansa ta rasa gane kansa me ya dameshi Oho,Haka Babansu ma,tambayar duniya sai yace ba komai,Ya rame sosai ya Kara wani haske,Wayoyinsa ma kaf kashewa yayi Babu Wanda ke samunsa,abubuwan daya aikata munana a rayuwar kawai yake tunawa Yana kuka da tuba ga Allah.
Ganin Yan uwansa da iyayensa sun Shiga damuwa ganin halin da Mus'af yake ciki sai ya yanke Shawara gwara yaje ya fara neman yafiyar mutanen daya zalunta tun lokaci Bai kure Masa ba,tun suna raye, Matan Hunaif daya Fara aura ya nema ya Basu hakuri sabo da lokacin daya auresu ya wulakantasu ya sakesu ba bisa laifin komai ba,duk da cewa yasan sunwa Hunaif laifi Amma Dole dai ya nemi yafiyarsu,ta karshen Daya tafi wajenta Ameera ce wacce ya barta da ciki,sannan yarsa data Haifa Bai ko Santa ba,Ameera wani Dan Majalisar tarayya take aure, Ya nemeta har kasa ya duka tare da Bata hakuri,Ameera tayi Murmushi tace Allah ya min canji na Alkhairi na yafe maka,sannan cikin da ka barni dashi zafin abinda kayi min yasa na zubar da cikinka,da sauri Mus'af Yace Ina yata fa Meenal? Na jefar da ita wata baiwar Allah ta tsinceta ta raineta tsakani da Allah,ka godewa Allah Ina bibiyar rayuwar Meenal dita.

Da sauri yace Dan darajar Allah Ameera wace ta tsinceta? Wlh ko wace sai na Bata abinda na Mallaka kaf,Murmushi Ameera tayi tace Lallai ka tuba Mus'af Allah ya yafe Mana Baki daya Meenal itace wacce Khairat matar Abokinka ta rike duk talaucinta a lokacin tasan darajar Dan Adam a kansu ta nemi aiki a Company naku Dan ta sata schl,ka dinga gana Mata azaba tare da yaran da take rikewa,ko ita bata San Yarka bace,ka dinga tsinewa Yar cikinka baka sani ba,tsinannun Yara etc,Kar tazo maka da Yara Office,duk Ina monitoring naka.
Shi yasa ake so ko me mutum zaiyi yabi duniya a sannu,baka dauki Dan Adam a komai ba sabo da kana da dukiya.

Mus'af yace to wannan yaron Kuma Dana ga Khairat dashi na waye? Wlh ban San na waye ba shima dai tsintarsa tayi, Meenal ce yarka kawai cewar Ameera tana zaro wayarta katuwa tare da nuna Masa Hotunan Meenal iri iri,ya karba ya tura Pics din a wayarsa Yana Jin Dadi,sannan yace to naji Ummi tace su Meenal suna katsina wurin kanwarta ta bar Mata su,ae Haka Zancen yake suna can cikin daula domin Mijin kanwar Ummi Hamshakin me kudi ne yaransa Biyu kacal shi yasa suke kaunar Yara.
Bayan Sun Gama Magana da Ameera Mus'af mutanen Office yaransa da abokai tare da duk Wanda yasan ya batawa sai da ya nemi gafarar,Mutanen Company din sai mamaki sukeyi suna Jin Dadi yanzu Oga ya Zama mutumin kirki,kowa da abinda yake cewa,ga taimako yanzu kowa a mutunce suke Muamula ba zalinci da cuta,shi kanshi yanzu yafi Jin dadin rayuwarsa,Abu daya ne ya dameshi Bawa Hunaif da Ummi Hakuri tare da Khairat ya rasa ta inda zai iya Furta musu abinda ya aikata iri iri.
Tunawa yayi da Yan Uwan Khairat su Zainab a Kano suke,Sunday da yamma ya figi motarsa tare da tafiya gidan,Wani yaro ya aika yace ya Kira Masa Zainab,Zainab fa yanzu Jin Dadi ya samu tayi kyau da haske Ana ta daukan wanka dama Ita Yar kwalliyace Bata yarda ta zauna kurar baya ba.

Ta fito sanye da doguwar rigar Lace tayi kyau matuka tayi Yar kiba ko Ina a cike,tana kamshi,ganin Mus'af tayi tunanin Hunaif ya Aiko shi ko Khairat,a mutunce cike da ladabi suka gaisa, Mus'af da kyar ya daure ya bawa Zainab labarin irin abinda ya shukawa Hunaif da Ummi har Khairat,sannan da tuban da yayi da komai ya Bata labari kaf Babu abinda ya boye Mata,Zainab ta jinjina Hali irin Na Mus'af sai taga duk abinda ta aikata Ashe ita Yar Aljanna ce Akan Mus'af, Amma ya Bata Tausayi Kuma,sannan taji dadin tuba da yayi sannan Imani ya shigeshi,yace to yanzu me zan iya yi maka? Mus'af yace ki tayani Dan Allah muje Abuja tare na Basu hakuri,nasan Hunaif Yana matukar son Khairat idan Kika lallabata zata yafe min sannan zata sa Hunaif ya yafe min.

Zainab tace to Allah ya taimakeka shekaran jiya muka Gama exam munyi hutun Sati biyu Zan sanarwa Iyayena cewar Khairat tana nemana sai muje,Farin ciki ya Kama Mus'af yace na gode sosai Nan sukayi sallama tare da exchange na number wayarsu.

Washe gari Monday da yamma Mus'af da Zainab suka bi jirgin karfe biyar zuwa Abuja,Nan danan sai gasu a Abuja city,Gidan Ummi sukayi masauki Kar a takurawa Amarya da Ango.

Ummi tayi mamakin ganin Zainab Yar Uwar Khairat da Mus'af,sai da suka huta tare da cin abinci,har dare Mus'af ya fita,Zainab ta samu Ummi a Bedroom dinta tana shirya Kaya,tiryan tiryan kamar yanda Mus'af ya Bata labari Haka ta bawa Ummi.
Ummi batayi mamaki ba sabo da tasan za a rina,karshe Zainab tace Dan Allah Ummi wlh ya tuba yayi Nadama da gaske Imani ya shigeshi,kunyarku tasa ya kasa fada muku, Murmushi Ummi tayi tare da cewa ko Mai dadewar abu a duniya zaizo karshe,tun sanda Mus'af ya tafi Naga irin halin daya ke ciki na gane shiriya tazo Masa,na Dade da ganewa kawai Allah na barwa lamarin sabo da nasan mutum Bai Isa ya maka abinda Allah Bai maka ba,sannan Mata daya aura ban damu ba sakamakon dama Hunaif Ni na zabo Masa su Bai taba auren so ba sai a Kan Khairat,sannan Wanda ya aura bamu sani ba Basu da tarbiya Basu Dace da Zama Matan Hunaif ba.

Zainab tace haka ne Ummi Dan Allah ku yafe Masa kisa Baki Hunaif ma su yafe Masa,nasan Hunaif zai yafe ba sai ma nayi magana ba sabo da shi me yafiya da hakuri ne Akan komai Allah ya yafe Mana Baki daya.
Ameen Amma Khairat Kam nasan za a Kai ruwa rana da ita Bata ji nasan halinta cewar Zainab, Murmushi Ummi tayi tare da cewa a'a yata me hakuri ce wlh ga hankali karma ki fara cewa za asha wahala da ita.
Dariya sukayi gaba daya. Da dare Mus'af ya dawo Yana bin bango Yana kunyar Ummi,Ummi tace gidanku Mus'af zo Nan Allah ma ana Masa laifi Yana yafewa,aini naji Dadi da Allah ya ganar da Kai gaskiya da wuri,Haka Ummi ta dinga Masa fada da Nasiha ba ji ba gani yayi mukus dashi.

Washe gari da Yamma Zainab da Mus'af suka tafi gidan Khairat,Mus'af kirji na dukan uku uku.ko Hunaif zai yafe oho kun San me hakuri fa Bai iya fushi ba.


Nasan Fans zaku ce ansa Mus'af ya shiryu Bai Sha wahalar rayuwa ba,Dan Allah ku Fahimci sakon Novel din Nan ba Lallai fa Shan wahalar duniya ce ke sa mutum yayi tuban Dole ba,Dan Adam Haka kawai Allah Yana sa Masa shiriya ta kankanuwar Sila, wani wahala ko Talauci ba Lallai suke sa Dan Adam ya shiryu ba,Hasalima wani sai dai ya Kara lalacewa.
Ku bini a sannu gaba zaku gani.






Nagode Fans masu Sharhi Ina kaunarku wlh.🥰🤣💋😍





AsmaBaffa
[10/18, 2:57 PM] Sis Asma: 🦚🦚ME MAGANI🦚🦚








76-80








Official









By
AsmaBaffa










Mamu Galadima,Mmn Nura,Momy Suraj,Mariya Habu Gumel,Maman MD,Nanerh,Hauwa j,wacy Baby,Nana Aicha,MRS MMGN,Walakosalata,Sayyada,Aisha Musa Gidado,Hassyna Z Usman and Ummeeloh.
Ga page naku mutanena.








Khairat da Hunaif lokacin Suna Palo sai kokawa suke Lallai sai Khairat ta kyaleshi ya sake second Night tun sau daya daya yayi First Night Bata sake Bari ko Romance Sunyi ba, yau Hunaif ya Gama kaiwa karshe domin yayi Hakuri har 1wk Khairat na azabtar dashi ta hanashi komai,shi Kuma ya kasa hakuri da ita sabo da yanda yaji Zumarta.
Kyaleta yayi yace nine fa Hunaif dinki, Kafada ta makale,to kin San Haka ne me yasa kike sa English wears kullum kina makale min a jiki? Kin San azabar Dana ke Sha? Gwara ma ki bani wlh yau ta karfi zan Miki idan na kamaki,ko ki bani ko na kaiki Boaden schl makarantar kwana nayi Amaryata sabuwa,Dariya Khairat tayi ta koma jikin bango ta makale tace wlh bazan je makarantar kwana ba.
Door Bell ce tayi Kara Hunaif yayi tafiyarsa sama sabo da Khairat ta Bata Masa rai, ita kanta Bata ji dadin fushin nasa ba,ta wahalar dashi har 1wk.

Hijab ta dakko Kato me hannu tasa sannan ta bude kofar ganin Zainab sai da ta tsorata sabo da Bata San da zuwanta ba tace Allah yasa dai ba Kawu ne ko wani bane ya mutu?
Dariya Zainab tayi tace banza surprise na Miki,ko bakya so na koma,Murmushi Khairat tayi harda rungume Zainab tana murna, fara'arta ce ta tsaya cak ganin Mus'af a Bayan Zainab, shigowa sukayi tare da Zama,Khairat ta janye Zainab bedroom dinta,tace ke Kuma me ya hadaki da wannan mugun? To baza ki aureshi ba idan ma Zaki canja ki canja, Zainab ta kalli Khairat tace ke ba wannan ya kawo Ni ba Ni,Ga dai wannan inji Ummi tace a Baki yanzu ki shanye maganin Gyaran Mata ne,Khairat ta karbi robar faro ta dage magani ta shanye sai kadan ta rage.

Hannun Khairat dake rike da roba Zainab ta kamo sannan ta shiga sanar Mata abinda ya kawosu,tare da Bata labarin komai da Mus'af ya fada Mata da tubansa,Khairat tace wait yanzu dama Meenal yarsa ce? Kwarai kuwa cewar Zainab,Kai Amma Mus'af ya Bata kansa wlh,wannan wacce irin zuciya ce dashi haka,shi kuwa me ya dauki duniya Allah sarki Hunaif Dina Ashe Mus'af ne ya tura aka bige min Dan Mijina da mota har ya Hadu da cutar mantuwa Amma wannan ya cika azzalumin banza,Ni abinda yafi bani haushi daya sa aka bige Hunaif da mota.
Zainab tace kuyi hakuri tunda Allah ya ganar dashi abinda ake so da Dan Adam idan har an bashi hakuri ya yafe,wlh tunda har Kika ga duk abinda yayi baiji kunya ba ya fadawa mutane to ya tuba taubatun nasuha ma kuwa ingantaccen tuba yayi,ki roki Mijinki ku yafe Masa,Ana son me hakuri Wanda aka zalunta Kuma ya hakura, Dan Adam ajizi ne,kowa Yana yiwa Allah laifi.
Hmmm Khairat taja numfashi sannan tace na yafe Masa duniya da Lahira,Sannan Meenal Kuma yanzu basa Hannuna yaje wurin Ummi su bashi a barsa idan Yana so.
Zainab tace to saura Ogan naki kije ki lallaba Mana shi,Khairat tace sai dai na Kira muku shi yaji Daga bakin sa.

Dakin Hunaif taje Nan ta iske shi Yana latsa System tace Mijin Khairat kafa Yi Baki ka fito main Palo.
Mikewa sukayi suka fito tare,ganin Mus'af yace ka Gama kashe wayar ka fito, Mus'af kunya duk ta cikashi da kyar ya daure ya fara karanto Abubuwan da yake wa Hunaif kenan Hunaif ya dakatar dashi sannan ya kalleshi yace na Dade da sanin komai,Har bigeni a mota Kaine kasa,Nan Hunaif ya dinga fadar abinda Mus'af yayi Masa,karshe yace Ko Memoryna ya Dade da dawowa Normal sabo da na gwadaka na nuna ban warke ba Kai Kuma kayi ta rantar kudi ahannu na baka biya sabo da tunaninka bana ganewa,Haba Mus'af ba irin mu akewa Haka ba sai marar kwakwalwa kyaleka kawai nakeyi Naga iya gudun ruwanka,sannan Nasan duk abinda yayi farko zaizo karshe sannan Allah Baya barin zalinci.
Yafiya kuwa har kudin komai na yafe maka,naji Dadi da Allah ya ganar dakai,ka kula karka Kara komawa gidan jiya sai ka kiyaye gaba.

Farin ciki da Godiya Mus'af ya shiga yiwa Hunaif,shi Kuma yace ba komai, Hunaif kam a ransa ya dade da kudurcewa ransa bazai taba sakin jiki da Mus'af ba kamar da, sama sama kawai, shi yasa tun tuni ya rage muamula dashi,ko aurensa Farouq ya shige Masa gaba.

Khairat ta kawo musu kayan ciye ciye dana Sha suka ci lokacin tuni Hunaif yayi Shirin tafiya masallaci sallar Magrib,Tare da Mus'af suka je Sallah,Zainab da Khairat Sunyi tasu a gida Suna ta hira Khairat tana rokar Zainab ta kwana a gidanta Zainab tace Ina gidan Ummi yarinya, Khairat tsoron Hunaif yasa take neman Zainab ta kwana a gidan Dan ta fake da bakuwa Amma Zainab Taki yarda,Bayan Sunyi Sallar Isha Mikewa sukayi tare da musu Sallama suka tafi gidan Ummi,Mus'af sai godewa Zainab yakeyi Akan kokarin da tayi Masa sai yanzu ya samu sukuni a zuciyarsa yanzu Iyayensa da Yarsa kawai ya rage Ya dawo ya gyara komai,Amma Yana tunanin to Mohd din Khairat Wanda ake rike su tare Dan waye,yaron ya Dade Yana Masa Kama da wani.

Khairat wurin da aka Bata ta gyara tare da wanke kwanukan ta shirya kitchen dinta sannan ta koma Bedroom dinta tayi wanka tare da Shirin bacci cikin Wata Yar bingilar rigar bacci kamshi takeyi kawai,maganin Da Zainab ta Bata tace inji Ummi ta Karasa shanyewa,ji takeyi jikinta duk ya canja tunda Tasha maganin Sha'awa ke taso mata sama sama,ga Niima ta sakko Mata tare da Karuwa Akan da tayi Makil da ita.

Bedroom din Hunaif ta wuce ta samu yayi shirinsa tuni ya kwanta abinsa tunaninta bacci yake ma,ya Bata tausayi kullum tana ta faman ja Masa Rai Kuma ya hakura Bai Mata Dole ba,Hunaif ba bacci yake ba Yana jinta har ta kwanta a bayansa tare da Rungumeshi, sai da kashinsa ya motsa sabo da yanda yaji Khairat a jikinsa,hankalinsa ya tashi Amma yasan ko yace ma fada zasuyi kawai ta Bata Masa Rai,sai ya share ta, Khairat tayi mamaki Dan ta gano idonsa biyu baiyi bacci ba,shareta kawai yayi,Hannunta tasa ta bayansa tare da shafo fuskarsa zuwa Dan sajensa da gemunsa kadan,Ko motsi baiyi ba, sai taji Bata ji Dadi ba, ta Saba Yana kulata ko basuyi komai ba suna Hirar soyayya

Please Login or Register in order to submit comment