Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kora barasarsa ta katse shurun da ajiye Masa takardarsa a saman table ta Fara magana Morning sir, wannan dokar taka bata yi min ba, guda biyu a cikin bazan iya su ba,tun kafin ta fadesu ya gane wanne take nufi,yaushe Zan iya Zama Dole sai kayi bacci zanje na kwanta jariri ne Kai? Sannan na tashe ka da Asuba ai Kai ya Dace ka tasheni Kaine namiji.

Hmm yayi Dan guntun Murmushi kana ya kalleta da idonsa me tsananin kyau yace Ummi kike so na Nemo ta min? Ni da kike ganina Haka Ummi take min Bata bacci sai ta tabbatar nayi bacci tana kusa Dani tana min adduoi,idan nayi bacci ta kashe min light ta tafi,sannan da Asuba ita ke tashina nayi Sallah,ai Lada ma Zaki samu idan kuma auren ne bakya so to sai ki zauna a Haka Baki San danginki ba,yanzu Kinga Ni har nasan inda suke a garinku Taraba.
Jin abinda yace sai Khairat ta turo lips dinta gaba tare da daukan takardarta ta rules tace Haka Zan auri Dan shaye shaye? Nan take idon Hunaif ya koma red yace watch ur tongue shaye shayen me nayi? Tsoronsa ya kamata tace Allah baka hakuri ai ruwa nake nufi ba giya ba,ka fiye son ruwa, tayi waje da sauri.

Tana fita tayi kicibis da Musaf zai Shiga Office Din Hunaif ya bigeta da karfi takardar dake hannunta ta Fadi da sauri ta dauka ta tafi da sauri, shi Kuma yaja kwafa ya tsaneta,me yake kawo ta Office din Hunaif ne shine abinda ya kasa ganewa Kenan Amma a ransa ya kudurce sai ya gano gaskiya.

Hunaif washe gari da wuri yayiwa Ummi magana suje a kwaso Meenal da Mohd Yaran da Khairat ke rikewa lokacin Kuma Kan Ummi Yana ciwo tace Bazan iya ba Hunaif kaje ka kawo min su kawai.
Already ya rigada yayiwa Khairat waya Amma yace kayansu kar ta Basu ko tsinke Ummi zata siya musu sababbi masu tsada,Da Kansa yake driving zuwa gidan Khairat,jiki a sanyaye Khairat ta fito da yaranta harda Hawaye Bata son rabuwa dasu,Baba Isyaku ta sanarwa Yace mashaallah kin huta kema Allah ya taimakeki,Khairat tace ai aure zanyi,Shi kanshi Baba Isyaku yayi mamakin ganin Mijin da Khairat zata aura ga kyau ga Naira,su Khairat sun Saba da ganin Hunaif sai Basu yi kuka ba suna ta dagawa Khairat Hannu suna wasansu a mota har Hunaif ya bar unguwar.

Bayan kwana Uku tsakani Hunaif ya tura Driver ya dakko Khairat tare da kayanta kaf wasu Kuma ta bawa Baba Isyaku,sukayi Sallama da me Unguwa Wanda take haya a gidansa da makwaftanta ta shige mota suka tafi sai gidan Kawu Sabiu Makaho,lokacin Kuma ta bawa Hunaif Address yaje kofar gidan da jerin motocinsa securities na take Masa baya.

Talatu Jin motoci Sunyi yawa suna ta tsayawa a kofar gidansu sai ta leko tunaninta mutanen Zainab ne ko Kuma wurin Rahinatu suka zo,to ita dai Zainab Bata da matsayin da zata kula irin wannan bare Rahinatu,Talatu taga Hunaif sai tace La balarabe ne to ko Service din Mtn ne ya Fado a gidanmu za a siye gidan? ai ko da munyi kudi,da gudu ta koma gida,tana bawa Kawu Sabiu labari,yaranta sukayi ta lekowa,Lokacin Soja yazo Weekend gida,Zainab tana Nan tana girki zatayi bakon saurayinta daga Zaria.

Khairat ce sanye cikin doguwar rigarta sabuwa dal wacce Hunaif ya Bata yace tasa,Tasha makeup kowa yaga Khairat zai rantse Yar gidan wani Hamshaki ce harda sa Takalmi me tsinin gaske tana taku dai dai.
Gidan ta Shiga da Sallama kwas kwas,Talatu tana ganinta ta rafka salati tana Malam fito kaga Khairat,Kawu yace Ina Naga idon da Zan ganta me tayi? Ta Zama Yar dagwas,Yar gayu,Ashe ita ce tare da me kudin Nan Dana ke baka labari,ai sai su Zainab suka fito da gudu suna kallon Khairat da Hunaif sun jero ga securities suna take musu baya.

Da sauri Zainab ta Shimfida sabuwar tabarma sai kallon Hunaif sukeyi,Bayan mun zauna ya sallami securities cewar su jirashi a waje,a mutunce ya gaida Talatu ta amsa da sauri tana washe Baki,Kawu ma da baya gani Yana gefe suka gaisa yace duk da bana gani kamshinka kadai ya Isa a San Kai babban mutum ne,Hunaif ya daure fuska ba mutunci yace abinda ya kawoni na dawo da Khairat gidane zata zauna kafin ayi bikinmu,sabo da kyan ya Mace gidan Ubanta ko mijinta,ta bani labarin yanda kuke Mata Kuna zaluntarta,gata na dawo da ita kafin ayi bikinmu ta bar muku gidanku,Wlh wlh kunji na rantse kallon banza kuka yiwa Khairat masoyiyata sai na daureku ko waye ba ruwana,ku Fadi kudin da kuke so na zamanta a gidanku Zan biya ko nawa ne,ba kyauta zata zauna ba,Ammar Wanda duk ya gigice ganin me kudi Haka yace ai ba ko kwandala ma ta zauna sabo da ai mu Yan uwanta ne Kawu ma Babanta ne.

Zainab tace wlh kuwa ai gidansu ne,Kawu Sabiu yace Wai Kai waye ne Malam,da Sauri Zainab tace wlh Kawu Bin Mahmood ne Wanda ake ta zancensa a radio da gidan tv,Kawu ya ja baya a tsorace wanna yaron Dan balarabe me kudi dai? Talatu tace shi fa,Kawu ya jinjina yace Khairat da samun irin wannan tab Allah kenan.
Khairat tana iyayi tace ku Fadi kudin zamana a gidanku How much? Talatu tace iyye nasan Zaki aikata Khairat,to ka bamu dubu dari Uku,Hunaif yace kacal? Baki bude Talatu tace kacal duk wannan uban kudin,Yace ga Dubu dari biyar Zan baku check,sannan Kawu bani address na family dinku dake Taraba da Dangin Maman Khairat, jiki na tsuma ya fara musu bayani,Khairat tana rubutawa a paper har ya Gama Basu Address.
A hannun Kawu ya damka check din kudi Hunaif ya Kara da cewa Khairat kema kamar gidanki ne kudi aka biya su, duk Wanda ya Miki ko Harara ki fada min wlh kunji na rantse sai na daure mutum,aiki ba abinda zata yi muku,Abinci Kuma safe rana da dare.
Talatu jiki na tsuma tace ba abinda za ayi Mata Abinci ma sai ta barshi,Bayan Hunaif ya mike zai tafi Yace Muje Sweetheart ki rakani mota,kiyi hakuri kiyi manage a wannan gidan da abincin kafi a daura aure,kamar gaske Khairat tace Babu damuwa Honey Dan Allah karka damu da tunanin Ina wannan gida marar kyau Zan jure, Murmushi yayi kawai Yana kallon ikon Allah wurin Khairat yanda take ta yanga da iyayi tana lankwashe murya.

Talatu tace ai yaro indai Khairat ce zaka Sha iyayi wannan da gidan kudi ta taso to ba a San me zatayi ba sai ta taka mutane,ba Wanda ya kula Talatu sai ma gani sukayi Hunaif ya riko Hannun Khairat suna magana kasa kasa sun fice kofar gida, Zainab ji take kamar ta hadiyi zuciya,Ina ma itace ta samu Hunaif,Rahinatu ma Haka take jin inama itace,Soja yace Alhmdllh na Samu kudin komawa schl,gobe sai makaranta,Rahinatu tace muma a biya Mana kudin waec da neko dama an kusa rufewa,Zainab ta karbi check tace zanje na Ciro kudin Nima gobe Zan koma Hostel.

Khairat kuwa suna fita ta kwace hannunta wani shock take ji a jikinta Wanda shima hakan Yake ji, dariya sukayi sannan Khairat ta dauki Jakar kayanta da Wanda Hunaif ya siyo Mata sababbi da Wanda ya dinka Mata atamfa,shadda,laces etc,ya siya Mata sabuwar waya katuwa me tsadar gaske,sannan ya Bata 50k tayi amfani dasu.
Ciki ta Shiga da kayanta sukayi Sallama Kan Next wk su Abbinsa zasu zo daga Kuwait Zasu kawo kudin aure da lefe sai a tsai da Rana.

Khairat tana komawa gidan kowa sai wani Nan Nan akeyi da ita suna lallabata,Kawu yace Khairat Yar Dan uwana,Khairat yata zo Nan muyi hirarmu,yanzu Khairat sai ki gudu ki barmu ko tunawa damu Baki yi ba? cewar Talatu,Khairat sai kallon ikon Allah takeyi.
Ko tsinke Hana Khairat dauka sukayi sabo da suna tsoro Kar Hunaif ya daure su,duk da Haka Khairat sai da ta Taya Talatu aiki Bata bar gidan da kazanta ba sai da ta gyara ko ina.dakin Khairat ma Talatu kwashe komai tayi na shirgi da suke Tarawa a ciki,Khairat ta gyara abinta.

Saura Kwana Uku dangin Hunaif na Uba suzo neman aurensa yana Kan Hanyarsa ta komawa gida da yamma likis sai motarsa ta tsaya ,Driver yayi iya yinsa taki tashi,sai Hunaif yace jeka hau Napep ka dauko Me min gyara Ni Bari na Kira wani Driver yazo ya tafi Dani,Driver yace to sannan ya Shiga Napep ya tafi,Hunaif yana Kiran Driver Amma taki Shiga,ya fito gefen titi Yana tsaye Yana gwada Kira sai ga wani abokinsu Farouq da mota ta saya hannun Opposite ya tsaya Yana ma Hunaif horn,Hunaif ya daga Masa hannu Yana Shirin motoci suyi sauki ya tsallaka titi kawai wata mota Ta taho da Masifar gudun gaske direct dama Kan Hunaif ta nufa Aiko kafin ya farga motar ta kwashe shi yayi sama ya Fado dam a kasa shi kuma me motar ya take da matsiyacin gudu kafin kace me ya bacewa kowa.

Babu inda Hunaif yaji ciwo sai a kansa,jini Yana malala a kasa Kuma Yana yashe a kasa,abokin nasu Farouq da gudu ya fito a gigice ya tsallako titi tare da karasowa wurin, mutane sun cika makil a kansa,Driver ma daya dawo da bakanike Kuka ya saki,A motar Farouq aka sashi zuwa asibitin Private,Ummi ma an sanar Mata sai kuka takeyi tun kafin ta Isa asibitin,Musaf shi ya fara zuwa a gigice Yana hawaye, ganin Halin da Hunaif yake ciki da kyar idan zai tashi,kansa ya bugu,a jikinsa Haka lfy Lau Bai ji ciwo ba sai iya kansa.
Ummi tunda ta ganshi take kuka kawai kamar zatayi hauka.
Iyayen Musaf ma tuni suna can asibitin,Ummi tace waje zata fitar dashi,Nan tare da Farouq sukayi shige da fice sukayi visa ta Germany kwana Uku suka daga zuwa Germany tare da Farouq da Ummi Mus'af ma ya bisu a baya.

Meenal da Mohd Kuma Ummi ta kaiwa Yar uwarta Haj Amina ajiyar su Meenal taci gaba da kula dasu kafin su dawo,Su Meenal har sun Saba da kowa harkarsu sukeyi.

Ummi Hawaye takeyi kawai har suka Isa Germany Hunaif Bai farfado ba,likitoci suka fara aikinsu a kansa Ana ta gwaje gwaje,Doctor ya Kira Ummi ya Sanar Mata cewar Hunaif ya samu matsala a kwakwalwarsa,ko idan ya farka zai iya farkawa da Ciwon Hauka,ko Kuma ya kasa tuna rayuwarsa ta baya,sannan Kullun ko me yayi a ranar idan yayi bacci ya farka bazai tuna abinda yayi a jiya ba,Babu abinda Memory dinsa zai ajiye, kullum idan ya tashi a bacci to fresh zai tashi ya manta abinda yayi na jiya bazai dinga ajiye komai a kansa ba.
Ummi ta barke da kuka,Dr yace karki damu ko Ciwon hauka ne ko Memory dinsa baya ajiye komai na wani lokaci ne kadan zai warke Baki daya ya dawo normal,sai dai za a dan dauki dogon lokaci,Zan hada ku da babban Dr a Abuja take aiki zaici gaba da kula da magungunan Hunaif sannan ko ya kuka ga canji Hunaif yaje Yaga Dr a sanar mana,sai lokacin Ummi ta Danji sanyi Jin zai warke,dama tashin hankalinta ace bazai warke ba.

Khairat Bata San me ya faru ba taji duk wayoyinsa basa Shiga har sati guda Shuru ba shi ba alamarsa sannan Bai turo dangin nasa ba,yau Monday da wuri ta shirya taje Building dinsa Company Aminu duk Basu San me ya faru ba su dai sunga ba Musaf ba Kuma Hunaif,Aiki ya tsaya cak,sannan Musaf Kwana Uku yayi kacal a Germany ya dawo Kano Yana zuwa aiki Amma yaki fada musu komai Ina Hunaif yake babu Wanda ya sani,tunanin kowa Hunaif yayi tafiya ne maybe tunda ya Saba.

Abin takaici Khairat bat a San kowa na Hunaif ba sai Musaf Wanda ya Gama tsanarta,Haka Bata San gidan su Hunaif ba,Bata San Ina su Meenal suke ba,to Taya zata nemi Gidan su Hunaif,zuwanta Company sau uku Musaf ya Mata cin mutunci yace ya koreta idan ma aiki take zuwa ya sallameta,Ummi kuwa tana ganin Halin da Danta yake sai tasa aka rufe a accnt dinsa Baki daya,sannan tabi Companies nasa da sauran Abubuwa da kadarorinsa kaf ta hada kansu ta kwashe takardun komai ta hada su wuri guda ta Adana yanda ba me sanin inda suke Dan ita hankalinta Bai kwanta da Musaf ba,Duk tabi ko Ina ta daura mutane masu Amana data sani suke kula da Business din Hunaif da komai,iya Company biyu kacal ta barsu a hannun Musaf na kano Dana Rivers state, Wanda dama a hannunsa suke,Dalilin Haka yasa Mus'af ya Kara Tsanar Ummi Yana tunanin daukan mataki a kanta mummuna.

Farouq kuwa mutumin kirki shine ya tsaya sosai yake jinyar Hunaif har Ummi ta dawo Germany suka ci gaba,Kuma Farouq cikin frnds din su Hunaif yafi kowa hankali da nutsuwa Kuma shine Wanda ma Hunaif Bai damu dashi ba baya wani Shiga harkarsa sosai Amma sai gashi Farouq shine yayiwa Hunaif Rana fiye da kowa.

Wasa Wasa Khairat ta Fara damuwa an kwashe 3wks babu alamar Hunaif,tana ta faman sintirin zuwa Company Amma Babu Wanda yake da labarinsa,Koda Musaf yaga ta dameshi ma sai ya fara tunanin mene tsakanin Hunaif da Khairat data dameshi Haka kullum sai tazo Office tana rokonsa Kan ya fada Mata Ina Hunaif yake,ba irin wulakancin da Mus'af baiwa Khairat ba Amma sai yaga ta jure Kullum sai tazo,sai yayi tunanin akwai wani Abu a kasa Bari yayi Amfani da wannan damar ya gano gaskiya a wajen Khairat.
Katsam yau ma da Sassafe sai ga Khairat tazo da wuri tana ganin Musaf ta dinga binsa tana rokonsa har Office.

Zama yayi a nutse ya kalleta sannan ya kunna sigarinsa ya zuka tare da feso hayakinta ta hanci ta Baki sannan yace kina so na fada Miki inda yake? Khairat tace ae da sauri,Murmushin mugunta yayi sannan yace fada min mene alakarki dashi? Wanne Abu ne tsakaninku da kika damu kanki sai kin San a Ina yake Bayan ke ba kowansa bace face Yar shara da goge goge?
Khairat tayi niyyar fadawa Musaf gaskiya sai ta tuna halayensa,sannan ta tuna yanda baya kaunarta sai tace Wani agogonsa ne na Diamond me tsadar gaske yace na ajiye Masa a Hannuna zai karba,Kuma a kalla yace zai Kai Million Talatin,shine Zan bashi abinsa Kuma ban ganshi ba,Musaf yayi Murmushi yace karya kike baki da matsayin da Zaki San sirrin Hunaif ko kadan,kin San zurfin cikinsa kuwa?.
Bari na fada Miki Khairat kike ko wa Ki daina Bata kafarki kina zuwa Hunaif ya koma kasarsu Kuwait da Zama idan kina da kudin binsa bismillah sai ki bishi Amma wlh baya kasar Nan Kuma ba yanzu zai dawo ba hasali ma ya Gama Zama a Nigeria Baki daya, kajifa mugu.
Khairat ta yarda Hunaif baya kasar ga yanda taga da gaske Musaf yake fadar Maganar,sai tace to Ba damuwa ta tafi gida jiki a sanyaye tana goge kwalla.







AsmaBaffa.
[10/18, 2:50 PM] Sis Asma: 🦚🦚ME MAGANI🦚🦚







21-25









Official









By
AsmaBaffa







Sweet Mum,Ayshertuh,Zee I.G, Queen of Shebah, Hadiza Hussain,Maman Humaira,Mmn Moustapha.
page dinku ne na hannun dama.






Jiki ba kwari Khairat ta fito tana Hawaye sabo da tsakani da Allah Dan muamular da sukayi da Hunaif sonsa ya kamata,ta rasa ya akayi ta fada sonsa me zurfi Haka,yanzu ya zata yi,dama karya yake ba aurenta zaiyi ba,gashi yayi tafiyarsa ko sallama Babu,ya rabata dasu Meenal dinta gashi Bata San Ina suke ba,gashi ya dawo da ita gidan jaraba wurin su Talatu Bata aikin komai kuma,duk ranar da su Talatu suka gano ya gudu ya barta Allah kadai yasan azabar da zasu gana Mata,ga Son Hunaif Yana cinta a zuciya,da kuka ta dawo gida,Talatu suna zaune a tsakar gida Khairat ta shugo bako sallama tana Rusa kuka,Bata kula kowa ba ta shige dakinta,Talatu suka Fara kallon kallo da yaranta suna gulma kasa kasa lfy? Ita Kuma me ya sameta? Rahinatu tace oho ko fada sukayi da Mijin yace ya fasa?Zainab tace maybe ciki yayi Mata ya gudu,shewa sukayi da dariya idan tayi wari maji cewar Talatu.

Hunaif kuwa ya farfado lfy Lau Kuma yasan kowa Yana gane komai daga Sanda Khairat ta samu aiki a Company dinsa zuwa yanzu baya iya tuna komai,Haka kuma duk abinda ya faru yau da zarar yayi bacci ya tashi to ya manta shi,gashi a Haka lfy yasan kowa Banda shekarar data wuce Wanda a lokacin Khairat ta samu aiki a Company baya iya tunata,har hatsarin da yayi baya tuna komai.
Duk abinda ya faru a ranar kullum kafin Hunaif yayi bacci sai ya rubuta a littafi idan ya tashi a bacci sai ya karanta yaga me ya faru,Ummi in Banda tausayinsa ba abinda takeyi,sai da suka kwashe wata biyu cir a Germany ya Gama Shan Magunguna Dr yace suci gaba da jira watarana zai dawo normal,Amma duk abinda ya faru ko chanji suka gani su sanar Masa a waya,Hunaif shima ya tausayawa kansa halin daya Shiga,Nigeria suka tattara zasu dawo Hunaif yace shi bazai zauna a Kano ba ya Gama Gina katafaren gidansa a Abuja Haka kuwa Suka sauka a Abuja,sannan Ganin zai iya Business dinsa sai ta damka Masa komai,sannan tace ya kula duk abinda yayi Kar ya sake ya kwanta bacci bai rubuta ba.

Da Farko Hunaif baya rubutawa sai Frnds nasa suka dameshi da karban bashi Yana kwanciya bacci sai ya kasa tuna komai sai su cinye kudin,ganin Haka Ummi ta matsa Masa kullum sai yayi rubutun abinda ya faru kafin yayi bacci, yayi iya yinsa Kan ya samu ya tuna ko wani abune ya kasa,Haka Yana so ko bacci ya kwanta ya tashi yaga ya tuna wani abin Amma ko kadan Baya tunawa,sabo da Haka sai gaba daya Hunaif Rayuwarsa ta canja ya koma so silent sosai baya Magana,Bai son a takura Masa,Ya Zama Masifaffe me bacin Rai da kunci baya faraa ko kadan yanzu.

Tunda Allah yasa Mus'af ya gano shike Nan ya nacewa Zuwa Abuja wurin Hunaif ko yaushe sai ya shato kudi Wanda zasu Kai million goma sai yace Hunaif ya ranta Masa zai biya, shi Kuma Hunaif ganin Mus'af ne sai yace ka tabbatar ka biyani bashin sai suyi dariya sai shi Kuma Hunaif ganin Mus'af ne Frnd nasa sai yaki rubutawa tuna ninsa zai bashi Kuma baya biyansa shi Kuma baya iya tuna komai.

Ummi Bata da sukuni ko kadan kullum tana dawainiya da Hunaif ya zata yi taga ya warke burinta kenan.ta manta Kuma Sunan budurwarsa da zai aura tunda Hunaif sau daya ya taba fada Mata Sunan Khairat,Ga yaran tuni Yar uwarta Amina tace ita a bar Mata su sun shaku hakan yasa Ummi ta barwa Yar uwarta su Hajiya Amina kuma tana rike dasu Meenal lfy a garin Katsina da take auren wani me kudi.
Ummi da kanta ta Nemo Mus'af Kan ya fada Mata Sunan budurwar Hunaif tunda tasan abokinsa ne Dole zai sani, Mus'af yace Ummi wlh ban San Yana da wata budurwa ba Ni,kin San Hunaif da zurfin ciki ba komai yake fada ba,Ummi tace Ni na manta sunanta Amma ya fada min sau daya ko Khausar ko Karimatu tsakanin dai haka,Mus'af sai yayi zargin ko to Khairat ce a ransa,a fili sai yace Babu wata me suna Haka da Hunaif ke muamula da ita,Ummi tace wayyo Ina ma nasanta da Haka za'a daurawa Hunaif aure da ita ko zai samu kwanciyar hankali,bana Jin dadin ganin Hunaif a Haka kullum cikin kunci.
Harara Hunaif ya watsawa Ummi a boye,a fili kuma ya kwantar Mata da hankali da kalamai masu dadi,kwanansa days suna tare da Hunaif ya tafi Kano abinsa, Farouq kuwa Allah sarki mutumin kirki kullum Yana Kan hanyar Abuja duba lafiyar Hunaif,Har ganin Likita kusan idan lokaci yayi da shi ake tafiya.

Farouq ganin irin Su Musaf suna ta cutar Hunaif sai bawa Ummi Shawara kan Karawa Hunaif matakan tsaro duk inda zaije da masu take Masa baya gudun matsala,in kaga Hunaif ba karamin kyau da haduwa ya Kara ba sabo da yanda yake samun hutu da kulawa.
Su Meenal kuwa gani Ummi ta sama musu matsugunni gurin Yar uwarta ba ta damu ta dakko su ba,Ummi sai takaici takeji Bata San wacce Hunaif zai Aura ba bare ta wuce gaba ayi musu auren haka.

Ummi tana zaune watarana katsam ta tuna Sunan Budurwar da Hunaif yace zai Aura Khairat,tace kwarai sunanta Khairat.
A waya ta Nemi Musaf ko yasan wata Khairat? Musaf ya sani sarai Amma sai yace Mata Bai sani ba ko daya, Ummi ta gama bincikenta Babu labari sai ta hakura taje ta karbo su Meenal suke zamansu wajenta,tace baza ta bawa Yar uwarta ba ta fasa tunda ita tana da Yara da yawa, Koda Hunaif yaga Ummi tare da Meenal da Mohd Sam Bai sansu ba sai ma tambaya da yayi Ina ta samo Yara? Tace kawai a gidan Raino ta karbo su zata rikesu.

Khairat kuwa su Talatu sun Fara ganeta,musamman ramar da tayi kullum kuka ne aikinta,gashi an wuce 3mnths Hunaif Shuru kawai sai Talatu ta Fara kokarin dawo da halayyarsu ta Baya Kan azabtar da Khairat,Khairat tana daki a kwance zazzabi me zafi ya Kama ta,Wata kawar Talatu ce tazo daga Abuja suna Hira kawar Talatu Hajiya Abu tace Wai Talatu Ina yarinyar da kuke rikewa ne wannan kyakyawar? Talatu ta tabe Baki tare da cewa tana Nan da ta samo wani attajirin Matashi balarabe Amma munji Shuru.
Hajiya Abu tace kina zuba Mata Ido ke Kuma yarinya me kyau Haka Talatu ai jarice a wajenki,da kin min magana ai da tuni kin Zama me kudi,Talatu tace Dan manzon Allah?, Kwarai kuwa cewar Abu,ki bani ita na tafi da ita Abuja na kaita gidan wata Hajiya uwar Karuwai ce,Kinga manyan sanatoci,Yan majalisu da manyan masu fada aji ake kaiwa su suna biyan kudi,idan ta samo kudin Rabi naki ne,Uwar dakinsu tana da quarter itama yarinyar tana da Quarter.
Shewa Talatu tayi tace na yarda,Abu ta ce ai ke kawata bugu da Kari sai dai kiga Kuna zuwa Makkah,motoci sai kun zaba,to yarinyar taurin Kai gareta da kyar zata yarda,Hmm ai karya za ayi Mata kice aiki za a kaita birni tana kula da wata yarinya albashinta dubu Hamsim Kinga taji kudi sannan Bata son Zama daku Kinga zata Amince.

Hmmm Abu yarinyar Nan addini gareta ko an kaita baza tayi karuwanci ba,ke irin wannan sunfi kowa iskanci ki Bari a kaita ki gani Bayan Haka ma idan Bata son maza akwai Matan Alhazawa da suke neman Mata kyawawa suna amfani dasu Zaki Zama me kudi Ni Nan duk wata Zan karbo miki kudin na kawo Miki ko na Aiko Miki dasu wlh,ki lallaba ta Sigar dabara mu samu kudi ta hanyar wannan zukekiyar budurwar,samun irin Khairat sai an tona kowa sai ya sota.
Talatu tace an Gama Dole ma ta biki zanyi duk yadda zanyi Dole ki tafi da ita Nima na Zama me kudi,ai yanda take da kyau sai dai kiga Gomnoni na binta cewar Abu,Talatu tace shegiya sai kugu kamar na babbar mace ga kirji me kyau.

Bayan sun Gama maganganun su Khairat Bata San me suke cewa ba taji dai kawai suna ta faman shewa, washe gari Talatu har daki ta samu Khairat,ita kanta Khairat

Please Login or Register in order to submit comment