Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nidayane bakowa sainayi tajin tsoro kaga nasamu abokin zama toshikenan godiya nake bakomai Safwan nida kai aimunzama daya bawani banbanci ko daya abinda za'ayi yanzu kaje kadauko kayanka saimutafi domin nafara jin yunwa kadafa abincine kafin kafito a'a zamujedai gidan abinci toshikenan inazuwa yatafi yadauko kayansa yasa mota suna cikin tafiya Safwan yakalli Salim yace my friend da mota kazo makaranta eh Safwan Abba ne yasa akawomin ita waikarnayi wahalar abin hawa amma gaskiya yakyauta kafin su'isa gida sunbiya gidan abinci sunci sannan suka wuce gida sunshigo Safwan yaga gidan yakalli Salim my friend dole katsorata awannan gida amma gidan yayikyau my friend kanada yan uwa anan a'a Abba ne yakamamin wannan gidan gaskiya my friend Abba yana matukar sanka sosai Safwan kenan danma bakaga Ummi ba duk dayake kataba ganinta amma irin sanda Ummi takenunamin abin bazai faduba saidai Wanda yagani gaskiya my friend kana cikin gatan iyaye tare da samun kulawarsu hakane Safwan amma kaima aiba'abayaba hakane my friend iyayena suna sona kuma suna nunamin kulawa saidai bazaka hada soyayyar da dayaba da kuma da huduba Safwan Ku hudune agidanku eh kace kanada abokan fira nikuma su Ummi ne abokan firata shiya kafishakuwa dasu nikuma kaga nafi shakuwa da kannena akan iyayena domin nafi fira dasu kuma nafi sanin matsalarsu shiyasa nafi damuwa dasu banasan duk abinda zaizame masu matsala ko damuwa acikin duniyarsu kayi dai-dai

2⃣2⃣

Safwan inama ace nima inada kanwa da bazan iyafuta sanda zannuna mataba domin zansota fiye da raina zanbata kulawa ta musamman zanbata farin ciki dajin dadi a'iya rayuwata ya rufe idansa ba'abinda yake gani face Safna yafada azuciyarsa Allah kabayyanamin kanwata kacika zuciyarta da farin ciki Safwan yafahimci yashiga damuwa yadafashi my friend lafiya yabude idanunsa abin mamaki Safwan yaga hawaye afuskarsa my friend maiyake damunka bakomai Safwan saidai ina tinanin gidane lallai my friend shine harda kuka to zanbaka shawara tinwuri kacirewa zuciyarka tinanin gida idan bahakaba to inamai tabbatarma da bazaka tabayin karatuba kuma iyayenka bazasuji dadiba domin burinsu gareka shine kayi karatu kazama watatsiya dafatan kafahimceni amma kayi tinani akai wane tinani kuma Safwan bayan nasan gaskiya kake fadamin aibawani tinani dazanyi kawai zanyi amfani da shawararka domin cigabana gaskiya nayi dacan samun aboki nagari inama Allah godiya my friend kenan kaima kanada hali nagari Wanda akeso kowa zaiso yayi abota dakai domin kai mutumen kirkine suna cikin magana wayar Salim tadau ruri yaduba yaga sunan Ummi yayimurmushi yadaga tare dayin sallama sungaisa yafada mata yahadu da Safwan a makaranta kuma suna zaune agida daya haryabata Safwan suka gaisa tayi farin ciki sosai haka Safwan yasanarda Abbansa cews tare take da Salim agida daya suke zaune Abba yayi farin ciki dajin hakan domim yarigaya dayasan Salim kuma yasan iyayensa Dan haka baida tantama akansa haka sukayita zamansu cikin jindadi tamkar jini daya domin mutane da dama suna tinanin wa da kanine ganin komai atare sukeyi har kayan sawarsu wani sa'in iri daya suke sawa gasu da kokari da maida hankali ga karatu

Kaduna


Zainab da Safna sundage da karatu tukuru saboda duk kanninsu sunasan yaya Safwan yadawo gida hakan yasa sukamaida himma sosai suna karatu bawasa ko Safna da take sarkin wasa yanzu tadena domin hartafi Zainab ganin nawar yaya Safwan yadawo


By Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
2⃣5⃣
By


Gwambe


Allah Sarki haj Aisha abar tausayi dangin mijinta sunsakata agaba wai taki haihuwa kuma tahana dan uwansu yakaro Aure tobara kiji kokinaso kobakyaso saiya karo Aure kuma sai matar tahaihu saidai kihadi zuciya kimutu munafuka sunyi mata cinmutunci sosai sam yanzu sundena ganin girmanta kawai danbata da yara sunmanta da Allah sannan sunmanta data taba haihuwa akullum aduk inda suka hadu da ita hantararta sukeyi sunhanata sakat sunki subarta da damuwar da take damunta sunkara mata da wata hakan yasa damuwa tayimata yawa gurin maigidanta kawai takejin sanyi dominshi sam bayasan ganin damuwa atare da"ita wata rana tasami mijinta adakinsa tazauna kusa dashi tace Alhaji inasanyin magana dakai to inakinki Alhaji dan Allah inasan kakaro Aure dasauri yatari numfashinta Hajiya lafiya maiyasaki fadar wannan maganar bakomai Alhaji nidai ina bukatar kakaro Aure domin bazaiyuwu kazauna ba daba yakamata kayo Aure inda rabo saita haifa mana wasu yaran a'a Hajiya nibazanyi abinda zaijefa zuciyarki acikin damuwaba domin inasan kikasance acikin farin ciki nasani Alhaji wannan bazaizamo matsalaba insha Allah nidai dan Allah kakaro Aure kuma banasan abin yadau wani lokaci kaji Hajiya wai maiyake faruwane tabbas dole akwai wani abu kuma yakamata nasanshi meyeshi kifadamin naji bakomai Alhaji a'a karkifadi haka nasan kosuwaye su fa'iza ne domin suntareni da wannan zancan shine da bankulasuba sai sukazo gareki ko maisuka fadamaki dan nasan dole saisun fadi wani abu dazai bata ranki bakomai Alhaji karka damu da zancan su fa'iza domin nasan bazasu sakaba kuma bazasu hanakaba domin kannankane ammani inarokonka amatsayina na matarka kuma uwar ya'yanka dan Allah kakaro Aure to shikenan tinda kinmatsa kibarni nayi tinani akai to shikenan nabaka lokaci bayan kwana biyu tasake tintibarsa da zancan yarasa maizai fada mata yakalleta Hajiya farin cikinki shine nakaro Aure ko eh Alhaji tonaji karki damu badai Aureba to zanyi inajin indainayi shikenan ko eh shikenan to Allah yaimaki albarka Amin mijina Allah yabaka mata tagari wadda zamuyi zaman lafiya da lumana Amin Hajiya yaje yafara naiman Aure su fa'iza labari yakai garesu sai murna suke tamkar baitabayin Aureba idan suka hadu da Haj Aisha saisuyita yimata habaici basusan cewar itace jigonyin Auranba fa'iza tace to Aisha bako Hajiya danrashin mutunci dakiso da karkiso yayanmudai zaikaro Aure zaidauko mana saban jini wadda zatazo tacika mana gida da 'ya'ya bakeba dakike cika mana gida da kashiba Haj Aisha takalleta fa'iza kenan dadin abindai kafin tahaifa ninafara haifawa haihuwa kuma dakiketa magana akanta dadinta natabayi balantana kikirani da juya dan haka nafi karfin kori agurinki kuma inda yarana suka tafi hanyace shararriya kowa saiyaje dan haka banida wata matsala ko tashin hankali game da Auran da yayanku zaiyi wannan matsalarkuce batawaba tana gama maganarta tatafi dakinta tabarmasu falo sai arerewa suke tamkar wasu yaran 'yan mata


2⃣6⃣


Bayan kwana biyu Haj Aisha tana zaune afalo maigidanta yayi sallama yashigo tazo tatareshi da fari'arta yazauna takawo masa ruwa maisanyi yasha to yagajiyar tafiya lafiya qlau gajiya tabi jiki toya shirye-shirye Hajiya kenan harkinfini zumudin bikin nan toba doleba za'akawomin yar kanwa aidole nayi murna to Allah yahade kanku yasa abokiyar zamace ba kishiyaba Amin Alhaji anshiga satin biki ankawo kayan Amarya anyi Jere gefenta daban bama kusa suke da junaba sunada yar tazara atsakaninsu ranar biki tayikwalliya tayi kyau sosai tamkar ba mijinta akedaurama Aureba fuskarta cike da annuri farin ciki yasauka afuskarta yan uwanta sunjidadin ganinta acikin farin ciki sosai su kuwa su fa'iza sai habaice-habaice suke tayi tamkar bataji sunayiba taba banza ajiyarsu tamkar basu gidan taci gaba da hidimarta tare da mutananta da abokan arziki da dare aka kawo Amarya dakinta bayan kowa yawatse Alh mansoor yashigo yashigo dakinta yasameta azaune bakin gado yazauna kusa da ita sannu da kokari yafama da jama'a Alhamdulillah aikafini fama da jama'a takalli agogo taga karfe tara 09:00pm katashi kaje gurin Amaryarka karta rufema kofa idan tarufe sai nadawo nakwana anan tab bako adakinaba to adakinwa inada inda yafinan ne tayi murmushi to tashi muje narakaka ko to shikenan tinda kinmatsamin keko dan kishinnan bakyayi sai dariyarsa take au dariyatama kikeko to yihakuri tarakashi harbakin kofa tayimasa sallama tatafi yayi sallama yashigo yasameta zaune afalo yazo yazauna inda take yakira sunanta Jamila tadago kai takalleshi tashi kije kiyo alwala tace inada alwalata toshikenan tashi muyi sallah ta amsa da to tamike sunyi sallah yayi addu'a sosai game da zamansu bayan sunci kaza da lemu sunje sunkwanta Hajiya Aisha tadawo dakinta takwanta taga gadonta yayimata fadi tinda tayi Aure da Alh mansoor bata taba barci batare dashiba sai ayau yau zaikwana tare da wata abin yatsaya mata azuciya to yazatayi tatashi tayo alwala tayi sallah raka'a biyu tayi addu'a sosai sannan takoma takwanta

Washe gari yahadasu yayimasu nasiha sosai yakuma nunawa Jamila cewa Haj Aisha tanada matukar muhimmanci agurinsa dan haka tabita sauda kafa tayimata biyayya koba komai ta girmemata ashekaru kuma ta girmemata a gidan miji dan haka yakamata tabata girmanta ta'amsa da to insha Allah zankasance maiyin biyayya agareta kamar yanda kabukata Haj Aisha taji dadi sosai yanda mijinta yanuna tanada muhimmanci agurinsa hakama tayaba da hankalin Jamila sosai kafin wadancan sarakan zuga da munafurci zusata agaba watosu fa'iza Alh mansoor yayi addu'a sosai dafatan zaman lafiya sun'amsa da Amin tare da shafawa


By Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
2⃣7⃣
By

Fauziya Usman

Makaranta


Salim yashigo yasami Safwan yanata waya da kannensa abin yabirgeshi saiyaji inama ace kanwarsa tana tare dashi da yabata kulawarda bawani yaya dazaibawa kanwarsa lokaci daya yashiga tinani yayinda damuwa takawo masa ziyarar bazata bayan Safwan yakarasa wayarsa yadawo da kallonsa garesa kallo daya yamasa yafahimci baya cikin walwala yatashi zaune yana tambayarsa my friend lafiya maike damunka ne bakomai kawai ina tinanin gidane tomaiyasa zaka damu bayan kasan munkusa hutu zaka koma gida kusa da Ummi da Abba zakaci gaba da rayuwarka ta farin ciki sabanin nan kullum kana cikin tinani duk da cewa su Ummi suna zuwa amma sam wannan baya gamsar dakai kafisan kakasance atare dasu akoda yaushe kaga nikuma kannena nayi marmarin gani domin suna cikin raina koyaushe ina tinaninsu Abba amma nafi tinaninsu Zainab yayi murmushi Safwan kenan inama ace nima inada kanwa da tasha lele da gata dana bata kulawa ta musamman fiye dani kaina saidai nikadaine banda kanwa yayinda yake magana fuskarsa da zuciyarsa cike suke da damuwa Safwan sai kallonsa yake yayi ajiyar zuciya kaga my friend baikamata kasa wannan arankaba kaga gashi lokaci daya kasawa kanka damuwa da bacin rai hakan baidaceba dan Allah kadena nasan iyayenka suna matukar farin ciki da samunka domin kaidaya ne tamkar da dubu wannan ne dalilin da yasa suke matukar sanka domin kakasance abin alfahari agaresu dan haka kakula da iyayenka kadena damuwa da rashin kanwa idan da rabo wata rana zakasamu amma dan Allah kadena damun kanka da abinda bakada maganinsa kajiko abokina eh naji kuma nagode zanyi amfani da abinda kafadamin yauwa domin inasan naganka acikin farin ciki saboda kyau yakeyima

Kaduna

Su Zainab sai murna sukeyi domin sunsami labarin Safwan zaidawo farin ciki agurin Safna abin sai Wanda yagani ranar da zaidawo bataso zuwa school ba to amma yazatayi domin tasan idan Safwan yadawo yasami labarin yau bataje makaranta ba to tabbas saisun bata itakuma batasan hakan wannan dalilin ne yasata zuwa school kuma karin takaicinta shine Zainab bazuwa zatayiba tinda takare itakadai zata hakadai tahakura tayi tafiyarta bayanda ta'iya misalin karfe sha biyu 12:00pm Safwan yashigo gida da sallamarsa Zainab tazo da gudunta tatareshi tana yimasa sannu da zuwa bayan yazauna yagaisa dasu Umma yakalli Zainab yana tambayarta ina Safna tana school yaya Safwan yayi murmushi Allah sarki kanwata ashe takara hankali tinda har tatafi makaranta yau Abba yace aisam bata wasa da karatu badan komaiba saidanka koyaushe tananan akan karatu Allah sarki Safna yafada yana murmushi lokaci daya yatashi Umna tace ina kuma zaka bakaci komaiba Umma zanje inwatsa ruwane wallahi duk agajiye nake to afito lafiya Allah yasa Amin Umma yatashi yatafi abinsa karfe daya da minti goma 01:10pm Safna tashigo gida fuskarta cike da annuri tana shigowa tayi karo da Zainab Zainab takalleta Safna kindawo eh Aunty Zainab

By Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
2⃣8⃣
By

Fauziya Usman


Ina yaya Safwan yatafi yashirya yanzu kema kitafi kishirya kafinnan yafito kinga sai kugaisa domin nasan halinki da dan banzar surutu yanzu idan kika hadu dashi wankanma bazakiyiba gaskiyarki Aunty Zainab kinsan komai game dani lallai kinyimin farin sani to natafi nashirya to afito lafiya tatafi tana dariya bayan tashirya tafito tasamesu afalo taje inda yake tagaishesa ranta fari kal dakaganta kasan tana cikin farin ciki ga fuskarta cike da annuri Abba da Umma sai kallonta suke Safna wannan irin farin ciki haka Abba ina farin cikine abisa ganin yaya Safwan ne nafajima sosai bangansaba wannan shine yayinda Safwan yaketa kallonta yaji tabirgeshi Safna da fatan kina lafiya ya school lafiya qlau yaya Safwan yahanya yagajiyar tafiya Alhamdulillah komai is normal tamika masa wats yar leda yaya Safwan gawannan ya amsa yana murmushi yabuda ledar dan ganin miye aciki yaga chocolate ne murmushinsa yakaru yayi dariya Safna wannan duk ni kikaba eh yaya Safwan to inagodiya kinji kanwata sai dariya take Umma tace Safna ni ina nawa chocolate din tayi dariya babu Umma nifa yaya Safwan ne kawai nasiyowa Safna yanzu bakisiyomin ba kenan kinfisan Safwan akaina a'a Abba kuyi hakuri gobe zansiyo maku naku chocolate din Auntu Zainab kema zansiyo maki to Safna inagodiya suna cikin firarsu saiga indo tafito bayan tagaisa da Safwan tayimasa sannu da zuwa tace Hajiya ankammala komai to indo jeki inazuwa ta'amsa da to tayi tafiyarta Umma tabi bayanta bayan wani lokaci tadawo tace to kutaso bismillarku abinci yayi ready suntashi anje gurin cin abinci Umma tazuba makowa sannan tazauna ana cikin cin abinci Safwan yalura da Safna baci takeyiba wasa kawai takeyi amma da zarar sukayi ido biyu saita saka cokali abakinta kamar tanaci sunyi hakan sau biyu akaro na uku yakira sunanta safna kici abinci kamar yanda kikaga kowa yanaci idan kuma bahakaba zanbata dake kuma yanzunnan zantashi nakoma inda nafito bazaki sake ganinaba tinda bakya sancin abinci kumani kinsan banasan hakan dan Allah kayihakuri yaya Safwan karka bata dani kuma karka tafi zanci abinci sosai amma dan Allah kadena cewa zaka tafi wallahi banasan katafi tonaji amma kici abinci tukunna to nanfa tafaracin abinci abin yabawa su Abba mamaki matuka yau Safna ce kecin abinci da kanta kuma babu hawaye afuskarta lallai tanayi da Safwan sosai taci abinci sosai yakalleta lallai Safna zamu shirya dake idan harkinacin abinci haka domin banasan naga bakyacin abinci yaya Safwan daga yanzu zanrika cin'abinci sosai kamar haka yauwa kanwata Yar albarka su Umma sunkoma falo sunbarsu saboda Safna ce karshen cin'abinci Zainab takalleta duk mamakinta yakamata tace Safna dama ashe zaki iyacin abinci haka amma kike hana kanki a'a Aunty Zainab nacine saboda yaya Safwan domin banasan yabata dani sannan kuma banasan yatafi shiyasa naci Safna kenan kinasan yaya Safwan yarika zama agida ko eh Aunty Zainab suna cikin firarsu saiga Ammar yazo yasamesu alokacin yana dan shekara biyu Safwan yadaukeshi ya'azashi kan tebur nanfa yace aiki gamaiyinka yadinka barna da kayan abinci duk yabata gurin Zainab tadaukeshi tadireshi akasa sannan tagyara gurin


By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
2⃣9⃣
By

Fauziya Usman

Kano

Ummi saishiri takeyi domin dawowar Salim saboda girke-girke yasa batabi Abba ba yayin zuwa daukoshi sun kammala aikinsu ita da Larai tatafi domin tashirya saboda batasan su iso bata shiryaba tayi nasarar karasa shirinta kafin su iso saukarta keda wuya falo saigasu sun iso dasaurinta tazo tataresu ciiin murna da dauki Salim sai farin ciki yake abisa ganin Ummi acikin farin ciki bayan sunzauna tazauna kusa da Salim tanayimasa sannu da zuwa ya'ansa sannan yagaisheta ta'amsa tanata fari'a Abba sai kallonta yake yalura farin cikin da take ciki abin bazai misaltuba yayi murmushi sai lokacin yayi magana Hajiya yau tinda Salim yadawo shikenan bazakiyi tawaba ko toshikenan aizai koma zaki dawo gareni lokacin nikuma zanrama tayi dariya shima Salim dariyarsu yake haba Alhaji kabari nakare da yarona sai nadawo gareka a'a yanzufa ni ainagama magana Salim yamike inakuma zaka Ummi inasan naje nadan watsa ruwa saboda gajiya toshikenan afito lafiya to Ummina saina fito yayi tafiyarsa yashiga dakinsa yadan kwanta akan kujera shikam yanajin dadin zama dasu Ummi sannan zaman Abba da Ummi yana birgeshi Sam basa fada da junansu basa daukar zafi arayuwarsu sam basusan bacin raiba kullum suna cikin nishadi da farin ciki tare dajin dadi shi abin yana birgeshi lokaci daya yatashi yaje yayi wanka yafito yazo yashirya yadauki wayarsa yakira layin Safwan bayan sungaisa yatambayesa yagajiyar tafiya my friend gajiya tabi jiki yasu Ummi da fatan suna lafiya lafiyarsu qlau inasu Zainab da kuma babbar kanwa duk sunanan qlau suna gaisheka ina amsawa sundan jima suna magana daga bisani sukayi sallama bayan yakarasa wayar yafito yadawo falo saidai yatarar da babu kowa kaitsaye sashen Larai yawuce yashiga tare dayin sallama cikin fari'arta danuna jindadinta tazo tanayimasa sannu da zuwa yagaisheta cikin girmamawa ita tanajin dadin irin yanda yake girmamata yana bata girmanta sosai Salim ya makaranta gidanmu sai yayi badadi lokacin da bakanan yanzu komai zaidawo dai-dai tinda kadawo yayi dariya Aunty Larai kenan ainaga hutu naxo kuma komawa zanyi idan yakare to kafinnan dai aimunganka ko eh hakane kam yazauna sunata fira yanajin dadin zance da ita domin yanajin dadin zancanta Ummi taga yajima baifitoba taje dakinsa dan ganin maiyakeyi tasamu bayanan tabuga kofar toilet nanma shiru tadawo falo Abba yaganta kamar maineman wani abu yace Hajiya lafiya wallahi Salim nake nema baya dakinsa kuma baya toilet to ko yafitane amma to idan yafita inazaya nasan baya fita saiyafada to yana ina Abba kallonta yake kinga kindubashi dakin Larai a'a tokije kigani mebi yanacan kacire mebi domin nasan yanacan kasan wallahi ni harna manta da Larai agidannan aida tindazu naje dakinta dama kasan idan yana fira da ita sam baisan tashi

By Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
3⃣0⃣
By

Fauziya Usman

Tana zuwa tasamesu sunata fira cikin nishadi sai dariya suke Larai tace Hajiya kinshigo eh Larai takalli Salim dama kananan kasani inata nemanka tindazu yayi murmushi nema kuma Ummi eh mana naje dakinka bakanan toilet bakanan falo bakanan wallahi nashiga rudani Allah sarki Ummina kuyi hakuri kiyafeni sanda zanso alokacin falo bakowa shiyasa banfadaba bakomai Salim yanzu tashi muje kaci abinci kaji to Ummi yatashi suntafi sunje sunci abinci Abba ya tambayesa Salim waikayi waya da Safwan eh Abba munyi waya dashi toya isa gida lafiya ko eh lafiya qlau to madallah Allah yahutar da gajiya Amin Abba am Salim na'am Ummi zuwa jibi zamuyi tafiya zamuje sokoto gidan Aunty binta zamu kwana biyu acan sai kashirya kajiko to Ummi zankasance acikin shiri to Allah yaimaka albarka Amin Ummina yatashi yace Ummi zantafi nadan kwanta kafin lokacin sallah yayi to Salim afito lafiya Abba yakira sunansa Salim Ummi dai kake fadama bandani ko sorry Abbana zanje nakwanta toshikenan afito lafiya to Abba yatafi abinsa yayinda suka bishi da kallo gaskiya Alhaji mukam munyi sa'ar samun yaro irin Salim ina matukarsan zama dashi idan muna atare banasan yatafi idan ina tare dashi farin ciki yake kamani burinma idan yakirani da Ummina wallahi nikadaice nasan dadin da nakeji araina Hajiya kenan nikaina inajin hakan azuciyata wallahi Hajiya Allah kadai yasan alkhairin da yaron nan yake tare dashi inamai addu'ar Allah ya albarkaci rayuwarsa Amin Alhaji washe gari da yamma sunfita siyayya domin dasafe ne zasu tafi sokoto bayan sundawo sunkarasa shirinsu suntafi sunkwanta saboda tashi dauwuri sukarasa abinda zasuyi Ummi takira Larai tafada mata cewa zasuje sokoto dan haka takula da gida yanda yakamata ta'amsa da to tayimasu rakiya har bakin mota sunkama suntafi sun'isa sokoto cikin koshin lafiya Hajiya binta sai murna takeyi tatarbesu sunzauna Ummi tace Aunty binta ina Nafisa wallahi tafita amma nasan yanzu tana hanyar dawowa Salim ya makaranta lafiya qlau Aunty to Allah yataimaka yabada sa'a Amin suna cikin firarsu saiga Nafisa tashigo Nafisa andawo eh mama Luba kawu inawuninku tagaishesu sun'amsa cikin jindadi yaya Salim ya school kwanakin baya natafi lokacin kana school sainaji gidan wani iri badadi saboda bakanan haba eh mana to yanzu nadawo yaushe zakizo zanzo insha Allah to dahaka ai idan zamu koma saiki bimu mutafi tare ko Ummi eh Salim haka za'ayi insha Allah kobazakiba zanje mana yaya Salim Aunty tace kuzo kuci abinci to suntashi sunje sunci abinci washe garin ranar sunfita domin ziyarar yan uwa da abokan arziki cikin tafiyarsu harda Nafisa domin tasaba da Salim sosai hakama yana birgeta saboda yakasance mutumin kirkine halayansa nagari kwanansu biyu a sokoto suka dawo gida tare suke da Nafisa sun'iso gida cikin koshin lafiya dajin dadi Larai tataresu cikin farin ciki tanayimasu sannu da zuwa takawo masu ruwa maisanyi tabasu lemu mai sanyi sannan tashirya masu abinci kan tebur sannan takoma sashenta bayan sunhuta sunsha ruwa da lemu

By Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
3⃣1⃣
By

Fauziya Usman


Suntafi sunwatsa ruwa domin surage gajiya Nafisa tafito tasami su Ummi afalo tazauna kamar mintuna biyar amma Salim baifitoba sai waiwaye take Ummi talura da ita saidai batai mata maganaba Nafisa takasa hakura tace Ummi yaya Salim fa ko yafitane a'a yana sama baifitoba tamike tsaye tayi dakinsa tabuga kofa daga ciki yace ina zuwa yazo yabude yaganta abakin kofa Nafisa kece eh yaya Salim banganka afaloba shiyasa nazo nagani ko lafiya yayi murmushi lafiya qlau Nafisa kawai nadan kwantane ina hutawa shigo mana tashigo tazauna yaya Salim kagaji dayawa a'a Nafisa kawaidai nasami kaina da inasan nakwanta amma badan nagajiba a'a yaya Salim dole akwai gajiya atare dakai dirabin fa kayi tindaga sokoto har Kano kagako dole akwai gajiya ko baka fadaba nima da nake azaune nagaji balantana kai dakake tuki yanzu bara natafi nabarka kahuta a'a kizauna mana ai ahakanma hutawar nake suna cikin firarsu saiga Ummi taturo kofa tashigo tasamesu sunata firarsu cikin nishadi sannunku da hutawa yauwa Ummina to kuyihakuri kozo muci abinci kunji to Ummi suntashi sunfito tare sunwuce gurin cin'abinci sunci abin cinsu cikin farin ciki da walwala bayan sunkarasa cin'abinci Salim da Nafisa suntafi sashen Larai dominyin fira da ita sunsameta zaune adakinta tana ganinsu tatashi yayinda fuskarta take cike da walwala Aunty Larai ko barci kike a'a Salim yagajiyar tafiya gajiya tabi jiki to Allah yahutar da gajiya Amin ya Allah Nafisa yasu Auntu binta suna lafiya sunce agaisheki to ina amsawa suncigaba da firatsu

Kaduna

Zainab tashiga secondary j.s.s one yayinda Safna take primary five Safna tashaku sosai da Safwan shiyasa yanzu sam tadena wasa ko rashinji da surutu da tayi wani abin sai acemata Safwan zaitafi ita kuma sam batasan abinda zaisa tayinisa da Safwan shikansa Safwan yanasan ganin Safna atare dashi abu daya yake hadashi da Safna rashin cin'abinci domin komai suke shiri ko suke cikin farin ciki to da zarar akazo gurin cin'abinci to sai sunsami matsala wani lokaci harkuka takeyi itadai tafi dasan kayan zaki idan tasameso to batsbukatar abinci haka haka sukaci gaba da karatunsu lokacin da yan primary six zasu kare malamin su Safna yabata katarda tace takaima Abbanta takawo masa yabuda yaduba malamin yace maizai hana yabiyama Safna kudin exam takare tare da yan primary six tinda tanada kokari washe gari yaje makarantar da kansa yasami malamin sunyi magana sosai dashi malamin ya kuma yarda da tazana exam din tare da yan primary six yabashi kudin da akebukata sannan yatafi haka kuwa akai Safna tarubuta exam daga primary five takare tawuce secondary makarantar da Zainab take Zainab tana j.s.s. two ita kuma tana j.s.s. one alokacin Ammar yanada shekara uku shima ansakashi amakaranta naziri one akasashi tinbaya yarda yana kuka harya hakura yamika wuya yadena kuka da fitina fanin islamiyya shima basa wasa domin sunyi nisa sosai acikin hardarsu abin gwanin Sha'awa

By Fauziya

Please Login or Register in order to submit comment