Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
4⃣6⃣
By

Fauziya Usman

Takarasa shirinta tsab cikin wasu riga da wando kayan sunyi mata kyau sosai Zainab takalleta wow Safna kinganki kuwa wallahi kinyi matukaryin kyau ko Aunty Zainab sosaima kuwa duba madubi kigani a'a basai naduba ba ganinki yawadatar dani nagode sosai bakomai tonafita saikin fito domin bazan'iya jirankiba to Aunty Zainab nima ganinan fitowa to afito lafiya Allah yasa Amin tafita tabarta tasauko saidai bakowa afalo baifi mintuna uku da fitowartaba saiga Safwan yasauko yaya kafito eh duk ina mutanan gidan su Umma dai inajin ko sunje suwatsa ruwane to Safna fa tanacan tana aikin kwalliya Zainab ammafa kinyikyau sosai nagode yayana kai wannan kwalliyar tayi yawa barana dubota yatashi domin tafiya dubata saigata tafito sunyi ido biyu da juna yasakar mata na mujiya yanata kallonta harta sauko tana murmushi shima murmushin yakeyi sai lokacin yakoma yazauna yace kanwata kece kika girma haka kinga yanda kikayikyau kuwa kai nayi sa'ar kanne kyawawa gaskiya sukuma sai dariyarsa suke Safna tace yaya Safwan kenan wallahi kagodewa Allah domin damunyi daya daga cikin kyawanka to dabanan kusaba kaikyak kyawane na gasken-gaske samun irinka ko acikin kyawawa to sai antona kuma sai anje danisa amma banan kusaba Safna kenan yayana yahanya yagajiyar tafiya to Alhamdulillah gajiya tabi jiki to masha Allah ina yaya Salim yana nan qlau shima yana hanyar zuwa gida to Allah yakaishi lafiya Amin ya Allah Aunty Zainab inasu Umma suna ciki inatinanin ko sunshiga suyi wankane eh aidole ankwaso gajiya bayan wani lokaci su Abba sunfito Safna tataresu da murmushi tayi masu sannu da zuwa sun'amsa cikin jindadi daganan sukatashi sun'isa gurin cin'abinci Safwan yakalli Safna yace kanwata dafatandai yanzu kinacin abinci tayi murmushi wanda yakara fitar dakyan fuskarta eh yayana inaci sosaima da sauri Zainab takalleta tace to'aizamu gani dama hausawa sunce gani yakoriji haba Aunty Zainab maikikeso kifadane a'a aibanfadi komaiba to kudena wannan surutun kuci abinci to Umma nansuka faracin abinci Safna ko tabasu mamaki domin taci abinci sosai Safwan yakalleta gaskiya kanwata kinyi kokari sosai yaya Safwan kenan aini yanzu sam bana wasa dacin abinci yayinda Zainab taketa kallonta domin mamakinta yagama kamata Aunty Zainab maiyasa kike kallona haka kamar kina mamakina a'a Safna sam bahaka bane kinji to shikenan sundawo falo sunata fira bayan wani lokaci Abba da Umma suntashi sunyi masu sallama zasuje sukwanta sabida gajiya to Abba saida safe Umma saida safe to Allah yabamu alkhairi Amin ya Allah sukuma suncigaba da firarsu saida dare yayi sosai Safna tace yaya Safwan yakatama kaje kakwanta kahuta to shikenan kanwata suntashi gaba dayansu suntafi sunkwanta Safwan yakwanta amma sam yakidaukarsa sai ganin babynsa yakeyi a idansa yayinda zuciyarsa take cike da farin ciki da fatan Allah yasa yasamets domin shidai yana matukar santa da kaunarta gata tana Burgess shiyasa komai yake ita yake gani a idansa da wannan tinanin barci yadaukesa

Washe gari bayan sunyi sallar asuba Zainab tatashi tafara shirinta nazuwa school yayinda Safna takoma takwanta kan gado domin ita batada school anata shirin xuwanta makarantar Zainab tagama shirinta tsab takalli Safna toni natafi to Aunty Zainab Allah yakiyaye yabada sa'a Amin saina dawo adawo lafiya Allah yasa Amin tafita tayi tafiyarta tasami Umma tana shirma Ammar domin zuwa school Zainab harki fito eh Umma to Allah yabada sa'a Amin Ammar mutafi ko bayan fitar Zainab Safna nakwance sai taji ringing din wayar Zainab da sauri tadauko wayar tafito saidai tasamu tafita Umma takalleta dasauri Safna lafiya kinfito afirgice Umma Aunty Zainab ce tamanta da wayarta lokacinne Safwan yasauko yauwa yaya Safwan dan Allah mikawa Aunty Zainab

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
4⃣7⃣
By

Fauziya Usma


da bazan'iya fita ahakaba shikuwa sai kallonta yake yakarba batare da yace da ita komaiba yasamu suna kokarin fita yatsayar dasu yabata sungaisa sannan yadawo yasamu ita daya afalo tayi kwance kan gukera daga ita sai rigar barci wadda tsayinta iya gwaiwa hakama rigar tayi kwance ajikinta yaya Safwan kadawo eh nadawo ina Umma takoma takwanta dama shirin Ammar ne yatasheta kasanshi yafisan Umma tashirya masa akanni ko Aunty Zainab sai lokacin yazauna yakalleta tsab yace Safna kinga shigar datake jikinki kuwa kuma kinyi kwance afalo yanzufa kinwuce matakin yarinya kingirma yakamata kidena fitowa da irin wannan shigar kinji to yayana zandena ko yanzu wayar Aunty Zainab ce tafito dani da yanzu inacan ina barcina tinda ba school shikenan yanxu bakida wani aiki sai barci da hutu ko a'a yaya Safwan ai inazuwa islamiyya to maza kitashi kije kicanza wannan shigartaki kinjiko to yayana tatashi tayi tafiyarta shima tashi yayi yatafi dakinsa saboda bazai iya zama shidayaba afalo tana shiga daki kaitsaye toilet tafada tayo wanka tafito tashirya cikin kananan kaya riga da wando ta gyara gashin kanta tayi kwalliya maikyan gaske tafito batagansa afaloba hakan tasa taje dakinsa tabuga kofar amma shiru taturo ahankali tashigo tasamesa akwance idansa arufe tayi zaune kusa dashi tanata kallonsa tayi murmushi tafada azuciyarta lallai yayana kyak kyawane sosai saitaji yabirgeta tinlokacin datashigo yaji shigowarta saidai yaki magana ne saboda wani abu da yake tinani tajuya zata tafi yariko hannunta tajuyo sunyi ido biyu yace inazaki ainaga kana barci ne shiyasa zantafi to waya fadamaki barci nake ganin nashigo bakayi maganaba kuma idanuwanka arufe shiya tabbatarmin da barci kake a'a ni ba barci nakeba to dayan biyu idan ba barci kakeba to tabbas tinani kake tinaninme kakeyi haka yaya Safwan bakomai Safna saidai ina tinanin yaushe zankara haduwa da my friend yayana kenan wannan ai ba'abin damuwa bane kana kusa dashi sosai zaku'iya kaiwa junanku ziyara aduk lokacin da kuka tashi dan haka kadena tinani kaji eh zandena amma gaskiya yaya Safwan naji mamaki da kacemin tinanin yaya Salim kake domin kyak kyawan saurayi irinka kuma hadadde saidai asamesa yana tinanin budurwarsa badai abokinsa ba amma saigashi kai ansameka kodayake duk namiji irinka yaji da kansa gurin jawa 'yan mata aji kuma dole subi domin samun irinka yana da matukar wuya awannan zamanin Safna kenan kincika kodani dayawa kina fasamin kai da yawa harkisa naji araina niwani ne dariya takeyi sosai yayana kenan aidole nakodaka domin kacancanci hakan to shikenan amma kisani kema kyak kyawace sosai inagodiya yayana to tashi mukoma falo ko ta mutafi sundawo falo sunzauna basu wani jimaba saigasu Abba sunfito sungaisa dasu sannan sunje gurin cin'abinci Abba yace yanaganku kubiyu ina Zainab tatafi school ok aikema kinkusa fara zuwa insha Allah to Allah yakaimu Abba Amin Safna kina murna ko eh Abba to shikenan lokaci nazuwa nan suka fara cin'abinci harduka gama bayan sunkarasa cin'abinci sundawo falo Abba yace Safwan tinda kakammala karatunka yakamata kafara aiki akamfanina koya kagani eh Abba hakama dai-daine saidai ni gaskiya nafisan sanayi N.Y.S.T na sannan nafara aiki toshikenan Allah yanuna mana Amin Abbana to Hajiya nizanfita to Allah yakiyaye adawo lafiya Allah yasa Amin Abba Allah yakiyaye Amin Safna Abba Allah yatsare Amin Safwan saina dawo yafita yayi tafiyarsa abinsa indo tafito ta tambayi Umma abinda za'a girka Umma tace to indo mutafi kicin din nagani suntashi suntafi

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
4⃣9⃣
By

Fauziya Usman


Satinsu daya da dawowa Salim yakira Nafisa yace nafara gajiya da zancanki nacewa kinanan tafe yakamata kicanjashi a'a yaya Salim karkayi fushi dan Allah inanan tafe acikin satinnan toshikenan naji amma idan satinnan yakare bakizoba to munbata kuma bazamu shiryaba kinyarda insha Allah hakanma bazata faruba to shikenan saikinzo sunyi sallama ya'aje wayarsa Nafisa tasamu mahaifiyarta tace Aunty dan Allah inasan zuwa kano nafada maki amma bakice dani komaiba Nafisa kenan maikikesan nace dake bayan kinrainani sam bakyajin maganata tinyaushe nake fadamaki magana daya amma sam kinkiji sai yanzu kuma zaki bijiromin da bukatarki to baki'isaba ba inda zaki ko cikin garin sokoto balantana kikai Kano Aunty dan Allah kiyihakuri wallahi zanrikajin maganarki amma dan Allah karki hanani zuwa Kano kinji Aunty Nafisa kinsanni yanxu banda wani buri araina wanda yawuce naga na'Aurar dake amma duk wanda yazo yana sanki korarsa kike maiyasa kike hakane maiyasa bakyasan kiga nasauke nauyin dayake kaina haba Nafisa kefa barayinya bace yakamata kinatsu kiyiwa kanki fada kekanki kinsan da'ace mahaifinki na raye da kinjima adakin mijinki kinajin yanda dangin mahaifinki suke fadamin magana akan cewa naki Aurar dake nabarki saiyawo kike ahanya harsuna cewa kinfi karfina ko kinasan haka tacigaba da faruwane Nafisa a'a Aunty nafahimci damuwarki kuma zanyi kokari naga nafidda miji nayi Aure insha Allah kinga Nafisa idanma keyakasance bakida zabin kanki toni inadashi zanzaba maki a'a Aunty kibani dan lokaci namaki alkawarin zanfito da mijin Aure to Allah yasa Amin Aunty to Aunty yabatun tafiyata Kano Nafisa waimai akeyi akano dakikesan kitafi dama kinbar zancannan domin ba'inda zaki tashiga yimata magiya amma taki barinta tamatashi tabar mata gurin Nafisa tatashi tayi dakinta tafada kangado tana maifadin nashiga ukuna yazanyi da alkawarin danayiwa yaya Salim nacewa inanan tafe kuma gasharadin daya shardan taman gashi kuma Aunty tahanani tafiya yazanyi yanzu miye mafita lokaci daya dabara tazo mata takira layin Ummi tafada mata komai Ummi tace karki damu Nafisa zankira Aunty zamuyi magana da ita to Ummi amma karki fadamata nakiraki karkidamu to shikenan Ummi nagode dahaka sukayi sallama haka kuwa akayi Ummi takira Aunty bayan sungaisa tace Aunty wai ina Nafisa kwana biyu najita shiru bayan tafadamin tananan tafe amma sai shiru nakeji Haj Luba kenan wallahi tanasan zuwa Kano sosai tayimin maganar nicedai nahanata Aunty maiyasa saboda sam batajin maganata nayi-nayi da ita akan tafidda mijin Aure amma taki narasa maitake nufi ni inagama zanzaba mata dakaina kotanaso ko bataso saidai kawai taji zancan daurin Aure tinda abin nata yayi yawa a'a Aunty bahaka za'ayiba yanzu kiyi hakuri kituromin ita inasan nayi magana da ita insha Allah za'asamu mafita to shikenan insha Allah zanturota zuwa jibi to Aunty Allah yakaimu Amin dan Allah Aunty kicire damuwa aranki kinji to shikenan Allah yashige manager gaba yayimana jagora Amin Aunty saina ganta to saitazo dahaka sukayi sallama
Washe gari
Aunty tafito saidai bataga Nafisa ba tayi murmushi tawuce dakinta tasameta akwance taje kusa da ita tazauna tace haba Nafisa maiyasa kike hakane dan Allah dan kawai nace bazakije kanoba saiki dauki fishi dani hakan tasa yau ko fitowa bakiba a'a Aunty yanzufa nake kokarin fita naje nagaisheki saigaki kinshigo ni bana fishi dake Auntyna

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
4⃣8⃣
By

Fauziya Usman

Kano


Su Ummi sun'iso gida lafiya Larai saimurna take tana yimasu sannu da zuwa sunshigo sundan huwa Larai takawo masu ruwa maisanyi da lemu Ummi tayimata godiya sannan suka gaisa tayiwa Salim fatan alkhairi yajidadi sosai haka su Ummi bayan sundansha ruwa da lemu suntashi kowa yawuce dakinsa somin yawatsa ruwa saboda gajiya Salim yana shiga dakinsa kaitsaye yawuce toilet yayo wanka tare da dauro alwala yashirya cikin kananan kaya nashan iska sannan yayi sallah yana cikin sallah wayarsa tafara ringing bayan ya'idar yayi azkar dinsa sannan yadauko wayar danganin Wanda yakirasa yanadubawa yaga number Nafisa yayi murmushi sannan yakirata tana dagawa tayi sallama ya'amsa tagaishesa yaya Salim ya hanya Alhamdulillah aimunkaraso harnayi wanka koda kika kirani ina sallah ne ok kunjima da sauka kenan eh to basosaiba masha Allah to yagajiyar tafiya gajiya tabi jiki yasu Ummi suna lafiya baki kiratabane eh to kirata kiyimata sannu da zuwa aizankirata yanzu da mungama waya yauwa Nafisa kince idan nadawo zakizo Kano to yaushe zakizo karka damu zanshigi nan badajimawa ba a'a nidai nafisan kisamin rana to kabari saina shirya saina fadama to shikenan amma karkisa lokaci mai tsayi kinji aibazansaba domin inasan nazo sosai to shikenan nikuma zanyita saka ido tindaga yau har izuwa lokacin da zakishigo toyayikyau yauwa inagaida Aunty dan Allah zataji yanzu maza kikira Ummi to yayana zankirata yanzunnan insha Allah to shikenan sai anjima tosai anjima dahaka sukayi sallama yana ajiye wayar takira layin Ummi sungaisa tayimata sannu da zuwa da kuma fatan alkhairi akan karewar Salim Ummi tajidadi sosai aranta sunjima suna magana daga bisani kuma sukayi sallama Larai tashirya masu abincinsu akan tebur sannan takoma bangareta Ummi da Abba sunfito sunsamu falo bakowa tace badai baifitoba tomai yakeyi kodai yana dakin Larai bara nadubashi acan tatafi dakin Larai saidai bata sameshi acanba nan Larai tafada mata tashirya komai na abincinsu akan tebur to shikenan Larai mungode sannu da aiki yauwa Hajiya Allah yahutar da gajiya ta'amsa da Amin tafito tayi tafiyarta tadawo Abba yace ina Salim din bayacan inaga yana dakinsa bara nakirasa yazo muci abinci ko tokirashi ta tafi Abba yabita da kallo Hajiya kenan itadai batasan tazauna bataga Salim ba yayi murmushi tabuga kofar tashigo yana kwance akan sallaya yatashi zaune Ummina kinshigo eh Salim kafito muci abinci to Ummi sunfito tare sunwuce gurin cin'abinci Ummi tazuba masu sannan tazuba nata takalli Salim kunyi waya da Nafisa eh Ummi takirani ina sallah bayan na'idar nakirata tayimin sannu da zuwa tare da fatan alkhairi tama fadamin cewa zata shigo amma bata fadamin ranar dazata shigoba nima takirani kamardai abinda tafadama shita fadamin nakuma bata Abbanka sungaisa sunci gaba dacin abincinsu suna fira har suka mammala alokacin dare yayi Salim yamasu saida safe yayi tafiyarsa Ummi takallesa anya lafiyarka Salim lafiya qlau Ummi kawaidai gajiyace to shikenan saida safe Allah yabamu alkhari Amin Abbana yamasu sallama yatafi sundawo falo nadan wani lokaci suntashi sunyi ciki domin sukwanta yashigo daki yakwanta ringing din wayarsa ne yasashi bude idansa daga rufesu da yayi yana dubawa yaga sunan Safwan yadaga tare dayin sallama my friend barka da dare dafatan bantasheka daga barciba a'a Safwan yanzuma nakwanta yagida yasu Safna suna lafiya yagajiyar hidima da gajiyar tafiya gajiya tabi jiki to Allah yahutar da gajiya yasu Ummi duk suna lafiya nabarsu afalo basaniba yanzu ko sunje sukwanta to shikenan dan Allah kagaishesu zasuji insha Allah to yayi nagode saida safe to Allah yabamu alkhairi Amin yarabbi dahaka sukayi sallama

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
5⃣0⃣
By

Fauziya Usman

Inakwana lafiya qlau Nafisa kenan to abinda nakeso dake yanzu kitashi muje muci abinci saura kuma kicemin bakyajin yunwa dan nasan halinki sarai badan tasoba yatashi saidan bayanda zatayi sunfito sunci abinci Aunty takalleta Nafisa kece auta kuma kekike wahalar dani ko a'a Aunty to maiyasa kike fishi dan kawai nace kiyi Aure ko dan nahanaki tafiya Kano a'a Aunty bako daya to shikenan kije kishirya gobe zakije Kano Aunty da gaske eh lokaci daya tashiga farin ciki tatashi tayi dakinta da gudu tana murna Aunty tabita da kallo ko murnarme takehaka

Washe gari takarasa shirinta tashirya tsab tafito bayan tayi break fats tayiwa Aunty sallama tafito tasa kayanta mota direba yajata sai Kano sunyi sa'ar isowa lafiya tashigo Ummi tatarbeta da Larai sannunki da zuwa Nafisa an'so lafiya lafiya qlau Aunty Larai Ummi ina wuni lafiya qlau Nafisa yahanya Alhamdulillah ya Aunty tana lafiya tace agaisheku to muna amsawa taga bataga Salim ba takasa hakura tace Ummi ina yaya Salim yafita amma Masan duk inda yake yana haryar dawowa gida yanzu abinda za'ayi shine kitashi kije kiahirya kafin yakaraso kinji to Ummi tatashi yayi daki tanashiga tafada bandaki tayo wanka tafiyarta keda wuya saiga Salim yashigo fuskarsa cike da annuri Salim kadawo eh Ummi yahidan lafiya qlau to madallah Ummi ina Nafisa tayi murmushi tashiga daga ciki domin tashirya tadai iso lafiya ko lafiya qlau bayan tafito tashirya tsab cikin riga da siket na atamfa kayan sunyi mata kyau sosai tayi daurin daukwali wanda yakara fitar da kyanta tafito saiwani kamshi takeyi tafiya take sannu ahankali saiwani murmushi take abin gwanin shawa tayi matukar birge Salim sosai sai wani kallonta yake hartasauko tazauna kujerar datake kallon ta Salim suna kallon juna yaya Salim kadawo eh Nafisa yahanya kun'iso lafiya yagajiyar tafiya Alhamdulillah to Allah yahutarda gajiya Amin Ummi haka Nafisa takara girma takara kyau tamkar nashekara goma bangantaba eh Salim shiyasa Aunty taketa zancan Auranta to aidole Ummi domin nasan tana da tarin samari shiyasa Aunty zataso ta Aurar da ita koba haka bane tayi murmushi bare da tayi maganaba to waye gwanin naki kanwata tayi shitu batayi maganaba yayi dariya Nafisa kardai kunyata kike kenan bazaki fadamin sunan sirikin nawaba har zuwa wannan lokacin batayi maganaba to shikenan idan bakifadaminba aizangansa kuma kifada masa yazo yagaisheni yana cikin magana saiga Abba sallamarsa ce tasashiyin shiru ya amsa masa sallama sannu da zuwa Abba yauwa Salim Abba ina wuni lafiya qlau Nafisa anzo lafiya yahanya ya Aunty lafiya qlau Alhamdulillah tace agaisheku to muna amsawa Ummi tayimasa sannu da zuwa ya'amsa yayi ciki Ummi tabi bayansa Nafisa kema hakan takusa kasancewa dake Nafisa Amarya awannan lokacin nine babban abokin Amarya kuma yayan Amarya kinga nasamu matsayi biyu kenan ko bahaka ba batadaice dashi komaiba yakallete yaga yanayinta yasauya yakira sunanta Nafisa tajuyo takallesa batare data amsaba lafiya tindazu naga inata magana kinyimin shiru meyake faruwane tahirgiza kai alamar bakomai yace kinga kidena yimin maganar kurame kiyimin magana tayanda zanfahimceki kifitomin amutun tayanda zanganeki kafin tace wani abu Ummi tafito tashiga kicin batajimaba tafito hannunta dauke da kular abinci tace Salim dan Allah kamikawa direban dayakawo Nafisa

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
5⃣1⃣
By

Fauziya Usman

Wallahi tindazu mantawa nayi to Ummi takoma tadauko filat da cokali tafanin abinsha tadauko ruwa da lemu maisanyi suntafi sunkai masa sundawo lokacin Abba yasauko Abba amma yau kajima baka dawoba wallahi Salim wani guri naje shiyasa to wannan zancan yatsaya anan kutashi muje muci abinci to Ummi suntashi Salim yakalli Nafisa yace Nafisa waimai yake damunkine bakomai to shikenan mutafi sunzo sunzauna Ummi tazubama kowa sannan tazuba nata tazauna kowa nacin abinci amma banda Nafisa Ummi tace Nafisa wai lafiya kike kuwa naga duk yanayinki yasauya Ummi kinfasan 'yan mata idan suka kusa Aure haka suke to itama shine tafara kanwata kinkusa kizama Amarya gaskiya zanyi missing dinki sosai abin yamata yawa tamarasa abinda zatayi ganinsu Ummi sunata dariyar abinda Salim yafada saikawai tasaka kuka tatashi tayi daki Salim yana kiranta amma ko kallonsa batayiba da gudu tayi daki tarufe yataso yabiyota saidai tasama dakin sakata yayi bugawa amma sam taki budewa yadawo Ummi tace lafiya tarufe kofar nabuga amma bata budeba tomaiyake damuntane to Ummi taya zansani tinda bata fadaminba amma gaskiya da akwai abinda yake damunta wanda itakawai tabarwa kanta sani to kadawo kaci abinci a'a Ummi nagoshi nizanshige saida safe to shikenan Allah yabamu alkhairi Amin Abba saida safe Allah yatashemu lafiya Amin Abba yayi tafiyarsa daki yashiga yakwanta amma sam bayajin barci sai tinani yake to maiyake damun Nafisa ne wanda yake da girma haka domin yafashimci damuwarta babbace da wannan tinanin yayi barci Nafisa adaki takasa zaune takasa tsaye ba'abinda take sai kuka to ita yanzu yazatayi miye mafita agareta yanda taga rana haka taga dare awannan daran batayi barciba abin duniya yadameta gashi kuma tarasa mafita da safe Ummi tazo dakinta taji kofar arufe tabuga tare dafadar sunanta Nafisa kibudemin kofa kinajina tazo tabude mata tashigo tazauna Nafisa tagaisheta ta amsa Ummi takalleta tace Nafisa waimaiyake damunki ne dan Allah kidaure kifadamin domin kinsamu adamuwa duk kanmu bawanda yayi barci jiya kinbarmu acikin duhu yakamata kifadi damuwarki domin asamamaki maganinta kinji tafashe da kuka sosai kinga Nafisa dan Allah kiyi hakuri kibar kukannan kifadamin silar damiwarki nikuma nayimaki alkawarin idan har inada abinda zantaimakeki dashi to zanbaki gudunmuwa dan Allah kudaure kifadamin kinji cikin muryar kuka take maganarta tace Ummi wallahi yaya Salim ne kawai maganin damuwata domim ina matukar kaunarsa wannan shine dalilin dayasa banasan kowane irin namiji wanda yazomin da sakon soyayyarsa tinda jimawa nakesansa bajiya nafara sansaba bakuma yauba saidai nafashimci shiyamin wata dauka daban yayinda nikuma banasan narasashi Ummi kitaimakeni yaya Salim yayarda yasoni domin idan narasashi amatsayin miji bashakka nayi babban rashi Ummi takalleta tayi murmushi Nafisa kenan wannan shine damuwarki eh Ummi to share hawayanki domin daga yau damuwarki takau insha Allah zaki samu maganin damuwarki saidai abinda nakeso dake shine kenasan kifadama Salim da kanki cewar kina sansa dafatan kinfahimceni karkiji nauyi ko kunya domin idan har Salim yayarda to babbas zanfiku murna da farin ciki zakifada masa eh Ummi kinyimin alkawari insha Allah to shikenan Allah yamana zabi nagari Amin Ummi to ni zantafi amma kafinnan inasan naga farin ciki akan fuskarki banasan ganin damuwa ko bacin rai kinajina eh to yimurmushi kona hana Salim amincewa tayi dariya itama dariyar take yauwa kokefa amma kinwani bata fuska kinhadeye rai to Ummi nadena to shikenan kikwanta kiyi barci to Ummi saina fito afito lafiya Allah yasa Amin tafito tayi tafiyarta

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
5⃣2⃣
By

Fauziya Usman


Misalin karfe goma 10:00am Salim yafito bayan yayi wanka yashirya yasami Ummi da Larai afalo sunata fira abin gwanin shawa domin inba wanda yasaniba bazakace Larai yar aiki bace gata kullum tsab bata da kazanta Salim kafito eh Ummi ina kwana lafiya qlau antashi lafiya Alhamdulillah Ummi ina Nafisa tana dakinta kardai haryanzu bata fitoba eh to lafiya bara nadubata nagani ko to dubuta kagani yatashi yatafi yasami kofar arufe yabuga tare da ambatar sunanta tazo tabude masa yakalleta sinhada ido yayinda idanuwanta suke zubar da kwalla taje tazauna kan kujera yabita shima yazauna kusa da ita kusa sosai yace Nafisa kukanne har yanzu tinjiya lallai matsalarki ko damuwarki babbace Nafisa yaza'ayi nasan abinda yake damunki domin wallahi banasan ganinki acikin damuwa ko bacin rai Nafisa ina rokonki da Allah da girman Allah akan kidaure kifadamin abinda yake damunki kukanta takoma sabo domin ita sam bata tinanin samunsa yace subhanalillah Nafisa bazaki fadaminba nahakura a'a yaya Salim zanfadama to fadamin inajinki cikin sarkarkiyar murya take maganarta yaya Salim agidane Aunty bata da wani buri ayanzu daya wuce taga nayi Aure nikuma duk namijin dayazo gidanmu daneman Aurena korarsa nake ran Aunty yabaci dani sosai tomaiyasa kikeyin haka Nafisa kebakya da wanda kikeso ne ko bakida zabin kankine a'a yaya Salim inadashi to tinda harkina da wanda aiyakamata kisanar masa domin yafito ya baiyana agaban Aunty domin keda ita damu mukasance acikin farin ciki kallansa kawai takeyi tana zubar da hawaye kinga Nafisa kidena wannan kukan kifadamin waye zabinki wakikeso cikin muryar kuka tare da sunkuyar dakai kasa tace yaya Salim kainakeso kuma Kaine ZABINA wallahi tinda nake bantaba jin sanwani mutumba face kai soyayyarkace tahanani yarda da sosayyar duk wani maisona saidai na fashimci cewa kai bakayimin soyayyar Aure ssidai kanayimin soyayyar kanwa amma kasani yaya Salim bazan iya hakurin rashinkaba domin zuciyata tana matukar kaunarka fiye da tinaninka samunka agareni shine fatana rashinka dai-dai yake da rasa raina domin kai ruhine agareni sannan kuma soyayyarka numfashinace bazan rayuba saidakai adamana tinanina duk yakare agareka farin cikina kaine nawa har kullum har koyaushe I LOVE YOU shidai kallonta kawai yake yayinda zuciyarsa tacika da mamakinta yaya Salim dan Allah kayarda da soyayyata domin wallahi zan'iya mutuwa idan narasaka yaya Salim dan Allah kayimin magana kafadi wani abu miye ra'ayinka akaina amma kasani bazanso natilassaka akainaba inasan dan Allah kafadamin gaskiyar abinda yake zuciyarka akaina harzuwa wannan lokacin kallonta yake lokaci daya yasami kansa da zubar da hawaye domin baitaba tinanin zaisami mace irin Nafisa ba kasancewar yanda yake duk da cewa Ummi da Abba suntsaya masa amma harkar Auratayya tafi danan tatsinke masa tinaninsa da tambayarsa yaya Salim kukanme kake mekake tinani bakomai Nafisa

Please Login or Register in order to submit comment