Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayarda Amin da haka sukayi sallama

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
4⃣0⃣
By

Fauziya Usman

Gwambe


Haj Aisha tana zaune afalota Jamila tashigo tare dayin sallama Haj Aisha ta amsa mata cikin sakin fuska tare dayimata maraba tashigo tazauna bayan sungaisa tace Hajiya kifito kici abinci tayi murmushi harkin kammala eh to shikenan mutafi ko sunfito tare sunsami maigidansu akan kujera shikadai yakalli Haj Aisha tagaishesa ya'amsa sunfara cin'abin tare da fira suna cikin cin'abinci Jamila ta dafe kai tana bata fuska Haj Aisha tace Jamila lafiya wallahi hajiya kainane yake wani ciwo to kinsha magani a'a tinyaushe kannaki yake ciwo gaskiya bazan'iya ganewaba domin ankwana biyu to kinga yanzu abinda za'ayi shine mukarasa break fast dinnan sai muje asibiti domin musan abinda yake damunki kinjiko to shikenan ammani sam banama san cin'abincin domin banajin dadinsa kokadan duk da haka kiyihakuri koda kadanne kinji to shikenan zanci yauwa Alh mansoor sai kallonsu yake gaskiya yanajin dadin yanda matansa suke zaune lafiya musamman Haj Aisha yanda tadauki Jamila tamkar kanwarta wadda suka fito ciki daya da it's shikam saidai yayiwa Allah godiya bayan sunkarasa cin'abinci suntafi asibiti anyimata aune-aune ance sudawo gobe su'anshi result sundawo gida Haj Aisha tace Alhaji inafaganin yarinyarnan juna biyune da ita najima inaganin yanayinta yana canzawa to Hajiya koma miye aizamugani tinda munje asibiti ko hakane to Allah yajishemu alkhairi Amin Hajiya

Washe gari Alh mansoor bayan yatashi daga office dinsa yabiya ta asibiti yakarbo result yadawo gida ransa fari kal baitsaya ko inaba sai gurin Hajiya domin yasan suna tare dashigowarsa sunsan yana cikin farin ciki yace Hajiya hasashenki yazama gaskiya Jamila tana da juna biyu ga result dinnan na'anso kaimadallah Allah mungodema Allah ya inganta Amin Hajiya farin ciki yakamasu itadai Jamila batace komaiba saima tashi datayi tayi dakinta ga alama kunya takeji yayinda sukabita da kallo suna mamakinta

Washe gari sunje anyimata scan cikinta wata uku tindaga wannan lokacin Haj Aisha tahanata yinkomai koda kuwa itace da girki ganin yanda aikin gida gaba daya yadawo kan Haj Aisha ne yasa Alh mansoor yakawo masu mai aiki domin bayasan ganin Hajiya acikin wahala Jamila tasamu gata sosai agurin Haj Aisha tamkar ita tahaifeta kafinsu fa'iza susan tana da ciki kenan domin tinda suka sami labarin cewa jamila tana da ciki suka sake buda kwandansu narashin mutunci suka suka dingayiwa haj Aisha bakin ciki iri-iri kala-kala tare da cinmutunci sunsami Jamila sunfada mata cewa Haj Aisha bata santa zagon kasa takeyi mata kuma da zata samu dama data zubarmata da ciki domin yanda bata haihuwa da yaya mansoor haka batasan kowace mace tahaihu dashi da farko Jamila bata daukar maganarsu to yau da gobe sai Allah tinbata dauka har magan ganunsu suka fara tasiri agurinta tafara dauka domin sunnuna mata matukar so shiyasa tayarda dasu hakama talura da yanda Alh Mansoor yake matukar san Haj Aisha wadannan abubuwan ne sukayi tasiri azucirta harta shagala shedan yayi nasara gareta lokaci daya tafara canzawa sam tadena jin maganar Haj Aisha sannan tadena bata girma tafara yimata rashin kunya da rashin mutunci lokacin da cikinta yacika wata tara Haj Aisha tasamesa adaki tashigo tazauna Jamila kwance ake eh batare datajuyo takalletaba bataji haushiba tace Jamila tashi ga magani nakawo maki domin yanzu cikinki yakai lokacin haihuwa wannan maganin zakine kuma zakiji saukin nakuda insha Allah tamika mata maganin cikin wata Yar kwalba tadauki kalbar taduba awulakance tamere baki sannan tadawo da kallonta gareta tace Hajiya cikin daga murya nafashimci kingagara samun yanda kikeso game da cikinnan nawa kinyi duk iyakokarinki danganin cikina baikawo yanzuba kinkasa shine yanzu kikazomin da wannan sabon salon kika kawomin abinda zansha dan cikina yamace ko to wallahi baki isaba ta Allah ba takiba kuma kokinaso ko bakyaso wsnnan cikin saina haifeshi lafiya saidai kihadiye zuciya ki mutu idan zaki iya harda wata kissa wai maganin zaki atinaninki bansan komaiba ko kinxo kicuceni to wallahi Allah yafiki dama fa'iza ta fadamin komai game dake da dadai banyar daba amma yanzu naga zahiri Dan haka tashi kifitarmin daga daki koba zaki fitaba sai nayi maki rashin mutunci

By Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
4⃣2⃣

By

Fauziya Usman


Haba Hajiya maiyasa kike yimin hakane taya inaganin damuwa akan fuskarki sannan kifadamin cewa ba'abinda yake damunki dan Allah da girman Allah kifadamin maiyake damunki toshikenan muje falo yatashi sundawo falo tace Alhaji dan Allah inaneman wata alfarma agareka shine nake faduwar gaba tare da fargabar fadama domin banajin zansamu abinda nake nema agurinka Hajiya kenan kidena jintsoro ko fargaba kifadamin damuwarki nikuma nayimaki alkawarin zanyimaki duk abinda zaizamo farin ciki agareki toshikenan Alhaji sonake dan Allah kayarda nakoma kaduna da zama tinda kanada gidaje acan saina zauna daya dags ciki domin zanfi jindadin zama acan wannan shine farin ciki ki idan namiki haka zaki kasance cikin farin ciki eh insha Allah to idan har wannan shine farin cikinki to zansa agyara maki gidan da yake a j.r.a saiki zauna acan shikenan damuwarki takau eh to shikenan nizantafi office am Hajiya na'am zanso kibari sai Jamila tahaihu sannan saiki tafi ko to shikenan nabari yauwa kings zuwa lokacin ma ankarasa gyaran gidan to amma kisani bazan barki kizauna kedayaba saboda banasan kadaici yayimiki yawa saboda yanasa yawan tinani shikuma tinani yanahaddasa damuwa kokin gane eh dama idan kayarda zanyiwa lami magana sainaje da ita muzauna tare to bamatsala kiyi magana da ita kiji to maigidana godiya nake Allah yasaka maka da mafificin alkhairi Amin ya Allah Amin Hajiya natafi saina dawo to Allah yakiyaye adawo lafiya to Allah yasa Amin

Washe garin ranar Jamila tatashi da nakuda itadaya adaki Alh Mansoor yafita office Haj Aisha tana dakinta domin takama kanta da ita saboda kare nutuncinta Jamila takasa zaune takasa tsaye sai azabar nakuda takeji gata haihuwar farin batasan komaiba dakar tasamu ta'iyadaukar wayarta takira layin Haj Aisha saidai batayi maganaba akaro nabiyuma batayi maganaba ganin takira layinta harsau biyune yasa tayi tinanin kodai batada lafiyane to amma kuma batayimata maganaba to baridai taje taduba tagani koma miye Haj Aisha tatashi domin taje taga ko lafiya Jamila take kiranta daga shigarta tajiyo nishinta dasauri takai inda take tanafadin sannu Jamila tadau waya takira Alh Mansoor tafada masa dasauri yazo yadaukedu sai asibiti ina karfinta yarigaya daya kare doctor yace masa saidai ayimata theater domin tawahala dayawa saboda tajima tana nakuda idan kuma bahakaba za'a iya rasata ko abinda yake cikinta Alh Mansoor yasa hannu nantake akawuce da ita dakin theater anyinasarar ciromata 'ya mace bayan anfito da ita doctor yace yana bukatar ganin Alh Mansoor office Alh Mansoor yabiyo bayansa dominjin abinda zaifada masa bayan sunshigo yace masa da farko inamai baka hakuri domin matarka tasami matsala ga mahaifarta sakamakon doguwar nakuda datayi gaskiya bazata sake haihuwaba saidai hakuri Alh Mansoor ba'abinda yake fada face innalillahi wa'inna'ilaihiraji'un ayihakuri Alhaji sannan yabashi takardar magani bayan anfito da ita alokacin su fa'iza sun'iso saimurna suke sunhana Haj Aisha 'Yar itadai batace dasu komaiba saima komawa datayi gefe tayi nisa dasu saboda gudin matsala tana daga zaune tahangi maigidanta yana tafiya ga damuwa duk tabayyana afuskarsa dasauri tataresa tare da tambayarsa lafiya yafada mata abinda doctor yafada masa tace innalillahi wa'inna'ilaihiraji'un to Allah yabata lafiya Allah yaraya mana baby yasamata albarka karkasa wannan aranka domin duk mutum baya wucewa kaddararsa yace ta ansomasa yarinyar taje saifa wannan lokacin tasamu damar daukar babyn takawo masa ya'ansheta yayimata huduba tare da radamata suna Nusaiba Haj Aisha tayi murmushi Allah yaraya mana Nusaiba Amin Hajiya ya'isa inda yan uwa anyimasa barka yamikawa Haj Aisha'Yar yace yatafi yadawo

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
4⃣1⃣
By


Haj Aisha mamaki yacika zuciyarta yanda taga yarinya karama tana fada mata magana yanda taga dama tace zanfita Jamila kenan dama nasan cewa yinhakan batinaninki bane saki akayi tare da samiki wani tinani akai to kisani ni bana hassadarki balantana nayi hassadar abinda ke cikinki ni tsakani da Allah nake tare dake amma bazaki yardaba tinda har fa'iza tana tare dake amma wata rana gaskiya zatayi halinta zaki fahimci komai hakama zakisan wacece fa'iza cikin daga murya tace karya kikeyi ni bakyasona kuma nasani kina bakin ciki da abinda ke cikina adai-dai lokacin ne Alh Mansoor yashigo Haj Aisha ranta yabaci sosai lokaci daya hawaye suketa zuba akan fuskarta tahuyo tana kokarin fita taci karo da mai gidanta yagirgiza mata kai alamar a'a yazo inda Jamila yakira sunanta yace kinsan kowacece wannan kinsan abinda kike fada akanta kuwa da lafiyarki ko kinsha wani abune ko zugaki ake a'a kodaya ni bawani abu danasha hakama ba wanda yazugani kawai nagane gaskiyane domin wannan matar munafukace bata ankaraba taji saukar mari afuskarta Jamila ashe bakida kirki bansaniba to kimaida hankalinki kuma kisani wannan sabon iskancin dakikazo dashi gidannan bamaiyuwu wabane idanma wani yake zigaki to kinyi kuskure domin bazan daukar makiba cinmutuncin uwar gidana uwar 'ya'yana wallahi bazan daukar makiba nikaina ina girmamata dan haka yazamemaki dole kigirmamata bands shashasha yaja hannun uwar gidansa sinfita sunbarta nan tana kuka tare da bacin rai azuciyarta sunzo dakinta yace Hajiya dan Allah kiyihakuri domin komai akai maki ninajanyo maki da banyi Auranba da baza'aci mutuncinkiba bakomai mijina wannan ai bakomai bane karkasa wannan aranka ni agurina yawuce to sjikenan Allah yaimaki albarka Amin mijina to yanzu abinda za'ayi shine kaje kararrashi matarka domin nasan ranta bakaramin baci yayiba Hajiya kenan aibanyi komaiba domin badan cikin da take dashiba wallahi dataraina kanta a'a aibazaka biyemataba domin ita yarinyace natada ishashshen hankali yanzu dai kaje kararrasheta toshikenan zantafi tinda kinmatsa yatashi yagatayi zamanta yace aubazaki rakaniba to baranazauna nafasa a'a yihakuri muje tatashi tarakashi harkusa da kofa sai fari'a take tamkar wani abu baifaruba da itaba yashigo yasameta azaune ranta bace sai hawaye kezuba afuskarta yayi kamar baigantaba nan tafara ciccika wai ita anyimata laifi tace masa yanzu abinda kayi kenan kakyauta mainayi kamareni agaban wata sannan kacimin mutunci sannan har katambayeni maikayi oho ashe badadi sannan ashe da zafi ita da kikaiwa sokike tahadiyi zuciya tamutu to wallahi baki isaba idan har kinasan kiyizaman farin ciki acikin gidannan to wallahi yazame maki dole kiyibiyayya agurin Hajiya idan bahaka ba kuwa wallahi zakisha mamakina Hajiya tafikarfin wulakanci ko cinmutunci agidannan da fatan kinfahimta yatashi yayi tafiyarsa Haj Aisha bayan takoma daki sai tinanin 'ya'yanta yazo azuciyarta yamata zaune sai kuka domin tinlokacin da 'ya'yanta suka rasu bata taba bacin rai ba irin na yauba domin anfada mata magana maizafi yanzu yazame mata dole ta kama kanta ga Jamila domin tsira da mutuncinta saidai tana farin ciki da irin mijin da Allah yabata Wanda baimanta da bayaba da wannan tinanin tayi barci

Washe garin ranar da safe Alh Mansoor yashigo dakin Haj Aisha kafin yatafi office saidai baisameta afaloba kaitsaye yawuce bedroom yasameta akwance ga alama tinani take domin yafashimci batagansaba yakarasa inda take yakira sunanta tare da rika hannunta tajuyo sunhada ido Hajiya maikike tinani haka bakomai a'a kinga dan Allah kifadamin naji miye damuwarki karka damu Alhajina bakomai inakwana lafiya qlau

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
4⃣3⃣

By

Fauziya Usman


Misalin karfe biyar nayamma 05:00pm Jamila tafarka Basira ce tazo gurinta tana yimata sannu yauwa Aunty Basira nan akashiga yimata yajiki anbata 'yarta tagani sai fari'a take kwananta biyar akabata sallama suka dawo gida bayan kwana biyu da sallamarta yakama sati daya da haihuwa akayi bikin suna inda yan uwa da abokan arziki sukayita zuwa tamkar itace haihuwarsa tafarin kasancewar baitaba haihuwa anan kasarba Salim da Safna duk akasar England akahaifesu kuma gasu sunrasu hakan yasa akayi biki Wanda yakeshine itadao Haj Aisha tana gefe domin bada ita akeyin komaiba anmaida ita yarkallo hakan baisata bata raiba domin tasan bawanda ya'isa yayimata yanda Allah yamata kuma gareshi tamaida lamurranta domin shizaimata mafita bayan bikin suna da kwana biyu Alh Mansoor yatara matansa yakalli Jamila tare da kiran sunanta inasan kinatsu domin kiji abinda zanfada maki yaune ranar nadamarki idan kinada hankali doctor yafadamin cewa mahaifarki tasami matsala bazaki sake haihuwaba sakamakon dogowar nakuda da kikayi wannan wannan itace nadamarki domin da ace lokacin da kike zama lafiya da Hajiya ne toda dayardar Allah hakan bazata faruba domin zata taimakeki tinkafin kiwahala dan haka yanzu yarage naki idan zakiyi hankali kifarka to idan kuma bazakiyiba to yarage naki itadai gaskiya dayace kuma kinsanta lokaci daya tafashe da dariya hehehe Alhaji kenan tanan kuma akabulloman to wallahi bazanyardaba tasaka adaki tayima dadin baki ko dan anganeni yarinya anaso acuceni to wallahi duk kanku baku'isaba dan kawai ita batahaihuwa shine nima akesan adakatarmin da haihuwa to bazan yardaba haihuwa kuma yanzu nafara naga wanda xsidakatar dani aikin banza duk Kansu kallonta kawai suke Haj Aisha tagirgiza kai batare da tace komaiba Alh Mansoor yakalleta Jamila nikike fadawa wannan maganar to Alhaji nariga nagama fahimtar cewa kariga kagama zama mijin tace duk abinda tafadama shikakeyi nikuma sam bakayimin adalci to bari kiji nafada maki wannan batsarinmu bane tsarin Allah ne shiya kaddara maki Haifa 'ya daya arayuwarki wani abinma da bakisaniba shine jibi Haj Aisha zatabar garinnan zata koma Kaduna dazama domin bazata iyada rashin mutuncinkiba hakama bazsnbari kukashemin ita da bakin cikinkuba domin ina bukatarta arayuwata yana gama fadar wannan yatashi yayi tafiyarsa itama Haj Aisha tashitayi tayi tafiyarta sunbarta anan tanata maganganu iri-iri Haj Aisha taje gidan talatu bayan sungaisa tace talatu dan Allah inaneman wata alfarma ahurinki dafatan zansamu Hajiya kenan wace irin alfarma kike nema agurina mainake dashi wanda kike bukata nikuma nayi alkawarin zanbakishi tayi murmushi bakomai bane talatu dama inasan Lami ne natafi da ita kaduna domin zankoma can da zama haba Hajiya wannan aibakomai bane yaushene tafiyar jibine kuma tafiyar safece zata iya shirinta zuwa gobe to shikenan Hajiya Allah yakaimu saikinganta to talatu godiya nake a'a wallahi Hajiya bakomai wamnan aiyiwa Kaine to shikenan sainaganta goben to saitazo dahaka sukayi sallama tayi tafiyarta


Washe gar Haj Aisha tayi duk kannin wani shirinta da yamma saiga Lami tazo hajiya tace a Lami harkin iso eh Hajiya inna tace nagaisheki to ina amsawa washe gari da safe tatashi takarasa shirinta tatashi Lami tashirys tsab bayan sunyi break fast Alh Mansoor yashigo yasameso afalo tatareshi da murmushi shikanshi murmushin take Alhaji barka da zuwa yauwa Hajiya Lami tagaishesa cikin girmamawa ya'amsa Hajiya kunkarasa shirin eh munkammala komai kaikawai nake jira to shikenan kufito mutafi ta'amsa da to sunfito saidai tabiya ta gurin Jamila domin suyi sallama tasameta afalo tashigo tace Jamila muzamu tafi takalleta Sama dakasa kallon wulakanci tare da mera baki to Allah yakiyaye tayi murmushi ta amsa da Amin ina Nusaiba tana daki barci take to idan tatashi kigaisheta to zataji sunyi sallama tafito tadawo sunshiga mota sunkama hanya sai kaduna sun'iso gidan lafiya sunshiga daga ciki gidan yayikyau iyakyau komai masha Allah sannan gashi anzuba masa kayan zamani masukyau masutsada irinsu kujeru kayan gado firij T.V dadai sauransu hakama ankawata mata kicin dinta tamkarna budurwa komai nagidan masha Allah domin ko toilet din gidan abin kallone farin ciki Yakama Hajiya saimurna take da dauki Wanda har takasa boyewa azuciyarta Alh Mansoor yafahimci hakan shikansa yana cikin farin ciki Domin bayasan yana ganinta acikin damuwa ko bacin rai sunshiga yanuna mata ko ina nagidan sannan sukazo suka zauna bayan sunhuta sunci abincin da Haj Sadiya ta aikomata dashi domin ita batasamu damar zuwaba Haj Aisha tanunawa Lami dakinta sai murna take wannan duk dakintane eh Lami nakine Alh Mansoor kwanansa biyar yatafi shima badan yasoba dominshi sam bayasan rabuwa da Haj Aisha duk da cewa sunman yanta amma haryanzu sunasan junansu ana igobe zaitafi ya siyomata motamaitsadar gaske yakuma kawomata direba gamai gadi ga kuma yaron aikace-aikacan gida yabata mukullan gida gaba daya tare da kudi maiyawa koda wata bukata tazo mata farin ciki Kamata sosai har takasa fadar komai sai nagode

Washe gari bayan sungaisa sunyi break fast sundawo falo sundan taba fira kadan yatashi domin tafiya jiyake kamar karyatafi to amma tafiyarsa tazama dole saiyaje haka yatashi yafito Haj Aisha tarakoshi harbakin mota tare da yimass kyakkyawar addu'a sunyi sallama yatafi


By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
4⃣5⃣
By

Fauziya Usman


Koda sunboye basu nunaba to dole yana damunsu azuciya dan Allah Safwam kadena kaji eh naji kuma zandena yauwa to yanzu kokaifa yayi murmushi yatashi sundawo falo Salim kafito dashi eh Abba suncigaba da firarsu harzuwa wani lokaci sannan sukayiwa juna saida safe Salim yakira layin Nafisa ringing daya tadaga tare da cewa Amincin Allah yatabbata agareka babban yaya tare da ke kanwata yagida yasu Aunty lafiya qlau suke dafatan bantadake barciba a'a banyi barciba nadai kwanta kawai Nafisa kinyimin laifi maigirman gaske nikuma eh ke yaya Salim wane irin laifi nayima dan Allah kafadamin da sauri zuciyata tajima dashiga rudani Nafisa kenan to kwantar da hankalinki girman laifin baikai gahakanba to naji amma dan Allah kafadamin wane irin laifi na aikatama kinaso kijiko eh inaso naji sosaima kuwa to laifin shine maiyasa bakizo bikinmu nakarewaba yaya Salim yaushe akeyi bikin aiba ayiba sai gobe za'ayi su Ummi sunzo sainaga bangankiba shine abin yaban mamaki dana tambayi Ummi saitace bata fadamakiba laifintane wallahi yaya Salim banjiba danazo karki damu bakomai yawuce to yaushe zakudawo jibine idan akayi biki gobe to jibi insha Allah zamudawo zakizo Kano ne eh inasan nashigo saidai idan kadawo sannan to shikenan Allah yakaimu yanuna mana Amin yarabbi dahaka sukayi sallama ya'ajiye wayar yadawo da kallonsa ga Safwan Wanda yake akwance shibaiyi barciba shibaiyi maganaba Safwan bazaka denaba ko a'a my friend wallah layinsu nake kira amma nagagara samu to kaga kayihakuri wannan badagasu bane daga network ne kabari da safe saika sake gwadawa kajiko toshikenan Allah yakaimu yauwa Amin

Washe gari bayan sunyi break fast sunshirya wayar Safwan tadau ringing yadauko yaduba yaga sunan Safna yadaga tace yayana barka da safiya nasan cewa baka cikin farin ciki kasancewar bamuzo bikin karewarkaba to kasani muda muke anan munfika kasan cewa acikin halin damuwa yayana dan Allah karka bari damuwa tayi tasiri azuciyarka zanso ayau kafi kowa kasancewa acikin farin ciki kasani farin cikinka shine namu damuwarka ko bacin ranka illace agaremu dan Allah kakasance cikin nishadi yayi dogon numfashi tare da ajiyar zuciya yace bakomai kanwata wallahi naso ace kina anan gurin to saidai hakan bata samuba zankasance acikin farin ciki domin samun naki farin cikin yauwa yayana inagodiya abisa yarda da shawarata ga Aunty Zainab tamika mata sungaisa tayimasa fatan alkhairi daga bisani sukayi sallama Salim yace to Safwan hankalinka yakwanta ko eh my friend yafada yana murmushi sun'isa gurin bikin anyi biki yayikyau sosai yakayatar da jama'ar da aka gaiyato anbasu kyaututtuka na musamman ba'atashi gurin bikinba saida yamma sosai sundawo gida sunyi shirinsu natafiya washe gari bayan sunyi break fast sunyiwa juna sallama sunkama hanya su Salim sunkama hanyar Kano yayinda su Safwan suka kama hanyar Kaduna acan gida kuma Zainab da Safna sai murna suke da dauki sunyi girke-girke da dama sannan sunhada lemunna sungyara gida yayikyau sosai ko ina lungu da tsako sai kamshi ketashi hakama sungyara ma Safwan dakinsa harzuwa toilet yayikyau sosai bayan sunkarasa aikinsu sintafi domin sushirya Zainab tafara shiga wanka bayan tafito Safna tashiga fara wankanta keda wuya su Umma suka iso indo ce take musu sannu da zuwa Zainab tasaka kayanta dasauri tafito tanayimasu sannu da zuwa yaya Safwan yahanya an'iso lafiya lafiya qlau Zainab ina Safna tana gurin wanka nima fitowata kenan nasako kayana nafito tonima baranaje nawatsa ruwa tinbakasha ko ruwaba a'a Umma kibarsa domin yanzu idan Safna tafito tasamesa anan to wankansa saidai nadare to shikenan yatafi Zainab ma tashitayi taje tagyara jikinta da fuskarta tana shiga Safna nafitowa Aunty Zainab su yaya Safwan ne eh sune amma yashiga wanka saikisamu kishirya ko to nan tafara shirinta cikin tsanake

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
4⃣4⃣
By

Fauziya Usman

Kaduna


Shekara kwana su Safna sunkarasa karatunsu na secondary school inda Zainab har tashiga aji daya a jami'a yayinda Safwan yakare nashi karatu ansamasu ranar biking karewa saidai Zainab bazata sami damar zuwaba saboda makaranta yayinda Safna suke exam a islamiyya wannan dalilin ne yasa basu samu damar zuwaba su Umma kawai suka tafi sai Ammar Safna harda kuka saboda bacin rai Abba ne yake rarrashinta akan tayi hakuri haka tahakura tinda bayanda zatayi lokacin dasu Umma suka iso Safwan yana ganinsu yashiga murna da farin ciki yatambayi Umma inasu Safna Umma takallesa suna gida basu samu damar zuwaba saboda makaranta Umma Safna batakareba eh takare saidai suna exam islamiyya kaga bazatazo tabar exam dintaba ko Zainab kuma test sukeyi lokaci daya yabata fuska ransa yabaci Abba yace haba Safwan kayihakuri mana kaima kasan dolace kawai zatahana Safna da Zainab zuwa bikin nan wallahi Safna harda kuka tayi saida nararrasheta sannan mukazo shine kaida kake babba kuma sai kayi fishi amaimakon farin ciki daganinmu bahaka bane Abba wallahi nasa araina zasuzo shiyasa naji badadi araina karka damu domin duk kansu suna tare da kaunarka kuma suna daukin ganinka nasani Abba nima inadaukin ganinsu sosai Safwan wai ina Salim ne naga tinda mukazo bangansaba yafita zaiyowa Ummi siyayya suna cikin zancansa yashigo tare da yin sallama Safwan ya'amsa masa yashigo yagaisa dasu Abba saidai yafahimci Safwan bayacikin walwala yace Safwan lafiya naga baka farin ciki bayan gasu Umma atare dakai to kaimadai kafada inji Umma a'a Salim sam bahaka bane kafi kowa sanin yanda nasarai akan zuwan kannena koba hakaba eh haka to ya'akaine my friend su Umma ne kawai sukazo batare dasu Zainab ba shiyasa duk nakejin badadi araina Salim yadawo da kallonsa gurinsu Umma yace Abba maiyasa bakuzo dasuba saboda makaranta Salim shiyasa tokaji Safwan makaranta ce tahana su zuwa dan Allah kadena damuwa ni wallahi banasan naganka acikin damuwa raina baci yake inasan naganka acikin nishadi da walwala to shilenan my friend komai yawuce yauwa brother kokaifa bayan wani lokaci saigasu Ummi sunshigo Salim da sauri yaje inda suke tare da fari'arsa yataresu sunshigo sunzauna angaisa Ummi ta tambayisu Safna Umma tace suna gida maiyasa basu zoba saboda makaranta ayya to Allah yataimaka Amin Hajiya Salim yace Ummi ina Nafisa ya'akai batazoba Salim kenan Nafisa na sokoto shiyasa batazoba amma kinfada mata a'a Salim banfada mataba to maiyasa Ummi wallahi Salim hankalina ne yadauku to shikenan zankirata tobamatsa kakirata Safwan yatashi yayi ciki fuskarsa duk ba walwala Salim da sauran mutanan dake falon duk sunbishi da kallo Ummi tace Hajiya waimaiyake damunshi kodayake Salim yakamata natambaya Salim maiyake damun Safwan ne Ummi yana fishine akan rashin zuwansu zainab yakasa fahimtar dalilin rashin zuwansu yamike tsaye Ummina inazuwa to Salim saikadawo Salim nifa Abbana kenan yanzu nake kokarin ambatar sunanka kayimin rigagi to shikenan afito lafiya to Abba yayi ciki inda Safwan yasamesa akwance yazauna kusa dashi haba Safwan maiyasa kakr hakane yakamata kacire damuwa aranka kabar komai yawuce nasan dole bazakaji dadiba to amma hakan bayanufin kakasance acikin damuwa ko bacin rai kasan cewarka cikin farin ciki shizaisa komai yawuce ni bakaganiba wallahi nayi tinanin Ummi zasuzo da Nafisa kasan yanda nasa Nafisa araina tamkar kanwata amma basuzo da itaba araina banji dadiba ammame bannunaba domin bana bukatar abinda zaibata ran Ummina ko Abbana ko nayi abinda zaisa suji basu kyautaminba hakan badai-dai bane domin su Umma bazasuji dadin hakanba

By Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan:

Please Login or Register in order to submit comment