Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nima inasanki inasanki har cikin zuciyata kuma inasan kisani kece ZABINA kekadai nakeso kuma inafatan kikasance uwar 'ya'yana nangaba take farin ciki Yakamata yaya Salim da gaske kanasona eh Nafisa inasanki fiye da yanda kike sona kai amma yau inacikin farin ciki tamike tafito da gudu yana kiranta amma ina kojuyowa batayiba tafito aguje tana fari'a tafada jikin Ummi tana dariya farin ciki haryamata yawa Larai tace Nafisa farin cikinme kikeyi haka murmushi kawsi tayi mata tajuyo ga Ummi tace Ummi yayarda dani ya amince da soyayyata Ummi gaskiya yau inacikin farin ciki sosai Nafisa kenan aibasai kinfadaba ganinki kawai yatabbatarmin da hakan fatana Allah yasanya alkhairi yasa ayi damu Amin Ummi Larai tace Hajiya zan'iya jinkomiye eh Larai Nafisa CE da Salim suka dai-daita Kansu

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
5⃣3⃣
By

Fauziya Usman


Kai masha Allah wannan abu yayikyau sai lokacin yafito yana kokarin shiga dakinsa Ummi takirashi Salim zomana yazo gani Ummi Nafisa tafadamin cewa kaida ita kunasan junanku hakane domin inasan nasamu tabbaci agurinka kainake sauraro yasunkuyar da kansa kasa eh Ummi hakane tayi murmushi to naji dadi sosai kuma nayi farin ciki koma nace nafiku far in ciki Larai tace to injindai kafada mata nice uwar gida domin bazan yardaba maganarta tabasu dariya domin duk Kansu dariya suke Aunty Larai kenan ainasai nafadaba itakanta tasani duk wata mata da zan'Aura tana bayanki yauwa kinadaijiko tayi dariya Aunty Larai Allah bazaki iya kishi daniba to shikenan aiza'mugani shida Ummi sai dariyarsu suke Ummi tace duk kudakata badai akan Salim bane eh Hajiya toke Larai tinda kindan fara manyanta kibada sadaki dubu dari biyu da hamsin saimuyi maneji kekuma Nafisa zakibada dari shida domin yarona nadabanne bakamar sauran mazaba nan sukace mezasuyi inba dariyaba lokacin Abba yasauko yasamesu cikin fari'a sai dararraku suke Abba sannu da zuwa yauwa sannunku Larai tagaishesa ya'amsa cikin kulawa zata tashi yace a'a yizamanki mana takoma tazauna hajiya firarme kuke haka maicike da nishadi nan talabarta masa komai shima dariyar yake toke hajiya banda abinki da sankai awane garine mata suke bawa maza sadaki Alhaji kenan ba yarona sukesoba to dansuna san yaronki sai subada sadaki eh mana gaskiya Salim inamai farin ciki dajin wannan labarin Allah yasanya alkhairi Allah yayi mana jagora Amin Abba bayan wani lokaci suka tashi domin yin break fast lokacinne Larai tayi bangaranta sunzo gurin break fast Ummi tace to Alhaji tinda Salim yakarasa karatunsa aisai ayimaganar Auransu ko eh hakan yayi a'a Ummi nidai nafisan abari sainayi N.Y.S T dina sannan domin yanzu haka zancan da akeyi bazai wuce nanda wata dayaba tafiyarmu kinga idan nakarasa sai ayi koya kuka gani bakomai za'ayi shirin komai bayan ka kammala N.Y.S T din sai ayi bikin yauwa Ummina tokai Abba yakagani naji kayi shiru bakace komaiba toni mezance aikunriga kungama magana to shikenan Allah yanuna mana Amin ya Allah bayan sunkarasa cin'abinci Abba yafita Ummi tatafi kicin itada Larai yarage saura su biyu afalo Nafisa takallesa haba yaya Salim maiyasa kayi haka mainayi kuma maiyasa baka bari anyi bikinmuba kafin zuwanka N.Y.S.T Nafisa kenan bazaki ganeba shikenan saina tafi nabarki tomiye saina zauna tare da Ummi a'a nidai nafisan saina karasa lokacin danake da time alokacin dazan baki cikakkiyar kulawa nima namorema Amarcina koya kikagani to hakanma dai-daine saidaini wallahi banasan kanayin nisa dani karki damu insha Allah wannan shine nakarshe zankasance akullum inatare dake harsai kince dan Allah nafita tab aikuwa wannan ranar bazata taba zuwaba har'abada domin ni bankiba ace akullum kuma ako wane lokaci inatare dakaiba domin ganinka kawai yana sani nishadi yaya Salim wallahi bazaka gane inasankaba sai lokacin da kakasance miji agareni lokacin da babu wani shamaki atsakaninmu alokacin nayi alkawarin shayarda kai ruwanso da kauna alokacin zaka fahimci cewa ashe inasanka Nafisa kenan nayarda dake fiye da tinanina inamaki soyayyar da bawani miji da yake yiea matarsa fatana akullum Allah yakaimu lokacin Auranmu Amin YAYA Salim bayan sati biyu Salim nadakinsa wayarsa tadau ruri yadaga aduba yaga sunan Safwan yadaga tare dayin sallama bayan sungaisa Safwan yake tambayarsa yabatun N.Y.S.T dinshi yaga sunansa eh Nagano Safwan jiya naje naduba wallahi inatasan nakiraka nafadama kuma sai namanta DanAllah kayi hakuri wallahi bakomai yawuce to inagodiya naga tafiyar satin samane ko eh hakane to Allah yanuna mana lokaci muje lafiya mudaeo lafiya Amin ya Allah dahaka sukayi sallama

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
5⃣4⃣
By

Fauziya Usman


Ya ajiye wayar tindaga wannan lokacin yafara shirin tafiya Nafisa jitake tamkar tahashi zuwa saidai batada wannan damar hakan yasa dole tahakura tinda bayanda zatayi ana igobe zashi sunjima shida Nafisa suna fira saida dare yayi sosai sannan sukayiwa juna sallama kowannansu badanyaso ba da safe yafito bayan yashirya yasami su Ummi afalo yace Ummi ina Nafisa bayan sungaisa aibata fitoba yatashi yasameta adaki tayi zugum tamkar wadda ruwa sukaci ga alama tinani take yaje inda take yarika sunanta amma bata amsaba yadanja hancinta sai lokacin tadago kai takallesa yaya Salim yaushe kashigo taya zakisan lokacin da nashigo bayan kinyi nisa cikin tinani Nafisa tinaninme kikeyi haka bakomai a'a karki boyemin kifadamin gaskiya tayi ajiyar zuciya yaya Salim ina tinanin halinda zanshiga ne lokacin da bakanan saina sami kaina dajin tausayin kaina yayi murmushi Nafisa kenan karki damu domin ba'abinda zaisameki koba komai kirika tinawa inatare da soyayyarki yaya Salim nasaba da soyaytarka idan katafi zanshiga kunci narashinka Nafisa banasan kisaka damuwa aranki domin nikaina inajin hakan hakuri kawai nakeyi zantafi nabar Ummina Abbana da kumake kingani niyakamata nadamu bakeba dan Allah kidena damuwa kinji eh zandena to Allah yabaki ikon cikawa Amin yarabbi yauwa to taso muje indasu Ummi tatashi sunfito bayan sunyi break fats yaje yayiwa Aunty Larai sallama yafito su Ummi sunyo masa rakiya harbakin mota yamasu sallama yashiga mota yatafi bayan sundawo ciki Nafisa tayi daki tanata faman kuka Ummi tasameta tana rarrashinta tare da bata magana dole tahakura tinda bayanda ta iya

Kaduna

Da yamma lis Zainab tadawo daga makaranta saidai abin mamaki babu gajiya atare da ita Safna tace Aunty Zainab sannu da zuwa amma ga duk kanni alama kinbiya tawani guri to uwar surutu maikika gani naga bagajiya atare dake eh nabiya tagidan Hajiya ne shiyasa ok Allah sarki tana lafiya lafiya qlau take kekuwa maikikeyi adaki kowa yana falo bakomai a'a kicedai sabida yaya Safwan bayanan to ashe kinfahimta ehmana to amma su sauran mutanan gidan bakyasan fira dasune a'a kawaidai nasami kaina da zama anan har zuwa lokacin da yaya Safwan zaidawo to idan yatafi N.Y.S.T yakenan wannan kuma aidole zanhakura harzuwa lokacin da zaidawo ni wallahi wannan shakuwar taku keda yaya Safwan wani lokaci har mamakinta nake to miye kuma na mamaki bayan kinsan komai kuma kina ganin komai Safna wallahi naga nawar kifara zuwa school domin nafara gajiya da zuwa nidaya ai Abba yace nakusa fara zuwa insha Allah to Allah yanuna mana yakaimu lokaci Amin Aunty Zainab toya school Alhamdulillah nibara natashi nawatso ruwa ko jikina zaiwarware Aunty Zainab amma Umma tasan kinbiya ta gidan Hajiya a'a banfada mataba to idan Hajiya tafada mataba ai'ita Hajiya sam bahaka takeba batashiga hurumin da banataba idan kuma kasata aharkarka to lallai zakasha mamakinta domin zatayima komai yanda yaka mata halaiyar Hajiya sunada kyau sosai ita sam baruwanta gata dasan mutane dasan raha hakama idan kina fira da ita sam bakyasan tafiya domin firarta tana kayatar da mai sauraranta sannan kuma kana karuwa da firarta sosai kai amma wallahi Aunty Zainab harnaji inasanta kuma inasan naganta karki damu zaki ganta insha Allah to Allah yakaimu lokacin da zanganta Amin ya Allah to nidai nashiga wanka to afito lafiya Allah yasa Amin tashiga wanka batawani jimaba tafito tashirya tsab cikin kananan kaya riga da siket kayan sunyi matakyau sosai kuma sun ansheta takalli Safna sunyi ido biyu Safna tace kai masha Allah Aunty Zainab kinga yanda kikayikyau kuwa nagode Safna lah bakomai

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
5⃣5⃣
By

Fauziya Usman


Wallahi to tashi mufita ko bazakiba a'a tinda kinanan zanje mana to sarkin surutu saura idan sauka kidafama Umma cewa nabiya ta gidan Hajiya kinjiko kai Aunty Zainab aibazan fadaba kodama ace zanfada aibayanzuba sai ankwana biyu to bara kiji wallahi bakwana biyu ba koda wata biyune bance kifadaba kinajina ko eh najiki Allah yabani ikon rikewa wannan kuma ruwanki kinga bama afalo zamu zaunaba to inazamuje can harabar gida zamuje muzauna to shikenan ninamafi san zama acan to mutafi sunfito Umma taga suna kokarin fita takallesu ina kuma zaku zamuje harabar gida toshikenan suntafi sunzauna nadan mintuna biyu zuwa uku Zainab tacema Safna taje takawo masu ruwa da lemu maisanyi ta'amsa dato ta tafi takawo masu takoma tazauna suna cikin firarsu saiga Safwan yadawo Safna tatareshi da murmushi shikansa yasami kansa dayimata murmushi kannena sannunku da hutawa yauwa yayana barka da dawowa yauwa sannunku yaya Safwan kazauna mana to zanzauna amma sainashiga ciki na watsa ruwa nacanjo kayana saidai lafin nafito inasan Safna kikawomin kayan fruit da juice maisanyi da kuma ruwa to yayana angama tana murmushi shima murmushin yake yayinda Zainab take kallansu tana murmushi yashige ciki sunbishi da kallo bayan yashige Safna tace Aunty Zainab gaskiya yau nafashimci yaya Safwan yana cikin farin ciki sosai gaskiya hakane amma maizai hana mu tambayesa domin muji aikuwa haka za'ayi bara yafito tukunna to shikenan toni bari naje nayi aikin da yasani karya fito banyi komaiba ok saikin fito ta tafi tahado kayan fruits tafito dasu sannan takoma tadauko ruwa da juice kafin tafito yatareta sunfito tare yace kanwata sannu da kokari yauwa yayana sunkaraso sunzauna tamika masa kayan fruits yakarba yasa abaki tamikama Zainab takarba sannan tazuba masu juice a cup Safna sannu nasaki aiki da yawa nasan yanzu haka kingaji ko a'a yayana aini sam bana gajiya da aikinka ni har farin ciki nake idan kasani aiki to godiya nake kanwata lah bakomai yayana to kema kick mana a'a saika koshi sannan zanci a'a banyardaba tare zamuci to shikenan haka dukaci tare duk kansu sunaci suna fira Safna takallesa yayana in tambayeka wani abu eh kanwata tambayarni inajinki yauwa yaya Safwan nikuwa nakula dakai akwanakinnan kana cikin walwala da annashuwa kozamu iyajin miye dalili Safna kenan bakomai kawai ina faricikine saboda na kammala karatuna nadawo gida kusa daku domin inasan naganni akusa daku sainaji farin ciki yanata shigata yaya Safwan kenan to yanzu gashi zaka tafi nesa yakenan wwllahi nima shine abinda naketa tinani akai amma banida wana mafita dole sainatafi karka damu yayana insha Allah wannan itace tafiya takarshe agareka wadda zakayi nisa damu nima inafatan hakan Safna agari daya zakayi N.Y.S.T da yaya Salim a'a saidai muna kusa da juna domin bamuda wani nisa atsakaninmu to kace zakurika haduwa da juna sosaima insha Allah to Allah yabada sa'a Allah kuma yataimaka Amin ya Allah suna cikin haka saiga Abba yadawo yashigo yasamesu afarfajiyar gida suna fira sai raha suke yasamesu sunyi masa sannu da zuwa ya'amsa cikin sakin fuska yau kuma anan kuke hutawa eh Abba to Allah yaimaku albarka Allah yaraya manku Amin Abba yashige warsa ciki yabarsu anan sundan kara wasu mintuna sannan saga bisani suka dawo ciki tare da dauko kayan fruit Umma tace sannunku tindazu kuna waje kunbarni dagani sai indo kunacan kuna furarku ta yanwa ko shine baku tashi shigowa ba saida Abbanku yadawo ko a'a Umma bawai dan Abba yashigo bane saidan yamma tayi koma nace dare yasomayi domin duhu yafara aifa yanzu ni nasan zaman da nakeyi daku agidannan sunyi dariya to Umma Allah yabaki hakuri Allah yahuci zuciyarki Amin Abba yakalleta yanzu duk wannan surutun sabodani kike haba Abban Safwan aidole nayi mita tinda naga agidannan ana nunamin banbanci

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
5⃣7⃣
By

Fauziya Usman

Yadawo ciki yayiwasu Umma sallama yace zaije gidan Hajiya to sai kadawo inkaje muna gaisheta to zataji yafito yatafi Abba ma yafito yatafi office su Safna sun iso makaranta bayan sunyi parking sunfito Zainab taraka Safna har class sannan tawuce nata class din tanashiga class tasami kujera tazauna bawani jimawa sosai malami yashigo yana cikin darasinsa yahangi Safna zaune yakalleta kallon tsab yaga baisantaba yazo inda take yace ke anan class dinkike takallesa eh anan nake to amma ya'akai bana ganinki sabida bantaba zuwaba saiyau tomai yahanaki gaskiya banda dalili ok to shikenan amma kisani nabada Assignment kuma yau zanyi test yanzunnan tayi murmushi ok zaka'iyayin test dinka dominni banda matsala da wannan Assignment dinma zaka iyabani nawa inyaso saina kawoma zuwa gobe wannan ba matsala bane kowa sai kallonta yake wannan wace irin yarinyace maitakeji dashine kuma maitataka malamin yaji haushinta domin yaga tana da izza to zainuna mata yafita izza dan haka zaiyi test yanzu yakoma gaban allo yarubuta masu test sannan yabasu mintuna shabiyar lokacin da yake rubuta quation din Safna tana karantawa tana murmushi fuskarta cike da annuri sai fari'a take wadanda suke kusa da ita sai kallonta kawai suke sunfara tubutawa shikuwa malamin sai wani hadiye rai yake sannan yana fatan Allah yasa Safna tafadi wannan test din domin itazaimaida matsayin exam dinsa Allah manyasha'u Safna tana cikin safun farko nawadanda suka fara karasa test dinsu yahangeta zaune bata rubutu yazo kusa da ita yana murmushi ke lafiya naga kowa yana rubutu amma ke bakyayi itama murmushin takeyi tare day in yar dariya kadan wadda takara baiyana kyan fuskarta yafusata kewai bakiji mainaceba najika to dariyarme kike bakimai to maiyasa bakya rubutu sabida nagama nawa test din eh kana manakine dasauri wadansu suka juyo suna kallonta tare da mamakinta to wannan wace irin yarinyace to gashi kagani domin gani yakoriji yakarba yana kallonta yaje yazauna gurin zamansa yana duba test din bayan yakare dubawa yakalli time yaga lokacin da yabasu haryasoma wucewa yatsayar dasu yasa ankarbo masa test din harzai fita tace Malan to yabatun assignment din ok kawo littafi natubuta maki tamika masa littafi yarubuta mata yabata yayi tafiyarsa bayan fitarsa wata dake kusa da ita tace mata sannu bakuwa yauwa sannu yasunanki sunana Safna kefa nikuma Hafsat amma gaskiya kinbirgeni Safna ko eh tonagode kinsan wani abu kuwa a'a saikin fada tinda mukafara zuwa school malaminnan idan yashigo baida aiki sai kassaramu komai mukayi saiyace bamu iyaba sai gashi yau yafita da mamakinki da gaske kike eh mana koke bakiga hakanba nikam banluraba sabida bakisan yanayin yanda take bane shiyasa tayi dariya toni maiya dameni dashi bakimasan wani abuba kinga wannan test din eh to sabidake yayita domin yanasan yasami damar dazaiyi maki wulakanci da gaske kike wallahi kuwa tab aikuwa bai'isaba domin nagaba yayi gaba baya kuma sai labari domin wannan test din tasa batayi girman ko Isar dazata wahalar daniba wannan test din maisaukin gaske aibaisan wacece Safna bane shiyasa aini ba alfahariba amma ba'akureni sannan kuma ba'akaini bango yayi kuskure domin bazai iyajayayya daniba kuma munanan tare dake zakigani wata rana agabanki saina kuresa kuma zakigani wani daga cikin maza wanda yanajin duk abinda take fada yace to wannan wacece lallai zaisa ido akanta harsai yafahimci ko wacece ita lokaci daya tamike tsaye tagaisa da matan dake class din tare da fadamasu sunanta itama tana tambayar nasu sunaye domin Susan June tadawo bangaren maza tayi masu sallama kawai batare data tambayi sunayansuba sannan ita bats Fada masu nata sunanba taje gaban allo tadauki maka tafara amsa quation din test daya bayan daya sannan tadawo tazauna kowa sai mamakinta yake Hafsat tace aikuwa nafadi no 4no5 kuma bankarasashiba lokaci yayi ayya sorry insha Allah bazaki kara faduwaba indai inatare dake aikuwa godiya nake a'a karki damu toshikenan Safna Allah yabar tare Amin

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
5⃣6⃣
By

Fauziya Usman


Tofa tomaida wukarki kube yawuce daga yau insha Allah andena ko Safna eh Abba to Allah yasa Amin Umma yauwa waiko nace tinda kadawo kaje gidan Hajiya eh Umma amma saudaya naje aikuwa bakakyau taba duk yanda kake da Hajiya ace saudaya kaje aizankoma kafin natafi N.Y.S.T dina yadaikamata lokaci daya Zainab taji faduwar gaba jin"anyi zancan gidan Hajiya domin tana tsoran kar Safna tafadi wani abu Umma nima inasan zuwa gidan Hajiya sosai domin inasan naganta Aunty Zainab tabani labarinta Zainab sai harararta take amma ina sam taki fahimta tajuyo tace Aunty Zainab idan zaki kara zuwa gidan Hajiya zakije dani tayi ajiyar zuciya Safna kenan cewa zakiyi idan zani ba idan zankomaba kirika gyara maganarki saikace ba bahausaba Umma takalleta karki damu Safna zankaiki gidan Hajiya harma kikwana acan farin ciki yakamata sai dariya take Abba yace Safna ankammala komai na makarantarki dan haka saikiyi shirin fara zuwa kinjiko to Abba godiya nake yayinda farin cikin ta yakaru yaya Safwan zanfara zuwa makaranta inamaki murna kanwata Allah yataimaka Amin Aunty Zainab taharareta tare dacewa meye haba Aunty Zainab mainemikine kike hararana bansaniba kodan nafadi cewa kekinga kiyi shiru haka kinji to shikenan nayishiru Zainab yau kuma da kanwar taki kike fada rabu da ita yaya Safwan taya zanrabu da kanwata kunga nikubarni nakarasa zancena tukun sai kucigaba domin bazanshiga fadankuba to Abba munajinka yauwa nasa akawo maku mota wadda zakurika zuwa school basai kunjira ankaiku ko andauko kuba kaima Safwan nasa akawoma domin yakamata kacanza ko nagode Abba Allah yasaka da alkhairi Abba mungode Allah yabiyama da bukatunka na alkhairi Amin lallai Abban Safwan kanafa sankarta yarannan da yawa Hajiya kenan idan banyiwa 'ya'yana ba banbasu jindadiba daga abinda Allah ya wadatani dashi to miye amfanin arzikin nawa wannan bakomai bane domin zan'iyayimasu abinda mayafi wannan to Abban Safwan Allah yakara wadata Amin Hajiya nizanshiga daga ciki to Abba afito lafiya yatafi abinsa Umma tabi bayansa Zainab takalli Safna keko zaki sani tatashi tayi daki Safwan yace Safna wai maiyake faruwane maikika yiwa Zainab naga tadauzafi dake lokaci daya wanda hakan sam bahalinta bane tashi tayi danzuwa inda Zainab Safwan yabiyo bayanta tashigo dakin jikinta duk asanyaye tazauna kusa da ita Aunty Zainab dan Allah kiyi hakuri wallahi insha Allah bazankaraba Zainab waimai yake faruwane yaya Safwan dazune daga school nawuce gidan Hajiya domin najima banjeba shine dana dawo nafada mata to Umma da Abba basusan najeba saboda banfada masuba nakwabi Safna akan karta fada amma kaga batajiba saida tafada saidaisu basu fahimci abinda take nufiba gaskiya Safna baki kyautaba wallahi yaya Safwan mantawa nayi aikuma kagasu Abba basu ganeba dan Allah Aunty Zainab kiyi hakuri wallahi nadena daga yau bazansake fadar wani abu abakinaba face abinda akatambayeni wannan alkawarinane yaya Safwan dan Allah kace tayi Hakuri Zainab kiyi hakuri kinga tayimana alkawarin tadena to Allah yasa da gaske take Amin to kinhakura eh yawuce to kinji tahakura saurake ainima nadena yanzu kuma saikizo kifara shirin tafiya makaranta aikuwa banmantaba domin abin yana rains gashi kuma Abba yasiyo man's mota Allah yasa kakoya mana tuki kaga da ankawo bawata matsala tukawa kawai zamuyi kaima ancanzama gaskiya Abba yana kokari damu Allah yabamu ikon cika zuviyarsa da farin ciki Amin kanwata bayan kwana biyu akakawo masu mita datasu data yaya Safwan motocin sunyi kyau har sungaji sunkara yiwa Abba godiya shikanshi Abba yana cikin farin ciki ganin yanda yaran suke farin ciki sakamakon ganin motarsu abinya mass dadi sosai

Washe gari Safna tashirya tsab ita da Zainab sunfito bayan sunyi break fast sungaisa dasu Umma da yaya Safwan Abba yayi murmushi yace Safna 'Yar makaranta Safna 'Yar jami'a sai dariya kawai take sunfito sunshiga mota Safwan yace to kanwata adaiyi ahankali da samarin jami'a kinji to yayana zankula sosai kuma zan'ankare domin gudun matsala da kuma samarda tsaro to Allah yataimaka Amin saimundawo to adawo lafiya Allah yayarda Amin ya Allah suntada mota suntafi Safna ce take tuka motar

By Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
5⃣8⃣
By

Fauziya Usman


Bashir yatashi yazo inda take yace kina nufin nafadi no 3 domin yanda kikai nibaha nayiba tayi murmushi taya zance kafadi tinda banice malamarka ba saikayi hakuri harzuwa lokacin da zaidawoma dashi saikagani Hafsat takalli Bashir tace lallai indai bahaka kayi no3 dinkaba to bashakka kafadi yace aikuwa bazai yuwuba shinwai kai intambayeka mana no 3 ne kawai kakeda matsala dashi a'a tosai wane no 5 tobara kaji idandai har bahaka karubuta test dinkaba to wallahi kaji narantse akwai matsala kuma kafadi amma zaka gani kuma zaka yarda Bashir yadawo gurinsa yacewa abokansa acikinku waya rubuta test dinsa kamar haka Abdul yace kaibahaka karubuta ba eh to gaskiya kasamu matsala domin yanda yarinyarnan tarubuta tayi haka yake tab ammafa yarinyarnan tanada basira akwai ganewa inasan nasan komai akanta aikuwa aiki yasameka bawani aiki domin duk abinda kasa kanka to sam bakaganin wahalarsa sannan kuma sam baka gajiya gaskiya wannan bakaramin abubane cewa saikasan komai game da ita kaidai baruwanka iyakacinka ido toshikenan gamu gani aikuwa zaku gani bayan wani lokaci saiga malamin yadawo domin basu test dinsu yasamu duk ancike amsar kowane quation yakira kowa da number sa yabashi yabarta karshe itada Abdul bayan yakirata sannan yakira Abdul yacewa Abdul kai bazanyi mamakinkaba sabida munyi karatu dakai nasan dole zaka iyaci tokefa ya'akai keda kikafara zuwa yau tayi murmushi bakomai dama yana akaina shiyasa amma ke dalibace ko malama tayi dariya sosai malama kuma a'a ni dalibace amma a school dinnan bakasan Zainab Abubakar ba wadda akabawa kyautar tafi kowa kokari awannan whekarar eh nasanta kinsantane sosaima kuwa a'ina kikasanta bakaji sunana bane Safna Abubakar itadin yayata ce a lallai bazanyi mamakiba domin Zainab koda malami tana cingyara tasan karatunsa sosai to shikenan namaki murna tinda kintsallake siradina kije Allah yataimaka amma Assignment dina gobe nakesansa kinfahimta karkaji komai in Allah yayarda gobe zankawoshi to lokacin tafiya gida yayi nina tafi yafito yayi tafiyarsa mutane sai fits suke kafin takaiga fita saiga Zainab tashigo ga alama agajeye take tace haba Safna waimai kike jirane sorry Auntyna wallahi mutane sunyi yawa shiyasa banfito dasauriba tamika mata makullin mota takalleta maikike nufi bakiga yanda nake agajiyeba to Aunty Zainab naga dazu nina tuka to koyanzuma kezaki tuka shige mutafi suntafi abinsu alokacin Bashir nanan duk yana kallonsu kuma yanajinsu bayan suntafi ya kalli Abdul yace gaskiya yarinyarnan Autace bakaga yanda take maganaba tanashagwaba wannanfa yayartace yakake tinani idan take gurin mamarta ko babanta abin zaibada gud result kokai bakaga hakanba gaskiya yarinyar tanada birgewa insha Allah sainayi kawance da ita Bashir kenan nidai dazaka biye tawa daka rabu da ita domin bakada abinda zaisa ta kulaka saboda tafika ganewa tafika fahimta sannan kuma Yar masu kudice to kagani tawuce da saninka kawai kabarta kayi karatunka danshi yakawoka amma inkayarda Abdul kenan aiyanzu kayi magana zanrika zuwa wurinta daukar darasi tahaka zansamu nakulla kawance da ita to shikenan Allah yabada sa'a yauwa abokina Amin to mutafiko sunfito sunyi tafiyarsu su Zainab suna kanhanya Safna takalli Auntynta tace Aunty Zainab wai lafiya wallahi Safna nagaji tinfa 12:00pm nafito class naketa jiranki har wannan lokacin duba kigani har 02:00pm tawuce sorry Aunty Zainab gaskiya kinyi kokari dole kigaji yanzu abinda za'ayi idan kika fito kikarigani tashi kizo kikarbi mukulli kitafi idan natashi saina kira habu yazo yadaukeni wannan bamatsala bane kinji amma dan Allah kidena tauye kanji akaina banasan hakan to shikenan yauwa Allah yataimaka Amin sun'iso gida sunshigo indo kawaice afalo tayimasu sannu da zuwa sun'amsa sunyi sama Zainab tafada kangado tayi kwance Safna takalleta tayi murmushi lalkai Aunty Zainab kingaji sosai taje tadauko mata juice mai sanyi da cup takawo mata

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:32] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
5⃣9⃣


Please Login or Register in order to submit comment