Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fad'a d'aki, tana jin ihun Fahad yana ambaton sunansa. 
   Ihun ne ya janyo hankalin Ihsan da Mami wadanda suke dakin daga cikin falon Mami suna magana akan dinkin da za'a yiwa Mamin na ankon bikin Baraka. Da sauri Ihsan ta fito, ganin Faruk ta hau dariya, cikin daga murya tace. "Mami dagaske ya ke, Yaya Faruk ne."
  Jin haka yasa Faruk suka k'arasa ciki, daga lokacin kunnuwanta suka daina jiyo sautikansu.
  Ta zauna a kasan kafet tana mai jingina kanta jikin bango. Haka kawai ta tsinci kanta da murmusawa. Wani sanyi ya doki zuciyarta. Ta tabbatarwa kanta akwai wani abu a ranta game da Faruk, tafi danganta abin da kauna ta don Allah irin wacce ta ke yiwa Antinta Amina, haka kawai Faruk ke burgeta. 
   'Kodai kina sonshi?' Gabanta ya fadi jin tambayar da ya darsu a zuciyarta. Ta zaro ido kamar wani na ganinta.
  'Ina ni ina Yaya Faruk? Ai ko zan so wani na gwammace ya kasance cikib samari masu takuramin a hanyar makaranta da dai son abinda bazan ta6a samu ba.'
  Ta ayyana a ranta, tunaninta ya katse sa'ilin da ta ji Fahad ya kwalamata kira.
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

    31
  "Ok, daman naji ance ke kika d 'aga waya ne, shiyasa na buk'aci k'anina da ya ba ki mu gaisa. Fatan komai lafiya?"
  Ta ja ajiyar zuciya wanda ya jishi har cikin ransa, ya tsinci kansa da lumshe idanu.
  "Lafiya lau, ya su Hajiya? Agaishesu don Allah."
  Ta burgeshi, hakan da ta yi ya nuna tana da hankali. Murmushi ya yi mai ban mamaki wanda da wani cikin yan uwansa zai ganshi da ya zargi koda wata budurwarsa ya ke wayar.
  "Zasu ji, thank you."
"Um."
Shiru ya biyo baya ta cire wayar a kunnenta ta ajiye gefe gami da zuba tagumi.
  "Na shiga uku, meya kaini d'aga wayar Yaya Adnan tun farko? Yanzu wace masifar zan jawowa kaina?"
Tayi maganar a fili wanda tsaf ya shiga kunnen Faruk kasancewar bai riga ya katse kiran ba, sai lokacin ya kashe ya sake kira. Har razana ta yi gami da ja baya. Ido waje ta duba ta ga shine har lokacin, ta d'aga ta kara a kunnenta.
  "Ba..bari na mik'aaa mishi, ya fita."
  Ya girgiza kai tamkar tana ganinsa alokacin da ya koma d'aki ya zauna saman kujera.
  "No, ke nake nema ai. So nake nasan masifar da na jawo miki?"
  Muryarta na rawa yayinda hawayenta suka zubo ta girgiza kai.
"Wal..walla..."
"Ki zama jaruma a komai na rayuwa Ummi, matsoraci bai zama gwani. Duk abinda zakiyi a rayuwa kiyishi da zuciya d'aya, ki zauna da kowa zaman gaskiya. Komai da zakiyi kiyi don Allah ba don wani halitta ba ok?"

Ta gyada kai gami da numfasawa, sosai nasihar ya shigeta, haka kawai ta tsinci kanta da jin wani sanyi a zuciyarta.
  "Nagode Yaya Faruk."
  Ya yi murmushi mai sauti kafin ya amsa.
  "Mu'assalam."
Daga haka ya katse wayar, batayi gangancin k'ara wani tad'in a fili ba sai a ranta. Gaba daya batasan cewar kiran bai katse ba. Lamarin ganinsa takeyi tamkar a mafarki, wai itace ke waya da Yaya Faruk? Ikon Allah! Yau kuma meke a kansa? 
  Haka tayi lamo a saman katifa cike da fargaba, sallamar Adnan ta sanya ta mikewa zaune tana mishi murmushi na yak'e. Fuska a sake ya kar6i wayarsa da take mik'o mishi gami da fadin.
  "Har an gaisa? Wai daman kun ta6a gaisawa da shi?"
  Ta gyada kai.
"Eh, shi ya taimaka ya kawoni gida ran fatin Yaya Haidar ai."
  Ya dan daga kai alamar tunani kafin kuma ya dan daga gira.
  "Oh, na tuna anyi haka fa. Kinsan Yayannawa ba dai kirki ba."
  Murmushin dai ta k'ara yi sannan ya juya ya fice.  Ta zauna ta yi tsuru cike da tunanin wannan lamari. A karshe dai da ta ga babu wani abu da ta tsinkayo ta share batun.
           
                    ***  ***  ***
   'Me nayi?' Ya jefawa zuciyarsa tambayar da baisan amsarta ba. Ya jingina kansa jikin kujera gami da k'urawa talabijin ido. Babu abinda ya yi banda sada zumunci. 
   'Kar ka d'arsawa zuciyarka wani abin daban, kana tausayinta ne kawai.'
  Cewar wani sashe na zuciyarsa. Ya kauda maganar gaba d'aya ta hanyar kunna talabijin.

                     ***  ***  ***
  Sallamar da aka doka ne ya katse hirar da Habiba ke kwasa da mijinta. Ganin mai sallamar yasa duk suka washe baki, mijinta Yahuza ya mik'e.
  "Kai lale da mutan Kaduna."
  Fad'in Habiba kenan tana kokarin gyara tabarma. 
    Bayan sun zauna aka shiga gaisawa, Habiba ta zari gyale ta fita siyo ruwa. 
   Hajiya Munira kenan, 'yar kanwar Yahuza mijin Habiba, wacce ke auran babban ma'aikacin gwamnati a Kaduna. Ta zauna suka soma gaisawa da kawunta yana tambayar sadda ta iso. 
  "Kwanana biyu kenan ai Kawu."
  Ya jinjina kai kafin su cigaba da hira a haka har Habiba ta dawo dauke da leda mai ruwan sanyi da lemu tana fad'in.
  "Um, kaga fa tsabar zumud'i ko kudi ban dauka ba, bari yarinyarnan su zo su mik'a mishi."
    Suka dara sannan aka hau hira. A haka Dija ta dawo ta samesu. Ta ji dadin ganin Munira, suka shiga hira harma a karshe Munira ta nuna tana gayyatarta Kaduna koda na sati ne. Babu musu Dija ta nuna zata. 
   Kawu Yahuza da Habiba sunyi murna kwarai, ko ba komai sa dan huta da surutun mutane na cewar anbar yarinya ba aure sai gantali. Man aka tsaida idan Munira zata wuce, tare zasu tafi.
       Koda ta gama kwanakinta a kauyen, suka shirya tare da Dija da yaranta biyu, direbanta ya kwashesu zuwa Kaduna.

                   ***  ***  ***
                       ABUJA
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  33

A kofar dakin sukayi kici6us, ya  sanarmata wai ta zo ta k'aro faranti su Yaya Faruk zasu ci abinci. Ta amsa da to, a sanyaye ta gyara daurin dankwalin atamfarta sannan ta bi bayansa. A zaune ta gansu a saman tebur gaba daya, ta dauke kanta ganin shi dinma gogan idanunsa akanta suke, kicin din ta fad'a ta bi umarnin Mami. Ta dauraye ta goge sannan ta karasa garesu cikin sassanyar tafiyarta, sam bata da kwaramniya...

     Ta kawo falon, tana kokarin ajiye suka had'a ido da ihsan ta samu tsarabar harara kuwa. Ta ajiye a gaban Faruk, wani daddad'an kamshi na turare ya bugi hancinta.
  "Thank you."

 Daga haka ta juya ta bar wajen, ya bi bayanta da kallo kafin ya numfasa muryar Ihsan ta doki kunnuwansa.
"Let me serve you."
  Ya dubeta ya dan murmusa gami da gyada kai, cikin siririyar muryarsa ya amsa.
  "Kar ki cika, ban tare da yunwa."
  
Suna ci suna hira, jefi-jefi yakan dubi hanyar da ta bi, Mami ke faman jan shi da hira yana bata amsa. Ihsan gaba d'aya ta gama tafiya a kallonsa, sai yanzu take tabbatar da hakikanin gaskiyar abinda take ji game da yayannata. 
   
  Ummi a d'aki zaune ta yi zugum tana tunani. A karshe ta d'aga rigarta ta shinshina gami da lumshe ido. Ita kam tana son kamshi a rayuwarta don dai babu yanda zatayi ne ta samu. Musamman wannan turaren da ta ji awajen Faruk, sai ta ji ya doke duk wadanda ta saba shak'a wajen masu gidan. 
   'Komai na Yaya Faruk ba irin na kowa bane, komai nasa daban. Ya ji dad'in rayuwa.' Cewar wani sashe na zuciyarta. 
   'Kada ki kai kanki inda Allah bai kaiki ba Hasiya, babban goro fa sai magogin karfe, a komai na rayuwa Faruk ya d'ara ki, babu gatan da Allah bai ba shi ba. Yafi karfinki nesa ba kusa ba.'
  Wannan tunanin yasa ta numfasawa, wani hawaye ya taho mata wanda bata iya hanashi kwaranyowa ba, shikenan su yan aiki basu da gata? 
  A daren dakyar ta iya kokawa da zuciyarta har ta samu ta runtsa domin kuwa bata k'ara fita falon ba, asalima batasan sadda Faruk ya bar gidan ba, ta dai ji maganar Ihsan na fad'in  Babban Yaya wanda ya nuna shima yazo daga baya.

     Tunanin duniya ya ishi Ihsan, ta gama tabbatarwa lallai tana kaunar Yaya Faruk, a wannan daren yini ta yi kallon hotonsa wani dad'add'e da sukayi da Adnan da Haidar. Karshe dai ta kirashi a waya, bayan sun gaisa ya nemi sanin wace don bil hakki ba shi da lambarta. 
  "Ihsan ce." 
  Ya yamutsa fuska cike da mamaki sa'ilin da yake goge fuskarsa da tawul daga shi sai gajeran wando ya fito wanka.
  "Oh, kanwar Adnan?"
Ta ji haushin kanta, wato ko lambarta babu a wayarsa? Da tasan da haka da bata bayar da kai wajen kiransa ba. Kamar zata yi kuka ta amsa da eh.
  "Ok, fatan lafiya?"
Ta daure ta had'iye 6acin ranta.
"Daman na kira na ji ya kuka isa gida?"
  Ya dan saki fuska.
"Alhamdulillah. Nagode."
  "You are welcome."
Ya dan murmusa gami da jinjina kai.
"Good night.". Daga haka ya ajiye wayar batare da ya katse kiran ba ya cigaba da abinda yake yi. Babban Yaya na gefen gado zaune yana tura sak'o email a laptop dinsa.
  Takaici da bakin ciki suka tararwa Ihsan, ta katse kiran don kanta. Duk da ta ji haushinsa, hakan baisa ta ji zuciyarta ta bar magagin kaunarsa ba. Inama zai aureta? Ta ayyana a ranta, wani tsalle tayi a saman gadonta gami da kwakwume filo tana murmushi, a haka har bacci ya soma fisgarta ta yi addu'a ta kwanta.

                    
    Faruk yana kwance, ya zurfafa cikin tunani, a gefe yana dan tsintar hirar Babban Yaya da matarsa tamkar wasu sababbin aure, ya lumshe ido yana mai fatan bacci ya yi awon gaba da shi ko don ya daina ganin abinda ya ke gani a kwayar idanunsa, hakanan yabar jin sautin muryar da ta k'i gushewa a dodon kunnensa ba don komai ba sai don tsoron kada tunaninsa ya tabbatar da hakan, bayaso yanayin ya sauya zuwa ga abinda ya ke tsananin gudu. 
  Haka bacci ya sureshi cike da tunani da mafarkai masu dadi da ban mamaki.
   Washegari da wuri suka tashi, bayan sun kammala shiri suka dunguma zuwa daurin auren da Daddy ya turasu, sosai kuwa Alhaji Labaran ya ji dadin zuwansu, a karshe sukayi sallama suka nufi gidan Hajiya Mama. Basu jima ba suka wuce don a ranar zasu juya zuwa Abuja. 
   Suna komawa gida kuwa suka tattara suka bar garin Kano...!

       [truncated by WhatsApp]
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

35
                  KADUNA
  Mutan Kaduna sun isa lafiya lau, Dija cikin garin ya zamemata bak'o don bata ta6a zuwa ko'ina ba banda Katsina kauyen k'urfi inda nan ne asalin mahaifinta Yahuza. Ta yi mamakin ganin k'erarren gidan da Munira ke rayuwa cikinsa a unguwar Malali, ta sauke ajiyar zuciya har ta kasa 6oye mamakinta ta fito da shi fili.
  "Gidanki mai kyau."
Munira ta murmusa.
"Nagode 'yar uwa."
  
  Bayan shigarsu ciki ne ta gane wajen ba komai bane, domin sakin baki tayi tana karewa falon kallo wanda ya yi bala'in had'uwa. Zata iya cewa tunda take bata ta6a zuwa gida makamancin wannan ba. Haka Munira ta rakata har dakin bak'i a sannan ta koma ga yaranta Tasleem da Haris. 
  Ita dai Dija k'arewa komai kallo takeyi, tsaf, kamar ansan da zuwanta. Gado ne sai aka shimfida kafet a k'asa, a gefe sif ne maidaidaici na kaya, sai bandaki. Ina zata samu wannan a kauyensu kuma gidansu? Tunda dai akwai masu ginin zamanin, amma bata ta6a kwana ba. Tayi tsalle saman gado don dadi saikace wata 'yar shekara goma. 
    Munira ta dawo ta ajiyemata sabulu da soso a bandaki, ta umarceta da tayi wanka. Bayan ta kammala ta shirya tsaf sannan ta fito suka ci abinci saman tebur abin sai ya yiwa Dija banbarakwai, hatta yaran and saida sukayi mata dariyar yanda ta dunga nuna kauyenci saman tebur. A karshe suka tashi sukayi magriba mai aiki ta kwashe komai. 
Suna zaune a falon ita da yaran suna kallo, Munira kuwa na kicin tana shiryawa maigidanta abinci, suka ji sallamar maigidan.
    Gaba daya yaran suka mike suna ihun murna, hakan yasa Dina kallonsa. Sakin baki ta yi yayinda gabanta ya hau dukan tara-tara, haka mijin Munira ya had'u?
     
   Sanye yake cikin farar shadda, bak'i ne kuma dogo, yana da kyau babu laifi. 
  Ya rungume yaransa yana mai farincikin ganinsu, zuwan Munira da sauri ne yasa shi bud'emata hannu ta karaso ta shiga ya hadasu ya rungume gami da lumshe ido, a hankali ya yiwa matarsa rad'a ta dubeshi tana murmushi ta sakarmishi hararar wasa shima ya kashemata ido yana murmushin.
   "Sannu da zuwa."
Maganar Dija ta maidosu hayyacinsu, sukayi saurin sakin juna, ita kuwa tuni ta tafi a kaunar mijin Munira. Munira ta matsa da sauri shi kuwa ya dake ya amsa yana mai tambayarta mutanen kauye.
  "Duk suna lafiya, sunce a gaisheku."
  Ya amsa fuska a sake sannan ya maida hankalinsa ga Tasleem da Haris.
  "To, a jira nayi wanka na fiddo muku tsaraba ko?"
  Suka hau tsalle da ihun murna. Ya jinjina kai.
"Kuma ku nemomin tsarabar da ku ka kawomin idan ba haka ba nima zan fasa baku."
  Nan ya yi gaba yana dariya Munira da Dija na tayashi. Yaran kuwa kansu ya dauki chaji don basu yowa babannasu tsarabar komai ba. Haka sukayita tunani lokacin har Munira ta bi bayan mijinta, hakan yasa suka koma ga Dija don ta nemomusu mafita.
   Munira na shiga mijinta Deen (Zahraddeen) ya d'agata cak yana juyi da ita gami da fadin.
  "Oyoyo sweetna." Sukayi dariya, dakyar ta zame daga rik'on da ya yi mata ta dan daki kirjinsa. Cikin muryar shagwa6a tace. "Kaidai wallahi ba ka rabo da abin dariya."
Ya k'ara janyota yana murmushi da nok'e kai.
  "Eh mana, musamman ma idan agaban sweetna nake."
  Tayi dariya ta kwace jikinta gami da fad'awa bandaki don had'amishi ruwan wanka.
   Acan kuwa Dija ta kasa sukuni, hankalinta gaba daya baya wajen Tasleem da Haris masu tambayarta tsarabar da zasu bawa babansu. Mik'ewa ta yi.
  "Kuje kicin ku nemi wani abun da mamanku ta kawo.".  Da gudu suka wuce, dakinta ta koma ta zauna tana tunani, tunda take bata ta6a susucewa akan kowane d'a namiji ba kamar wannan, ta yi murmushi gami da k'udurta mugun abu a ranta.

                    ***  ***  ***
     Da sallama ta shiga turakar mijinta, ya amsa yana mai dubanta fuska a sake, ta ci ado har ta gaji sai kamshi ke tashi ajikinta. Ya yi ta dubanta itama idanunta akansa ta karaso ta zauna.
  "Barka da..." Maganarta ta katse ganin irin razanar da Alhajinnata ya yi gami da mik'ewa yana mai saurin toshe hanci. A tsorace Mami ke dubansa da mamaki.
  "Lafiya Abban Adnan?"
  Ya girgiza kai.
"Wane irin turare ne kika fesa haka Madina?"
  Mami ta dubi jikinta kafin ta dubeshi cikin rashin fahimta. 
  "Bangane ba?"
Ya kauda kai gami da k'ara ja baya.
  "Don Allah ki shinshina jikinki, wallahi turaren naki sam babu dadin shak'a, ki tashi don Allah ki je kiyi wanka kinji?". Ya karashe da muryar rarrashi da kwantar da kai. 
   Mami ta jinjina kai ranta na soyuwa, ba don Muhammad bane ayau da ta gasa mishi magana, saidai girma da darajarsa a idanunta yafi gaban haka, ga kuma soyayya tsantsa a gefe.
    Mik'ewa ta yi bayan shigewarsa daki da sauri da sauri, ta fice ta koma zuwa sashenta. 
    
   Ummi dake zaune su kadai a falon ita da Fahad suna kallon (Harry porter) sai ji sukayi ana kwankwasawa, Ummi ta bude, kallo daya ta yiwa Mamin ta fahimci akwai damuwa shimfide saman fuskarta, itama Mamin zubamata ido ta yi domin ta ga ko zata nuna wata alama na cewa ta ji wari ajikinta, sai ma ta ga duk hakan bata kasance ba. Wannan yasa ta sauke ajiyar zuciya ta giftata, ga mamakin Ummi, Mami har waiwayenta ta yi, ko me take son hangowa? Oho.
   Fahad ya mike zaune.
"Lah Mami, ya kika dawo?"
Ta yi yak'e. "Mantuwa nayi ne."
  Daga haka ta shige zuwa dakinta da sauri-sauri. 
  Suka cigaba da kallonsu, can kuma da jimawa, har Fahad bacci ya daukeshi saman kujera, Ummi kuwa na jiran Mami ta fita ta k'ulle k'ofar, sai ga Mamin ta fito tana zuba wani tsadaddan k'amshi na ban mamaki. Ummi dai tun kafin Mamin ta karasa fitowa kamshin ya ratsa kofofin hancinta. Tana mamaki kodai Mami 6arin turaren ta yi. Ta fito sanye cikin doguwar rigar abaya wanda daga k'asa kayan bacci ne,ta dora hijabi saman doguwar rigar. 
   "A'a, bacci ya yi?"
Ummi ta amsa a ladabce.
"Eh."
Ta jinjina kai fuskarta na nuna alamun bata so hakan ba. Ta dubi Ummi jiki a sanyaye.
"Ki kaishi makwancinsa."
  "Toh." 
  "Saida safe."
"Allah Ya tashemu lafiya." Cewar Ummi tana kokarin cika umarnint. 
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

34
  Ya gama buge-bugensa akan k'asa kafin ya yi wata arniyar dariya ya dubesu.
  "Shakka babu kun hadu da yarinya mai basira da har ta yi muku dabara batare da ta shiga matsalarku ba."
  Hajiya Binta ta dubi kawarta Luba sannan suka maida hankalinsu ga bokansu.
  "Kamar ya ranka shi dad'e?" Cewar Hajiya Binta kenan cikin rawar murya.
Ya girgiza kai.
"Babu wani k'ulli da ta sanya a k'asan gadon abokiyar zamanki, asalima acan kwatami ta yarr."
  Wani bakin ciki ya turnuk'e zuciyar Hajiya Binta, ta ji wata muguwar tsanar Ummi ya turnuk'eta, maganar Luba ta katse tunaninta.
"Yanzu ranka shi dad'e ya za'ayi? Tabbas munyi kuskuren saka wata, kada dai ta tona asirinmu?"
  Ya girgiza kai yana dariya.
"A'a, yarinyar ba haka ta ke ba, kada ku ji ko d'arr, yanzu me kukeso ayi?"
  "A maimaita mana irin wancan."
Fad'in Hajiya Binta kenan tana dubansa da jajayen idanunta wadanda 6acin rai ya kad'a. Nan take bokan ya turnuk'e fuska yana watsamata kallon banza na baki isa ba. Hakan ya kad'amusu 'yan hanji. Ya cigaba da magana da kakkausar murya....!

    
   "Kafin na baku na gayamaku wuyar k'ara samun aiki irinsa, domin a shekara, sau daya Aljani Tsingil ya bani damar tambayarsa buk'ata, saidai ko kuyi hakuri har wata shekarar."
  Hajiya Binta ta narke tana rok'onsa ko akwai wani abu da za'a iya yi?
Ya jinjina kai.
"Tabbas, abu mai sauki, zamu sanyamata warin ja6a, ta yacce ko ta ra6i mijin zai ji gaba d'aya ya tsaneta, amma hakan bazai sa soyayyarta ta fice a ransa ba, za dai ya kaurace mata kamar yanda kukeso, itama zata shiga tashin hankali. Ke kuma ga wannan (ya mik'a mata wani k'ulli) Ki dunga shafa kwallinnan aduk sadda za ki turaka, hakanan ki dunga shafe fuskarki da turaren nan, ina mai tabbatar miki za ki samu kulawar da ya saba bata, hakanan kuma ba dai kije da buk'ata ba, ya k'i aminta. Idan hakan ya yi muku..."

   Hajiya Binta da Luba suka amsa da eh har suna rige-rige. Yayi murmushi mai k'ara fiddo muninsa.
   "Ku tafi, ku saurareni nan da kwana uku, zakuga aiki da cikawa."
   Suka mik'e suka bar wajen da sauri gaba daya a tsorace. 
        A mota suna tafe Hajiya Binta na faman surfawa Ummi ashar tamkar tana gabanta. 
  Luba ta dakatar da ita.
"Laifin fa duk namu ne Binta, munyi wawancin sanya wata ta yi alhalin bamu gama fahintar halayenta ba. Wannan bata da son abin duniya kamar Zinaru tsohuwar 'yar aikin Hajiya Madina. Ya dace ko nan gaba mu kiyaye."
   Ta saki huci.
"Naji, yanzu me kike ganin zamuyi mata?"
  Luba ta murmusa.
"Me kike ci na baka na zuba ne? Wannan k'aramar alhaki ce muddin kika zama uwargidan Alhaji Muhammad Modibbo."
    Jin haka yasa Hajiya Binta kyalkyalewa da dariya itama aminiyar shaid'ancin nata na tayata. Ta jinjina kai.
  "Tabbas zasu san basu da wayo."
  
  Alokacin da suka iso kofar gidan, Ummi na kokarin shigewa ciki, dawowarta kenan daga islamiyya, gabanta ya fad'i ganinsu, suka bita da mugun kallo har ta shige lokacin da maigadi ke wangale musu k'ofa. 
   Ummi wani zargi ya d'arsu a ranta, ta tabbata mutanennan da wuya idan sun kyaleta, tana kuma jiyewa uwar dakinta tsoronsu, ta tabbatar basu hakura ba, dole akwai abinda suke shirin k'ullawa. Ta sauke ajiyar zuciya sadda isa kofar sashensu. Da ace ita din tana da dama, da ta shawarci Hajiya akan ta dage da addu'a don ta fuskanci Umma akwai mugun abun da ta taka.
      
                    ***  ***  ***
                      ABUJA
    Zaune yake saman kujera (resting chair) a 'yar barandarsa, ya sanya (sketch board) a gaba wanda aka kafa ajikin katako ya tsaya kyam, hannunsa alkalamin zane ne, daga shi sai singilet da gajeran wando, dawowarsa kenan daga aiki ya yi wanka, hannunsa na hagu rik'e da kofin (coffee) yana sha, ya dukufa sosai wajen kokarin zana abinda ke ransa, yana yi yana shan(coffee), saida ya kammala ya dubi zanensa yaga babu abinda ya manta sannan ya saki murmushi mai burgewa.  Komawa yayi ya kwanta jikin kujerar bayan ya tara kansa da hannunsa na hagu yana mai cigaba da shan (coffee) dinsa da dama, ido ya zuba k'irr yana k'arewa zanen kallo alokaci guda kuma zanen na k'ara shiga ransa.
  "So beautiful." Ya fad'a a bayyane, ya jima sosai yana kallon zanen kafin daga bisani ya mik'e ya dauko laptop dinsa ya yi aikin gabansa. A karshe ya nemi makwancinsa cike da dumbin tunani, abinda bai taba yi ba kenan duk tsawon rayuwarsa, kwana da tunanin abinda ya ke yiwa kallon 6ata lokaci a baya.

                ***   ***   ***
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  36
Har Mami ta kusa k'ofa sai kuma ta juyo alokacin Ummi na susar hancinta dake k'aik'ayi. Gaban Ummi ya fad'i ganin ta dawo. Mami ta dubeta lokacin da take matsowa gabanta.
  "Kinji wari ajikina Ummi?"
  Da sauri Ummi ta girgiza kai a tsorace.
  "Wallahi a'a, asalima kamshi kikeyi sosai Mami."
  Mami ta dubeta na dan lokaci kafin ta saki ajiyar zuciya.
"Amma naga kin toshe hanci."
  Ummi mai saurin kuka tuni murya ta raunana.
  "Aa wallahi k'aik'ayi yakemin shine na sosa."
   Mami ta numfasa.
"Saida safe." Ta furta a hankali sannan ta yi gaba tabar Ummi na binta da kallon mamaki. Ga dukkan alamu dai akwai abinda ke damun uwar dakinnata. Ta yi shiru, duk tunaninta bata gano komai ba hakan yasa ta basar da zancen ta tashi Fahad ta kaishi makwancinsa sannan ta rufe k'ofar. 
    A hankali bacci ya soma fisgarta ta ji ana kwankwasa k'ofa sannu-sannu. Mik'ewa ta yi a tsorace ta fito falo, agogo ya nunamata sha biyu harda mintuna. Ta karasa ta bud'e ta fita don bude kofar sashen. Shima Adnan lokacin ya mike ya fito don jin k'arar bugun don bai riga ya yi bacci ba yana karatun jarabawa. Ya dubi Ummi da mamaki.
"Waye haka?"
  "Adnan ku bud'e ni ce."
  Suka firgita jin muryar Mami, da sauri Adnan ya bud'e k'ofar. Ta shigo,ta dubesu da jajayen idanunta kafin ta wuce a sanyaye bayan ta umarci Adnan da rufe kofar. 
    Ummi ta tsaya a falo cikin tsananin firgici, Adnan ya bi bayan mahaifiyarsa, can ba jimawa ya fito rai babu dad'i.
"Rufe kofar Ummi."
Ya fada batare da ya kalleta ba hankalinsa na kan hanya da alama Mamin bata ba shi fuskar sanin damuwarta ba. Itama ta rufe jiki babu kwari ta koma dakinta.
   
  Daren daga Adnan har Ummi babu wanda ya yi bacci isashshe, gaba daya hankalinsu ya tafi ga Mami wacce basusan dalilin damuwarta ba. Hakanan ta yi abinda shi Adnan tun tasowarsa bai ta6a gani ba, wato ta baro sashen Abba aranar (duty) dinta, abu ne da bai ta6a faruwa ba saifa a yau. Itama Ummi abinda ya dauremata kai kenan, domin tunda take agidan tsawon wata daya da kwanaki bata ta6a ganin Mami ta kwana a sashenta ba alhalin Abba na garin kuma itace da aiki. 
    Inaga mai gayya mai aikin, wato Mami, wacce kwana ta yi tana kuka tana kai kukanta ga Mahaliccinta. Ta kasa zaune ta kasa tsaye, idan ta runtse ido babu abinda ke fad'omata a rai sai tsawan da Mijinnata ya dakamata a sadda ya nufeta da niyyar runguma ya rarrasheta ya nunamata dazun da gaske ya ji wari da baisan dalilin wanzuwarsa ba a tattare da ita. Yana jin warin kuwa ya tureta da k'arfi gami da jan tsaki. Ta matso da nufin tambayar ko lafiya, ya yi azamar matsawa gefe gami da dakamata uban tsawa akan kada ta kuskura ta k'araso inda ya ke. Haka ya kyaleta ya fice daga dakin, ta jima anan tana kuka, har ta ji maganarsa inda ya ke bata umarni kan ta fita zai kwanta. Haka ta tashi ta fito nan ma hancinsa a toshe har wani runtse ido.
  Haka ta k'araci zamanta a falo, ganin babu Sarki sai Allah yasa ta mik'e ta bar masa sashennasa.
   Mami ta numfasa ta kwanta lamo saman filo, a iyakar rayuwarta da Muhammad, matsala makamancin haka bai ta6a shiga tsakaninsu ba. Kullum cikin yabonta yakeyi musamman a 6angaren kwalliya da tsafta. Ayau ga wani sabon lamari ya 6ullomata.
     
  Washegari da

Please Login or Register in order to submit comment