Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka fi kama da abokansa, a hannunsa kuwa, wata kyakkyawar yarinya ce wacce bata fi shekaru uku ba tana bacci saman kafad'arsa. Har aka tashi daga wajen babu Faruk da Babban Yaya. 
     Duk da irin gajiyar da Ummi ta kwaso, wannan bai hanata watsawa jikinta ruwa ba kafin ta chanja sutura ta kwanta.
                      ☆☆☆
  Washegari ya kama ranar da za'a daura aure da kuma yini. Tun safe da mutanen dakin Mami suka farka, babu wanda ya koma bacci. Daga Maigidan har sauran yaransa maza, shirye-shiryen karyawa sukeyi su wuce d'aurin aure, yayinda Mami itama ke shirin tafiya gidan biki. Ummi kuwa, ayyukanta ta shiga yi cikin sauri-sauri bisa umarnin Mami, don kuwa a son Mami, tafiso tana can a daura aure maimakon ace bata isa ba. Itama Ramma sanin da tayi na cewar Mami da wuri zata fita ne, yasa ta shiryawa da wuri, bata da wani aiki a kanta mai yawa kasancewar yaranta sun je k'auye. Wannan karon dai Ummi ta ji maganar Amina, don kuwa ta shafe fuskarta da hoda sannan ta sanya jan baki kalar ja sai kwalli data zizara a idonta. Ita kanta tasan tayi kyau, irin kyawun da bata ta6a ganin ta yishi ba, ko don ba kwalliyar takeyi ba? 
  Ankon bikin da Mami tayi musu ne a jikinta, ya zauna d'abas kamar a jikinta aka d'inkashi, ya fito da kyakkyawar surarta wanda ita kanta batasan tana da diri mai kyau ba kamar haka. Har ta dauki mayafi ta yafa sai kuma ta ga sam ba zata iya ba, hakan yasa ta janyo farin hijabinta wanda ya hau sosai da atamfarta mai adon fari da koren fulawoyi. Kiran da Mami ta kwalamata ne yasa ta amsawa da sauri don bata da masaniyar cewa Mamin ta shigo falon domin itace a fadar Alhajinsu. 
  "Masha Allah." Shine furucin da Ummi tayi a ranta, duk iyakar yanda take ganin ta fito tayi kyau, sai ta raina shigarta ganin shigar Mami, ba irin ankonta bane a jikinta. Wani tsadadden  leshi ne ruwan madara mai duwatsu dinkin doguwar riga da zani ta sanya, anyi aiki a gaban rigar leshin wajen kirji, banda kamshi babu abinda kakeji yana tashi a falon. Hannunta rike da jaka da mayafinta. Ta dubi Ummi duban tsaf kafin cikin sakin fuska tace. "Ashe dai kin iya kwalliya." Abin  ya bawa Ummi mamaki, kodayake dai tasan yau Mami cikin farinciki take. Ramma dariya tayi kawai, itama tayi tsaf da ita tana rike da karamar jaka na kaya wacce ta tabbatar na Mami ne.
   "Shiga ki cewa su Hajiya Binta idan sun shirya su fito mu wuce."
  "Toh." Sannan ta kama hanya da mamakin wannan irin iko na iyayen gida irin Mami, wato bata damu da ta sanarmusu su shirya ba tun farko saida ta tashi tafiya. Sashen Hajiya Binta ta soma zuwa, a zaune ta sameta tana latse-latsen waya ko wanka batayi ba. Ciki-ciki ta amsa sallamar Ummi, gabanta na dukan tara-tara, ta durkusa ta shaida mata sak'on Mami. Kamar ba zata ce komai ba saidai ta dubeta a wulakance har saida ta ji ta muzanta.
     DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
     
     20
  
  Ta sauke ajiyar zuciya, gami da zame jiki ta durkusa a wajen. Yau Faruk ne yayi mata murmushi? Sai tace tun zuwansu bata ta6a ganinsa cikin fara'a haka ba. Mai yiwuwa saboda farincikin bikin dan uwansa ne. Jin da tayi ana ihu da shewa daga falon ne yasa ta saurin mikewa itama ta samu dama dakyar tana lek'e. Turare ta gani wata tsohuwa cikin wadanda suka zo daga Adamawa tana ta fesawa Ango da Amarya. Masu hoto suna faman yi, Faruk na daga hannun kujera zaune agefen wata mace da bata fi shekaru ashirin da bakwai ba, wacce itama cikin bak'in Adamawa take. Sai hira sukeyi suna dariya. Sunyi kama kwarai, kana gani ko ba'a fada ba kasan jini d'aya suke. Haka dai aka gama hotuna, Ango Haidar da tawagarsa suka fita. Wannan karon banda yayyun Haidar da Faruk, su kam zama sukayi ana gaisawa da hira da 'yan uwa. Tana ji anata yiwa Faruk tsiya akan shima ya dace yayi aure, abin banda dariya babu abinda yake ba shi, domin shi dai har kawowa wannan lokacin bai ga matar da ta kwanta mishi a rai ba har yakejin cewar zai iya aurenta. Duk cikin masu nuna masa kauna da so, duk cikin masu yi kishi tallar jikkunansu batare da sun buk'aci ko sisinsa ba, babu wacce ya ta6a yiwa kallon rahma. Asalima wannan d'abi'ar gaba daya haushi take ba shi wai ace mace ke tallatawa namiji kanta, yana daukar hakan a matsayin rashin aji da sanin darajar kai. 
   Dakyar ya samu ya silale ya fito daga falon, Ummi ta bi bayansa da kallo sannan ta maida hankali ga tsoffin dake faman shige da fice suna rabon abinci. 
  "Ummi." Ta ji muryar Amina a kanta. Wani sanyi ya mamayeta, ko babu komai zata samu abokiyar hira. Ta zaro ido tana murmushi.
  "Anti, kinga kuwa yanda kikayi kyau? Masha Allah." Ta harareta kadan
  "Lallai ma Ummin nan, wallahi ban kaiki ba, kinga yanda kikayi kyau kuwa yau?" 
  Ummi ta girgiza kai. 
  "Ban kaiki ba Anti."
Amina ta dara gami da jan hannunta.
  "Taso mu zagaya baya, tun dazu ai ina can."
   Ummi ta mike suka zagaya. Babban fili ne mai shuke-shuke, nan dinma akwai mutane saidai ba kamar cikin gidan ba, kusan ma yanmata sunfi yawa anan. K'asan wata bishiya suka zauna asaman kujeru inda wasu yara biyu da Mace rike da yarinya wacce bata fi watanni uku ba suke zaune. Ummi ta hango kamannin matar sosai da Amina, hakan yasa ta gaisheta, cikin sakin fuska itama ta amsa. Amina ta dubi yaran. 
   "Ahmad, ja  Kulsum ku tafi wasa Antinku ta zauna."
  Ba musu yaron ya amsa sannan ya mike suka bar wurin, daman sun k'agu su tafi wasansu amma ta hanasu da cewar sai sun ci abinci. 
   Bayan sun zauna Amina ta kalli 'yar uwarta wacce daga ita sai ita a haihuwa. 
  "Anti Hauwa, wannan itace Ummi da nake baki labarinta. Ummi wannan itace yayata Anti Hauwa, daga ita sai ni a wajen Innarmu. Babbar yayarmu Anti Fiddausi tana Katsina, acan take aure. Yaranta biyu, da Kulsum da kuma wannan bebin, Anisa. Ahmad shine auta wajen Innarmu."
  Bayan ta kai aya, Anti Hauwa ta sanya dariya.
  "Toh 'yar jarida, oh Amina." Ta karashe tana kama ha6a, abin sai ya bawa Ummi da Amina dariya.
   Anti Hauwa ta dubi Ummi fara'arta ta k'aru don kuwa babu abinda Amina ta 6oyemata dangane da Ummi.
  "Sannu Ummi, fatan kina lafiya?"
Ummi ta gyada kai gami da sakin kyakkyawan murmushinta. 
  "Lafiya kalau Anti. Ya wajen su Inna?"
  Abin ya yiwa Anti Hauwa da Amina dadi.
  "Inna tana lafiya, taso ta zo amma matar kaninta bata ji dadi ba, ta je dubota. Watakil daga can tayo nan."
  Ta gyada kai gami da yi mata fatan samun lafiya.  Nan kuma hira sosai ta 6arke tsakaninsu. Anti Hauwa da Amina suka gangaro kan batun Saurayin Aminan, Bello wanda ya matsa akan shi zai turo magabatansa. Anti Hauwa ta bata shawara akan ta sanarwa Inna idan yaso sai a had'ashi da wani ya rakashi har can Nijar su gaisa da yan uwan mahaifinsu. 
  Haka suka tsayar da shawara.
  Sun wuni tare, Anti Hauwa sai bayan la'asar ta bar gidan, Hajiya Mama harda bata kudi tayi na mota. Dakyar ta kar6a don mutunci da karamci irin na Hajiya Mama har yana so yayi yawa, mace ce da babu ruwanta. Harda kayan rabo ta had'a ta bata, ta sanya aka yiwa Inna (takeaway) na abincin biki tace ta kai mata domin ba wani nisa ne tsakanin gidansu Inna da gidan Anti Hauwa ba. Ta kar6a da godiya. 
  Tafe suke gaba dayansu da Anti Hauwa da Ummi da Amina, wadanda suka yo mata rakiya don ta samu abin hawa, kasancewar babu laifi akwai 'yar tazara tsakanin gidan da babban titi. Ummi na rike da Anisa wacce ke faman kalle-kalle idanunta tarr a bud'e. Yarinyar ta shiga ranta, haka kawai ta ji tana kaunarta ko don bata ta6a ganinta rik'e da yarinya k'arama haka bane? Oho. 
   A farfajiyar gidan, samari ne da d'aid'aikun yanmata suna hira, daga ganinsu kaga yan uwan juna. Suka wucesu suka fita. 
   Suna tafe suna hira a haka har suka iso titi, bayan sun samarmata d'an sahu, ta shiga sukayi sallama. Ta dubi Ummi da murmushi mai bayyana hakora a saman fuskarta.
  "Toh Ummi, sai na ganki a gidana wataran ko?"
  Ummi ta amsa da toh tana maida martanin murmushin. Suka juya tare da Amina suka kama hanyar komawa. A hanyar ma hira sukeyi, Amina na yi mata korafi akan ita ko dan fita unguwa bata tambayar Mami ne? Ummi ta ta6a baki kadan.
  "To Anti wa nake da shi a garinnan?"
  "Kina da mu, wataran ki tambayeta kizo na kaiki wajen Innarmu ku gaisa."
  Murmushi Ummi tayi wanda yayi daidai da giftawar wata farar honda mai bakin gilasai ta gabansu.
  "Wannan kamar motar gidan su Alhaji." Cewar Amina kenan. Ummi da batasani ba ta bi motar da kallo kawai wacce ta koma tafiya sannu-sannu tamkar matuk'in baya so. Kafin daga bisani ya fisgi motar ya k'ara gudu. 
  Ai kuwa kamar yanda Amina ta fad'a haka dinne, don suna isa kofar gidan suka iske motar a fake, na cikin motar baikai ga fitowa ba saidai kafarsa d'aya da ya fiddo waje. Ta madubin hannun kofar, Ummi ta hangeshi. Kansa a jingine jikin kujera yana amsa waya. Akayi katari suka had'a ido, gani tayi ya yafito ta da hannu. Abin ya bata tsoro, gabanta ya hau dukan tara-tara. Tayi saurin dauke idanunta don bata gaskata hakan ba.  Har zasu shige ciki ya danna hon.  Wannan ya sanyasu dakatawa.
   "Da ku ake." Cewar Maigadi. Amina ta dubi motar, saidai bata hangi ko wanene ba sakamakon duhun gilashin. Suka zagaya suka isa ta mazaunin direba, idanunsa akansu, suka durkusa a ladabce suka gaisheshi. Yaya Faruk ya dago kanshi ya dubesu da idanunsa masu tafiya da dukkan wata diya mace mai lafiya da zata kalleshi. Ya gyad'a kai kafin ya maida dubansa cikin motar, hannu yasa ya janyo leda bak'a babba ya mik'awa Ummi.
  "Ki mik'awa Hajiyata." Ta sanya hannunta dake faman rawa don gaba daya wani kwarjini yayi gareta, ta kar6i ledar wanda bisa kuskure hannayensu suka gogi juna har ta gogi tattausan gashin dake kwance a hannunsa, a gigice ta dauke hannunta had'i da kar6ar ledar tana mai amsawa da toh wanda bai fito sarari ba saidai kawai le66anta da ya nuna alamun hakan. Baice uffan ba har suka fice ya bisu da kallo, ya lura yarinyar kamar a tsorace take da shi. Ya dan ta6e baki cike da mamaki, mamakin bai wuce na ganin yara kyawawa haka ba ace wai suna aikatau ba karatu ba, tabbas ya tausayamusu. Ya kuma raina iyayensu wadanda tunaninsa yafi ba shi cewar kwadayin abin duniya ne kawai yasa suke sakin yaransu sakaka suna yawon gidajen mutane don bauta da neman kudi wanda duk yawan abinda zasu samu bazai haura dubu goma ba, aganinsa wannan cutar da rayuwarsu ce kawai. Ya lumshe ido, ya jima a haka kafin ya maida kafafunsa ciki ya rufe kofar gami da yin ribas yabar unguwar.
              
DAN ADAM
  @RUFAIDA OMAR

  21
   Acan kuwa Ummi kasa shiga ciki tayi haka kawai bata son shiga cikin mutanen gidan, tana jin nauyinsu. Amina ce ta kar6a ta mik'awa Hajiya Babba sannan suka koma inda suke. Sai misalin karfe bakwai kowa ya soma shirin tafiya wajen (Party) wanda Ango ya shirya na musamman da iyayensu da yanmata da samari. Abin har ya bawa  Ummi mamaki, aganinta wannan kawai rashin sanin abinda za'ayi da kudin ne, ko kuma dai kudin ne suka yawaita garesu. Tana gani Amina tayi mata sallama suka wuce sakamakon yara da zata kula dasu a gida kafin dawowar Hajiya Maman. Ummi ta dubeta.
  "Nima na tabbatar yanzu zamu wuce ko don Ramma."
  "Wace Ramma? Ramma ai ta tafi gida tun dazu tare da su Hajiyar Iklima. Baki ga su Iklima sunzo dazu ba?"
  Ummi ta zaro ido.
"Aa banma gansu ba wallahi, na tabbatar Mami ta manta ne da ta had'a tafiyata da su. Toh yanzu wa zan bi?"
Amina ta jinjina kai.
"Mamin ce zata barki ki tafi da kishiyoyinta? Wasa kike ma. Na..."
  "Ummi, kizo inji Mami." Suka tsinci muryar Fahad wanda yayi sanadin katse Amina daga maganarta. Ta dubeta.
"To saida safe, nasan kuma mu da kara haduwa ba yanzu ba." Sukayi sallama Amina ta wuce. 
  Ummi tana d'ari-d'ari haka ta daure ta shiga falon, Mami na daga zaune wata tana d'aura mata d'ankwali.
Ta gaida mutanen falon sannan ta koma gefen Mami. 
  "Gani Mami." Mami ta dan dubeta.
"Ramma ta riga ta tafi, nikuma da wuya idan zan dawo ta nan gaskiya don gaba d'aya zamu tafi can wajen party, ki zauna a inda zan ganki idan mu  fito."
  "Toh Mami."
  Daga haka tayi gaba, tana ji wata tana zolayar Mami wai da alama ita bata iya rayuwa saida 'yar aiki, har sauran suna dariya. Suna tsokanarta wai sai kace itace autar innartasu.
    Ummi ba haka taso ba, don alal hakika ita zuwa wajen wani party ko waje mai hayaniya baya burgeta, da ace Mami zata barta anan da ta zauna har zuwa lokacin da zasu ci su cinye su dawo su tafi. Ta dubi jikjnta bayan wucewar wasu yanmata da suka dauki ado cikin wani leshi yellow da nadin kai ja, ta yaya ma zata shiga taron jama'a da kayan nan? Ta tabbatar ita kadai zata bambanta acikinsu. Ta langa6ar da kanta, kodayake daman ita din ba kowa bace face 'yar aiki. Bata da wani daraja, babu wani wanda zai ra6eta da sunan kauna ta jini ta yan uwantaka, shiyasa take matukar kaunar Amina, ta tabbatar su Amina  suna kaunarta saidai bata da sa'ar 'yan uwa. Batasan halin da suke ciki ba a yanzu, da ace ma zatasan dangin mahaifiyarta, lallai da ta kai kanta garesu komin nisan dake tsakaninsu. Ta sauke ajiyar zuciya kafin kuma da saurinta ta share hawayen da suka zubomata.
  Ko mintuna biyar batayi ba awajen, Mami ta aiko kiranta, kaya ta dunga kwasa tana kaiwa boot din motarsu, sannan ta zauna a motar tare da Fahad da wasu iyaye matan, Mami na fitowa suka wuce wajen party. 
     Tun a farfajiyar otel din Ummi tayi bala'in raina kanta. Ta sauke ajiyar zuciya gami da sakin baki galala tana kallon yanda wajen ya k'ayatu, anyiwa wajen adon fulawoyi wadanda sai buso sanyi sukeyi, hakanan kuma wajen sai kamshi yakeyi. Daga can ciki kana jiyo tashin kid'a. Wadanda basu shiga ba suna tsaitsaye a farfajiyar wajen. Haka suka dunguma zuwa ciki. Sanyi ba bak'on Ummi bane don tun bata saba shan sa ba a falon Mami, har ya zamana yanzu ta saba. Wajen kowa ya dauki kwalliya. Matasa masu ji da ilimi da gayu sai kuma iyaye wadanda kallo daya zakayi musu ka tabbatar cewa kud'i sun riga sun gama jik'asu. Zugwui-zugwui take bin bayansu Mami, gaba dayanta a d'arare take, gani takeyi kamar kowa awajen ita ya zubawa ido. Idanunta suka cika da kwalla, bata saba da irin haka ba. Tunaninta ya katse sadda ta ji an damki hannunta. Ta juya da sauri, Ihsan ta gani ta ci ado har ta gaji da haduwa, saidai fuskarta a murtuke. Bata ce mata uffan ba ta soma janta, gaban Ummi na faduwa haka ta bi bayanta har zuwa d'an (Corridor) na shiga dakin taron. 
  "Uban wa yace ki shigo? Kalleki kiganki, typical 'yar kauye, wallahi kika yi kuskuren shigowa wajennan sai na miki wulakancin da baki ta6a zato da tsammani ba. Shegiya kawai marar galihu!" Daga haka ta ja tsaki tayi gaba ganin mutane sun nufo hanyar shigowa. Ummi kuka ya taho mata, da saurinta ta juya zata fita, ta bawa mutanen hanya suka wuce ta bi ta gefe ta fita da gudu-gudu. Kai tsaye ta wuce bayan motoci inda babu  mai ganinta ta durkushe ta soma kuka mai shiga rai. Kuka sosai takeyi, lallai ta k'ara gaskata cewar halayen DAN ADAM sun bambanta. Ta gaskata cewar ita din ba wata bace face marar galihun kamar yanda Ihsan ta jaddada mata. Kaiconta! Kaicon rayuwarta! Ace mahaifinka ya bude baki yayi furucin cewa ko bangon duniya za'a kaika, ba matsalarsa bace, baka da wani makusanci mai kaunarka, daga dangin mahaifin harma da shi kansa mahaifin. Takan rasa abinda ta yiwa mutane, wai meyasa dangin mahaifiyarta bazasu nemeta ba? Ta tabbatar koda duniya ta k'i ta, su bazasu ta6a gudunta ba, ta tabbatar zasu bambanta da sauran 'yan adam din da ta sani kuma ta rayu da su. Tana fatan su zamto irin Amina da su Anti Hauwa, tana fatan su zamto masu nunamata so da kauna ta gaskiya. 
   DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

22
   K'arar rufe motar da ta ji ne yasa ta saurin mik'ewa a firgice. Ido hud'u sukayi, kallonta yake cike da tsantsar mamaki, yayinda ita kuwa take mishi kallo tamkar wacce ta ga wani dodo. Gaba d'aya tsoro takeji kada ya bud'emata wuta akan me takeyi anan. Ta sunkuyar da kanta tana duban motar, sai lokacin ta lura cewa motar da suka ganshi dazu a ciki ce. 
  Kamar yayi mata magana, saidai ya fasa ya juya ya soma tafiya. Ta mike ta bar wajen ta soma tafiya kai tsaye ta nufi k'ofar fita daga Otel din. Kamar ance ya juyo, ya ganta. 
   "Ke!"
Ya fad'a a sannu yanda yasan zata ji don ba wani nisa tayi ba. Ta juya gabanta na fad'uwa. Sai lokacin ta lura da shigarsa, ya had'u karshen haduwa, a yanzun yana sanye da shadda ruwan kasa mai duhu wacce aka yiwa dinkin da ya zauna daidai a jikinsa. Takalmi da hular da ya dora ma su kansu abin a kalla a k'ara kalla ne. A haka har ta karasa wajensa ta durkusa. Ya bata umarnin ta mik'e. Bayan ta mike ya kare mata kallo sannan ya jefota da tambaya.
  "Ina zaki?"
  Ta soma rawar murya.
  "Gi..da." Ya yamutse fuska.
  "Ke kika kawo kanki?"
  Ta girgiza kai.
  "To shiga ciki."
  Tunanowa da maganar Ihsan yasa ta soma zubar hawaye ta dubeshi da jajayen idanunta wadanda kuka ya maidasu hakan, sai lokacin shima ya lura da su. 
   "Kayi hakuri Yalla6ai, bazan iya shiga ba."
  Shiru ya biyo baya ayayinda ya kafeta da ido yana kallon fuskarta. Haka kawai sai ya ja guntun tsaki.
  "Akan wane dalili?"
"Ih..ih.san tace kada na shiga zata wulakantani."
   Ya ji wani abu a ransa, sai kuma ya cije le66ansa na kasa.
  "Ko menene ku kuke jawowa rayuwarku, da ace kun hakura da yanayin rayuwa, kun godewa kad'an din da kuke samu a gidajenku, da babu abinda zaisa kuzo ana wulakantaku ana baku tamkar wasu karnuka."
  Batasan sadda ta cigaba da 6ul6ulo da ruwan hawaye ba. Ta so tayi shiru ta barwa zuciyarta amsa, saidsi ta tsinci kanta da kasa aikata hakan.
   "Ka gafarceni Yalla6ai, saidai akwai lokutan da ba'ason ran mutum yajr aikata abinda ya aikata ba. Akwai tilastawar rayuwa, wani ba shi da yanda zaiyi ne, sai yaga da yaje ya aikata abin turr gwara ya gwammace ya rufawa iyayensa da kansa asiri ta hanyar nema ta halal. Wani kuwa, rashin gata da rashin samun kulawar yan uwa ke sanyashi tsintar kai a halin da yake ciki. Kowane bawa da yanda Allah Ya tsaro rayuwarsa, ba mu muka za6awa kanmu wannan rayuwar ba. Akwai KADDARA."
  Daga haka ta juya da sauri-sauri ta bar wajen gami da nufar get, batayi wata-wata ba ta fice daga wajen batare da tasan inda ta nufa ba, burinta kawai tabar wajen ko ranta zaiyi sanyi....!
       

  Ta dubi sararin samaniya, hasken farin wata ya taimaka kwarai wajen k'ara haskaka unguwar, hakanan kuma akwai hasken fitili domkn unguwa ce ta manya. Ta numfasa ta soma bin hanyar da taga Danliti ya biyo da su dazun. Tafiya kawai takeyi batare da tasan takamaiman inda zata nufa ba bayan nan, hakazalika batajin ko son ta koma wajen walimar. Ta gwammace idan ma saceta ayi muddin za'ayi nasarar rabata da wajen nan. Ita kam ta tsani cin zarfi da disgi. Tayi nisa amma ba sosai ba, ta ga mota a gefenta tana tafiya sannu-sannu, wannan baisa ta tsaya ba ballantana kuma ta waigo. Ta ji k'arar hon da k'arfi, ta runtse ido tana mai cigaba da tafiya kai ka rantse Ummi tsabar yanga ce takeyi, ga wanda ya santa kuwa yasan tafiyarta ce hakan, saidai duk da hakan na yau yafi na kullum don tana taku ne jikinta babu laka, gaba daya a sanyaye yake, zuciyarta banda bugu da sauri-sauri babu aikin da takeyi. 
   "Ummi."
Taji faduwar gaba jin muryar Yaya Faruk. Ta waigo da sauri ta dubi motar, kasa jure kallon kwayar idanunsa tayi masu kyau da fisgar hankali tayi gefe da idanunta batare da ta cigaba da tafiya ba. 
   "Shigo."
  Ta daure ta kara dubansa tana mai share hawayen da suka zubomata, girgiza kai tayi.
  "Kayi hakuri Yaya Faruk, bazan iya komawa..."
  "Gida zan kaiki." Ya katseta da fad'in hakan. Ta danyi jim, tana tsoron kada Hajiya tayi fad'a saidai kuma ta gwammace fad'an Hajiya da dai ta k'ara komawa wajen da ba'a dauketa a bakin komai ba face wulakantacciya. Jiki babu kwari ta sanya hannu zata bud'e gidan baya, ya rigata bud'e na mazaunin gefensa.
   "Nan za ki shigo." Gabanta ya fad'i. Ta kasa cewa komai duk kuwa da cewar ta raina aji, matsayi da kuma girmanta ace wai itace zaune agefen matashin da ya had'a dukkan wadannan abinda takejin ita din bata da shi, abin kamar dai a mafarki. Da bismillah a bakinta ta shiga ta rufe a sannu, ajiyar zuciya ta saki jin wani azababben kamshi ga kuma sanyin Ac da ya ratsa jikinta. Ya soma tuk'i cikin gwanancewa bayan ya maida gilas ya rufe, ya k'ara k'arfin Ac kad'an. Saida suka bar layin gaba daya sannan ya rage gudun da yakeyi ya soma magana tamkar baya so, magana mai cike da nutsuwa da kasaita.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  23
   "Bansan da haka ba, idan ma nasani toh watakila zuciyata ce wacce ke jin tsananin tausayi yaran da kuma jin haushin iyaye masu barin yaransu yawan aikatau, ya sanyani kasa nutsuwa nayi tunani mai kyau akan haka. Akan abinda na fad'a, ina neman afuwa, kiyi hakuri kinji?"
   Ya karshe yana k'ara k'ank'an da muryarsa tamkar mai rad'a. Wannan yasa zuciyar Ummi cigaba da harbawa da sauri-sauri. 'Nayi hakuri fa yace?' Ta tambayi zuciyarta, ta lumshe ido ta bud'esu, ashe daman masu kudi sukan yi laifi kuma su bawa 'yan aikinsu hakuri? Ikon Allah. 
   "Kinji?" Ya k'ara furtawa cikin kara kankanta murya, sai kuma alokacin ya dubeta. Gani yayi fuskarta ta yi fayau, hakanan idanunta sun d'an kumbura adalilin kukan da ta ci. Haka kawai ta ga ya gangara gefen titi ya tsaya. Tayi duba da wajen, wajejan gidan gwamna ne na garin Kano, abinda yasa ta rike hakan ma bai wuce adalilin Fahad da ta ta6a ji ya fad'a ba. 
    Ta dubeshi kad'an, shima ita ya fuskanto. Ta kauda kai tayi narai-narai da fuska tamkar mai shirin yin wani kukan.
  "Na hakura, ni daman banyi fushi ba. Ni wace da zanyi fushi da.."
  "Ni d'in wanene da na fi karfin ayi fushi da shi?"
  Ya katseta ta hanyar jefomata tambayarnan. Tayi kasa da kanta batare da tace uffan ba. 
   "Ni ba kowa bane face DAN ADAM, kuma duk dan Adam ajizi ne, yakan kuskuro, wani da saninsa wani kuma baisan ma kuskuren bane. A rayuwa, bani da raayin shiga lamuran da bai kasance matsalata ba, ban fiye damuwa da shiga rayuwar mutane  har ma na takura musu ba ok? Abinda ya kaini har nayi miki batun bai wuce na fusata..."
  Sai kuma yayi shiru bai k'arasa ba.
  "Kiyi hakuri." Shine abinda ya k'ara furtawa. Cikin rawar murya Ummi ta share fuskarta wanda zuwa yanzun batasan dalilin kukannata ba, ta dangana da tuna mahaifiyarta da tayi wacce kokusa bata ta6a jin dumin jikinta ba. 
  "Ya wuce Yalla6ai, don Allah ka daina bani hakuri."
  Ya zubawa fuskarta ido kafin ya saki murmushi mai 6oyayyar fassara. 
  "Thank you." Daga haka ya soma tafiya, tana jin wayarsa na faman ruri. Duk bai dauka ba, sai ana uku ta ga ya dauka. Haidar ne, hakuri ya shiga ba shi ya sanarmishi wani uzuri ne ya hanashi karasowa da

Please Login or Register in order to submit comment