Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Idanunta sunyi masifar budewa wanda hakan nai ta6a damun Hajiya Binta ba, acewarta, idan bata kasance wayayyiyar ba, a ina har zata samarwa kanta miji dan zamani. 
      Acan kuwa su Baraka suna shiga Iklima ta rungume Baraka tana ihun murna don sosai kawarta ce, kusan halinsu yazo d'aya na son gayu da samari. 
  "Shegiyar gari, daman kinzo shine ko ki nemeni?"
  Baraka tana dariya tace "Afuwan tawan, kinsan tun dazu na so shigowa Allah baiyiba, ina su Yaks?"
  Fad'in haka yasa ita da Ikliman suka tuntsire da dariya ita dai Ihsan ta zama 'yar kallo, ko ita da suke tare da Ikliman basu hira mai tsayi har haka, lallai ba karamin sabo Baraka da Iklima sukayi ba.
   "Yana inda yake, kwana biyu munyi fad'a ma, zan baki labari kedai. Ina mijina?"
  Cewar Iklima tana mai kashe mata ido d'aya, Baraka ta ja guntun tsaki tana dariya. Ta fahimci Faruk take nufi, tun daga sau daya da ta ga ta dora hotonsa a dp lokacin shi kuwa yana gani ya shigo har dakinsu ya hauta da fad'a har yakai ga mangarinta, yace tayi gaggawar goge dukkan hotunansa a wayarta. Daga ranar bata kara dora hotonsa. Daga ranar Iklima ta makale akan lallai ita fa sai ta hadata da shi, hakuri kawai ta bata ta gwadamata Faruk sam ba irin nasu bane don ba shi da wannan rawar kan akan mata.
   "Kedai ki kama kanki baruwana na gayamaki."
  Cewar Baraka. Iklima tayi dariya.
  "Ina ruwanki? Bazan kama ba sai randa kika bani lambarsa."
  Ihsan duk bata fahimci komai ba saida ta ji Baraka na fadin.
  "Kizo muje da kanki ki tambayeshi, ga shi can a waje." Ai sai Iklima ta zaro ido.
  "Dagaske?"
"Wallahi." Cewar Baraka cikin dariya, tuni ta ja dankwalinta ta rufe kanta, daman riga 'yar kanti ce a jikinta sai siket ruwan madara na leshi da dankwalinsa.
  "Muje wallahi na gaisheshi na tambaya."
  Suka kamo hanya Baraka cikin dariya ta na fad'in.
"Kamar gaske, bakisan wanene Yaya Faruk ba wallahi."
  Gaban Ihsan ya fad'i, me Baraka ke nufi? Wato Iklima batun Faruk take? Aikuwa ba zata sa6u ba, saidai su yi BIYU BABU. Muddin ita bata samu soyayyarsa ba, to babu wata ta jininta da zata samu, ta gwammace ya je ya auri bare akan tana ji tana gani ya auri wata jininsu. A ganinta, itama fa tana da aji, ba zai yiwu ta zauna wani namiji na sha mata kamshi ba, ta tsani dukkan wani namiji mai ji da kansa, baruwanta da kyansa, idan kyau ne, akwai wadanda suka fishi da suka nuna suna sonta tana sha musu kamshi. 
     Anan kofar shiga sashen Alhaji Modibbo suka ga takalman Mami da Hajiya Babba, wannan ya tabbatar musu suna ciki. Da rawar jiki Iklima take tafiya, Allah-Allah takeyi ta had'u da Faruk ko don shima yasan da zamanta. Ta tabbatar ba kowane namiji ne zai iya dauke idanu daga kanta ba. Haka suka karasa bakin motar, alokacin Haidar da Adnan ne kawai tsaye sai Ikram wacce ta jingina jikin mota tana danne-dannen waya. Iklima suka gaisa da Haidar, Adnan sai dauke kai yakeyi. Itama bata bi ta kansa ba ta dan lek'a motar, kasancewar akwai wadatar haske a farfajiyar gidan hakan yasa ta hangi Faruk dake zaune a mazaunin direba ya d'ora tafin kafarsa akan kujera, kansa jingine jikin kujerar yayinda kunnensa ya sanya (Earpiece) yana shan sauti. Idanunsa a lumshe. Wani wawan ajiyar zuciyar Iklima ta saki, ta ko'ina Faruk ya had'u. Ta gaida su Yaya Usman suka amsa mata fuska a sake kafin tayi ta wajen Faruk tana gaisheshi. Ko kusa baisan ma tana yi ba saida Usman ya cire mishi kunne d'aya na (Earpiece) sannan ya juyo da rinannun idanunsa, da alamu ma bacci ya soma.
   "Au bacci kakeyi ma? Ana gaisheka." 
"Ina wuni." Ta k'ara fad'a. Ya juyo ya zubamata idanu, ai ji tayi kamar ta saki fitsari tsabar yanda kallon ya kad'ata, duk inda take zaton Faruk a kyau da komai, ya wuce nan. Kansa kawai ya gyad'a mata sannan ya dauke kai. Ji tayi ta kasa koda kwakkwarar magana, to ta ina ma zata iya furta mishi wani abun har ya kai ga tambayar lambarsa? Ba zata iya ba, hakan yasa ta koma ga su Baraka wadanda ke yi mata dariya har Ihsan wacce ba karamin dadi abin ya yi mata ba. 
     "Wace ne?"
  Faruk ya tambaya ba tare da ya bud'e idanunsa ba.
   "Iklima, step-sister dinmu." Cewar Adnan. Ya yamutse fuska.
  "Har yanzu Hajiya bata fito ba? Wallahi na soma bacci."
  Kafin waninsu yayi magana, sai ga Mami da Hajiya tafe suna hira, Yaya Ridwan ne yayi magana.
  "Ai idan iyayenmu mata suka had'u wallahi har mamaki suke ban, ko kusa basu kaunar rabuwa da juna."
  Faruk da Usman suka d'an dara, kamar ba zasu karaso ba haka suke tafe suna hira. Ganin dai da gaske basu da niyyar tahowa ya sanya Faruk dannan hon, wannan ya maido hankalinsu wajensu. Ya koma can gefen mazaunin direba yana fad'in.
  "I can't drive wallahi, bacci ya soma kama idona."
  Haidar ya bude mazaunin direba ya shiga yana fad'in.
  "Ai nayi mamaki ma da ka iya kaiwa war haka, kodayake na dole ne. Mutumin da wani sa'in takwas ma yayi bacci."
  Murmushi kawai Faruk yayi ya kara lumshe idanunsa sannan ya budesu. Hajiya Babba ta karaso ta shiga, ganin haka yasa yanmatan sallama da juna, bayan shigarsu Iklima ta zubawa Faruk ido kamar ta had'iyeshi, tsaf ya lura da kallon da take jifansa da shi, wannan yasa a sannu ya zuge gilas wanda ya kasance mai duhu, shi ya yi mata katanga daga dubansa. Ta sauke ajiyar zuciya, ta juya ta kama hanyar ciki bayan ta gaishe da Hajiya Babba, sun kara sallama da Baraka. 
                     
                     
   "Maganar banza ce kikeyi, wacce ba zata ta6a kasantuwa ba matukar Binta na raye wallahi. Da kinsan yanda nake kishin Madina da danginta, da baki soma tunanin son Faruk ba Iklima."
   Cewar Hajiya Binta tana faman hura hanci fuska a murtuke kamar bata ta6a bud'a hakoranta ba don dariya. Iklima ta tur6une fuska tana kunkuni ta mik'e ta barta tana faman bud'e wuta. 
   "Eh lallai, gwara tun wuri na tashi tsaye kafin kema ki rikita lamurana, shawarar Hadiza zan bi."
  Ta karashe tana daukar wayarta, Hadiza ta dannawa kira sannan ta mike ta fad'a d'aki. Suka gama kulla-kullarsu akan yanda Alhaji zai shigo hannunta sai yanda tayi da shi, da kuma irin nau'ikan muguntar da za'a yiwa Madina a lalata rayuwar 'ya'yanta, itama a dusasar da tauraronta dake haskawa a idanun Maigidan da surukarsu. Haka suka ajiye wayar cike da jin wani nishad'i ko babu komai itama tana dab da samun matsayi babba.
   
                        ☆☆☆

 Haka rayuwa tayita tafiyarwa Ummi, yau dadi gobe babu dadi. Yawanci matsalarta bai wuce Ihsan ba don Mami matukar zata yi abinda ta sanyata to fa babu ruwanta da harkarta. A wannan halin ne wata ranar Asabar ta tashi da ciwon mara marar misali, tun tana dauriya har ta kasa, ko tashi ta kasa yi balle ta kai ga aikace-aikacenta. A wannan hali Ramma tayi sallama ta shigo bisa umarnin Mami da  ta dubo ko lafiya bata fito ba har ga Ramma ta rigata zuwa. 
   Ganinta ba lafiya yasa ta fita ta sanarwa Mami. Kafin su dawo ta soma jin ta da lema, saida Ramma ta d'agata ne suka fahimci abinda ke faruwa. Ramma ta taimaka mata bayan ta kar6o (Always) wajen Mami, ta gwada mata yanda zatayi, saida ta kimtsa sannan suka rankaya kemis da Ramma. 
   Tun daga wannan ranar Ummi ta fahimci girma ya hau ta, Ramma ta k'ara jaddada mata hakkokin da suke akanta yanzun wadanda ta riga ta sani don a makaranta duk ana koyardasu. 
  Mami bata yarda da kazantar kunzugu ba, hakan yasa ta bata (pads) cikin na Ihsan wacce ta rigata somawa tuni. Saida tayi kwanaki hud'u sannan tayi wankan tsarki. Daga wannan lokacin ta k'ara kame kanta ta zama mai kula sosai da takatsantsan musamman ma ga sallolinta. 
                   ☆☆☆
   
      A KWANA A TASHI...!
DAN ADAM
  @RUFAIDA OMAR

  12
  Daga haka bata da masaniyar abinda ya karu don kuwa tuni sun bar wajen sun sauka da niyyar dauko sauran kayan. Larai ta taimaka musu itama. Haka sukayita zirga-zirga, bayan sun kammala kawowa, suna shirin tafiya, Hajiya Mama tayi musu magana.
  "Yauwa Amina sauranku lemu da ruwa ko?"
"Toh." Amina ta amsa. 
  "Muje." Cewar Amina tana duban Ummi wacce ke tsaye. Suka nufi falon kasa, suna jin sadda Hajiya Fatima ke tambayar Inna ko Ummi sabuwar yar aikinta ce. Inna ta amsa da aa, Hajiya Mama ta sanarmata a wajen Mami take. Nan fa Alhaji ya hau fadan yawan chanje-chanjen masu aiki da takeyi. Daga haka basu kara jin tattaunawar ba suka yo k'asa suna dariya don abin ma dariya ya basu. Amina ta dubeta.
  "Kinsan wani abu kuwa? Duk fa abin su Mami, suna gudun abinda zai 6ata ran iyayensu, duk abinda suka ce suyi basa musawa shikenan ta zauna. Wallahi suna burgeni yanda suke kaunar iyayensu." Ta karashe lokacin da take kokarin bude firij.
  Ummi tana murmushi tace
"Toh Anti ai sune abin alfaharin, idan baka da mai maka fad'a ina wani jin dadi a rayuwa?"
   Amina ta jinjina kai sadda ta soma ciro lemuka tana dorawa a saman firjin. 
   "Gaskiyane kam, mik'o tire a kicin mu dora."
  Larai ta tambaya ta mikamata, ta goge sannan ta koma suka dora akai, wannan karon Ummi ce a gaba tana biye da ita, saida suka zo daidai dan korido wanda daga shi sai kofar shiga, ta ja baya ta marairaice.
  "Don Allah Anti shiga gaba."
Abin sai ma ya bawa Amina dariya, babu musu ta shiga gaba da sallama sannan itama Ummin ta bi bayanta. Ido hud'u tayi da wannan matashin na dazu, ya tamke fuska ya kauda kai, hakan da ta gani yasa itama dauke nata idanun da sauri ta cigaba da tafiya a tsanake, tuni sun soma zubawa, har Hajiya Fatima na yiwa wani cikin matasan fada akan bayason cin abinci alokacin da kowa yake ci, wanda akeyi domin shi murmushi kawai yakeyi. 
"Shiyasa fa bana sonshi, wannan idan mukayi aure mai yiwuwa nima haka zai dunga hora ni da yunwa, barni dai na lalla6a da Gadanga." Cewar Inna kenan, aka sanya dariya gaba d'aya. 
  "Kai tsohuwa, dad'ina dake kenan. Ai Faruk banda harkar neman kudi bana jin akwai abinda yasa a gaba, yanzu sai ya juya miki biyar zuwa dubu."
Cewar wani wanda ga dukkan alamu shine babbansu, don fuskarsa kadai ya nuna akwai shekaru. 
  "Yauwa Usmanu, ashe ka fahimta."
  Ummi da Amina tuni suka bar wajen, Amina na rike da Samir d'a awajen Rahila babbar d'iya ga Hajiya Madina.     
  Haka sukayita zolayarsa ko kusa bai mayar da martani ba, asalima banda murmushi babu abinda yakeyi, idan kuma abin ya wuce murmushi, sai ya dara. 
     Acan k'asa suma abinci suka ci sukayi nak, bayan sun kammala kuma sukayi zaman hira har zuwa sadda akayi kiran sallar La'asar. Sai lokacin samarin suka sauko, Ummi ta bisu da kallo kamar yanda Amina ta umarceta. Ta kara jaddada mata cikin rad'a-rad'a.
"Kinga na farkon nan mai dan jiki shine babban d'an Hajiya Babba ta Abuja, Yaya Usman yana da matarsa d'aya da yaransu uku, na biyun shine Yaya Faruk, shine autansu baiyi aure  ba, na ukun mai farar shadda shine Yaya Ridwan, shima yana da matarsa daya 'yar Ghana ce, yaransu biyu. Na karshen shine Yaya Haidar, shi ake shirye-shiryen bikinsa yanzu tare da Yaya Intisar babbar d'iya ga Hajiya Mama, bikin baifi ragowar sati uku ba."
  Wannan dogon bayanin da Amina takeyi, tuni wadanda akeyi don su sun fice saidai Ummi ta fahimta kuma ta gane, kenan dai Yaya Faruk shine wanda ta gani dazu a tsakar gidan yana waya? Ta tambayi kanta kuma ta bawa kanta amsa. Ba karshen dai Adnan ne wanda ba sai an mata bayaninsa ba.
  Koda suka idar da sallah, anan suka zauna tsakar gidan suna ta hirarsu har zuwa lokacin da samarin suka dawo suka shiga ciki banda Faruk wanda ya tsaya amsa waya acan farfajiyar gidan.
   Kiran da Larai ta kwalawa Amina yasa ta mikewa tana amsawa. Nan ta bar Ummi da Samir yaro mai shiga rai. Wasa ta shiga yi mishi, babu ruwansa sai 6angale dariya yake. Ya shiga jan dankwalin abayarta yana dariya, ta rike hannun.
"A'a Samir, daina."
  Maimakon ya daina, saima ya karasa janyewa gaba daya yana ihu da dariya, ta mike da zummar kamoshi, saidai da gudu ya shiga zagaye a wajen. Abin ya bata mamaki da dariya, a garin ta cafkoshi ganin yayi hanyar kofa, ba tsammani tayi karo da mutum har ya kai ga faduwar abin hannunsa. 
  "Bismillah." Ta fad'a batare da ta shirya ba.  Ta dago kai sukayi ido hud'u da Yaya Faruk, fuskarsa ba yabo ba fallasa. Bakinta ya soma rawa saidai ta kasa fidda ko kalma d'aya, tana so ta bashi hakuri amma batasan ya akayi hakan ya kasa fitowa ba, wani kwarjini kawai ta ga yayi mata. Ta durkusa da sauri ta dauki wayarsa da ta tarwatse ta hado mahadinta wato batir da murfi ta mik'a mishi batare da ta mike ba. Sai lokacin ta samu yin magana.
"Don Allah kayi hakuri."
  Ta fada cikin sanyin murya. Yasa hannu ya kar6a.
  "Is ok." Ok din karshe kawai ta fahimta, ya kad'a kai ya barta anan, ganin haka da sauri ta mike ta bi Samir wanda  maigadi ya cicci6o a hanya ganin zai fice, ta kar6eshi ta kuma kar6i dankwalinta ta rufe gashinta. 
  Ba su suka tashi tafiya ba sai bayan Magriba, anan dinma kamar baza'a tafi ba, don ta jima a tsaye a farfajiyar gidan bayan ta kammala sanyamusu kayayyakinsu a mota tana jiransu. Su dinma ji sukeyi  kamar kada su rabu don dadin da gidan yayi musu ganin kowa an had'u. Haka dai suka fito suka fice. Tana jin sadda Ihsan ke rok'on 'yan Abuja akan su kawo musu ziyara kafin su tafi.
  "Haba Lil, ai ba saikin rok'a ba." Cewar Yaya Haidar cikin sakin fuska. Daga haka suka rabu, Ummi ta saki ajiyar zuciya ganin sun hau titi don daman gaba daya ta gaji likis har ta ji inama a gidan suka barta bata biyosu ba.

                  ☆★☆★☆★
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

    13
 A gajiye likis Ummi take, suna zuwa sallolin dake kanta kawai tayi ta kwanta. Bata kara sanin abinda ke faruwa ba a duniyar sai bayan farkawarta da Asuba. Bayan ta idar da sallah ta zauna anan addu'o'i har garin Allah Ya waye, kasancewar babu makarantar boko ballantana ta tashi had'e-had'en karin yaran yasa ta komawa tayi kwanciyarta, baccin da tayi har ya fiye mata na farko dadi, ta jima tana bacci kafin kuma ta soma jin ana bubbuga kafarta ana kiran sunanta. Farkawa tayi a firgice tana salati, ganin Fahad yasa ta sauke ajiyar zuciya. Kira ne daga Maminsa akan ta soya mishi kwai ta had'a da biredi da shayi. Dole ta mike ba don baccin ya isheta ba ta fad'a bandaki ta wanko bakinta da fuska sannan ta bi bayansa. 
  Saida ta kammala komai sannan ta fad'a d'akinsu, ganin Ihsan bata farka ba yasa ta fitowa batare da tayi abinda ya kaita ba(wato gyaran daki). Tana gudun ta shiga bandakin don wankewa Ihsan ta yi mata rashin mutunci tace ta hanata bacci. 
   Misalin karfe biyun rana, kowannensu yayi shirin Islamiyya, kai tsaye yaran wajen mahaifinsu suka nufa sanin da sukayi cewar yana garin suka kwashi gaisuwa ya sallamesu da abin kashewa bayan makaranta sannan suka d'uru cikin mota, suka tafi. Sai lokacin ne Ummi ta samu sararin yin nata shirin na makaranta tana ta zabga uban sauri adalilin lattin da ta so yi, haka ta fito cikin shiri ta yiwa Mami sallama. Mami ta amsa gami da yi mata fatan alheri, har ranta ta ji dadi don abu ne da sam Mamin bata saba ba, alamun Mami gaba daya a yau sun nuna tana cike da nishadi wanda babu damar tambayar dalilinsa. Ta sanya kai ta fice daga gidan. 
  A makaranta nan dinma ta ji dadi sosai don kuwa ta kai haddarta saidai ta sha gyara duk da baikai yawan yanda a baya Malamin nasu ke cin gyaranta ba, ta lura yana yi mata uzuri ganin ko bak'i bata iya had'awa ba, wannan dalilin yasa ya ware mata lokacinta daban yake koyar da ita wasula da bak'ak'e. 
   Koda suka tashi, cike da nishadi ta dawo haka kawai a yau batasan farincikin ko menene takeyi ba, ta godewa Allah yafi sau biyar a zuciyarta. A farfajiyar gidan ta iske motar Danliti, hakan ya bata tabbacin cewar Ihsan sun dawo. Hajiya Binta ta gani tare da wata wacce ba yau ta soma ganinta ba ga dukkan alamu kuma kawarta ce. Ta gaishesu a ladabce, suka amsa ciki-ciki suna karemata kallo. Bata kai ga karasawa ba ta ji suna maganarta, inda matar ke cewa. 
"Ina mamakin Hajiya Madina, ko a ina ta kwaso wannan mai ruwan buzayen? Wannan ko Alhajinku ya gani mai yiwuwa yayi ta hud'u da ita."
  Ta karashe tana dariyar zolaya. Hajiya Binta ta ja tsaki.
"Ai kuwa da anyi girman kwabo, ballantana kuma sanin kanki ne Alhaji banda waccan shegiyar babu mai fad'amasa ya ji acikinmu, abin na kona raina."
  "Ai ku kukayi sake, ki bada hadin kai kika yanda komai zai chanja mana."

  
  Iyakar abinda Ummi ta tsinkaya kenan cikin zantukansu kafin kuma ta ta6e baki kawai, a kasan ranta kuwa tana tsoron ranar da Mami zata gaji ta korata daga gidan, watakil shikenan kuma dukkan gatan da ta soma samu na ilimi ya rushe. Saidai kuma tayi mamakin yanda Hajiya Binta take kula kawaye irin haka, da ace sun saba kwarai, da babu abinda zai hanata yin shishshigi wajen bata shawarar watsi da zantukan wannan mata. Da sallama ta nufi shiga falon, saidai kuma tayi turus ganin takalman maza har sawu hud'u da kuma na mata a bakin kofar, haka kawai ta ji gabanta ya fad'i, koda ta shiga bata ga kowa ba a wannan falon, ta numfasa ta karasa ciki, har ta chanja sutura tana cike da tunanin wadanda suka zo, sai kuma ta tunano da su Yaya Haidar, watakila su d'inne suka zo. Ta shirya cikin atamfa riga da zani da dankwali bayan tayi wanka sannan ta d'auro alwala ganin Magriba na dab da yi, fitowa tayi falo, tana son zuwa sanarwa Mami cewa ta dawo saidai kuma batason iske bak'in gaba d'aya nauyinsu take ji.
  A kicin ta had'u da Ramma, ta gaisheta. Ramma ta amsa tana fad'in.
  "Yanzu kuwa Hajiyar ke tambayarki, ta ji shiru nace kin dawo kina ciki. Kije tana nemanki."
  Gaba daya ta ji tsoro ya kamata har yanayin fuskarta ya nunawa Ramma.
  "To ai naga tana tare da bak'i yanzu."
Ramma ta kama baki. "Su waye bak'in? Ai 'yan gida ne, Hajiya Babba ce fa da yaranta."
  Ta gyada kai sannan ta juya ta nufi hanyar falon Mami gabanta na dukan tara-tara, ita da ba don ance Mami ke nemanta ba da babu inda zata. Har ta kai kofar shiga sai kuma ta juya da sauri don ji tayi ba zata iya ba. Muryoyin da ta jiyo daga bayanta na matasan yasa dole ta juyo. Gaba daya mazan ne suka fito da alamu dai masallaci suka nufa sakamakon kiraye-kirayen sallar da aka soma. Kallo d'aya tayi musu ta durkusa da sauri ta gaishesu. Suka amsa sannan ta basu wuri don su wuce. D'ago idon da zata yi sukayi ido hud'u da Faruk wanda dagaske kallonta yakeyi, ta gwammace ace bai kalleta din ba domin kuwa kallo ne ba na arziki ba face kallon raini, fuskarsa babu wata alamar fara'a; ta sadda kanta da sauri. 
  "Ai kuwa Mami na ta cigiyarki da alama kin mata wani gagarumin laifi Ummi." Cewar Adnan ya karashe da dariyar zolaya. 
  "Um." Shine abinda ta furta kawai da murmushi dauke saman fuskarta. Bayan sun wuceta ta bi bayansu da kallo. Wannan karon, Yaya Usman ne kadai ya sanya manyan kaya, gaba daya su ukun k'ananun kaya ne jikinsu. Hajiya Babba Allah Ya bata arziki na zaratan maza wadanda dukkansu basuyi kama da ragwaye ba a komai da ya shafi gwagwarmayar rayuwa da sauransu. Saidai da ace za'a bata za6in wanda yafi kyau da burgewa a fuska acikinsu, toh fa babu abinda zai hanata nuna Yaya Haidar bisa hujjarta na ganin duk ya fisu fara'a. Koda kuwa tasan da yawa cikin wasu matasan yanmata irinta, zasu iya bugun kirji su za6i Yaya Faruk, ita kam banda ita. Tsakani da Allah ta ji haushin kallon da ya bita da shi tamkar wanda ya ci karo da kashi, ta numfasa don tuni sun jima da kauracewa ganinta ta juya, gabanta ya fad'i ganin Ihsan tsaye ta harde hannuwa a kirji ta zubamata na mujiya fuskarta dauke da wani mugun murmushi. Ummi ta kauda kai ta bi ta gefenta zata wuce saidai maganganun da ya soma fitowa daga bakin Ihsan ya tsayar da ita cak!
   "Mutum dai ya tsaya iyakar matsayinsa, ko kusa kada yayi tunanin zai iya da Babban Goro, duk cikinsu babu sa'an aurenki, don haka ki maida maitarki, kurwar kaf dinsu, ta fi karfinki."
   Daga wannan ta sanya kai ta fita tana kwalawa Ramma kira. Iyakar radadi da bacin rai, Ummi ta ji shi a ranta, batasan sadda idanunta suka ciko da kwalla ba, wannan cin zarafi har ina? Kai tsaye an yankemata mummunan hukuncin da ko a mafarki bata yi zaton koda mak'iyinta zai shaideta da aikatawa ba, toh daman ina ita ina ire-iren wadannan mazan? Yaudarar kai ne, koda ta auna cewa Ihsan batasan irin zargin da ya kamata tayi mata  ba, yasa ta yin murmushi mai ciwo, da alama Ihsan bata gama sanin bambancin matsayinta da su ba, tabbas ta cucesu tunda har ta had'asu da ita, watakil da zasu ji da sai sun had'a da kai mata bugu don haushin abinda tayi musu. Ta share batun gami da goge fuskarta sannan ta juya ta koma don ta tabbatar a yanzun Mami ta shiga sallah. Dakinta ta koma itama ta tayar da nata sallar, saida ta idar ta kaiwa Allah kukanta akan Ya ji6anci lamuranta. Bata da kowa sai Shi, Shi ne gatanta. Yayi rahma ga Mahaifiyarta. Haka tayita kwararo addu'o'i har tana fidda ruwan hawaye kafin kuma ta shafa. Bata kai ga mikewa daga wurin ba ta ji Fahad na kwala mata kira adaidai sadda ya murd'a kofar dakin nata.
  "Ummi! Kizo inji Mami."
  Ta mike batare da ta cire hijabin ba ta bi bayansa.
    
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

15


Anan ta iskesu tsaitsaye ana hira banda babban yaya wato Yaya Usman da ke zaune cikin mota tare da Faruk wanda gaba d'aya ya matsu su koma gida don jinsa yake a gajiye.
Ihsan ta bita da kallon harara, hakan yasa ta kauda kanta.
"Kanki ake ji." Ta fad'a a ranta. Ta dubi wata doguwar budurwa siririya bak'a, bata san itace Ikram ba ko kuma Baraka, don sunayensu kawai Amina ta sanarmata ba ta nunamata su ba a fuska.
"Ga wannan a ina zan ajiye?"
Ta dubeta, sannan ta nunamata motar da yatsa batare da dogon bayani ba.
"Kinga, saka anan."
Ta dubi Yaya Haidar dake nunamata boot wanda yasa hannu ya bud'e. Ta karasa ta ajiye gami da fad'in.
"Allah Ya tsare hanya." Daga haka ta juya ta bar wajen.

"Adnan ina mutuniyata ne? Ban ganta ba."
Adnan ya yamutse fuska yana duban farar budurwar siririya da tayi mishi magana, wato Baraka.
"Wa kenan?" Ya tambaya cikin basarwa kamar bai fahimci ko wa ta ke nufi ba da gaske.
"Abokiyar fad'arka mana, your lil sis."
Ya harareta, ya gane Iklima take magana akai.

"Ai kinsan hanyar gidansu ko? Sai kije."
Baraka tayi dariya.
"Kwarai ma kuwa wallahi, idan ma kana ganin kamar bazan iya zuwa ba zaka sha mamaki. Kada fa ka manta k'awata ce, mun riga mun saba da uta adalilin (whatsapp group) da muke ciki tare. Zo muje Ihsan ki rakani."


Please Login or Register in order to submit comment