Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Amin."
Nan suka shantake suna hira, can sai ga Mariya d'iyarta mai shekaru bakwai ta shigo hannunta rik'e da kud'i. Da gudu ta k'arasa ga Habiba tana dariya.
  "Lah, Baba yaushe kika zo?"
Habiba ta rungumeta tana dariya.
"Yar Baba, ban dad'e ba. Mene wannan a hannunki kamar d'ari biyar?"
  Mariya ta kwakume kudinta tana dariya. Ganin haka yasa Saude rik'ota.
  "Waye ya baki kud'i auta?"
Ta mik'awa uwarta.
"Usi mai kanti ne fa ya bani, wai na kawomiki ki sakamin a bankin gwangwani."
  Ta kar6a tana washe baki.
"Kai madallah, Usman ba dai kyauta ba, ince dai kin mishi godiya?"
   Habiba ta gutsiri goro ta soma tauna.
  "Haka yaronnan ya ke ai, ba dai kyauta ba."
  Daga nan suka cigaba da hira kafin daga bisani suyi sallama.

                   ***  ***  ***
           BAYAN SATI BIYU

  Rai a matukar'ar 6ace ta ke dubanta, duban da ba k'aramin kad'a 'yan hanjinta ya yi ba. Ta daure ta numfasa, cikin dakiya ta russuna.
  "Ina wuni Umma."
Maimakon ta amsa, sai ta nunata da yatsa, da kakkausar murya ta soma magana.
  "Kar ki ce za ki ci amanata har haka! Kinyi kad'an ba ki isa ba wallahi!"
  Cikin rawar murya ta soma magana.
"Me..me..nayi Umm.."
Bata kai ga k'arasawa ba, ta sanya hannu ta d'auketa da mari wanda har ta daina ji na wasu 'yan dak'i k'u. Maganarta ce ta maidota hayyacinta babu shiri.
   "Ya kikayimin aikin da na sanyaki?". 
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

28

Gaban Ummi ya fad'i. Ta had'iyi wani miyau dakyar tana duban ofishin mai kula da makarantartasu inda anan ne Hajiya Binta ta zo ta sameta har Malamin ya basu wuri suyi magana bayan an jik'ashi da kud'i. Babu dai alamar akwai wanda zai kawomata d'auki, dole ta maido dubanta gareta idanuwanta na zubda ruwan hawaye, dakyar ta iya magana.
"Nayi yanda kikace bayan nayi bismillah."

Hannu Hajiya Binta ta d'ora a ka tana buga salati.


"Kin kasheni Ummi! Uban wa yace kiyi bismillah? Akan wane dalili zaki karyamin dokar..."
Sai kuma tayi shiru don tsabar takaici da tsananin 6acin rai har idanunta sun ciko da ruwan hawaye, ita kad'ai tasan irin wuyar da ta ci kafin samun magani garanti wanda aka tabbatar zaiyi aiki sosai akan Hajiya Madina, har bokan ya tabbatar mata cewar matukar'ar bata ga aiki da cikawa ba, toh ta dawo ta kar6i kud'inta. A dokokin saida ya tabbatar cewar a kiyaye ambaton Allah. (Wa'iyazubillah). Mik'ewa tayi jiki babu kwari ta watsawa Ummi wani mugun kallo tayi kwafa sannan ta fice a zuciye.
Bayan tafiyarta Malamin makarantar ya dawo, da sauri Ummi ta mik'e ta fice, saida ta zagaya bakin famfo ta ci kukanta ta kuma godewa Allah da Ya kimtsa mata wannan dabarar sannan ta wanke fuskarta ta bar wajen zuwa aji.
Salma wacce ta kasance k'awarta kuma abokiyar shawararta ta dubeta.
"Lafiya dai Ummi?"
Ummi ta k'ak'alo murmushi.
"Bakomai."
Salma ta girgiza kai.
"Ina mamakin wannan amincin namu, sai nake ganin tamkar ba ki daukeni komai ba."
Ummi ta girgiza kai.
"Kiyi hakuri Salma, wani abin ba ya bukatar magana. Kedai ki tayani addu'a. Kada kiyi kokwanto akan yacce nake ganinki, Allah ne Ya had'a zumuntarmu."
Salma ta murmusa.
"Shikenan, Allah Ya yayemana dukkan matsalolinmu."
"Amin." Ummi ta fad'a sannan suka bar magana sakamakon karatun da aka soma.

Tun zuwan Ummi makarantar bata shiga harkar kowa, daga baya ne suka saba da Salma d'iya ga d'aya daga cikin malaman makarantar, Malama Zainab. Tun bata bayarda fuska, har dai ta dan sakarmata suka saba ganin da ta yi nutsastsiya ce.
Haka ranar suka tashi jikinta duk babu kwari. Tana zuwa gida ta soma kici6us da Ramma a tsakar gida.
"Au, kinga 'yar halak d'inma, to ki shiga ku gaisa da Yaha."
Gabanta ya fad'i.
"Yaha?"
"Eh, wacce dai kikasani." Ramma ta bata amsa wanda ya sa ta fahimci maganarta ta fito fili. Ta saki murmushin yak'e, ta tabbatar zuwan na kar6ar kud'in watanta ne ba wai na bincikar lafiyarta ba. Allah Sarki, shiyasa ta ke tausayin kanta, tana tsoron ranar da Mami zata soma gajiyawa da ita ta korata, ita kam wa zata runguma?
Ta ja kafafunta wadanda suka k'ara yin sanyi ta k'arasa cikin falon da sallamarta. Yaha ta amsa tana daga zaune saman kafet yayinda Ihsan ke zaune ko kayan makarantar islamiyya bata cire ba tana danne-dannen waya. Fahad kuwa ya cire daga shi sai singilet da short yana kallon (cartoon). Ta washewa Ummi hak'ora cike da mamakin yanda ta chanja.
'Shegiya, birnin ya kar6eta.' Ta fad'a a ranta. Ummi ta k'arasa ta gaisheta tana mai k'ok'arin sakin fuskarta bayan ta kauda kanta daga duban Ihsan wacce ke jifanta da murmushin rainin hankali da k'ara kallonta a ba komai ba.
"Ashe kinzo, sannu, ina wuni."

"Yauwa Ummi, lafiya lau. Oh! Haka kika bi kika chanja? Eh lallai."
Ta karashe tana k'aremata kallo gami da d'an ta6e baki.
Murmushi kawai Ummi tayi.
"Ai dole ta chanja, cimar ai ba d'aya ba. Anan ai akuyar d'aure ta samu sake."
Muryar Ihsan suka tsinta ta tsomo musu baki.
"What the hell is this?"
Daga baya aka bata amsa. Suka dubi mai shi, Adnan ne wanda ya fito daga d'akinsa daga shi sai dogon wandon makaranta da singilet. Yana watsawa Ihsan wani kallo mai nuni da lallai bai ji dadin maganarta ba.
Ihsan ta had'e gira gami da d'aga kafad'a mai nuni da ko ajikinta ta cigaba da danne-dannenta tana dariyar rainin hankali. Yaha kuwa ta bata amsa.
"Ai fa, da gaskiyarki 'yar Mami."
Ummi ta mik'e.
"Bari na chanja kaya."
"Muje toh." Suka d'unguma da Yaha zuwa ciki, duk kokarinta saita hawaye ya zubomata ta daukesu da hannunta, wannan cin zarafi ya soma yawa, amma bakomai, tana ji a jikinta komai zaizo k'arshe in sha Allah.

Tana chanja kaya, Yaha kuwa na tsaye tana k'arewa d'akin da ita kanta kallo. Dakin yana ayanda ta ta6a ganinsa saidai suturar Ummi take kallo duk ta chanja. Baki ta ta6e.
"Oh'oh, hum, da gaskiyar Ihsan. Wannan irin samun sake? Yaushe aka sanyaki a makarantar?"
Ummi cikin dakiya ta amsa.
"An kwan biyu."
"Lallai, amma bakomai tunda kina abinda ya dace, har kud'i Hajiya ta k'ara na aikinki. Kinga nan dubu shida, ta bani dubu uku. Idan naje zan damk'awa uwarki."
Ummi ta amsa da to kawai, daman batasa ran za'a bata komai ba.
"Ina su Baba?"
Yaha ta harareta.
"Kalau suke, da dai kin bar saka kanki a layin 'yan gidan Balarabe, bana tunanin ma wani cikinsu yana tunaki."
Ummi ta jinjina kai tayi 'yar dariya na dole.
"Bazan bar tuna shi ba, ko ba komai shi ne ya haifeni."
"To 'yar makaranta. Bari na rage mara dai."
Bayan shigarta bandaki, kuka sosai Ummi ta yi, dakyar ta rarrashi kanta.
Saida akayi Magriba sannan Yaha ta shirya tafiya, har titi ta rakata, tafiyar bata dad'i ba don kuwa magana take gaggasamata wai ita ko 'yar satar nan ma batayi don a samu a tara na aurenta cikin sauri, har suka rabu batayi mata hud'ubar arziki ba. Ummi dai ta gama tabbatarwa a duk duniya babu wani dan uwanta na jini mai kaunarta. Ko a hanyarta ta komawa gida tana tafe ne tana hawaye saids ta iso daf da gidan sannan ta gyara fuskarta. A farfajiyar gidan suka had'u da Adnan, ta dauke kai zata shige yayi azamar shan gabanta. Ta dubeshi tana dan murmushi.
"Lafiya?"
"Sorry." Ya fada cikin sassanyar murya harda rik'e kunne.
Abin sai ya bata dariya, ta dara.
"Me kayimin?"
Ya gyara tsayuwa.
"Banyimiki ba amma Ihsan ta miki."
Ta girgiza kai.
"Ayya, ni ya wuce. Kuma ai gaskiya ta fad'a."
Ya daure fuska.
"Ba gaskiya bace. Karki k'ara daukar hakan amatsayin gaskiya. Ga idanunki sun nuna alamun ma kin koka. Kiyi hakuri Ummi."
Ya burgeta, yasan darajar DAN ADAM. Ta numfasa hakoranta a bayyane tana murmushi har zuciyarta.
"Ya wuce."
Ya dara.
"Yauwa kokefa, keep smiling always."
Daga haka ya juya ya tafi, me yake nufi? Oho, bata da masaniyar fassarar turancinsa, amma duk da haka ya burgeta. Ta girgiza kai ta shige ciki itama.


*** *** ***
UMARUL FARUK DANZAKI
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

29

      UMARUL FARUK DANZAKI

Kwance yake saman doguwar kujera dake a tsararren falon mahaifiyarsu. Idanunsa a lumshe kai ka rantse bacci ya ke, a can d'aya 6angaren na falon kuwa wanda nan ma komai ya ji, Hajiya Babba ce da bak'uwarta suna lissafin kayayyaki. Rabin hankalinsa na garesu, rabin kuwa kan jefashi duniyar tunani wanda kokusa baya kaunar hakan. Ya ja guntun tsaki gami da mik'ewa zaune, wayarsa ya d'auka ya bud'e (data), nan take sak'onni suka shiga tururuwar shigowa wayarsa, duk daga (Whatsapp). Ba sabon abu ne awajensa ba, yana da tabbacin kusan maza abokan aikinsa da yan uwansa sunfi yawa, mata masu turomasa sak'o k'alilan ne don bai basu damar mallakar lambarsa ba, saidai har mamaki yakeyi na yacce mafi yawa na 'yanmatan suka samu. Babban dalilin kenan da ya yiwa kannensa gargad'i akan kada su yarda su k'ara bawa kowace yarinya lambarsa. Sun ji gargad'in kuwa don sun kiyaye.

   Kai tsaye ya soma bud'e sak'onnin yana karantawa. Ga mamakinsa ya tsinceshi a wani group na Zumunta. Koda ya shiga yan uwansu ne burtik, mata da matasan. A sunayen (Admins) ya hangi wacce ta tsundumoshi ciki.
  "Iklima?" Ya fad'a a fili fuskarsa cike da mamaki, ya koma cikin group inda ya ji tana mishi marhabin da shigowa. Ayayinda wani dan baffansu dake Adamawa ya sanyo alamun dariya. Guntun tsaki ya ja gami da ficewa batare da yace uffan ba.
  Yana fita kuwa suka hau kyakyata mata dariya harda masu turo sak'on murya wanda hakan ba k'aramin k'ular da ita ya yi ba. Daman sun san halinsa, ba yau ya soma arcewa daga groups ba, da dai zaka mishi magana ta akwatin sirri, anan kam zai iya baka amsa, harma idan ka ci sa'arsa kuyi hira mai tsayi da dariya.  
    "To sai anjimanku."
Muryar Bak'uwar Hajiyarsa ce ya katseshi daga danne-dannen da ya ke a waya. Ya dubeta ya gyad'a kai cikin dan murmushi ya amsa 
  "Allah Ya kiyaye hanya."
Daga haka ta yi gaba tana mai amsawa da Amin. Mik'ewa ya yi ya koma wajen da Hajiyarsa ke zaune. Ta maida lesussukan gabanta gefe ta dubeshi fuskarta dauke da murmushi.
  "Miskili kafi mahaukaci ban haushi, Sadauki nawa ya akayi ne?"
  Ya d'an turo baki kamar mace, abin ya bawa Hajiya dariya ta girgiza kai.
"To shagwa6arce ta motsa?"
Ya shafi sumarsa yana 'yar dariya, itama tana tayashi, aduk yaranta tafi so da tausayinsa kasancewarshi mutum marar son hayaniya ga kuma hak'uri da rauni. Kullum addu'arta bai wuce na Allah Ya had'ashi da mace ta gari ba, ba wacce zatayi amfani da rauninsa da hakurinsa ta cuceshi ba. Ya katse tunaninta ta hanyar sanarmata batun group da aka sanyashi ya fice. Da murmushi dauke saman fuskarta tace.
  "Toh banda abinka Sadaukina, ai k'ara dank'on zumunta ne, ina zaka so ku had'u da d'an uwanka a hanya ayi abin kunya ba ka san da zamansa ba? Kaga mu ma duk muna da group na zumunci, na yan Adamawa daban, namu na dangin mahaifinku daban."
  Ya dauki filo ya sanya agefenta ya kwanta yana mai juya mata baya. Ya lumshe ido.
  "Hajiya duk wannan takura rayuwa ce, nafi ganewa mu gaisa ta private ko kuma na kira mutum ko ya kirani. Surutu ne zalla sukeyi."
  Ta dafa kansa.
"Zumuncin kenan Sadauki, wani ma hakan ya nema ya rasa. Wasu na can basu da dangin ma da zasuyi musu hakan."
  Bud'e idanu ya yi, tabbas Hajiya ta fad'i gaskiya, babu wacce ya tuna sai Ummi. Yana ji ajikinsa, akwai wani babban lamari a rayuwarta, har yau ya kasa cire kwad'ayi akan sanin tak'amaiman tarihinta.
   "Hakane Hajiya."
Daga haka ya basar da zancen.
"Wai yaushe yarannan zasu dawo?"
  "Af, su Baraka ai ansamu gidan zuwa, suna can nasan suna zuba da Intisar."
  Ya girgiza kai gami da ta6e baki.
"Ai Yaya Haidar shi ya barsu."
Hajiya ta rik'e ha6a.
"Au kai kace babu mai zuwa gidanka?"
  Ya mik'e zaune ya rungume filon yana dariya kad'an-kad'an.
   "Bance ba, amma kada a yawaita."
"Eh lallai Sadaukina, ga shi har yau ni banga surukar tawa ba, Alhajinku ma na fama."
   Ya yamutsa fuska.
"Ni wai..." Sai kuma ya yi shiru gami da mik'ewa da daukar wayarsa.
  "Aifa, daga ansoma maganar gaskiya saika gudu."
  Ya yi murmushi mai bayyana hak'ora.
   "Kai Hajiyata, ya dace dai ku d'an huta, ga na Baraka nan fa tafe, abin sai ya yi muku yawa."
  Hajiya ta harareshi.
"Wane irin yawa? Ai hutunmu yana bayan aurar da ku lafiya."
  Ya gyada kai.
  "Hakane, bari na d'an fita."
  Ya fice da sauri kada ta cigaba da magana d'aya wanda shi amsarsa har zuwa lokacin bai wuce A'a ba, don kuwa ba zaice ya ta6a soyayya ba balle  har ya ji yana son auren wata mace.
    
                   ***  ***  ***
    
  
Ahmad Bashir Danzaki, haifaffen garin Kano. Ya kwashi tsawon shekaru sittin a rundunar sojoji yana aiki kafin ya yi ritaya. Matarsa d'aya tun lalle, Hajiya Fatima wacce suke kira da Hajiya Babba. 
  Yaransu shida cif, Usman shine wanda ya yi karatunsa kacokam akan kasuwanci. Ridwan ke bi mishi, shi din ya kasance kwararren likita a fannin mata, sai Haidar wanda ya ke lauya, sannan Faruk wanda yake ma'aikacin banki.  Baraka wacce suke sa'anni da Adnan da Iklima, tana aji na karshe a sakandare wanda tare suke tafiya. Sai auta Ikram, wacce sa'ar Ihsan ce, itama tare suke tafiya da ihsan, suna aji na biyu a babbar sakandire.  
       
  Umarul Faruk ya kasance ma'abocin son zane, daidai da dakinsa idan ka shiga haka zakayita cin karo da takardu masu dauke da zane kala-kala. Sau da yawa haka mai gyara sashensa, Bala, zaiyita kwasarsu yana zubarwa. Son zanensa bai ragu ba saida ya soma aiki ka'in da na'in, alokacin ya zamana babu kwakkwarar lokacin zane, wani sa'in kuwa sai ranar da babu aiki yakan ta6a.  Idan kuwa ka ganshi a falo, to fa hira ce ta motsa. Kokuma yan uwansa sunzo nan zasu had'u suyita kwasar hira suna dariya har mahaifinsu. 
   Rayuwarsu tana tafiya cike da sha'awa, ga ilimin addinin da na boko. Babu mai takurawa wani, hakan bai hanasu kiyaye dokokin Ubangiji ba.

             WANNAN KENAN..
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

  30
   Alhaji  Muhammad zaune a k'ayataccen falonsa bayan ya kammala cin abinci. Ya kai duba ga sanyin idaniyarsa da ta fito daga d'akinnasa bayan kammala feshe d'akin da maganin sauro, murmushi suka sakarwa juna, ya rik'o hannunta ya zaunar da ita a gefensa.
   "Bakya tsufa Madina, menene sirrin?"
  Mami tayi dariya gami da yin farr da ido. 
  "Oh Abban Ihsan, kai dai kullu yaumin baka rabo da zolaya."
  Ya yi dariya.
"Ina zolaya anan? Babu sai tsagwaron gaskiya."
  Sukayi dariya. Ya rik'o yatsunta yana murzawa.
  "Kiramin d'ana."
  Ta cire yatsunta, zata mik'e ya dakatar da ita.
  "Ina wayarki? Kiyi amfani da ita mana."
  Ta sa hannu ta dauki wayar a saman tebur kafin ta hau laluben lambar Adnan. 
  Lokacin yana zaune a falo suna kallon Dadin Kowa suna kyakyata dariya har Ummi dake gefe zaune. 
  Bayan ya d'aga ta sanarmishi kiran Abba, a take ya mik'e ya fita.

   
Da sallama ya shiga falon bayan sun amsa. Ya k'arasa ga Abbansa ya zauna agefen kafafunsa.
   "Abba gani."
  Da murmushi saman fuskarsa ya dubi d'annasa.
  "D'an Abba, ya makaranta? Naji kun soma jarabawar karshe ko?"
  Adnan ya sosa kai yana murmushi.
"Eh Abba, komai yazo karshe in sha Allah."
  Abba ya jinjina kai. 
"To haka akeso, Allah Ya taimaka."
  Mami da Adnan suka amsa. Ya cigaba da magana.

  "Kaje kayi nazari dakyau, saika zo ka sanarmin makarantar da kakeson zuwa k'aro karatu a k'asar waje. Kada kayi gaggawa ka bi sannu, idan ka sanarmin sai mu bincika mu ga yanayin ingancinsa. Allah Ya yi maka za6i na alheri."
  Wani dad'i ya daki zuciyar Adnan, ya yita nanata ambaton Allah a zuci, a k'arshe cikin tsananin murna da d'oki ya hau yin godiya ga mahaifinsa. Haka ya tashi ya koma falon Mami cikin tsananin murna.
   Yana shiga ya saki k'ara don tsabar farinciki har yana doka tsalle. Tunda suke basu ta6a tsallaka Nijeriya ba, sai a wannan karon da yake fatan burinsa ya cika.
  Gaba daya suka zubamishi ido. Ihsan a guje ta taso.
  "Yadai broda?"
Nan ya sanarmata, ai don dadi itama ihun ta sanya gami da rungumeshi, shima Fahad agefe yana tsalle. Ummi kanta itama saita tsinci kanta cikin farinciki matuk'a, domin burinta ta ga duk wani masoyinta cikin farinciki.
    Ya yi dakinsa a guje, Ihsan ta mara mishi baya tana mai cewa.
  "Yi browsing mu dudduba makarantun."
   Bayan shigewarsu ta numfasa, babu jimawa da shigarsu wayar Adnan ta dauki k'ara. Da sauri Ummi ta mik'e ta dauka da zummar kai mishi. 
  Hoton Faruk ta ci karo da shi 6aro-6aro akan screen din wanda Haidar ke  rik'e da hannunsa shi kuma yana dubansa da murmushi mai bayyana hak'ora. Gaba d'aya sai ta tsinci kirjinta na bugu.
  "BRO FARUK." Sunan dake saman screen din kenan, ta ajiye wayar da sauri, ta kama hanyar d'aki har lokacin wayar na k'ara, haka ta juya ta koma ta dauka. Haka kawai ta tsinci kanta da d'agawa batare da tasan dalili ba. Ta gwada (sliding) wajen koren kamar yanda ta sha ganin Adnan ya yi idan zai d'aga waya. Cikin sa'a kuwa ta soma jin maganarsa yana sallama. 
   Ta kasa magana don gaba daya ta tsorata, jin maganar Adnan kawai ta yi a kanta.
  "An kirani ko?"
A razane ta juyo ta mik'amai. Kasa magana tayi sai kai data gyad'a. Allah Ya taimaketa batare da Ihsan suka fito ba. 
  Ta juya da sauri ta nufi dakinta. Tana ji sadda yake fad'in.
"Afuwan dan uwa wallahi Ummi ta d'aga, fitowata kenan daga d'aki."
  Daga haka ta shige ciki da sauri.

  Shigarta d'akin ba wuya ta ji an kwankwasa k'ofar, a gigice ta dubi bakin k'ofar. Adnan ne tsaye yana murmushi. Ya mik'omata waya.
  "Kar6i, za ku gaisa da Yayana. He's my best." Ya k'arashe cikin muryar rad'a yana mai kanne mata ido d'aya, ta yi mamakin rashin ganin kowace alama a fuskarsa kamar yanda nata fuskar ya nuna tashin hankali tsantsa. Ta kasa kar6ar wayar har saida ya yi mata magana karo na biyu, alokacin tasa hannu ta kar6a, kasancewar har lokacin cikin zumudin daddadan albishir na mahaifinsa yake, yasa yana mik'amata ya juya zuwa dakinsa on don ganin abinda Ihsan ta binciko da (Laptop) dinsa. Ta tsaya cak tana duban wayar har lokacin a matukar tsoro take. Kawai sai ta ji idanunta sun cika da kwalla, to wai me zata ce? Inama tun farko bata d'aga wayar ba? Batasan cewa ya katse ba saida ta ji sabon ringing wanda ya kad'a har cikin ranta. Hotonsa ne dai 6aro 6aro wanda idan kiran ya katse bata gani, hakan ya tabbatarmata cewa a sunansa kawai ya sanya. 
  Tana hawaye ta danna ta kara a kunnenta, ji takeyi inama kada ta d'aga, ita kam ta shiga tara...!

   
  "Assalamu alaikum." Ta fad'a cikin rarrauniyar muryarta wanda sautin kuka ya ta6a.
  Faruk dake tsaye a barandar dake a sama wajen dakinsa yana duban  farfajiyar gidannasu, ya numfasa jin muryarta.
  "Waalaikumussalam, Ummi kina lafiya?"
  "Umm, ina wuni Yaya Faruk." Ta fad'a gami da kai gwuiwoyinta k'asa kamar yana ganinta. 
   Murmushi ya yi lura da ya yi na cewar ta tsorata da shi.
"Lafiya lau."

"Wai Ummi dodo na zame miki? Gaisuwa kad'ai na buk'ata fa..."
Sai kuma ya yi shiru kafin ya d'ora maganarsa.
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

   32
Ranar juma'a da misalin karfe bakwai, gaba daya yaran Hajiya Babba sun had'u suna hira kamar dai yanda suka saba, duk juma'a anan suke wuni matuk'ar ba wani aikin ne ya tasowa dayansu ba ko duka. Wannan lokacin ma Faruk baya tare da su, a haka ya dawo daga aiki ya samesu suna ta zuba hira suna dariya ga kayan marmari agabansu a babban faranti an yayyanka suna sha.
    Yana sanye cikin riga kalar sararin samaniya, ya d'ora kwat dinsa bak'i akan hannunsa na dama, d'ayan hannun kuwa (briefcase) ne, gaba d'aya fuskarsa ta tona gajiyarsa. Suka amsa sallamar da ya yi ciki-ciki. Cikin dariya Ridwan ya dubeshi.
   "Kaga manyan ma'aikatan banki."
  Gaba daya suka dara, shi kuwa gogan sai ya k'ara marairaice fuska ya karaso ciki ya zube a saman kujera gami da fad'in.
"Wash!"
  Haidar ya birkita sumarsa.
"Sannu lil, haka muke fama."
Faruk ya murmusa.
"Kai, anya kana aikin da mukeyi?"
Cewar Likita (Ridwan) kenan. 
  Usman ya cafe.
"Mu da ke wuni a shago sai mu ce me?"
  Nan da nan kuma sai hira ta koma musu tamkar wasu abokai kowanne yana k'ok'arin nunawa sauran zafin aikinsa musamman  Babban Yaya da Likita wanda idan da sabo sun saba. Ikram na goyon bayan likita ayayinda Baraka ke bayan Barista Haidar kasancewar itama fannin da ta ke son karanta kenan. 
     Faruk dai sulalewa ya yi zuwa dakinsa don watsa ruwa. 
   Bai fito ba saida ya yi wankansa tsaf ya sanya riga t-shirt bak'a da farin wando wanda da kadan ya wuce gwuiwa, kasancewarsa farin mutum, ba karamin kyau da haske ya yi ba, ya jona wayoyinsa a chaji ya fito.
    Alokacin sun nufi masallaci, shima ya bi bayansu.
  Tare suka shigo gaba daya har Daddy dinsu. Bayan an kammala cin abinci ne, kowanne Daddy ya tambaya ko da wani matsalar. Duk suka tabbatar mishi babu, Babban Yaya ke sanarmishi zai je Kano ganin wani babban dan kasuwa da ya buk'aci ya shigo mishi da kaya suyi lissafi.  Daddy ya gyada kai.
  "Allah Ya bada sa'a." Suka amsa da amin. Faruk wani abu ya tuno hakan yasa ya dubeshi.
   "Ko nayi maka rakiya?"
  Babban Yaya ya washe baki.
"Wallahi da ka kyauta, daman banson bin hanya ni d'aya babu abokin hira."
  "Toh kai baka da wani uzurin ne goben?" Cewar Daddy yana duban Faruk. Faruk ya daga kafada kadan yana girgiza kai.
  "Babu."
  "Ai kuwa da kun biyamin gidan Alhaji Labaran, akwai saurin auren 'dansa ran lahadi, bazan samu zuwa ba. Kuje a madadina."
  Sukayi na'am har Haidar na fadin ba don yana da abin sabgogi ba a goben da ya bisu.
  Faruk ba murmushi ya karkata wuya zuwa saitin kunnen Haidar.
  "Kaidai fad'i gaskiya, Intee ce zata hanaka zuwa."
  Haidar ya dubeshi ya harara da wasa, hakan ya bawa Faruk dariya, ya saki murmushi mai bayyana hak'ora.

   Basu jima ba anan, duk matasan suka mik'e. Haidar saida ya tsaya a falon Faruk sukayi kallon ball kafin ya wuce gidansa bayan waya da Intisar ta dameshi da shi. 
   Faruk haka kawai yakejin nishad'i game da zuwansu Kano. Yana matukar kaunar k'ara sanyata a idanu.

                   ***   ***   ***
   Washegari kuwa misalin tara suka bar Abuja da Babban Yaya, koda suka isa saida sukayi  La'asar a gidan kakansu Modibbo suka ci abinci sannan Babban Yaya ya k'arasa ga abinda ya kawoshi, shi kuwa Faruk waya ya yiwa Adnan ya sanarmasa yana Kano, ba jimawa kuwa sai ga Adnan suka fice yawo. Idan ka gansu kamar abokai don babu laifi shima Adnan ba dai tsawon k'afa ba. 
    Saida suka gama zagayansu sannan suka nufi gidansu Adnan domin ya gaisa da Mami.

      Ummi na zaune a inda ta saba, wato can hanyar kicin tana kallon tashar cartoon wanda Fahad ya sanya, ko kadan kallon ba dadi ya ke mata ba, asalima ba ba fahimtar komai take ba, wannan dalilin ne yasa ta mik'e gami da nufar hanyar d'akinta. Ya yi daidai da sallamarsu. Adnan na gaba, yana biye da shi. Ta amsa tana dubansu. Yana sanye da riga T-shirt ja da dogon wando bak'i. Shima idanunsa cikin nata, ta tsinci kirjinta da bugawa da sauri-sauri. Da sauri ta zube tana gaisheshi cikin rawar murya. Ya sauke ajiyar zuciya kafin kuma ya amsa. Daga haka ya bi bayan Adnan, ta mik'e jiki a sanyaye ta karasa dakinta da sauri. Juyowa ta yi a sadda ta kai kofar shiga, suka had'a ido sa'ilin da yake cire takalmi shima din ita ya waigo. Alokaci guda suka janye idanunsu bayan da suka ji wani sauyin yanayi na daban a jinin jikinsu. Ta yi wuf

Please Login or Register in order to submit comment