Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan yarannata haka. Suna zaune a saman kafet ga katuwar leda agabansu an shimfid'a sai kulolin abinci duk Ikram ta zuzzubamusu.  Haidar ya sanyo batun auren Faruk da irin kyauta ta musamman da ya tanadar mishi.
  "Mata biyu lokaci guda? Ai wannan ni kadai nasan tanadin da na yi ma."
Ya fada saitin kunnen Faruk , ya yi kamar bai ji ba ya cigaba da cin abincinsa. Babban Yaya na jin haka ya ajiye cokali gami da dan kora ruwa sakamakon kwarewar da ya so yi babu shiri.
  "Wai wa zai auri mata biyu?"
  "Oh, baka da labari fa ashe Dan uwa." Cewar Dakta. 
  "Abincin za ku ci ne ko hira zaayi?"
Suka tsinci muryar Daddy wanda ya katse hanzarin Haidar da Dakta masu zuci-zucin bawa Babban Yaya labari kamar wasu yara.
    Ya karaso fuska a sake ya zauna.
"Ke kuma na lura duk ranar da 'ya'yanki ke gidannan kina mantawa da lamurana, ina ga dai na kusa hanaku irin wannan zuwan."
Ya karashe yana kallonsu, suka yi dariya har Faruk.
"Kai amma da na ji dadi Daddy." Ya fad'a yana kanne ido daya. Suka watsamishi hararar wasa banda Babban Yaya da ya ke dariya.
"Kwana nawa ne kaima?" Fadin Haidar kenan.
  Daddy ya dakatar da su da hannu.
"Ya isa hakanan, a ci abinci a nutse. Idan kun kammala ina nemanku."
Daga haka ya tashi Hajiya ta bi bayansa. 
  Bayan sun kammala suka hadu sashen Daddy har Ikram. Ya soma da fadin.
"Ku amanar Allah ce awajena, ya kuma zama dole na dunga nusar da ku akan lamura na rayuwa." Ya cigaba da yi musu nasiha mai ratsa jiki kafin ya sanyo batun auren Faruk da Ummi.
  "Idan Allah Ya shiryo hakan babu wanda zai hana, hakazalika kowa da kaddararsa a rayuwa."
A karshe dai ya kara nusar da su batu na hadin kai, akan ko bayan ransa yana fatan su rike zumunci. 
   Sun jima anan, Babban Yaya bai nuna wata alama ta k'in sha'anin ba, Ikram dai har lokacin zuciyar bata lafa ba, koda ta yi yunkurin hakan da zarar ta tuno da wacce zaa aurar sai ranta ya yi bak'i. Ko yar uwarta Baraka lamarin baiyi mata dadi ba, Intisar ma ta nuna rashin yardarta ga Hajiya Mama nan ta ci karo da fushinta, dole ta ja bakinta ta yi shiru ba don ranta naso ba, ga mijinta shima da ya goyi bayan dan uwansa. 
    Haka taro ya tashi zuciyar kowa a sake har Ikram don ta samu dama Faruk ya sakarmata fuska.
     Bayan fitarsu Daddy ya sanarwa Hajiya cewar lokaci ya yi na dauke Ummi daga sashen yan aiki, itama daman ta yi tunanin hakan saidai tunanin da ya yi mata yawa akan k'in daga wayarta da Madina ta k'i yi duk kuwa da cewar ta samu magana da Hajiya Mama ta nunamata komai lafiya amma sam hankalinta bai kwanta ba. Sunyi waya da Adnan ya sanarmata gobe zai wuce, ta bishi da kyakkyawar addua da kuma nasiha.
    
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

78
                      KADUNA

Amarya Dija an dirji amarci, Deen kamar ya haukacemata tsabar rud'ashin da ta yi, ita kanta tasan ta yi aure ta samu miji na nunawa sa'a. 
  Munira baiwar Allah, a wannan daren ta ci kuka har ta gode Allah, tana yiwa ranar kallon bak'ar rana agareta, wai mijinta da yar uwarta da ta dauketa tamkar wadda suka fito ciki daya, sune tare a makwanci guda. Dakyar ta iya saita kanta don a daren ba wani bacci da ta yi. Da safiyar litinin ta daure ta rigasu fitowa ta hada karin kumallo na gaba dayansu. Kamar ta je ta kwankwasa musu sai kuma ta tuno cewar ko sallama a daren jiya Deen fa baizo ya mata ba, koda a waya bai nemeta ba sai ita da ta mishi sakon taya murnar aure nan ma bai amsa ba. Anya yanzu ba bada kai bane ta je kwankwasa musu? Ai ta daure ma da ta yi girkin. Juyawa ta yi ta koma suka karya da yaranta ta shiryasu ta fice kaisu makaranta. 
   Su kuwa masoyan basu tashi ba sai bayan takwas, suka shiga wanka bayan sun gama suka shirya. Dija ta hade cikin wani leshi kore dinkin da ya kama jikinta, shi kuwa kananun kaya ya ci don ya samu hutu wajen aikinsu na amarci.
  Koda Munira ta shigo, dariyarsu ce ta bata shaidar sun tashi, ta daure ta hadiye abinda ta ke jin ya tasomata a zuciya ta shige dakinta.

  Su kuwa karya kumallo sukeyi hankali kwance, Deen na so ya je ganin Munira saidai yana gudun 6acin ran Dija. Bayan sun kammala suka koma daki, wayarta ta dauki k'ara, ganin mai kiran yasa duk ta dan diririce ta wayance da katsewa gami da saurin sanya wayar a(silent), ta jefa wayar k'asan filo tana murmshin yak'e.
"Mutane ayita takura mutum."
Ya yi murmushi yana mai janyota jikinsa.
"Madam ko za kimin rakiya mu gaisa da yarana?"
  Ta daure fuska.
"Kodai kace za ka ga matarka?" 
Ya ja karan hancinta.
"Ta ci albarkacin yaranki mana."
Zata k'i sai kuma ta tunano da kiran da Raihana ke mata, ta yamutse fuska.
"Jeka kai daya, ni babu inda zanje."
Ya yi murmushi.
"Shikenan." Ya mike ya fita saida ta tabbatar ya tafi din sannan ta ciro wayarta a k'asan filo. Mayyar lokacin m wayar kiranta ne ke kara shigowa. Takaici ya isheta, ita fa yanzu duk ta ficemata aka, idan ma abinda ya shafi bukatarta ne to yanzun ta samu mai daukemata, duk wannan haukan ya fice daga kwanyarta daman ba ta6a aikatawar ta yi ba a fili. Ta daure ta kai zuciyarta nesa ta daga wayar. Daga can kuwa Raihana har wani gwauron numfashi ta saki wanda Dija ta ji shi har ta ji kamar ta shiga wayar ta mak"urota. Ta daure "Kin kira ban kusa."
  "Eh kina can kina amarci ai, ni na dauka ma ko wani laifin nayi miki."
  Ta cije le66anta.
'Laifin uwaki.' Ta fad'a a ranta, a fili kuwa ta dan yi murmushi mai sauti.
"Haba ni ina na yi wannan isar da za ta ce haka gareki? Ko kusa."
"To ya ango? Dijat kada fa ki k'i cika alkawarin da ki ka dauka, ki yi hankali, idan har ki ka ce za ki juyamin baya zan iya daukar kowane mataki."
  Hankalin Dija ya tashi, yau ta shiga uku, hankalinta ina ya tafi da ta mance da batun bokanyar uwarta har ta amince da Raihana akan ta sama mata mafita? Kodayake lokacin ji ta ke ko menene ma zata iya aikatawa matukar zata samu ta auri Deen.
  "Kinyi shiru."
Ta dan gyara murya.
"Ina na isa na mance da hakan? Karki damu ina sane."
Raihana ta yi dariya.
"Ina Kaduna, da zarar kin gama satin amarci, zamu soma namu."
  Ai saita mike tsaye tsabar kaduwa. Kasa magana ta yi ta kashe wayar gaba daya, ta koma ta zauna gefen gado. Babu wata mafita face na kiran Babarta, dole ta bar yin rufa-rufa gareta yanzu, idan yaso ta je mata wajen Bokanya ta gayamata duk halin da ake ciki. 
      Acan kuwa, Deen ya shiga dakin Munira, tana zaune gaban madubi daga ita sau daurin kirji ta yi wanka. Ganinsa ba sai ta juyo ba, sallamar ma a ciki ta amsa. 
   Zama ya yi gefen gadon yana dan satar kallonta tana shiryawa, tunaninsa bai wuce tsakanin matannasa biyu ba wace ta fi k'ira? Yana lura da abubuwa da dama wanda Munira ta mallaka, Dija bata mallakesu ba saidai ya dan lura da ramarta, ya kasa jurewa ya mike ya isa gareta gami da rungumota ta baya.
  "Wai ba gaisuwa?"
Ta tureshi kadan sannan ta gaisheshi, ya amsa. Cikin gatse ta tambayi amarya, ya shafi kansa ya amsa a dan kunyace.
"Idan na kammala abinda nake na je mu gaisa."
  "Am ina yaran nan?"
Ya fada cikin basar da wancan maganar, ta watsamishi wani kallon da bata shirya ba.
"Ka manta yau litinin?"
Ya jinjina kai yana dan kame-kame.
"Oh hakane fa."
Daga haka bata k'ara ce mishi uffan ba, har ta kammala shirinta ta hau gyara, ganin haka yasa shi ficewa sum-sum. Ta bishi da kallon tausayawa kanta. Kamar ba Deen din da ta sani ba, gabadaya ya chanja, ta soma tunano kyakkyawar rayuwar da suke gudanarwa kafin zuwan Dija, yanzu kam babu shi. Hawaye ya zubomata, ta kasa cigaba da aikin don daman kanta ciwo ya ke, kwanciya kawai ta yi bayan ta sha magani, cikin taimakon Ubangiji kuwa bacci ya yi awon gaba da ita.
                    ***   ***   ***  
                        ABUJA
  Ta rude iyakar rudewa jin da ta yi wai yau zata koma gefen dakin da Ikram ta ke wato dakin Baraka harma da batun da Binta ta zo mata da shi na cewar ayau dinne sabbin yan aiki biyu zasu zo. 
   Binta ta zunguri kafadarta.
"Wai kina daukar hakan wasa? Wallahi dagaske nake, Hajiya na ji tana sanarwa Ikram kar kiso kiga yanda yarinyar nan ta hada fuska, karshe ta kwalamin kira ina daga kicin akan na zo na kiraki."
   Ummi ta jinjina kai, wato shikenan ta tashi daga matsayin 'yar aiki? Allah kenan mai yanda ya so.
   Jiki a sa6ule ta bi bayan Binta, ai kuwa kamar yanda Binta ta fad'i haka dinne ya tabbata wato dai za'a chanja mata muhalli, ita kuwa Binta ta samu k'arin albashi wanda yafi ba baya tsoka. Wannan abu ba karamin dadi ya yi mata ba.  
  Ita ta taimakawa Ummi suka gyare dakin tsaf, dakin sak irin na Ikram ne, saidai bambanci and kala, na Baraka komai adon ruwan hoda akayi, ita kuwa Ikram (sky blue)da fari. 
   Binta cewa ta ke..
"Ki godewa Allah Ummi, Allah Ya daukaka ki lokaci guda ke kam alherin Allah ne ya kiraki Kano ki ka hadu da Yalla6ai har ga shi sanadinsa kin samu matsayin dab an ta6a ganin wata 'yar aiki ta samu ba. 
  Ummi kam murmushi kawai ta ke, gaskiyar maganar kenan da Binta ta fad'a. A ranta godiya kawai ta ke ga Allah, saidai a gefe guda tana jimamin haduwarsu da Antinta Amina, anya lamarinnan zaiyimata dadi?
    Bayan sun kammala ta zauna bakin gado ta zuba tagumi tana kallon Binta wacce ta dage sai an jera kaya a sif, ita kuwa sam bata so hakan ba, gani ta ke kamar za'a maidata sashenta. Ta daga kai ta dubi(Ac) da Binta ta kunna sai aiki ya ke yi, acewarta gwara ta dinga shan ra6a itama ta murje. 
   Aka banko kofar aka shigo babu ko sallama Ikram ce, ta rike k"ugu tana bin dakin da kallo kafin ta yi musu duba na raini. Sai kuma ta kyalkyale da dariya.
"Abinka da wanda bai saba ba kenan."
   Ta dauki(remote) ta kashe Ac, sannan ta dubi Ummi tana yamutsa fuska.
"To sarauniya dangin matsafa ki zo Hajiya na kiranki."
   Daga haka ta fice bayan ta yi wurgi da remote din har yana dukan k'afar Ummi. Ummi murmushi kawai ta yi ba tare da nuna damuwa ba ta dubi Binta.
"Ina zuwa."
Binta ta yi kwafa.
"Wallahi da ni ce ke Ummi sai na gayawa yar banza bak'ar magana, bansan sadda Ikram ta 6aci haka ba. Wallahi ki daina ragamata, ya dace ki dunga kwatarwa kanki 'yanci, ko babu komai yayanta za ki aura."
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

79
  Ummi da har lokacin bata bar murmushi ba ta ce.
"Meye duniya? Wataran don kanta za ta gaji ta bari."
  Binta ta ja tsaki.
"Ai ke daman hakurinki kusan ma ince ya yi yawa, ba fa komai za ki zuba ido ayimiki ba wannan raini ne."
  Ummi ta yi hanyar fita tana fadin.
"Gwara dai na tafi kada na yi laifi."
"Je ki dawo ranki ya dade!"
Ta karashe cikin zolaya, itama Ummin tana jinta bata tanka ba bayan dariya da ta danyi.
  A falon sama ta tarar da Hajiya, agefenta wasu atamfofi ne da leshi. Sai wata mace wacce daga gani ba bahaushiya bace zaune a can gefe. Bayan ta gaishesu ne, Hajiya ta bata umarnin zuwa ga matarnan.
  "Hafsa aunata."
Wacce aka kira Hafsa ta amsa da gur6atacciyar hausarta sannan ta shiga auna Ummi bayan tasa ta cire hijabin jikinta. 
   Saida ta gama sannan Hajiya ta bata umarnin tafiya, haka ta koma daki jiki duk a sanyaye, wato har dinkuna zaayi mata.
   A kwanaki uku kuwa sai ga Hafsa da dinkuna kala goma kala-kala. Atanfa biyar leshi biyu sai wasu yadi guda biyu. Ta rasa bakin godiya tsabar murna, Hajiya kam ta sha addua har saida ta dakatar da ita da fadin"Yiwa Kai ne." A ranar kuma ta hadata da Ikram don ta zuwa siyo kayan undies da na shafa. Jin da Ikram ne Faruk ya kira wayar Ikram ya yi mata gargadi da babbar murya don tun a daren da Hajiya ta sanarmata ta ke faman cika da batsewa, ya tabbatar mata ya lura da hakan. Hakan da ya yi sai ya samawa Ummi lafiya, Ikram na dawowa daga makaranta suka wuce. Har gaba ta ke yi wai don kada su jera da Ummin don ta lura sai wani d'ar-d'ar Ummin ta ke na rashin sabo da shiga ire-iren wajen da sai dan wane ko wance. Don mugunta babu abinda ta za6ar mata saita barta da za6in wannan yasa Ummi ta d'ibi undies kala bibbiyu, a 6angaren shafa ma ta rasa kalar da ya dace kawai sai ta dauki wani(Cream) da batasan ko na menene ba, hoda ma ta dauki daya sai janbaki da jagira, daganan Ikram ta fiddo kudi masu yawa ta ciri adadin abinda Ummin ta dauka ta biya suka tafi babu mai yiwa wani magana. Ummi gaba daya sai ta ji tausayin kanta, wane irin rayuwa ne haka za ta yi cikin mutanen da suka fi ta? 
'Allah Ka dafamini." Ta fad'i a ranta.

Yana kwance yasa filo tsakaninsa da mahaifiyartasa sannan ya dora kansa saman filon suna 'yar hira akan ginin gidansa wanda ya yanzun ya yi nisa sosai. A haka suka yi sallama suka shigo, ya lumshe ido jin muryar abar kaunarsa kafin ya bude ya kai idanunsa gareta. Bata ko kalleshi ba saboda idon Hajiya dake kansu, ya mike zaune gami da rungume filon kujerar a kirji. 
   "Wash! Sannunku da gida." Cewar Ikram, itama Ummi ta gaishesu. Sannan ta mike don zuwa gabatar da Magriba don a hanya ta yi musu. Kasancewar Ikram na fashin sallah, ta dakata gami da budewa Hajiya ledar kayayyakin kamar yanda ta buk'ata. 
  Tun ganin kayan Faruk ya daure fuska, ya yi shiru yana jiran abinda zai fito daga bakin Hajiya. Ita dinma fuska ba walwala ta dubi Ikram.
"Menene wannan ki ka kwaso kuma? Wannan cream din nasa haske fa?"
  Ta girgiza kai.
"Ita fa ta za6i abinta wallahi, bari na yi ta za6i abinda ranta ke so."
  Suna hada ido da Faruk ya watsamata wani mugun kallo da ya yi sanadin kadawar yan hanjin cikinta, ta daure ta kauda kai. Baice komai ba, yana ji Hajiya ta hauta da fad'a sosai akan wannan ba daidan ba da ta yi mata. 
"Haka na sanyaki? Bance ki za6omata ba? Ko don kinsani ita din bawani za6e zata yi ba?"
   Gogan waya ya hau dannawa abinsa yana mai nazari, amma kwarai Ikram ta rainashi, wannan ba Ummi ta raina ba, shi ta raina. 
  "Ai dole sai kin koma gobe..."
"Is ok Hajiyata, ki yi hakuri."
Ya katse Hajiya da ke faman sababi, ta mike ta wuce sashen Daddy daman yana nafilfilu shiyasa ta zauna nan.
   Bayan fitarta ya dubi Ikram.
"Tashi muje."
Ta kasa motsi ta hau ba shi hakuri, ya dakamata tsawa.
"Na ce ki tashi!" Ba shiri ta mike shima ya mike tsaye ya nufi dakin Ummi, tana zaune saman darduma mai taushi ta idar da salla tana addua, saida ya jira ta kammala sannan ya bata umarnin ta taso. Ba tambaya ta bi bayansa sanye da hijab ajikinta. 
  Tare suka fice bayan ya sanarwa Hajiya ta waya, gudu kawai ya ke shararawa a saman kwalta, har suka isa wani katafaren boutique wanda duk Abuja babu irinsa indai a fannin saida kayan amfanin mace ne. Haka ya shiga ya lodowa Ummi kayayyaki masu matukar kyau da tsada wanda Ikram zata iya rantsewa ita kam bata ta6a amfani da irinsu ba, saidai ta yi ta burin ta siya. Jikinta ya yi sanyi tana kallo takalma kala-kala da kananun kaya masu kyau da tsada amma babu halin ta ce ya siyamata. Ta k'ulu matuka, wato don ya ramawa Ummi ya yi mata haka kamar ba kanwarsa ba, saida ya gama jidar son ransa har da abaya kala uku da kayan shafe-shafe masu kyau da gyara fata sannan ya biya ta hanyar Atmcard dinsa. Haka aka loda kayan a boot wasu a gefen Ikram da ke zaune bayan mota sannan suka tafi, a hanya ma sai jan Ummi da hirar soyayya ya ke tana kakkaucewa, wani abin kuma ya sanyata dariya. Wannan ya k'ular da ikram matuka. 
  Hajiya ita kanta ta yi mamakin yawan kayan da Faruk ya siyo saidai tasan don an 6ata mishi ne, yasa Ikram ta shigar mata da su daki, kamar ta yi kukan wannan abu haka ta yita kwasa tana shigarwa. Ya shigo har dakin ya tsaya bayan komawar Hajiya sashen Daddy, ya umarceta da ta jeramata na shafar a gaban madubi, tana hawaye tana yi, Ummi na zaune bata so hakan ba saidai ya hanata motsi, asalima zama ya yi gefenta ya soma nunamata wasu hotunanta a wayarsa da ya dauka batare da saninta ba, soyayya dadi, nan ta mance da wata Ikram, saida ta juyo ta ganta ne yasa ta dan janye daga hirar. Bayan ta kammala yasa ta jera takalman harda su abayoyin da sauran kananun kayan na shigar mutunci a kwaba. Faruk bai bar dakinnan ba saida ta shirya komai tsaf sannan ya dubeta.
"Get out now."
   Ya fada gami da maida dubansa ga abar kaunarsa, ta dubesu suna hada ido da Ummi ta watsamata harara sannan ta fice tana goge fuskarta. 
  "Da ka barshi wallahi zanyi Yaya Faruk, ba ka gudun janyomin bak'in jini?"
  Ya daga kafada.
"Sun jima basu yi ba, karki damu kanki ai kin wuce haka a wajensu, kannenmu ne fa."
Ta yi murmushi kawai can kasan ranta damuwa ce fal, ta lura shi ko a jikinsa, dakyar ta korashi kada Hajiya ta ganshi. Ya fice yana dariya ta bishi da kallo tamkar ta hadiyeshi don so.
                    ***   ***   ***
                         KANO
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

80
                         KANO
Ranar litinin ya kama na tafiyar Adnan, ranar ne su Rahila da Aisha suka zo gidan. 
  Suna zaune a dakin Mami su duka banda Adnan sai kuma Mamin dake labartamusu batun auren Ummi da Faruk. Salati su Rahila suka shiga yi.
"Tabdi! Ni narasa ma yanda zan fassara wannan lamarin? Wallahi karki sake ki yarda a had'a darajarki da wata can wacce ba komai ba. Anya haka Ummi ta barsu?" Rahila ke maganar cikin 6acin rai.
"Wallahi nima ina tunanin da walakin, goro a miya. Amma don Allah ku yi tunani, ta ya ya Yaya Faruk zai so Ummi har ma wai ace son aure ya ke mata? Na yarda yarinya ba laifi ta hadu saidai anya kuwa ba zaa bawa Hajiya Babba shawara akan dagewa da rok'on Allah ba? Nikam wallahi ina tantama idan bawan Allahn nan cikin hayyacinshi ya ke."
Ta k'arashe cikin jimami, Ihsan na jinsu saidai takaici ma ya sa ta kasa cewa komai. Mami ta ta6e baki.
"Su suka sani, idan aure ne suyi ta yi, munanan sai ta auri wanda yafi Faruk din kud'i in sha Allah."
  Haka sukayita tofa na bakinsu, ko kusa Mami bata sanarmusu da sa'insar da ta shiga tsakaninta da Hajiya Mama ba. Sai a ranar ma ta daure ta amsa wayar Hajiya Babba, ta kuma fadamata cewar Ihsan kam ta hakura da Faruk akwai wanda ke sonta.
  Hajiya Babba gaba daya ta fahimci Madina fushi ta yi, ta nunamata hakan ma karin dankon zumunci ne idan akayi.
  "Kenan za'a fasa da Ummi ya aureta ita kadai?"
Hajiya Babba daga can ta dan yi shiru, ina ita ina yiwa Sadaukinta wannan gangancin?
"A'a Madina, menene idan ya auresu duka? Ina ce shi ya ga zai iya?"
Mami ta yamutse fuska ta ji haushin maganar sosai. 
  "To Ihsan dai ta dawo kuma ta tabbatar min matukar ba ita kadai zai aura ba to bata son auren."
   Hajiya Babba ranta ya 6aci, wannan son kai ne kawai.
"Amma Madina kin ban mamaki, menene ciki..."
"Don Allah Hajiya ke babba ce, ina ganinki da girma, na gayamaki raayin 'yata tunda bazai samu ba hakan to don Allah ki samamin lafiya, aure kuma idan ana daurawa sau dari a daura na Faruk da Ummi."
Daga wannan ta kashemata waya.
     A daren Adnan ya tafi, koda suka hadu da su Rukayya a(airport) hankali kwance suka gaisa yanda suka saba don babu wanda yasan wani abun, sun yi hotuna har Adnan na hawaye suna tayashi, haka suka yi bankwana cike da jin kewar juna.
                 
Hajiya Mama na zaune a falonta tana kallo, yayinda Amina ke gefe daga kicin tana 6arar tafarnuwar girkin rana, yaran gaba daya sun wuce makaranta. Lokacin karfe sha daya na rana. Wayarta ta dauki kara, Hajiya Babba ce, gabanta ya fadi, to har yaushe ne za ta yi ta 6oyon wannan lamari ga yayartasu? Ta rage k'arar talabijin ta dauka. Bayan sun gaisa Hajiya Babba ta jefomata tambaya.
"Sadiya ya za ki 6oyen gaskiyar yanda ku ka yi da Madina?"
  Hajiya Mama ta gyara zama, shikenan fa ranar da ta ke gudu ya zo don jin muryar Hajiya Babba ta yi duk a sanyaye. Kafin ta nemo abin fadi Hajiya Babba ta zayyane mata yanda suka yi da Madina ta waya. Ran Hajiya Mama ya 6aci.
"Bata isa ba wallahi ta yi kadan, auren Faruk da Ummi saidai ikon Allah ne kadai zai sa a fasa shi, Madina ta raina mutane. Hajiya kada ki soma yarda da wannan banzan maganarnata, itace sama da mu ne?"
  Cikin damuwa Hajiya Babba ta ce.
"Sadiya zumunci nake dubawa, da dai Madina za ta yarda da tsarina da nafi kowa jin dadi."
  "To Hajiya tunda ta nuna mana iyakarmu ba sai mu fita hanyarta ba? Ko ita ce ta haifemu?"
  "Hannunka bai ru6ewa ka yanke ka yarr Sadiya. Bari dai zan duba na gani, idan na samu zuwa Kano a satinnan zan zo mu hadu a tattauna."
  Hajiya Mama bata so hakan ba sai don dai Hajiya Babbar ta dage akan hakan ne, dole ta amince suka yi sallama akan hakan.
      Amina dake kicin mutuwar tsaye ta yi jin an ambaci wata kamar Ummi kuam wai da Yaya Faruk aure. Anya kumnuwanta sun jiyemata daidai? Sai kuma ta ji Hajiya Mama na faman surutai tana fadin.
  "Ai ba ita ta haifemu ba, a da Ummi ke yar aiki amma yanzu yarinya ta tashi anan, sai ta hada diyartata kishi da yayan masu da shi, shegantaka kawai." 
Batasan lokacin da ta bar abinda ta ke ba tana salati, ta dafe kai don tsananin kaduwa, ji ta ke kamar ta saki fitsari anan, haka Ummi ta yi? Ina shawarar da ta bata? Shikenan ta kawo rarrabuwar kai acikin zuri'ar nan. Hawaye ta ji ya soma zubomata, inama tana da hanyar da zata bi ta samu Ummi koda ta waya ne su yi magana, anan kam babu abinda za ta ji sosai. 
'Ba ki yiwa kanki dabara ba Ummi, ba ki kyautawa rayuwarki ba.' Ta fad'a a ranta cike da tausayin Ummin, kokisa bata son abinda zai ta6ata, ita mamakin ma karfin halinta ta ke yi na yanda ta iya bari suka kai ga haka da Faruk wai magana har kunnen iyaye? Sai kuma ta tuna abin na Allah ne, idan Ya yi babu mai iya hanawa. Ta sauke ajiyar zuciya.
'Allah Ya kauda dukkan fitinu. Ya yi miki za6i na alheri a rayuwa.'
Daga nan ta cigaba da aikinta bayan ta je ta rage marar, yinin ranar cikin sanyin jiki ta yishi, tunaninta ko wane yanayi Ummin ke ciki a Abuja? Tasan dai ba kowa ne zai so aurennan ba. 
                  ***   ***    ***
              BAYAN SATI DAYA        
                         ABUJA
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
   81
              BAYAN SATI DAYA        
                         ABUJA

  Ummi an soma gogewa, fatarta fara ta kara haskawa sai sheki da wani sul6i da jikinta ke k'arawa, hakanan har wata 'yar k'iba ta yi, Ikram kadai ce matsalarta sai kuwa Baraka da matar Babban Yaya(Fadila) da Jidda idan sun zo. Su dinma a fili suke nuna rashin goyon bayansu. Wannan abu na yi mata zafi saidai fad'an da ya fi karfinka....!
   Hajiya Babba ta bi jirgi zuwa Kano ita kadai tun ran alhamis, gidan ya rage daga Ikram sai kuwa su din.   Ranar Asabar misalin biyar na yamma Ummi zaune acikin (garden) tana sauraron wakokin hausa a waya wadanda Binta ta aikamata su

Please Login or Register in order to submit comment