Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

daya jikinta yayi sanyi, cikin rawar murya tace.
"Eh su kadai ne masu d'an dama-dama Hajiya."
Hajiya tayi shiru da mamaki, kafin tace. "Daukomin duka kayanki nagani."
Ta mik'e da sauri ta cika umarninta, Hajiya ta sanyata ta zazzagesu. Kayan duk ba wani na kirki kam da gaskiyar Ummin.
"Kwashesu ki maida ledar, kada su koma wannan d'akin. Fita kimin kiran Ramma."
Ta amsa da toh, ta mayarda kayan jaka sannan ta fita ta kira Ramma. Tana ji Hajiya tace idan ta kammala tayi magana zata bata kudade gobe ta shiga kasuwa ta siyo mata kananun atamfofi guda hud'u sai dogayen riguna yan kanti su kuma guda uku sai wanduna da vest guda shida-shida. Ramma ta amsa da toh, zata mike Hajiya ta dakatar da ita.
"Tafi da wannan ledar a zubar don Allah." Ramma na dariya ta dauka tayi gaba tana fadin toh.
A washegarin kuwa Ramma bata zo da wuri ba sai wajen sha d'aya na safe. Sai gata da kayan da Hajiya ta umarceta. Hajiya ta duba sannan ta bata atamfofin ta kai dinki, tayi kiran Ummi ta mik'a mata ledar kayan ta kara jaddada mata cewa ta kula da tsaftar jiki da dakin da take kwana. Ummi ta amsa tayi godiya ranta fari k'al ta zubawa Hajiya ruwan addua wanda hakan ba k'aramin faranta Hajiya Madina yakeyi ba. Saida ta shiga ta zazzage kayan tana duba, ai kuwa dai abinda Hajiya ta karanto shi d'in aka sissiyo harma da k'arin man shafawa da turare (Lovilla) na roba. Har wani tsalle tayi na murna, ko babu komai a makaranta yan ajinsu zasu dinga jin tana k'amshi kamar yanda ta ga yan babban aji a makarantar suna yi idan sunzo giftasu ko kuma monitoci.
☆☆☆
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

10

 Wani ajiyar zuciya Ummi ta saki ganin yanda aka k'awata farfajiyar gidan da shukoki, wurin motocin da ta hango acan wata 'yar rumfa ta ga sun nufa suma, saidai bai karasa ba ya faka.  Duk suka fito, sannan ya karasa ciki.
  Suna gaba tana binsu a baya hannunta rike da Fahad wanda zuwa yanzu ta saba da shi ba kad'an ba kasancewarshi yaro mai son mutane. Banda kalle-kalle babu abinda takeyi har suka iso wata kofa da kai tsaye ta sadasu da wani dan karamin tsakar gida wanda aka dan yi gewaye a tsakiyarsa aka dasa shukoki. Ihun da ta ji ne ya katseta, wasu yan mata ta gani sun rungume Ihsan yayinda shima Adnan ya hau cafkewa da wasu maza a karshe suka hau rungumar juna ana dariya. 
   'Wadannan kuma su wanene?' Ta wurgawa zuciyarta tambayar, bata kai ga gama tantancewa ba ta k'ara ganin wasu yanmata biyar suma sun fito  suna fadin oyoyo Anti Mami. Ukun dai ta sansu, da Intisar ne da Rukayya da kuma Maryam yaran Hajiya Mama, biyun ne dai bata sansu ba duk kuwa da cewar sun had'u a sunan Aisha. 
  Bayan sun kammala rungume-rungumensu ne suka dunguma zuwa ciki gaba daya. Ihsan ta juyo da sauri ta matso daidai gefen Ummi. Tana dubanta duba na raini tace.
  "Saura kiyi karambanin biyomu, ki nemi wuri ki zauna anan."
  Ta amsa da toh sannan ta ja baya ta fasa niyyarta na binsu. Bayan shigewarsu ta koma can gefe ta ja kujerar roba daya cikin hudun da ke zagaye da tebur ta zauna ta zabga uban tagumi. Ko kusa bata ganin laifin Ihsan, daman ai ita ba wata bace a wajensu face  yar aiki, dole ne kuma ta cigaba da amfani da nasihun Antinta gudun abinda zai jawo a dizgata gaban mutane. 
  'Dizgi?' Ta  tambayi zuciyarta, toh kuma dizgi ya wuce wanda ta gama sha awajen shakikanta wadanda su kadai ne zata iya bugun kirji ta kira a matsayin nata? Sun gujeta sun manta da ita, tunda suka kawota har gashinan ta kusa yin wata a garin da babu iya babu baba, a wajen mutanen da bata da had'i da su sai na Allah. Bata kara sanin tayi rashin uwa ba sai bayan ta soma zuwa makarantar islamiyya, yanda ake kara koyar dasu gami da nuna musu muhimmancin biyayya ga iyaye. Ita kam bata da wannan gatan, har fargabar ranar da Hajiya zata gaji da ita ta koreta daga gidanta takeyi, tana rantsuwa da Allah batasan hanyar da zata bi ta koma garinsu ba a karan kanta matukar ba Yaha ce zata zo ta maidata ba. 
  Daddad'an kamshi da kuma zazzakar muryar da ta tsinta awajen ne ya katse mata tunani, ta d'ago kanta tana duban mai ita. 
   Tsaye yake ya zura hannunsa na hagu acikin aljihun wandonsa, hannun damansa kuwa, waya ce wacce ya kafa a kunne. Farin bafulatani ne, kansa cike da suma, saje a kwance saman fuskarsa yayi luf-luf. Yana da matsakaicin tsawo,hakanan yana da fadin fuska kadan, idanuwansa daidai misali hakanan siririn karan hancinsa da tsukakken le66ansa ruwan hoda, ya kara taimakawa wajen fiddo da tsantsar kyawun halittar da Allah Ubangiji Ya mishi. Sanye yake cikin shadda ruwan k'asa, kansa babu hula, agogon daya d'ora a hannun hagunsa ya kara fiddo da kyawun hannunnsa wanda ke cike da gargasa.
  A tsanake yake fidda kalmomi, hausa da turanci kawai yake gwamutsawa, idan yayi hausa, can gaba kuma ya jefa turanci, abin sai ya burge Ummi. Tayi shiru ta zubamasa ido tana sauraron yanda yake hada yare biyu lokaci guda duk da cewa ta sha jin hakan daga Ihsan, saidai ko rabin kwarewarsa Ihsan batayi ba. Daidai lokacin da yayi sallama da wanda suke wayar da shi, suka had'a ido, babu shiri tayi gaggawar janye nata idanun daga gareshi. Koda ta k'ara d'agowa, bata ganshi a wajen ba don tuni ya koma ciki. 
   Ta sauke ajiyar zuciya, ta tuno da 'yar ajinsu wata Khadija, wacce bata da aiki sai hirar samari a aji, burinta bai wuce ta samu namiji kyakkyawa kuma mai kudi ta aura ba. Har mamaki suke bata, duka-duka tasan da wuya idan suma zasu fi shekara goma sha biyar kamar ita(GYARA) amma har ace sun waye da batun samari har haka, sai kuma ta tuna da cewar da ace a kauyensu ne da tuni watakila itama an aurar da ita. Abin kuma sai ya sanyata murmushi, wa zai aurar da ita? Ai kenan ma  Saude ta nunamata gata, akan kunnenta ta sha jin tana fadin saidai ta karar da rayuwarta a bauta mata, aure ne saida ta ga ana yi ba dai ita tayi ba. Hawaye ta ji suna kokarin taho mata da takaici, gaskiyar Saude tunda yanzun ma gatanan acikin hali na aikatau wanda duk a sanadinta ne, kudin da ta riga tasan na amfaninsu ne banda ita. An barta dai da wahalar.
  "Kamota nan!"
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

11

Firgigit ta dubi wanda ya tsoratatan don gaba daya ta zurfafa cikin tunani. Ganin Amina yasa ta mikewa tsaye da mamaki, sai kuma suka hau dariya.
"Kai Ummi, tunanin me kikeyi haka wai?"
Ummi wacce ta kasa rufe bakinta don tsabar murnar ganin Amina ta amsa da fad'in.
"Bakomai, kikacemin ba zaki zo ba?"
Amina dauke da murmushinta na sabo tace.
"Wallahi ban saka ran zanzo ba, Hajiya Mama ta matsamin akan na biyosu kawai."
Abin ya bawa Ummi mamaki, ta kara gaskata cewa Hajiya Mama ba ruwanta.
Amina ta dubi ledar hannunta.
"Ina zuwa bari na mikawa Anti Rahila famfas nazo."
Daga haka ta shiga ciki da sauri ta nufi ciki. Ummi ta koma ta zauna ranta yayi fes cike da murnar sake haduwa da Amina wacce ta dauki matsayin Anti kacokam ta bata ba don komai ba sai don yanda ta nuna kauna gareta a farkon haduwarsu da kuma yanda take da kokarin yi mata gyara aduk lamuranta na rayuwa. Bata jima da shiga ba sai gata kuma ta fito, tana kokarin jan kujera ta zauna ne ta dubeta.
"Meyasa baki shiga ciki ba?"
Ummi ta zaro ido kadan.
"Ciki kuma? Um um, Ihsan tace kada na sake na shigo."
Amina ta ja guntun tsaki.
"Bansan sadda yarinyar nan zata dawo saiti ta gane cewa shima dan aiki mutum ne ba. Ki dai kara hakuri."
Murmushi kawai Ummi tayi.
"Anti 'yan Abuja ma sunzo ne?"
"Su ai tun jiya suna garinnan, basu je gidan Mami ba kenan? "
Ta girgiza kai.
"A'a."
"Sunzo, Ikram, Baraka, Yaya Usman, Yaya Ridwan, Yaya Haidar da kuma Yaya Faruk."
Jinjina kai kawai Ummi tayi batare da tace uffan ba.
Sai kuma suka fad'a hirar da ta shafesu, sun jima sosai anan kafin kuma wata dattijuwar mace ta leko.
"Ke Amina, kuzo ku taimaka mu kaiwa bak'i abinci."
"Toh Larai."
Ta dubi Ummi.
"Muje."
Ummi ta mike gaba daya sai ta ji wani nauyi, kamar kada ta je haka take ji, fatanta kada Ihsan ta ci zarafinta a bainar jama'a. Takalma baja-baja a dan koridon shiga falon, suka shiga da sallama. Saidai abin mamaki bata ga kowa anan ba sai ta dunga jiyo muryoyi da dariyarsu daga can sama, hakan ya tabbatar mata suna can. Zugui-zugui tayita bin Amina har zuwa wani kicin mai girma. Nan taga kuloli manya guda hudu sai tarkacen filettoci da cokula da kofina a saman teburin dake tsakiyar kicin din.
"Yauwa ku soma kaiwa, Amina ga ledar nan ki soma da shinfid'ata."
"Toh" kawai Amina tace sannan ta ja linkakkiyar ledar ta hada da filas guda d'aya, itama Ummi ta dauki filas d'aya don girma ne da su, ta bi bayanta suka soma taka bene.
★★★★★

Wani sanyi da daddadan kamshin (roomfreshner) ne ya soma yi musu marhabin kafin dariya da hirar jama'ar falon ta doki kunnawansu. Suka shiga da sallama, Ummi gabanta banda bugu babu abinda yakeyi. Ga wadanda kunnensu ya ji suka amsa musu sallamar, wadanda basu ji ba kuwa, sai hira suke.
Babban falo ne wanda ba'a cikashi da kayan ado sosai ba, saidai iyakar wadanda aka dan kawatashi da su masu kyau da tsada ne. Kujeru masu jikin leda farare tas ne zagaye a tsakiyar falon, iyayen na zaune saman kujera harda dattijon kwarai, wato maigidan Alhaji Atiku Modibbo, tare da uwargida ran gidansa, mahaifiya ga Hajiya Fatima, Hajiya Madina da karamarsu gaba daya wato Hajiya Sadiya(Hajiya Mama).
Sune a zaune saman kujera, su kuwa jikokin suna a kasan tattausan kafet din dake shimfid'e a tsakar falon. Kallo d'aya Ummi tayiwa 6angaren da suke tayi gaba ta bi bayan Amina zuwa inda ta nufa. Tsakiyarsu ne Amina ta shimfid'a katuwar leda ta cin abinci, suka ajiye komai anan. Anan ne ta ji Amina ta shiga gaishesu, itama ba shiri ta gaishesu. Ba zata iya tantance wadanda suka amsa ba da kuma wadanda basu amsa ba don kuwa sauri takeyi su bar wajen, haka kawai ta kara jin ta raina kanta, ji take kamar wari takeyi ma tsabar kamshin wajen. Cikin yaren fulatanci ta ji wata cikin yanmatan tayi magana da bata fahimci ko menene ba. Gaba daya matasan suka dara, tana ganin sadda wani a samarin ya jefamata filo.
"Baki da kirki."
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

10

Wani ajiyar zuciya Ummi ta saki ganin yanda aka k'awata farfajiyar gidan da shukoki, wurin motocin da ta hango acan wata 'yar rumfa ta ga sun nufa suma, saidai bai karasa ba ya faka. Duk suka fito, sannan ya karasa ciki.
Suna gaba tana binsu a baya hannunta rike da Fahad wanda zuwa yanzu ta saba da shi ba kad'an ba kasancewarshi yaro mai son mutane. Banda kalle-kalle babu abinda takeyi har suka iso wata kofa da kai tsaye ta sadasu da wani dan karamin tsakar gida wanda aka dan yi gewaye a tsakiyarsa aka dasa shukoki. Ihun da ta ji ne ya katseta, wasu yan mata ta gani sun rungume Ihsan yayinda shima Adnan ya hau cafkewa da wasu maza a karshe suka hau rungumar juna ana dariya.
'Wadannan kuma su wanene?' Ta wurgawa zuciyarta tambayar, bata kai ga gama tantancewa ba ta k'ara ganin wasu yanmata biyar suma sun fito suna fadin oyoyo Anti Mami. Ukun dai ta sansu, da Intisar ne da Rukayya da kuma Maryam yaran Hajiya Mama, biyun ne dai bata sansu ba duk kuwa da cewar sun had'u a sunan Aisha.
Bayan sun kammala rungume-rungumensu ne suka dunguma zuwa ciki gaba daya. Ihsan ta juyo da sauri ta matso daidai gefen Ummi. Tana dubanta duba na raini tace.
"Saura kiyi karambanin biyomu, ki nemi wuri ki zauna anan."
Ta amsa da toh sannan ta ja baya ta fasa niyyarta na binsu. Bayan shigewarsu ta koma can gefe ta ja kujerar roba daya cikin hudun da ke zagaye da tebur ta zauna ta zabga uban tagumi. Ko kusa bata ganin laifin Ihsan, daman ai ita ba wata bace a wajensu face yar aiki, dole ne kuma ta cigaba da amfani da nasihun Antinta gudun abinda zai jawo a dizgata gaban mutane.
'Dizgi?' Ta tambayi zuciyarta, toh kuma dizgi ya wuce wanda ta gama sha awajen shakikanta wadanda su kadai ne zata iya bugun kirji ta kira a matsayin nata? Sun gujeta sun manta da ita, tunda suka kawota har gashinan ta kusa yin wata a garin da babu iya babu baba, a wajen mutanen da bata da had'i da su sai na Allah. Bata kara sanin tayi rashin uwa ba sai bayan ta soma zuwa makarantar islamiyya, yanda ake kara koyar dasu gami da nuna musu muhimmancin biyayya ga iyaye. Ita kam bata da wannan gatan, har fargabar ranar da Hajiya zata gaji da ita ta koreta daga gidanta takeyi, tana rantsuwa da Allah batasan hanyar da zata bi ta koma garinsu ba a karan kanta matukar ba Yaha ce zata zo ta maidata ba.
Daddad'an kamshi da kuma zazzakar muryar da ta tsinta awajen ne ya katse mata tunani, ta d'ago kanta tana duban mai ita.
Tsaye yake ya zura hannunsa na hagu acikin aljihun wandonsa, hannun damansa kuwa, waya ce wacce ya kafa a kunne. Farin bafulatani ne, kansa cike da suma, saje a kwance saman fuskarsa yayi luf-luf. Yana da matsakaicin tsawo,hakanan yana da fadin fuska kadan, idanuwansa daidai misali hakanan siririn karan hancinsa da tsukakken le66ansa ruwan hoda, ya kara taimakawa wajen fiddo da tsantsar kyawun halittar da Allah Ubangiji Ya mishi. Sanye yake cikin shadda ruwan k'asa, kansa babu hula, agogon daya d'ora a hannun hagunsa ya kara fiddo da kyawun hannunnsa wanda ke cike da gargasa.
A tsanake yake fidda kalmomi, hausa da turanci kawai yake gwamutsawa, idan yayi hausa, can gaba kuma ya jefa turanci, abin sai ya burge Ummi. Tayi shiru ta zubamasa ido tana sauraron yanda yake hada yare biyu lokaci guda duk da cewa ta sha jin hakan daga Ihsan, saidai ko rabin kwarewarsa Ihsan batayi ba. Daidai lokacin da yayi sallama da wanda suke wayar da shi, suka had'a ido, babu shiri tayi gaggawar janye nata idanun daga gareshi. Koda ta k'ara d'agowa, bata ganshi a wajen ba don tuni ya koma ciki.
Ta sauke ajiyar zuciya, ta tuno da 'yar ajinsu wata Khadija, wacce bata da aiki sai hirar samari a aji, burinta bai wuce ta samu namiji kyakkyawa kuma mai kudi ta aura ba. Har mamaki suke bata, duka-duka tasan da wuya idan suma zasu fi shekara goma sha biyar kamar ita(GYARA) amma har ace sun waye da batun samari har haka, sai kuma ta tuna da cewar da ace a kauyensu ne da tuni watakila itama an aurar da ita. Abin kuma sai ya sanyata murmushi, wa zai aurar da ita? Ai kenan ma Saude ta nunamata gata, akan kunnenta ta sha jin tana fadin saidai ta karar da rayuwarta a bauta mata, aure ne saida ta ga ana yi ba dai ita tayi ba. Hawaye ta ji suna kokarin taho mata da takaici, gaskiyar Saude tunda yanzun ma gatanan acikin hali na aikatau wanda duk a sanadinta ne, kudin da ta riga tasan na amfaninsu ne banda ita. An barta dai da wahalar.
"Kamota nan!"
[8:55am, 12/4/2016] Sister ruffy: DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

14

 Anan falon farko ta iske yanmatan suna ta hirarsu. Gaba d'aya suka zubomata ido. Ta gaishesu suka amsa suna binta da kallon tara saura. Bata kara cewa uffan ba ta yi hanyar falon Mami. 
  "Wannan 'yar aikin taku ai har ta so ta k'ere ki a kyau."
   Abinda ya daki kunnuwanta kenan har saida ta ji faduwar gaba. Ta tabbatar da Ihsan sai ta fusata. 
  Da sallama ta isa falon, Hajiya Babba (Hajiya Fatima) na zaune  saman darduma tana addu'a yayinda Mami ke zaune saman kujera tana danna waya. Ganinta baisa ta d'ago kanta ba. Ta durkusa ta gaisheta. Mami ta amsa har lokacin idanunta na kan wayarta.
  "Ya akayi ba ki wankemin bandaki ba?"
  Sai lokacin ta tuna, shaf ta mance sakamakon sadda zata wuce makaranta, Mamin na wanka, hakan yasa ta fice da zummar idan ta dawo sai tayi. Cikin tausassan muryar Ummi, ta amsa.
  "Kiyi hakuri don Allah Mami, dazun kina wanka shiyasa ban samu yi ba."
  Kafin Mami tayi magana Hajiya Fatima ta rigata.
  "Wannan 'yar fulanin fa Madina?"
Mami ta dubeta.
  "Ummi ce, ita ku ka gani ranar (meeting) dinnan ai. Aiki takemin."
  Hajiya Fatima ta sauke mayafinta har lokacin tana duban Ummi wacce ta gaisheta, ta amsa mata. 
   "Shikenan ai, shiga kiyi yanzu."
  "Toh."
  Ta mike ta shiga d'akin Mamin. Kai tsaye band'aki ta nufa. Cikin mintuna baifi goma sha biyar ba ta kammala wanke band'akin ta fito.
  Acan kuwa bayan shigewar Ummi, Hajiya Babba ta dubi kanwarta.
  "Ga dukkan alamu kinyi sa'ar mai aiki wannan karon Madina, na lura yarinyar tana da nutsuwa kamar ba zata bada matsala ba."
  Mami ta jinjina kai da murmushi dauke saman fuskarta, ko babu komai tana jin dadi idan wanda ya fita ya dame ta a kudi da komai na rayuwa ya yabi wani abu nata. Tabbas Mijin Hajiya Babba ya fi nata kudi da komai, da shi ake damawa a k'asar gaba d'ayanta kasancewarshi tsohin soja wanda a shekarun baya ake matukar ji da shi. Bayan wannan ma, ita kanta Hajiya Babba tana kasuwanci sosai, takan fita zuwa Dubai ta saro kayayyaki, a yanzun da yaranta suka tasa, sai ta hutarwa kanta don kuwa Yaya Usman shi ya cigaba da fita yana saro mata, a karshe sai ta bud'e shago babba na suturun mata.  Shiyasa babban burinta bai wuce Faruk ya nuna yana son Ihsan ba, koda ita Ihsan din ta nuna, to babu abinda zai hana auren. 
   Ta gyara zamanta ta numfasa.

   "Haka Ummi take, a farko ma nayi zaton rashin sabo ne, sai bayan ta kwana biyu na gane haka halittarta take, bata da rawar kai sannan ba laifi tana da kamun kai."
   Hajiya Babba ta girgiza kai.
"Kai ai kuwa kinyi sa'a, ni kinga da na dauki mai shekarunta bamu wanye lafiya ba, don saida ta dankaramin sata na kudi da sutura sannan ta gudu."
  Mami ta mike sosai ta zauna tana dubanta.
  "Yaushe akayi wannan banda labari?"
  Nan akalar labarin ta chanja. Acikin wannan hirartasu ne, Ummi ta fad'o falon bayan ta kammala, a ladabce ta sanarwa Mami ta kammala. Mami ta amsa da toh shikenan, daga nan ta mike ta fice. 
     A falon farko ta tarar da 'yan matan da mazan sai hira da dariya sukeyi. Kallo d'aya ta yiwa 6angaren da suke ta kauda kai, ta so ta wuce batare da ta gaishesu ba gudun kada Ihsan ta k'aramata wani sharrin, saidai ta ji ba zata iya aikata hakan ba, ta durkusa daga nan bayan kujera ta gaidasu. Hankalinsu sam baya kanta don ya tafi a hira hakan yasa basu ko lura da ita ba. Tana kokarin mikewa suka had'a ido da Faruk, kai ya gyad'a mata alamun amsawa, sai ta dan ji sanyi, ko babu komai an amsa mata, ta bar wajen a nutse. Saida ta isa kofar dakinta ta juyo kadan, ga mamakinta idanun Faruk a kanta har lokacin, saidai suna hada ido ya kauda kansa ita dinma da sauri ta fad'a d'akin ta rufe da mamaki dauke saman fuskarta wanda ko kadan ya gaza 6uya. Toh shi kuma wannan haka yake da kallo? Ta tambayi kanta, sai kuma ta girgiza kai had'i da ta6e baki. Yunwa ta ji ya addabeta, rabonta da abinci tun wajen sha biyu na rana, ga shi batason fitowa ba don komai ba sai don nauyin mutanen falon da take ji. Hakanan ta hakura ta yi sallar isha'i sannan ta zauna tana jiran tafiyarsu. Babu jimawa sosai ta tsinci muryar Mami tana kiranta. Da sauri ta fito falon, Hajiya Babba tare da ita suna tsaye, Hajiya Babba ta sha mayafi ta zura takalmanta.
  "Dauki ledar can ki bi bayan su Ihsan a sanya a mota."
  "Toh Mami." Ta fad'a a ladabce sannan ta bi umarninta.
[8:56am, 12/4/2016] Sister ruffy:   DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR
   
    15

  Anan ta iskesu tsaitsaye ana hira banda babban yaya wato Yaya Usman da ke zaune cikin mota tare da Faruk wanda gaba d'aya ya matsu su koma gida don jinsa yake a gajiye. 
   Ihsan ta bita da kallon harara, hakan yasa ta kauda kanta.
  "Kanki ake ji." Ta fad'a a ranta. Ta dubi wata doguwar budurwa siririya bak'a, bata san itace Ikram ba ko kuma Baraka, don sunayensu kawai Amina ta sanarmata ba ta nunamata su ba a fuska. 
   "Ga wannan a ina zan ajiye?"
  Ta dubeta, sannan ta nunamata motar da yatsa batare da dogon bayani ba. 
   "Kinga, saka anan."
Ta dubi Yaya Haidar dake nunamata boot wanda yasa hannu ya bud'e. Ta karasa ta ajiye gami da fad'in.
  "Allah Ya tsare hanya." Daga haka ta juya ta bar wajen. 
     
    "Adnan ina mutuniyata ne? Ban ganta ba."
  Adnan ya yamutse fuska yana duban farar budurwar siririya da tayi mishi magana, wato Baraka.
   "Wa kenan?" Ya tambaya cikin basarwa kamar bai fahimci ko wa ta ke nufi ba da gaske.
    "Abokiyar fad'arka mana, your lil sis."
  Ya harareta, ya gane Iklima take magana akai.

    "Ai kinsan hanyar gidansu ko? Sai kije."
Baraka tayi dariya.
  "Kwarai ma kuwa wallahi, idan ma kana ganin kamar bazan iya zuwa ba zaka sha mamaki. Kada fa ka manta k'awata ce, mun riga mun saba da uta adalilin (whatsapp group) da muke ciki tare. Zo muje Ihsan ki rakani."
    
  Ba musu ta ja Ihsan suka tafi. Hajiya Binta suka soma gani a falo tare da Usman, Jabir da Hanif, gaba daya kallo ya daukemusu hankali. Sallamarsu ce ta sanyasu maido hankali garesu. Ta soma shan kamshi yayinda ta amsa ciki-ciki.
  Suka karasa suka gaisheta. Saida ta k'arewa suturar dake jikin Baraka kallo sannan ta numfasa, ta riga tasani iyalan Hajiya Fatima ba su ta6a zama a baya wajen suturu da sauran kayan more rayuwar duniya. 
   "Baraka ko?"
Baraka fuska a sake ta amsa.
"Eh ni ce Umma."
   "Sannu, yanzu kuka zo?"
"Za mu tafi ne dai, ina Iklima?"
  Hajiya Binta ta nunamusu hanya.
"Ku shiga tana d'akinta."
  Suka shige ta bi bayansu da kallo cike da jin wani tuk'uk'i a ranta, dole Madina ta dunga yi musu wani gani-gani kasancewar daga ita har Lubna, ba wasu 'ya'yan masu kudin azo a gani bane, a komai dangin Hajiya Madina sun k'ere musu, yana daga dalilin da yasa suke matukar kishinta. A gefe kuma tana tak'ama da cewar ita din fa jinin Alhajinsu ce, shi kansa Alhajin koda hira akeyi da ya shafi danginsu, sau da yawa yakan yabawa bajintar mahaifin Madina, da irin yanda ya iya rik'e iyali da sauransu. Wannan yasa ko kad'an acikinsu babu mai kaunar suyi wata doguwar hirar da ta shafi dangin Alhaji Modibbo. Babban burinta yanzu, bai wuce yaranta su kasance wasu shahararru ba a fannin kudi, ta ci buri akan Iklima wannan yasa ta haneta abota da dukkan wani jinin talaka, dukkan abokan Iklima 'ya'yan wasu ne. Koyaushe tana hanyar biki da party. Babu laifi takan samu samarin masu ji da kudi saidai da yawansu ba da aure suke sonta ba, saidai wata manufarsu ta daban.

Please Login or Register in order to submit comment