Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na cewar bata kaunar ko kusa ta k'ara takowa Ringim har su hadu da shi.
Ya dago ya dubi Saude da babu inda ba ya kadawa a jikinta tsabar tsoro, cikin alamu na rashin gaskiya ta hau fadan borin kunya.
"Ke Yaha ashe bakar munafuka ce mai shirin kashe auren sunna? Yaushe mukayi haka dake? Inace Malam da kansa ya ce a kaita aikatau?"
Malam Balarabe da har lokacin ita ya ke kallo ya mike yana tunano yanda ta dunga iko da shi har ta rabashi da diyarsa, baisan lokacin da ya cira hannu ya kwasheta da mari ba wanda ya sanyata soma fitsari a wando, kafin ta yi wani yunkurin ya k'ara marinta a daya gefen kuncin. Babu wanda cikinsu ya yi yunkurin hanashi sai Babban Yaya da Ridwan, Faruk kuwa ko gezau baiyiba sai ma wani murmushi da ya ke yi, acikin ransa kuwa godiya kawai ya ke yi ga Ubangiji Ma ji rokon bawa.
Ummi kuwa kuka ta ke yi don ganin lamuran ta ke tamkar a mafarki, tana kukan tana hadawa da dariya. Bata gama mamaki ba sai sadda ta ji marin da Malam ya kwashe Saude da shi.
"Allah Ya isa tsakanina da ke makira! Azzaluma!! Mai fuska biyu!!! Kin cuceni Saude na yi da na sanin aurenki, bana fatan k'ara koda kwakkwaran awa ne tare da ke! Ki ficemin na sakeki! Na sakeki!! Yanda ki ka cuceni ki ka cutarmin da d'iya kema in sha Allah zaayi miki fin haka, duniya ce cikinta muke!!"
Ya dan numfasa kafin ya dora, daidai lokacin wayar Hajiya Babba ta yi kara ganin lambar mijinta ne yasa ta fita wajen cike da tsantsar mamaki da wani mugun tausayin Ummi da mahaifinta.
Malam Balarabe ya nuna Saude da yatsa.
"Hasiya ta daukeki abokiyar zama ba kishiya ba, Hasiya ta bauta miki tamkar kanwarki, abinda Hasiya ta yi miki ko kanwarki da ku ka fito ciki daya ba za ta yi miki ba, yan uwan Hasiya suna miki kallon mutuniyar arziki, ko alheri ne zasu yi, basa ta6a bambantaki da jininsu, ashe ke din da zuciya biyu ki ke tare da su? Da har ki ka kasa rike Ummi riko na gaskiya da amana? Kin cutar da ni! Ni bani da tabbacin ko kina wani abin, amma ina rantsuwa da Allah bansan yanda akayi na kuntata rayuwar diyata ba."
Sai kuma ya sunkuya cikin zubar hawaye wata razananniyar k'ara Saude ta sanya, ta nufi hanyar waje tana fadin.
"Daman Bokanya ta fad'a! Wayyo na shiga uku na lalace!! Allah Ya tsinemaka Balarabe, Allah Ya sa ka gamu da nau'ikan azabobi kala-kala, wayyo ni Saude!!"
Haka ta ke tafe tana surutai kamar wata sabuwar kamu, burinta ta isa ga Bokanya. Mariya zata bi bayan uwarta, Malam ya janyoya a fusace, ta isa ga Yaha tana ajiyar zuciya don ta tsorata yau da babannata.
Hajiya Babba da mijinta suka bi Saude da kallo, ta dubi mijinnata.
"Wannan itace kishiyar uwar Ummin. Bari na shiga na gani."
Gen. Ahmad ya jinjina kai yana mai bin Saude da kallo cike da jimami.
"Baba ni ban ta6a rik'onka a zuciyata ba, duk wani abu da ka yimin na yafemaka, nima ina rokon gafararka har..."
"Kul Hasiya, kar ki ce komai, ni nan ba ki ta6a yimin laifin komai ba, ni ne mai laifin daman. Yanzu kuma tunda gaskiya ta fito, in sha Allahu bazan k'ara aikata makamancin hakan ba."
Dariya kawai ta ke yi tana hawaye, suka hada ido da Faruk ya mikomata hankicif ta kar6a.
"Alhamdulillah, yau ranar sa'a ce. Allah Ya k'ara kauda shaidan."
Cewar Yaha kenan, sai lokacin hankalin Malam ya dawo jikinsa, ya dubi su Hajiya Babba da su Faruk.
"Sannunku, ina wuni."
Nan matasan wadanda mamaki da farinciki ya cika, suka gaisheshi sannan ya juya suka gaisa da Hajiya.
"Saidai ban gane fuskokin ba?"
Ya karashe da duban Ummi fuskarsa cike da fara'a. Itama yau bakinnata ya k'i rufuwa, kafin ta ce komai Yaha ta koro mishi bayanin ko su su waye da kuma abinda ke tafe da su, ta k'ara da fad'in.
"Maigidan ma yana k'ofa tsaye." Jin haka yasa Malam Balarabe mikewa da sauri yana fadin.
"Ya Salam." Daga haka ya fita ya shigo da Daddy soron gidan, bayan sun gaisa.
Tabarma Ummi suka shimfida musu, matasan suka fita waje sai Yaha da su Hajiya a tsakar gidan suna magana kan lamarin Ummi, Mariya kuwa ta yi gum sai kallonsu da ido.
Bayan Daddy ya zauna, suka k'ara gaisawa. Malam Balarabe ya hau mishi godiya sosai da addu'o'i game da taimakonsu ga diyarsa wacce aka so wulakanta rayuwarta.
"Ba komai, wannan yiwa kaine ai."
Cewar Daddy. A karshe ya koro mishi bayanin dake tafe da su. Malam ya yi shiru yana nazari, can kuma ya soma magana.
"Hakika na yi farinciki matukar gaske da wannan magana, sannan na yabawa karamci irinnaku da har ku ka taso daga Abuja zuwa nan don Ummi, tabbas kun kasance cikin mutane masu daraja DAN ADAM, ko don wannan bazan hana Umar auren Hasiya ba. Saidai ina neman wata alfarma daga wajenka Yalla6ai."
Daddy ya gyara zama kadan.
"Ina sauraronka Baba."
"Na yi kuskuren da zan so gyarashi kafin komai ya faru. Ummi da ka ke gani, babu wanda ta sani cikin dangin uwa da na ubanta. Hakazalika ni kaina na manta rabona da zuwa wajen yan uwana. Ina neman alfarmar soma zagayawa da ita muje ta ga dangi idan yaso daga baya sai ayi zancen aurensu. Ina fatan hakan ba zai zamto matsala..."
Cikin 'yar dariya Daddy ya ce.
"Haba Baba, wannan ba matsala bace. Tabbas gaskiya ka fad'i, saidai me zai hana a tsaida lokaci idan yaso kafin zuwan lokacin an zaga dangin?"
Malam Balarabe ya yi shiru, idan ya aminta da hakan tabbas ya kwasowa kanshi aiki babba, yanzu me ya mallaka na aurar da Ummi cikin wadannan mutanen 'yan babban gidan? Ya dan girgiza kai yana duban Daddy.
"Ka yi hakuri Yalla6ai, ni mutum ne da yasan girman alk'awari! In sha Allahu Hasiya bata da miji sai Umar matukar tana sonsa. Ku kwantar da hankalinku, a satinnan in sha Allahu zan wuce da Hasiya."
Cikin gamsuwa Daddy ya jinjina kai.
"Bakomai Baba, hakan ma ya yi, Allah Ya k'ara dankon zumunci."
Cike da jindadi Malam Balarabe ya amsa kafin kuma Daddy ya mik'e.
"Bari mu wuce dare yana yi mana."
Sukayi musayar lambar waya sannan Malam Balarabe ya shiga ciki ya yi kiran Hajiya akan zasu wuce. Ummi ta yi musu rakiya don kuwa ita kanta yanzu zumudin kwana ta ke yi wajen mahaifinta ko ta dandani gatan da ta ke burinsa a rayuwa wanda ta rasa zamanin kuruciya.
Faruk ji ya ke tamkar kada ya tafi, shikenan kuma za suyi nesa da juna? Ya kafamata ido, itama a sace take kallonsa. Gaba daya sai ya bata tausayi ganin yanda jikinsa ya yi sanyi, shi fa gani ya ke tamkar za'a rabasu ne.
Hajiya ta yiwa Yaha kyauta mai tsoka hakanan Ummi itama, suka rabu zuciyoyinsu cike da kewar juna musamman ga masoyan da basu ji tattaunarwar iyayennasu maza ba.
Bayan tafiyarsu suka koma ciki, yaran makwafta sai bin Ummi suke da kallo tamkar tauraruwa. Matan makwafta kuwa wadanda suke jin komai har da dan lekensu don kawai su ga bak'in birni da kuma Ummi. Ai kuwa yara aka yita cika gidan ganin Ummi, da yawansu ma basu santa ba, wadanda suka santa duk sunyi aure a yanzun. Ummi sai hawaye ta ke yi, ta dubi kanwarta Mariya wacce har lokacin ta ke dan kuka-kuka hankalinta na ga mahaifiyarta. Ta jawota jikinta ta rungume.
"Mariya ko?"
Mariya ta gyada kai. Murmushi Ummi ta yi cikin hawaye ta shafi kanta.
"Ni yayarki ce, sunana Ummi."
Jin haka Mariya ta yi kuri da ido tana dubanta, Malam Balarabe dake alwalar sallar Magriba yana duban Ummi diyarsa tamkar ya maidata ciki tsabar so da kauna ta uba da da. Komai na Ummi da murmushinta, sanyin maganarta duk irin na Hasiya mahaifiyarta ne, take ya tsinci zuciyarsa ta cika da kewar Hasiya, matar da aka yi musu auren zumunci kenan don kuwa iyayensu aminan juna ne.
"Tashi ki dora alwala kinji Hasiya. Bari naje masallaci."
Ya fada yana dubanta bayan ya idar da alwala, ta amsa da to tana mai jin ranta tas, bayan fitarsa ta cika ruwa a butan ta soma alwala tana duban Mariya wacce ta makure a lungu, daga sun hada ido sai Mariyan ta dauke kai. Murmushi kawai ta yi don ta tausayamata, rashin uwa ai ba dadi. Yanzun ko ina uwar ta tafi?
*** *** ***
Saude da Habiba gaban Bokanya....
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  90

                    RINGIM

  "Wayyo Allah!!" Ta yi furucin da karfi tana mai mikewa zaune a firgice. Malam Balarabe ya tashi a tsorace yana duban Saude. Sai uban gumi ta ke had'awa duk kuwa da cewar garin ya danyi sanyi.
  "Lafiya Saude?"
Ya tambaya cike da fargaba.
Saude dake dafe da kirjinta tana numfarfashi, ta dubeshi, sai lokacin ta dawo hayyacinta. Ta yi tsai da ido tana dubansa domin kuwa tsoro ya ke bata, gani ta ke yi kamar mafarkinta gaskiya ne, wai Malam Balarabe ne da daukarta ya jefa a rijiya bayan ya bata kyakkyawan mari har biyu a gefensa kuwa Hasiya kishiyarta ce tsaye tana faman kyakyatar dariya. 
  "Addua ya kamata ki dunga yi idan kinyi mafarki ba wai ihu ba. Duk kin tsorata ni."
Daga haka ya ja guntun tsaki ya juyamata baya, ta bishi da kallo cikin zubda ruwan hawaye sannan itama ta kwanta rigingine tana goge fuska. 
'Meke shirin faruwa? Kada fa asirinmu ya tonu.'
  Ta ke maganar a zuciyarta, ta kudurta komawa wajen Bokanya gobe don ta k'ara bincika mata lamarin.  Dakyar ta samu ta koma bacci a wannan daren.  
                   ***  ***  ***
                      ABUJA
Mutan Abuja da karfe biyu suka kama hanyar Ringim, wannan zuwa na musamman ne, Hajiya da Gen. Ahmad ne sai ko Babban Yaya da Ridwan sai kuma uban gayyar Faruk da Ummi da Yaha wacce suna shigowa Ringim ta soma rarraba ido na son nuna inda za su sha kwana. Haidar kadai ne bai samu zuwa ba.
Ummi gabanta sai bugu ya ke da sauri-sauri, ga mararta da ta k'ulle, tana cike da tsoron irin cin kashin da za'a yiwa bayin Allahn da suka san daraja ta dan Adam. Wane irin tarba zata samu daga mahaifinnata? Sam, bata da masaniya. Hajiya Babba ta lura da yanayin da ta shiga, ta ji ta bata tausayi don kuwa ta ji daga bakin Yaha irin wahalar da ta sha a hannun ubannata da matarsa, ta dan dafa hannunta, wannan yasa Ummin dubanta. Murmushi na karfafa gwuiwa ta sakarmata.
"Ki kwantar da hankalinki Ummi, ki yi ta addu'a, babu abinda yafi karfin Ubangijinmu."
   Ta jinjina kai tana dan murmushi. Daga haka ta cigaba da addu'o'inta har Yaha ta nuna layin da zasu shiga.

  Saude ce tsaye rik'e da k'ugu tana faman jan tsaki, a zaune saman kujerar falon, Habiba ce tana faman kai lomar dan wake. Mariya na waje suna wasa da yara.
   "Ki yiwa Allah ki taso mu wuce, wai menene haka?"
  Habiba ta dauki dunkulen dan wake guda ta jefa a bakinta tana mai dubanta cikin yanayi na santi.
  "Ai kwarankwatsa sai na gama, wa ya ce ki yi dan wake alhalin kinsan bana ganinsa na kyale balle kuma da yanzun ma babu abinda na saka a cikina, na fadamiki fa daga kasuwa na fito."
   Ta k'ara sud'e man wanda ya hade da yaji sannan ta cigaba da magana.
"Na fadamiki ki saka ranki a inuwa, ko makamancin tunaninki bazai afku ba, idan yar banza ta takura mana sai ma mu saka Yaha ta maido diyarta ta mu kasheta mu kashe banza."
   Saude wacce ta gaji da tsayuwa ta zauna sai lokacin ta dan numfasa.
"Anya hakan ma bai fi ba?"
  Kafin Habiba ta samu abin cewa, sallamar Malam Balarabe ta karad'e kunnuwansu. Suka dubi juna da mamaki kafin kuma Saude ta yi wuf ta fito. 
  Ya ajiye ledar hannunsa a gefe.
"Malam lafiya yau ka dawo da wuri?"
Ya dauki buta jikinsa duk a sanyaye ya nufi hanyar bandaki yana fadin.
"Ina zuwa."
Ganin yanda ya ke magana a sanyaye ya kad'a yan hanjin cikinta duk kuwa da cewa tasan halittarsa can daman ba mai zafi bane, idan har kaga bacin ransa to ba karamin kai shi bango ka yi ba.
Habiba ta fito rike da kwanon dan wake a hannunta, cikin muryar rad'a ta ce. 
"To bari na koma na cigaba da bawa cikina hakkinsa kafin nan kun kammala."
Ta karashe da dariyar shakiyanci Saude na harararta.
"Malama yanzu zan shigo."
Ita dai Habiba ta sa kai ta fice. 
  Bayan fitowar Malam Balarabe ya ja kujera yar tsugunno ya zauna gami da zabga uban tagumi. Cikin fargaba ta ce.
"Wai menene? Ko babu kasuwar balangun ne yau naga ko rana bata ida faduwa ba ka taho."
  Ya numfasa.
"Haruna(yaronsa) na bari a can na taho, jikin nawa duk babu dadi, haka kawai na tsinci kaina da jin wani sanyin jiki, fatana Allah Yasa alheri ne."
  Saude ta yi tsuru da idanu, yau kuma meke shirin faruwa? 
  Shigowar Mariya a guje ne ya katse tunanin kowannensu.
  "Umma! Umma!!"
Suka maida hankali gareta jin yanda ta ke ihun kira, babu wanda gabansa bai fad'i ba acikinsu. Malam Balarabe ne ya riko hannunta.
"Menene 'yar Baba?"
Tana haki tana nuna kofar waje da yatsa, bakinta a washe ta ke fadin.
"Wasu ne suka zo da katuwar mota suna..."
Kafin ta karasa magana suka tsinci sallama mutane, Yaha ce a gaba Hajiya Babba na biye da ita. 
  Saude ta zaro ido.
"Yaha?" Malam Balarabe ya mike yana mai amsa sallamarsu yana dubansu duban rashin sani don daidai da Yahar bai rike kamanninta ba.
Kafin kuma wani cikinsu ya kara cewa komai, Ummi itama ta sanyo kai da sallamarta wanda dakyar ta iya daurewa ta yi shi don a matukar tsorace take. 
   Ganinta yasa Malam Balarabe zaro ido ya nunota da yatsa.
"Ha...ha..si..daman ba ki mutu ba?!"
Kawai sai ya zube anan, ihu da salatin Ummi ne ya ankarar da Saude cewa lallai yau ABINDA AKE GUDU ya afku! 
   Ta kasa koda kwakkwarar motsi tana ganin Ummi ta yi kanshi tana jijjigawa. 
Faruk da suke waje, yana jin ihun Ummi baisan sadda ya sanya kai cikin gidan ba su Babban Yaya na biye da shi.
Hajiya Babba ta hangi buta, da sauri ta nufi butar ta dauko, Faruk ne cikin zafin nama ya kar6a ya soma yayyafa mishi, aka ci sa'a ya farfado. Saude jikinta sai kadawa ya ke yi tamkar mazari, ana haka itama Habiba ta shigo don kuwa ta ji hayaniya saidai bata gask'ata ba hakan yasa ta zo ganewa idanunta. Wata budurwa ta gani sanye da tsadaddun kaya durkushe tana kuka sai mazan dake tsaye a wajen.
Malam Balarabe aka kamashi ya zauna gami da jingina da bango.
"Sannu Baba."
Cewar su Babban Yaya, bai amsa ba sai binsu da ya ke yi da kallo kafin ya sauke idanunsa akan Ummi, da sauri ya runtse ido ya soma salati. Duk sai ya basu mamaki, babu kamar Ummi, mamakinta bai wuce na ganin wai mahaifinta ke tsoranta ba.
"Wai Malam lafiya?"
Saude ta yi maganar cikin rawar murya tana mai fatan ace Malam Balarabe ya koresu daga gidan matsayin ya ga fatalwa matarsa.
Ya nuna Ummi.
"Wai Hasiya ce dai ta dawo? Daman ba ta mutu ba?"
Tambayar da ya yi ne yasa hankalin su ya dan kwanta banda na Saude da Habiba wacce jin hakan yasa ta sulale ta koma gidanta, bata yi wata-wata ba ta dauki mayafi sai gidan Bokanya har jikinta na rawa tsabar firgici.
Acan kuwa, Yaha ta amsawa Malam.
"Aa Malam, wannan Hasiyar Ummi ce diyarka diyar marigayiya."
Ya kurawa Ummi idanu kamar yau ya soma ganinta, Ummi! Ummi!! Shi kuwa ina ta shiga kwana biyu ba ya ganinta?
  ((Ku yi hakuri, rashin chaji ke sa ku ji ni shiruuu..))
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  92
        
  Saude tana shiga gidan Bokanya ta yi turus sakamakom ganin Habiba da ta yi zaune itama tana faman kuka. Habiba na ganin Saude ta mike da sauri ta nufi wajenta. 
  "Yanzu Mai Bori ta ke gayamin kin tafe daman, munyi sake Habiba, lamura sun yi 6acin da gyarasu sai Bokanya. (Wa'iyazubillah)"
Saude ta wuce zuwa gaban Bokanya ta zauna. Bokanya tana dubansu tun soma maganganinsu tana dariyar k'eta. Kafin Saude ta ce komai ta rigata.
  "An sakeki Saude, Balarabe ya miki saki biyu ko? Hahaha."
Ta kyalkyale da dariya, Habiba ta razana da jin wannan, ta zaro ido ta dubi Saude ta koma duban Bokanya.
"Kunyi kuskure babba! Kun kasa kiyaye dokokina, yanzu ku ka soma fuskantar kalubalen rayuwa! Babu wani abu da zan iya, lokacin afkuwar ABINDA AKE GUDU ya iso!"
  "Karya ki ke wallahi! Ke din banza, idan ba ki yi mana aikin ba kin dauka babu dubunki?" Cewar Saude kenan wacce sam ba cikin and hayyacinta ta ke ba. Ita kuwa Bokanya dariyar keta kawai ta ke yi babu kakkautawa.
  "Allah Ya isa tsakaninmu da ke, ashe bokancin naki ya k'are tunda ki ka kasa gyara abinda ki ka san zai 6aci."
Cewar Habiba itama cikin kuka. Sai lokacin Bokanya ta dan tsagaita dariyarta tana mai duban Habiba.
"Kun yi kuskuren zagina! Sakamakonku zai biyo baya! Ke Habiba! Ke ki ka kashe Hasiya! Tare da taimakon Saude! Diyarki tana can ta fad'a harkar madigo! Aurenta zai mutu! Sai na karya duk aikin da na yi mata! Sai kun koma abin tausayi. Asirinku sai ya tonu! Ku tashi ku bar nan azzalumai!!"
  Ta karashe fuska a daure, suka mike don ko damar bata hakuri basu samu ba, Bokanya ta karanto musu laifinsu wanda duk a zatonsu asirinsu ya rufu ruf babu ta inda zai fito don kuwa su biyun cewarsu sun aminta da juna. 
  Suna tafe ga duhun Magriba, Saude fadi ta ke.
"Allah Ya isa tsakanina da ke, duk kece ki ka soma kaini wajen bokanyar nan yau ga shi nan abinda ya afku. Ga shi yau aurena ya mutu."
Habiba da ke kuka da tunanin tashin hankalin da ke gabanta na mutuwar auren diyarta ta dubeta.
"Au, haka ma za ki ce?  Kin mance dadin da ki ka ji a baya ta sila ta shine yau da akayi miki ba dadi za ki zageni? Lallai DAN ADAM mai mance halacci, DAN ADAM butulu, ban ta6a kashe rai ba sai akan kishiyarki, shi ne tsabar son ki nunamin ke kina cikin masu mance halacci za ki ce na cutar da rayuwarki? Ai babu wacce aka cuta sama da ni."
  Wannan kalamin na Habiba ya tunzura Saude, nan suka hau cacar baki suna tafiya, wannan ta fad'a, wannan ma ta maida martani, karshe haka suka rabu baram-baram, Saude kai tsaye ta kama hanyar gidan kawunta wanda shi da banza duk daya ta daukesu, sai kuwa a yau din da ta ke neman agajinsu kan su rok'i mijinta akan ya maidata dakinta.
    Habiba hankalinta idan ya yi dubu to fa ya tashi, babu abinda yanzu ke damunta kamar batun diyarta Dija, yanzu idan auren ya mutu ta yi ya ya? Ta dauki waya da zummar kiranta saidai ko kusa batasan yanda ake sarrafa wayar ba, sau da yawa idan za ta yi kira saidai ta shiga makwafta budurwar gidan ta danna mata. Tana nan zaune duk tunaninta ya jagule, Malam Yahuza ya shigo gidan da sallamarsa saidai bata ko amsa ba.
"Habiba, lafiyarki kuwa ina sallama ba ki ko kalleni ba balle ki amsa?"
  Sai lokacin ta dubeshi gami da jan tsaki.
  "To menene kuma? Za ka cikani da hayaniya, mtsw."
Ta karashe gami da jan tsaki.
"Habiba ni ki ke yiwa tsaki kuma? Toh bazan dauki wannan rashin kunyar banzar ba, ki kiyaye!"
  Sakato ta yi tana duban mijinnata, yau Yahuza ne ya samu 'yancin d'aga murya sama da nata? Tabbas Bokanya dagaske ta soma karya dukkan ayyukan da ta yi musu, ta yi tsuru don tsoro ma ya bata, ya kammala komai ya dubeta.
"Ina abincina?"
A sanyaye ta amsa.
"Ai ba ka bada kudin cefane ba."
Ya yi kwafa kafin ya mike ya fice zuwa masallaci. Ta bishi da kallo kafin ta dora hannu a ka ta hau kuka.
"Oh ni Habiba wannan wace irin bak'ar rana ce gareni?"
Ta fad'a a fili babu mai amsa mata.
                 
  Ummi farincikinta ba ya misaltuwa a wannan rana, ta yi sallar Magriba anan tsakar gidan, saida aka yi sallar Isha'i sannan Malam Balarabe ya shigo rike da leda, da sauri ta mike ta kar6a suna duban juna da murmushi saman fuskar kowannensu. Kauna ta da da mahaifi shi ke yawo a jinin jikinsu. Tarr ya ke ganin diyartasa sakamakon wutar lantarki da suke da shi don a baya sosai suna samun wuta a kauyen, sai ayi kwana biyu ba'a dauke ba, koda kuwa an dauke, to fa babu jimawa za'a maido musu, yanzun kuwa da aka shiga yanayi an dan rage samu kamar da.
    "Sannu da zuwa Babana." Ta karashe cikin jin wani irin sanyin dadi a zuciyarta, yau ga ta ga mahaifinta kamar yanda ta ke yawan mafarkin ta gani har ya damu da ita ya sakarmata fuska. Kwalla ta cika idanunta sa'ilin da ta ke kokarin ajiye ledar ya dakatar da ita da fadin.
"Sannu 'yar Baba, dauko faranti a ciki nama ne da gurasa ku ci."
Ta bi umarninsa, ta kawo ta juye, ta dubeshi.
"Baba mu ci."
Yana murmushi lokacin da ya ke share hawayen da suka zubomishi ya soma ci shima. Mariya itama ci ta ke sosai don daman da yunwarta.
   Bayan sun kammala ta debomusu ruwan randa mai sanyi suka sha kafin su yi zaman hira. Malam Balarabe ya dubi Ummi.
"Kamanninki da mahaifiyarki har ya 6aci, tamkar an tsaga kara an karya, hatta sanyin muryarta."
Ya danyi shiru kafin ya numfasa.
"Allah Ya jik'anta."
"Amin." Ummi ta amsa jikinta a sanyaye tana dubansa kafin ta ce.
"Baba kana da hoton Ummana?"
Ya gyada kai yana murmushi.
"Bazan rasa ba saidai yanzu nasan yana cikin kaya, sai zuwa gobe zan dubo miki. Bani labarin zamanki a hannun bayin Allahn nan."
Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta soma labartamishi tun farkon zuwanta har kawowa yau da suka taho nemawa dansu aurenta.
   Malam Balarabe dake ta faman jinjina kai, wani abin ya yi murmushi ya ce"Allahu Akbar" wani abin kuwa ya yi hamdala idan ya ji. Bayan ya kammala ya dubeta.
"Babu abinda zanyi na biya mutanen nan da shi sai addu'a. Hakika sunyi abinda Allah baiyi ni zan miki shi ba. Babu abinda yafi faranta raina kamar sanyaki a makaranta da suka yi basu barki kin zauna da jahilci ba.  Haka kuma rayuwarki bata lalace ba, har kuma suka tako daga Abuja zuwa kauyenmu don kawai su nemawa dansu aurenki, tsakanina da su sai addua, Allah Yasa aljanna ce makomarsu, in sha Allahu ba ki da miji sama da Umar. Zuwa yanzu na dakatar da maganar don nafison ki soma sanin dangina da na mahaifiyarki, ayi aurenki kina cikin dangi. Itama Amina Allah Ya yi mata albarka, Ya bata mijin da zai rik'eta rik'on Amana."
"Amin Baba." Ummi ta amsa da murmushi mayalwaci saman fuskarta, ai ko don zagin da su Ihsan ke mata, zata so ta hadu da dangin iyayenta, ta ga gatanta. Sai kuma ta dubi mahaifinnata, lokacin Mariya ta soma bacci saman tabarmar.
"Baba inason jin tarihinku da Ummana, ku din 'yan ina ne?"
Malam Balarabe ya murmusa kafin ya ja baya ya jingina da bango ya soma magana.
"Yanzu za ki ji takaitaccen tarihinmu da Ummanki, sauran idan munje kya ganewa idanunki."
Suka yi murmushi tare kafin ya cigaba da magana....!




 
 
  
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

93
  ((Wannan shafin naku ne yan uwa sis Aisha Samarou & Maman Adil))
 
"Da ni da mahaifiyarki duk yan gari daya ne, wato Gombe. Saidai ita din  ta yi rayuwa ne a kauyen Jar Kwami dake Gombe. Da mahaifinta, Malam Manu(Usman)

Please Login or Register in order to submit comment