Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta shirya cikin riga fara da siket ruwan toka, sai farin hijabi da safa fara, ta saka bak'in takalmi. Shima Adnan irin kayan Ihsan ne saidai wando ne nashi dogo, da farar hula (Face cap) wanda aka buga tambarin makarantar daga gaba. Shima bak'in takalmin ne sai farar safa, wanda hakan ya kasance tsarin makarantar.
   Ba karamin kyau da burge Ummi sukayi ba, gaba d'aya sai ta shagaltu a kallonsu tana murmushin inama itace ta samu wannan gatan na zuwa makaranta. Tana son karatu sosai saidai bata da mai mata gatan nan. 
  Adnan na kokarin zura (belt) na wando ya ankara da ita. Ya dubeta batare da ya cigaba da abinda yakeyi ba, bai kai ga magana ba, tayi sauri ta durkusa ta gaisheshi, ya amsa sannan ta juya ga Ihsan wacce take zura littafi cikin jakarta ta makaranta, itama gaisheta tayi. Ihsan ta amsa tana hura hanci cike da jin ita d'in ta isa ta kai. Adnan ya girgiza kai ya ja karamin tsaki. "Na gayamaki ki daina gaisheta ko? Kodayake don kanki zaki bari ai."
   Ihsan ta turo baki. "Nidai wallahi broda kana ban kunya a gaban 'yan aiki. Kaga banason irin haka, wannan jawomin raini ne fa."
  Harararta kawai yayi baice uffan ba. Ta dubi Amina. "Ki zubomin shayi."
  Amina ta juya bayan ta ajiye na Fahad a gabansa da biredi da bota. Can sai gata ta fito da kofuna biyu a hannunta. Ta ajiyewa Ihsan d'aya, sai Adnan wanda take yace bazai sha ba. Ta ajiyewa Fahad filas d'in abincinsa sannan ta ja Ummi suka fad'a d'akin da  Ihsan da Fahad ke kwana. Karamin daki ne sai gado mai hawa biyu na yara. Saman an saka zanin gado kalar ruwan hoda mai zanen (Barbie), na k'asan kuwa an saka bulun zanin gado mai zanen (spider-man). A gefe kuwa, kwabar kaya ne guda biyu, shima d'aya ruwan hoda da fari, dayan kuma bulu da fari. Sai kafet mai duka kaloli ukun da aka kawata tsakar dakin da shi, da kuma k'arami na takawa a daidai hanyar bandaki. Daga can kuwa, karamin madubi ne, sai kwaba da abu mafi yawa akansa, kayan kwalliyar Ihsan ne. Fanka ce kawai a d'akin, sai bada wadataccen iska take. Ba k'aramin burge Ummi dakin yayi ba. Ta saki baki tana kallo. 
   "Ummi ki dunga lura kina rike abubuwan da nakeyi fa, don kuwa gobe zai iya kasancewa ke d'aya zakiyi. Da zarar Hajiya Mama ta dawo zan tafi."
  A sanyaye Ummi tayi magana. "Yaushe zasu dawo?" 
  Tana murmushinta na sabo ta amsa. "Hausa nayi miki, ni kaina bansan sadda zasu dawo ba amma na tabbatar ba zata kaisu da nisa ba tunda an koma makaranta, yara zasu je. Nufina yau idan ina nan gobe bana nan, kece zakiyi."
  Ta jinjina kai. Tare sukayi aikin, har inda ake daukar sabon zanin gado idan na kai sunyi datti saida Amina ta nunamata. Suka fito, tuni yan makarantar sun tafi lokacin takwas ma ta wuce, saidai sam Hajiya bata lek'o ba. Saida suka shiga dakin Adnan nan ma suka gyarashi tas, shima madaidaicin daki ne, da katifa babba wacce bata da bukatar katakon gado. Komai na dakin adon fari da bulu ne, babu wani tarkace a dakin sosai. Amina ta barta da gyaran gado don taga yanda zatayi, sai kuma ta bata mamaki don tayi kokari ba laifi. Ta dan gyaggyara inda baiyi ba sannan Ummi ta share dakin, anan kam ko Amina ba zata nunamata iyawa ba. Bayan sun fito, shayin suka zuba suka sha da sauran biredin sannan suka maida komai kicin suka koma dakinsu. Suna daga kwance Amina ta soma magana.
  "Zanso kafin na fad'amaki halayen mutanen da zakiyi zama tare dasu, na soma gayamaki tsarin gidansu don ya dace kisan da wadanda zaki zauna."
  Ummi ta muskuta tana dubanta gaba daya ta tattara hankali da nutsuwarta ga Aminan. Ganin haka Amina ta soma.
DAN ADAM
@Rufaida Omar
(03)

"Assalamu Alaikum." Cewar Yaha alokacin da ta murd'a k'ofar falon ta sanya k'afa. Wata dattijuwa wacce ke zaune, wata budurwa mai kimanin shekaru sha shida. Tana zaune a k'asan lallausan kafet tana daddanna mata k'afa. Ta nutsu sosai, kamar kace arr! Ta arce.
Ummi dai kallonsu take, daga yanayin yanda ta ga Hajiyar na dubanta, ta sha jinin jikinta, da alama dai matar ba ta da mutunci don kuwa fuskarnan nata babu ko alamun fara'a.
"Ranki ya dad'e baya goya marayu, barkanki da hutawa."
Hajiya tayi wani murmushi, da alama ta ji dadin wannan kirari na Yaha. Ummi dai kallon ikon Allah take, yanayin shigarta da komai ma, sun isa shaidar tana cikin rayuwar daula. Wani kallo da Yaha ta watsa mata ne ya sanya ta ba shiri russunawa sosai gami da rankwafar da kanta ta gaisheta. Hajiyar bata ko amsa ba, saidai ta k'ura mata ido tana k'are mata kallo. Can kuma ta yamutse fuska ta rausaya kai gami da maida dubanta ga Yaha.
"Wannan ce?"
Yaha ta washe baki tana jinjina kai.
"Kwarai kuwa ranki ya dad'e uwar gida ran gida, itace, sunanta Hasiya amma Ummi ake kiranta."
Ummi dai sai zazzare ido take kamar shege a rabon gado, Hajiya Madina tayi murmushi, ko babu komai takan ji dadin wannan kirari da Yaha ke mata.
"Tayi sosai, na tabbatar, zata iya dukkan ayyukan da na na bata. Ince dai bata da son jiki?"
Yaha har lokacin bakinta ya k'i rufuwa don ji take kamar ta shid'e don dad'i domin kuwa ta sha kawowa Hajiya Madina yara, basu yi mata ba.
Ta janye k'afafunta, gami da kallon budurwar batare da tace uffan ba, ta mik'e ta wuce don ko Hajiya batayi magana ba, ta karanceta, wato dai ta basu guri.
Bayan komawarta ciki ne, Hajiya Madina ta dubi Yaha.
"Yahanasu, ina fatan kin shaida mata cewar banason wasa, ba kuma na son son jiki. Dukkan wasu ayyuka da na sanyata, inaso ta kammala su alokacin da ya kamata. Ba kuma na son k'azanta, ta kula sosai don kuwa naga yanayinta, da alama k'azamar ce."
Ummi ta sunkuyar da kai tana sosa gashin kanta wanda amosani ya bi ya takura mata, idan ma ance da kwarkwata lallai babu musu don bata da gatan da Saude zata wanke mata kai.
"Kiyi hakuri, na tabbatar ba zaki samu wannan matsalar ba. Sau daya aka gwada mata yanda zata gyara jikinta, na tabbatar babu wata matsala da zata biyo baya."
Hajiya Madina ta jinjina kai alokaci guda ta yamutse.
"Yauwa, don kinsan banason abinda wadancan shirmammun zasu samu damar zagina. Ko kusa banason wani mishkila ya fito daga d'akina."
Dariya Yaha tayi, ta gane Hajiya Madina tana nufin kishiyoyinta, Hajiya Rakiya da Hajiya Munira.
"Ai kin wuce nan Hajiyata, baya goya marayu. Kar kiji komai, yarinya ce mai kaifin basira. Zata bi dukkan umarninki batare da kin 6ata rai ba.
Kwarai, ta ji dadin kalaman Yaha. Daga nan ta mike da nufin zuwa gabatar da sallar la'asar, bayan ta umarci budurwar nan da ta ambata da Amina, da ta nunawa Ummi wajen kwanansu.
Amina a gaggauce ta bi umarnin Hajiya. Suka wuce tarr har Yaha wacce zata d'auro alwalar sallah itama. Ummi ta dubi d'akin, katifa d'aya ce sai filo, a gefe kuma jakar kaya ne. Sai kofa daya wacce ta ga Yaha ta shiga ciki, wannan ya tabbatarwa Ummi, bandaki ne. An malale dakin da ledar tsakar daki. Fentin dakin mai wani kyalkyali ne, fari da ruwan hoda, saidai babu komai na more rayuwa ciki.
Acan kusa da jakar kayanta, ta ajiyewa Ummi nata da murmushi saman fuskarta ta dubi Ummi, haka kawai ta tsinci kanta da murna sosai, ko babu komai ta samu abokiyar hira.
"Nan zaki dunga kwana."
Ummi ta mayarmata da martanin murmushin, saidai har lokacin bata saki jiki ba don kuwa ko k'arar k'ofa ta ji sai ta firgita. Ta riga da ta saba da hakan.
Yaba ta fito ta shimfida dardumar dakin ta tayar da sallah. Itama Ummi ta shiga, saidai tayi turus don kuwa bata saba da bandakin yan gayu har haka ba.
"Bari na nuna maki yanda zakiyi."
Cewar Amina daga bayanta, wannan yasa Ummi matsawa, ta shigo.
Nan ta gwada mata komai, Ummi tayi godiya cikin muryarta sassanya sannan ta shiga ta d'an kara k'ofar don ta tsorata, bata so ta rufe ta kasa bud'e kanta.
Bayan tayi alwala, irin yanda ta saba ganin mutane nayi don kuwa ko alfarmar zuwa makarantar islamiyya, Ummi bata samu ba. Tayi yanda ta iya sannan ta fito ta tayar da sallar. Tasan ana yin sallah raka'a hud'u a lokacin nan hakan yasa ta soma babu wani karatun kirki don babu abinda ta iya. Ta idar ta zauna tana motsa baki sannan ta yi jugum tana kalle-kalle.
Bayan Yaha ta kammala suka fita, Ramma ta basu abinci, nan suka ci sannan Hajiya ta sallami Yaha ta tafi da abin arziki
      DAN ADAM
    
      06

Maigidan, sunansa Alhaji Muhammad Modibbo. Shi d'an asalin garin Adamawa ne, bafulatani ne. Hajiya Madina 'yar uwarsa ce, saidai ita mahaifinta anan Kano ya rayu, anan ya tara zuri"arsa. Soyayya ta kullu tsakaninsu har ta kaisu ga aure lokacin shi Alhaji Muhammaf ya dawo Kano da karatu ya kuma kama aiki anan.  Yana da mata biyu bayan ita, Hajiya Binta itace wacce kika gani rannan, sannan amaryarsa Hajiya Lubna, ita 'yar Maiduguri ce, yanzun ma da baki ganta ba, taje biki can Maiduguri da yaranta su hud'u gaba d'aya. 
   Hajiya Madina tana da yara takwas kamar yanda na fadamaki, ita kuwa Hajiya Binta yaranta shida. Iklima itace babbar budurwar 'yarta sannan Hanif, Sadiya, Nafisa, Usman da Jabir.

  Ita kuwa Hajiya Lubna, yaranta biyun farko 'yan biyu ne mace da namiji. Hassan da Hussaina, sai Adam da Hajara.
    Bar ganin gidannan kamar ba shi da girma Ummi, sai kin shiga can 6angaren zaki k'ara tabbatar da girmansa. Sashe hud'u ne har na Alhajin. 
   Saidai duk haduwar sashen matan bai kai na maigidan ba, da girma da komai. 
   Hajiya Madina duk ta fisu fada a wajensa, ko don tana ganin ita din 'yar uwarsa ce kuma tana da daurin gindi wajen mahaifiyarsa Gwaggo ne? Bani dai da masaniya. Amma tabbas Gwaggo bataso ko kusa Hajiya ta kai k'ararsa wai ya 6ata ranta, yanzun nan zata bud'emishi wuta. Shiyasa daga Hajiya Binta har Hajiya Lubna, basu kaunar zuwan Gwaggo Kano, kawai saboda bambancin da take nunawa tsakaninsu da Hajiya Madina. Hakanan tafi zuzuta kaunar 'ya'yan Hajiya Madina har yakai ma bata iya 6oyewa.
    Bada son ranta akayiwa Hajiya Madina kishiyoyi ba, saidai kawai don Hajiya Madina ta nunamata tafison kwanciyar hankalin mijinta akan tashin hankali da damuwarsa. 
  Gaskiya Ummi a wani 6angaren, Hajiya Madina tana da mutunci duk kuwa da cewar bata kama k'afar Hajiya Mama ba. Hajiya Mama ciki d'aya suka fito, saidai ita bata da raina 'yan aiki kuma yaranta sunsan girman ★DAN ADAM★ basu rainashi ko yaya ne. Toh yanda Hajiya Mama take, hakanan itama babbar yayarsu, Hajiya Fatima take. Su uku daman cif a wajen babansu, daga su bai kara haihuwar wasu ba kuma matarsa daya, Baba Ummahani.
  Ita a Abuja take zaune. Tana da yaranta hudu samari manya, sai yan mata biyu. Ta aurar da yaranta maxa biyu na farko, matan da ragowar mazan biyu sune dai basuyi aure ba. Mijinta tsohon soja ne kafin daga baya yayi ritaya. 
     Amina ta d'an tsagaita sannan ta d'ora tana duban Ummi wacce gaba daya kacokam ta maida hankali gareta tana sauraro.
  "Hajiya tana da saukin hali idan kika zama mai bin umarninta kan lokaci, sannan tafiso kafin tayi korafi akan bakiyi aikin da kika san kina yi ba toh ki kammala shi. Ko kusa bata son kazanta, hakanan bataso kice zaki wulakanta abinda ta haifa. Batason kuma shigen d'akunan abokan zamanta, idan kika kiyaye bakinki daga daukar magana ki kai wani dakin toh fa zaku d'asa da ita. Ba ruwanki da shishshigi a lamuranta matukar ba ita ta so ki tanka ba. Ki kiyaye kawo mata gulma, nan ma zaku 6ata da ita. Sannan ko wani abu marar dacewa kikaga ta yi, bataso ki tanka mata, nan kuwa zaku 6ata. Batason ta kamaki da cin amanarta. 
Yaranta suna da saukin hali Ummi, matukar kika kama kanki ba zasu rainaki ba. Ihsan ce ma mai matsalar, ita kuma kiyi kokarin fita harkarta. Idan dai ta sanyaki aiki kada ki k'i, kiyi hakuri kiyishi hakan saboda itace ma musabbabin da yan aiki basujin dadin zaman gidan. 
     A duniyar nan, kawai dai ki tsare abinda za'a ci mutuncinki ko yayane, kedai ki tsaya matsayinki baruwanki da cusa kai kinji ko?"
    Ummi ta danyi murmushi alokaci guda hawaye suka zubomata ta sharesu, wai yau itace da samun mai bata shawara a lamarin rayuwa? Itace ta samu wannan gatan har haka? Wani irin kaunar Amina ya k'aru a zuciyarta. 
  Amina da mamaki ta mike zaune.
"Ummi kukan kuma na menene?"
Ummi ta girgiza kai.
"Bakomai."
Amina ta ji wani tausayi ya dabaibayeta. Tasan akwai wata matsala a rayuwar Ummi, tafi kuma tunanin bata da iyaye. Ta numfasa, batason ta matsa mata da tambaya, ta tabbatar wataran don kanta zata gayamata tarihinta. 
   "Komai yayi zafi maganinsa Allah Ummi. Ki bar damun kanki da lamuran rayuwa har haka kinji ko? Ki rik'i addu'a da karatun Alkur'ani da sallar dare. In sha Allah komai zakiga ya wuce."
   Ummi da fuskar tausayi ta dubeta.
"Nifa bansan komai na Addini ba wallahi. Kawai dai ina yin sallah idan naga lokaci yayi mutane sunayi."
  Mamaki karara ya bayyana saman fuskar Amina, batasan ya akayi ta jefomata tambaya ba.
"Wai Ummi, iyayenki basu raye ne? Shekarunki nawa yanzu?"
  Ummi tayi k'as da kanta ta soma hawaye. 
"Mahaifiyata ta rasu tun ina jaririya, babana yana raye. A hannun matarsa na taso."
  Kwallah ta cika idanun Amina, ta gano bakin zaren. 
  "Idan ba damuwa ki sanarmin tarihinki mana."
  Tiryan-tiryan ta sanarmata da irin rayuwar kuncin da ta rayu ciki. Cikin muryar kuka tace.
  "Kalmar da ta kasa ficemin a rai bai wuce da babana yace wai ko birnin sin ne na tafi ba shi ba damuwarsa bace. Babana baya sona yanda yakeson kanwata Mariya."
  Kuka sosai takeyi, itama Amina tana tayata. Wani kaunar Ummi ya k'aru a ranta, ji takeyi tamkar kanwarta ce ta jini. Dakyar Amina ta rarrasheta tayi shiru sannan ta dubeta da kulawa.
                
"Karki damu Ummi, ki cigaba da hakuri sa mik'awa Allah lamuranki. Komai kika gani, daga gareshi ne. Watarana zaki ga komai kamar ba'ayi ba, nan gaba zakiji dadi a rayuwa in sha Allah. Kada kiyi bakinciki da zuwanki gidan Hajiya, na tabbatar ko a kwana d'ayan nan da kikayi, kinga chanjin rayuwa ballantana kuma idan ya zamana kin shure satittika anan. Nasan dai duk wani wuya da zaki ci anan bazai kai rabin wanda  kika labartamin ba. Hajiya bata duka, bata zagi haka kawai, saidai idan ka ta6a jininta, zata budemiki wuta tayi fada sosai harma idan baki taki sa'a ba ta goranta miki. Duk kuma wani abu na rayuwa ki daukeshi mukaddari ne daga Allah, ba wanda zai tsallakewa kaddararsa kinji ko?"
  Cikin jin wani sanyi ta gyad'a kanta. 
"Toh Anti nagode."
Amina tayi murmushi. Baccin safen da basu samu komawa kenan ba, sukayi ta hira a karshe Amina ta mike ta shiga wanka. Bayan ta fito Ummi itama ta fad'a. 
  Ta kammala ta fito, Amina tuni ta shirya cikin doguwar riga ta yadi, daga gaban rigar, anyi adon duwatsu, ire-iren dai wanda take samu daga Hajiya Mama ko yaranta. Ummi ta dubeta, tayi mata kyau, zata soma duba jakar kayanta ta ji muryar Amina.
  "A'a Ummi, ga kaya ki saka."
Ta juyo don ganin ko ta ciro mata ne, saidai ta ga wasu da ba nata na asali ba, riga doguwa ce ta abaya. Ta dubi Amina ido a waje.
  "Lah, anya kayanki zasu yimin Anti?"
Amina ta murmusa.
"Wannan na jima bana sakashi, na kuma tabbatar ba zai k'i yi miki ba. Kedai gwada mugani. Idan kin kammala ki fito ki gaida Hajiya, nasan yanzu ta farka."
  Ummi ta amsa da toh, Amina ta fice. Rigar ta kar6eta kwarai tayi mata kyau kasancewarta farar yarinya. Ta dauki dankwalin ta d'aure gashinta wanda idan mutum yaga yanda yayi mata, zai iya cewa tayi d'aurin acuci. 
   Saida ta dauke shimfid'a ta d'an gyara d'akinnasu duk da ba daud'ar azo a gani don Amina akwai tsafta, sannan ta bi bayanta.
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

07

  A falon ta tarar da Hajiya Madina zaune cikin kwalliya tana karyawa, Amina bata nan, ta karasa ta durkusa ta gaisheta a ladabce. Hajiya Madina ta amsa fuskarta a sake, bai wuce ganin yanda Ummin tayi fes ba don ita ba mace ce mai son zama cikin k'azanta ba.
    Ummi ta zauna, idanunta akan talabijin, saida Hajiya ta kammala sannan ta umarceta  da d'auke kayan, ta d'aukesu ta kai kicin. Acan ta had'u da Ramma tana faman gyare-gyare. Ta gaisheta a mutunce, Ramma ta amsa har tana zolayarta wai har ruwan birni ya soma kar6arta ta chanja saidai k'ashin wuya. Ita dai murmushi tayi kawai. 
   Tana shirin fitowa sukayi kici6us da Amina, hannunta rik'e da tsintsiya da kwandon shara. 
  "Kinga yayi miki kyau ko? Nima na gyaro d'akin Hajiya ne, kije tana kiranki ma."
  Ai da sauri Ummi ta fita don amsa kiran. 
  Wannan karon a kan kujera ta sameta tana amsa waya. Zama tayi har ta kammala sannan tayi magana.
"Gani Hajiya." Ta dubeta a nutse sannan ta soma magana.
  "Yauwa Ummi, dafatan dai Amina ta nunamaki dukkan ayyukan da takeyi? Toh inaso ki zamo mai rike amana, muddin kika ci amanata, bazan kyaleki ba. Yanda zan rik'i amanarki da gaskiya a matsayinki na Amanar a hannuna, haka kema nakeso ki rike, ki kula da dukkan ayyukan da zaki dunga yi."  Ta k'ara karanto mata ayyukan harma da na gyaran sashenta ciki da falonta na biyu, banda wannan da suke ciki don duk cikin aikin Ramma ne. Ta k'ara jaddamata cewar batason k'azanta, hakanan ta kiyaye tsaftar suturunta, duk sadda zatayi wanki, ta tambayi omo zata samu. A dai maganganun Hajiya, Ummi ta fahimci cewa dagaske batason k'azanta kuma tana da kyankyami. 
   Ta rausaya kai.
"In sha Allahu Hajiya zan zama mai kula da dukkan abinda kukace, nagode Allah Ya k'ara girma da arziki."
Har a ranta ta ji dad'in maganganun Ummi.
  "Shikenan kina iya tafiya."
                       ☆☆☆
   Tun daga wannan ranar, Ummi ta kama aikinta sosai, Amina na taimakonta. Har ya kasance wani sa'in kafin Amina ta tashi, ta rigata tashi. Tana jin dad'in zama da Amina saboda shawarwarin da take bata, har karatu tana koyamata. Duk da cewar Amina na cin wuya don Ummi ko bak'i bata iya ba. Duk sai ta bata tausayi, haka take lalla6awa ta biyamata, amma ta tabbatar muddin tana wajen Hajiya Madina, bazata ta6a bari ta zauna mata da jahilci ba, duk wadanda suka ta6a zama sukayi aiki awajenta, ba wacce bata sanya a islamiyya ba, boko ne dai ba lallai ka samu ba. 
     Saida Ummi tayi sati da zuwa, sannan Amina ta soma shirin tafiya don Hajiya Mama sun dawo. Gaba daya ta ji babu dadi, tana zaune gefe tana duban yanda take ninke kayanta tana sanyawa ciki jaka. Amina ta ankara da duban da takeyi mata, itama sai taji batason rabuwa da ita.
  "Haba Ummi, menene abin damuwa har haka alhalin muna gari d'aya? Karki damu, na tabbata zamu dunga ganin juna. Kedai ki cigaba da hakuri da zama da su tsakaninki da Allah."
   Ummi ta gyad'a kai.
"Toh Anti." Sai yamma suka tafi har Hajiya da su Adnan, gidan ya rage Ummi kad'ai da Ramma. Bayan ta kammala ayyukanta ta fito farfajiyar gidan tayi zamanta. Bata kai mintuna biyar a zaune, budurwar da bazata ta6a mance fuskarta ba wacce suka samu sa6ani da Adnan a farkon ganinta da su, ta fito daga sashensu tare da k'awayenta har su biyu suna dariya. 
   Hararar da ta sakarmata ne yasa ta dauke kanta babu shiri ta saddar a k'asa, ta gabanta sukazo wucewa, ai kuwa ta sanya takalminta mai tsini ta take yatsun k'afarta har saida tayi k'ara. Ta juyo ta rankwasheta.
"Munafuka, sharri zakiyimin kina gidan ubana kina cin arziki? Shegiya kawai."
  K'awayen dariya kawai sukayi, d'aya tana fad'in "Kai Iklima baki da kirki."
Iklima ta ta6e baki.
  "Na kaiku?"
Suka fice Ummi ta mike da sauri tabar wajen, saida ta tsaya a lungun ta share kwallah sannan ta k'arasa ciki. Ta zauna a kicin tana kallon yanda Ramma ke faman had'a miya, tana dan jan Ummin da hira har ta share batun Iklima ta saki jikinta.
                      ☆☆☆
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

08

Bayan tafiyar Amina, Ummi dole ta sabarwa kanta hira da Ramma, don Ramma mace ce mai abin dariya. Ayyuka ko kusa basu bata wuya sosai don a ganinta ta saba da fin haka acan gidansu. Sau da yawa takan tuna Mahaifinta, tana tunanin ko wane hali yake ciki yanzu, saidai daga zuciyarta ta tunano mata irin tsana da tsangwanar da take sha a wajen shi kansa, sai ta ji tunanin ya kau.
A d'an zaman da sukayi da Hajiya Madina ta fahimci Ummi lallai bata da wani ilimi da addini, ta lura ko sallolinta akwai gyara ciki, wannan dalilin ne yasa ta sanya Ramma kaita makarantar da yaranta(ita Rammar) ke zuwa, karfe biyu suke zuwa su taso k'arfe biyar na yamma. Babu ruwanta da shiga sashen kowace matar gidan don sosai ta dauki gargadin Hajiya Madina, hakanan tana rike da nasihar Antinta.
Alokacin Hajiya Lubna amaryar gidan sun dawo daga Maiduguri, ta lura yaranta suna da kirki basu da hali irin na yaran Hajiya Binta. Saidai uwarsu ce sai a hankali, mace ce mai shan k'amshi, saika gaisheta sai ta ga dama take amsawa.
Maigidan ma bai rufe sati biyu ba ya dawo. Ranar da ya kasance Hajiya Madina ce da aiki, sun ci aiki sosai, har da Hajiya Madinar. Ummi banda wanke wannan mik'o wancan babu abinda takeyi. Abinci kusan kala uku ta ga anyi ciki harda suyar kaza bayan an tafasa an tura shinkafa da kayan hadi a k'asanta an toshe bakin da dankali babba guda d'aya. Sai lemun zo6o da taga sun had'a sai kamshin abarba yakeyi. Aka kammala aka zuzzuba, suka ajiye a saman tebur. Ummi da Ramma suka tattara kicin din, can bayan magriba, lokacin Ramma ta tafi, sai ga Hajiya Madina ta fito daga dakinta ta ci ado cikin wani (yellow lace) wanda ya sha adon duwatsu, tayi kyai sai k'amshi kawai ke tashi a jikinta.
Ummi na rak'u6e a can gefen kofar kicin tana kallon wani fim na yak'i da su Adnan suka nutsu suna kallo.
"Wow! Wallahi Mom kinyi kyau."
Cewar Ihsan tana mikewa tsaye, daga ita sai riga iyaka gwuiwa da riga tshirt kanta hula ce ta sanya. Ta isa ga Mamin tana mai sanya hannu ta k'ara gyara mata zaman d'aurin. Murmushi kawai Hajiya Madina tayi.
"Naji, taho ki kaimin kayannan sashen Abbanku."
Ihsan tayi dariya.
Tare suke fice ta dauki wasu Ihsan ta dauki sauran. Ummi ta bi Hajiya Madina da kallo cike da sha'awa don kwalliyar ta burgeta. Idan kana da kudi babu abinda ba zakayi ba.
Har ta gaji da kallon, ta koma daki ta hau duba karatunta, a karshe da ta gaji, kwanciya tayi abinta wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita don bata ta6a aikatuwa irin na yau ba saboda girkin dawowar Alhaji da ta taimaka da shi.
Bayan kwanaki biyu da dawowar Alhajin, ranar juma'a bayan ta je ta gaida Hajiya. Hajiya ta dubeta a nutse. Doguwar bakar abaya ce jikinta na wajen Amina.
"Wai ke baki da kaya ne sai wadannan guda ukun? Yau idan kin saka doguwar riga bak'a, gobe sai jan atamfa kodadde, jibi ma haka? Bakizo da kaya bane ba?"
Ummi ta sunkuyar da kai gaba

Please Login or Register in order to submit comment