Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita bace? Kina jin mijinki na kira ki ka yi shiru ko?" Ya karashe a shagwa6ance, ai daman tasan ko wata macen ba fa zata nunawa Faruk shagwa6a ba, don ko ita ba zata iya yanda ya ke yi ba.
  "Um." Ta fada kanta na k'asa tana wasa da kasan t-shirt din dake jikinta na bacci.
  "Kin zama matata yau, shikenan na girma, haka Hajiya ta ce."
Har lokacin murmushin ne dai ta yi.
"Gobe za ki zo gareni Hasiya, ina fatan kin shirya tarbata?"
Ta zaro ido a tsorace.
"Kamar ya?"
"Au ba ki sani ba? Shikenan sai kinzo din."
Ta tsorata, ta tunano maganganun su Anti Halima, ya zama dole ta yi takatsantsan don kuwa dagaske ba fa za ta bari ajinnata ya zube ba.
   Ya cigaba da janta da hira, hirar da ba zata iya dauka ba, ganin dai dagaske ba zata bude baki ta ce wani abin ba yasa shi yi mata sallamar dole ba don yaso ba. Daga nan suka kwanta kowanne zuciyarsa cike da begen dan uwansa....!
  Washegari...!!!
  
   DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  102
Bayan Ummi ta kammala karyawa, ko mikewa daga wajen ba ta yi ba, Dada ta mik'omata wani abu a kofi, ta dubi kofin, tasan daman tun zuwanta tana bata nonon saniya tana sha, saidai wannan karon wani abu ta gani cikinsa mai kama da lalle, ta dago kai tana dan yamutse fuska ta dubeta.
"Menene wannan Dada?"
"Kar6i ki shanye sai na gayamaki." Ba musu ta kar6a ta shanye tas gami da saurin korawa da ruwa don dacin bakinta ya kau. Murmushi Dada ta yi sannan ta mik'amata wani kullin itatuwa a farar leda. Ummi ta kar6a tana dubanta.
"Maganin sanyi ne, da zarar kin dawo kafin biki, za ki dunga sha kina tsarki da shi, mahadinshi jar kanwa, wannan da ki ke gani ba'a wasa da shi, sakacin iyayenku kenan, sai a yita dabkawa mata kayan gyara amma ba a basu maganin sanyi. Sai ki ga bayan aure anzo anata faman zaryar zuwa asibiti."
    Ita dai Ummi a kunyace ta ajiye ledar a gefe, Dada ta dauka tana cigaba da fadin.
"Ki dage wajen kula da jikinki, ko yanzu ai ke kanki kin ji chanji ba kamar yanda ki ka zo garinnan ba."
Ummi ta yi shiru, kwarai kuwa da gaskiyar Dada, don kuwa tun zuwanta kullum da abinda za ta bata ta sha, daga ta ce maganin basir sai kuwa na ciwon jiki. Ita dai hakanan ta ke sha batare da tasan wani abu na maganin ba. 
    Misalin bakwai na safe, Faruk ya yi mata text ya shaidamata tahowar direban tun biyar na Asuba, alokacin tana zaune Dada ta kira wata makwafciyarsu tana tsantsara mata kananun kitso, ga kunshi ana yi mata. Sun kwashi awanni uku suna yi kafin a kammala kitson, sannan ta wanke lallen, kowa ya ga kitson da kafarta sai ya tanka, wannan yasa ta rufe gashinta mai laushi da bak'i. Kafar kuwa ta makamishi safa. Ta yi wanka ta hade cikin wata doguwar rigar abaya mai ru6i biyu, bak'i da ruwan k'asa, wanda ya fiddo (shape) dinta, daga gefen hannuwan kuma sai aka yi shi mai fadi kamar buba. Ta yane kanta da mayafinsa.
  Wajen karfe goma sha biyu da mintuna, Babanta ya kirawota, ya yi mata nasiha sosai akan ta kula ta kuma bi mijinta sau da k'afa a karshe ya sallameta bayan ya sanarmata cewa an damk'awa Dada sadakinta zata bata, nauyi ya hana Ummi cewa komai ta tashi ta wuce.  
  Shigarta ciki babu jimawa ta ji yaran gidan na ihun mota ta zo. Gabanta ta ji ya soma bugu, haka kawai ta ji kamar za ta kara yin nesa da yan uwanta.  
  "To Hasiya, tashi ki yi sallah za ku kama hanya. Shiru ta yi domin yau da asuba jini yazo mata. Shirunta ya fahimtar da Dada, kawai sai wuce ta dauki jakar kayanta ta mikawa Aliyu d'a na biyu wajen Baffa Haruna wanda baifi sa'an Adnan ba. 
  Ummi ta soma sharar hawaye, tana nan zaune har zuwa lokacin da aka ce ta fito su wuce. Nan ta rike Dada tana hawaye, Dada dakyar ta iya daurewa ta cireta daga jikinta.
"To mene na kukan kuma? Kiyi hakuri kinji, ai ba'a rabu ba. Rike wannan, sadakinki ne." Ta girgiza kai.
"Ki yimin abinda ki ka ga ya dace."
Daga haka ta zira takalminta mai tudu ta janyo jakarta bak'a wacce da ita ta zo sannan ta fito Dada na rike da ita. 
  Haka dai da kuka Ummi ta rabu da gidannan, mahaifinta shi kansa saida ya ji kamar ya yi kukan, Baffa na gaba ita da Abida suna baya. 
   Wayar direban ta yi kara, nan ya ke sanarwa da mai kiran cewa sun taho, ya yi musu adduar isowa lafiya sannan sukayi sallama. Ya dubi Baffa yana dan dariya.
"Yalla6ai ne." Baffa ya yi murmushi kawai. Direban kuwa dan surutu, sai ya hadu da Baffa shima ba kanwar lasa ba, tun Ummi na jinsu har ta yi matashi da cinyar Abida bacci mai nauyi ya dauketa. 
  Basu suka isa Abuja ba sai karfe bakwai da wasu mintuna, shima don sun yi tsaye-tsaye ne yin sallah da sauransu. 
   Tunda aka shigi garin Abuja Ummi ta ji kamar ta ruga aguje ta koma Gombe, da wane ido zata kalli Hajiya? Wai shikenan fa itama ta zama suruka a gidan. 
  Bayan isarsu kofar gidan, ya yi hon, da sauri Maigadi ya budemusu suka shiga yana dagamusu hannu. Ta rike hannun Abida. Abida wacce ta suma a kallon gida, ta dubeta, ganin yanda duk ta firgice yasa ta fadin.
"Ki yi ta addua." Sai lokacin ta tuna ta shiga yi, a harabar gidan babu kowa har zuwa lokacin da suka fito sai lokacin kuma suka Gen. Ahmad ya shigo dawowarsa kenan daga masallaci, a bayansa kuwa Haidar Danzaki ne sai ko Faruk Danzaki. 
  Ummi sai sunne kanta ta ke yi, Baffa ya karasa ya mikawa Daddy hannu suka yi musabaha, yana tambayar yanda suka iso. Su Ummi suka russuna suka gaishesu, sannan suka shiga ciki. Faruk ya tsunduma a kallonta baya ko kifta idanu, saida Haidar ya dan mintsileshi a kafada sannan ya dafa wajen yana 'yar kara kadan. Dariya suka yi.
"Control yourself mana."
Murmushi kawai ya yi kafin ya russuna yana gaida Baffa, sannan sukayi ciki.
  Da Binta Ummi ta soma karo, suka rungume juna suna murna, harda hawayenta don Ummi kam akwai arhar kuka. 
   Binta ta dubeta.
"Kinga yanda ki ka koma kuwa? Ranki ya dade."
Dariya sukayi, lokacin da ta share hawayenta. Saukowar Hajiya daga sama ne yasa ta sunkuyar da kai a kunyace. Hajiya wacce ta kasa 6oye farincikinta ta karaso tana duban Abida.
"Sannunku da zuwa, diyata kunya ta shiga tsakaninmu kuma?"
Ta karashe tana mai rikota, dariya Abida da Binta sukayi. 
  Ta ja su zuwa sama, dakin Ummi suka sauka, saida sukayi wanka suka chanja kaya sannan Abida dake zaune saman darduma ta idar da sallah ta dubeta.
"Kai Ummi ki godewa Allah, na tayaki murna wallahi. Irin wannan karramakin da su ke yi? Ga uwa uba kuma suna da arziki? Kinyi sa'a sosai, sai naga ma haduwar gidan ta zarce yanda nake kissimawa."
   Murmushi kawai Ummi ke yi lokacin da ta ke kokarin jona matacciyar wayarta a chaji. Tana sanye da doguwar riga(cotton) wacce da kadan ta wuce gwuiwa tana da botila a gaban rigar mai dogon hannu sai ta dora zani akai. Kanta rufe da hula, aka kwankwasa kofar da sallama, suka amsa sannan Binta ta shigo. Suka kara gaisawa da Abida kafin ta fadi sakon Hajiya na su fito su ci abinci. 
Kamar ta tambayi Binta ina Ikram, sai kawai ta share.
   Ta yafa mayafi suka fita itama Abida da lullu6inta. 
    A saman katuwar ledar cin abinci aka jera komai, Hajiya Babba ta yi musu bismillah, Ummi da kanta ta zuzzubamusu a ranta ta ji sanyin rashin ganin Faruk awajen don kunya ta ke ji. 
   Bayan sun kammala ta tattara, Hajiya na fadin ta barshi saidai bata saurara ba, ta yi k'asa, Abida ke fadin.
"To Hajiya ai an zama daya." 
Saukarta yasa ta gwammace bata sauko din ba don kuwa Haidar ne da gogan zaune suna cin abinci. Dole ba yanda ta iya ta karasa saukowa, ta dan durkusa ta gaida Haidar, ya amsa fuska a sake.
"Sannu Amarya ya hanya?" Ta kasa dubansu, ciki-ciki ta amsa da Alhamdulillah. 
  Faruk ya bi le66anta da kallo don kuwa maganar bata fito sosai ba, murmushi ya yi sannan ya kauda kansa ya cigaba da cin abincinsa hankali kwance. 
   Ta mike ta karasa kicin, suka fito tare da Binta suka koma sama, nan suka iske Hajiya Babba da Abida suna ta hira, suka tattara suka koma kasa. 
  A kicin dinne Ummi ta samu danar tambayar Binta dake faman binta da kallo.
"Wai ina Ikram?"
Dariya Binta ta yi.
"Wallahi tana dawowa daga makaranta ta hada jaka ta gudu gidan Yaya Haidar, saidai fakewa ta yi da cewa zata taimakawa Intisar da ayyuka tunda cikinta ya soma tsufa, har shi Yaya Haidar din ke cewa ta barshi tunda ba tun yau ba yaso zuwannata ta k'i. Yanzu dai ta tafi can, nasan kuma karya ta ke yi wallahi saboda bakin cikin za ki zo matsayin matar Yalla6ai ne."
  Murmushi mai ciwo Ummi ta yi, tasan daman da wuya Ikram ta chanja.
   Saida ta lek'a ta ga sun bar falon sannan ta fito daga kicin ta haye sama. Babu kowa a falon wannan karon, Hajiya Babba ta yi wurin mijinta, Abida kuwa ta shiga daki, tana shirin murda kofa ta shige daki ta ji sallamar Faruk a bayanta. A rude ta juyo ta tabbatar shi dinne. Ya zubamata idanu yana sanye da riga da wando fari da ja.
   "Waalaikumussalam."
Ta amsa a hankali. 
Ya karaso daf da ita gami da sanya hannu ya dago ha6anta. 
"Ki sameni wajen pool...please."
Ya karashe a tausashe. Ta gyada kai cikin rawar jiki, ya saketa sannan ya juya ya fice, ta bishi da kallo. Bata koma ciki ba sai kawai ta bi bayansa jiki ba kwari. Haidar ya wuce, ta gama waige-waigenta kamar mara gaskiya kafin ta murda kofar ta shiga. Kofar na waje baya ganin na ciki saidai na ciki ya ga na waje. Yana zaune yana duban ruwan, shigowarta yasa shi dago kai yana dubanta. Ta yi kasa da kanta tana mai kara gyara zaman mayafinta. Tana kokarin zama a kujerar gefensa ya janyota ta fada saman kafafunsa ba da niyya ba. Ji ta yi gaba daya ta rude, ta shiga kokarin mikewa saidai ya tare dukkan hanya. Take kuka ya tahomata.
"Don Allah ka yi hakuri."
Ya lumshe ido yana shak'ar kamshin turarenta. Ganin haka ta fisge da karfi ta mike gami da ja baya. Jingina kansa ya yi jikin kujera yana dubanta fuska dauke da murmushi. 
  "Come to me please Ummi."
Ko gezau ba ta yi, come dai ai ko dan kauyen yau da gobe zai san me kalmar ke nufi.
"Ka yi hakuri ka kyaleni na tafi." 
Har lokacin bai motsa ba, saida ya kusan mintuna biyu yana dubanta sannan ya janyo kujera ya nunamata.
"Zo ki zauna."
Saida ta tabbatar dagaske ya ke sannan ta karasa ta zauna.
  "Kun iso lafiya?"
Kai ta gyada don har lokacin cike ta ke da fargaba.  
"Idan ba ki yi magana ba zan sanyaki yin ta dole fa."
  "Alhamdulillah." Ta fada da sauri har muryar na hardewa, abin yaso ba shi dariya. 
   "Na so mu yi hira saidai na lura kamar kina tare da gajiya ko? Tafi ki kwanta, saidai Antinmu na tafiya za ki had'a kayanki ki komo dakina."
Ta zaro ido tana dubansa, shi kuwa ya hade fuska kamar gaske. 
  Kawai sai ta sunkuyar da kanta ta soma hawaye. 
  Karamin tsaki ya ja ya durkusa gabanta.
"Why? Komai kuka awajenki ko Ummina?"
Ya fada a sanyaye, bata ankara ba ta ji ya soma lashe hawayen, ta soma girgiza kai kafin ta yi yunkurin tureshi tana fadin.
"Don Allah Yaya Faruk..."
Yasa hannu akan le66anta kafin ya girgiza mata kai.
"Karki hanani please. Idan bakyaso ki daina kuka. Bakisan suna da tsada wurina ba?"
Ya karashe da murmushi saman fuskarsa. Sannan ya mike yana dubanta.
"Tashi na rakaki."
Ta mike da sauri don daman abinda ta ke zuci-zucin ta ji kenan. 
   Saida suka kai kofa ya riko kugunta ya kai bakinsa daf da kunnenta.
"I LOVE YOU."
Ta lumshe ido, abinda tunda suke bai ta6a furtamata kenan ba, jikinta ya dauki rawa, zata murda kofar, ya kai hannunsa kan nata suka murda tare. Da sauri ta fice.
"Hey!" Ya fada yanda yasan za ta ji, ta tsaya cak batare da ta juyo ba. 
"Ba ki ban amsa ba."
Da sauri ta cigaba da tafiya har da gudu-gudunta. Ya bita da kallo yana murmushi sannan ya juya ya nufi samansa yana dan rera waka cike da nishadi.

      DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

103

Koda ta koma daki, kwance ta iske Abida saidai bata kai ga baccin ba. A kunyace da alamun rashin gaskiya. Abida bata ce mata uffan ba, itama ta cire mayafin jikinta sannan ta hau ta kwanta bayan ta yi alwala ta kashe musu fitila. 
   Ta lullu6e jikinta da bargo tana tunano abinda ya faru yanzun. Runtse ido ta yi ta bude, ganin abin tamkar mafarki ta ke, ta dan saka hannu ta mintsili kugunta, nan take ta yamutse fuska irin na jin zafi. Sai kuma ta rufe kanta da bargo tana murmushi, shakka babu dagaske ne, amma kuma abin ya bata tsoro. 
   Har Baffa da Abida suka yi kwana biyu bisa umarnin Gen. Ahmad don su  niyyarsu washegari su juya. Ummi wasan 6oyo ta ke yi da Faruk, don daga ta ji Magriba ta yi zata shige daki suyita hira da Abida. Hakanan idan ya bugo waya bata dagawa.  Washegari kuwa yana tafiya ofis, suma su Abida suka tattara suka wuce, har hawaye ta yi haka suka rabu zukatansu cike da kewa. Tare sukayi komai da Binta na abincin rana, har lokacin Ikram bata dawo ba. Acewar Binta, ba zata dauwama acan ba, koda ta yi an dai riga da anyi abinda bata so, Ummin ta zama matar yayanta. 
  Hajiya Babba zaune a falonta tare da Ummi da har lokacin bata saki jikinta ba, waya Hajiyar ke yi da Hajiya Mama. A karshe ta dubi Ummi dake zaune a kasa tana mai mik'amata wayar.
"Amsa ku gaisa da Sadiya."
Kunya ta cikata sanin kowacece Sadiyar, Hajiya Mama. Ta kar6a a kunya ta yi sallama. Daga can Hajiya Mama ta amsa mata murya a sake. 
Ummi ta gaisheta, ta amsa.
"Sannu surukarmu, kinga yanda Allah ke ikonSa ko?"
  Kanta kawai ta dukar tana murmushi.
"Um." Ta fad'a a kunyace. 
"Allah Yasa alheri, Ya baku zaman lafiya, sai a dage a nemi ilimi banda wasa kinji ko?"
Ta gyada kai."
"To Hajiya." Daga haka ta mik'awa Hajiya Babba wayar, itama sallamar suka yi.
  Bayan sallar isha'i tana kwance saman gadonta, ta juyawa kofa baya, ba bacci ta ke yi ba saidai ta yi shiru tana tunane-tunane, ga ruwan sama da ake kwarawa kamar da bakin kwarya, sam ba ta ji sadda ya murda kofar ba sai jin mutum ta yi a bayanta ya rungumota. A firgice ta mike zaune za ta yi ihu ya yi saurin rufe mata bakin.
"Shii..." Ta tsaya tana mai dubansa daga shi sai riga marar hannu sai dogon wando na Adidas, ta sauke ajiyar zuciya, ta ja baya, ya saketa, ta sauke kafafunta daga saman gadon shima ya yi yanda ta yi yana mai dubanta fuskarsa a daure. Sai wani jan riga ta ke yi don sanye ta ke da t-shirt mai karamin hannu sai zani da dankwali, gaba daya t-shirt din ta matseta don kuwa ba Ummin da ya sani a baya bace, wannan ta yi k'iba ta k'ara haske. 
   Ya kauda kansa yana ta6e baki kadan, tana gaisheshi saidai bai amsa ba. Ya zarce da maganarsa.
"Laifin me na yi ki ka k'i amsa wayata sannan bakya tunanin zuwa gaisheni kafin na fita ko kuma idan na dawo, kin manta yanzu duk wadannan hakkine a wuyanki?"
  Ganin ba alamar wasa a fuskarsa ta kara sunne kanta.
"Ka yi hakuri don Allah."
Shikenan ta gama da shi, wuyarta ka ba shi hakuri, yana iya yafemaka.
  Ya dubeta yana murmushi.
"Ya wuce."
Da dabara ta janyo hijabinta zata sanya caraf ya rike hannun. Ta dubeshi kamar za ta yi kuka shima ya narkar da nashi idanun cikin nata.
  "Wai Ummina yaushe ne za ki bar wannan halin? Har yanzu kunyar..."
Sai kuma ya yi murmushi sadda ya je janye hijabin.
"Kodayake, laifina ne."
Ta ja baya a tsorace tana mai turo baki kadan don ita gani ta ke yi ya takura rayuwarta. 
  "Nidai don Allah ka fita kada Hajiya ta leko ta ganka."
Ya dan daga gira yana gyada kai.
"Oh, gani na nawa kuma? Da nasan ita ki ke tsoro ai da ban shigo ba, yanzu tashi ina bukatar shan ruwan lipton, saidai nafison ki cire wannan ledar ta jikinsa ki zazzage garin ki zuba sugar idan ya dahu ki tacemin, ok? Idan kin kammala ki kawomin." Ya mike ya yi gaba batare da jiran amsarta ba.
Ranta a dan 6ace ba ta bishi da kallo ba don komai ba tasan wayo zaiyi mata dole ta shiga sashensa. Yanzu idan ya ce zaiyi mata abinda aka ce kada ta yarda sai an kaita gidansa fa?
Ta kauda wannan tunanin ta mike ta chanja kaya zuwa doguwar rigar jallabiya ta sanya hijabi sannan ta fito. A falon ta tarar da Hajiya na shirin ratsawa sashen mijinta, ta dubeta.
"Ya akayi Ummi?"
A kunyace Ummi ta bata amsa.
"Shayi ya ce na hadamishi."
Hajiya ta gyada kai ta yi shiru, kamar ta ce wani abu sai kuma ta chanja tunani da fadin.
"To idan kinje ki dawo." Daga haka ta shige abinta, Ummi ta gane hausar. Ta mike ta sauka. Kicin din har an kashe fitilu, sai walkiya da ke haskoshi ga kuma karar ruwan sama wanda ake makashi sosai. Ta kunna fitila a ranta tana mai godiya ga Allah da wannan yanayin na damuna mai dadi. 
   Saida ta kammala kamar yanda ya ce sannan ta juye a flask ta sanya karamin kofin tangaran a filet dinsa sannan ta nufi saman. 
  A bude ta tarar da shi don haka ta shiga da sallama, fitilun a kashe suke sai ko hasken talabijin da ke aiki, yana zaune a falon da laptop saman cinyarsa yana dannawa. Shigowarta ne yasa shi maida dubansa gareta. Ya sauke kafafunsa saman tebur ta ajiye kafin ta zubamishi. 
  "Gashinan."
"Thank you."
Ya fada cikin kankan da murya, ta juya ga kallon barandarsa wacce ke a bud'e ga kuma labulen dakin dake kadawa har ruwa na fallatsowa, ta ga alamun baya jin sanyin. 
  "Saida safe." Zata mike ya fisgota. Cikin kankan da murya ya ce.
"Na sallameki ne?"
Ummi wacce yanayinta ya sauya ta kasa magana sai girgiza kai. Ya gyara mata zama sannan ya sa hannu ya soma kokarin ciremata hijabin.
"Ke bakya jin zafin gari ko? Cire ki shak'i iska mai rahma."
Bata da kata6us har ya cire ya yi saura daga ita sai hular kanta da doguwar rigar. Ta hade hannuwanta wuri guda gami da dan muskutawa ta ja baya da shi. Idanunsa akan laptop saida ya murmusa, wai shi yarinyarnan ke kakkaucewa? Ya share batunta ya soma shan ruwan shayinsa yana danne-dannensa cikin email account dinsa. 
  Ita kam Hajiya kawai ta ke tsoro, yanzu don Allah idan ta ji ta shiru me za ta ce? 
  Faruk bai k'ara duban inda ta ke ba sai bayan ya kammala sannan ya kashe laptop dinsa ya dubeta. Duk ta 6ata fuska kiris ya rage ta soma kuka.
    Yasa hannu ya janyota jikinsa.
"Zo ki fadamin me ya 6ata ranki?"
Babu amsa, ya shafi gefen fuskarta har zuwa wuyanta nan ma ba ta ce komai ba, ganin yana kokarin yin son ransa ne yasa ta saurin rike hannunsa gami da ja baya.
  "Don Allah zan tafi kada Hajiya..."
"Tell me, Hajiya ki ke aure ko Faruk wai? Tsoron me ki ke yi mata haka alhalin tasan kina wajen mijinki? A baya ina miki haka ne?"
  Ya na magana a hankali saidai muryar na nuni da 6acin rai. Ta girgiza kai sai kuma ga hawaye, runtse ido ya yi gami da kwantar da kansa jikin kujera, ba kuma yaso ta zargi ko abinda ya ke so daga gareta kenan, baya son 6acin ran Ummi. Saidai shi kunyar ce baya so, yanzun kuma ya lura harda tsoro ma. Tunda ya ke a rayuwarsa bai ta6a ko rungume wata diya mace ba balle ya aikata wani abin. Ya ja guntun tsaki.
  "Tashi ki tafi. Saida safe." Ya yi maganar a sanyaye.   Ta dubeshi sai ta ji soyayyarsa na karuwa ga kuma tausayi, tasan bata kyauta ba. Murya na rawa ta ce.
"Don Allah ka yi hakuri Yaya Faruk."
Ya dubeta yana murmushin karfin hali da kokarin hadiye abinda ke taso mishi.
  "Karki damu ba fushi na yi ba, muje na raka ki."
   Suka mike yana rike da hannunta, ya janyo hijabinta ya sanya mata, ta zura takalminta, suna isa kofa baisan sadda ya fisgota ba har ta firgita, ya hada bakunansu wuri guda, saida ya gaji don kansa ya saketa ya ja baya kadan yana dubanta.
  "Goodnight." Itama da sauri ta fita, ya rufe kofar. 
  Ta juya ta dubi kofar sannan da sauri-sauri ta fice tana numfarfashi. 
      Wannan daren daga ita har shi sun jima kafin bacci ya kwashesu...
                    ***  ***  ***
Abu kamar wasa, Ummi ta shiga yi mishi 6oyo, duk wata hanya da zasu ke6ance ta tosheta, shi kuma idan ya ganta tare da Hajiya ba ya iya cewa uffan don mikewa ta ke yi ta bar falon. Zuwa yanzu ta dan soma sabo da Hajiya don Hajiya Babba ta sakarmata sosai ta yi ta janta da hirar Gombe, itama har ta sake ta yi ta bata labari.  Bai kara sanyata a ido sosai ba sai ranar Asabar, shima ta fito cikin shirin Islamiyya ne. Gabanta ya fadi, ta durkusa ta gaida Hajiya sannan ta gaisheshi. Ya tamke fuska kwarai har Hajiya saida ta yi mamaki. 
  ((Manage pls...jiki da jini....))
   DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

104

"Ba kai ake gaisarwa ba?" Cewar Hajiya.
Ya yamutse fuska kadan.
"Lafiya."
  Ya mike.
"Hajiya bari na je na dawo."
"Aa, to ka tafi da ita mana kawai. Tunda duk hanya ne."
Ya runtse ido kadan sannan ya yi gaba, Hajiya ta dubeta.
"Tashi ku je."
Ummi wacce duk jikinta ya yi sanyi, ina laifin mai sonka? Ta ji haushin kanta na 6atawa Faruk rai, mutumin da ya so ta tun kafin ta zama 'yar gayu haka, tun tana matsayin 'yar aiki.  Sam bata kyauta ba, Faruk bai cancanta ta dunga 6atamishi rai haka ba. 
   Ta iske tuni ya fiddo motar yana jiranta, ta karasa kanta a k'asa, ta bude gaban mota ta shiga, sanyi da kamshi ya doketa, garin ya yi sanyi hakanan babu rana kamar zaayi wani ruwan. Ta rufe kofar gami da satar kallonsa saidai ko inda take ba ya kallo, fuskarsa babu digon walwala, gaba daya haushin kanta ya kamata, suka soma tafiya nan ma babu alamun zai shiga harkarta, wannan ne dalilin da yasa ta daure ta soma magana dakyar.
"Yaya Faruk."
Bai amsa ba hakanan bai kalleta ba. Ta sunkuyar da kanta idanunta suka ciko da ruwan hawaye, ta dubeshi cikin rawar murya.
"Yaya Faruk don Allah ka yafemin."
Ya lumshe ido ya budesu yana mai duban gefen da zai yanka kwana, can cikin zuciyarsa babu dadi, ji ya ke tamkar ya janyota ya rarrasheta, ko kusa ya tsani kukanta. 
  Ita kuwa ganin ya yi shiru yasa ta kauda kanta ta maida dubanta ga gefenta tana sharar hawaye. Shiru ya biyo baya har dai suka isa. 
Daidai Islamiyyar ya tsaya, dalibai har sun shiga wasu kusa na tsaitsaye a k'ofa, gaba daya suka zubawa motar ido don ganin wanda zai  fito. Ya cire (Lock), bata dubeshi ba ta bude kofar ta fita bayan ta share fuskarta. 
  Haka ta shiga ciki, mintuna uku da shigarta suna tsaye wata Malama na tambayarta ko ita sabuwar daliba ce, ya shigo. Gaisawa ya yi da wani Malami sannan ya yi ciki zuwa ofishin headmaster bayan ya yi mata umarnin ta biyoshi. Nan ya bada hakurin rashin zuwanta na tsawon lokaci, ya nuna babu komai. Aka sallameta ta fito, da isarta kofar ajinsu suka hadu da Husna da wasu. 
  "Lah, ashe dagaske ki ke Fati, Hasiya ce."
Cewar Husna kenan, Ummi cikin rashin fahimta ta dubesu, saidai kafin ta ce wani abu, ta ji suna duban bayanta wata na fadin.
"Gashinan wallahi, wayyo Allah, very handsome, please Hasiya ki hadani da shi, wallahi yayanki ya min, kalar mijin da nake fata kenan."
Cewar wata Shukra Aminu.
Wani mugun kishi ya turnuk'e Ummi, ta juya ta dubi Faruk sa'ilin da

Please Login or Register in order to submit comment