Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yawa, sanye take cikin wata atamfa ruwan madara mai adon fulawoyi, fuskarta fayau sai hoda da kwalli da ta sanya, kadan-kadan ta ke motsa lilon ta kwantar da kanta saman lilon idanunta a lumshe tana mai jin dadin wakar da ta ke bi na Alan waka na (Ummina). A hankali kuma hawaye suka soma zuba saman fuskarta, ta k'ara gyara zaman (earpiece) din kunnenta. Daidai lokacin da Faruk ya shigo gidan, dawowarsa kenan daga nan makwaftansu wajen wani dan makocinnasu mai mutunci da bai ji dadin jikinsa ba, kasancewar sun saba haduwa duk weekend yawanci anan kofar gidan su gaisa yasa koda ya ji ba shi da lafiya ya yi yunkurin zuwa dubashi. Yana sanye da riga koriya da wandon jeans bak'i, kai tsaye hanyar cikin gidan ya yi saidai idanunsa ya hangomasa sanyin idaniyartasa zaune saman lilo, ya dan kuramata ido duk a zatonsa ma bacci ta ke yi a hakan ganin yanda ta lumshe ido, ya taka a sannu ya karasa gareta, sai lokacin ya lura da(earpiece) dake a kunnenta ga kuma hawaye da ta ke zubarwa. Zama ya yi gefenta kamshi na turarensa ya ankarar da ita zuwansa. Da sauri ta bude idanunta gami da sa hannu ta share hawayenta, duk yana kallo saidai baice komai ba hannu yasa ya ciro kunne daya yasa a kunnensa, ya yi shiru yana nazarin wak'ar kafin kuma ya cire daga kunnensa yana mai dubanta, ta maida hankali ga wayar don kashe wakar.
   "Kina tunawa da Ummarmu ne?"
Ta kasa magana sai gyada kai. Ya sauke numfashi.
"Hakan yana da kyau, saidai ba kukanki ne abin so awajenta ba, addua ya kamata ki yi mata idan har kina son ta yi farinciki da ke. Duk wanda ya mutu yafi bukatar adduarmu sama da komai."
   Ta gyada kai.
"Hakane."
"Allah Ya jikanta."
"Amin."
Shiru ya dan biyo baya.
"Ni kuwa Ummi kin ta6a ganin hoton Ummanki?"
  Ta girgiza kai, wannan ma na daya daga cikin abinda ke sosa ranta muddin ta tuno.
  "Ko a hoto bansanta ba, nasan dai muna kama ta bakin matar babana shima sai tana zagina ta dunga hada yanayina da ita sai ko makwafta da zan ji suna fadin kamarmu da ita."
  Ya jinjina kai.
"Allah Sarki. Kenan babu wani nata da ki ka ta6a gani?"
Ta amsa da eh. 
  Shiru ya biyo baya kafin kuma ya ce.
"Bayan wuya sai dadi in sha Allah, wataran za ki zama abin so da alfahari wajensu."
  Ta yi murmushi don har cikin ranta ta ji dadin maganar.
"Allah Yasa."
"Amin."
Sun jima suna yar hira tana amsawa a kunyace kafin su mike su shiga ciki.
                     ***   ***   ***
                           KANO
    Hajja ta dubi Fatima babbar diyartata da kulawa.
"Ke kam menene haka mai muhimmanci da ya taso ki daga Abuja zuwa Kano, maimakon ki bari tunda sati na sama ne zaayi taron zuri'a (family meeting) ku taho gaba daya da yara?"
Hajiya Babba ta murmusa, kwananta biyu kenan da zuwa amman kullum sai Hajja ta yi mata korafin zuwannata don gani ta ke yi kamar wata matsalar diyartata ta samu da maigidannata. 
  "Ke kam Hajja ba wani abin bane ba fa, daga zuwa ganinku duk kin bi kin damu kanki da tunani."
"A'a to, gani na yi ba ki saba wannan zuwan haka ba."
  "To ke tunda kinsan bata saba ba, ai kinsan banza bazai kawota ba, akwai wani abun, bari yan uwannata su zo ko menene sai mu ji."
   Cewar Dattijo Modibbo mahaifinsu.

Jin haka Hajja ta rausaya kai.
"Ai shikenan na bari."
A karshe ma suka shiga wata maganar inda Modibbo ke fadin ya dace ma su kai ziyara Adamawa don sun jima basu je ba, ya ce idan anyi zaman taro zai fad'a. 
Sai bayan Azhar Hajiya Mama ta iso ita daya sai autarta Mufida. Bayan an gaggaisa suka zauna hira da zaman jiran Mami, ba ita ta zo gidan ba sai yamma. Nan din ma ta zo ne tana daure-dauren fuska, ko kallon inda ta ke Hajiya Mama bata yi ballantana wata gaisuwa ta shiga tsakaninsu. Sai lokacin Hajja ta fahimci akwai matsala. 
Bayan sun zauna har mahaifinnasu, Hajiya Babba ta zayyane batun auren Faruk da Ummi da kuma maganar Ihsan kaf ta fadawa iyayen, sai kuma Hajiya Mama ta dora da yanda suka yi da Madina a gidanta. 
  Shiru ya biyo bayan gama saurare, can kuma Modibbo ya yi maimaita Innalillahi wa inna ilaihir raajiun har sau uku.
  "Hakika shaidan ya so shiga tsakaninku, ina nema muku tsarin Allah daga sharrinsa."
Ya dan yi shiru kafin ya dora.
"Kin bani mamaki Auta, kinyi abinda ban ta6a zatonki da aikatawa ba, da ace wani bare ne ke sanarmin kin yi wannan gagarumin laifin da babu ta yadda zan amince da hakan. Karki manta cewar Aure shi kaddarar Ubangiji ne, idan Allah Ya kaddarowa shi Farukun da ita Ummi aure, to babu mahalukin da zai chanja yin Allah, hakazalika idan kaddararsa ce aurensu su biyu duka, nan ma duk wani tashin hankula da zaayi zai je ya dawo ne ba fa zaa fasa abinda Allah Ya shirya ba."
  Shiru ya dan biyo baya, Mami ji ta ke yi ranta na zafi, wato iyayensu ba su ga hadin da ake so ayi na diyarta da yar aiki ba? To wai ma Faruk kadai ne namiji da har zaayita takurawa akansa? 
  Modibbo ya cigaba da yi mata nasiha don ba shi da zafi sosai, ita kuwa Hajja shiru ta yi, wannan fadan da ake yiwa Madina yafi komai yi mata zafi, tana ji da yar autarta ta. Bayan Modibbo ya kai aya ta soma magana a fusace.
"Nifa banga laifin Madina ba yarinyar nan da gaskiyarta. Ke banda rashin wayo da girman kwabo ki rasa da wacce za ki had'a dangantaka saida yarinyar da bakisan komai game da ita ba, 'yar asali ce, shegiya ce, oho! Duk ba daya da ki ka sani,duka-duka ko wata uku bata cika ba inace tare da mu, kece kuma har da marin kanwarki saboda..."
  Tsawar da Modibbo ya dakamata ne yasa ta yin shiru tana kwafa, zuciyarta na tafarfasa kamar ta rufe Fatima da Sadiya da duka haka ta ke ji.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
  82
"Ke meyasa baki da tunani ne? To ko fita idona tun ban sa6amiki ba wallahi! Kina ganin ana kokarin gyara lamari ke kuwa kina neman ki k'ara dagula shi? Ko an gayamaki shi Amadun ba shi da hankali da ba zai yi bincike ba kafin hada zuria da su? Haba!"
  Ya juya ga yarannasa kafin ya kai ga magana Mami ta soma.
"Ka yi hakuri Baffa, amma don Ihsan ita ta hakura, mahaifinta ma ya yi mata miji bata sani ba."
   Ta fadi hakan don ma kada ya ce lallai hakan zaayi, Modibbo ya so fahimtar kawai ta fada ne saidai ya yi tunanin barin mutum da halinsa, ya jinjina kai ransa baiyi mishi dadi game da wannan sa6ani da aka samu ba tsakanin yaransa wadanda ya ke alfahari da su wajen kokarin zumunci da hadin kai.
     Haka dai aka rabu ran kowa babu dadi. 
    Hajiya Babba kuwa ji ta yi kamar ran lahadi ta bi mota ta bar garin Kano sakamakon Hajja da ke ta jifanta da bakaken maganganu marasa dadi, daman Hajja ta na da fada idan an ta6ota musamman idan aka ta6a autarta. Ranar litinin kuwa jirgin safe Hajiya Babba ta bi zuwa Abuja zuciyarta a cunkushe, saukinta ma ta samu goyon baya wajen mahaifinnasu inda ya ce kuma ta dage nemawa dannata za6in Allah, Allah ba Ya bacci, Shi Mai amsawa ne.
   Da wannan hankalinta ya dan kwanta, itama Hajiya Mama ta jaddadamata ta kwantar da hankalinta, karon kanta Mamin zata zo ta gano kuskurenta, wannan zamanin namiji mai rikon aure sai an auna, tana kyautata zato akan Faruk. Madina zata yi da na sani acewarta. 
                    ***  ***  ***
                       RINGIM
  Salati Habiba ta shiga yi tana kallon Saude wacce ta shigo a rude ta zubar da Mariya akan kujera tana rusa ihun kuka sakamakon maganar da wata makwafciyarsu ta kawomata akan ta sanya ido akan yarinyarta don ta ganta sun shiga wani lungu da Dauda fitinannen d'a ga Zinaru itama makwafciyarsu, wannan dalilin yasa ta duba diyar ta tabbatar ana amfani da ita.
  "Kingani ko? Daman na sha kwa6arki akan sakacin da ki ke na barin yarinyar nan tare da wannan yaron, itace har shagon Usi mai kanti, yanzu ga irin ABIN DA AKE GUDU!"
   Ita dai Saude ba bakin magana, don cuta an gama cutarta diyarta kenan daya a duniya, tana ji da ita ta kuma ci buri akan aurenta idan ta girma don yanzu duka-duka shekarunta bakwai a duniya. 
   "Ba kuka ya kamace ki ba, mu lalla6a mu kaita asibiti a aunata ko tana da cutar kanjamau, idan babu duk sauran mai sauki ne."
   Suka dunguma zuwa asibiti, anci sa'a bata da cutar saidai ciwon sanyi da ya yi mata yawa a jiki, likitan ya tabbata musu ana amfani da yarinyar, abu ne da suka riga suka sani, ya nemi yardarsu a yi mata dinki suka k'i acewarsu sunsan yanda zasuyi. 
  Daga asibiti suka wuce wajen bokanya nan ta hadamusu magunguna, anan kuma Habiba ta je da batun matsalar Dija da Raihana, Bokanya ta ce zata yi aiki akai.
  Haka suka wuce ran kowannensu ba dadi, Saude ta so zuwa gidan Zinaru ta zagesu tas saidai Habiba ta kwa6eta gami da nunamata wannan tonon silili ne don wanda bai sani ba ma zai iya sani. Basusan cewa ba, mutanen gari sunsha tarar Malam Balarabe akan ya saka ido akan diyarsa, anan kuma Saude idan ta ga ya hana diyar fita ta nunamishi bai isa ba.  Daman yasan shi din ba shi da wani kata6us a gidan, yan uwansa ma an rabashi da su, ba wanda ke takowa Ringim da zummar ganinsa tun bayan rasuwar Yayar Malam Balaraben da ta rik'eshi, itama har ta mutu bata ta6a haihuwa ba. Daman iyayen na Malam Balarabe sun rasu da jimawa. 
                 ***   ***   *** 
                    KADUNA...

Lamura sun ca6ewa Dija tun ranar da Raihana ta yi mata waya akan tana nan zuwa, ta fahimci dukkan wani abu da su ke yi don a rabasu ya ci tura hakan bai samu ba, ranar da Deen ya koma dakin Munira a ranar Raihana ta zo. Da shirinta ta zo wajenta don kuwa wani shegen kwalli ta sanya a idanunta da yasa Dija kasa yi mata musu a dukkan abinda ta ce, ga wani dan iskan turare mai saukar da shaawa. A wannan ranar Raihana bata bar gidan Dija ba sai dare, Dija kuwa saidai ace Allah Ya kwatota don kuwa tuni ta fada tarkon shaidaniya Raihana. Tun daga ranar suka kara shak'uwa ta waya, har Raihana ta yi zuwa biyu gida, mutan gidan ba wanda ya ta6a kawo munin abu irin wannan a kansu saidai sun shaida Raihana ba ta yi kalar nutsastsun mata ba.
                   ***   ***   ***
                        KANO

  Ihsan ta yi tsai tana duban hoton saurayin da Maminta ta bata, babu laifi kyakkyawa ne kuma bak'i, yana da 'yar kiba. Ta numfasa, ba wai ta ji sonsa a ranta ba, kawai dai ya kai yanda zaa iya auren huce haushi da shi.
  "Dan wani babban abokin Abbanku ne dake Adamawa, mahaifinsa babban Injiniya ne, Alhaji Kabir Jimeta."
  Ihsan ta ajiye hoton a gefe.
"Yana da d'a Abubakar?"
Cikin dariyar mamaki Mami ta ce.
   "Ashe kin sanshi ma, ai shine wannan din."
  Ta dan ta6e baki.
"Yana da kirki, muna chatting da shi ai saidai ban sanshi a hoto ba, ya sha gwada yana sona saidai ni ce ban ba shi fuska ba."
     "Ai kuwa ya zama dole ki so shi, kin kuwa san matakin arzikinsa yanzu a Adamawa? To ana sanyashi cikin goman farko na yara matasa masu kudin garin sannan kalleshi da kyau ba shi da makusa a halitta."
  Ihsan ta danyi jim, kafin ta ce.
"Yana da mata fa Mami."
Tsaki Mamin ta ja, ta soma fusata da lamari na diyartata kuma.
"Shikenan sai ki zauna jiran aurenki da Faruk ki yi kishi da wacce bata kai ba, ni wallahi bansan irinki ba, ina ruwanki da matarsa? Matarsa gogaggiyar yar boko ce kuma bata ta6a haihuwa ba da shi, shi kuwa ba shi da burin da ya wuce na ganin ya haihu a duniya. Idan ki ka haihu da shi tabbas mun warke, kada ki bar wannan dama ta wuce mu. A zamanin nan samun matashin da ba shi da aure kuma mai rikon aure sai an tona, gwara ki auri wannan da kowa ya shaida kyawawan dabi'unsa."
   Haka Mamin ta yi ta kod'a Abubakar a wajen 'yarta, ita Ihsan har mamaki ta ke yanda uwar ta sanshi haka, sai kuma ta tuna sunan mahaifiyarsa da ta ambata, wato Hajiya Salma kusan tare suka tashi da Mamin a Kano, aure ya rabasu. Dole Ihsan ta amince da hakan, saidai abinda ta kasa sanar da Mamin shine, Abubakar ya sha janta da hirar da bata dace ba tana k'in ba shi fuska, hakan yasa ma dangantakarsu ta yi tsawo.  Ai kuwa kamar jira Mamin ta ke, Abba na dawowa ta tare shi da zancen, ya ji dadi matuka don kuwa acewarsa daman Alhaji Kabirun ya ta6a neman tayin hakan tun akan Aisha saidai Allah baiyi rabon dannasa bace, yanzu kuwa yasan zai ji dadi idan ya kasance da Ihsan, daman burinsu a k'ulla zumunci. 
   Kwana biyu da yin hakan Alhaji Muhammad ya yi magana da abokinnasa.
"Kamar kuwa kasan ina kan ga6ar nemarwa dan nawa aure, ina burin ganin jikokina, fatana Allah Yasa idan anyi hakan mafarkina ya tabbata."
  Nan suka sasanta magana inda Alhaji Kabiru ya tabbatar mishi cewar cikin(weekend) zai zo tare da dan nasa don su ga juna. Da wannan suka ajiye wayar ran kowa ya yi dadi. 
Bayan Abba ya ajiye ne ya dubi Mami.
"Kinga cikin ikon Allah sai a had'a auren harda na Iklima, itama ta tsaida yaron nan dan gidan tsohon kansila, Mu'azzam. Itama Hussainar ba barinta zan yi ba, lokaci guda zan aurar da su idan Allah Ya yarda, da zarar sun kammala wannan ajin, ba don ma yaron ya ce sai ya gama gini ba, da sai a soma na Iklimar."
  Mami ta gyada kai, ranta baiso ba, ta so ya zamana ba za'a hada auren diyarta ta da na kowa ba, ko don a fi ganin kalar bajintar da zata yi. Amman ta riga ta saba da binshi yanda yaso.
"Hakan ma ya yi, Allah Yasa ayi muna raye."
Ya amsa da amin cikin jin dadin sha'ani na uwargidan tasa wanda ya sha bamban da Hajiya Binta, da ita ce sai sun kai ruwa rana, gwara-gwara Hajiya Luba, itama akan yi abin arziki da ita idan kishinta bai motsa ba.
                   ***   ***   ***
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
83
                       ABUJA

   "Allah Mai Iko." Shine abinda Gen. Ahmad ya fad'a sa'ilin da ya ajiye waya da Alhaji Atiku inda suka tattauna a mutunce. 
  Hajiya Babba da ke kokarin zuba mishi abinci babi abinda ta ce, tamkar duk bata ji abinda suke tattaunawa akai ba. Shima Daddy ita ya yi shiru yana duba.
  "Meyasa ki ka 6oyemin wannan batu? Na yi tsammanin don shi ki ka je Kanon?"
Hajiya ta ajiye (serving spoon) tana mai duban mijinnata cike da kulawa. 
   "Me fa?"
"Ai shi Alhaji Muhammad ya riga da ya yiwa diyartasa miji, d'an abokinsa, Alhaji Kabir Jimeta."
  Hajiya Babba ta yi wani murmushi.
'Madina kenan.'
Ta fada a zuci, a fili kuwa ta nuna rashin damuwarta.
"Allah Yasa alheri, ni sai yanzu da ka fada na sani daman iyakar tattaunawarmu da ni da Madinar ce, watakil sai bayan ta sanarmishi itama ta ji hakan don da ace ta san da haka ba zata 6oyemin ba."
   Ta fad'i hakan ne don batason ta nunawa mijinta basu dadi da yar uwarta. Ganin fuskarsa ta cika da damuwa ta ce.
"Ba wani abu fa, kasan babu mai aurar matar wani, watakil ba rabo tsakaninsu, idan akwai sai kaga lamarin ya juye."
   Ya jinjina kai cike da gamsuwa da maganganunta.
"Hakane kuma, to Allah Ya za6amusu abinda yafi alheri. Ita wannan ya ake ciki?"
   "Ga dukkan alamu lokacin zuwan matar da ta kawota ya k'arato inaga tunda ga watan saura kwana biyu ya mutu, ( family meeting) din namu shima ina tunanin jibi ne zaayi."
Cewar Hajiya kafin kuma ta cigaba da zubamishi abinci. 
            
    Kwance a saman lallausan katifa a saman gado, Ummi ce tana faman duba wasu litattafan addini da Hajiya ta had'ata da su, ta ji dadin hakan kwarai, Hajiya ta k'ara da batun sanyata Islamiyyar da Ikram ke zuwa don zuwa lokacin hatta form an kar6omata, hakanan an bada a dinka mata (Uniform). Ga shi kuma gogan ya nuna yana mata sha'awar karatun boko, acewarsa neman ilimi ko gemunka na ja a k'as ba ka yi latti ba. Wannan shine kyakkyawan albishir gareta. 
    Wayarta ta yi k'ara alokacin da ta tsunduma cikin karatu, ta sanya hannu ta janyota. Tsai ta yi da ido tana duban lambar wacce ta ta ganta banbarakwai, har ta katse bata iya ta d'aga ba, sai a karo na biyu ne ta d'aga da sallama. 
  Daga can Adnan ya amsa yana dariya.
"Kaga sabon shiga kin tsoraci kada a gudu da ke ne?"
  Ta so gane muryar saidai bata da tabbacin shi dinne ko aa, ta dan saki fuska.
"Ba haka bane."
"To ina My Best?"
Kalmarnan babu a bakin wanda ta santa sai Adnan, ta washe hakora gami da mikewa zaune.
"Lah, Yaya Adnan?"
Sai kuma ta yi dariya shima darawar ya yi. 
"Ni ne nan kanin Angonki."
"Kai Yaya Adnan."
"Ai gaskiya ne, yanzu ko kin yi tsada karki so ki ji kashedun da aka yimin kafin a bani lambarki."
Ta yi murmushi.
"Ina wuni." Ta fada cikin basar da wancan maganar. 
  "Ba zan amsa ba tunda kin yi waya amma ba ki nemi a ba ki lambata ba."
  "Ka yi hakuri to, ya su Mami?"
  "Suna k'asarku, ni ina nan Dubai."
Ta dan bude ido kadan.
"Au na manta, Yaya Faruk ya gayamin kwanaki wai za ka karatu ko?"
   "Inye! Abu ya yi nisa haka ashe?"
Ya karashe yana dariya, ita kuwa murmushi kawai ta yi, ita sai lokacin ta tuna da ashe fa da yaya Ihsan ta ke magana, sam halinsu ya bambanta.
  Adnan ya sake da ita suka shiga kwasar hira sosai yana bata labarin Dubai tamkar wata abokiyarsa,  duk da tana jin wani dan kara(din-din) ta cikin wayar bata fahimci ko na menene ba. Bayan sun kammala wayar ne ta ajiye, nan ta fahimci Faruk ke kira. Kafin ta kai ga yunkurin kiransa sai ga shi ya kara kira.
  Bai ko amsa sallamarta ba.
"Da wa ki ke waya?"
"Yaya Adnan ne."
Ya sauke ajiyar zuciyar da har ta ji.
"Ok, amman kun jima kuna waya, me ya ke fadamiki haka?"
   Ta yi murmushi kadan.
"Hira ce ta makarantarsu ya ke min."
"Ok, kina da labarin tafiyarmu Kano gobe?"
Gabanta ya fadi.
"Har da ni?"
"Au, Hajiya bata sanarmiki kenan? Watakil sai zuwa anjima, family meeting zaayi, kusan wannan karon ni da ke ne masu muhimmanci a gurin, akwai wani ma albishir din amman ba yanzu zan yi miki shi ba."
  Ita kam duk ta tsorata, ta lura shi gogan ma bai gane hakan ba.
  Suka dan ta6a hira kafin su yi sallama.
   Ai kuwa a daren Hajiya ke sanarmata cewa ta shirya kaya ko kala uku ne. 
      Washegari gaba daya da misalin biyu na rana suka kama hanya har yayyun Faruk da matansu, a motar can lungu ta zauna don gujewa wani abin da zai je ya zo, tana ji Intisar, Baraka da Ikram suka juye harshe zuwa fulatanci suna hirarsu, duk ta bi ta tsargu duk da basu ko kallon inda ta ke. 
                    ***   ***   ***
                         KANO
     Acan kuwa gidan Mami, da misalin karfe uku Yaha ta diro. Mami ta dubeta bayan ta zauna.
"Aa Yaha sai yau ki ke tafe?"
"Wallahi kuwa Hajiya, Minna na je shiyasa na kwan biyu ba ki ganni ba, su ma can gidan su Ummin suna min waya wai sun ji shiru."
   Murmushi Mami ta yi na takaici. 
"Ai kuwa Ummi bata gidannan yanzu."
Yaha ta karkato gami da yin sakato da baki. Mami ta koramata bayani.
  "Jar Uba!" Shine kawai abinda Yaha ta ambata....!

  Don gyara ko shawara a tuntu6en...
omarrufaida@gmail.com or through facebook acc. Rufaida Omar
  "Jar Uba!" Shine kawai abinda Yaha ta ambata....!
  DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

84
    Yaha ta yi furucin cike da tsananin mamaki, ba don Mami da kanta ke sanarmata ba da kai tsaye zata kira hakan da shaci fad'i.
Mami ta cigaba da magana.
"Ba abin mamaki bane, shi DAN ADAM idan ya samu guri fin haka zai iya aikatawa, banda haka ki duba irin yanda na dauki yarinyarnan, tunda nake yin yan aiki ban ta6a yin wacce na kyautatawa ba kamar ita, har wai yar aiki ta samu matsayin da zan zauna na dan yi hira da ita. Anan menene bai faru ba.."
Sai kuma ta yi shiru tana mai jin zafi a ranta.
  Yaha ta yi shiru cikin nazari, to ita fa Saude kudi ta ke nema, ita dai acewarta ko karuwanci yarinyar zata fad'a to ta fad'a matukar zata samu abin duniya sanadin haka, ga kuma yanzu a karshe da suka yi waya ta sanarmata kada ta kuskura yarinyar ta k'ara koda kallon hanyar garinsu ne ballantana wai ta kawota ganin gida. Yanzu ya za ta yi? 
  "Ki ka yi shiru? Idan za ki iya komawa gobe ki dawo to, idan kuwa za ki yi zaman jiran zuwansu daga Abuja yau din to babu laifi."(Ta sani ne ta hanyar Ihsan wacce su ka yi maganar da Ikram.)
    Sai lokacin Yaha ta dawo cikin hayyacinta, lallai kam tana bukatar nazarin.
"Bakomai ranki ya dad'e, zan iya tafiya na dawo goben."
Mami bata ko kara kallonta ba, daga haka itama ta mike ta bar gidan ba tare da ta samu ko na mota daga Hajiyar ba kamar yanda ta saba yi mata duk zuwanta.
   Bata zarce ko'ina ba sai gidan 'yar yayarta Abida wanda anan ne ta saba sauka duk sadda ta shigo garin Kano. Abida ta yi mata kyakkyawar tarba yanda ta saba. Yaha ta sauke mayafinta.
"Su Abu sun wuce makaranta ne?"
  "Eh sun dan jima."
Sai bayan ta ci abinci ta yi sakato tana tunani, Abida da ke gefe tana kokaarin zuba kananzir cikin risho tana mata hira amman shiru hakan yasa ta dubanta.
"To Inna meke faruwa ne haka?"
Yaha ta hau lashe kwana kafin ta tureshi gefe ta dubeta. 
"Bani shawara Abida, kaina ya cushe na rasa ma menene abin yi."
  Abida ta maida risho ta gyara sannan ta karkato tana dubanta.
"Ina jinki Inna."
Ta karanto mata tun kai Ummi aikatau da kuma ire-iren abinda Saude ke sanarmata akan yanda ta ke son ganin Ummi har ma da yanda suka yi da Mami. Ta karashe da fadin.
"Yanzu wallahi gaba daya jikina jinsa nake a sanyaye, ni tunda nake kai yan aiki ban ta6a haduwa da mai hakuri irin Ummin nan ba wallahi, zan iya ce miki tun tashinta a hannun Saude bata huta ba, ga kuma tsangwama da tsanar da ubanta ke nunamata tamkar ba jininsa ba."
  Abida ita kam mamakin Innarta ne ya cikata, ashe daman zata iya mugun abu har irin haka? A haka idan ka ganta tamkar ba zata aikata ba. 
  "Allah Mai Iko!" Ta fada a fili kafin ta cigaba da magana.
"Inna a farko ina mai baki shawara kan ki ji tsoran Allah, ki kuma sani cewar dukkan wani abu da muke aikatawa za'a tashemu gobe kiyama a kuma tambayemu. Wannan sam ba daidai bane a hada baki dake wajen cutar da rayuwar baiwar Allah wacce bata ji ba, kuma bata gani ba, ki sanya Rahma (diyar Yahan) a matsayinta ki auna ki gani, za ki ji dadi ace yau babu ranki Kulu(kishiyarta tun mijinsu na raye) ta aikata hakan agareta? Kada hakkin Ummi ya kamaki anan gaba Inna, don Allah ki yi tunani wannan ba daidai bane ko kadan."
  Daga haka Abida ta juya ta cigaba da aikinta zuciyarta cike da dumbin tausayin Ummi duk kuwa da cewa labarinta kadai ta ji. Yaha wacce ta yo shiru tana nazarin maganganun Abida ne, jikinta ya yi sanyi, babu abinda ke yawo a kwakwalwarta face irin zagi da hantara da ta dunga yiwa Ummi a hanya da kuma zuwansu Kano, harma da zaginta da suka yi zaman yi da su Saude duk akan abim duniya wanda ba wani mai yawan azo a gani bane. 
  Ta sauke ajiyar zuciya kawai.
                 
  Mutanen Abuja sai Magriba suka shigo garin Kano, Ummi sai rarraba idani ta ke har suka shiga gidan Modibbo. Sai lokacin ta soma jin kamar ta saki fitsari a

Please Login or Register in order to submit comment