Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ai kin wuce aiki yanzu."
Ummi ta dan daure fuska.
"Ni wallahi bana son hakan da ki ke yimin."
"Jimin 'ya, Hafsatu ko karya nayi ne? Ina Ummi ina aiki?"
Hafsatu dake mikawa Ummi tsumma ta yi dariya kawai, ai kuwa Ummin na kar6a ta fice da sauri don dagaske Larai ta bata haushi.  Tana jin dariyarsu. Ta soma taka matattakala ta ga an kunna fitilun falon, hakan yasa ta kai dubanta ga mai shi. Ido hudu sukayi da shi yana sanye da riga da wando yan kanti sai jacket da ya dora bak'a a saman rigar wacce kana hangota fara k'al, hakanan farin wando ne dogo na jeans a jikinsa. 
    Idanunsu suka sark'e cikin juna, wani kyau ta ga ya yi mata na daban duk da ta lura da jan da saman hancinsa ya yi can kuma ya saki atishawa, ya rufe bakin ta hanyar amfani da dan hankicif din dake a hannunsa. Kafin ya kai ga cewa wani abu, Haidar ya shigo shima sanye cikin kananun kayan, da sauri ta haye sama bata bari ko gaisuwa ta shiga tsakaninsu ba. Ya numfasa yana duban Haidar wanda ke kokarin zama.
   "Wai murar ce haka? Ai saida nayi-nayi akan ka kashe fanka ka nuna kai zafi ka ke ji."
   Shima zaman ya yi yana mai dan ta6a karan hancinsa da ya ke ji yana mishi zafi. 
  "Daban da murata na zo saidai ba ta yi karfi haka ba sai yanzun."
"Ya dace ka nemi magani ka sha."
Haidar ya amsa yana kallon hanyar sama.
"Wai kada dai basu tashi ba? Muna da ayyukan yi fa."
  Ya tuna hasken idaniyartasa wacce shigarta ta yau ta daukemasa hankali, murmushi ya danyi.
"Sun tashi mana."
  
Acan kuwa Ummi ta tarar har Baraka ta shirya sun fice daga dakin ita da Intisar, ta goge inda ruwa ya 6ata kafin ta hau shara. Tana cikin yi itama Ikram ta fito, bayan ta kammala ta fito. Anan falon ta iske Hajiya da su Hajja sai kuwa Larai da Hafsatu dake jera kayan karin kumallo.
  Ta ajiye ta karasa ta gaishesu kanta a kasa, suka amsa, Hajja ko ciki-ciki ta amsa tana karewa yanda yarinyar ta chanja ta wani murje. 
  Har Ummi ta bar wajen da kallo ta ke binta. Kafin ta kya6e baki.
  "Wannan yarinya nan gaba sai ta ce bata sanmu ba.". Ta yi maganar ne da harshen fillanci ganin su Larai dake wajen ga kuma su Amal dake dudubniyarsu. Hajiya Babba 'yar dariya kawai ta yi na wayancewa don ita har ga Allah tana jin kaunar Ummi a ranta. 
    Ummi kasa sauka kasan ta yi jin muryoyin yan samarin Hajiyar tare da su Intisar ana hira, jin suna kokarin hayowa ne yasa ta juyawa da sauri har suna karo da Hafsatu. Ta numfasa.
"Don Allah Hafsatu taimaka ki karasamin da wannan."
  Ba musu ta kar6a, ita kuwa da sauri ta koma ciki, zata shiga daki ne Hajiya Babba ta dubeta.
  "Ummi kirawo yan uwannaki mu karya."
Dole ta nufi dakin su Jidda, ta tarar duk sun shirya, Jidda na sanyawa Ahmad wandon jeans. Ta gaishesu sannan ta isar da sak'on Hajiya Babba.
   Wannan karon ma a darare ta ci abincin, idanun Faruk kacokam yana kanta ko kunyar su Hajiya ba ya ji. Yana kammalawa Modibbo ya ba shi maganin mura ya sha.
   Karfe takwas saura suka kama haramar tafiya. Modibbo ya yi ta jan Ummi da wasa yana kiranta da amaryarsa. Ita kam kanta na kasa kawai tana dan murmushi har suka gama shiga mota. A mota wannan karon ita da su Amal suka zauna don har rige-rigen zama kusa da ita suke, shi kam Ma'aruf har lokacin bai sake da ita ba ya rike abinda Mominsa ta ce masa akanta. 
    Itama ta maida hankalinta ga yaran, duk a takure ta ke don duk dagowar da zata yi sukan hada ido da Faruk wanda ya saita madubi yanda zai dunga ganinta har Haidar na mishi dariya. 
    Ita kuwa damuwa ta yi jin yanda ya ke atishawa, tabbas mura ta kamashi. Garin ya danyi duhu, sunyi nisa aka soma yayyafi kafin kuma a soma ruwan ba mai karfi sosai ba, duk aka daga gilasai, abokan hirar nata duk sunyi bacci, wayarta ta yi karar shigowar sako, ta duba duk a nata zaton kamfani ne saidai Faruk dinne.
   "Ko na dawo nan?"
Ta dan dago suka hada ido cikin madubi, ya narkar da ido, da hanzari ta kauda kanta. Shi Faruk bai kunyar ma a dagosu? 
    Bata kara kallon madubin ba, shi dinma murmushi ya yi kafin ya soma lumshe ido maganin mura na son sakashi bacci, can kuwa ya shimfida hankicif saman fuskarsa bacci ya yi awon gaba da shi. Itama tun tana kalle-kalle har nata baccin ya iso.
   Haka dai har suka isa garin Abuja inda suka tarar ana ruwa kamar da bakin kwarya. Koda suka isa gidan Dakta ne ya yi amfani da lemar bayan motar ta kai yaran ciki, su Ikram kuwa iyayen son ruwa haka aka shiga a guje. 
   Ummi duk hankalinta na ga Faruk wanda ta ga yana shirin shiga ruwan shima, tana son ta haneshi saidai da kunya ainun, to ta ce masa me? Wata lemar Ikram ta daukomusu a ciki Binta na bin bayanta da guda uku, Hajiya ta shige tare da su Jidda, itama Binta ta mikamata tana dariyar murnar ganinta. 
   Ta kar6a gami da fitowa.
  "Ni fa?"
Ya fada yana dubanta da dan daga murya don karar ruwa. 
  Binta ta dubeshi, Haidar ne kadai ke wajen yana bada umarni ga maaikatan masu shirin kwasar kaya cewa abar kayan har ruwa ya tsagaita. Sai kawai ta mikawa Binta lemar da sauri gudu-gudu ta yi ciki rike da takalman su Amal wanda suka cire a mota.
   Faruk ya na murmushi ya kar6i lemar daga hannun Binta, itama ciki ta yi cike da shaawar yanda suke tafiyar da soyayyarsu. 
    Kai tsaye itama falon ta shiga.
"Aa, garin yaya kika shige? Kema biyewa Ikram ki ka yi kenan, maza tafi ki chanja kayannan."
Fadin Hajiya Babba kenan, ta ajiye takalman kafin ta nufi sama.
     Babu k'ura ko kadan a gidan don su Binta sun gyara tsaf, Binta ce ta gyara kuryar Hajiya. Ita dai ta yi mamakin ganin dakinta tas, ta jinjina kai, tasan aikin su Binta ne, wai kenan har ita keda wannan matsayin. 
    
    
           
  
   

  
    
    
   
   
  DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
  
   87

"Allah Mai Iko, abu ya yi kyau." Cewar Modibbo a sanyaye yana dan murmushi, tabbas yaso kwarai Faruk da Ihsan su yi aure, saidai kuma ba yanda zaiyi tunda Muhammad Modibbo ya daureshi da jijiyon jikinsa, ba zai kira Alhaji Kabir da bare ba don kuwa zumunta mai karfi ta auratayya ta shiga tsakani. (Za ku ji idan an shiga tuna baya)
    Saidai a ganinsa wata kusan ai tafi wata, haka dai ya sanya alheri a lamarin. Alhaji Kabir ya dubi matasan yaran Hajiya Babba yana mai fad'ad'a fara'arsa.
"Yanzu Hajiya Fatima wadannan duk iyalinki ne? Masha Allah duk sun girma."
  Hajiya Babba ta yi murmushi, zai iya mantasu kuwa a fuska don rabonta da shi tun tana goyon Faruk da ta je Adamawa, ko su Ikram bai sani ba. Hajiya Mama ce ta soma nunamishi yarannata.
  "Wannan shi ne Usman, ga Ridwan nan babban likita, sai Haidar da karaminsu a maza Faruk."
     Yana mamaki yana binsu da kallo da murmushi, idan kaga Alhaji Kabir ba za ka ce shi ya haifo Abubakar ba don kuwa shi farin bafulatani ne tas, dogo ne kuma siriri. 
   "Ai na dan gane Usman da Ridwan tun shigowata, wadannan ne dai bansani ba."
Ya nuna Haidar da Faruk. Akayi dariya, gaba dayansu yaran saida Modibbo ya yi mishi bayani akansu. 
  "Kenan dai Faruk kai ba ka yi aure ba? Me ka ke jira?"
   "Ai shima yana niyyar yin, akwai wacce zai aura. Ina ta ke ne ma?"
Cewar Modibbo yana waige-waige. Ihsan ta ja tsaki a ranta. Haka kawai za'a dunga tsoma wata can cikin abin zuri'arsu, daidai da Faruk din haushinsa ta ke ji yanda duk ya gama lalacewa akan wacce bata ketare ta a komai ba.
  Wata hirar da aka sanyo ce yasa Ikram wacce aka tura kiran Ummi ta yi mursusi ta gyara zama bata tafi ba, anan kuma Modibbo ya sanarmusu da batun zuwa Adamawa, aka bari sai idan anyi hutun makaranta. 
    Daga nan aka yi zaman cin abinci, Abubakar hankalinsa ya kasu biyu, ga tunanin yarinyar da ya gani mai kama da Inno, sannan ga kallon Ihsan wacce ya ke jin kamar ya sanyata a aljihu ya fice da ita ko babu komai irin kalarsa ce. 
    Mami na tare da yan uwanta wadanda Modibbo ya hadasu ya musu nasiha sosai, duk da har lokacin takan ji zafinsu saidai ganin irin mijin da diyarta ta samu na nunawa duniya kadai yasa ta sassauto aganinta ko babu komai ta burge. Wayarta ce ta yi kara wanda ya yi sanadin katsewar lomar da ta ke shirin kaiwa bakinta. Ta duba ta ga Yaha ce, ta dauka, bayan sun gaisa ne Yaha ke sanarmata cewar ta iso gidanta bata sameta ba. Mami ta yi murmushi.
"Kinsan gidanmu na Sharada ko?"
"Kayya Hajiya, na kwan biyu banje ba koda na shiga layin ba lallai na gane gidan ba."
  "Karki damu ki taho sai ki kirani idan kin shigo."
  Daga haka ta ajiye wayar, Hajiya Babba wacce sam bata da fushi sosai ta dubeta fuska a sake.
"Wacece zata zo?"
Mami ta amsa.
"Yaha ce wacce ta kawo Ummi, ta bukaci ganinta ne da kar6ar kudin wata na sanarmata bata wajena yanzu."
  "Don bata wajenki idan kin fidda kudinki kin bayar sai cibi ya zama k'ari?"
  Cewar Hajiya Mama a kufule don daman har lokacin bata gama hucewa ba. Mami ko kallonta bata yi ba, Hajiya Babba ce ta danyi dariya.
"Ke kuma menene abin daukar zafi to? Kefa haka ki ke ba dai zuciya ba Sadiya."
Ta maida abin wasa hakan yasa Hajiya Mama ta dan sake itama.
"Ai Madinar ce sai a hankali."
Mami itama dan murmushin ta yi kada ta bada su agaban surukai (Jidda da Fadila).
     
  Ummi tana tare da Amina suna hira anan kicin tare da su Larai har sadda Larai suka tafi kai abinci. Alokacin Amina ta dubeta.
"Wallahi kar ki so kiga yanda fatarki ta kara kyau saidai kin rame don har gwara kafin zuwanki Abuja."
  Ummi ta ta6a wuyanta tana murmushi.
"To Anti ba dole ba, nifa koyaushe cikin tunani na ke na wannan abu wallahi."
  "Ya za ki yi to?"
Alokacin da Larai suka dawo ne ta dubesu.
"Wai kuwa kunsan cewa wannan saurayin da ya zo shi zai auri Ihsan?"
Amina da Ummi suka dubi juna ido waje kafin su dubeta.
"Anya kuwa?" Cewar Amina.

"Wallahi kuwa, sunansa Abubakar nima zan fito na ji su Rahila na zancen wai sun dace kuwa."
    Ummi ta yi shiru kawai batare da ta tantance yanayin da ta ke ciki ba, Amina zuciyarta fal murna, hankalinta ya kwanta Ummi ba zata hada kishi da Ihsan ba kenan.
  "Lallai, Allah Ya tabbatar da alheri."
"Ameen dai, ai daga gani dan hutu ne, wannan baisan talauci ba."
  Suka danyi dariya.
"Kai Larai." Fad'in Amina kenan. 
   Nan suka shantake don gaba daya Ummi nauyin fita ta ke ji, ko kusa batason wani ya ganta, tana ganin Faruk na faman dokomata kira saidai ta kasa dagawa har ya gaji ya daina. Har lokacin bata bar tuna kallon da wanda aka kira da Abubakar ke jifanta da shi ba, ta rasa ko na menene.
     Sai bayan sallar Magriba su Abba suka tafi banda Abubakar da ya tsaya hira da Ihsan ya ce zai taho, gaba daya suka yo musu rakiya.
  Shigowar Mami kicin dinne yasa Ummi kallonta cikin rudewa. Ta durkusa ta gaisheta murya na rawa. Daga kallo daya bata k'ara duban inda ta ke ba ta soma magana.
"Amina ki je ki taho da Yaha tana nan bakin titi wajen kantin Nura."
  "Toh." Amina ta amsa, daga haka Mamin ta fice. Ita kuwa Ummi ta shiga tashin hankali matsananci, Yaha kuma? Shikenan yau zata koma garinsu, tasan abinda Mami ke shirin aikatawa kenan. 
  "Muje ki rakani."
Ta bi bayanta jiki a matukar sanyaye, a falon kasa, su Rahila ne da su Jidda gaba daya sun hadu hankalinsu ya tafi a kallon (Swaragini) a tashar Bollywood, sam hankalinsu ya tafi a kallo. 
   Suka fito, a farfajiyar gidan su Faruk ne tsaye, lokacin walkiya ake yi da cida na alamun saukar ruwa duk sadda Allah Yaso.  
  Idanunsa ya kai kanta, ya yi tsai yana dubanta da tunanin inda za ta je a daren nan, kasa jurewa ya yi ya kira sunanta. Ta juyo tana mai amsawa. 
Ya karaso. "Ina za ku je?"
Amina ta sanarmishi aiken da Mami ta yi musu. Ya gyada kai kafin ya dubi Ummi.
"Ina wayarki?"
Ta dago mishi ita ta mik'a batare da ta yarda da kallonsa ba. Ya kar6a duk da ya so kallon kwayar idanunta ko zata fahimci 6ata mishi ran da ta yi na k'in daukar wayarsa saidai hakan ya gagara. 
Suka wuce wayar na hannunsa. 
  Abubakar dake can gefe saman kujera tare da Ihsan suna hira ya yi tsai yana k'ara duban Ummi.
  'Kamar ta yi yawa.' Ya fad'a a ransa. Ya kai duba ga Ihsan wacce gaba daya ta gama k'uluwa da wannan kallon da Abubakar ke yiwa Ummi, kada ace shi dinma ya fad'a tarkonta ne? 
   "Honey, wacece wannan please?"
Ranta ya 6aci.
  "Bansanta ba nima." Ganin yanda ta yi maganar a fusace ya sanyaya mishi jiki, ya sassauta murya yana mai dan dafa cinyarta.
"Sorry i don't mean to hurt you."
Ta dan janye cinyarta gami da jan guntun tsaki.
"Please Abbakar babu kyau fa abinda ka ke yi, kada ka k'ara ta6ani."
   Ya numfasa.
"Ki yi hakuri zan kiyaye, ke dince kin hadu ne Ihsan samun irinki sai an tona."
Ta dan ji sanyin abinda ya ce har cikin ranta, wannan yasa ta dan sassauto, shima ya ajiye maganar Ummi gefe ya cigaba da shigar da kansa wajen mutuniyartasa.
                   ***   ***   ***
   Ummi sun danyi tafiya kafin su ga Yaha. Koda suka isa gareta, baki bude kawai ta ke kallon Ummi, wani arnen material ne a jikinta dinkin riga da siket, ta kara wani kyau sosai, duk da ramar da ta yi, dirin jikinta yana yanda ya ke bai girgiza ba. 
  "Ummi ke ce?"
Ummi da har lokacin bata bar shakka-shakkar Yahar ba ta yi dan murmushin yak'e. Gaisuwar da Amina ta yi mata ne ya katse tunaninta tana mai amsawa sannan suka soma tafiya. Yaha ta dubi Ummi.
"Na ji abin arzikin da ya sameki ai jiya a bakin Hajiya."
Furucin da ta yi yasa suja dubi juna ita da Amina fargabarsu ta dan kau jin ta kira hakan da abin arziki.
  "Um." Shine kawai abinda ya fito daga bakin Ummi.
  "Allah Mai Iko kenan, in sha Allahu babu abinda zai hana wannan aure naki sai ikonSa, yarinya kin yi goshi. Na gano kuskurena Ummi, ki gafarceni kinji 'yarnan, bana so hakkinki ya kamani alhalin ba kiyi min laifin komai ba haka siddan na biyewa makiran nan(Saude da Habiba) na tsaneki."
Ta k'arashe kamar zata yi kuka, wanda hakan ya basu tabbacin da zuciya daya ta ke maganar. 
  Farin ciki yasa Ummi soma zubar da ruwan hawaye ba tare da ta ankara ba, tana kuka tana dariya don murna, ta daga kai ta dubi sararin samaniya yanda ake faman walkiya. Yau ta kira wata babbar rana da ba zata ta6a mancewa ba. (Wani abun na gaba Ummi), Yau ita Yaha ke yiwa magana cike da nuna kulawa da nadama? Amina ta dafa kafadarta.
"To sarkin kuka, akan hanya ki ke fa, kada a dauka sato ki mukayi."
Suka yi dariya har Yaha, ta yi kasa da kanta tana share fuskarta da mayafin jikinta kalar yadin. Banda hamdala babu abinda ta ke yi har suka karasa Yaha na basu labarin auren cin amanar da Dije diyar Habiba ta yi da mijin yar uwarta. Tabbas Ummi tasan wacece Dija don kuwa kusan bata da iyaka da gidansu, duk sadda ta so shiga ta ke yi, itama ba dai mugunta ba kodayake ba a k'asa ta dauka ba. 
"Ina Babana?" Yanda ta yi tambayar cikin sanyin jiki ne yasa suka ji tausayinta musamman Yaha wacce tasan ko sau daya bai ta6a tambayarta ba, saidai batason ta karyamata zuciya ta yi dan yak'e.
"Babanki yana nan cikin koshin lafiya."
  Har suka k'arasa hirar Ringim sukeyi, Yaha na bata labarin irin abubuwan da suka faru.
    Koda suka isa gidan Amina ce ta karasa da ita wajen Mami don kuwa ita Faruk ne ya tsaidata, duk yanda ta so k'i hakan bai samu ba don Yaha sun ce ta dakata. Sai anan ma Yaha ta ganshi, shakka babu Ummi ta yi katari da babban goro. 
     Can gefe suka tsaya k'asan bishiyar dogon yaro. Haidar da Dakta sun fita kai Abubakar masaukinsu. Ya dubeta fuska ba walwala.
"Shi ne ki ka k'i daukar wayata ko?"
Tana wasa da gyalenta ta ce. "Ka yi hakuri ina cikin mutane ne."
Ya dan ta6e baki.
"Don kina cikin mutane kuma shikenan sai ki kasa amsa wayata Ummi? Kinsan yanda na ji kuwa?"
  Shiru ya biyo baya kafin ta furta kalmar hakuri.
"Da abinda ki ke kwarata kenan, kinsan duk girman laifin mutum matukar zai ban hakuri to nakan hakura, amma idan ya k'ureni za'a ji kanmu fa."
  Murmushi kawai ta yi. Iskar da aka soma mai zafi yasa suka dan rufe idanu.
  "Kwanakin nan ana zafi Alhamdulillah, gwara ruwan ya sauka ko an dan ji sanyi." Fadin Faruk kenan. Ita dai 'Um' kawai tace.
  Saida iskar ya lafa ya dubeta.
"Ko ki tambayi albishir da nace zan miki ko?"
"Ina shirin tambaya ne."
"Aa Ummina banda karya fa, shikenan ma na fasa sai aurenmu ya tashi. Ga wannan."
Ya mik'omata wani k'aramin gida na zobe, ta dubeshi ya dan daga mata gira.
"Kar6i mana, ko na sakamaki?"
Ta girgiza kai sannan ta kar6a.
"Oya bude ki saka na gani."
Ta bude a hankali, wani kyakkyawan zobe ta gani mai kyau ruwan gwal, watakil ma na gwal dinne bata sani ba. Ta sanya a yatsanta na kusa da karamin, ya zauna das sai daukar ido ya ke. Ya zubawa yatsun idanu tamkar ya sumbata ya ke ji, sauke ajiyar zuciya ya yi yana mai dubanta.
"Ya miki kyau sosai."
Ta dan russuna kadan.
"Nagode Yaya Faruk, Allah Ya k'ara arziki."
Har cikin ransa ya ji dadin adduarta. Ya amsa da murmushi. Ganin an soma yayyafi ne yasa dole suka yi sallama ta nufi ciki rike da gidan zoben.
                   ***   ***   ***
  Acan kuwa Yaha na tare da su Hajiya Babba suna magana akan Ummi, Hajja da Mami suna zaune babu damar aibata abin don kuwa Modibbo na zaune a gefe don kusan anan falon ya ke wuni. Hajiya Mama ce ta sanarwa Yaha dukkan abinda ake ciki, Hajja sai kallon banza take watsawa Yaha ganin yanda ta wani washe baki kamar gonar auduga.
  "Daman dole ta yi murna tunda an gama tsafe miki d'a kin kasa ganewa."
Ta yi furucin a hankali cikin harshen fulatanci, babu wanda ya tanka saidai Yaha ta tsargu don ta lura kamar tsohuwar bata farinciki da hakan. 
  Nan dai aka gama tattaunawa Yaha ta tabbatarmusu ba'a yiwa Ummi miji ba, karshe aka tsaida magana inda bayan shawara da Modibbo da kuma Gen. Ahmad (ta waya) cewar Asabar mai zuwa za'a je can Ringim bisa jagorancin Yaha a tsaida magana da mahaifin Ummin sannan a saka rana. Da haka aka rufe tattaunawar, Yaha ta so tafiya anin an soma ruwa suka tsaidata sai ta ci abinci, idan yaso sai su fita tare da su Hajiya Mama. 
    A dakin su Larai Ummi ta zauna tare da Yaha. Yaha na cin abinci ta dubeta.
"Amma sai naga kamar mutanen nan ba suyi marhaba dake ba Ummi, kinga yanda tsohuwar nan ke dubana kuwa?"
  Ta dan yi yak'e ba tace komai ba. Yaha ta kai loma.
"Um, Allah dai Ya fiddamu daga zargin mutane, kada a dauka wani mugun abin muka k'ullo."
Fadin hakan yasa idanun Ummi cika da kwalla, ai hakan ma ake zargi. Ta yi nasarar sharesu bata ko bari Yaha ta lura ba. 
  Saida wajen takwas suka yi shirin tafiya, suma su Ummin gobe da safe zasu wuce Abuja. Ta kar6i lambar Antinta Amina da Yaha don a dazun Faruk ya bata wayarta. Da hawaye ta rabu da Antinnata.
"Ki gaishemin da su Anti Hauwa da Inna." 
Amina ta amsa itama idanunta cike da ruwan kwalla.
"Za su ji Ummi, nasan har ku wuce Ringim ba lallai mu hadu ba, saidai ko waya, ki dage sosai da addua karki gaji, in sha Allahu Allah zai taimakemu."
  Da wannan suka rabu zuciyar kowannensu babu dadi. Itama Mami alokacin suka fice. 
                   ***   ***   ***
  
    DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

89

  Yana zaune yana shan(coffee) alokaci guda kuma ya lula duniyar tunani har Alhaji Kabir na mishi magana sam bai ji ba. Ya dan ta6o shi.
  "Abubakar." Ya dan dubeshi sannan ya sauke ajiyar zuciya.
"Naam Baffa."
"Tunanin me ka ke yi ne har ina magana ba ka ji ba? Me kuma ya faru? Ko akwai wata matsala?"
  Ya girgiza kai.
"Aa, saidai Baffa jiya naga wata yarinya mai kama da Inno sak, na yi mamaki."
    Alhaji Kabir ya dan yi shiru kafin kuma cikin rashin fahimta ya ce.
  "Ikon Allah, watakil kawai kamanni ne. Kasan ana samun haka sosai."
Abubakar ya girgiza kai.
"Wannan kamar har ta so ta 6aci, ba don sanin da na yi cewar Inno bata raye ba da sai na ce itace, anya wannan itama ba daga Gombe ta fito ba?"
  Shi dai Alhaji Kabir abin mamaki kawai ya ke ba shi, wacece wannan da har ya ke had'ata da danginsu na Gombe?
Har suka bar Kano Abubakar bai kara sanyata a idanu ba wanda ba haka yaso ba. Yaso ko hotonta ne ya daukarwa mahaifinnasa ya ganta.
  
                 ***   ***   ***
A satin Ummi ta soma zuwa islamiyya yare da Ikram duk kuwa da cewar Ikram din bata so hakan ba, saidai dadinta daya, ita tana aji na karshe na yan hadda ita kuwa Ummi aji biyu aka sanyata. Ta hadu da wata daliba mai kokari, Husna, wacce a kwana biyu kacal jininsu ya hadu da ita. Ita din diyar wani mai kudi ce don kuwa makarantar ta masu da shi ce, wayayyiya ce amma ba irin wayewar nan ta banza ba. Har musayar lambar waya sukayi. 
    Ranar juma'a Yaha ta dira a Abuja, Hajiya Babba har tasha ta sanya direba ya daukota. 
   Wannan ne zuwanta na farko gidan Hajiya Babba, lallai Mami ba cikin gida take ba, ga inda gida ya ke. Bayan gama cin abincinta ta shiga dakin Ummi inda anan ne zata kwana. Yaha baki ta saki tana mai karewa ko'ina kallo har sadda Ummi ta shigo dakin ta ajiye mata robar ruwa a gefen gado. 
   Ta bi Ummin da kallo.
"Ummi, wannan dukiya har haka?"
Ummi murmushi kawai ta yi ba tare da ta san abin cewa ba. 
   "Kinsan fa ban sanar da Saude batun zuwanki ba don kuwa sam bata kaunar ki je."
  Tasan hakan daman ba wani sabon abu bane, matar da ta yi mata mummunan rik'o ina za ta amince da k'ara sanyata a ido? 
  "Ina Minna ta kirani ta jaddada min cewar kada na yarda ki je Ringim, acewarta ko nawa nake so zata dunga bani cikin albashinki, ita dai fatanta kada ta budi ido ta ganki a Ringim, ta ce na yi mata wannan taimakon har zuwa sadda wani buri nata a kanki zai cika."
  Gaban Ummi ya fad'i, wannan tsana har haka? Yanzu ko me zuwan nata zai haifar? Ta sauke ajiyar zuciya cike da damuwa. 
   "Idan ma wani mugun abun ne ki kwantar da hankalinki, Allah zai kareki."
                ***   ***   ***
                  RINGIM
((Pls kuui manage))
 
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

91

Abubuwa da yawa suka shiga dawo mishi tamkar a mafarki, shi dai yasan sadda aka haifi Ummi da irin kauna da so da ya nunamata har izuwa sadda ya soma tsanarta, karshe kuma yana ji yana gani aka turata aiki ba tare da ya ji ko digon damuwa ba. Daga nan kuwa komai da ya shafi Ummi ya mance, Mariya kadai ya ke yiwa kallon diyarsa.
Me zai cewa Allah ranar da Ya tsaidashi da tambayar amanar da Ya ba shi?
Sai kawai ya soma kuka gami da jawo Ummi jikinsa.
"Ummi ki gafartamin, na yi babban kuskure a rayuwa, na tabbata idan ba ki yafemin ba Allah bazai yafemin ba, na yi watsi da lamuran rayuwarki."
Yana kaiwa nan Yaha kamar jira ta ke ta cafe, tiryan-tiryan ta bada labarin yanda sukayi da Saude akan Ummi

Please Login or Register in order to submit comment