Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuri amma yana nan tafe. Daga haka sukayi sallama. 
  Ummi tayi lamo tana tunane-tunanenta, ko a mafarki idan akace mata  Faruk nada mutunci har haka, toh zata iya musawa idan tayi la'akari da yanayinsa koyaushe cikin daure fuska, sa'a ce ke sanyawa kaga fuskarsa a sake kamar yanda sa'ar ce ta ci ta ganta dazun dauke da murmushi.
   "Mene sunanki na ainahi?"
  Ya watsomata tambayar batare da ya maida hankali ga dubanta ba.
  "Hasiya." Ta fad'a a tsanake kamar ta karawa sunan dadi domin kuwa babu wacce ta fad'omata a rai alokacin sai mahaifiyarta wacce sunanta ne ta ci.
  "Nice name, suna kika ci ne?"
  Ta gyada kai.
"Sunan mamana ce."
  Da mamaki ya dubeta.
"Mamanki tana nan?"
Ummi idanunta suka k'ara ciko da ruwan hawaye, ta k'ara narkar da murya tana son yin kuka.
"A'a ta rasu wajen haihuwata."
Maganar ta dakeshi, ya daure ya hadiye abinda ya ji na tausayinta, saidai duk da hakan saida muryarsa ta kasa 6oyewa.
  "Allah Yayi rahma agareta."
Ta amsa da amin cikin zuciyarta. Duk da wani 6angare na zuciyarsa tana so tasan fin haka game da ita, saidai bai ga wata hujja da zai kare kansa ba idan ta nemi sanin dalilin tambayar duk da baya zaton haka din. 
   Har suka isa babu wanda ya k'ara cewa uffan, hakazalika, kowanne da irin tunanin da yake. A zahiri Ummi ta fi karkata ne ga tuna rayuwarta, babban abin tambayar da bata da amsa shine inda zata ga dangin mahaifiyarta, a 6angare guda kuwa, tana mamakin Faruk da halinsa wanda batasani ba. Bata manta gargadin Ihsan gareta a kwanakin baya.
  'Mutum dai ya tsaya iyakar matsayinsa, ko kusa kada yayi tunanin zai iya da Babban Goro, duk cikinsu babu sa'an aurenki, don haka ki maida maitarki, kurwar kaf dinsu, ta fi karfinki.'
  Wani murmushi mai ciwo ya su6uce mata daidai kuma lokacin da Faruk ya kallota, kawai sai ya tsinci zuciyarsa cikin jin sanyi, ko babu komai bazata fita motarsa da fushinsa ba. 
  Tsayuwar da ta ji yayi ne yasa ta fahimtar sun iso don gaba daya ta luluk'a tunanin dabi'un Ihsan wanda ya sha bamban da na sauran yaran Mami.  Suka dubi juna ido cikin ido, gaba daya sun ji wani iri wanda tsakaninsu babu wanda ya bada tunani na daban. 
  "Saida safe." 
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

   24
  Ya sanya hannu ta 6angarensa ya ciremata (lock). Batare da ta amince sun kara hada idanu ba ta amsa.
  "Nagode, Allah Ya tsare hanya. Don Allah ka sanarwa da Mami na taho gida kada ranta ya 6aci, idan da hali kada ka nuna kai ka kawoni don Allah."
  Yayi shiru yana mamakin dalilinta na fadin hakan,  sai kuma ya ta6e baki ya daga kafada kadan.
  "Nifa ban iya karya ba, ba kuma zan fara saboda ke ba ok? Idan ta tambaya zan fadamata."
  Ya karashe da murmushi yana dubanta, ta kauda kanta. Banda toh babu abinda tace ta sauka. Ta rufe kofar batare da ta kara kalla ba sakamakon duhun gilashin.
  Ya bita da kallo har ta shige ciki, ya numfasa. Mace kam har mace Ummi ta kai. Shine kawai abinda ya ayyana a ransa daga haka ya ja motarsa yabar wajen a miliyan. Mintuna goma bai cika ba ya isa ga wajen party. Ya kuwa iske Mami na nemanta, nan ya sanarmata yanda akayi, yayi kokarin cewa a hanya ya ganta tana kuka tana tafiya ya taimakamata baisan abinda ya faru gareta ba. Mami tayi mamaki, karshe ta yanke da zarar sun koma zata ji ko menene.
  "Mutuminki gashican ya iso."
  Da sauri Iklima ta kai dubanta ga inda kawarta Hassana take mata nuni, wani wawan ajiyar zuciya ta sauke har tana hamdala a fili. Abin ya bawa Hassana dariya, kawai gani tayi Iklima ta ja hannunta.
  "Muje ki rakani na gaisheshi."
  Hassana ta so k'in zuwa don gudun kada ya disgata, saidai dole hakanan ta bi bayanta suka nufi inda yake a tsaye bayan amarya da ango suna 


Haidar ya dubeshi yana mai kai bakinsa saitin kunnensa.
  "Tsaya muyi hoto mana."
Yana murmushi yayi kokarin zillewa, abin saima ya bawa Haidar domin kuwa yafi kowa sanin Faruk bai fiyeson hoto ba. Ya dank'eshi, a hakan ma sunsha hotuna wajen jama'a masu wayoyi, dakyar ya tsaya yana duban Haidar fuskarsa dauke da wani hadadden murmushi, a haka aka daukesu. 
  Cikin masu daukar hoton, har da Iklima wacce gaba daya ta gama narkewa cikin so da kaunar Faruk wanda ya gama tafiya da ruhinta.  Bata bi ta kan Hassana ba ta mara mishi baya da sauri tun baikai ga k'arasawa wajen yan uwansa ba wadanda su yake yiwa kallon abokai domin Faruk ba shi da babban amini ke6antacce da za'a kira nasa akoyaushe. Bazai rasa abokan ba, duk wata shawara acewarsa yayyunsa sun isheshi.
  "Ina wuni Yaya Faruk." Muryar da ya tsinkaya kenan daga gefensa. Ya kai dubansa gareta, take kuma sai ya tsuke fuska tamkar ba shine ke murmushi ba yanzun. Kansa kawai ya gyada sannan yayi gaba. Da sauri ta juya itama tun baikai ga bata kunya ba. Tun kafin ta kai ga Hassana, take watsa mata harara har ta dangana da mazauninta. Alokacin ne ta samu damar yi mata magana.
  "Ai ga irinta, saida nace kada kije amma kika k'i saurarona, yanzun da ya jefeki da kallon banza ai kinji dadi."
  Tana maganar a fusace. Iklima idanunta akan Faruk wanda ke hira abinsa hankali kwance, ta murmusa.
  "Yasan ya had'u ne shiyasa yake shan kamshi ga yanmata. Wallahi ina sonsa fa."
  Hassana ta ta6e baki. "Shi kuma baisan da zamanki ba."
  Sai alokacin ta dubeta tana harara.
"Wai me kikeson ki cemin? Kin manta  alak'armu da shi ne?"
  "Naga Ihsan ma k'arewar alak'a da shi ai." Hassana ta fada gami da jan dogon tsaki sannan ta cigaba da maganarta.
  "Shi namiji idan yaga kin fiye zakemishi rainaki zaiyi wallahi, ki kula dakyau leema, kisan dai dabarar da zakiyi ki shawo kansa, amma idan har zaki cigaba da yi mishi irin wannan shishshigin agaban jama'a, toh fa zaki raina kanki."
  Iklima tayi shiru tana sauraronta, ga dukkan alamu dai maganganun Hassana yana shigarta. Tayi na'am da shawararta na cewa ta dinga yi mishi ladabi a fili da kuma online.(chatting), a sannu idan suka saba sai tayi kokarin shawo kansa.
  Haka aka tashi taron kowa cike da farinciki idan an cire Iklima wacce bataji dadi ko kadan ba na yanda Faruk ya gwatsaleta ba.
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR
   
   25
    
Koda su Mami suka koma gida, ta tuntu6i Ummi akan dalilinta na barin wajen (party), bata 6oyemata yanda sukayi da Ihsan ba, da kukan da Faruk ya ga tana yi ya taimaka ya kawota gida. A take Mami ta nemi Ihsan a waya amma fir ta karyata tace batasan ma da zaman wata Ummi awajen ba. Ranar duka ne kawai Ummi bata ci ba, amman ta sha fad'an Mami sosai, acewarta bazata lamunci a dinga yiwa yaranta karya ba akan abinda bai zama halinsu ba. 
  Haka Ummi tana ji tana gani aka k'aryatata aka bata laifi, dole ta bawa Mami hakuri sannan ta bi umarninta ta chanjawa Fahad kayan bacci ta nemi makwancinta. Bacci gaba daya gagararta yayi don ta kasa tsaida hawayenta, sai wajen asuba ta samu ya dauketa. 
       Washegari suka shirya tafiya Abuja kai amarya. Da yawansu ta mota zasu tafi, ciki harda Mami. Hakan yasa da sassafe ta kammala komai, kasancewar kwana daya zasuyi ta amince Ummi ta zauna agidan tare da su Adnan. Ta mascara mata cewa ta rik'e amanarta. Daga haka sukayi sallama, ita da Ramma na binsu da adduar sauka lafiya. 
   Misalin karfe biyar na yamma, babu kowa a sashen Mami sai Ummi dake kwance a tsakar gida. Fahad da Adnan sun fice yawo, Ihsan kuwa har lokacin bata dawo ba, da alama da ita aka nufi Abuja, Ramma kuwa daman tun tafiyar Mami tana kammala ayyukanta ta bar gidan. 
  Muryar da ta ji tayi sallama ne yasa babu shiri ta mike zaune a matukar razane. 'Hajiya Binta?' Ta fad'a a ranta cike da mamaki. To mene ya kawota sashen Mami alhalin a baya ba shigowa takeyi ba? 
  Fuskar Hajiya Binta a sake  ta k'arasa shigowa ciki tana d'an waige-waige. 
   "A'a Ummi, ba kowa ne sai ke kadai?"
Ummi ta russuna cikin ladabi ta amsa mata.
  "Eh Hajiya. Ina wuni."
Hajiya ta zauna a saman wata kujerar roba cikin karamar murya kamar mai rad'a ta amsa.
"Lafiya lau Ummin Hajiya. Sai kyau kike k'arawa Masha Allah."
  Murmushi ta dan yi mai kama da yak'e domin ba wani sabo tayi da ita ba, banda munanan kalamai da take watsamata aduk haduwarsu, babu abinda ke shiga tsakaninsu. Maganar Hajiya Binta wacce ta k'ara matsowa dab da ita ya katse tunaninta.
  "Ummi ina neman wata alfarma daga gareki, matuk'ar kika amince kika yi yanda na sanyaki, toh ina miki rantsuwa da Allah zakiji dadin rayuwarki. Ina tabbatar miki sai kin samu 'yanci agidannan kamar kowace 'ya matukar kikayi yanda nace."
  Ummi ta ji kanta yayi dumm. Ta rasa gane alkiblar da maganganun Hajiya Binta suka dosa. Ta dubeta duba na neman karin bayani. Hajiya Binta ta kara lek'en bayanta, bata ga wani ko wata dake tahowa ba. Ta fiddo wata bak'ar leda daga zaninta ta bud'eshi gami da nunawa Ummi. Ummi ta zaro ido cikin matukar kad'uwa ganin wani abu wanda aka duk'unkule da farin zare mai yawa wanda har ya zamana baka ganin komenene aciki sai zaren da yayi kamar bal. 
  Ji tayi ta soma gumi cikinta kuwa wani hautsinewa ya yi na ban mamaki. 
   Hajiya Binta wacce gaba daya ta gama kwadaituwa da samun cikar burinta ta cigaba da magana.
  "Wannan kadai zaki ajiye a k'ark'ashin gadon uwardakinki, daga tsakiyar gadon, shikenan kin kammala mini komai. Wallahi Ummi zakiji dadin rayuwa fiye da zatonki. Zaki samu duniya yanda baki ta6a kawowa ba. Za kuma ki jera da yaran gidannan a zuwa makaranta mai tsada, a fannin ci da sha da kuma sutura. Rik'e kiyimin yanda nace."
  Ummi na k'ok 'arin magana ta tsaidata ta hanyar damk'a mata abin a hannunta. Ta jefeta da murmushi.
  "Zan nemeki gobe." Daga haka ta mik'e sai kuma ta dawo baya. Fuskarta a murtuke ta dubeta, duban da ya k'ara hautsinata.
  "Karki soma yunk'urin tonamin asiri, muddin kika soma sai na lahira ya fiki jin dadi. Ki kula." Daga haka ta fice da sauri. A nan kofar shiga ta tarar da aminiyarta ta, Hajiya Luba wacce ke tsayuwar gadi kada wani ya taho ya iskesu.  Tana ganinta cikin rad'a tace.
"Angama?" Hajiya Binta tayi dariya.
"Ta isa daman ta k'i?"
  Sukayi dariya k'asa-k'asa gami da cafkewa sannan suka bar wajen da sauri.
  Ummi ta shiga tsaka mai wuyaaa....!
  
     DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

   26
   Gaba d'aya gigicewa tayi, tayi sauri yarr da kullin a kasa kafin ta cigaba da ambaton Allah a fili. Ita kuwa Hajiya Binta me take nema haka a duniya da har zata iya yiwa wani asiri? Ummi a iyakar tsawon rayuwarta ta tsani mugunta ta tsani mai yinsa. 
   Ta k'ara kallon kullin cikin zubar hawaye, tunanin kada Adnan ya dawo ya isketa da shi yasa ta mike a gaggauce gami da daukarsa da hannun hagu don kuwa tsoro da kyankyaminsa take. Allah Yayi mata tsari da aikata mummunan aiki irin wannan. Shine addu'ar da take ta nanatawa a ranta.  Kai tsaye ta nufi dakinta da shi ta kulle cikin bak'ar leda da zummar washegari idan zata makaranta ta yarr koda acikin kwata ne. 
   Bayan ta adana shi inda babu mai gani tunda ba mai shigowa dakinta, ta fito ta zauna jigum, gaba daya a tsorace take. Kuka kam ta sha, a karshe dai tayita addua akan Allah Ya ku6utar da ita daga sharrin Hajiya Binta. 
  Bayan dawowar su Adnan dole ta saki ranta kada su gane. Ya damkamata karamar robar (ice-cream) da suka siyo, suma suka zauna a falon suna kallo suna shan abinsu hankali kwance. Ita dai sha takeyi amma kokusa kallon baya gabanta, koda ta soma jin dadinsa da zarar ta tuna da Hajiya Binta sai jikinta yayi lakwas. Karshe rufe robar (ice cream) din tayi gami da shigewa daki bayan ta nemi zubomusu abinci sun tabbatar mata sun k'oshi. Daman ta ga alama, kawai dai gudun kada ace tayi laifi ya sanya ta tambaya.
   A ranar Ummi dai bata runtsa ba, gani takeyi kamar wani abin zai sameta asanadin kullin da ke a dakinnata. Bata ta6a fatan ace tana da wayar hannu ba sai a wannan dare, da babu abinda zai hana ta sanarwa Antinta ko don ta bata shawarar yanda zatayi. 
     
     Washegari Adnan suka fice makaranta, ya tabbatarmata su Mami sai wajen yamma zasu dawo. Hakan yasa suna tafiya ta bude dakin Mami don daman mukullin yana hannun Adnan sai a yanzun ya damk'amata. Ta tsaya cak a tsakar dakin tana tuno da mugun aikin da Hajiya Binta ta sanyata. Tausayin Mami ya mamayeta.
  "Baiwar Allah kenan, tana zama da ita da zuciya d'aya, ashe tana da wani mugun kulli dangane da ita." Cewar Ummi a fili don bil hakki tausayin Mami ya gama mamayeta. Haka ta gyaramata ko'ina tsaf ta wanko bandaki ta goge duk inda ya dace sannan ta feshe dakin da turare ta kulle. 
   Tana shirin soma gyaran falon Mamin ne. Ta tsinci sallamar Hajiya Binta. Gaba daya saida ta ji tsayuwa na neman gagararta. Dakyar ta samu nutsuwa bayan karanta addu'o'i. Ta nufi falon tana mai amsawa cikin dakiya. Wani zun6ulelan hijabi ne ajikinta, fuskarta ya nuna bata jima da tashi daga bacci ba. Ta sanya hannunta a k'ugu, fuskarta a murtuke wanda ya rud'a Ummi saidai tayi iyakar kokari bata bari ta fahimta ba. Da sauri ta durkusa.
  "Ina kwana Umma."
Batare da ta amsa ba, ta zarce ga abinda ya kawota.
  "Kinyi aikin da na sakaki?"
  Ummi ta k'ak'alo murmushi.
"Fitowata kenan ma daga aikin Umma, nayi yanda kika umarceni."
  Wani sanyi ya ratsa zuciyar Hajiya Binta don har ga Allah bata yiwa Ummi kallon mak'aryaciya, dari bisa dari ta yarda da cewar ta aikata. 
  "Tabbas kin biyani Ummi, kuma muddin Hak'ata ta cimma ruwa, bazan watsamaki k'asa a ido ba. Abu d'aya nake gargadinki akai, ki kiyaye bakinki. Wallahi Ummi kikayi kuskuren tonan asiri saina k'ullamiki mummunan sharri."
  Daga haka ta fice da sauri. A can kofar da ta raba sashensu da na Hajiya Madina, sukayi kick6us da Ramma. Ta gaisheta tana cike da mamakin ganinta. Hajiya Binta ta amsa cikin basarwa gami da fad'in.
  "Ashe kuma Hajiyar bata dawo ba? Na dauka tana nan na aikomata tallar dogayen riguna."
   Ramma ba don ta gamsu da wannan shirgaggiyar ba, ta amsa da.
  "Ai Hajiya munyi waya sai zuwa yamma tacemin zasu iso."
  "Allah Ya kawosu lafiya."
  Daga haka ta wuce da sauri don ta tabbatar da wuya idan karyarta ta samu shiga. Ummi wacce tub jiyo muryar Ramma ta biyo bayanta a guje cikin kad'uwa, ta ji tattaunawarsu. Tayi saurin komawa. Bayan shigowar Ramma ta hau kwalamata kira da k'arfi, a rud'e ta k'araso. 
   "Baba Ramma ashe kin zo, ina kwana." Cewar Ummi ba a nutse ba. Ramma ta zubamata ido, gaba daya zargi ya d'arsu a ranta. 
  "Lafiya naga Hajiya Binta anan? Ki fadamin gaskiyar abinda ya kawota."
  Ummi wacce ta soma had'a zufa ta bata amsa batare da ta kalleta ba.
  "Um..nima nayi mamaki,  tambayata tayi ko Mami sun dawo nace aa shine ta tafi."
  Ramma ta gama hango rashin gaskiya k'arara a fuskar Ummi, saidai kasancewar tasan k'arya baya daga cikin d'abi'arta yasa nan take ta amince.
  "Toh Allah Ya kyauta, wannan dai salon munafuncine, tana nan ba'a shigo ba sai bayan da ta k'aura. Mutane dai ba tsoron Allah, Allah Yasa ba wani mugun abin ta..."
  Sai kuma ta datse maganar da fad'in.
  "Um, Allah na tuba. Bari na kama abinda zai fishsheni."
  Daga haka ta fice daga falon, Ummi Ta sauke ajiyar zuciya don gaba daya ta gama tsorata. Ita kanta jinta takeyi wata marar gaskiya. 
    

Koda ta fita bata k'arasa makaranta ba har saida ta raba kanta da k'ullinnan ta hanyar wurgashi cikin wani k'aton kwata nesa da gida.

  Ummi na zaune acikin ajinsu da misalin karfe hud'u kowa ya fito don yin alwala da sallah kamar yanda aka saba a makarantar, ajin babu kowa sai ita da wasu yanmata kusan sa'annin juna su uku wadanda suma da alama suna fashin sallar ne. 
  Abin duniya gaba d'aya ya tarar mata, babu abinda take tunani sai Hajiya Binta, mamaki da tsoro lamarin mutane ke k'ara bata, idan mutum yana son kansa da yawa babu abinda ba zai iya aikatawa don samun cikar burikansa ba ashe? Ta tsunduma tsundum cikin wannan tunanin ta tsinkayi muryar d'aya cikin yanmatan nan mai suna, Maijidda tana magana wanda yayi sanadin maida hankalinta garesu.
  "Wallahi ban ga wawuya irin Anti ba a duniya, shiyasa da zarar ta fita nake yanda na so a gidannan, ko jiya da ta ficewarta wurin aikin dare a asibiti, kar kuga tsaleliyar budurwar da Abba ya kawo gidannan, agaban idona suka shiga d'akinsa da ita."
  Ido waje suka dubeta, wata fara mai bille, 'yar siririya, Amina ta soma magana.
  "Ke Jidda! Maimakon ki gayamata?"
Wata uwar harara ta watsamata kafin tace.
  "Wa kike tunanin zai gayamata? Amma wallahi ba ki da wayo, bakisan irin kud'aden da nake samu ta hanyar yin shiru da bakina ba? Ai wallahi da dai nabar samun wadannan kud'ad'en na gwammace nayita rufawa Abba asiri. Ko iyayenmu ban sanarmusu ba ballantana wata suruka. Ke Surayya ai kin ta6a ganin Antin, kinga dai bata rageni da komai ba amma wallahi akan kud'i banga wani abu da zai gagareni aikatawa ba. Wai ma da kikemin wani ihu, ba gwara ni ba akan ke da kike dauka ba'a sani ba?"
  Fad'in haka yasa cikin sauri Amina ta kai dubanta ga Ummi wacce saika rantse hankalinta baya kansu yana ga wani dan littafin addu'o'in dake hannunta. Tana jin sadda Amina ke fad'in.
  "Ummi na jinmu fa."
Surayya da Maijidda suka dara.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  27
   Surayya tace.
  "Itama ai rik'onta akeyi, na tabbatar nata idan an bincika yafi namu bak'i."
  Wannan maganar ya shiga kunnuwanta saidai bata nuna ta ji ba. Suka cigaba da magana. Surayya na fad'in abinda tayi ayau.
  "Ai wallahi kunganni, ko gobe na ziyarci Katsina, sai na k'ara ziyartar Malamin nan, yanzu bakiga yanda nayi mugun raina Saddik'a ba, dad'in zama 'yar aikin budurwa kenan wallahi, agaban mijin saiki rantse ba ni bace mai zugata, idan kin ganmu saikiyi zaton k'awayennan ne, shegiya kuw a duk abinda nace shikenan yayi zaman dirshan a kwakwalwarta. Ko yau da safe saida nabata shawarar ta rage shayar da Khalifa idan ta k'i nononta ya zube."
  Suka tuntsire da dariya.
"Ke Sury, shakka babu kin fimu shu'umanci." Cewar Amina kenan.
   Hirarsu ta katse sa'ilin da d'alibai suka soma dawowa aji, banda 'Innalillahi' babu abinda Ummi ke ayyanawa a ranta, hawaye suka cika idanunta, bata samu nutsuwa ba har saida ta nemi izni wajen Malamarsu da zummar zagayawa ta sha kukanta sannan ta goge fuskarta. Tabbas DAN ADAM nada halaye mabanbanta, yana da wuyar gane hali. Wa zai ga Maijidda, Amina da Surayya ace zasu iya mugun abu kamar haka? Tun zuwanta Kano, jiya da yau ne kad'ai ta fi girgizuwa. Batun Hajiya Binta, da kuma na wadannan bayin Allahn uku. 
  Haka ta koma gida sukuku, ta sha tambaya wajen Ahmad wanda ya kasance babban d'a awajen Ramma kuma mai wayo sosai akan dalilin yin sanyinta saidai babu kwakkwarar amsar da ta iya bashi har suka rabu ta iso gidan. 
   Ta tarar da su Mami sun dawo, ta ji dad'i ainun. Bayan tayi mata sannu ta shige d'aki ta chanja sutura sai bayan isha'i sannan ta fito falon lokacin Mami ta fita gaida Alhaji. Ta wuce zuwa kicin ta dauki abincinta ta zauna agefe tana ci. Daga can saman tebur, Ihsan ce tare da su Adnan, tana ji tana labartawa Adnan had'uwar gidan Intisar da Yaya Haidar, akarshe hotuna ta shiga nunamishi. Zuwa yanzu babu ruwanta da shirgin Ihsan domin ta tsani halayenta, ita kad'ai ta fita zakkah a yaran Mami. 
                        
                   ***  ***  ***
     
   Buguzum-buguzum take tafiya tamkar zata tashi sama, babu ko sallama ta shiga gidan ta hau kwalamata kira.
  "Dije! Dije!!"
Wacce aka kira da Dije ta fito da sauri daga d'aki hannunta rik'e da waya.
  "Zan makivfulashin anjima."
Daga haka ta kashe wayar tana mai watsawa uwarta ta wani kallo kamar mai shirin dukanta. 
   "Menene wai haka Baba?"
  Habiba ta ja hannun 'yarta suka koma d'aka. Cikin sauri ta fiddo da k'ullin magani ta dubeta idanu a waje.   "Kinga Dije wannan, shine warwarar dukkanin matsalolinki, daga gidan Mai Bori nake, ta tabbatar muddin kikayi sha da wankan turaren nan, to fa kin gama samun miji tsayayye a duniya."
   Dija ta yamutsa fuska.
"Karki k'ara kirana da Dije nasha gayamaki nafison Dija, idan bazaki iya fad'a ba ki cemin Khadija."
  Habiba ta washe baki.
  "Allah Ya huci zuciyarki to, don Allah kiyi."
Dija ta kalli k'ullin ta ta6e baki.
"Yanzu idan baki manta ba shekaruna fa ashirin da takwas yanzu, tun inada ashirin kike faman takuramin da shaye-shayen magungunan da basu amfanata da komai, nafi zargin babu abinda suke k'aramin sai bak'in jinin samari. Nidai gaskiya..."
  Tayi saurin toshewa 'yarta ta baki.
"Kul! Kada na k'ara jin kin yiwa kanki mugun fata, wannan bana tantama za'a dace. Ke kad'ai gareni Dije, kinga dole na damu da rashin aurennan naki."
  Dija ta tur6une fuska, ita a yanzu auren ma ya daina damunta tunda tana samun abinda take so hankali kwance. 
   Haka uwar tayita lalla6ata har a k'arshe ta amince zata yi, jin haka ta numfasa gami da washe baki.
  "Yauwa kokefa, tace har ki bushe kada wani ko wata ya ganki, bari na shiga gidan Saude ki rufe k'ofar kada Malam ya dawo."
  Ta amsa sannan uwar ta juya ta shuri takalmanta ta fita, kai tsaye gidan aminiyarta kuma makwafciyarta ta fad'a, gidan da idan baka san shi ba, to fa bazaka ce shine ba saboda gyararrakin da ya samu. 
  A zaune ta isketa a falo tana kallo. Wani gud'a ta saki.
  "Ayyiruri nanaye! Dakyau uwargidan Balarabe, uwa ga Mariya da Atika. Kina sha'aninki fa."
  Suka tuntsire da dariya cike da nishad'i.

  Saude ta bata hannu suka cafke kafin ta k'ara gyara zamanta akan kujerarta wadanda ta siya a sakan tana musu kallon masu kyau adalilin a baya bata mallakesu ba. 
   Habiba ta zauna sharab akan kujera tana k'ara washe hak'ora. 
   "Wallahi duk sadda na ganki kina watayawa bakiji yanda nakejin dad'i a raina ba, kai duniya."
  Wata dariya Saude ta saki.
"Bari kawai Habiba, a duniya banajin inada aminiyar da ta kaiki, karki tona zuciyata kiga tarin kaunar da ke dank'are aciki tamkar wata yar uwata ta jini, ke kin fiyemin dayawa cikin 'yan uwannawa ma wallahi."
  Habiba har lokacin bakinta ya gaza rufuwa. 
  "Burinmu kenan, yanzu don Allah ya kikaga ranar wannan shegiyar? Ai matukar za ki cigaba da bin shawarata za kiyita ganin aiki da cikawa."
  Saude ta lumshe ido ta budesu tsabar dad'in da zantukan Habiba sukayi mata.
  "Tabbas nagani, yanzu fa Balarabe ba shi da kata6us a rayuwa, komai nashi nike iko da shi, hatta da kadarorin da ya gada na iyayensa, yanzu sun dawo mallakina. Bakiga yanda k'aramin albashin wannan Shegiyar na farko ya juyemin zuwa babban jari na siye da siyarwa ba? Ai har abada ke mai kaunata ce Habiba, shiyasa na damu da damuwarki."
   
  "Ga kuma k'iyayyar da kika jazamata a dangin Mahaifiyartata." Cewar Habiba kenan suka feshe da dariya har suna fidda ruwan hawaye. Saude ta nunata da yatsa.
  "Maakira."
"Ban kaiki ba." Habiba ta amsa mata.

  Sai kuma Saude ta koma kalar damuwa.
  "Yanzu Habiba babbar damuwata bai wuce na ranar da Boka yace mu kiyayi zuwansa ba, ranar da Balarabe zaiyi tozali da Ummi."
  Habiba ta harareta.
"Wa zai bar wannan ranar ta zo aka gayamaki? Har abada bazamu kyale ba, wannan bari sai Yaha ta dawo daga Kaduna, ita zatasan tuggun da zata shirya duk lokacin da bukatar zuwa ganin gidan Ummin ya taso."
  Saude ta jinjina kai cike da gamsuwa daga haka suka rufe babin Ummi suka koma na Dija inda take bata labarin maganin da ta samo mata.
  "Hakan ma yayi, Allah dai Yasa a dace. Ni kaina rashin namiji tsayayye ga Dije yana ta6an zuciya. Allah Ya had'ata da mai mota."
  Habiba ta dara cike da jin dadin wannan kyakkyawar addu'ar da ya fito daga  bakin aminiyar kwarai. 
 

Please Login or Register in order to submit comment