Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bayan isha'i sannan suka bar gidan zuwa gidansu. Nan kuwa aka shiga rainon ciki babu wasa, yarinya karama aka kawomata, batafi shekaru goma sha hudu ba. Farkon kawota Ummi idanu ta zubamata tana kallonta cike da tausayawa sannan ta dubi wacce ke tare da ita wacce aka kira da mahaifiyarta da ko kusa bata ga kama ba.
   "Yanzu Baba wannan aiki zata dunga yi?"
  "Eh, aiki kowanne da ki ke so ki sanyata, babu wanda ba zata iya yi gareki ba."
  Ta k'ara duban yarinyar wacce ta yi wani firi-firi da idanu. Tausayinta ya kamata. 
  "Shikenan."
Jin haka matar ta hau washe baki tana gyara mayafi zata mike.
"To bari na koma tunda naga gidan, ke kuma Batula ki kula, kada inji kar in soma gani kin sa6awa uwar dakinki kinji ko? Hajiya don Allah ki dunga kula yarinyar akwai shegen munafunci."
  Ummi da ke jin kamar ta makureta ta ce.
"Wane irin munafunci kuma?"
  "Um, kada ta dunga yi miki la6e wai, to shikenan ai, sai anjima, Allah Ya kara arziki."
Ta karashe cikin basar da wancan maganar. Ummi ta bata dubu biyu ta hau mota. Nan ta hau zuba godiya ta fice. 
  Ta maida hankali ga yarinyar da aka kira da Batula.
  "Sannu Batula, inaso ki saki jiki da ni, ki rikeni tamkar yayarki, ni bazan cutar da ke ba, zan kuma rikeki bisa amana kinji ko?"
Cikin mamaki mai tsanani da rashin gaskatawa ta gyada kai don gani ta ke kamar wani salo ne na cutarwa, gida na uku kenan da aka kawota, wadancan biyun duk guduwa ta yi saboda matsi da takura.
   "Fadamin gaskiya Batul, mene alak'arki da wannan matar? Dagaske itace ta haifeki?"
Ta girgiza kai cikin raunin zuciya kiris take jira ta fashe da kuka.
"A'a, kanwar mamana ce uwa daya uba daya da ta rasu."
  Runtse idanu Ummi ta yi ranta na suya.
  "Meyasa ta ke kawo ki aikatau?"
"Babana ne ya aureta bayan rasuwar Mamana, ba da son ransa ta ke kawoni gidan aiki ba, ko yau da zamu taho da kuka muka rabu da shi. Kullum saita dakeni, komai ni nake yi mata."
  Hawaye Ummi ta shiga fitarwa, DAN ADAM kenan, ace 'yar yayarki ki ke yiwa rikon sakainar kashi? Duniya abin tsoro.
   Ummi ta tabbatar mata zata riketa bisa amana, ta bata kyakkyawan muhalli ta sanyata a makaranta. Ita da kanta ta wankemata kanta bayan ta tsefemata kitso, suna yi suna hira Batul na kara bata labarin kauyensu Maraba. 
   Cikin kayanta ta dauko wanda ya yi mata kadan ta bata ta sanya kasancewar yarinyar akwai tsawo nan suka zauna das a jikinta. 
   Koda Faruk ya dawo, ya yi mamaki, bai gane ko wacece ba ganin tana zaune a kasa suna hira da Ummi suna dariya. Batul ta gaisheshi ta yi ciki, ya zauna yana duban Ummi wacce ta tashi ta tarbeshi.
"Ummina wacece wannan?"
Da murmushi ta amsa.
"Itace wacce Hajiya ta turo zata tayani aikace-aikace."
Ya jinjina kai.
"Naga kamar wata kanwarki kunata hira ai."
Murmushin ta kara yi.
"Kanwartawa ce ma. Tausayi take ban."
Nan ta labarta mishi labarinta, shi kansa ya yi mamaki.
"Allah kenan, DAN ADAM babu mai iya masa sai Allahn da Ya halicceshi, Allah Ya datar da mu."
"Amin."

Tun daga wannan ranar Ummi ta riki Batul bisa amana, har makaranta an sanyata na Arabi. 
   Haka har azumi ya zo, nan ma komai tare sukeyi, cikin azumin ne kuma Intisar ta haihu diyarta mace. Kowa ya yi murna da hakan, ranar suna aka sanya sunan Hajiya Mama, wato Sadiya. Hajiya Mama ta ji dadin wannan karar da sukayi gareta. 
   Anci suna an kare lafiya kowa na yaba yanda Faruk ke nan nan da Ummi ko gaban mutane ne ba ya iya 6oye son da ya ke mata. 
  A ranar sunan ma ganin yanda Ummi ke yiwa Batul saida su Jidda suka tofa.
"Wai wannan inace 'yar aikinki ce ki ke mata haka?"
  Murmushi ta yi.
"Ni ina mata kallon mutum mai daraja."
"Don kema a baya yar aikin ce ko?"
Cewar Fadila.
Abin ya ta6a zuciyar Intisar da su Ikram, Ummi kuwa ko a jikinta ta soma bata amsa. 
  
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  126

"Ko bayan wannan, yan aiki mutane ne kamar kowa, hakazalika suma suna da nasu daraja da k'imar, da yawa cikinsu kan fito aiki bisa kaddara ba da son zukatansu ba, wasu anfi karfinsu ne wasu kuwa halin rayuwa ce. Ni Ummi bana fatan ranar da zata zo na wulakanta wani DAN ADAM a duniya, da yawa suna kuskure, sukan dauki kansu wasu har su dunga wulakanta masu tayasu hidima don kawai tak'amarsu biyansu su ke yi, sai yaronki karami ya budi baki ya zagi dattijuwar da ko ke ta haifa amman ba zaki kwa6eshi ba kasancewar kina mata kallon yar aikinki, sai ya zagi direba ko maigadinki duk ba za ki ji ko darr ba, asalima har ya kai ga kin shigarwa danki don kawai kina yi musu kallon kaskantu, watakil kuma sun fiki matsayi a wajen Allah. Ba ma akan masu aiki ba, kowaye kada ka wulakantashi don shakka babu bakasan mai yi maka rana ba, ko ya ya, bana mance halacci."
    Fadila da Jidda suka k'ulu da maganganun Ummi, musamman Jidda wacce ke ji kamar da ita ta ke, basu kadai ba har da wasu cikin gayyar sunan wadanda sun kasance suma sukan dauki yan aiki ba komai ba face kaskantu maganar Ummi ta shigesu, nan kuma wasu suka hau fadin ai yan aikin ma suna suka tara akwai mugaye. Ita kuwa Fadila bata kara cewa uffan ba don ta cika da mamakin yanda har Ummi ta yi kaurin wuyar mayarmata da martani.
  "Ku bar ganinta haka, yar aiki ce a baya shiyasa ta fiye wannan zakalkalewar, ai duk inda mutum wanda bai saba da arziki ba ya ke to fa sai kun gani ko a jikinsa ko furucinsa." Cewar Jidda a fusace.
Ummi ta dubeta, kamar ta ce wani abu sai kuma ta hadiye kawai tana murmushi.
"Kai don Allah Anti Jidda." Cewar Intisar kenan, Jidda ta watsamata mugun kallo.
"Na ambaci sunanki?"
  Ta rausaya kai.
"Ko ba don wani abu, ku yi duba fa da cewar cikin azumi ake..."
  "Please ya isheni, wani abin nace?" Jin haka Intisar ta ja bakinta kawai.
Wata hamshakiyar mace da ta hade cikin wani tsadadden leshi ta tofa.
"Kwarai Jidda suna haka, don wallahi wata yar aiki da kawata Mariya Sadik ta ta6a yi, ai kinsanta, yarinyar a dakin mijin ta kamata. Ai babu butulu kamar dan aiki saidai mata mu kiyaye."
Nan kuma babin ya koma hirar yan aiki, Ummi ganin abin nasu kamar da biyu ne, yasa ta mikewa ta bar dakin zuwa falo, Intisar da Baraka suka biyo bayanta har Ikram don abin ya 6ata ransu suma. Ta nunamusu ba komai ganin yanda suka damu. Ita kuwa damuwarsu akai ma kadai ta sanya komai gogewa a zuciyarta.

   Sai Magriba Faruk ya zo daukarta, anan ya sha ruwa da su Haidar hakanan suma nan ciki suka sha ruwa sannan  ya shigo ya ga bebi, anan ne Fadila da Jidda suka kai mishi k'arar Ummi akan ya ja mata kunne. Ya cigaba da danne wayarsa yana yiwa yarinya hoto, gefensa Haidar ne zaune sai Ridwan wanda shima bai jima da zuwa ba. 
  "Wai muna magana ka maidamu wasu shashashai." Cewar Jidda mai saurin fusata. 
"Wai meyafaru? Me Ummin ta yi muku?"
Cewar Dakta yana duban Jidda. Jidda ta yi kwafa. 
  "Mene idan ba rashin kunya ba har tana kiranmu masu raina mutane. Yaushe kan mage ya waye da har raini zai shiga tsakaninmu?"
  Faruk ya bar abinda ya ke ya dubi Jidda ransa a 6ace kamar ya yi magana saidai shigowar Ummi da Intisar falon Haidar ya katseshi, sanye ta ke cikin wani leshi bak'i mai adon orange flowers, sai mayafinta (orange) da ta yafa, hakanan jakarta da takalminta marar tudu. Idanunta akansa suka soma sauka. 
  Wani sassanyar murmushi suka sakarwa juna kafin ta karaso ciki ta gaida Angon karni da Dakta. 
   Faruk ya mik'awa Dakta bebin.
"Bari mu wuce."
  "Ai daman fuskar da ta samu wajenka ne yasa ta ke..."
  "Ya isa! Haba!" Cewar Ridwan ga Jidda wacce ke zak'alk'alewa. 
"A'a Dakta, babu batun ya isa fa, magana ta gaskiya."  Cewar Fadila tana taunar cingam da kallon banza. 
  "Ummi me ya hadaki da yan uwanki?" Cewar Dakta kenan, Faruk na tsaye hannuwa ciki aljihu kawai yana kallonsu. 
   Ta dan murmusa don ita bata ga abin daukar zafi ba.
"Ba abinda ya hadamu."
  "Karya ki ke yi uwar kissa." Cewar Fadila. 
  "Ya isa, Intisar me ya hadasu ne?" Cewar Dakta. 
Tiryan-tiryan ta fadi duk yanda aka yi, Faruk ransa ya yi mugun 6aci ya soma magana.
"Ku rike girmanku, ina girmamaku, kada ku janyo abinda zaisa nabar ganin girmanku. Duk wacce ta kara cin zarafin matata bazan lamunta ba, ko wacece cikinku komin girma da kimarta da nake gani zan yi watsi da shi wallahi!"
   Jidda da Fadila ba bakin magana, shiru sukayi sai faman harararsa sukeyi amma ba bakin magana, ko babu komai yana da kwarjini. 
  Haidar ya dubeshi.
"Ka yi hakuri mana. Gaskiya ba ku kyauta ba Maman Ma'aruf,  kune masu laifi ba Ummi ba, sai ku duba matsayinta a yanzu a Family namu, ku dunga sakaya bakinku."
  Shima Dakta cikin tsananin 6acin rai ya hau zazzagawa matarsa fad'a, Ummi dai ganin mijinta ya nufi hanyar fita, itama ta yi musu sallama ta bi bayansa. 
   A mota ta sameshi zaune yana jiranta, ta shiga gami da dubansa, idanunsa sun kada bai ko dubeta ba ya figi motar a guje, ganin Batul yasa ta yin shiru ba don taso ba, duk da haka saida ta mishi magana.
"Don Allah ka rage gudu."
Ta fada gami da dafa hannunsa dake rike da sitiyari. Ya lumshe idanu yana mai jin zafin abinda ya faru, ganin ta damu yasa shi sassauta gudu har dai suka isa gida, Batul ta yi shiru tana mai tausayawa uwar dakinta don kuwa ta ji kadan cikin abinda ya faru.
    Koda suka isa, dakinta ta nufa. Ta cire mayafi kenan ta isa gaban madubi da zummar cire dan kunne da sark'a ya shigo, ta dubeshi ta madubi suka hada ido.  Murmushi ta sakarmishi a kokarinta na 6oye damuwarta. Karasowa ya yi da sassarfa ya rungumeta ta baya yana sauke ajiyar zuciya idanunsa a runtse. 
  "I'm sorry." Ya fada a hankali, ta lumshe idanu, sai lokacin zuciyarta ta raunana, ta ji kamar ta zubar da hawaye saboda tsananin farinciki na samun miji kamar Faruk mai so da kaunarta. 
   Ta juyo ta dago fuskarsa gami da girgiza kai yayinda hawayen da ta danne suka shatato. 
   "Haba FAR HAS, don Allah ka daina  inajin wani iri wallahi."
Ta rungumeshi tana hawaye yayinda lokaci guda ta ke murmushi mai bayyana hakora na farinciki. 
  "Ko babu komai wannan kaunar da ka ke yimin ta zarce komai a wurina, ta isa wankemin dukkan wani 6acin rai dake zuciyata. Wallahi na yafemusu bazan kuma rikesu da hakan ba, DAN ADAM ajizi ne."
  Ya dago kanta yana murmushi gami da share mata fuska. 
"Shiyasa nake kara sonki Ummina, halayenki sunfi komai burgeni. Na damu ne don nasan koda ya miki ciwo ba za ki bari na fahimta ba, cin zarafi ne abinda suka yi gareki wanda wallahi Allah idan suka ce haka za su dunga yi gareki bazan lamunta ba, zan jure komai idan ni ka yiwa amman banda abinda ya shafi lamuranki. Kema kin sani ko?"
   Tun soma maganarsa ta zubamishi idanu tana murmushi gami da jin tamkar ta hadiyeshi don so, ya hure mata idanu hakan ya basu dariya.
"Eh mana naga kamar mai shirin hadiyeni, wannan kallo haka?"
Ta bugi kirjinsa tana kukan shagwa6a.
"Kai don Allah."
Ya ja karan hancinta yana dariya kafin ya taimakamata da abinda ta soma kokarin yi.
     
  Su Jidda daidai ga Hajiya saida ta nunamusu rashin dacewar abinda su ka yi, hakuri suka bawa Hajiyar kasancewa suna ganin girmanta ainun don bata kasance cikin surukai masu sanya idanu kan abinda ya shafi zamantakewar yaransu ba, ta kama girmanta hakanan bata daure musu fuska. 
   Bayan wucewar watan azumi aka gabatar da karamar sallah. Ko ranar da suka hadu da sallah a gidan Hajiya banda gaisuwa babu abinda ya hadasu duk kuwa da cewa basu bita da kallon banza ba. 
    Nan kuma ta soma shirin zuwa Kano halartar bikin Amina wanda dakyar Faruk ya aminta ganin tana fama da jikinta itama. Ko su Ikram sun zo zuwa saidai makaranta, itama Baraka na fama da ciki dan wata biyar babu damar zuwa. Da kansa ya kaita, kai tsaye gidan Mami ta soma zuwa inda zata yi kwanaki uku sannan ta wuce gidan Hajiya Mama har zuwa gama biki. Babu tarbar arziki daga Ihsan sai dai ta samu sosai daga Mami da sauran mutan gidan wanda yanzu suke zaman aminci. 
    Mami sai nan nan ta ke yi da ita, abin ya sanyata farinciki sosai. Ihsan kuwa kallo bata isheta ba, sai idan ita ta gaisheta ko ta yi mata magana sannan zata tankamata a dakile kamar bata so. Ga shi kuma daki daya suke kwana, wannan abin na bawa Ihsan haushi don dai ba yanda ta iya ne.
  Yau Ummi na kwance saman gadon Fahad wanda yanzun ya ke kwana dakin Adnan, tana tunanin yanda ita ke gyarashi a baya, lokacin sha dayan dare bata jima da gama waya da rabin ranta ba inda ya ke fadamata tsananin kewarta da ya yi. Ihsan ta shigo dakin daga falo, jin haka yasa ta yin makwas tamkar mai bacci. Itama duk a zatonta bacci ta ke yi, hakan yasa ta saka waya a handsfree tana amsawa.  Ita da Abubakar ne wanda rikici ne zalla.
  "Kasan ina sonka shiyasa, kuma kasan bazan iya rabuwa da kaunarka ba amma a yanda na ke jin labarin irin yanmatanka da tuni na yi watsi da lamuranka."
  Ummi ta yi shiru jin amsar Abubakar wanda ta ke mamakin inda ya bar matarsa a wannan lokaci.
"Ki kara hakuri da halina, ni nasan ina da son mata, ki yarda kawai wannan kaddar..."
"Kada ka karasa, wannan son zuciyarka ne. Daga waccan yarinyar ta sanka, sai waccan ta dora hotanka a dp dinta, na soma gajiya Abubakar, kishi na neman fasamin zuciyata."
Kawai sai ta sanya kuka, ya rude yana faman kiran sunanta da magiya kan ta yi hakuri, saidai ina, tuni ta katse kiran da ta ga bai bar kira ba, kawai sai ta kashe wayar gaba daya. 
Ta jima tana kuka kafin ta kwanta cike da tausayawa rayuwarta, yanzu idan suka yi auren haka zata dunga fama da shi? 
  Ummi ta ji babu dadi kwarai, tana ganin Abubakar kamar bazai aikata irin haka ba, ashe kusan jirgi daya ya kwasosu da Kb dan uwan su Faruk, koda bikinsu bata ganshi ba ta ji ance yana Ghana karo karatu. Ta tausayawa Ihsan ainun, ta dan juya ta dubi gadonta, ta bata baya saidai ta tabbatar bacci ya kwasheta, juyar da kanta ta yi gami da numfasawa.
'Rayuwa kenan, kowa da kalar jarabtar da Ubangiji zai mishi, Allah Yasa mu dace, amin.' Ta fadi a zuciyarta kafin ta yi adduoi ta kwanta itama.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
  
  127

Kwananta uku gidan Mami har ankon bikin Amina, Mami ce ta bada a dinkamata. Har ta cika kwanakinta babu wata jituwa tsakaninta da Ihsan duk da ita Ummin bata dauki gaba da ita ba don duk wayewar gari sai ta gaisheta matsayin yar uwarta musulma, a dakile Ihsan ke amsawa. 
  Saida Mami ta soma biyawa da ita wajensu Hajja suka gaisa, har Hajja ta matsa akan sai ta kwana, dole ta barta anan ta yi musu kwana daya daman acewar Mamin, ya dace ta kwanarmusu, a wannan kwanan saida Hajja ta kara neman afuwar Ummi don shakka babu ta ji kunya musamman jin cewa Ummin na dauke da juna biyu, tabbas idan Rabo Ya Rantse to duk kiyayyarka da auren sai an yishi. 
    Ummi ta ji dadi ta nunamata babu komai, sun sha hira kwarai har da dariya da su Modibbo wanda ke jikinsa ya matsa mishi a yan kwanakin, washegari ta wuce gidan Hajiya Mama.  
  Nan ma ta ga kulawa da tarba mai kyau daga iyalan Hajiya Mama har ita kanta. Su Maryam kamar su hadiyeta.
  Amina Amarya ta yi kyau ta gyaru tsaf, anan gidan zaayi yinin biki, kwarai Hajiya Mama ta yi musu kara. Acan gidan Innar Amina, yan uwan babansu ne na Nijar da na Innarsu anan Kano suka cika gidan. Amina ta sha mamaki jin cewa Malam Balarabe da kaninsa Baffa zasu zo daurin aurenta, ta hadata da Dada ta waya inda ta bata hakuri gami da nunamata ta so zuwa saidai bata samu dama ba, Amina ta nuna babu komai. 
    Da dare suna zaune a dakin su Maryam gaba daya suna hira da dariya, wayar Maryam ta yi k'ara, ta mike da sauri ta fita. 
  "Mene na gudun? Ai munsan mai kiran, Adnan ne."
   Cewar Rukayya cikin daga murya. Amina da Ummi suka dara. Amina ta cafe.
"Kai ke kuma ba'a sirri dake." 
  Dariya Rukayya ta yi.
"Ai naga sai wani 6oye-6oye sukeyi kamar bamusan komai ba, gwara mu nunamusu mun d'agosu."
  Ummi da mamaki ta ce. "Wai don Allah soyayya su ke yi?"
"Ba ki da labari? Gaskiya Amina kinci amanar kauna da ba ki fesamata ba, ai kullum suna mak'ale da juna ta waya duk da wani 6oye-6oyen da sukeyi munsan komai, daidai da Hajiya Mama ta sani."
  Ummi fara'arta ta karu.
"Kai na ji dadi wallahi, Yaya Adnan ya yi dace kam, Maryam ba ruwanta halayenta na burgeni. Sun dace wallahi."
"Karshe ma." Cewar Rukayya daidai lokacin da Maryam ta shigo ta mikawa Ummi wayar.
"Ga Yaya Adnan ku gaisa."
Ta kar6a tana tsuke baki. Ta yi sallama ya amsa gami da fadin.
"Allah Ya kiyayemana ke ranki ya dad'e."
   Ta hadiye dariyarta.
"Ai ni na yi fushi Yaya Adnan, ka daina nemana kuma ko na kira layinka yanzu ba ya shiga."
"Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun! Na ji kunya biyu. Na farko kirana da Yaya Adnan da ki ka yi, na biyun kuma, kiran da ban yi miki da sabon layina ba kasancewar wancan ya fad'i sai na barshi. Ki yi hakuri Ranki ya dade matar bestie."
  Sukayi dariya a tare, ta girgiza kai.
"Har abada, Yayana ne kai wallahi. To na hakura, ya fama da biro da takarda?"
  "Gashinan sai kuyita tayamu da addua. Kinga surukarki ko? Ta yi ko akwai gyara?"
Ta daga idanu ta dubi Maryam da su Rukayya ke tsokana ta yi dariya.
"Ta yi 100%."
Ya yi dariya cike da mamakin yanda tasan wani 100% domin ko kusa ba shi da labarin ana mata darussa. Saidai kuma bazai iya tambayarta ba.
   "Yauwa Ranki ya dade, ai da kince akwai matsala tuni zan dakata."
"Wace ni da fadin haka?"
Suka dara kafin su yi sallama.

  An soma bikin Amina lafiya, ana gobe daurin aure Malam Balarabe suka zo, sun sha hira da diyarsa har ya rasa inda zai sakata don tsabar farinciki. Ita ta yi musu jagora har wajen Inna don yi mata fatan alheri, wani abu ya darsu a zukatan tsoffin sadda suka yi arba da juna. Bayan an daura auren ne Malam Balarabe ya kasa jurewa har saida ya sanarwa Baffa kaninsa don daman ya samun labarin cewa yanzu Inna bata da aure, hakanan yana iya cewa tun bayan Hasiya babu wacce ya kara gani ya ji yana so ya karashe rayuwarsa da ita matsayin mata kamar Inna Bilkisu. Baffa ya ji dadi kwarai kuma zai so hakan. Abinka da batun manya nan suka tuntu6i babban Yayan Bilkisu, Mahmuda, nan ya nunamusu jin dadinsa a fili don kwarai ba ya son zaman kanwartasa haka babu aure duk da cewa ta aurar da yara biyu Fiddausi da Hauwa, sai Amina ta uku, ga kuma autanta Ahmad mai shekaru goma sha daya a yanzu, ya yi musu alk'awarin tuntu6ar Inna Bilkisu. A karshe sukayi musayar lambobin waya sannan a karshe sukayi sallama da kowa suka tafi, Ummi har hawaye ta yi don kewa, shi kuwa babanta dadin yanayin da ya ganta ya ji don ta yi k'iba ta kara kyau. 
   Inna ta ji lamarin banbarakwai duk kuwa da cewa a ganin farko da ta yiwa Malam Balarabe ya kwantamata, ba musu ta amince da hakan. Nan ya kira ya shaidamusu, basu yi wata wata ba suka sanarwa iyayensu, Malam ya ji dadi haka ma Dada wacce ke tausayawa dan nata. Aka tsaida magana nan da sati biyu za'a je a daura aure. 
  Su Anti Hauwa sun ji abin banbarakwai, wai Innarsu aure. Tun basu ji ko waye mijin ba suka nuna rashin goyon bayansu, acewarsu da shekarunta na arba'in da takwas me ya ragemata banda ibada? A bakin matar Kawunnasu suka ji waye manemin auren, hankalinsu ya kwanta suka ji dadi, kusan Amina ta fisu jin dadin lamarin don a take ta bugawa Ummi wacce ke shirin komawa Abuja.
    "Albishirinki." Ummi ta ware ido.
"Goro fari k'al Antina."
  "Inna zata zama matar Babanmu."
Cikin rashin fahimta ta ce.
"Anti inace kin cemin Baba ya rasu."
Ta ja tsaki.
"Dallah can, babanmu fa na Gombe."
Daskarewa ta yi a tsaye ta bar ninke kayan. Ita abin kamar mafarki haka ta jishi. 
"Ke ya ki ka yi shiru, wallahi dagaske ne." Tiryan-tiryan ta labartamata abinda ta ji. Hawaye kawai Ummi ta shiga fitarwa tana kara jin kaunar Amina da yan uwanta. Banda hamdala babu abinda ta dunga nanatawa a fili. 
   Bayan komawarta Abuja ta sanarwa Faruk wanda shima ya ji dadi ainun, ya sanyawa lamarin albarka. Kowa ya ji sai ya sanya albarka ciki. Koda ta kira mahaifinta, dariya kawai ya yi ya ce.
"Lamarin Allah kenan Hasiya, a tayamu addua."
Farinciki fal cikin ranta haka suka sha hira suka yi sallama.
                ***    ***    ***
        BAYAN WATANNI BIYAR
Ayau ake bikin yaye su Ikram daga sakandire, acan Kano ma su Ihsan na nasu shagalin don lokaci guda aka yi bikin yayesu. 
   Duk yayyun Ikram sun je mata banda Baraka dake wankan jego ta haifi danta namiji wanda ya ci sunan mahaifin Mijinta suke kiransa da Abulkhair. Ummi ma da cikinta dan wata bakwai katon gaske haka ta zo. Fuskarta duk ta chanja, tana sanye da wata tsadaddiyar abaya Faruk na rike da hannunta. 
    Ikram duk bata tare da walwala sai lek'e-lek'en wuya ta ke faman yi. 
"Wai me ki ke nema haka?" Cewar Fadila wacce ta kasa shiru. Ikram ta dubeta, kafin ta yi magana suka ji sallama a gefensu duk suka waiga, mamaki karara ya bayyana a fuskokinsu. 
  Yana sanye da doguwar riga da wando na shadda dark green wacce ta sha aiki, ya dora hula mai fari da koren din sak'a, ya yi kyau kuma ta haskakashi ainun. Sai murmushi ya ke faman dokawa.
  "Yaya Gidado?" Ummi ta furta da tsantsar mamaki kafin kuma ta saki fara'a sosai. 
Ya bita da murmushi kafin ya karasa ya soma mikawa Mazajen Hajiya Babba hannu suna gaisawa. Suma sun saki fuskokinsu, Fadila da Jidda suka yi turus suna kallon ikon Allah, sun kuwa gane waye shi amman idan ka ganshi saika rantse ba daga kauyen Jar Kwami ya fito ba tsabar iya daukar wanka. 
  Ikram ta kasa rufe baki, zuciyarta na kara nutsawa cikin kogin so da kaunarsa, babban abinda yasa ta ke kwadayi da mafarkin zuwan wannan ranar kenan don kuwa ya bata tabbacin zai zo mata da kyakkyawan albishir duk ranar da ta yi Candy. Toh yau ga ranar ta zo. 
    "Ashe kana tafe ba ka sanarmana ba mu yi maka kyakkawan tarba?"
  Cewar Faruk cikin sakin fuska. Gidado ya danyi dariya.
"A yi hakuri surukina, ai gani yanzu ma bata 6aci ba."
  "Lallai kam, saidai kamar zuwan ba namu bane na kanwarmu ne ko?." Cewar Haidar wanda ya riga yasan dawan garin daga Intisar., ya fada yana duban Ikram.
   Suka yi dariya, kunya ta kama Ikram.
"Eh to, kusan hakan."
  Cewar Gidado, shi kuwa babban Yaya da Ridwan mamaki sukayi don basu zata ba , hakanan Faruk shi kansa bai ji daga matarsa ba. Ya dan matse hannunta ta yi karamin kara. 
  "Shine ko ki gayamin?"
Ta waro ido.
"Babu wani abu fa tsakaninsu."
Murmushi kawai ya yi.
  Har aka tashi taron Gidado bai samu ke6ewa da Ikram ba sai bayan sun koma gida, bayan ya gaisa da su Hajiya suka ke6e da ita a dakin bak'i. 
Ya fiddo wani akwati daga aljihunsa ya mik'amata.
"Ga kyautar da na zo miki da ita, ki yi hakuri babu yawa.". Ta kar6a tana washe baki.
"A wajenka ne babu yawa."
Sukayi dariya. 
  "Ba za ki bini bashin zance ba Ikram, yau zan sanarmiki abinda ban ta6a sanarmiki ba. Haka kuma zan cika alkawarin da na daukar miki."
  Ta lumshe idanu ta budesu.
"Ina jinka Yayana."
  Shiru

Please Login or Register in order to submit comment