Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ke kokarin sanya kansa a waje ya fice. Sanye ya ke da bak'ar t-shirt bodyhug wanda ya taimaka wajen fiddo da kyakkawar halittar da Allah Ya yiwa jikinsa na kirar karfi, sai farin wandon jeans da ya sanya, sumarsa kwance luf, bak'ak'irin kamar mai sanya (hair dye). Ta juyo ba ta ce uffan ba ta nufi ciki, tana jinsu suna kod'a mijinta saidai bata da bakin magana. 
  Gaba daya suka biyota ajin. Husna ke tambayarta game da Gombe, su kuwa tambaya suke akan Faruk, duk sun isheta, Allah Ya taimaketa Malam ya shigo ajin, wannan yasa duk aka nutsu. 
  Ranta a matukar 6ace ya ke, har aka fito sallah basu bar bibiyatar da son jin ko wanene ba, tana tsaye bakin famfo tana daure dankwalinta, jiran Husna ta ke yi ta idar su bar wajen, idanunta ya kai ga Ikram suna nufo famfon ita da tawagarta. Ba shiri ta ja hijabinta ta rufe fuskar gami da basu baya, saidai duk da hakan bata tsira ba Ikram ta ganta, saidai bata ko nuna tasan da itan ba bisa gargadin Haidar wanda ya gargadeta sosai akanta. Dogon tsaki ta ja kawai wanda Ummin ta ji, daidai lokacin ne kuma Husna ta kammala ta dubeta.
"Mu tafi."
Suka bar wajen zuwa masallaci. Zuciyar Ummi ko kadan babu dadi har aka tashesu, direba ya dauketa. 
   A farfajiyar gidan suan fakawa ta fito, idanunta ya kai ga baranda Gogannata. Yana makale da earpiece a kunne, hannunsa na hagu lemun gwangwani ne da ya ke kur6a, sai sketct-board a gabansa yana zane. Ta dubeshi sosai, ganin zai kallota ne yasa ta saurin k'asa da kanta gami da soma tafiya zuwa ciki, ta goge kwallar da ta tahomata.  Wannan cutarwa ne, ba zata jure wannan fad'an nasu ba. Ba haka ya sabarmata ba a mu'amalarsu. 
    Bayan sun gaisa da Hajiya, ta shiga ciki ta watsa ruwa ta sauya kaya zuwa riga da siket na Atamfa mai fari da (orange), bata daure dankwalin ba saidai kawai rufashi da ta yi. Fita ta yi zuwa kicin wajen Binta. Anan ta zauna, Binta ta yi akan ta ci abinci saidai ta ce ita sam bata jin yunwa duk kuwa da irin yanda ta ke jin yunwa na addabarta saidai damuwarta na rashin ganin fuskar Faruk yafi komai damunta.  Tana daga kujera yar tsugunno suna hira da Binta. Anan ta ke bata labarin yanda suka yi da Ikram. Dariya sosai Binta ta yi.
"Duk yanda akayi ba banza ta kyaleki bata tofa ba."
Murmushi kawai Ummi ta yi wanda bai kai zuci ba, da ta ji hirar babu abinda ta ragemata sai ma k'ara hargitsata da ta yi don kuwa Binta ta sanarmata da zuwan matasan gidan da iyalinsu gobe, anan zasu wuni, duk sai ta ji hankalinta ya k'ara tashi, hakan yasa ta mikewa.
  "Bari dai na dan zagaya."
Kai tsaye (Garden) ta nufa, zama ta yi saman lilo ta kwantar da kanta jikin igiyar, a sannu ta ke lulata tana tunani, rayuwarta na tafiya daki-daki, daga matsayin yar aiki zuwa ta surukar gida, har ta gangaro ga irin kyautatawar da Faruk ya yi mata zuwa ga yanzu da ta 6ata mishi rai. 
   Bata ji motsin zuwansa ba, saidai ji ta yi yana share mata hawaye. 
  "Yaya Faruk!"
Ta fada da sauri tana dubansa, sai kuma kunya ta kamata ganin dagaske ba mafarki ta ke ba shi dinne zaune durkushe gabanta yana dubanta. 
   "I'm sorry. Ki yi hakuri kinji?"
Ya fada cike da damuwa a fuskarsa, ta girgiza kai.
"Ni zan baka hakuri, don Allah ka gafartamin kada Allah Ya yi fushi da ni."
Ta burgeshi har baisan sadda ya dora gwuiwoyin hannunsa ba akan kafafunta yana mai dubanta.
"Sai kin chanjamin suna."
  Ta rufe fuska tana dariya.   Ya riko hannunta gami da mik'ar da ita.
"Oya, muje mu ci abinci."
Ta mike ba musu suka shiga ciki yana rike da hannunta. 
  Kusan tare suka ci abincin a falon Hajiya, Hajiyar na sama ta yi bak'uwa mai zuwa sarar kaya. 
   Suna ci daga zai bata a baki sai ta yi saurin kaucewa, har ya gaji ya bari, abin kan ta6a zuciyarsa, shi sam ba ya kaunar rayuwa haka, Yana yawan hangowa kansa rayuwa ta wayewa, baya kaunar kunyar Ummi ta cucesu a zamantakewa, idan har hakane, zata tauye musu jin dadi....

'((Nagode da adduoinku.. Allah Yabar zumunci..ameen))

DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

105

Ya ji abincin ya fita ransa dole ya ja baya gami da zuba ruwa ya sha. 
   Ta dubeshi, tana son tambaya ko ya k'oshi saidai ta kasa, ita batasan meyasa duk kunyarsa yanzu ta ke ji ba, ta fahimci kuma ba haka ya ke so ba. Yana kallonta tana faman juya cokali, kawai ta mike ta dauke zuwa kicin. Koda ta fito bata ganshi a falon ba, itama sama ta nufa don jin an soma kiraye-kirayen sallah. 
   Saida ta idar sannan ta ciro Al-kur'ani ta dan karanta inda aka biyamusu sannan ta rufe. Wayarta ta dauko, tana son kiran Antinta Amina don neman shawara saidai babu kudi cikinsa, tunawa ta yi da kudin da babanta ya bata cikin wanda ta ba shi da ta taho da shi, ya ragomata koda za ta siya wani abun, hamdala ta yi kafin ta mike ta nufi jakarta ta rataye, dubu daya ta ciro sannan ta fita, daman da hijab a jikinta. 
   Allah Ya taimaketa Hajiya bata falon hakan yasa ta zarcewa kasa. 
Kai tsaye farfajiyar gidan ta nufa, saida gabanta ya fadi ganin Faruk ya shigo, da alamu dai daga masallaci ya ke, shi dinma ita ya zubawa ido da mamaki, ta ja ta tsaya har ya karaso.
"Ina za ki?" 
Ta nunamishi kudin hannunta.
"Kati nake so shine zan bayar a siyomin."
Jin haka ya tamke fuska.
"Meyasa ba ki sanarmin ba? Hakkina ne fa nasan dukkam abinda ki ke so, ya kamata ki chanja Ummina, banason wannan kunyar taki a yanzu, bani da bukatarta, please ki saki jikinki da ni. I'm now your husband."
Ya karashe da murya mai kamar rada sannan ya gifta ta ya yi gaba, gaba daya jikinta ya yi sanyi dole ta bi bayanshi. Sashensa ya nufa, itama ta yi nata dakin. Kwanciya ta yi saman gado ta yi shiru kawai, haka har aka soma kiraye-kirayen sallar Isha'i, ta gabatar, jimawa kadan ta fito falon bayan ta cire hijabin ta linke.
Hajiya ta tarar zaune tana waya da Hajiya Mama inda suke tattaunawa akan bikin dangatan nata har ta ke sanarmata da batun zuwan su Babban Yaya gobe don tattaunawa. Ummi daman bata zauna falon ba, kai tsaye k'asa ta sauka don kuwa saida ta yi da na sanin fitowa don tuni ta fahimci maganar me sukeyi. 
  A kasa ta samu su Binta sina kallon wani series da akeyi da harshen larabci, zama ta yi saman kujera kafin ta dubesu sannan ta maida dubanta ga talabijin din kawai kuma sai ta kwashe da dariya sosai, dariya wacce rabonta da irinta tun dawowarta daga Gombe da suna hira da Binta a kicin. Suka dubeta.
"Lafiya Ranki ya dade?" Ta dan harareta da wasa don ita ta nuna sam batason sunan saidai kamar da gayya ma Bintar ke yi. Dariya itama Bintar ta yi.
  "Ku ku ka sanyani dariya, kun nutsu kun zubawa talabijin idanu kai kace kunsan abinda su ke cewa."
Suka dara, Samira wacce ta zo bayan tafiyar Ummi Gombe ta dubeta.
"Ai soyayyar kadai idan ki ka kalla wallahi ranki fari zaiyi, kinga nan."
Duk suka maida hankalinsu kan talabijin, abinci zata ba shi da cokali  yayinda ya ke jingine da filo a gadon asibiti, ya tarr ya hanata ba shi da cokalin, dole tasa hannu har wani take aka sakomusu, har idan ya 6ata bakin ta gogeshi mishi, karshe ma ya hada da yatsunta ya tsotsa. Ummi ta saci kallon su Binta suka kwashe da dariya, sai kuma suka nutsu. Shiru ta yi har da taguminta tana kallo da murmushi.  Basu ji zuwansa ba, hakanan bata ko lura da sadda ya yiwa su Binta alama da su bar wajen ba, balle kuma zamansa gefenta. Hankalinta ya lula wata duniya, tunaninta bai wuce inama itama za ta iya hakan gareshi ba, sumbatar da ta ji a wuyanta ne yasa ta juyawa a firgice tana salati a fili, murmushi ya ke jifanta da shi, idanunsa sun kankance yana dubanta. Gabanta ya hau bugu, ta waiga babu su Binta ko dalilinsu, ta dubi talabijin, tuni ashe an wuce wajen sai ma likita da ta ga ya shigo dakinnasu(a film din), ta dan ja baya gami da shafa goshinta. Duk ta rasa me zata yi don kunya ta hau wasa da zoben gwal din dake hannunta wanda ya bata. Ya matso daf da ita.
"Kina so kina kaiwa kasuwa kenan?"
Ya watsamata tambayar cikin narkakkiyar muryarsa wacce soyayya ta cika. Ta hau girgiza kai batare da ta ce komai ba. Bai saurareta ba ya ja hannunta sadda ya mike tsaye.
"Oya, taso ki ga wani abu."
Ta mike ta zare hannunta da dabara kafin ta bi bayanshi a sanyaye. Ganin hanyar da ya nufa na samansa yasa ta tsaya cak duk a firgice. Ya juyo ya dubeta idanunta ya yi rau-rau, tsoronta lokacin cin abinci ne kada Hajiya ta nemesu, kada ma Hajiyar ta dauka ita ke zuwa wajensa tunda ta ga sadda ta sauko.  Hannunta ya kama ya soma taka matattakalar, tana zamewa kadan-kadan saidai bai saketa ba har suka isa. Tsoro ta ji ganin sun wuce falo har ya sada ta da k'uryarsa. 
   Dakin yana nan yanda ta sanshi, bai jira cewarta ba ya sanyata jikinsa. Tun tana a'a, da kuma rokonsa akan ya kyaleta, kamar baisan ta na yi ba. Ganin yana kokarin zuge mata zif yasa ta yin baya da sauri ta fito falo, tsaki ya ja, abin kuma ya soma ba shi haushi, wannan sam ba zai lamunta ba, tana abu kamar wacce batasan menene aure ba, ya dauki dankwalinta ya biyota da shi, tana tsaye hanyar matattakala, mik'amata ya yi fuskarsa a murtuke. Yana dubanta da jajayen idanunsa wanda har da 6acin rai cikinsu ga kuma fitina. Wannan abun ya zama sakarci kuma, ina laifin ma da ya iya jurewa har aka daura auren? Da ace tasan yanda ya ke mutuwar so da sha'awarta da bata soma tunanin yi mishi gardama a dan abinda zai yi na rage zafi ba, sam ba shi da nufin wani abu bayan kalilan din da ya ke kwadayi a yanzun. Anan zasu samu matsala.
  "Kina iya tafiya."
Ta yi narai-narai da fuska.
"Ki tafi nace!"
Ya fada da dan daga murya, ta soma hawaye sai kuma ta juya da sauri-sauri ta bar wajen. 
    Ta ci saa Hajiya ta yi sashen Daddy, ta wuce dakinta ta kwanta ta soma kuka. Saida ta yi mai isarta sannan ta share fuskarta, wayarta ta ji ta yi karar shigowar text, ta janyota, shi dinne ya turomata kudi daga acc na banki. Ya saba yi mata hakan shiyasa tun bata gane ba ta fahimta, bata yi wata-wata ba ta dannawa Amina kira, saidai bata sameta ba, shaf ta mance cewar sun je Nijar. Ta ciji le66anta, shigowar Hajiya Babba ne ya sa ta gyara fuskarta da sauri, ta amsa sallamarta. Hajiya ta lura akwai wani abun, ta karasa rike da wata roba a hannunta ta zauna gefen gadon.
"Lafiyarki kuwa?"
Ummi ta yi murmushin yak'e.
"Bakomai Hajiya."
"Ya za ki cemin bakomai alhalin ga idanunki a kode?"
"Kaina ke ciwo." Ta samu bakinta da shararo karya. Hajiya ta numfasa.
"Allah Ya sauwake."
"Amin."
"Rike wannan."
Ta mikamata robar, ta dubeta.
"Da safe da dare ki dinga sha da madara kinji? Akwai wasu ma da na sanya akawomin, Ummi ina miki kallon diyata, abinda zan yiwa Ikram zan miki shi, wannan kunyar tawa nakeso ki daina jinta kinji ko? Ki daukeni kamar uwa agareki."
Kanta a kasa ta gyada kai.
"In sha Allahu Hajiya."
Murmushi Hajiya ta yi sannan ta dafe kanta.
"Allah Ya yi miki albarka, ki tashi ki je ki ci abinci."
Da murmushin itama ta amsa da toh. 
Ta bi bayan Hajiya da kallo, ji dai yanda mutanen nan suka dauketa da girma, ta tuna yanda ta ke 6atawa dansu a rai akan hakkinsa, dagaske batasan rayuwar aure sosai ba, duk wani kissa ko kisisina bata ta6a hirarsa da wani ko wata ba, to waye mai koyamata ma? Duka-duka idan a makaranta ake koya, yaushe ta soma zuwa makarantar? Ko wata biyar cikakkiya bata yi ba a makarantar Kano, sannan ita din ba karatun litattafai ba, hakan kuma bai hadasu da Amina, ta dai soma jin kadan daga bakin su Abida, kamar biyayya da bin umarni da sauransu. Dole ta zage damtse ta koya, kamar dai yanzu da ta ga kulawar matar nan ga mijinta duk da cewar a fim ne, amma kwarai sun burgeta. 
   'Mijinki dan boko ne wayayye, sai kin zage damtse kin kula da shi.' Cewar wani sashe na zuciyarta. 
     A ranar basu kara haduwa ba, ta kira wayarsa yafi sau biyu bai daga ba, hakanan ta hakura, ranar bata iya baccin kirki ba.
  Washegari....

  DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

106

Suna zaune a falo da Hajiya dake lissafe-lissafenta na kaya hannunta rike da biro da dan(Memo) na lissafi, yayinda Ummi ke gefe tana karyawa, zuwa yanzu ta soma sakin jiki da Hajiyar. Sallama ya yi ciki-ciki, suka amsa, Hajiya bata dubeshi ba dalilin batason 6ata a k'irgenta. Ummi ta saci kallonsa, fuskar babu digon walwala, ta daure ta gaisheshi, ya amsa ganin Hajiya na wurin. Ta mike ta janyo tebur gabansa da niyyar hadamishi kari.
"No barshi, sai anjima zan karya."
Ta kada kai kawai ta koma mazauninta, Hajiya ba tare da ta dubeshi ba ta ce.
"A'a, kodai ba ka tare da yunwa ne? Wannan lokacin nasan kana karyawa Sadaukina, maza Ummi gama ki hadomishi."
  Ta amsa da toh. Ya yamutse fuska yana duban Hajiya.
"Wai kwanab biyun nan wa ke gyaramin daki ne? Toilet dina k'arni. Ko kusa gyaran bai yi."
"Samira ce." Cewar Hajiya tana dubanshi. Ya dan muskuta. 
"Daga yau ta daina bana bukata, sam bata iya aiki yanda ya kamata ba."
Hajiya ta dubi Ummi, kamar ta ce wani abu sai kawai ta share da fadin
"Allah Ya kyauta." Daga haka ta bi bayan wayar da aka kirata har ta yanke bata daga ba. Shi kuwa kwantar da kanshi ya yi jikin kujera ya lumshe idanunsa, shi kadai yasan me ya ke ji a zuciyarsa. Har Ummi ta gama ta hadamishi abin kari bai dago ba balle ya kalleta, itama dauriya kawai ta ke yi hakanan tana jin kunyar kanta bata son Hajiya ta fahimci akwai abinda ya hadasu, saidai tuni ta dagosu shiru kawai ta yi ta zubamusu ido. 
    Kai tsaye kicin ta sauka ta maida kofi da filet sannan ta yi hanyar sashensa, gyara ta hau yi, saida ta kammala ta tabbatar komai ya yi kyau sannan ta koma ga bandaki ta hau wankewa, saida ta kammala ta goge sannan ta fito rike da tsummokaran a bokiti, ta dubi ko'ina ta ga ya yi kyau sannan ta rufe kofar. Allah Ya taimaketa har ta zagaya wajen garden basu hadu ba, zama ta yi da niyyar wanke tsummokaran, sai kuma ta dakata cikin tunani, Allah Sarkin bayinSa kenan, kamar bata taka matsayin 'yar aiki ba kafin zuwan wannan lokaci da ta ke matsayi na Matar Dan Gida.  
  Acan kuwa Faruk koda ya hau samansa ya tarar da komai tsaf ya yi mamaki sosai da sosai, kamshi daddad'a kawai ke tashi, da sauri ya karasa ga dakinsa, nan ma an gyare tas hakanan bandaki wanda ke kamshi babu wannan k'arnin. 
"To wa ya gyara?" Ya tambayi kansa, ya fito ya nufi barandarsa don ganin nan dinma ko an gyara, shima(tiles) din kamar ba'a ta6a takawa ba.
Kamar ance ya dubi ciki garden, ya hangota tana faman wanke tsummokarai, ya kasa gaskata idanunsa, sai kuma ya ga ta mike tana matsewa gami da shanyawa. Ji ya yi kamar ana k'ara kwararo mishi sonta, ga wani tausayinta da ya ji ya dirar masa, ina laifin ma ta yi gyaran kawai banda wannan wanke-wanken? Ya soma ja baya yana girgiza kai.
"No Ummina, matsayinki ya zarce haka gareni."
   Kawai sai ya juya ya fita zuciyarsa na yi mishi babu dadi, ganinta ya ke yi kamar Ummin baya, wacce ta ke yiwa kanta kallon wata marar gata.  
   Ita kuwa tana tunane-tunanenta akan rayuwa har ta gama shanya, ta sanya hannu da zummar zubar da ruwan, sai ganin mutum ta yi tsaye, ta dubeshi shima din ita ya ke duba, ya kar6e bokitin ya ajiye, a kunyace ta sunkuyar da kanta. Ta kasa cewa uffan.
  "Kinyi min gyara, na gani kuma na ji dadi, Allah Ya yi miki albarka."
"Amin, nagode." Ta amsa jiki a sanyaye ganin ba digon walwala a fuskarsa har lokacin.
  "Don Allah Yaya Faruk ka yafemin na..."
  "Ki dunga barwa ita Samirar ta dunga wanke wadannan." Ya yi nuni da tsummokaran, fuskarsa a daure ya juya ya tafi. Ta bishi da kallo idanunta cike da kwalla, wannan fushinnasa yana cin ranta kwarai, saidai me za ta yi mishi ya huce?
  Misalin karfe sha daya Dakta da iyalinsa suka diro gidan, Jidda har daki ta biyota lokacin tana goge kayan Islamiyyarta, ta dan yi yak'e sadda gabanta ke bugu da sauri-sauri, tasan yau kam zaman gidan zai mata zafi saboda su da basu kaunar su bud'i ido su ganta. 
  "Anti Jidda sannu da zuwa, ina kwana."
Jidda wacce ta yi sakato tana dubanta da mamakin chanjawarta ta hau jinjina kai.
"Lallai kan mage ya waye, Ummin ce kuwa?" Ba kunya ba tsoron Allah ta furta a fili. 
Ummi ta na murmushi ta maida kanta ga gugarta batare da ta ce komai ba. 
Jidda ta ta6e baki sannan ta karewa dakin kallo kafin ta fice. Rufe kofarta ne yasa ta duban kofar, ga mamaki sai ta ji ta daure don ko kwallar bata yi ba, inda sabo kuma ai ta soma sabawa da wannan cin fuskar nasu. Fatanta lokacin makaranta ya yi ta wuce tun kafin su taru gaba dayansu abin ya zame mata da yawa, ga fushin Faruk gareta, sannan ga cin fuska daga su Jidda. 
    Faruk ya dubi Jidda, kwarai ya ji furucinta saidai ya basar ya cigaba da hirarsa da Dakta. 
   Ta iso garesu ta zauna gefen mijinta.
"Matarka ta yi k'iba ta kara kyau."
Ta fada tana duban Faruk, idan dutse zaiyi magana to ya yi gareta, ya cigaba da jan Dakta da hira. Jidda ta yi dariya kawai don tasan halin Faruk, koda zata wuni tana magana tunda kamar ransa a 6ace ya ke to fa bazai amsa mata ba. 
   Wajen karfe biyu saura sai ga Haidar da Intisar banda Ikram wacce daga can zata wuce makaranta, kamar hadin baki shima Babban Yaya ya iso alokacin da Fadila, Ummi na jin hayaniyarsu saidai bata ko lek'o falon ba, asalima alwala ta yi sannan ta shiga shirin tafiya makaranta. Turo kofar da akayi ne yasa ta waigowa, Intisar ce, ta shigo da murmushi saman fuskarta.
"Aa, Amarya Ummi sannu."
Ta gaisheta itama fuska a dan sake ganin ita dinma ba wani sabo suka yi ba amman bata bita da kallon banza ba irin na wadancan. 
   Ta karasa shigowa ciki tana fama da cikinta wanda ya doshi wata biyar saidai yana da girma. 
  "Makaranta za ki kenan? Ikram ma can muka barota a gida zata wuce, tare za ku yo nan."
"Toh." Ta fada cikin rashin sabo. 
Daga haka ta fita itama ta cigaba da shirinta, saida ta yi sallar Azhar sannan ta dauki jakarta ta fito. Duk suna falon, yaransu suna gida saboda Islamiyya sai an tashi zasu yo nan. 
   Duk suka dubeta, ta yi kasa da kanta tana karanto adduoi cikin ranta, haka ta karasa ta durkusa ta gaishesu, duk suka amsa.
"Amaryar Lil, Allah Yasa alheri." Cewar Dakta, bata amsa ba banda kasa da ta yi da kanta tana murmushi kadan. Hajiya ta dubeta.
"Ki tsaya fa ki ci abinci kan ki wuce."
"Toh."
Sannan ta mike daga durkuson da ta yi ta nufi kasa, Jidda kallon kafafunta ta ke yi da suka sha kunshi wanda ya kara haskakata, ta ta6e baki gami da yin kus-kus da Fadila suka dara gami da tafawa.
  Mazan suka dubesu kawai suka kauda kai. Faruk kuwa tsam ya mike. Ya dubi yayyunsa.
"Ina zuwa."
Daga haka ya sanya takalmi ya bi bayan Ummi, dariya sukayi, Hajiya kuwa murmushi kawai ta yi. Ta gama gaskatawa Ummi ce farincikin dan nata. 
   Ita kuwa baiwar Allah, a tsaitsaye ta ci fried rice din loma uku kawai ta yi, Binta na cewa ta k'ara, fadi ta ke a'a saita dawo. Ruwa ta sha sannan ta fito, har zata fita ta ji maganarsa.
"Ki jira na kaiki."
Ta tsaya cak batare da ta waiga ba, ya yi hanyar dakinsa, mukulli ya dauko, tana tsaye sai jin hon dinsa ta yi hakan ya fahimtar da ita cewar ta kofar baya ya zagaya. Ko a motar baice mata uffan ba, suna isa bayan ya tsaya ya dubeta.
"Yau me ya hanaki sanya safa?"
Cikin soma gajiya da wannan fushin na Faruk ta amsa cikin rawar murya.
"Na manta ne wallahi." Ya sa hannu gefensa ya bata wacce ya fito da shi ta sanya sannan ya cire lock ta fita. 
"Nagode." Shine abinda ta ce cikin rawar murya sannan ta rufe kofar ta fice. 
   Tana shiga su Shukra suka tareta.
"Anti Hasiya yau ma Yayanmu ne ya kawoki?"
Tsaki ta ja wanda batasan sadda ya fita ba, ta giftasu ta wuce, suka bita da kallo kawai. 
Husna ta lura kamar tana cikin damuwa, ta bi bayanta har kusa da kujerarta ta zauna gami da dafata.
"Lafiya kuwa Hasiya?"
Kamar jira ta ke yi kawai sai ta soma kuka, Husna ta rike kafadarta, ta duba ta ga ana kallonsu.
"Ki yi hakurin danne damuwarki, kinga idanuwa duk a kanki fa."
Jin haka yasa ta share idanunnata, ta daure ta nutsu, ayau ta ji kewar Antinta Amina kwarai, saidai itama Husna ta yarda da ita, tana da hankali, watakil ta samu shawarar da zata iya bata. .....
  DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

107

Saida aka tashi ne suka samu damar ke6ewa. Anan Husna ta yi shiru tana kallon Ummi, ganin haka yasa Ummi soma magana.
  "Wata shawara nake nema agareki."
Husna ta gyada kai cike da k'osawa don sau wajen biyar kenan tana furta hakan amman ta kasa magana. 
"Ina jinki."
  Dakyar ta samu ta labarta mata kadan cikin labarinta wasu abubuwan kuwa ta sakayasu, ta nuna mata kawai dai tana fuskantar matsala yanzu da saurayinnata da aka daura aurensu aka bar biki daga baya. Ta karanto mata matsalar a sakaye sannan ta k'ara da fadin.
  "Husna kin ganni ko? Ban budi ido naga mahaifiyata ba, sannan ban samu wata kulawa daga kishiyarta ba, har zuwa yanzu da aka zo batun aurennan, sannan ni duka-duka ma a Islamiyyar Kano da na ke fadamiki ban jima ina zuwa ba, wani sa'in idan wata fita ta zo shikenan bana zuwa.  Ina cikin tsaka mai wuya Husna, ina 6atawa mijin aurena rai, ki taimakamin da iya abinda ki ka sani, yarda dake ne yasa na sanarmiki abinda ban ta6a fadawa kowa ba a makarantar nan."
Husna wacce ta cika da mamakin wai Hasiya yanzu matar aure ce, ta numfasa bayan kalamanta na karshe wanda yasa ta jin tausayinta.Murmushi ta sakarmata.
"Ki sha kuruminki k'awata, in sha Allah daga gobe zamu soma. Saidai abinda nakeson ki sanyawa ranki, shi fa mijinnan wajibi ne gareki ki bishi sau da k'afa, karki bari damarki ta wuce, idan ance biyayya ciki har da ba shi hakkinsa na aure idan ya nema tunda dai ansan da igiyarsa akanki, wannan zamanin ba'a sakaci Hasiya,  mata da yawa neman mai aurensu su ke yi, wasu kuwa kamar su jawo namijin ya kwanta da su su ke ji, ballantana kuma idan mijinki wani hadadden ne, tuni za ki yi sake. A baya ne za ki ji duk iyayenmu na irin wannan kunya-kunyar, ansan tana da kyau saidai bisa shawara ki rageta, ki rungumi mijinki hannu bibbiyu. Karki damu, yanzu kinga dai anzo daukata, bari zuwa gobe zan taho miki da wani littafi SIRRINMU na wata tsohuwar marubuciya sai kuma wani  Sinadarin Rayuwa shima marubuciyar ta yi kokari matuka wajen koyawa mata salon kula da miji da gida, zan kuma k'ara miki a kai. Duk fa litattafan Antina ne matar Yayana da nake hannunta, zan rufa miki sirrinki Hasiya koda baki nemi hakan ba."
Ummi ta dan ji sanyi, ta yi mata godiya sannan suka zagayo farfajiyar makarantar, anan suka yi kici6us da Fati. 
"Yauwa, anzo daukarki fa tun dazu Anti Hasiya."
Ummi na jin haka ta daure fuska.
"Nikam karki kara kirana Anti banaso wallahi."
Fati ta rike ha6a.
"Ah, ai sai na kiraki da fin haka, kin kai wallahi. Sai

Please Login or Register in order to submit comment