Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saurin janyewa saboda gudin kar tayi masa mummunar fahimta,

“Wai mai ne ya ‘kare ko kuwa wata matsalar ce ta faro da motar?”

Yaji ta waigo tana tambayar sa, idanunsa kyar a cikin nata tayi saurin janyewa saboda wani irin abu da taga idanunsa sunyi, har kirjinta ya fara bugawa gani take tamkar zai iya aikata mata wani abun a halin yanzu, sam ba ta san wane tsautsayi ne yasa ta biyo shi ba domin zai iya yiwa Aliya karya na cewa itace tace ya kaita. A hankali ta murd'a k'ofar da nufin ta gudu amman abin takaici a rufe taji ta kuma matsawa jikin kofar da take zaune zuciyar ta cike da addu'a kan Allah ya temake ta karya rab'e ta,

“Kibi a hankali ki dena kula irin wad'annan yaran, yanzu banda rashin sanin kai me wannan yaron zai iya tsinana miki idan kin aure shi? Dubeshi fa yaro ne sosai ba wani hakkin aure ya sani ba bare ya sauke miki, yazo sai shirga miki karya yake yi kina dariya.”

Fa'iza taji Sahal na cewa haka ba tare da ya kalleta ba don idan ya kalleta ba zai iya cewa komai ba, saboda tsabar shaukinta da yake hanashi yi mata fad'a.

“Gasiya ina son shi, kuma zan iya zama dashi ko babu ci da sha.”

Ta fad'a cikin son kona mishi rai, aikuwa tayi domin wani uban tsaki taji yayi tare da tayar da motar ya figeta, student dake tafiya sai kallansa suke yi da alama sun gano mai motar baya cikin hankalinsa.

“Toh kisa a ranki ba zaki auresa ba domin yayi kankanta da zama mijinki, daman akwai wani abokina da yace na yiwa Aliya magana ta sanar dake yana son ku gana, shi nake so ki bawa duk wani nutsuwarki.”

Idanunta a rufe domin tun lakacin da ya figi motar wani tsoro ya bugi kirjin ta shine har yanzu ta kasa dawowa dai-dai jira kawai take taji ance sun kifa suda motar. Duk a tunaninsa maganar da yayi ce ta shigeta dan haka ya rage gudun saboda lokacin ma sun karaso wajan da su Aliya suke ciki suna jarabawar.

A hankali yaga tana bud'e ido tare da saurin duba jikinta, ganinta a zaune daram yasa hankalinta kwanciya tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, yadda taji maganarsa da yake cewa ba zata auri wani ba sai abokinsa haka ta watsar da zancen a gurin domin ba wani jinsa tayi sosai ba bare tasan a yanayin yadda yayi furucin. Sake murd'a k'ofar tayi still a kulle alamar bai bud'e ba, gashi maganace a cikin Sahal da yawa amman yadda Fa'iza ta nuna masa cewar tana da wanda take so hankalinsa ya tashi, ya rasa gano mai zai yi wanda zai nuna mata tabbacin yana sonta.

“Bude na fita na gode.”

“Sai wadda tasa na kawoki ta fito sannan zaki fita.”

“Please dan Allah karka min haka, ka bud'e na fita bana son Babana yazo yaga na fito daga cikin motar nan kasan dai ba zai ji dad'i ba.”

Shiru yayi yasan ta fishi gaskiya amman baya so ya barta yana ganin kamar idan ya barta ta fita zata kuma yin wasu samarin, zuciyarsa sai azalzalarsa take yi akan ya sanar da ita gaskiya amman bakinsa ya gaza furtawa, jiki a sanyaye ya bud'e mata daman jakarta na hannunta dan haka fita kawai tayi ba tare da ta kalleshi ba.

Tana fitowa kuwa ta d'an bar wajan motar sai ga Baba Suleiman yazo tafiya dasu wanda suma su Aliya a lokacin sun fito, kai tsaye mota suka nufa ba tare da Aliya sun gaisa da Sahal ba gashi ta ganshi tsaye jikin mota wanda ya fito ne dan yaga ko Fa'iza zata kula wasu, sai kuma yaga mahaifin su yazo d'aukar su sai yaji sanyi tare da komawa tashi motar suna tafiya yana binsu a baya har suka fita daga gate d'in BUK.

Haka suka wuce Aliya duk ranta babu dad'i domin kiri-kiri tana ganin Sahal amman babu damar yi masa magana, ji take tamkar ta fashe da kuka dan takaici. Shi ya nufi hanyar jakara yayin da su kuma suka nufi Hotoro, duk irin tambayar da Fa'iza ke yiwa Aliya hakan besa ta kulata ba saboda haushi, ita kuwa Fa'iza dariya take zuwa yanzu daga Aliya har Sahal din dariya suke bata, tana son Allah ya barta da rai ko dan taga ya karshen soyayyar nan take.

••• ••• ••• •••

Dare ya zama safiya, safiya ta zama yammaci, yammaci ya zama dare, Lalle Allah qadirin ne ala manyasha’u! Rayuwa taci gaba da garawa kamar yadda alkalamin kudura ya rubuta, 'yan matan Baba Suleiman suna cikin kwanciyar hankali, hatta gwaggo Talatuwa yanzu ta dena yi masa zancen komawa gidan ta, Sahal yakan je duk lokacin da ya shigo garin kano, yayin da a bayyane yake zuwa gurin Aliya a b'oye kuma yakan tura sakon ‘kauna da soyayya zuwa wajan sahibarsa Fa'iza, wacce tun tana fargaba har ta dena, burinta da fatan ta guda d'aya shine Muhamman S ya bayyana kanshi domin ta sanar dashi cewar yayi hakuri tana da wanda take so, kullum fatanta kenan amman yaki bayyana masa kanta.

Kamar yadda ya saba baya barin duk randa zaizo ya zamana Baba Suleiman yana gida, yakan taki sa'a idan yazo kodai baya garin ko kuma yaji labarin cewar yanzu ya fita daga gidan kasan cewar sai ya fara aikawa yace aje ace ana sallama da maigidan sai a ce baya nan, idan yaji haka shine yake samun damar zuwa ya mik'a sakko yace a bawa Fa'iza.

Yauma kamar kullum Fa'iza da Aliya suna wankin kayan su kasan cewar su suke yi ba wai yi musu ake ba, daya tana sab'a na sabulu daya kuma tana daurayewa taje ta shanya haka suke yi, sallama yaro yayi suka amsa yace,

“Wai ance Fa'iza na nan?”

Daram gabanta ya fadi ta dafe kirji dama sanye take cikin riga da skirt na wani green da orange d'in less sai riga t.shit orange, kafin tayi magana Aliya tace,

“Jeka ce waye?”

Yaron ya fita yayin da Fa'iza ta zabga tagumi, Aliya tace,

“Ko kinsan ko waye ne?”

“Ina na wani sani? baki ga nima jiran yaron nake yi ba yazo muji”

Tana rufe baki yaron ya shigo tare da cewa,

“Yace sako aka bashi ya kawo mata, wai d'an lekowa kawai zata yi.”

Umma dage cikin parlour tana d'inki ta kwala mata kira tana cewa,

“Fa'izah! wai bake ake kira bane?”

“Umma banfa san ko waye ba.”

“Ohh to ba zaki je kiga ko waye ba zaki tsaya a cikin gida kina wani cewa ke baki san ko waye ba, kinzo kin dauki mayafi ko sai nazo na gwara kanki da bango.?”

Kamar zata yi kuka haka ta wuce d'akin su, hijabi ta sanyo ta fito fuskar nan a had'e ko hoda bata d'an murza ba, silifas ta saka taje wajan Aliya dake wanki tana mata dariyar mugunta k'asa-k'asa, a hankali ta furta,

“Sissy! zo muje tare.”

Dariyar da Aliya ke b'oyewa ita ta bayyana, ganin tana mata dariya ne yasa ranta ya b'aci bata kuma cewa tazo ta raka taba kawai tayi ficewarta. Babu kowa a kofar gidan ta fara waige-waige amman babu kowa, tana juyawa can karshen layin su ta hango hancin wata red car yana faman yi mata horn. Tamkar a gabansa take haka ta dinga aikawa motar harara tana jan numfashi tare da cewa,

“Idan ma kaine kake nemana in bazaka iya karasowa k'ofar gidan nan ba toh ka koma, kila ma d'an yankan kaine shi yasa ya tsaya a nesa toh bazan je ba.”

Tayi maganar a fili kamar wani take sanarwa a kusa da ita, akan idanunta taga ya kira wasu yara su biyu ba tare da ya fito daga motar ba ya bude musu booth, tana kallo yaran na fito da kaya daga cikin booth d'in, bayan sun gama taga d'aya ya leka cikin mota tare da zura hannu, wata kyakkyawar leda mai kyalli taga ya fito da ita kai tsaye kuma taga sun kwaso kayan sun nufo inda take tsaye wato k'ofar gidan su. A gabanta suka dire kayan tare da mik'a mata wata kyakkyawar envelope suka juya, wajan motar taga sun koma sun mika hannu da alama kud'in sallama ya basu, tana tsaye sakato ta kasa motsawa daga gurin sai kallan motar take yi, horn ya kuma yi mata ganin zai tafi yasa ta tsallake kayan zata bishi taga ko waye, alamun hakan da ya gani ne yasa shi saurin jan motar yabar wajan, Fa'iza kuwa harda d'an gudunta na son zuwa ta ganshi amman ya gudu, cikin damuwa ta tsaya tare da komawa gida bayan ta kira kannanta su Waleed sun shigar da kayan ciki.

Jiki babu kwari ta shiga gidan, Aliya tayi saurin mikewa ta karasa gurinta tare da cewa,

“Ya akai Sissy? Kinga ko waye?”

Kai Fa'iza ta girgiza tare da dago hannu ta mik'awa Aliya envelope d'in da aka bata, gurin Umma suka nufa daman kayan a gabanta aka ajiye sannan Aliya ta bud'e envelope d'in ta ciro wata takarda mai dauke da rubutu, da kalar biruka uku aka yi amfani wajan rubuta letter wato red, green da blue! tsarin yayi kyau sosai tamkar ba da hannu aka rubuta ba inda yake cewa,

_I want to be your friend
dear moon armour.
I don't think you have a clue, but there's something in the world I would like to have and you're the only one who can give it to me, your friendship, You know i'm a bit shy and that is why i'm using this letter as a resource, a tool to get near you. As a matter of fact, i've been wanting to get closer to you, to chat, to ask you things, to comment on trivial matters or even to talk a bit about me, but I was always afraid, afraid you wouldn't show the least interest in giving me your friendship and allowing me to enjoy your company. Maybe you find it strange that i'm using something as cold as this piece of paper to say how much I would like to touch your hand and kiss your face every time we meet; but i'm a bit bashful and I wouldn't know how to approach you in another way.
In short, the purpose of this letter is just to ask you if you want to be my friend my love and to be my wife. And if you agree, just say yes the next time we meet or just give me that beautiful smile of yours whenever I walk by. You can always reply to this simple letter, if you want to…a kiss from
MUHAMMAN S._

_*Today is a very special day, so I want to send my special wishes to someone very special I know, to make your birthday special, wish you happy birthday my armour Stay blessed.*_

Aliya na gama karanto lettern taja wani bahagon numfashi tare da kallan Fa'iza tana cewa,

“Karya kike yi Fa'iza kice baki san ko wanene wannan Muhamman S d'in ba, ya kamata zuwa yanzu ki bayyana mana waye shi domin alamu sun nuna yasan komai naki gashi nan har yasan yau kike cikar shekara, idan bake kika gaya masa ba ya akai ya sani? Malama idan zaki fadi ko waye ki fad'a ki dena wani b'oye-b'oye.'”

Wasu zafafan hawaye ne suka fito daga cikin idanun Fa'iza, bata san abinda zata ce musu ba dan taga hatta Umman su ma jira take taji karin bayani, cikin muryar kuka tace,

“Wallahi tallahi billahi nayi rantsuwar musulmai ban san ko waye ba, ko yanzu ma da yazo wallahi ban ganshi ba yaki fitowa daga motar, ya zanyi?”

Umma tayi shiru a hankali kuma ta fara bud'e kayan, ledar karshe data bud'e mai kyau da ta birthday cake ne an rantab'a sunan _HBD my Fa'iii_, mai kyau dashi ga tsada daga gani kuma zai yi arnan dad'i. Aliya da itama take bud'e kayan taci karo da waya iPhone 6s+ baki bud'e ta juya tana kallan Fa'iza tare da cewa.

“Dank'ari iPhone 6+?wallahi Fa'iza karya kike yi kinsan guy d'in nan kut...”

“Idan har na sanshi why ya rubuto wannan letter d'in.?”

“Oho na sani ko yayi k'ok'arin ki kulasa a zahiri ya gaya miki sakon zuciyar sa kika ki bashi dama, nasan ki sarai da kin kula samari 'yar rainin wayyo.”

Kanta ne taji yana barazanar fashewa hakan yasa ta mik'e a hankali tabar gurin, d'akinsu ta koma kwanciya tayi tare da kifa kai akan pillow ta saki wani marayan kuka, gabaki d'aya ta rasa gane kan mutumin nan gashi da alama ba karamin yaro bane, me yasa ya kasa bayyana a gareta sai kace yana tsoranta?

“Allah ka bayyana min ba wannan naka kodan na sanar dashi zab'in rai na.”

Ta fad'a a fili tana kuma cusa fuskarta cikin pillow, a haka Aliya tazo ta zauna kusa da ita tare da sanya hannu ta dafa bayanta, a sanyaye tace da ita,

“Sissy! karki damu insha Allahu koma wanene wannan Muhamman S d'in Allah zai tona asirinsa, na yadda dake cewar baki san ko wanene shi ba, insha Allahu nima zan cigaba da tayaki addu'a Allah yasa ya bayyana.”

A hankali Fa'iza ta d'ago tare da kallan Aliya wacce ke zaune itama damuwa ta fara shigarta ganin yadda ake son hargitsa kan 'yar uwar ta, murya na rawa tace,

“Babban tashin hankali na sisiyy da ban san fuskarsa ba, bana son ya ritsa ni a wani gurin ya cuce ni, idan ba mugu ba ta yaya za'ai ya b'oye kansa dan Allah.?”

“Haka ne ki rabu da shi insha Allahu zamu gano shi.”

Da haka suka tashi sukaje suka karasa wankin su, kayan kuwa sai da Baba Suleiman ya dawo Umma ta kai masa ya gani kasan cewar gwaggo bata nan taje can garin su (garin malam). Koda Baba Suleiman ya gani kawai fatan alkairi yayi tare da cewa koma waye zai bayyana kila akwai abinda yake tsoro shi yasa yaki kawo kansa kai tsaye. Koda aka rarraba abubuwan cimar aka bawa Fa'iza kin ci tayi Saboda tsananin tsoro, gani take kamar idan taci zata b'ace tunda da sunanta aka kawo, tana ji tana gani 'yan uwanta suka cinye komai, wayar ma tunda aka gani Umma ta b'oye ta tace har sai Baba Suleiman ya siyawa Aliya sannan zata bawa Fa'izan...
*ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE, DAN GIRMAN ALLAH MAI SO YA KARANTA, YA BIYA DUKA BIYAR DIN DARI 5 NE. SUNE KAMAR HAKA*

*BURI DAYA*
MAMUH GEE

*DAURIN BOYE*
SAFIYYA HUGUMA

*WUTSIYAR RAKUMI*
BILLYN ABDUL

*SAUYIN KADDARA*
HAFSAT RANO

*KAI MIN HALACCI*
MISS XOXO

*MASU SON SIYA, ZASU IYA TUNTUBAR LAMBOBIN MU KAMAR HAKA;*

08030811300
07067124863


*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO🧕🏼*

*26....*

Washe gari da suka je makaranta Aliya ta yiwa Nawal godiya sosai domin taji dad'in yadda ta kula da ita. Misalin karfe goma sha d'aya suna zaune suna hira kafin su kuma shiga wata lecture d'in, Nour Hadee ta kalli Nawal tana faman fiffik'ala tace,

“Nawal bani car key d'inki please zanje na dawo.”

“Kedawa zaku tafi keda ba tuki kika iya ba?”

“Dan Allah ki bani nida Lamfat ne yanzu zamu dawo kinsan bazan iya bari na rasa lecture d'in Mr Mahadi ba marar mutunci.”

Zaro wayar Nawal tayi ta mik'awa Nour domin ba zata iya hanata ba, Saboda amincin dake tsakanin su, ta karb'a ta wuce tana cillashi sama tamkar wani nata, taje ta mik'awa Lamfat dake tsaye jikin bishiya ya sanya wandon jean's ya zazzago shi tamkar wanda yayi kashi a cikin sa. Cilla masa tayi ya karb'a suka d'auki motar suka wuce, Nour Hadee yarinya ce kyakyawa bata da tsaho sosai fatar jikinta irin black beauty d'in nan ce, mahaifinta ba wani kud'i garesa ba, amman yana da rufin asiri domin yafi Baba Suleiman karfi nesa ba kusa ba, mutum ne shi mai tsattsauran ra'ayi dan da kyar ya bari Nour ta taho BUk tun daga Bauchi.

Wayayyar yarinya ce sai dai ba'a barinta yin wasu abubuwan a gida, Saboda rashin fuska da take samu daga wajan mahaifin ta, a gurin mahaifiyarta take samun damar yin wasu abubuwan domin itace ma take daure mata kugun yin wani abin. Tunda ta shigo Buk idanunta suka sake bud'ewa, Lamfat ya sake lalata mata rayuwa ya maida ita tamkar gonarsa da duk lokacin da yaga dama shiga yake, Saboda yana kashe mata kud'i domin duk abinda take so yana yi mata,

“Yanzu ke Nawal kike bawa Nour motarki bakya tsoron taje ta janyo miki abin magana ko? Kinsan dai duk inda ta shiga da motarki dole ayi zaton kece bare kinsan ita da wannan stupid saurayin nata zasu fita.”

Tab'a baki Nawal tayi duk da tasan cewar gaskiya Aliya ta gaya mata, amman kowa yasan ba zata iya hana Nour komai ba kamar yadda ba zata iya hana Aliyan ba, ita gani take duk abinda duniya zata fad'a akanta indai tasan bata yi ba toh ba wani abin saka damuwa bane hakan yasa bata tattare da damuwa sannan bata shakkar bawa kowa abinta, takan ce ita bata ga dalilin takurawa mutum ba akan irin rayuwar da ya zab'awa kansa. Aliya kuwa duk iskancinta duk abinta bata iya rabar namiji idan ba Sahal ba, shima kuma tun lokacin da ya gama tabbatar da cewar kaunar Fa'iza tayi masa illa ya dena yadda ko mayafin Aliya ya tab'a jikinsa bare kuma takai ga tab'a hannunta,

“Ya zanyi da ita liyaa? Kinsan dai bazan iya hanata ba so kawai ki barta tayi duk abinda zata yi.”

“Nawal ba zaki gane ba, nifa kullum Umma sai tayi mana fad'a kan irin kawayen da zamu dinga yi, takan ce mana abokin d'an iska to d'an iska ne koda baya aikata iskancin mutane ba zasu ga hakan ba, kinga dai mun shaku da Nour kuma farkon shigowarta makarantar nan wallahi ba haka take ba, mune ma muda ke ake yi mana kallan wad'anda zasu aikata abinda Nour take aikatawa, wallahi duk son da nake yiwa Yaya Sahal bazan iya bari mu aikata wani abun ba duk wannan rawar kan nawa da ake gani, nakan tuna idan nayi fa iyayena da suka rigamu gidan gaskiya za'a tashe su a nuna musu duk abinda nake yi, wannan yana daya daga cikin abinda yake sanya min kyamatar fasik'anci ko wane iri ne wallahi.”

Kallanta Nawal tayi taga yadda Aliya take maganar tasan tun daga cikin zuciya tayi maganar, tausayinta ya kuma kamata taji kaunarta har cikin zuciyarta, hannu tasa tare da bubbuga bayan ta tace,

“Tunaninki yayi kyau liyaa duk da ana son mutum yaji tsoran yin abu saboda Allah, idan yaji abin yana neman gazawa toh yaji tsoran idon duniya, idan yaji suma dan su ba zai sanya yaki yin abu ba toh yaji tsoran tozarta iyayensa, ko 'ya'yansa, muyi mata addu'a kawai Allah ya shirye ta, kuma itama idan kika duba duk lokacin da zata gida bata wannan banzar shigar da take yi, zaki samu ta shirya ta tafi tamkar wata mumina.”

Haka suka zauna suna jimamin abinda Nour keyi gashi duk sanda suka yi mata magana sai ta fara rantse-rantsen cewar ba abinda suke tunani take yi ba. Har suka shiga lecture bata dawo ba wayarta ma a kashe kuma sun san ta na da full charge.

A can old site kuwa Fa'iza ce zaune zaune tana kallon hotuna a wayar Raheenah, yawancin styles na dnki sunfi yawa a cikin wayar har sai da ta gaji da gani, fita tayi daga folder d'in ta shiga videos, can daga kasan wasu irin shaidanun videos ne na lesbians sunfi kala goma, jikin Fa'iza ya hau rawa bata tab'a zato ko tsammanin hakan daga wajan Raheenah ba, sai yanzu ta gano manufar yawan hugging din da take yi mata, duk a tunanin Fa'iza bada wata manufa take mata ba ashe da walakin, gashi daman bata bawa kowa wayarta ashe tasan abinda yake cikin wayar ba mai dad'i bane.

“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un..”

Shine kalmar da Fa’izah take ta maimaitawa...

*SWITZERLAND*
*UNIVERSITY OF ZURICH*

Siririn tsaki Shamsudden ya sake ja akaro na ba adadi, yai wa Yazeed kallon kara goma sha biyar ya watsar kafin yace,

“Ina tantama akan ka, domin bakasan menene ma’anar HALACCI a hausance ba, ballanta a aiwatance.. Ka saurare ni sosai ka bani nutsuwar ka, inaso ka kara ilmi sosai a fagen HALACCI.. A turanci kalmar HALACCI na nufin ‘legality’, A al’adar malam bahaushe kuma HALACCI ya kasu kashi na ba adadi, zuciya mai HALACCI bata manta alkhairi komai girman sharri, zaka iya fasalta HALACCI zuwa ma’anar temakekeniya, adalci, kyautatawa, sauyawa daga akasin haka da sauran su, shin wane HALACCI Afrah tayi mun a rayuwa?!”

Yazeed ya sa k’asan biro a kunnen sa yana sosawa, kafin ya shafo ‘keyar sa alamun kunya, cike da borin kunya yace,

“Soyayyar da take nuna maka mana...“

“Hmm! Guy kenan! Tabbas so masifa ne, So jarabta ce, So guba ne, kuma so makaho ne, Domin na ‘dan’dana na san yadda yake, Saboda haka ni zan samu Afrah yanzu, Zan sanar da ita komai, bandama So shirme ne ina ‘diyar sarki ina ‘dan talaka, wanda karatun ma kyauta aka ‘dauki nauyin sa... So intolerable!”

Murmushi kawai Yazeed yayi, Shamsudden ya mike yana harhade papers din dake gaban sa, ya mikawa Yazeed! Yana jaddada masa da cewa,

“Kaje kayi mana submitting pls.”

Kad’a kai Yazeed yayi, ya sa hannu ya karbi takardun dake dauke da rubutu boldly an rubuta.’ Postgraduate diploma in professional intentional law’.. Yana mika masa ya fice bayan ya shafe jikin sa da turaren ‘Calvin Klein’ don Shamsudden akwai iya ado da ‘kamshi, straight ya mike inda yasan Afrah na zama da ‘kawayen ta, ai kuwa nan ya hange ta zaune itada wata baturiya. Tana ganin sa ta nufe shi tamkar zata hadiyeshi don so! Murmushi ya mata, yaja kujera ya zauna, itama ta zauna tana maitar kallon sa, earpiece din kunnen ta zare d’aya tana rairaya bin wak’ar ‘slowly’, Wadda Shamsudden naji yagano don shi takeyi, ta zare dayan ma tana karashe kalaman da,

“Do you believe in love?How crazy it could be! Baby baby stop! Hmm take it easy..When you leave..I swear I can't breathe! Do you really care? Baby s.”

Yai saurin katse ta yana daga hannun sa sama alamun ta dakata, domin shi wakar neman ciwon kai tafara sa shima tsabar batai masa dadi ba, cikin sanyin muryar sa mai dadin sauraro yace mata,

“Afrah...”

“Na’am Pulchritude!”

“What is Love?”

Ya fad’a yana kallonta ta ‘k’asan idanu...Murmushin dake kan fuskar ta, ta kara fadada shi kafin tace,

“Al houb hayaaat.. Love is life, Love is complex set of emotions, behaviors, and beliefs, associated with strong feelings of affections, protectiveness, warmth’s, and respects for another person..”

Kad’a kai Shamsudden yayi, kafin yace,

“So true..! To Menene kalmar soyayya a hausance? Meyasa ake soyayya? Da wa yakamata ayi soyayya?..”

“Soyayya rayuwa ce! Soyayya kamar haduwar jini ce, Soyayya..”

Shiru tai tana lankwasa yan yatsunta, murmushi yayi hade da taune gefen labban sa kafin yace,

“Soyayya nada ma'anoni da dama, amma tafi tsayuwa akan gamon jini, da zarar jinin mutane biyu ya hadu, sai so ya dasu a zukatan su, soyayya wata abace dake shiga cikin zuciya ba tare daka sani ba, kuma itace jigon rayuwa.., Afrah ki sani wallahi baki da wani aibu da namiji zai ‘ki ki, kinada martaba, mutunci, dattako, kyau, sura, Ilimi, uwa uba jinin sarauta ce ke, what more could a man want in a woman? Nothing!, Afrah inaso ki nutsu ki bani hankalin ki, ki kuma tsaya ki dubi kalamai na da idanun basira,

“Kamar yadda kika sani sunana Shamsudden Al’amin Buhari!, Shekaruna a duniya 29!, ni ne na biyu kuma na ‘k’arshe a gidan mu, ma’ana nine auta, Nayi karatun primary da secondary a garinmu na Kano unguwar jakara, na kasance yaro matashi wanda ya tsani karatun boko, Na tsani boko fiye da tunanin mutum, duk wata harkar boko bana yinta, sai wata ‘kaddara tafaru dani, Wadda hakan yasanya dole nai nisa da gida sannan kuma nai ilimin boko ko dan na sake bunkasa harkar kasuwanci da nake so, karatun nan da nakeyi first degree dina wani ‘dan majalisar garinmu ne yai sponsoring dina ta hanyar scholarship, second degree dina danake MBA(master of business administration) sch dinnan ce ta bani scholarship saboda na kai beyond point din da suke bukata, wanda Insha Allahu! Nanda wasu yan kwanaki zamu gama, sai Post graduate diploma in international law da zanyi yanzu for just 6-9 months Insha Allah,

“Iyaye na ba masu hali bane Afrah,

Please Login or Register in order to submit comment