Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nad’a miki na jaki sannan na tasa ‘keyar ki m...”

‘Bai ‘karasa fad’a ba Dijama ta rarrafa ta rik’e ‘kafafuwan sa tana hawaye, cikin rawar baki tace dashi,

“Baba dan Allah kayi hak’uri..”

“Hakurin gidan ku! Zaki bude baki ki gayamin ko kuwa sai na tashi na faffalla miki mari tukun, Idan kika daku zaki fi bayani..”

Ganin ya tashi yana neman abunda zai doke ta dashi yasan ya Dijama fara girgiza kanta, tana daga hannuwa alamar zata fara kwararo bayani, cikin sarqewar murya tace,

“Baba zanyi bayani, wallahi tallahi Hafsat ce ta koyamin shiga harkar malamai, Saboda nace mata Shamsudden baya sona, shine tace aikin sa kamar yankan wuk’a ne, Shi..Shine muka je wajen sa, sunan sa Malam Namuduka. Allah Baba duka-duka sau uku muka je kawai..”

Tunda tafara magana Haj Maryam ke girgiza kanta alamun takaici, gaba d’aya sai duniyar ta sake bata tsoro, ace yarinya ‘karama tasan hanyar bin Malamai? Alhaji Garba ya ‘kara zare mata idanu,

“Shin mahaifiyar ki tasan kina bin malamai?”

“A’a Baba.”

“Toh kiyi min bayani, duk kan tambayoyin da nai miki..”

“Baba garin magungunan na hayaki ne ..d...da..dan janyo hankalin sa gare ni, d’aya kuma barbada masa zanyi a hanyar da zai taka ya wuce, Jinin al’adar kuma..Wa..Wai zai min magani ne na sharrin muguyen da bazasu so muyi auren ba, Jinin kazar kuma hatimi za’ai dad..Dashi na mallaka!”

Tunda tafara magana harta gama bakin Haj Maryam da Alhaji Garba a bud’e yake, Mamaki ne kawai ya cika su, jin kalaman Dijama tiryan tiryan. Baban ne yai ‘karfin halin cewa da ita,

“Kira Hafsat ‘kawar ki kice tazo, karki nuna mata ni ne nace ki kirata, Idan da rabo itama na had’a ku na lakad’a muku na jaki, sannan na kai ‘kararta gurin ‘iyayen ta da ‘yan Hisba abisa koyar dake bin bokaye datayi.”

Dijama ta daga kai, hannunta na rawa ta ‘dau wayarta ta kira Hafsat tace tazo akwal labari tanason ganin ta..Ba’a wani ‘dau lokaci ba Hafsat ta shigo gidan tana karkad’a jiki had’e da jera ‘kwayayen cingum ji kake ‘kas ‘kas ‘kas. Tun daga bakin ‘kofa take dokawa Dijama kira da,

“Kawata! Kina ina ne?”

Dijama tai saurin goge hawayen ta, ta lek’a tana d’aga mata hannu had’e da murmushin yak’e,

“Gani nan, ki shigo”

‘Karasawa Hafsat tayi, Dijama ta kama hannun ta suka shiga ‘dakin Baban atare, Hafsat ta zub’e a gaban Baba tana kwasar gaisuwa, ya amsa ransa a had’e, Ta gayda Maman itama ta amsa babu yabo ba fallasa. Baba ya kalli Dijama da Hafsat ya girgiza kansa cike da takaici, ransa a matuk’ar b’ace yace da Hafsat,

“Hafsat ko?”

“Eh Baba..”

“Shin menene yaja ra’ayin ki kika fara shiga harkar shirka?!”

Gaba d’aya Hafsat sai tasha jinin jikin ta, Ta dubi Dijama taga hawaye ne kawai ke zuba a idanun ta. Bakin ta na rawa tace,

“Shirka kuma Baba?”

“Eh! Had’a Allah da wanin sa kenan, Shin mahaifiyar ki tasan kina huld’a da bokaye?”

“Bokaye Baba?”

“Oh tambaya ta kike yi? Shin wanene Malam Namuduka?.”

Hafsat tai shiru tana raba idanuwa, Baba ya maimata tambayar tayi shiru, Mikewa yayi, Dijama da Hafsat suka cunkushe wuri d’aya duk azaton su dukan su zai yi, Hular sa ya saka, ya janyo mukullin motar sa kafin ya dubi Haj Maryam dake binsa da kallo yace,

“Ku sameni a mota yanzu.”

Kad’a kai kawai tayi, Ta tasa k’eyar Dijama da Hafsat suka shisshiga motar Baban, ya tashe ta suka hau titi, Sannan ya dubi Dijama ransa a matuk’ar bace yace,

“Ina ne gidan bokan da kuke zuwa.?”

Dijama ta kwatanta masa, kowannen su zuciar sa fal take da tarin tambayoyin me zasuyi awajen Malam Namuduka.? Sannu ahankali Baba yake driving har suka ‘karasa gidan Malam Namuduka, sunyi sa’a babu layi mutum d’aya suka tarar yana fita suka shiga, Malam Namuduka ya dashe hakora yana duban su Dijama dasu Baba, Gaisawa sukai da Baba kamar abun arziki, Malam Namuduka ya matsa da ‘kasar gaban sa kusa dasu, Kafin ya dubi su Dijama yace,

“Ai kuwa yanzu na duba zuciar mutumin ki Shamsudden kina ransa yanzu haka ke yake tunani, Tauraruwar ki nata haskaka zuciar sa, Ai hatimin nan naki har anyi kakki ji komai, Kema Hafsat mutuniyar ki takusa shallarawa can.”

Baba ya jaddada kai, Kafin cikin muryar umarni yace da Malam Namuduka,

“Malam kowacce irin duba kakeyi ko?”

Namuduka ya kara dashe yalayen (yellowish) hakoran sa da suka rune tamkar gansa kuka, sai hamamin wari ne ke tashi daga jikin sa, Cikin zana ‘kasar gaban sa ya dubi Baba yace,

“Kwarai kuwa, Meke tafe dakai? Ka kawo kuka gidan share maka shi? Kisa kake so ayi, ko kuwa haukatar da mutum? Kai idan kurciya kake so ko farraqu da raba aure duk muna yi anan..”

Baba yai murmushin yak’e sannan yace dashi,

“Duba min zakai yaushe zan mutu?”

Namuduka ya shiga raba idanuwa, yana jujjuya ‘kasar gaban sa, ya kasa magana, Baba ya sake tambayar sa nanma babu amsa, Baba yai murmushi kawai sannan ya sake cewa dashi,

“Allah ne mafi sani ko? Toh na janye wannan batun, ungo rik’e wayar nan”

Ya karasa fad’a ya zaro wayar sa a aljihu ya mikawa Malam Namuduka wayar, ya karba yana jujjuya ta yana bin Baban da kallon me zanyi da ita? Cikin tunanin abunda zai yi da ita ya jiyo muryar baba yana bashi umarni da,

“Na manta lambobin da nake bude wayar dasu ne, Nasan bude wayar nan ‘karamin alhaki ne agare ka, shine nake so ka cire min ita daga rufen da take..”

Namuduka ya had’iye wani abu daya tsaya masa a mak’ogoro, ya shiga fiffita fuskar sa da hannun babbar rigar sa, gaba d’aya gumi ne ke kwarara ajikin sa, kai da ka ganshi kasan yana cikin ruguntsumi. Ya shiga zana ‘kasar gaban sa da hannu d’aya, dayan kuma yana sharce gumin fuskar sa. Alhaji Garba Taura yayi murmushi irin nasu na manya, Ya dubi Haj Maryam yace,

“Maman su kingani ko?”

Haj Maryam ta jaddada kai kawai, gaba d’aya ta tsunduma cikin duniyar tunani, Sosai yanzu Dijama tsoro take bata.

“Kayi shiru Nasuduka, Shin ‘kasar taka bata gaya maka bane ko kuwa?”

Namuduka ya kasa cewa komai, kansa a ‘kasa yana raba idanuwa. Alhaji Garba Taura ya sake cewa dashi,

“Kai ko kunya baka ji Boka? Ni mahaifin Dijama ne, yarinya ta da kuka koyawa zuciar ta yarda da ‘karairakin tsibbuncen ka, Kasani har gaban abadan ba zan tab’a yafe muku ba, munyiwa yarinyar mu tarbiyya kun tarwatsa ta, daga ita har Hafsat wadda ta kawota nan nayi imani itama a gidah ba’asan tana yawon bokaye ba, Ka hau buzu ka tara uban gashin baki, ‘kasa agaban ka kana fadar ‘karairakin banza da wofi, Kana shagub’e da hawa *IGIYAR ZATO* (sabon littafi na mai zuwa) zato zunubi ko daya zamto gaskiya, kana kasan gaibu, Toh kasani babu wanda yasan gaibu sai Allah duk duniya, ballanta na kai karan kad’a miya dillalin kashi, makaryaci mamugunci, me aiki da aljanu da miyagun shad’ainu, Tir da hali irin naka da masu biye maka, kuna cinyewa mutane kudi ta hanyar cewa sukawo kaji za’ai aiki, duk munsani cinyewa kuke yi kuda iyalan ku. Toh kasani Allahu Gafurur Raheem ne, tun wuri ka nemi yafiyar sa ya yafe maka, domin shi d’in mubuwayi ne gagara misali. Kasani shirka had’a Allah da wanin sa ne, Ka tuba izuwa gare shi, ta’iya yiwuwa ya yafe maka kai da magoya bayan ka. Ku tashi mu tafi ku kuma..”

Yana gama fad’a ya fice, su dijama suka bi bayan sa suna hawayen nadama. Kai tsaye suka koma hanyar gidah, akan titin Maiduguri Road, Baba ke tambayar Mama kwatancen gidan su Malama Bintu, Nuna masa kwanar tayi, ya shiga da kan mota kansa tsaye.

*HOTORO NNDC QUARTERS*

Da misalin ‘karfe shida saura Shamsudden ya koma gidah a matukar gajiye, yana shiga ya tarar da Ummah na had’a kayan wankin su, Bala me wankin su yana tsaye yana jiran Umma tagama had’a kayan wankin ya ‘dauka, Zannuwan gado (bedsheets) da barguna na rufa (duvets) da sukai datti sutake ta hadawa, ciki har dana Shamsudden. Tana cikin zazzagar da pillowcase na Shamsudden taji kamar zobe aciki, Shamsudden da dawowar sa kenan ya zauna a wajen su Umman akan kujera yana shan ruwa, Ummah dake zura hannunta cikin pillown Shamsudden tana neman kullin abun da taji aciki tace dashi,

“Auta meka zura acikin rigar pilon nanne? Yaki ciruwa”

“Babu komai first love, Kilan dai sosan ciki ne.”

Ummah ta zaro abun, A hankali ta fito dashi, me zata gani? Laya ce tasha ‘dauri ta farin zare farace tas, Kallon kallo sukai da Umma, ta nemi kujerar kusa dashi ta zauna tana ‘ko’karin warware ta,

“Ko kai ka ajiye?”

“Laya fa ummah, A’a wallahi bani bane.”

“Toh! Allah ya rufa asiri, Bari na warware ta mugani.”

Bala dake tsaye yai saurin dakatar da Ummah ta hanyar cewa,

“Hajia kakki bud’e, bani nagani.”

“Toh ‘dan Malam.”

Mika masa tayi, ya karba yana kiciniyar warware zaren, A dai-dai lokacin su Haj Maryam suka shiga suna sallama, su Ummah suka amsa suna binsu da kallo, Shamsudden ya sake ‘daure fuskar sa tamau, duk azaton sa maganar auren ce takawo su, ganin rannan Dijaman tayi masa message wai ta amince za tai masa HALACCI ta aure shi. Ciki ciki ya gaishe su ganin har da baban Dijaman aciki, da wata budurwa kamar Dijama data tsura masa idanu tana binsa da mayataccen kallo. Parlorn Abba suka ‘karasa suka shiga, shima bai jima da dawowa daga wajen aiki ba, yana kallon news a TV. Gaisawa sukai da Baban su Dijama suka shiga hira dake sun san juna ta sanadiyyar matan su dasuke aminta!

Bala daya gama warware layar ya jima yana karanta rubutun cikin layar, Kansa tsaye ya shiga cikin parlorn yana cewa da Ummah,

“Hajia na warware layar..”

“Laya kuma?!”

Abban su Shamsudden ya tambaye ta yana binta da kallon ‘karin bayani, cike da jimami tace,

“Eh wallahi Abban su laya ce muka gani acikin pillown Shamsudden, Dan Malam zai wanko zannuwan gadon sai gata aciki, shine yace na bashi ya warware.”

“Toh Allah ya rufa asiri!”

Abba da Alhaji Garba suka had’a baki wajen fad’ar haka. Abba ya dubi Bala yace dashi,

“Yawwa dan Malam dan duba kagani, tunda fannin ku ne.”

Bala ya bude layar yana nuna musu cikin ta, da akayi rubutun da jini, wasu irin zane akayi cikin zanen kuma ‘dauke yake da sunan Shamsudden da Khadija, batare da ‘bata lokaci ba Bala yace,

“Alhaji layar mallaka ce, mai ‘karfin gaske, da akayi amfani da jinin farar saniya, anaso a mallaki zuciyar Yaya Shamsudden ta ‘karfi da yaji, ya zamto babu wanda zai so, so mai tsanani yafi na ku mahaifan sa fyace ita wannan wadda tayi layar, Gashinan dukiyar sa ma anyi hatimin da zai sadaukar mata da ita duka, ya zamto ko kara ta ajiye ba zai iya tsallawa ba sai yadda tayi dashi, duk abunda tace dole sai yayi. Gashinan hatimin ‘dauke yake da sunan sa da naku duka harda na yaya Garzali....”

Tunda yafara magana parlorn yayi tsit, Khadija kuwa hawayen nadama kawai take yi, ga kunya dukta cukwikwiye ta, Shamsudden yana hankalce da ita, gefe d’aya kuma dadi ne ya mamaye shi jin yanzu ya samu mafukar da zai ‘ki auren ta gaba d’aya batare da wani had’a zance ko karya ba. Abban su yai shiru yana kallon Bala, Alhaji Garba kuwa yasan da haka dama shiysa cikin umarni yace da Bala,

“Dan Malam ko?”

Bala dake tsaye yana jujjuya layar a hannun sa yace,

“Eh Alhaji..”

“Yawwa! Sunan yarinyar ko matar datai layar Khadija Garba Taura ko?”

Gaba d’aya sai kallo ya koma kan Alhaji Garba, Haj Maryam kuwa hawaye kawai takeyi, Umman Shamsudden tayi zurum tana duban Khadija, Bala ya sake gwale ido ya karanto sunan, cikin daga kansa alamun Eh yace,

“Tabbas! Sunan yarinyar Khadija Garba Taura, daga ‘kasan hatimin kuma an rubuta billaqnin (laqanin) Dijama...”

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un. Dijama wai hakane.?.”

Ummah ta tambayi Dijama, Dijama ta d’aga kai alamun Eh. Alhaji Garba yai gyaren murya kafin ya kwashe komai ya gaya musu har zuwa gidan Malam Namuduka da sukai da yadda sukai dashi, Ya kark’are da,

“Ranar da takawo miki meat pies a ranar ta sanya layar cikin matashin kan shi Shamsudden din, Saboda haka ni Alhaji Garba mahaifin Khadija na haramta aure tsakanin ta da Shamsudden ko bayan rai na akayi ban yafe ba, Wannan yarinya me suna Hafsat ita ta ‘dora ta akan komai, Saboda haka ku bude kunnuwan ku, dama banyi muku nasiha bane agidah saboda yadda zucia ta take daxun zan iya raunata ku, kuma ke Hafsat yanzu muna barin gidan nan zaki kaini gidan ku, zan zayyanewa mahaifiyar ki komai, Allah ya jikan mahaifinki da rahama, da yananan ba zaiso yaga wannan bakar ranar ba, Amma dukda haka zanyi tsayin daka wajen ganin mahaifiyar ki ta yarje na bada auren ki sadaqah, da ke da Dijama In sha Allahu indai ina numfashi sai anyi auren ku, na ba daku sadaqah,

“Kun san Hukuncin sihiri, da bokanci da abunda suka ‘kunsa? To ku sani baya halatta ga ko marar lapia ya je wajan bokaye da suke ikirarin sanin abubuwan da ke boye, wai don ya gano masa rashin lafiyansa, kamar yadda baya halatta ya gasganta su cikin abinda su ka bayar da labarin sa ba, domin su suna maganine ko kuma su kirawo aljanu domin su taimaka mu su akan abinda su ke so, to wadannan hukuncinsu shi ne ‘kafirci’ idan sun yi ikirarin – ilimin gaibi, hakika Muslim ya ruwaito cikin ingantaccan littafinsa, lallai Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce;
((من أتى عرافا فسأله عن شيء لم تقبل له صلاة أربعين يوما))

Ma’ana: “Duk Wanda ya je wajan dan’duba sai ya tambaye shi wani abu to ba za’a karbi sallar sa ba ta kwana arba’in”. Kuma daga Abuhuraira Allah ya kara masa yarda daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace:

((من أتى كاهنا فصدقه بما يقول فقد كفر بما أنزل على محمد صلى الله عليه وسلم)).

رواه أبو داود وخره أهل السنن وصححه الحاكم عن النبي صلى الله عليه وسلم بلفظ ((من أتى عرافا أو كاهنا فصدقه بما يقول فقد كفر بما أنزل على محمد صلى الله عليه وسلم)).

“Ma’ana: “Duk wanda ya je wajan boka sai kuma ya gasganta abinda ya ke cewa, to hakika ya kafircewa abinda aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi”. Abu dawud ya ruwaito shi kuma ma’abota littattafan sunnah hudu sun fitar da shi, kuma Hakim ya ingantashi daga Annabi tsirada amincin Allah su tabbata a gareshi da lafazin:
“Duk wanda ya je wuri dan’duba ko boka sai ya gaskanta abinda yake cewa to hakika – ya karficewa abinda aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agare shi”.
Kuma daga Imran dan Husaini Allah ya karama sa yarda ya ce: Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce:
((ليس منا من تطير أو تطير له أو تكهن أو تكهن له أو سحر أو سحر له، ومن أتى كاهنا فصدقه بما يقول فقد كفر بما أنزل على محمد
ﷺ‬)). رواه البزار بإسناد جيد

“Ma’ana: “Baya cikimmu duk wanda ya ke yin camfi ko a ke yi masa camfi ko ya yi bokanci ko ake yi ma sa bokanci, ko ya yi sihiri, ko ya sa ayi mishi sihirin, duk kuma wanda ya je wajan boka sai ya gaskantashi a aduk abinda yake cewa to hakika ya kafircewa abinda aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi”. Bazzar ne ya ruwaito shi da Isnadi mai kyau.
“ saboda haka ku sani, A cikin wadan nan hadisai masu girma akwai hani game da zuwa wajan ‘yan’duba da bokaye da masu sihiri (asiri) da makamantansu, da kuma hukuncin tambayarsu da kuma hukuncin gasganta su da bayanin narkon azaba akan haka. Domin hakika manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi hani akan zuwa wajan su da kuma tambayar su da gaskanta su, domin abinda ke cikin haka na muni maigirma da hatsarin da ya ke babba da mumunar makoma kuma domin lallai su makaryatane fajirai, kamar yadda ya ke cikin wad’annan hadisai dana baku, wadannan Hadisai dalili ne cewa boka kafirine da mai sihiri domin su biyun basu cimma manufar su sai ta hanyan yi wa aljanu hidma da bauta musu koma bayan Allah kuma wannan kafurcewa Allah ne da kuma yi masa tarayya – tsarkakken sarki,

“Kuma mai gasganta su cikin abinda su ke cewa na sanin gaibu ya kasance kaman su ne, kuma dukkan wanda ya karbi wadannan al’amura na abinda su ke bayarwa to hakika Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya barranta da shi, kuma baya halatta ga musulmi ya yarda da abinda su ke rayawa cewa magani ne. Domin lallai wannan yana daga cikin bokanci da rudar da mutane, kuma wanda ya yarda da hakan to hakika ya taimaka musu akan barnarsu da kafircin su,
Hakanan kuma baya halatta ga wani mutum musulmi ya jewajansu – domin ya tambayesu gameda wanda. Zai aurar da dansa ko wani makusancinsa ko kuma abunda ke iya kasancewa tsakanin ma auratan biyu da danginsu na soyayya da cika alkawari ko kuma kiyayya da rabuwa da makamantan haka;domin wannan yana daga cikin gaibi wanda babu wanda yasansu sai Allah tsarkakke mada’au kaki.

“Kuma sihiri yana daga cikin abubuwa haramtattu na kafirci kamar yanda Allah mai girma dad’au kaka yace cikin sha’anin mala’I kunnan biyu cikin suratul Bakarah: ﴿وَٱتَّبَعُواْ مَا تَتلُواْ ٱلشَّيَطِينُ عَلَى مُلكِ سُلَيمَنَ وَمَا كَفَرَ سُلَيمَنُ وَلَكِنَّ ٱلشَّيَطِينَ كَفَرُواْ يُعَلِّمُونَ ٱلنَّاسَ ٱلسِّحرَ وَمَا أُنزِلَ عَلَى ٱلمَلَكَينِ بِبَابِلَ هَرُوتَ وَمَرُوتَ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِن أَحَدٍ حَتَّى يَقُولَا إِنَّمَا نَحنُ فِتنَة فَلَا تَكفُر فَيَتَعَلَّمُونَ مِنهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِ بَينَ ٱلمَرءِ وَزَوجِهِ وَمَا هُم بِضَارِّينَ بِهِ مِن أَحَدٍ إِلَّا بِإِذنِ ٱللَّهِ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُم وَلَا يَنفَعُهُم وَلَقَد عَلِمُواْ لَمَنِ ٱشتَرَىهُ مَا لَهُ فِي ٱلأخِرَةِ مِن خَلَق وَلَبِئسَ مَا شَرَواْ بِهِ أَنفُسَهُم لَو كَانُواْ يَعلَمُونَ١٠٢﴾

Ma’ana: “Kuma basu sanar da kowa ba balle suce: mu fitina kawai ne, saboda haka ka kafirta,” balle har suke rarrabwa tsakanin mutum da matarsa dashi daga gare su. Kuma su (masu yin sihirin) basu zama masu cutar da kowa da shiba, face da iznin Allah. Kuma suna neman ilimin abin da yake cutar da su, kuma baya amfaninsu, kuma lallai ne, sun sani tabbas wanda ya saye shi, baya da wani rabo lahira. Kuma tir da abinda Suka sauar da raukansu da shi, da sun kasance suna sani)). Suratul Bakara, aya ta: 102,

“Sai kuma waccan ayar maigirma da ta yi nuni akan cewa lallai masu sihiri suna raba tsakanin mutum da matarsa. Kamar yadda ta yi nuni kuma cewa lallai sihiri baya tasiri don karan kansa ta fuskar amfanarwa ko cutaruwa, sai dai yana tasiri ne da iznin Allah wan ya riga ya kaddara kuma ya kasantar, domin lallai Allah tsarkakke madaukaki shi ne ya halcci alkhairi da sharri, hakika cutar ta yi girma kuma zaluncin ya yi tsanani ga wadannan masu kirkirar, wadanda su ka gaji wadan nan ilimomi daga mushrikai su ka zo suka rikita masu raunin kwakwale da su, lallai mu daga Allah mu ke kuma lalle mu gare shi zamu koma, Allah ya isar mana kuma madalla da wakili wanda yake shi ne Allah.,

“Ma’aikin Allah ﷺ‬ Ya sake cewa kuma

((من أتى عرافا أو كاهنا فصدقه بما يقول فقد كفر بما أنزل على محمد صلى الله عليه وسلم)).

“Ma’ana: “Duk wanda ya je wajan danduba ko boka sai ya gaskanta shi da abinda ya ke cewa to hakika ya kafircewa abinda aka saukar wa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agare shi”

“Anan zan dakata, ku sani duk wannan ayoyi da hadisai na kawo su ne domin ku, saboda ku tabbatar abunda kukeyi ba mai kyau bane, babban shirka ne, ko da nan gaba hakan zai zamto silar shiryuwar ku, Ta haka har Allah yasa ku janyo ra’ayin masu hali irin naku, zuwa turbar gaskia. Abunda na fada dai-dai Allah yabamu ladan, kura-kuren dake ciki rabbi yayafe min.”

“Ameen...” suka had’a baki d’aya wajen cewar hakan.

Mik’ewa Alhaji Garba Taura yayi, Abban su Shamsudden yace dashi,

“Alhaji kar kayi haka, shirmen sune irin na yara.”

“Wai kana nufin nabar Dijama ta auri Shamsudden?”

Abba ya kad’a kai alamun Eh, Alhaji Garba Taura yai murmushin yak’e kawai kafin yace,

“Ai Dijama ‘dan Kano ma banajin zan bari ta auri wani ta cuceshi, Jigawa zan tasa ta agaba muje, acan zan samu wani almajirin na had’ashi da ita..”

Shamsudden najin haka yayi wani smirking face kafin yace da Alhaji Garba,

“Baba na yadda zan au..”

“Karka soma wallahi tallahi billahi Khadija ba zata aure kaba, kai ko wannan ‘dan Malam da kuke kira Bala bazan bari ya aure ta ba...”

Shamsudden ya koma ya zauna kamar gaske, Ummah dai takasa magana, gaba d’aya tuno ranar da Khadija tace zata gyara ‘dakin Shamsudden take, Ashe yarinyar muguwa ce, Sumi-sumi da ita ba Allah a zuciar ta. Haj Maryam ta yi mata sallama itama duk a takure, Tabi bayan Alhaji Garban suka tafi. Khadija da Hafsat na binsu a baya, Suna fita Alhaji Garba yasa Hafsat tayi masa kwatancen gidan su, suka d’au hanyar, Toh Allah ya sauwake, wannan shine taga SAMU DA RASHI.. Allah ya tsaftace mu daga aikata SHIRKA, ya nisanta mu da duk abunda zai ‘kunshi SIHIRI! Domin komai nisan dare gari zai waye, Allah zai bayyana mai gaskiya, Toh ga gaskiya ta bayyana, Koda kuwa Allah bai fallasa asirin mutum ba, Toh gidan fa biyu ne, Akwai lahira.. Allah kai mana kyau.

Gaba d’aya su Abba da Ummah maimata zancen suke yi, Ummah ta basu labarin yadda su kai da Dijama ranar da zata saka layar. Koda Ya Garzali yazo sai da aka sake tisa zancen, daga ‘k’arshe Abba yace da Shamsudden,

“Tunda abun ya zama haka, Auta ka nemo yarinyar da kake so da kan ka, ayi magana da manyan ta, a aura maka ita...”

“Gaskia dai, Allah ya baka mata ta gari.”

Cewa Ummah, tana sake jaddada kai, gaba d’aya halayen Dijama sai suka shiga mata yawo a ‘kwa’kwalwa, Garzali dake gefe ya dafa kafad’ar Shamsudden yace dashi,

“Gaskia ne CEO, Allah ya baka mata, yar auta irin ka, ku taru ku shagwaban ce..”

Shamsudden yayi wannan tsadadden murmushin nasa da gefen kumatun sa ke lob’awa (dimples). Mikewa yayi har ya kai bakin kofa yace,

“Ameen Ya Rabbi! Tunda dai an fasa mun auren dolen ai shikenan,beside na kusa magana ma akan wadda nake so, duk kunsan yarinyar ma........”

Yana gama fad’a yai fucewar sa, Su ummah suka sa daria, Ummah tasa Bala yai kwalemar dakin Shamsudden gaba d’aya aka wanke shi aka gyare tsaf, gudun ko Dijama ta binne wani abun. Bala ya kira abokan sa suka sauke alqur’ani agidan baki d’aya...

ALIYA

K'arfe biyar saura Aliya ta shiga gida jikinta a sanyaye, daman tun asuba da Fa'iza taje gaida su Baba Suleiman yake tambayarta ina Aliya nan ta sanar dasu cewar ai ta tafi gurin siwes, Baba Suleiman ya jinjina kai yasan tayi hakan ne saboda tana cikin fushi da kuma bakin cikin abinda ya faru tsakanin ta da Sahal, shi yasa da zai tafi gurin aiki sai da ya biya ya tabbatar da tana ciki sannan ya wuce ba tare da kowa yasan cewar yabi sahunta ba.

Aliya na dawowa, Jakarta ta rataye sannan ta zare hijabin jikinta ta cillashi cikin kayan wanki duk da cewar wankakke ne yau tasa shi amman jin Shamsuddeen yace mata d'oyi take sai tayi zaton ko a jikin hijabin ne. Fa'iza ce ta shigo d'akin hannunta d'auke da plate ta zuba shinkafa da wake da salad da tumatur ga albasa akai gege d'aya yaji ne da yake ta kamshin tafarnuwa, ta ajiye a gefen gadansu tare da satar kallan Aliya wace take k'ok'arin cire riga.

“Sissy ga abinci na kawo miki kici.”

Abincin da yake ajiye idan ya tanka toh Aliyah ma ta tanka, wani irin takaicin Fa'iza takeji a ranta gashi yanzu tana neman raina mata wayo. Ji tayi Fa'izan sai damunta take yi akan tazo taci abinci hakan yasa sai da ta d'aura zani zata wanka ta kalleta idanunta duk sun kankance saboda tsabar kuka sannan tace.

“Banaci.”

Tayi maganar tana shirin barin d'akin, Fa'iza ta waigo tana kallanta tare da cewa.

“Kiyi hakuri Sissy amman wallahi ban san cewar Sahal shine Muhamman....”

Bata kaiga karasa maganar ba itama Aliya tayi saurin dakatar da ita, zuciyarta na rawa

Please Login or Register in order to submit comment