Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaba da abinda take yi.

Fa'iza ana yin sadakar bakwai ta koma gida saboda school, nan tabar Aliya wacce take jin nan kauyen yafi mata ko'ina duk da cewar basu da wutar nefa amman tafijin dad'insa fiye da can gashi wajan siwes d'in ma dasu Nawal suke zaton zataji dad'i sam baya mata saboda Shamsuddeen. A kwanaki na goma sha biyar ne Yazeed yayi mata text message akan cewar ya kamata ta dawo gurin aikinta karta samu matsala dan yaga kamar Shamsuddeen ya shak'a tun ranar da yace zai cire ta daga matsayin sakatariya ya dena yi masa wasa da dariya sai dai gaisuwa kawai itama kuma Yazeed d'in ne yake fara yin ta.

Babu yadda ta iya haka ta tattaro ta baro baffa da sauran 'yan uwa suna ta yi mata fatan alkairi. Ranar data shirya komawa gurin siwes bayan ta gama shiryawa ta yiwa su Umma sallama ta nufi k'ofar gida, mai napep d'in ta yau bai zoba saboda matarsa da take can asibiti zata haihu. A kafa ta nufi bakin titi tana tafiya tana addu'a kasan cewar safiya ce garin babu mutane sai ma'aikan office dake da wucewa a ababan hawansu. Tana ta tafiya kawai taji anyi parking d'in mota a gefenta, gabanta ya buga ta fara kamo addu'o'i tana yi dan ita ta tsani taji ance za'a rage mata hanya.

Fitowa mai motar yayi yaje gabanta yana yi mata sallama, amsawa tayi domin idan tayi rashin kunya namiji ne zai iya yi mata duk abinda yayi niya. Guy d'in kwanaki ne daya tab'a taresu ita da Fa'iza lokacin zasu makaranta har Sahal yazo yace shine zai kaisu. Ganin yadda take d'aga kai shine ya tabbatar masa da gane mai napep take nema dan haka ya had'e hannayensa guri d'aya tare da cewa.

“K'anwata badan na isa ba, ba kuma dan nakai matsayin ba a'a saboda kimarki da mutuncinki na d'iya mace, please ki bani dama wajan tayaki kare martabarki kizo nayi alkawarin kaiki duk inda zaki je please karki ce a'a dan Allah.”

A hankali ta d'ago ta kallesa, matashin saurayi ne wanda alamunsa suka nuna cewar ba d'an talaka bane. Black beauty ne ita kanta sai da ta kyasa domin babu makusa a tattare dashi, kallon titi ta kuma yi ganin babu masu napep d'in ne yasa ta yatsina fuska tare da cewa.

“Kiyi min alkawarin ba zaka cutar dani ba, idan kuma ka cuce ni kaida rabbil izzati.”

“Insha Allahu bazan cuce ki ba.”

Gyad'a kai tayi sannan tayi bismillah ta bud'e ta shiga, shima cike da murna ya zagaya ya shiga ya tada motar, sai da suka fara tafiya sannan ta gaida shi ya amsa tare da fara bayani kai kace ta tambayesa.

“Sunana na Mu'azzam Usman birnuwa, nine na biyu a wajan iyayen mu, nayi primary da secondary school d'ina a garin katsina sannan na taho nan Bayero university kano (BUK) nayi degree na d'aya dana biyu yanzu ina aiki a karkashin kamfanin mahaifina wanda kusan zance duk ni nake kula da komai, ina fatan kema zanji takaitaccen tarihinki idan babu damuwa?”

Murmushi Aliya tayi jin yadda yake mata bayani tamkar tazo d'aukar darasi, cikin sassanyar muryar ta yaji tace.

“Suna na Aisha ana kira na da Aliya, zan gaya maka ragowar nan gaba.l

Yayi murmushi tare da fadin.

“Kinji ki, wannan ai wayo ne, amman babu komai a sannu sannu zan sani d'in. Yanzu dai ina ta kwararo magana baki sanar min inda zan kaiki ba

Murmushi Aliya tayi tare da cewa.

“LIBROS/CAFFE24(SAB PENTHOUSES AND MORE).”

Tana gaya masa ya gano wajan nan da nan kuwa ya nufi kaita suna yi suna hira har sukaje, tana fitowa daga motar bayan ta yiwa mai motar godiya kawai suka had'a ido da Shamsuddeen wanda mai napep ya diresa. Bai tab'a jin haushin rashin mota ba sai yau, aikuwa taje ta wuce ta gabansa kai kace itace shugabar gurin, Shamsuddeen yaji tamkar yaje ya shako mata mayafin jikinta saboda b'acin rai.....


JIGAWA
DUTSE

Gwani Shehi Qasimu yai shiru na ‘yan wasu lokuta kafin yace da Alhaji Garba Taura,

“Kana ganin idan aka yiwa yarinyar nan auren dole ba’a shiga hakkin taba?”

“Hakki fa kace? Wane hakki aka tauye wa mai aikata shirka? Kuma hakan da zanyi ceto rayuwarta ne daga kogin halakar da kanta data faaad’a. Kuma ni anawa k’aramin tunanin nasan budurwa zab’a mata miji ake, Bazawara kumw ta zab’a da kanta kamar yadda koyarwar musulunci tazo. Wannan zamanin dai ne akai fatali da zancen ko ince yaran wannan ‘karnin sun bad’awa idanuwan su ‘kasa basa yadda, Idan har kaji koka ga anyi, Toh auren dole zakaji ana cewa, Kuma abunda yasa na kawo kukana wajen ka na yaba da hankali da nutsuwar almajiran ka ne, Amma idan har kaga bazeyiwu ba toh karkaji komai kar kuma ka tilastawa kanka, Zan gwada sa’a ta a wani wajen..”

“Eh hakane gaskia, Allah ya shige mana gaba Alhaji, Na kuma ji da’di ‘kwarai da gaske, Yanzu abunda za’ai shine akwai ‘daya daga cikin ‘kolon almajiri na mai suna Lado. Yaran nan yanada hankali da nutsuwa ‘kwarai da gaske, kuma mahaddacin AlQur’an ne ya kuma rubuta shi tun bara, Domin yayi primary school ma. Kaga yanada ‘bangaren boko duk kuwa da yawa. ‘Dan asalin ‘kauyen rano ne, Mahaifiyar sa tana can, almajiran ta ce takawo shi nan jihar tun yana shekaru bakwai a duniya, Mahaifin sa marigayi Malam Mudi aboki ne agare ni, domin tare mukai almajiran ta aure ne ya raba mana gari, Ya rasu shekarun baya, bayan rasuwar sa ne, Mahaifiyarsa Hansai takawo shi waje na, kan na rike shi har auren sa, domin yanzu haka tayi wani auren ma, kuma dama ‘ya’ya biyu ALLAH ya azurta su dasu , Daga shi Lado sai ‘kanwarsa Harira tayi aure tana ‘kauyan daka tsalle. Shekarun Lado ashirin da takwas yana sana’ar gyaren takalmi da gyaran farce, Shin zata iya auren sa a haka?”

“Me ze hana ta aure shi? Yaro matashi mahaddacin alqur’ani ga kuma sana’a yanada ita, da me tafi shi? Wallahi babu, shine ma nake tunanin kada a shiga hakkin sa tunda shi namiji ne yana da damar wadda zai zab’a..”

“Toh Ma Sha Allahu! Abu yayi kyau, Dan kuwa Lado ba shi da wata wadda yake so, Saboda kwanaki nayi masa magana, lokacin da zan aurar da yaron waje na, Yace min ba shida wadda ya tsayar, Idan kuwa hakane, kaga abu yazo da sauki..”

“Alhamdulillah! Hakan yayi, Sai yazo su fara dai-daita kansu, Dan banason a ‘dau lokacin bikin..”

Haka dai suka cigaba da tattaunawar su, Gwani ya aika aka kira Lado Alhaji ya zanta masa komai, Lado ya amince hade da adduar Allah ya basu zaman lapia idan anyi, Alhaji yasa Lado agaba suka tafi gidan sa, Yace ya jira a parlor zai turo masa Dijaman, D’akin da Dijama ke kwana Alhaji Garba ya shiga ransa a ‘bace, Tana zaune akan katifa tana hawaye, domin kullum cikin kuka take, tana nadamar abubuwan data aikata, Tana ganin sa tai hanzarin goge hawayen dake kwarara a fuskar ta, Sosai ta rame ba kad’an ba sai uban ‘kashin wuya, tayi duhu kuma, kallo d’aya zakai mata kasan tana tattare da damuwa, Ga yar wayar da take chatting Baban ya ‘kwace ya kyautar, layin kuma ya taune ya jefar. Cikin rawar baki tace,

“Baba! Sannu da dawowa.”

“Sannu! Kije parlor na bak’o yana jiran ki, ku gaysa da mutunta ka, wallahil Azim idan ya fadamin kin masa wulakanci sai na karairaya ki a gidan nan..”

“Toh Baba zan je, In Shaa Allahu bazan masa ba.”

Gyad’a kai yayi ya fita daga ‘dakin, zuciyarta sai dukan uku uku take tana tunanin ko dawa ya had’ata oho, kilan ‘dan abokin sa ne, wata zuciyar ta gaya mata. Hijabi ta zaro ta zura ta shafa Vaseline a lebanta ta tafi parlorn Baba, Tun daga bakin kofa ta jiyo tsamin warin ranar jikin sa, kusan wasu almajiran sai a hankali su da tsafta sunyi hannun riga, wani baya wanka sai jumu’ah jumu’ah ko a wata sau biyu, shiga parlorn tayi bakin ta’dauke da sallama, akan kujera ta hangeshi sai jera hamma yake akai akai, sanye cikin riga da wando na shadda farare sunci uban datti. ‘Kasan wandon nan yasha datti, gefan aljihun gaban rigar sa ya yage. Ba hula a kansa kannan yayi ‘kuda kuda ya hada datti. Fari ne shi amman wahala ta maidashi baki, yanada kyawunsa dai dai misali, yafi ta tsawo amman ba can ba. Idanuwan ta suka sauka akan farcen’kafar sa dana hannu da suka had’a uban datti gasu zak’a-zak’a bai yanke ba, Gaba d’aya takasa magana ganin yasanya hannun sa acikin hanci yana ‘kwakwular tasono yaja majina ya had’iye ya goge tasonon daya kwakwula a rigar sa, wani dogon salati Dijama taja, cikin ware idanu tace dashi,

“Kai ne bak’on da Baba yace zamu gana?”

Cikin lankwasa harshe irin na mahaddata alqur’ani da suka kwankwadi romon sa yace,

“Assalamu Alaikhi Ya Khadija! Na’am! Nine bak’...”

Bai ‘karasa ba Dijama ta kurma uwar kururuwa ta ‘dora hannuwan ta akai hade da sakin wani marayan kuka cikin tashin hankali tace,

“Wayyo Allah na Baba! Kayi min rai, dan Allah karka had’a ni da ‘kazamin mutumin nan, wa...”

Hajia Ayshatu da Alhaji Garba dake ‘dayan parlorn suna hira suka kwasa da gudu sukai kan Dijama, duk azaton su wani tashin hankalin ne ya faru, jin kalaman da take fad’a Alhaji Garba ya faffala mata mari, Tuni cikin zucia yai waje ya karyo karan bishiya yayi kanta da sauri yafara zuba mata ajikin ta, dakyar Haj Ayshatu ta hanashi, ransa a matuk’ar ‘b’ace ya dubi Dijama yace,

“Wallahi summa tallahi kika bari kunnuwana suka ‘karo jiyo irin maganganun yau daga fatar bakin ki wallahi sai na lahira ya fiki jin dadi, sakarya wadda batasan HALACCI ba..”

Dijama sai hawaye takeyi tana fa’din wayyo ‘din wahalar tular data sha, Lado sai hak’uri yake bashi, gashi soyayyar Dijaman kamar almara takama zuciar sa, Sai binta yake da kallo yana ayyono zaman auren da zasu yi, yaci alwashin gyara kansa domin samar mata farin ciki, Alhaji Garba sai haki yake tamkar shi aka tula, ya dubi Lado daya zubawa Dijama idanu yace dashi,

“Kai Lado jeka kacewa Gwani ya turo manya gobe idan ALLAH yakai mu a saka rana, domin banason bikin naku ya wuce ‘karshen watan nan..”

Ya amsa da Toh, Sannan ya zub’e yayi masa godia, cikin sauri ya fice ya nufi wajen malam dan sheda masa abunda Alhaji Garba yace. Alhaji Garba bayan fitar Lado d’akin sa ya koma ransa a matuk’ar’bace, Haj Ayshatu ce kawai ta rarrashi Dijama kafin itama takoma wajen Alhaji Garban. Nan suka bar Dijama a yashe a tsakar gidah tana rera kuka mai tsuma zuciar duk wanda ya saurara..

Toh duka-duka anan nima zan dasa ayar sashen Dijama, Fatana dai Allah ya basu zaman lapia da mijin ta Lado. Masu hali irin na Dijama ALLAH ya shirya yasa kuma su hankalta da sanin Allah shine mamallakin kowa da komai, boka ko Malam wallahi basu isa su sanar da kai gaibu ba ko cika maka burikan ka, Fyace ALLAH qadirun Ala manyasha’u ya zartar da hakan meyiwuwa ne. Allah ya’kara shirya mu ya ‘dora mu akan hanya madaidaiciya................

_Ina labarin Malam Namuduka? Tab tuni sihirta sihirtaccen aiyukan da yake yi ya ‘ballowa kansa ruwa. Budurwar Aljana ta dire tsallen albarkar sai shi zata aura, Malam Namuduka yayi NADAMA da dana sanin aikin tsibbu daya jefa kansa, ya rok’e su suyi hak’uri su nema mata wani, iyayen ta sukace tunda Aljana Sharhabilaiiye’ ‘diyar Numarudu ‘dan sarkin Aljanun kogin Chad tace sai shi to babu makawa dole sai anyi auren nan, Da ya saka gardama sukai masa kiranye ya koma can chadi da sabuwar amaryar Aljana sharhabilaiye. Iyalan sa sunyi tir da hali irin nasa, domin dama matar sama data zo neman temako wajen sa shine ya asirce ta ya aure ta, Mutane mabiyansa najin abunda ya faru dashi suka yiwa gidan zobe hade da kafa ‘kahon zukar nacin wai suna binsa kudad’e na ayyukan dayace zai magance musu, Daga ‘karshe iyalan sa sai dillalai suka nemo aka saida gidan sa da shi kad’ai ya mallaka aka rabe musu ku’din, babu wanda ya samu gadon sa. Dama gida daya ya mallaka domin duk tarin kudin da yake samu a tsiyace suke tafiya don ba albarka tunda kud’i ne yake samun su ta hanyar aikata aikin haram. Toh Allah ya kyauta, ya Rabb ka nisanta mu da aikata aikin shirka, cin haram dama sauran mugayen gurbatattun halaye, Ameen ya hayyu ya qayyum_

_Toh Hafsat ma dai anata ‘bangaren tana cikin tsaka mai wuya domin duk tarin samarinta mahaifiyar ta ta hanasu zuwa, domin datai bincike duk masu kyawun hali ne kuma ta tabbatar basu san mugun halin da hafsat ke dashi ba, shi yasanya cikin ruwan sanyi mahaifiyar tata ta sallame su, limamin masallacin unguwar su wanda aminin mahaifin su Hafsat dinne kafin rasuwar sa, maman su ta sheda masa yadda ake ta kuma ce tanaso ya aurar da hafsat din sadaqa ga duk meson yin aure, dake dama mahafin nasu irin buzayen Niger din nanne babu wanda yasan dangin sa, Hakan kuwa akayi ranar jumu’ah bayan anyi sallah an idar limamin ya sanar inda meson yin aure, Akwai budurwa da za’a bada ita sadaqah ga duk wanda ke son aure ko wanda zai ‘kara aure. Wani mutumi wanda ahaife yayi jika da ita yace yaji ya gani zai aureta ata hud’u, Alokacin aka ‘daura musu aure, abun dai sai sam barka kawai, kwanan hafsat uku a asibiti sakamakon suman datai tayi lokacin da zancen auren yazo kunnrn ta, haka dai aka mika ta dakin ta na sunnah, d’aki d’aya jal ba parlor kuma bandaki d’aya ne agidan, tayi NADAMA da dana sanin abunda ta shuka a baya, domin tasan yanxun shita girbe, Toh fa dama haka abun yake ko bakaga ishara a dunia ba Toh wata shari’ar sai a LAHIRA..._

_Anan zan dasa ayar bangaren su Dijama da angon ta Lado, hafsat da angonta Alhaji Falau, sai Malam Namuduka da aljanar amaryar sa sharhabilaiye, Allah ya bada zaman lapia mai ‘dorewa💃🏿_

_Toh masu karatu yanzu lokaci yayi da zamu tsunduma cikin ainihin labarin, #Chronicles of love triangle, legacy of unrequited love, woop woop🔥 turn up guys💃🏿💃🏿💃🏿 an fara😹_
*Wannan littafin na kuɗine, kiji/kaji/kuji tsoron ALLAH karki/karka/karku shiga haƙin wanda ya saya, kema idan kina buƙata ki nema wannan Numbers ɗin._👇🏻*

*08030811300*
*07067124863*

_*KAI MIN HALACCI......!💕_*


_*NA_*


_*_MISS XOXO🧕🏼_*_


_*44C_*

Bata kulashi ba bare tasan yazo wajan haka ta taka ta wuce lokacin Mu'azzam ya juya motarsa yabar wajan shima Shamsuddeen ya taka mata baya. Ma'aikatan wajan sai gaidashi suke yana amsa musu cike da farin ciki kafin yabi hanyar office d'in Yazeed dan suyi magana. Sam bai san Aliya can ta shiga ba, taje ne tayi masa godiya domin har can bunkure yaje yayi mata gaisuwa shi yasa tazo yi masa godiya.

“Karki damu Aliya, yanzu abinda nake so dake muje can caffe kiyi aikin ki a can idan yaso gobe sai kici gaba da zama a office/site d'inki.”

“Toh sir na gode duk yadda kace ai haka zanyi”

Murmushi Yazeed yayi tare da mik'ewa dan yi mata rakiya, suna fita suka ga Shamsuddeen hannusa rik'e da waya yana dannawa. Kallan kallo suka yi su duka ukun kowanne da abinda yake sakawa cikin zuciyarsa. Hannu Yazeed ya mik'awa Shamsuddeen suka gaisa kafin yace.

“Gurinka nazo.”

“Okay zanzo office d'inka bari naje cafe na dawo.”

“Malam yanzu zamu yi.”

“Okay muje ciki toh, Aliya jira ni na fito.”

Bata damu ba domin tasa saboda ita yaki yadda sai zuwa anjima suyi maganar, taje ta samu kujera ta zauna tare da zaro wayarta tana kallon hotunan su Baffa da tayi musu lokacin da zata taho. A cikin office d'in Yazeed kuwa duk tsayawa suka yi babu mai cewa komai har sai da shi kansa Yazeed d'in yace.

“Dude idan baka da abin cewa na tafi haba, kace zamu yi magana kuma kazo kayi shiru inada abinyi fa.”

“Eh da yake aikinta yafi nawa dole kace haka, malam zuwa nayi in gaya maka gaskiya ina buk'atar motar hawa.”

Dariya Yazeed ya kyalkyale da ita har yana rik'e ciki kafin ya kalli Shamsuddeen wanda yake faman yatsina fuska yace.

“Dude kasan mai kake fad'a kuwa? Cewa fa kayi mota, naga ko jiya sai da nayi maka maganar ka siya amman kace ba yanzu ba, toh yanzu kuma me yasa ka canza shawara?”

“Nidai kawai nace maka ina son mota ka bani shawara wacce zan siya?”

Yazeed yayi shiru na d'an wani lokaci kafin yace.

“Toh bari na duba maka dan kuwa kasan akwai masu zafi wallahi Dude sai dai idan baka yi niyar siya ba.”

Murmushi Shamsuddeen yayi yasan idan Yazeed yasan dalilin da yasa zai sai motar nan to babu wata shawara da zai bashi dan haka yabar dalilinsa a cikin zuciyarsa ko zai gaya masa toh ba dai yanzu ba sai ya mallaketa tukunna saboda kar yayi masa wulak'anci. Tare suka fito suna dariya Shamsuddeen ya gallawa Aliya harara wace d'agowarta kenan ta kauda kai tare da tab'a baki, har yayi gaba sai kuma ya waigo cikin had'e fuska yace da ita.

“KE ni kike harara?”

Aliya ta juya bayan ta dan a tunanin ta da wata yake, sai kuma taga babu kowa sannan ne ta tsargu tasan tabbas da ita yake. Yaushe ta hararesa banda tsabar sharri da kuma tsanarta da yayi?amman ganin akwai mutane sai ta rissinar da kai tare da sanyayaya murya tace masa.

“Kayi hakuri wallahi ba da kai nake ba.”

Tayi maganar tana maida wayarta cikin jakarta ba tare da ta kuma bin ta kansa ba tabi bayan Yazeed, shima kwafa yayi har zai wuce taji yace.

“Zo nan.”

“Ni?”

“Yeah”

Ya fad'a tare da wucewa ya danna lifta, Yazeed dake tsaye ya bishi da kallon k'arfin hali ganin yana neman yi masa takama akan Aliyar. Office ya koma yana dariya cikin ransa yana cewa 'dude nasan ba zaka bar yarinyar nan ta zauna a caffe ba, d'an rainin hankali kilama soyayya yake son ya sabunta ya rasa yadda zai yi.' Ya zauna yanaci gaba da aikinsa, su kuma sai da ya fara barinta ta shiga sannan shima ya shiga lift d'in ta rufe, Aliya ta koma can karshe ta tsaya sai ji tayi ya juyo yana kallonta cikin kare mata kallo. Sanye take cikin doguwar riga ta shadda orange ta yafa mayafi green tayi kyau sosai kawai taji yace mata.

“Ya hakuri?” Ta d'ago kai suka had'a ido tace dashi.

“Hakurin meh?”

“Na inda kikaje.”

Banza tayi dashi dan ta d'auki alkawarin ba zata tab'a amsa masa gaisuwar ba koda zai yi mata. Hannu yasa ya tsaida liftar ya tattaka tare da zuwa kusa da ita Aliya ta ware ido tana kallansa, jira kawai take taga iya gudun ruwansa amman taga k'ok'arin shiga jikinta yake dan haka da sauri tayi masa magana.

“Meye haka ne?”

“Abinda yayi haka shine yayi, bakya jin ina miki magana zaki min banza?”

Aliya ta tsuke fuska tare da d'auke kai jira kawai take taji ya tab'a ta dan idan bai yi wasa ba sai ta kwad'a masa mari. Shima yasa hannayesa duka biyu ya dafe glass din data jingina dashi ya sanya ta a tsakiya numfashinsu yana had'uwa dana juna taji yana cewa.

“Tunda ba zaki amsa ba bari na tambayeki aikin dana saki, shin Fa'iza tana sona? Wane irin so take min? A ganinki gwaggo Talatuwa zata barmu muyi aure? Dan gaskiya ina son na fara zuwa tad'i wajanta kar naje gwaggo Talatuwa tace bata yafe min lekaki da nayi ba.”

Ganin yadda take rintsa ido ne yasa shi d'an matsawa daga wajan ta yasan ba zata iya yin magana ba a yadda ya takureta, aikuwa yana matsawa yaji amsa daga bakinta tace.

“Gwaggo bata yafe ba dan haka babu wata da zata baka ka aura.”

“Damn it, dan Allah karki min wannan bakin dan bazan iya hakura da Fa'iza ba, bari na bude jikina kema ki rama abinda nayi miki dan gaskiya rabuwa da Fa'iza tamkar rabuwa ne da numfashi na.”

Yayi maganar yana k'ok'arin cire rigar jikinsa, hakan yasa Aliya ware ido tare da toshe baki kirjinta na bugawa tsabar tashin hankali ta kasa magana, sai gani tayi ya d'an tsaya tare da leko da fuskarsa ta cikin wuyan rigar domin ya fara cirewa dan ana ganin farar vest d'in jikinsa yace mata.

“But d'an kad'an zaki kalla domin lokacin da tsautsayi ya kaini ganinki ke kina kwaila kinga ni kuma yanzu i'm matured enough/grown up, so zaki iya ganin abinda zai tayar miki da hankali.”

Yana gama fad'a ya zare rigar yana k'ok'arin zuge tazuge, aikuwa Aliya tayi kasa tare da cusa fuskarta cikin cinyoyinta tana sakin ihu mai had'e da kuka. Cikin sauri ya maida rigarsa tare da danna lift din taci gaba da tafiya sai kuwa gasu a cikin office, a hankali taji yayi magana cewar.

“Ke malama tashi daga nan.”

“Wallahi sai ka bud'e min na fita ni ba 'yar iska bace, wayyo Allah na shiga uku Nawal kin kawo ni cikin masifa.”

Ganin kamar ba tasan sunzo ba sai faman ihu take yi shine yasa shi sanya hannunsa ya janyo nata, gabaki d'aya ta rude a tunaninta bashi da komai a jikinsa hakan yasa idanunta sukaki bud'ewa tana ta faman dak'irewa tana tsalle tana ihu ya fincikota daga cikin lift d'in ya tura ta office, karar a.c da taji ne yasa ta d'an bud'e ido mai cike da hawaye sai kawai ta ganta a center d'in dake tsakanin k'ofar office d'insa da gurin da take zama.

“Ki rufe min baki.”

Tayi saurin juyawa ta kallesa sai taga ashe yana cikin kayansa hakan yasa ta fara k'ok'arin had'iye kukan nata, tana nan kuma a tsaye a inda take har sai da ya kuma yi mata magana.

“Na gaya miki ina son Fa'iza ina son Fa'iza me yasa bazaki temaka min na samu Fa'iza ba?”

Itama cikin fushi tace dashi.

“Mene yasa dole sai nice zanje na karb'o maka soyayya da auran Fa'iza? Ko nice uwar Fa'iza ne? Nice mai bada auran Fa'iza da zaka takura min sai naje na samo maka zuciyar ta, shin duk wayar da kuke yi ka kasa cewa kana sonta ko ita ta kasa furta maka sai nice zanje na fad'a mata? Wallahi zan ajiye siwes d'in nan gara nayi deferring semester din idan yaso wata year din na sake a wani gurin, haba dan Allah mena tsarke maka ne, abinda ya faru a baya ya riga ya wuce so kowa yayi rayuwarsa mana haba.”

Tabbas gaskiya take fad'a domin ba itace zata hanashi ko bashi auran Fa'iza ba, amman menene yasa yake son dole sai ta shiga cikin lamarin? Yana ji har a cikin ranshi baya kyauta mata amman ya kan ji dad'i duk lokacin da yaga ya bata mata rai. Shigowa sabon sakataransa shine yasa shi wucewa office d'insa yana jan numfashi, mai makon ta bishi ita kuma sai ta koma ta shiga lift ta nufi office d'in Yazeed, har k'asa ta duka tana neman alfarmar ya maida ita cafe a yau ba sai gobe ba, Yazeed najin haka yasan akwai matsala hakan yasa ya kuma mik'ewa suka nufi cafe ya yiwa mutanan wajan bayaninta sannan ya bata duk wasu abubuwan da zata yi ya koma office yana mamakin yadda Shamsuddeen yake jin kansa akan yarinyar nan.

Tun daga lokacin basu sake had'uwa da juna ba, takan rigashi zuwa ko kuma ya riga ta kuma kowa da yazo gurinsa yake tafiya, a time d'in ne kuma ya samu damar fara zazzafar soyayya tsakaninsa da Fa'iza hakan kuma baya damun Aliya domin taga nuna damuwa shine yake sanyawa ayi mata duk abinda akaga dama. Itama kuma alakarta da Mu'azzam birnuwa tayi karfi sosai kusan yanzu Sahal ne kawai a cikin matsalar soyayya wadda take bashi wahala, gashi wani lokacin yakan riski Shamsuddeen yana waya da Fa'iza duk lokacin da ya ziyarci garin Abuja, kuma hakan yana barazanar lalata masa zuciya.

Yau kam shine ranar farko da Shamsuddeen zaije gidan Baba Suleiman dan mik'a gaisuwa a wajan su Umma, Aliya na kwance tana waya da Mu'azzam taga Fa'iza sai shirye-shirye take yi, girki kala-kala kuma bata sanar mata da kona menene ba hakama ita bata tambaya ba kasan cewar yanzu ba wani sakarwa juna jiki suke yi ba. Ana yin sallar la'asar Fa'iza akaje aka cancad'o wanka sannan aka zauna ana bawa kwalliya hakkinta, tana ganinta ta turare kaya wasu riga da skirt na less color d'in shi dark coffee da ratsin siraran milk d'in zare yayi masifar yin kyau, tana cikin daurin d'ankwali ne taji wayarta na ringing tayi murmushi tare da

Please Login or Register in order to submit comment